JIRWAYE CHAPTER 2
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tuqi yike suna ta hira, Fatima tana ta basa labarin childhood days dinta, shikuma yana ta sauraron ta yana dariya.+
“Habibi”. Ta kira sa kamar yadda ta saba.
“Yes dear”.
“Dan Allah mu shiga gun Hajjo kaji”. Juyowa yayi ya Kalle ta.
“Wai ke ya kike son gara ni ne haka”. Ya fadi ransa a dan bace.
“Toh naga muna kusa da layin su ne”. Ta fadi “Amma ba komi, mu wuce kawai” ta qara fadi. Shikuma yayi shuru bai ce mata komi ba. Can kawai yana tana fadi cikin wata iron murya da ta sosa mai ran sa
“Uwata ma yanzu hana ni ganin ta ake, in ban ganta ba yau waya san randa zan ganta”. Har da share dan kwallan ta duk sai yaji ba dadi, kamar bai mata adalci ba. Juyo kan motar yayi kawai ya shiga hanyar da zata sa da su da layin gidan iyayen Fatima.
Tafe suke ba me cewa kowa komi, sai radio da ke kunne. Suna isa wani makeken gida ya yi honking, ba tare da bata lokaci ba me gadi ya buda musu gate suka shiga. Da yayi parking sai ya fito ya buda mata qofa suka fara tafia hannayen ta a cikin nasa kamar yadda suka saba. Shiga suka yi cikin gida Hajjo ta tare su da fara’a. Suna zama masu aiki suka shigo musu da refreshments.
“Ai ba ma dadewa zamuyi ba, mun zo wuce wa ne nace mu shigo”. Fatima ta fadi wa Hajjo tana mata murmushi.
“Auu toh, Alhajin na nan ai, ku shiga ku gaisa”. Hajjo ta fadi cikin fara’a. Hajjo kamar yadda yaran ta ke kiranta ita ce mahaifiyar Fatima. Hajia Hajara ta kasance mace me kirki da haquri matuka, bata da hayaniya gashi tana daukar kowa tamkar nata. Bata kyamatar talakawa kamar yadda masu kudi ke yi, ita kowa nata ne. Fatima ita ce diyar ta ta uku, akwai maza biyu gabanta; ya Fu’ad wanda soja ne, sai kuma ya Abdul, shikuma engineer ne. A bayan ta kuma akwai maza biyu Muhammad da Mahmoud. Kasancewar ta the only girl ya sa aka fi ji da ita, fiye ma da yadda ake ji sa Auta Mahmoud.
A tsaitsaye suka gaisa da Alhaji sannan suka musu sallama suka wuce shopping mall domin siyawa Aryaman birthday present. Aryaman nephew din Fatima ne, yaron wan ta ya Fu’ad. Suna shiga mota ta Kalle sa ta saki wata murmushi wadda ya fito da dimples dinta.
“Thanks habibi, you always make my wishes your command”.
“The things we do for love”. Ya fada shima yana mata murmushi “yanzu dai kinga Hajjo dinki koh, hankalin ki ya kwanta”. Daga kai ta mai alaman eh hankalin ta ya kwanta.
Shopping mall din gidan bene ne me dauke da about 10 storeys. A nan ma suka shiga arguement.
“Gaskia elevator zamu shiga”.
“Haba dan Allah, kai wai baka ji abunda doctor yace mun bane rannan. Na dinga exercise sabo da cikin ya girma”.
“Toh ba muna strolling ba tare, gaskia Fatima I can’t take the stairs”.
“Shikenan, je ka shiga lift, ni zan taka stairs, mu hadu a 7th floor”. Ta fadi cikin bacin rai.
‘Duk na qosa ta haihu na huta da rigima’ ya fadi a zuciyar sa amma a fili sai ya jawo ta yana rarrashin ta.
“Aah haba habibty. Allah huci zuciyar ki. Muje mu yu exercise”. Ya hakura ya bi ta suka hau stairs ba wai dun ran sa ya so ba. A haka dai ya ta bin ta. Tun suna ma Aryaman shopping har Fatima ta koma side din cosmetics and body care products ta fara nata siye siyan shikuma yana gefen ta yana taya ta zabe.
“Ji mun wannan turaren, do you like the scent?” Ta tambaye sa.
“Why are you asking me if I like it, ba ke zaki sa ba. It’s nice tho”. Ya ansa ta yana sunsuna hannun sa inda ta fesa mai turaren yaji.
“I’m doing it all for you”. Ta fadi mai cikin murmushi.
Sai can yamma suka gama shopping dinsu. Har sun kama hanyar wuce wa ya hango wani set na sleep suits na babies sun mai kyau sosai yace mata suje su siya.
“We’re taking the pink one” ya fadi wa shop attendant din.
“No habibi, we’re buying the blue one. I can’t have my little Fadeel looking like a barbie doll”. Dariya kawai ya saki sannan yace a kawo masu blue ones din. Ya biya kudi suka wuce duk shi ke riqe da kayan da suka siya.
Kamar yadda suka zo, da zasu koma ma stairs din suka bi. Suna tafia suna hirar su, Fatima nata dariya. Kawai isar su 4th floor sun kai tsakiyar stairs din Fatima ta turgude sai rolling kawai yaga tana ta yi har ta kai qasa ta bugi cikin ta da wani bango. A gigice ya wurgar da jakkunan shopping inda ya riqe ya nufi inda take, jini kawai yike gani na fito wa daga goshin ta, ga kuma jini duk ya bata rigarta yana bi mata qafafu. Mutane an dan taru amma ba wanda ya nufe inda suke dana niyyar kai musu agaji. Idanu cike da hawaye yike kallon ta duk ya rasa yadda zai yi, ita kuma sai kuka take tana salati.
“Na shiga uku, zan mutu” take ta fadi cikin kuka.
“Sai ta mutu zaku taimaka min” ya juya ya fadi cikin ihu. Mutane ne a kansu sun fi a kirga amma ba ko mutum daya da ya nufo su da niyyar taimako.
Daukar ta yayi, jini duk yana bin jikinta yayi hanzarin isa exit din mall dun zuwa inda yayi parking motar sa. Gudu yike ta yi a mota yana mata sannu, ita kuma sai kuka take ta yi tana fadin duk adduar da ta zo mata baki. A hanya muka suka izza hold up ya hadu. Haka nan ba yadda zai yi dole ya jira for about 30 minutes har suka sama Wucewa. Suna isa Asibiti be jira an kawo stretcher ba ya daga ta a jikinsa ya ruga da ita ciki. Sanin ko shi waye da matsayin sa a qasar ya sa ba a tsaya wani formalities ba aka wuce da ita operation theatre. Can sai ga doctor ya fito ya kira sunansa.
“Mr Abdulmalik” ya kira sa.
“Yes yes doctor, how is she?”.
“In a critical situation, i’m sorry to say but gaskia operation inda zaa yi akwai chances in rasa mutum daya koh ita koh baby din”. A lokacin wani bugu zuciyar Abdulmalik yayi. Be taba tunanin akwai randa zai shiga tsaka me wuya irin wanda yike ciki ba a wannan lokacin. Dole ya zaba tsakanin matar sa da yike so kamar ran ransa ya fita koh kuma baby dinsa da yike ta zumudin randa zai koh zata iso duniya.
“Save the mother. Do whatever you want to do but you must save my wife at all cost” ya kalli doctor din da idanunsa wanda tuni sun koma jazur. Doctor din be ce komi ba ya koma operation theatre. Sai da aka yi kamar awa biyu tukun Abdulmalik yaga wutar theatre din ya sanja daga ja zuwa green, alaman an gama operation din.
Wata nurse ce ta fito bayan about 15 minutes da sanjawan wutan. Riqe take da dan karamin baby an lullube a wani blue shawl.
“Congratulations sir, it’s a boy”. Ta fadi gami da nuna mai baby din “The baby is about 8 weeks premature so we have to incubate him”. Ta fadi sannan ta wuce da baby din zuwa dakin da zaa sa shi a kwalba. Shi Abdulmalik koh Tsayawa be ma yi ba duba yaron dun shi babban abun da ke gaban sa a wannan lokacin shine sanin halin da zahrar sa ke ciki.
“Khalifa Abdulmalik Al-Haydar”. Doctor ya fito ya kirasa.
“Yes yes, how is she doctor, zan iya ganin ta?”.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Wayyo ni Hansatu diyar Mairo. Zahra ta ban tausayi sosai wallahi😢😢😢. Yaaaaaayyyyy who is eager to meet Baby Fadeel😍😍😍. Ku biyo ni a next chapter ku sha labari.Kallonsa doctor din yayi cike da tausayi, ya matso kusa dashi ya dafa mai baya. Kasancewar sa family doctor dun Al-Haydar family yasa shi da Abdulmalik suka shaqu.
“Khalifa, you’re a Muslim and I’m sure kasan qaddara. Kasan kuma ladan mutum wanda ya rungumi qadr; me kyau koh mara kyau…..”. Be gama statement dinsa ba Khalifa ya katse sa.
“Fatima fa? Fatima na fa? I want to see her, this minute!”. Ya bangaje doctor din ya ruga dakin da take da gudu.
“Time of death………. 9:21pm”. Kalaman da suka fara dukar kunnunwansa kenan da shigar sa dakin. Dago idanunsa yayi wanda sun dade da zama jazur, ya kalli dayan doctor inda ke dakin da wata nurse a gefen sa ta na rubutu a notepad. Ya kuma juya ya kalli zahra sa wadda take kwance, idanunta a rufe kamar me barci. Ji yayi an riqo sa amma ya sa hannu ya hankade wanda ya riqe sa, be ma damu da ya juya yaga ko wanene ba kawai ya nufi gadon da zahra sa ke kwance.
“Habibty….. ki tashi barci. I’m sorry you had to pass through all these pain just to have my baby. Na qosa na ganshi, naga da wa yayi kama amma in ba tare da ke ba bazan iya zuwa ganinsa ba. Dan Allah tashi muje muga dan mu, kinji zahra na”. Ya gama magana yana jiran yaga ta buda idanunta da yike matukar son kallon su a ko da yaushe amma yaji shuru.
“Hushi kike dani har yanzu? I’m sorry habibty, please wake up”. Wannan karan ya jawo hannun ta ya riqe a cikin nasa yana wasa da ýan siraran ýatsun ta.
“Sir you have to take it easy on yourself”. Wata nurse ta matso kusa dashi tana fadi amma sai tsawa kawai ya mata, ta tashi ta basa gu.
“Ki daina sa mun baki, i’m talking to my wife. Get out!”.
“Zahra dan Allah…….”. Be gama maganan ba wasu maza biyu suka shigo suna jawo sa waje shikuma yana kokarin fisgewa. Yana kallo wasu nurses suka kawo auduga suka sa ma Fatima a hanci, aka hada Jikin ta yadda ake wa gawa. Subhanallah! Ina zai mance, 7 months ago a idanunsa haka aka wa mahaifin sa. Wani irin kuka ya saki me shiga zuciya, ya zuba gwiwa a qasa yana kuka yadda ka san yaro karami. Duk mutanen da ke cikin dakin tausaya masa suke. Kowa ya kasa ce mai komi dan a wannan lokacin shi daya ya san yadda yike ji da kuma Allah wanda ya halicce sa.
“Fatima why….. why did you leave me. I told the doctor to save you for me. Why! Ya Allah sai da na fara son ki Fatima, sai da zuciya ta ta saba da ke, sai da idanuna suka zama addicted to seeing your face Fatima. What will I tell our son, what will I tell your Fadeel? Dan Allah Fatima ki tashi”. Yayi ta kuka har kalaman sa suka sa wasu daga cikin wanda suke gun hawaye. Hakika yaji wannan rashin da aka mai.
Da kyar aka samu aka ja sa out of the room. Shikuma doctor already ya kira family dinsa ya sanar dasu mummunar abunda ya auku. Can yana zaune shuru a corridor in dakin da gawan Fatima yike sai ga ýan uwansa da na Fatima sun shigo. Hajjo na hada ido dashi ta farke da kuka.
“Fatima ashe ban kwana kika zo mun yau. Shiyasa kika ta hugging dina, kina ta kallona. Harda mun addua Fati na. Wayyo ni”. Tai ta kukan ta ana bata haquri. Ita kanta mahaifiyar sa kuka take, sai dai amma tana da karfin hali, ita tayi ta fama bawa dan nata da surukarsa haquri. A nan dai close family members suka taru, masu kuka suna yi, masu suma nayi duk dai gu ya kidime. Shi dai Abdulmalik baya cikin hayyacin sa dan duk a gigice yike. Yaya Fu’ad ne yayi ta cika formalities din Asibiti kan aka gama suka tafi da gawar domin ayi mata sutura a kai ta makwancinta. A lokacin da zaa tafi ne ma aka tuna da dan jinjirin data bari wanda baza su iya tafi dashi gida ba. A nan dai aka cewa Hajja Ganah ta zauna da baby din kan a san yadda zaa yi. Ita Hajja ganah kanwa ce ga mahaifiyar Fatima.
Cikin kankanin lokaci duk an sanar da ýan uwa mummunar abunda ya samu Abdulmalik. Ana daukar gawar daga Asibiti gidanta aka kaita. Kasancewar da dare ta rasu, sai da aka jira wayewar garin Allah tukun aka yi janaizar ta. Har a wannan lokacin Abdulmalik baya cikin hayyacin sa, duk ya sanja, ya zama wani iri da shi, mutuwar ta taba sa ba kadan ba. Da kyar aka iya lallaba sa yaje yaga dan sa yayi mai khutbah da Tahneek. A ranar kam ya ci kuka, duk wanda ke gun ma sai da suka sha kuka saboda ya basu tausayi matuka.
“Da na bansan me zan ce maka ba, ban san da wani ido zan Kalle ka ba a ranar da zan tsinci kaina da baka wannan mummunar labari, cewa mahaifiyar a ranar da ta haife ka ta rasa ran ta. Ban sa ta ina zan fara ba, ban san ta ya zan tarbiyyantar da kai ba without your mother by my side. I don’t know what the future holds cause right now I can’t even see the future, I don’t know what it has in store for us. I’m sorry I could do little or nothing at all to save your mother, I’m sorry you’ll have to grow up without a mother, i’m sorry…. For everything son. Forgive your father for he is nothing but a mere mortal. All I can promise you is that I’ll always be there by your side son, it’ll always be us, you always nd is against the world. Even though it would not make up for your loss, I promise to give you all the joy and happiness in the world”. Kawai bai san sanda kuka ya kufce masa ba, tuna lokacin da yike gardama shi da Fatima takan sex din baby dinsu kawai yike.
“You were right zahra, we now have a little boy, our son. Your Fadeel. Allah ya raya mun kai ďa na muhammad Fadeel”. Ya tofa mai addua yayi hanzarin fita daga dakin idanu cike da hawaye. Bayan ýan watanni da rasuwar Fatima, anso Abdulmalik ya auri cousin sister dinta, Salma wadda ita da zahra tare suka tashi. Kasancewar Fatima the only girl ya sa Hajjo ta dauko Salma tun tana ýar yarinya ta tarbiyyantar dasu tare. Aka yi akayi ya aure Salma dun ta kula da Fadeel amma yaqi. In ba zahra sa ba, be ga ýa macen da zai taba zama da ita ba a doran qasa.
“It’s either my zahra or no woman at all”. Ya fadi.
Bayan sallamar Fadeel daga hospital aka sama mai nanny ya fara zama da family din Abdulmalik, wato mahaifiyar saboda Abdulmalik ya kasance shi daya tal aka haifa kuma ga arziki da Allah ya azurta iyayen sa da shi kamar me. Duk duniya an san khalif airlines and group of companies. Babban business empire ne wanda ya sama karbuwa da kuma support from different countries round the globe. Kan rasuwar Mohammed Mumtaz Al-Haydar, ya kasance mutum ne me fada a ji, yana da influence matuka a siyasar qasa da kuma business world ma in general. Bayan mutuwar sa kuma shi ne dan sa Khalifa Abdulmalik Al-Haydar ya gaje sa.
Bayan ýan watanni Hajjo tazo ta roqa dan Allah a ba ta jikan nata ta riqe, ko ganinsa zai dinga debe mata kewar diyar ta.
“In ya so duk randa Khalifa ya sama mata yayi aure sai na dawo masa da dan sa”. Amincin da ke tsakanin both families ya sa Khalifa ya yarda ba tare da bata lokaci ba.
Back to present…….
“Khalifa!” Yaji an kira sunansa da qarfi “Tunanin me kake yi haka ne”. Dago ido yayi ya kalli me magana.
“Nace ka dinga kirana Abdulmalik if we are in an office environment. At home you can call me Khalifa all you want”.
“Yes boss”. Ya fadi yana salute. “Ya kake? Done with the meeting?” Ya tambaya, Abdulmalik be ce mai komi ba ya gyada kai alamar ehhh.
“Ka zauna kana ta tunanin ta koh?”.
“Let’s go to the park”. Ya fadi ba tare da ya ansa tambayar da aka masa ba.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Toh jama’a……. who is confused here, hands up in the air dun ni kai na a rude nike. Ga Khalifatullah ga Khalifa Abdulmalik. Toh daya dai kamar me dan rufin asiri haka daya kuma me shegen kudi. Ikon Allah! And they’re both in Australia, gashi Laylah na neman daya, shikuma daya ya hadu da Laylah. Me ke shirin faruwa ne? Wane zuciyar Laylah zata so? Me kudi koh me rufin asiri? Wanne a cikin su zai yi accepting Laylah for the person she is. Allah kuma zai sa da ta da Khalifa Abdulmalik Al-Haydar? Domin burinta kenan for years, ta gansa, ta mai tallar jikinta. Hmmmm na gaji da surutu, kawai ku biyo ni a chapter na gaba muga ya labari zai cigaba. Wa ke son ya ji yadda Laylah da senator suka karashe? Ku biyo ni. Daukar tuxedo dinsa yayi ya mayar jikinsa sannan ya fito suka wuce. Yana fitowa bodyguards dinsa suka taho suna binsa a baya. Suna fita harabar building din daya daga cikin bodyguards din yayi hanzarin yin gaba domin buda wa Abdulmalik kofar mota. Wata Shegiyar mota aka buda mai wanda Tsayawa describing dinsa ma bata lokaci ne, kai da ka gan motar nan ka san kudi ne suke magana, iya haduwa motar ya hadu. Yana shiga abokin tafiyar sa ma ya shiga tukun bodyguard daya ya shiga motar dayan kuma ya shiga dayan motar na baya, motar escorts.+
“Yawwa Tariq called me kuna meeting, yace Al-Mubaraq couldn’t attend the meeting saboda abokin sa senator Junaidu na gari so they’ve been together”.
“Meyasa Mamu ke haka? Ba sai ya kira ya fadi ba and moreover in suka koma Nigeria ai sai su cigaba da abokantansu, business ya kawo mu Australia”. Ya fadi cikin bacin rai wanda Fuskar sa ke dauke da Kullum. Ba karamin abu bane ke sa Abdulmalik dariya.
Al-Mubaraq shine overall director din khalif airlines and group of companies kasancewar sa kawu a gun Abdulmalik. Shine general overseer na company din kuma shi ke tsayawa matsayin CEO a duk lokacin da ya kamata saboda Abdulmalik mutum ne mara son fame da popularity. Ko a cikin ma’aikatan sa ba duka suka san ko wanene khalifa Al-Haydar ba, sai dai su ji sunansa, manyan ma’aikatan ne kawai wanda yike haduwa dasu a meeting every six months suka san asalin shi wanene amma duk sauran Al-Mubaraq suka sani, sai dai su ji sunan Khalifa dan koh a TV ne baa taba nuna Fuskar sa sai dai ka ga Al-Mubaraq wanda bayan Abdulmalik, yafi kowa matsayi a khalif airlines and group of companies. Daga Al-Mubaraq kuma mutum na uku me babban matsayin a kampanin shine Nawfal muhammad Fadoul.
Suna isa park din yace wa escorts dinsa su bar masu mota daya su wuce.
“But sir”.
“It’s okay, I’ll be good”. Ya fadi masu “Tell Tariq to meet me here in the next 30 minutes” ya umurce su sannan suka wuce suka shiga ciki.
Yana zaune a gefe daya yana ta kallon yara na wasa yana ta dariya. Dauko camera yayi yata daukar hoto.
“I’ll show all these pictures to Fadeel when I get back to Nigeria”. Ya fadi a ransa. Tunanin dan sa kawai ya sa shi jin wani irin sanyi a ransa. Kawai dago kai da zai yi idanunsa ya gamu da wata ýar budurwa a can wani seat not too far from him a zaune. Tabbas! Ya san ta.
“Karbi ka riqe mun”. Ya cire tuxedo dinsa da tie ya bar blue shirt din da ke ciki kawai.
“Mene haka”.
“Kai dai karbi”. Ya fadi tare da je fa kayan kan jikinsa. Qasa yayi da kansa yaga palms ne qafar abokin nasa sai ya saki murmushi. “Nawfal give me your shoes and take mine”.
“Kai malam! Lafia kuwa? Dazun nan na sayi shoes dinnan saboda wanda na sa suna ci mun qafa”.
“Just take mine yar, zasu ma daidai”. Nawfal kam kai a daure ya cire takalmansa ya bawa khalifa.
“Khalifa wai me ne haka”.
“Kai sarkin kauyenku! Abdulmalik nace ma. Yanzu ya ka ganni?”. Ta tambaya “tsaya ka gani”. Cire agogon da ke hannunsa yayi, agogo ne me matukar tsada, sannan ya cire tuck in dinsa sannan ya kuma tambayar Nawfal.
“You look like a simple person, someone from a middle class background”.6
“Masha Allah”. Jirani. Har ya qarasa inda Laylah take zaune ya zauna bata san anyi haka ba. Daga gani kasan ta zurfafa a tunani har ýan hawaye suka fara saukowa daga idanunta. Kasancewar sa mutum me tsananin tausayi, most especially ga mata, ya tsani yaga ýa mace ta shiga wani hali, saboda wannan dalilin ne khalifa ya zura hannu cikin aljihun sa ya ciro hankie wanda ya daga hannunta ya sa mata a ciki. Tun da ya Kalle ta so daya ya cire ido a kanta. Duk sai ya qura idanunsa a kan wasu yara ýan mata biyu wanda suke ta wasa abun su.
“You!”. Ya ji an fadi da karfi har sai da dodon kunnensa suka nemi su toshe.
“Na tsani naga mutane suna kuka, barin ma ýar budurwa….. kyakyawa”. Sai da ya dan hanzarta tukun ya fadi kyakyawa.
‘Subhanallah! I didn’t check her out, did I? ‘Ya fadi a zuciya when realisation dawned on him cewa he just admitted to Laylah being pretty.
“Whenever distressed, remember Allah and say Alhamdulillah. You’ll feel okay” ya bata shawara sannan ya miqe ba tare da ya kuma kallon ta ba. Sai dai a zuciyar sa yana jin wani abu, abunda yayi shekara da shekaru be ji ba. Ji yike kamar wani force of attraction yana pulling dinsa towards this strange lady, ji yike yana so ya kuma ganin ta. Kawai sai ya tuna ai akwai ipad dinta a gunsa.
“Can I get your address?” Ya juya ya tambaye ta. Sai da taji dalilin son address dinta tukun ta basa. Shikuma Wucewa yayi ransa cike da tunani iri iri. Har ya isa inda Nawfal ke jiransa tunani yike, sai da Nawfal ya kwala mai kira tukun.
Sun shiga mota suna tafia ya fara tambayar Nawfal koh yasan Jk guesthouse.
“Ehhh, guest house din abokin Mamu ne ai, senator Junaidu. Nan yike sauka in yazo Australia”.
“Hmm” kawai yace yana dan shafar sajen sa kamar wanda ke nazari. Hakika bayan zahra baya ganin zai iya taba son wata ýa mace amma kuma ya rasa meyasa tunanin wannan yarinyar ke ta addabar sa, duk yaji yana so ya san koh ita wacece.
“Shi senator yana da wata diyar koh niece a country dinnan?”.
“Gaskia I don’t think so, but I’ll find out”.
“Okay do that” ya fadi “and please Nawfal shopping nike so ka mun, kaya masu araha. Banda masu tsada”. Ya fadi.
“Wai kai mai motive dinka na boye identity dinka, meyasa baka son mutane su san ko waye kai, gashi dai kana taimako, mutane suna son su nuna godiyar su gare ka amma ba dama”.
“Ni duk abunda nike yi dun Allah nike, and I’m going undercover ne to know who my friends are and who my enemies are. Very soon the world will come to see the true face of khalifa Al-Haydar” ya fadi. Sun dade ba wanda yace wa kowa komi sai can Jim kadan Nawfal yayi breaking silence din.
“Chuchu wanted to talk to you in the morning amma nace baka kusa”.
“Shine baka fada mun ba tunda na dawo” ya fadi ransa a bace. Wayar sa ya dauko ya fara neman number din Hajjo.wani irin tsaki na takaici ta ja sannan ta cigaba da durza lallausar fatar ta da soson da ke hannun ta. Durza take kamar zata daye fatar ta amma bata daina ba har sai da taga fatar ta yi jazur kuma yana mata zafi. Kuka sosai ta fara saboda tsananin takaici da ya ishe ta, duk yadda tayi kokarin ta goge, ta sama kanta da rasa iya goge jirwayen dake manne da jikinta.
‘Stop fussing about it Laylah, the stain is here to stay’ wani zuciya ya fadi mata.
Kuka take yi irin me ratsa zuciya tana zaune a cikin jacuzzi bathtub wanda ke cike da ruwan kumfa. Kullum ta tashi da safe bayan biyan buqatar customer dinta sai taji zafi a cikin ran ta, sai taji ta tsani kanta, ta tsani rayuwar ta, ta tsani randa ta taka qafa zuwa birnin tarayya. Ta dade tana tunani kan ta qarasa wankar ta, tayi drying jikinta ta fito out of the bathroom. Senator Junaidu ya riga ya koma Nigeria bayan rubuta mata cheque just as he promised amma kuma ya umurce masu aikin gidan da suta mata hidima, duk abunda take so a mata har randa zata bar Australia.
Tana fitowa tayi salatul nawafil kan ta shirya ta sa wani sweatpant da kuma wani shirt wanda was very loose a jikinta. Kasancewar ranar Sunday yasa tayi deciding zata zauna indoors. Har ta dauko wani novel din Dan Brown ta fara karantawa sai daya daga cikin masu aikin gidan suka shigo kiranta.
“There’s someone here to see you ma’am”.
“A male or female?” Ta fara tambaya.
“It’s a male, he says he came to return your ipad”.
“Oh that arse hole, i’ll be out in a sec”. Sai da ta dan bata lokaci kan ta tashi ta dauki sheilah ta rufe kanta sannan ta fita. A gazebo ta izza shi yana zaune, da cup din orange juice a hannu.
“Don’t tell me you’re planning on spilling that on me”. Ta katse mai tunani.
“Wa alaikum Salam, good day to you too lady, i’m very much good thanks for asking and yes, I’m not spilling the juice on you”. ya fadi cikin sarcasm.
Dariya kawai tayi ‘such a sarcastic guy’ ta fadi a zuciya amma a fili sai cewa tayi “Pardon my manners. Salaam alaika”. Ansawa yayi ba tare da ya kalli face dinta ba, dan Jim kadan ya miqa mata ipad dinta ya tashi ya mata sallama.
“Fi waqt akhar”. Har ya miqe zai wuce ta dakatar dashi
“Wait please”. Sai da ta bari ya juyo tukun ta tambaya sunansa “I’m Laylah and you?”.
Sai da ya dan yi nazari kadan kan ya ansa ta “I’m Abdul…. Abdulmalik”.
“Nice meeting you Abdulmalik”.
“The feeling is mutual”. Ya fadi ya wuce ita kuma bata miqe ba daga inda take zaune. Zaune take tana kallonsa as figure dinsa yike ta retreating out of Jk guesthouse. Dogo ne, yana da body build me kyau, like very exceptional. Kana ganin sa ka san it took him lots of hard work to attain that kind of body.
‘Just like a Greek god…. hmmm’ Ta fadi a zuciyar ta. Gashi nan ba fari ba, Amma dai yana da dan haske. Ga saje me kyau da yike dashi a face dinsa da gashin sa wanda is ebony black and silky. Gashi dai kamar Nigerian, kamar kuma ba Nigerian ba. Babban abunda ya ma fi daure mata kai shine ga English accent dinsa is flawless, in yana yi kamar bature. Ga kuma skin dinsa da ka gani kaga hutu amma kuma yanayin shigar sa bata yi kama da na mai kudi ba kwata kwata kuma gashin nan ga dukkan alamu ba da mota yazo ba. Tashi tayi ta wuce cikin gidan amma sai dai tana ta jin wani abu a zuciyar ta wanda ta kasa ganewa gaba daya. Wannan stranger din, Abdulmalik, bata san meyasa ba amma taji tana so ta kuma haduwa dashi. He seemed like a nice person to her.
STORY CONTINUES BELOW
Tana shiga ciki ta cigaba da karatun novel dinta sai dai can after a while ta tuna wani abu. Caraf ta miqe ta dauko wayar ta ta shiga Google. *KHALIFAH AL-HAYDAR* abunda ta fara typing kenan. Page din na budawa tayi ta ganin abu iri; *khalifa Al-Haydar’s son*, *Al-Haydar family*, *Khalifa Al-Haydar late wife*, *The Khalif business empire*, *Mohammed Mumtaz Al-Haydar*. Da dai several other pages amma duk inda ta shiga bata sama hoton khalifa Al-Haydar ba.
“Crap!”. Ta fadi cikin takaici ta wurgar da wayan. Can kuma dai ta dauka wayar tayi dialling number din Yasmeenah.
“My babyyyyy”. Yasmeenah ta fadi tana daga wayar “Guess who came to visit yau, ya zo neman ki?”.
“Wane?”. Ta tambaya.
“The one and only Ali Na sidi”.
“Ali Na sidi? Minister of finance?” Ta tambaya.
“Shi fa, nace baki nan amma da kin dawo zakiyi fixing date inda zaki tarbe sa”.
“Ni ba ma wannan ba. Yasmeenah wai me kika sani ne game da wannan Khalifa Al-Haydar din? Tun dazu nike surfing net koh zan sama just a photo, in ba hoto ta ya zanyi hunting for him”. Ta fadi cikin takaici.
“Haba Laylah na, kefa dadi na dake rashin haquri. Yanzu me kike so ayi”.
“Yasmeenah dan Allah ki sa a yi bincike a kansa. You’ll help me with that won’t you?”.
“Da gudu ma, bayan na san in muka samo sa muna iya jan miliyoyi daga jikinsa. Amma kema fa ki ware ido a Australia. He’ll be there this whole week aka ce and I heard kan ya tafi zaa yi throwing wani exclusive dinner for him, duk yadda zaki bi ki sama invite ki bi”.
“Har sai kin fadi? Lallaima Yasmeenah kin fara mance Laylah Jaan”. A haka dai suka cigaba da hirar su har suka wa juna sallama ta katse waya. Kwanciya tayi ta dinga nazari hanyoyin da zata bi dun samun invite zuwa dinner inda ake shirya wa Khalifa Al-Haydar.
Shikam khalifa yana daga waya ya soma dialling number din Hajjo. After 2 rings kam ta daga waya, basu gama gaisawa da ita ba Fadeel ya fisge wayan.
“Abba! Abba!…..”.
“Hey little champ”.
“Yo what’s up dad”.
Dariya ya saki sosai sannan ya ansa dan nasa “Chuchu who’s teaching you all that?” Ya tambaya.
“I heard ya Aryaman saying that over the phone”.
“Ohhh shine ka koya koh”. Sun dade suna magana kan Fadeel ya fara kawo qarar cousins dinsa, wato yaran ýan uwan mamansa wanda suma suna zama da Hajjo.
“Abba! Kaga salima and Kubra won’t stop calling me Fadeelah” ya fadi cikin wani irin murya me cike da shagwaba, kamar zai yi kuka “Wai I look like a girl because of my dimple”.
“Hey baby boo, don’t mind them. In na dawo Nigeria zanzo da bulala kaji”.
“Really really”.
“Yes son. Now be a good boy okay? Don’t trouble grannie. Abba wuvvvs you”. Suna gama waya ya jingina bayan sa da Jikin car seat din ya shiga duniyar sa na tunani kamar yadda ya saba. When it comes to complain, tsiwa da yawan kawo qara, Muhammad Fadeel sak Fatima yike. Komi kankarta abu sai yayi rigima a kai. Dariya kawai yayi ya girgiza kai. Da Fadeel mace ne da sai yace Fatima ce akayi reincarnating dinta saboda halin su daya sak. Sai dai kuma kamar sa sak ubansa, in ba hanci da dimple daya ya debo na mamansa ba amma da ka gansa ka san wannan jinin khalifa Al-Haydar ne.
Da yamma Nawfal ya dawo mai da shopping bags har 5 cike da kaya da takalma, cheap ones kamar yadda ya buqata. Yaji dadi ya wa Nawfal godia sannan ya kwashi kayan ya wuce dasu. The next day yace wa Tariq ya shirya zasu fita unguwa su biyu. Suna mota ne ya fara tambayan Tariq
“Did you carry out the task I asked you?”.
“Yes sir….. my investigator said senator Junaidu’s first daughter is just 18 and she studies in Qatar, kuma he doesn’t have a niece or any relative here in Australia. Sir I think she’s either a business partner or an acquaintance”. Kai ya gyada yana comprehending abunda P.A dinsa ya fadi mai.
“Stop the car here”. Ya umurci Tariq.
“But sir the guesthouse is still far from here”.
“I’ll manage, wait for me here” ya fadi sannan ya fita daga motar ya fara takawa da qafa. Da ya isa gidan sai da ya kai 30 minutes yana jira kanta fito. Ya bata ipad dinta ta mai godia ta tambayi sunansa. Suka gama sannan suka wa juna sallama da fatan alkhairi.
“Her name is Laylah….. send words to our investigator in Nigeria to find out about her. Everything you can get about her”. Ya fadi wa Tariq yana shiga motar.
‘Why are you taking all these troubles just to know a lady khalifa?’ Zuciyar sa ta tambaya. Shima a gaskia bayi da wani valid reason as to why ya qagu da ya san koh ita wacece.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Toh fa, Laylah na so ta san waye khalifa Al-Haydar, shima khalifa Al-Haydar yana so ya san wacece Laylah. Wa zai riga wani finding out? Oho nima ban sani ba. Ko Laylah zata samu invite zuwa dinner inda ake shirya wa Khalifa Al-Haydar? Ta ya zata samu? Duk fa sai kun biyo ni a chapter masu zuwa.