JIRWAYE CHAPTER 4
Www.bankinhausanovels.com.ng
Hawaye ne suka kufce mata data dago ta kalli kanta a mirror. Ta qura wa mirror dun ido, koh kiftawa bata yi, ga hawaye masu sanyi na ta zuba daga idanun ta.+
Special make up artist inda tayi hiring ce ta dago ta Kalle ta “What’s wrong? You don’t like the make up?”. Ta tambaya baki a tabe.
“Are you kidding me?”. Laylah ta fadi tana dan goge hawaye a hankula da wani dan hankie “I love it. I look…. exceptional. I feel great, I just remembered something and it made me teary eyed”.
“Oh come on, this isn’t the time to cry, sit let me add a few touch ups”. Ta zauna shuru make up artist din ta dan gyara mata make up din kadan. Ba wani abu bane ya sa ta kuka illa red lipstick inda ke bakin ta, da kuma Idanunta da suka sha kohl. Tuna can rayuwar ta a baya tayi, tuno mutum na farko da ya fara siya mata kayan kwalliya tayi, Mahmoud dinta.. Har ta shiga tunani taji an tabo ta an ce ta wuce ta shirya ta sa riga ta dawo ayi hairdo dinta. Miqewa tayi ta dau rigar ta wuce. Bayan kamar 10 minutes ta dawo tayi twirling tana tambayan make up artist din da hairstylist how she looks.
“Girl you look exceptional! Masha Allah”. Make up artist din wanda balarabiya ce tayi commenting. Zama tayi aka yi styling mata kan ta into a nice loose bun, aka dan ban few strands din gashi ta gaba. Bayan an gama komi da komi ta miqe ta Qure ma kanta kallo a floor length mirror inda ke passageway na stairs din. Ta yi kyau ta hadu cikin wani burgundy coloured satin dress wanda ke da Cape a baya. Dress dinta was looking hot and at the sake time fairly modest. (Duk me son yaga dress in Laylah should slid into my dm na nuna masa. 2k ne kacal ba tsada😉) Tun asali Laylah ta kasance ba me cika son sa kaya da ke exposing jiki sosai ba. Takalmin qafar ta kuma wani black stiletto heel ne me kyau designer, sai wani dan diamond stud earring da ta sa a kunne wanda ke da zoben sa. Ta daga wata ýar baqar clutch wanda yayi matching da hair colour dinta da kuma colour din takalminta. Wani black fur jacket ta daura a saman dress din kan ta sauko.
A hankula ta taka har qasa inda Mr Yates ke jiran ta, shima ya sha kyau cikin wani black tuxedo masu kyau da tsada wanda ta siya mai. Tunda bata san kowa ba a garin shi ta ma tayin ya rakata dinner din as her date.
“You look stunning ma’am”. Ya fadi bayan sun shiga mota.
“Laylah….. just Laylah. And by the way Simon, you’re not looking bad either”. Ta fadi cike da murmushi.
Suna isa gun aka buda mata mota ta fito sannan ta sa face mask dinta kan Simon ya riqo hannunta. Dama theme din party din kenan, kowa sai ya sa mask. Suna isowa kan a bari su shiga ciki sai da aka tambaya sunanta sannan ta nuna invite dinta kan aka basu table number aka kuma ansa jacket dinta suka wuce ciki. Qaton hall cike da jama’a from different walks of life, turawa ne, larabawa, Indians, Africans jama’a duk dai gasu iri iri kowa da date dinsa. Mazan duk sunyi kyau sun sha tuxedos su kuma mata kowa ta Qure ado cikin dinner gowns masu kyau da tsadan gaske ga kuma face masks iri iri kowa na sanye da, mostly duk face masks din idanun mutane suke rufewa, wasu kuma har zuwa hanci. Tunda Laylah ta shiga ake ta kallon ta, ana wondering wacece ita, diyar wani qusan ne koh kuma matar wani qusa ne. karya ne namiji ya Kalle ta so daga ya wuce, sai ya juya ya kuma mata kallo, rigar da ta sa ta matukar mata kyau gashi ya fito da figure dinta sosai.
Waiter na zuwa giftawa ta gun su Laylah ta tsayar da shi ta dauki cocktail drink tunda ita bata shan alcohol, shi kuma Mr Yates ya dau glass din brandy. Suna zaune suna dan hira jefi jefi suna dariya abunsu, suka juya suna kallon masu rawa. Dan kwanakin da Laylah tayi a Australia ta shaqu matuka da Simon dan hira suke sosai kamar sun dade sosai da sanin juna, kuma sakin jiki take yi in dai tana tare dashi. Sosai yike tuna mata da Abban ta in yana magana da kuma yanayin barkwancin sa. Gashi da kirki kamar me.
STORY CONTINUES BELOW
Wakar da ke playing aka tsayar kowa ya dawo gun zaman sa kan aka yi welcoming din host din party din, wanda ake dinner din in his honour; khalifa Al-Haydar. Ji tayi cikin ta har wani kulle wa yayi dun ta qosa ta ga wannan Khalifa Al-Haydar din. Maza uku taga sun shigo sanye da suits na alfarma, da ka gan su kaga kudi. Na farkon ta gane sa dun shakka babu Nawfal ne, yana dariya ta ganesa, na biyun kuma bata tunanin ta taba ganin sa, yana da dan jiki kuma be yi tsawo can can ba kuma ga bisa dukkan alamu dattijo ne shi ba yaro ba. Sai kuma na ukun wanda sanye yike da face mask wanda ta rufe kusan duka face dinsa, ta kasa gane koh waye shi, sai dai yadda yike tafiya da yana yin build din jikinsa ya mata kama da na wani wanda ta sani. Na farkon ji tayi anyi introducing dinsa as Nawfal Muhammad Fadoul sai kuma na biyun, wato dan dattijon aka yi introducing dinsa as Al-Mubaraq Bala, general overseer din khalif airlines and group of companies. Sai last but not least khalifa Al-Haydar, giant of khalif airlines and group of companies.
Kan ta a wannan lokacin ya matukar daure, wondering take ta yi koh da gaske Nawfal and khalifa are 2 different people koh kuma kawai Nawfal ya samo wani ne ya yi acting as khalifa.
“Wai wannan wani irin game khalifa Al-Haydar yike da mutane ne”. Ta fadi cikin wata sassanyar murya. Sai a lokacin suna na biyu da aka kira ya fara ringing on her head. Al-Mubaraq Bala, the name sounded very familiar. Tana cikin duniyar nazarinta ta ji an miqo mata hannu.
“A dance with the pretty lady, may I?”. Dago kan da zata yi taga wannan mutumin ne fa da aka yi introducing as khalifa Al-Haydar. Ji tayi kamar a mafarki, mutumin da ta dade tana farautar sa shine ya kawo kansa gare ta.
“With utmost pleasure”. Ta fadi gami da sa hannunta cikin nasa wanda ya miqo. A haka ya riqo ta har dance floor din inda *perfect* din *Ed Sheeran* ke ta tashi.1
*And in your eyes you’re holding mine
Baby, I’m dancing in the dark with you between my arms
Barefoot on the grass, listening to our favorite song
When you said you looked a mess, I whispered underneath my breath
But you heard it, darling, you look perfect tonight*
A hankula suke ta swaying to rythm din waqar sai ji tayi ya matso dai dai kunnenta “you look perfect tonight”. Ji tayi jikinta ya wani irin mutu, kamar a movie wai gata tana rawa da Khalifa Al-Haydar, har yace mata tayi kyau. Amma kuma voice dinsa kamar ta sansa a wani gu, harta Kanshin cologne dinsa was scenting very familiar. Tabbas! Ta taba jin voice dinsa a wani gu amma ta rasa a ina. Kawai sai tayi tunanin toh deja vu ne, maybe bata ji ba kwakwalwarta kawai ke fadi mata karya. Sai da waqar ya qare tukun ta lura su kadai ke dance floor din kuma idanun kowa a kansu yike. Murmushi kawai ta saki da taga sai hoto ake ta musu, ta san ta samu shiga, gaskia dole gobe ta kalli CNN, dan ta tabbata sai ta fito a news din gobe. Nima ai dole na kalli CNN koh dan naga khalifan nan😂😂3
Rakata yayi seat dinta yayi placing gentle kiss a hannunta wanda ke cikin nasa kan ya juya ya wuce. Zaman ta ke da wuya Nawfal Muhammad Fadoul shima ya qaraso inda take ya rada mata abu a kunne.
“Kin tafi da imanin dan uwana”. That was the only thing da ya fadi mata ya wuce. Rest of the party went well, mutane kowa sai son yike yayi hoto da Laylah, koh ayi magana da ita, koh rawa saboda yanayin shigar ta, ta hadu gashi kuma ana ganin ta ansan babbar yarinya ce.
Can wuraren 11 din dare ana ta party ana jira 12 yayi ayi fireworks sai kowa ya fara neman hanyar gida. Dama cross over night ne shiyasa ake ta jira 12 yayi, that’ll mark the beginning of a new year. Laylah na tsaye da wasu couples, Mr and Mrs shetty, Indians ne. Suna ta dan taba hira sai ga wannan dan dattijon ya gabato inda suke. Tunda ya buda baki yayi magana Laylah taji voice dinsa ya mata very familiar.
‘Nidai yau I find everyone’s voice familiar, sai kace wata wadda ta zautu’ ta fadi a zuciyar ta.
Miqo mata hannu yayi amma haka nan kawai taji bata son ta miqa mai nata hannun dun haka kawai sai ta basar da shi kamar bata ga hannun da yike miqo mata ba.
“I am Al-Mubaraq”. Ya fadi gami da daga mask inda ke face dinsa. Zufa ne ya fara keto wa Laylah ganin fuskar sa, cike take da mamaki, kan kace me jikinta ya fara rawa, koh a mafarki ta ga wannan face din zata gane, no wonder sunansa yayi sounding extremely familiar. Amma shi ga dukkan alamu be gane koh ita wacece ba. Juya tayi cikin sauri ta fara tafia zuwa inda Simon yike tsaye da wasu mutane suna magana, tana isa tace yazo su wuce. Koh sallaman kirki bata bari yayi da abokan hiran sa ba ta jawo hannunsa suka wuce. Jacket dinta ta ansa suka fita cikin sauri. Koh jira ya buda mata mota bata yi ba ta shiga ta rufe da kanta.
Simon be ce mata komi ba ya shiga ya fara tuqa su. Can kuma ya fara jin shasshekar kukan ta.
“Are you alright?”. Ya tambaya amma yaji shuru. Da ya yi tambaya a karo na biyu yaji shuru sai ya rabu da ita. Har suka isa gida kuka take bata san sun isa ba sai da Simon ya dan tabo ta. Har zata fita taji ya kuma tambayar ta if she’s okay.
“I’m okay Simon, just a blast from the past”. Ta fadi sannan ta mai sai da safe ta fito daga motar ta wuce ciki.
Tana shiga dakin ta ta nufa ta rufo qofa. Ta dade tana kallon kanta a madubi ba abunda take yi in ba kuka ba. Can kuma ta wuce bathroom ta cire shoe dinta ta shiga jacuzzi ta kunna shower ba tare da ta cire kayan jikinta ba ta zauna. Ruwan nata zuba jikinta tana kuka irin me taba zuciyar mutum, kamar wadda aka wa mutuwa.Abdulmalik na juya wa ya duba amma be ga Laylah ba. Dama all through the party his eyes were on her, dan fita da yayi ya ansa call din Begum shine ya dawo be ganta ba. Duk sai yaji ba dadi, ya qosa a gama party din ya wuce ya huta.+
Suna zaune da Nawfal a bayan mota driver na jan su, zasu koma gida kawai Nawfal ya fara tambayar sa.
“Khalifa you love the girl, don’t you?”.
“What girl?”.
“Laylah”.
“Nawfal so nawa zan fadi maka I don’t love her, ni kawai I don’t know why I feel ina da connection da ita. Ni ba kowace mace a zuciya ta in ba zahra ba”.
“Hmmm khalifa kenan”. Nawfal ya fadi kan ya dan yi shuru “I’m not talking about Laylah yanzu, i’m talking generally. Haka zaka mutu ba aure? Ya kamata ka gane fa zahra ta mutu, ta zama tarihi, ba zata dawo ba, it’s not the end of the world. Fadeel Kuma fa? Baka tunanin yana buqatar so da kulawa na uwa”.
“Duk yana samu a gun Hajjo”.
“Haba khalifa, ai duk kulawan da Fadeel zai samu in ba love and care of a family wallahi it’s nothing, he needs a family, he needs a mother, he needs you. Ya kamata ka sama wa yaron nan uwa, koh ita marugayiya zata so haka”. Ya fadi kan yayi shuru.
Shi dai Abdulmalik bai kuma cewa komi ba, rufe idanunsa kawai yayi ya jingina kansa da headrest din kujeran motar yana ta nazari akan maganar. Imagining rayuwa yike da wata mace wadda ba zahra ba, ta ya ma zai fara. Har suka isa gida tunani yike tayi. Yana shiga gida ya wuce dakinsa straight, ya tube ya shiga wanka, a gun wankan ma tunani yayi ta yi. A karshe ya fito ya shirya cikin kayan barci ya dauko wayar sa kamar yadda ya saba. Samun kansa yayi da strolling down to sunan Laylah “Buddy” kamar yadda yayi saving number din amma to his disappointment she was offline. Ranar dai kasa barci yayi, yana ta tunani, duk abunda ya faru a gun party din ya dinga replaying a mind dinsa har zuwa maganar da suka yi da Nawfal.
Ita kam Laylah ta dade a zaune a bathroom din kan ta tashi ta cire kayan Jikin ta ta sanya rigar sanyi saboda wani irin wawan sanyi da taji na damunta. Combing hair dinta tayi kan tayi drying dinsa. Tana cikin combing hair din ne ta tuno da comb inda khalifa Al-Haydar ya bata. Miqewa tayi ta dauko ta fara taje kan dashi kawai sai ta saki wata ýar murmushi. Tuno childhood days dinta take sanda take cewa abokan wasan ta in ta girma zata yi kudi ta bar garin, dan sarki zata aura koh kuma me kudi sosai. Da ta fadi haka sai suta mata dariya ana tsokanar ta. Haka lokacin da ta fara dating Mahmoud wanda Babansa malamin boko ne, shine headmaster din primary school din garinsu, aka ta mata dariya ana tsokanarta amma ita a lokacin koh a jikinta saboda so ya riga ya gama rufe mata idanu. Dariya kawai tayi da ta tuno da abubuwan nan, gashi har yau bata yi auran ba amma kuma ga kudi masu tarin yawa ta samu. Toh me ma amfanin kudin bayan ta hanyar banza ta same su? A question she asks herself everyday.
“Khalifa Al-Haydar is my last mission”. Ta qara tuna wa kanta.
Tsayawa tayi tana qarewa comb din kallo me kyau kawai sai ta fara tuno da da incidence inda suka auku a party din. Toh ta ya khalifa Al-Haydar yayi noticing dinta? Ita har ajin ta da kyaun ta ya kai ya jawo hankalinsa? Tayi ta nazari, Hakika ya saukaka mata aikin ta. Can kuma sabon abokin ta tuna, da sauri ta miqe ta dau wayarta ta fara scrolling through contacts dinta to his number. Dubawa tayi amma taga he’s offline dun haka kawai ta ije wayar ta kwanta amma duk ta kasa barci. Tunanin khalifa Al-Haydar kawai take ta yi, ita dai Tabbas she has a feeling ta sansa a wani gu, Amma a ina? Kuma meyasa take jin wani abu a zuciyarta, da tana tare dashi wani dadi ta dinga ji, kamar kar su rabu.
‘What’s happening to me?’ Ta fadi a ran ta ‘first it was Abdulmalik and now khalifa Al-Haydar’.
Washe gari bata tashi da wuri ba sai can wuraren 11 ta tashi, tana tashi breakfast ta fara kan tayi wanka. Fitowan ta wanka ke da wuya sai ga daya daga cikin masu aikin gidan tazo mata da bouquet din flowers da dan note a jiki. Ije flowers din tayi bayan ta gama sunsuna su ta kuma yaba da kyaun su.
*Rise and shine, it’s a new day. Don’t let the sorrows of yesterday ruin the beauty of today, morning sunshine. Khalifa Al-Haydar #Xx*
Tana murmushi ta gama karanta note din, cike da mamaki. Shikenan daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaqi, Lallaima khalifa Al-Haydar. Mamaki sosai ta dinga. Tana cikin shiri taji text ya shiga wayarta, tana dubawa taga daga Abdulmalik ne.
*Lunch at 2, don’t say no please*.
Murmushin ta ya qara fadada da ta gama karanta text din. Ta rasa meyasa Abdulmalik ke da irin wannan effect din on her. Kwanan nan bata da aiki wanda ya wuce na tunanin sa, yanzu kuma ga khalifa. Ita duk ta ma rasa wani irin wasa da hankali zuciyarta ke mata ba.
*Sounds fun*. Tayi typing me reply.
*perfecto! I’ll pick you up. Xx*. Ya kuma turo da wani text din.
Nan da nan Laylah ta rasa zama, tunanin kayan da zata sa ta fara. A haka ta cinye time dinta tunanin what to wear har sai around 1:30pm tukun tayi making up mind dinta ta sa wani gown din atamfa me kyau sosai, ta dora wani dan blazer a sama, kan ta kuma ta rufe da dan sheilah. Tsaf ta gama shirin ta tayi kyau, bata dade da kammala shiri ba aka shigo dan fadi mata baqon ta ya iso.
Tana saukowa ta gansa yayi kyau cikin wani sweatpant da ya sa da navy blue v-neck shirt. Sajen sa ya sha gyara, koh kama baya yi da driver.
‘Wannan da me kudi ne da an ga namiji me kyau’. Ta fadi a zuciyar ta. Ita ta gama yarda Abdulmalik ba wani me kudi bane saboda impression inda ya bata kenan and yanayin kayan da yike sa wa da wayar da yike riqe wa and wasu ýan abubuwa da tayi noticing ya sa ta yarda sosai da sosai shi talaka ne. Gaisawa suka yi kan suka nufi hanyar waje.
“Nidai talaka ne, bani da mota”. Ya fadi yana dan sosa kansa “hope you don’t mind taking a bus”. Ya tambaye ta.
“It’s been a while since I did that, it sounds fun”. Ta fadi fuskar ta a sake. A hankula suka taka har zuwa bus station suna ta taba hira. Suna shiga bus kuwa suka sama seat daya ne kawai vacant sai yace mata ta zauna shi kuma ya kama railing din sama ya tsaya. Ita ma miqewa tayi ta tsaya dashi. Kallon ta yayi yayi mata murmushi. Fashewa da dariya sukayi sanda bus din ya dan fada porthole suka ci karo.
“kutt! Wai ke kanki sai kace kwakwa. Na Biyu kenan muke cin karo”. Ya fadi suka fashe da dariya. Fito da sleek iPhone 7 dinta tayi ta fara daukan su hoto. Suna ta making funny faces suna dariya abunsu. A haka har suka isa park inda suka fara haduwa bayan isowarsu Australia. Eatery din cikin park din suka shiga suka zauna aka kawo masu menu suka yi placing order. Cin abincin suke suna dan taba hira.
Laylah ta sha mamaki yadda taga yana cin abinci cikin nutsuwa, with poise and class. A gaskia da ace bata san sa ba da bazata taba yarda shi ba mai kudi bane, he’s too good to be a driver.
“So, naga you look educated amma kuma kake aikin driving”.
Sai da ya kurbi ruwa kan ya bata ansa “I have a degree in Software engineering”. Ya fadi ba tare da fadi mata har masters garesa da PhD.
“Forreal! Shine kake aikin driving”.
“Toh ya muka iya, rashin aikin yi a qasar mu”. Ya fadi mata “ke fah? You look rich, or should I say you’re wealthy, da an ganki an ga ýar gidan naira”.
Dariya tayi kan ta basa ansa “Ni ba ýar kowa bace. I paved way for myself. I have a degree in business administration, last 2 years kuma nayi wani special course in events planning and management. I’m an events planner”.
“Ohhh you told me, Amma what business proposal do you have for Mr Al-Haydar if I may ask”. Ya tambaya. Rasa abun cewa tayi kawai dai ta kirkiro tarin karya kamar ta kware. Sai da ta gama tarin ta basa ansa. Lokacin ta samo karyar da zata mai.
“He’s a business man, so na ke yayi signing agency dina, mu dinga mai planning events a duk lokacin da yike da sha’ani koh wani abu”. Kai ya gyada mata alamun ya gane suka cigaba da cin abinci.
“Ya ban ganka ba a dinner din jiya?”.
“Ni a wa? Ina ni ina zuwa taron manyan mutane”. Ya fadi cikin dariya. Daga nan shuru suka yi suka cigaba da cin abincin su.
“Yawwa! Please waye Al-Mubaraq Bala a gun khalifa Al-Haydar, what’s the relationship between them”. Ta tambaya.Abdulmalik kan sa ya daure a kan meyasa take son sanin relationship inda ke tsakaninsa da Al-Mubaraq amma be bari ta gane ba. Gyaran murya yayi kan ya bata ansa.+
“Al-Mubaraq kawu ne a gun khalifa. Not like they’re related by blood amma tun khalifa na yaro karami Al-Mubaraq ke aiki da su. Mohammed Mumtaz Al-Haydar was his godfather”.
“Ohhhhhh I see”. Ta gyada kai kamar tana nazari.
“Is there something between you both? As in Al-Mubaraq da ke”.
“Aah! Not at all” ta ansa cikin sauri “He’s just a blast from the past. Nothing out of the ordinary”. Tayi dan murmushi.
Suna gama cin abinci suka fita zuwa cikin park din. Samun wuri suka yi suka zauna suna ta hirar rayuwa and all. Abdulmalik ya miqe ya je ya siyo mata ice-cream shikuma ya siyawa kansa popsicle dun ice-cream be cika damun sa ba. Suna zaune suna ta kallon wasu yara suna ta wasa, Abdulmalik ya ciro camera dinsa ya fara daukan hoto.
“Meyasa kake yawo da camera?”.
“My boy loves adventures, so duk sanda nayi tafia ina yawo da camera to capture all I can for him”.
“Awwwwnnnn. That reminds me, you were telling me about him the other….”. Bata kai da gama tambayar sa ba wayarta ta hau ringing. Sanda kuma ta gama answer call din ta mance so haka aka bar zancen. Zaune suke shuru ba me cewa kowa komi kawai Abdulmalik yaji saukar abu me sanyi a hancin sa. Juyawar da zai yi yayi facing dinta kuma yaga camera yayi flashing.
“Crap! Allah sai na rama”. Ice-cream ne tayi scooping ta zuba mai kan hanci.
“Ba sai ka rama mu gani ba”. Ta fadi tana mai gwalo. Cigaba da daukan sa hoto tayi shikuma ya biye mata. Can bata zata ba zata kai cone din ice-cream dinta baki kawai Abdulmalik ya dungure mata hannu ice-cream duk ya bata mata hanci da face.
“Who’s looking like a clown now huhh”. Ya fadi yana mata dariya. “Click” taji qarar camera dinsa ya mata hoto. Ita ma ciro wayarta tayi ta matso kusa dashi suka ta hoto. Sai da suka gaji suka daina. Nan kuma ta hade rai wai ya bata mata face yanzu ina zata sama ruwan wanke wa. Be ce mata komi ba ya ciro dan hankie from his breast pocket ya fara share mata face. Ita kuma shuru kawai tayi tana kallonsa. Wani irin bugu kawai zuciyarta ke mata. Koh shakka babu wannan Abdulmalik din ya fara samun gun zama a zuciyarta kuma haka be kamata ba. Tana gudun wannan sabuwar lamarin da zuciyar ta ta bullo mata dashi. A tsarin ta babu soyayya dun a ganin ta ba namiji da zai taba accepting dinta after seeing her true colours.
“Earth to Laylah. Tunanin me kike yi haka”. Ya tambaya.
“Nothing, let’s go to the fish pond”. Ta jawo mai hannu har zuwa fish pond din inda suka jima suna kallon fishes as they swam round the pond. Sai yamma sosai suka kama hanya. Bus station suka koma wannan karan suka yi saa akwai enough space, zama suka yi suna ta hirar su wata ýar tsohuwa kuma da ke zaune adjacent to them tayi ta kallonsu tana murmushi.
Suna sauka a bus stop din kusa da Jk guesthouse suka cigaba da takowa a hankula. Jefi Jefi suna dan taba hira. Suna isa wani florist shop yace su tsaya. Single rose flower ya siya ya bata sannan suka wuce. Har zasu tafi yaga wani bunch din lavender ya cira guda daya yasa mata a gefen gashi.
“Newly wed?” Ýar dattijuwan matar da ke da shagon ta tambaya. Dariya suka yi suka kalli juna sannan suka ce mata aah.
“I wish tho”. Laylah ta fadi a hankula amma sai da ya ji ta.
“We can make it a reality you know” Juyowa tayi ta Kalle sa tana dariya kan ta basa ansa.
“Daga wasa”.
“You look cute”. Ya fadi, his voice sending chills to her spine.
“And you’re so sweet”. Basu yi nisa da shop din ba aka fara yayyafin ruwa kan kace me ruwan yayi karfi. Jawo ta yike ta yi su fake a patio din wani gida amma ta qi.
STORY CONTINUES BELOW
“Come on! Let’s have a little fun in the rain”. Cigaba da tafia suka yi cikin ruwan can kuma ta fara gudu shikuma yana biye da ita.
Koh da yike yaro Abdulmalik be taba wasa cikin ruwa ba, kuma da girman sa be taba ko da tunanin yi ba amma sai gashi yau mace ta sa shi yi. Tsakiyar titi suna ta gudu suna wasa kamar yara. Ya dade be ji annashuwa irin na yau ba. Duk wani damuwa nasa ya mance dashi. Ya rasa abun da yike ji a zuciyar sa, abunda yike feeling for Laylah be tunanin koh ita Fatima da yike ikirarin yana so ta taba sa shi jin haka. Amma kuma ya kasa ganewa, could it be love? Or just a mere infatuation. Shi a tsarinsa tunda ya rasa Fatima ba wani aure, ba kuma lokacin soyayya dun yana tsoron kada ya sake aure a wulakanta me dan sa, yana tsoron having to divide the attention he’ll give to his son with someone else.
‘What is happening to me’.
‘Just follow your heart’. Wani voice a kan sa ya fadi mai and in that instant yayi making up mind in sa a kan abun da yike so. Giving love a shot isn’t gonna hurt afterall, or will it?
Tunani yayi ta yi har suka isa jk guesthouse. Laylah ta ce alambaran sai dai ya shiga ciki ya tsane, bazata bari ya tafi gida a haka ba. Ba gardama ya shiga ta nuna mai daki ta kuma aika mai da fresh clothes. Kan yayi changing ya fito har ta hada mai coffee tayi setting fireplace to keep them warm. Ansan mug din coffee din yayi ya mata godia.
“Na mance when last na samu farin ciki irin na yau” ta fadi idanunta sun ciko da kwalla “Thanks”. Ta fadi a hankula. Shuru kawai yayi be ce komi ba dun be ma san me zai ce da ita ba.
“I’ll be going back to Nigeria tomorrow, my work in Australia is done”. Ta fadi mai.
“Me too, gobe zamu bar Nigeria”.
“Da gaske? Duk da Khalifa Al-Haydar?”.
“Yes. Amma you seem very interested in khalifa Al-Haydar”.
“Very interested. Dole ne in hadu dashi”. Ta fadi with determination in her eyes. “I have a business waiting to be finished”.
“In na hada ki dashi kuma fa?”.
“Da gaske? Duk abunda kake so, name it and it’ll be yours”.
“Anya kuwa?”.
“Ni nace ai kayi naming”.
“Koh da zuciyar ki ne?” Ya tambaye ta. Shuru Laylah tayi ta rufe idanun ta, me yike nufi zuciyarta?.
“Kamar ya?”. Ta tambaye sa.
“It’s simple, your heart in exchange for a meeting with khalifa Al-Haydar”. Ta dade tana nazari shi kansa mamakin boldness dinsa yike.
“Abdulmalik you seem like a very nice and responsible person, ba zan so na bata maka rayuwar ka ba with my presence in it even though I wish for our friendship to go beyond Australia, ina so nayi keeping in touch with you even in Nigeria”. Dariya Abdulmalik yayi ya juya abun zuwa wasa.
“Kwantar da hankalin ki nima wasa nike, ba sai kin mun kora da hali ba. In ba karambani bama ina ni talaka ina ki”. Ya kurbi coffee dinsa. Ta buda baki zata yi magana kenan daya daga cikin masu aikin gidan ta katse ta.
“Your clothes are dry sir”. Ta fadi tana miqo mai kayan sa. Miqewa yayi ya anshi kayan yana mata godia. Ije cup din coffee din yayi ya wuce dakin da shirya dazu ya sanja zuwa kayan sa sannan ya fito ya wa Laylah sallama.
“See you in Nigeria or better still, till we meet again”. Ya fadi ya wuce his heart half broken. Yana tafia yana ta nazari. Ba abunda ya bata mai rai kamar yadda Laylah tayi turning dinsa down duk da dai he was kind of joking about it amma that wasn’t the response he expected. Wato su mata in baka da kudi basu rasa excuse din korar ka. Ya ja dan tsaki.
‘It happened for the best, dama babu soyayya a tsarinka’ zuciyarsa ta basa shawara.
Yana wucewa ta miqe ta wuce dakin ta bayan ta bada orders akan kada wanda ta dameta tana son ta huta. Hmm, what started like a wonderful day had to turn sour. Duk da Abdulmalik ya maida abun wasa, she couldn’t help but sight the sincerity in her eyes. Hawaye ne suka fara kwararowa daga idanunta a hankula. shakka babu she has fallen for this guy amma kuma ta san they can never be together. Yana gane asalin sana’arta zaya guje ta and kamar yadda turawa suka ce ‘prevention is better than cure’. Kuka take tana tausayawa rayuwar ta. Ita shikenan sai da taga wasu na soyayya? Sai dai taga wasu na aure suna starting families of their own? Haka zata zauna har ta mutu? Without love, without joy, without happiness, without anyone to call her own. In haka dukiyan yike toh Hakika gwara ta zauna cikin talauci with a family of hers, full of love and happiness da ta zauna ga tarin dukiya amma ba farin ciki da kwanciyar hankali.
Dauko wayarta tayi tana ta kallon pictures inda suka dauka. Ashe dai abunda ke shirin faruwa kenan da suka yi ta daukan hotuna, for memories. Yanzu Abdulmalik is nothing but history to her. Dama ba soyayya a tsarinta. Can kuma ta ja ýar tsaki, gashi har zata koma Nigeria ba abunda ta tsinana in ba tarin baqin ciki ba. Tunda har bata sama damar haduwa da Khalifa ba Australia bata tunanin zata iya a Nigeria dan samun haduwa da masu kudi kamar su khalifa abu ne me matukar wuya.
Daren ranar kasa barci tayi, da ta dan juya sai ta sama kanta da daukan wayarta dun kallon pictures inda suka yi snapping earlier. The next day ta tashi da wani irin wawan headache saboda rashin barci da bata samu tayi ba da kuma kukan da ya zama mata sana’a. A haka tayi sallama dasu ma’aikatan Jk guesthouse sa kuma family din Simon. Cike da hawaye Simon ya tuqa ta zuwa airport suka yi sallama.
“Time to go home Laylah”.Jirgin su na isa Nigeria ta tadda Yasmeenah na jiran ta. Cikin murna ta qarasa ta yi hugging din Yasmeenah.+
“Ya Allah! I’ve missed you Yasmeenah”. Ta fadi kawai ta fashe da kuka.
“Nifa dadina da ke kenan, shegen son kuka. Oya yi shuru, 3 weeks kawai fa kika yi biki ganni ba”. Yasmeenah ta anshi jakarta ta riqe mata suka karaso inda tayi parking mota. Laylah na maida sim dinta na Nigeria gida ta fara kira, ta yi dialling number din umman ta.
“Ummati”. Ta kira sunan mahaifiyar ta kamar yadda suke kiranta.
“Na’am ýar albarka, kin dawo kenan”.
“Shigowa na Nigeria kenan”.
“Masha Allah, ya aikin? Komi lafia koh?”. Ummati ta tambaya ita kuma Laylah ta ansa ta da komi lafia lau. Ta tambayi Abban ta da kuma ýan uwan ta.
“Duk lafia lau suke, Abban ki nema be ji dadi ba, jiki ya dan tasan me”.
Salati tayi kan ta ansa mahaifiyar ta “me ya same sa ne haka? Kuna da kudi isasshe? Zan turo kudi da na shiga gida kuma ina samun hutu daga gun aiki zan zo”. A haka suka ta zance har suka wa juna sallama ta ije wayar. Duk hankalinta a tashe da taji an ce Babanta ba lafia.
Bayan sun isa gida, sai da Laylah tayi sallah sannan ta ci abinci ta huta tukun ta kwashe tas duk abunda ya faru a Australia ta fadi wa Yasmeenah. Guda Yasmeenah ta saki.
“Ahhh Lallai! Diyata akwai ki akwai goshi. Tunda nike hada Junaidu da ýan mata ba wadda ya tabawa kyauta irin naki. Amma kuma Laylah baki ji, na sha fadi miki a wannan sana’ar there’s nothing like love, baa soyayya. Ke a ganin ki wa zai auri karuwa?”. Ji tayi kalaman Yasmeenah sun sosa mata zuciya amma kuma ta san gaskiyar zancen kenan, ba wanda zai taba accepting dinta.
“Yanzu mance wa zakiyi da wani Abdulmalik ki fara shirin tarban next customer dinki. Na fadi miki Ali Na sidi har nan gidan ya tako kafarsa yazo yace shima yazo Laylah Jaan ta lasa mai irin nata zumar”. Ta fadi mata “kuma kema kinsan kudi zasu fito jikinsa. Yanzu duk wani zancen Al-Haydar a watsar, wannan ya ma na nisa. Tunda ga wanda ke hannu sai mu kama su gam ai koh”. Yasmeenah ta fadi tana taunar chewing gum. Ita kam Laylah duk ji tayi wannan rayuwar ta fita mata a kai amma kuma bata san daga ina zata fara ba.
Tunda ta dawo rayuwar ta ta sanja, ta rage fita in ba dai aiki ne ya fita da ita waje ba. Kullum bata da aikin yi sai kallon hotunan ta da Abdulmalik tana zubar da kwalla. Duk yadda take son barin wannan sana’ar ta riga tawa kanta alkawarin bazata bari ba har sai randa ta ci kudin Al-Haydar. Amma kuma yanzu da babu Abdulmalik ta wace hanya zata samu ta hadu dashi.
Shikam Abdulmalik yana dawowa sai da ya fara biya wa ya duba lafiyar dan sa kan ya wuce gida. Nawfal ya lura da dan uwan nasa, tun ranar da ya hadu da Laylah, ana gobe zasu dawo be dawo normal ba, duk ya sanja. Kwata kwata ya ma daina zancen ta, baya so kuma a dago hirar ta.
“Khalifatullah”. Ya ji muryar mamansa. Matsowa tayi kusa dashi ta dora kanta a shoulder dinsa. Wani dan kiss ya dora mata a kai kan ya tambaye ta abun da ya faru.
“What’s wrong Begum?”.
“Duk ka sanja, wani abu ne ya faru a Australia?”. Ta fadi “Ni bani son ina ganin ka haka, duk sai naji ba dadi”.
Shafar lallausar suman kanta ya fara kan ya gyara murya. “Ke fa kin cika damuwa, nothing happened, everything’s going well. Na kusa kama barawo insha Allah”. Ya gama mata bayani kan ya tashi zai fice. Har ya kai bakin qofa sai ya juya ya kuma mata magana.
“Fadeel is moving back here next week”.
“Da gaske. Jikana zai dawo hannuna”. Ta miqe tana murna “Na dade ina jiran zuwan wannan ranar. Have you finally made up your mind? Akwai diyar qawata dama, yarinyar akwai hankali, nasan zata riqe mana marayan Allah tsakanin ta da Allah”.
“Begum ya isa please. Ban shirya aure ba har yanzu. Kawai dai zai dawo nan ne, na fi so yana kusa dani. Yola yayi nisa”.
“Kayya, for how long?, next month zaka yi 35 for heavens sake khalifa”.
“Begum let’s not start please. I’m stressed”. Ya fadi ya wuce dakinsa wanda ke ground floor din gidan. Tun faruwar incident din Fatima khalifa ya rabu da hawa bene, koh elevator sai ya dage ya rufe ido yike shiga.
Wuni yayi ranar a cikin bedroom dinsa dun koh da aka kirasa out for dinner sai cewa yayi a kawo mai nasa dakinsa baya ji da fita. Begum ta gane cewa akwai abun da ke damun dan nata kuma baya son sharing shiyasa yike dodging haduwa da ita dan haka ita ma sai ta fita harkar sa ta basa space. Ranar isowar Muhammad Fadeel ya zo, ranar babu sukuni Al-Haydar mansion. Masu aiki ne ke ta kai komo, ana shirin isowar karamin uban gidansu. Dama already tunda Abdulmalik ya fadi wa Begum cewa Fadeel zai dawo gun su ta sa aka sake interior in dakin da yike zama in yazo hutu, aka sanja komi na dakin an siyo sabo an saka. Kayan wasa ma duk an cika dakin dashi. Har game room aka hada mai. Garden din gidan shima haka an zuba kayan wasa.
Girki kam ana ta yi iri iri, a dora wannan a sauke wancan. Duk abincin da Begum ta san yana so ta sa a dafa mai. Sai da ta tabbatar an gama komi tsaf tukun ta wuce gefen ta dun ta shirya. Tana cikin shiri taji alaman shigowan motoci.
Shima dama Abdulmalik ba inda yaje ranar, yana gida jiran isowar dan sa, tun safe ya aika one of their private jets zuwa yola ya dauko dan nasa. Yana jin qarar mota ya fito waje. Motoci ne guda 3 masu na alfarma suka yi parking a harabar gidan. Fadeel be ma jira an buda mai qofa ba ya buda da kansa ya rugo da gudu zuwa inda Babansa ke tsaye. Gudu yike yana murmushi irin na mamansa, duk sanda Fadeel yayi dariya Abdulmalik gani yike kamar Fatima ce ke dariya. Dukawa yayi qasa sanda yaron nasa ya qaraso ya rungume sa kamar zai shige cikin sa. Be san sanda kuka ya kufce mai ba. Fatima kawai yike tunawa, yana jin wani so da kaunar dan sa na dada ratsa jikinsa.
“Ab….Ab…ba”. Yaron ya fadi yana numfashin sama sama sabida gudun da yayi. “Abba hayatee”.
“Chuchu na….. my little tiger”. Ya fadi still hugging the boy. “It’s good to have you back son”.
“Then stop crying, the occasion is a happy one”. Ya fadi yana gogewa mahaifin sa hawaye. Yana hango Begum ya ruga da gudu ya fada mata a jiki shikuma Abdulmalik ya qarasa inda Hajjo take, tana takowa a hankula ya anshi jakar da ta riqe da ya riqe mata har suka iso ciki.
Kan ka ce me Fadeel ya fara displaying halin sa na barna da rashin ji a gidan. Yana ta faman ba masu aiki ciwon kai gashi ba daman suyi bugu a bakin aikinsu😁. Sai da Hajjo tayi 2 days a Abuja kan ta koma yola. A ranar da zata koma kam ta sha kuka dan ba karamin kewar jikan nata zata yi ba, abun farin cikin ta amma ya ta iya. Week na zagowa aka hiring teachers inda zasu dinga zuwa gida suna koya wa Fadeel karatu. A duk lokacin da Abdulmalik ya sama kansa da shiga cikin damuwa in dai ya ga fuskar dan sa duk sai yaji damuwar ya gushe, a haka dai life ya cigaba gradually duk da akai akai ya kan yi tunanin Laylah amma koh so daya be taba yunkurin neman ta ba. A cewar sa, if they’re destined to meet again to komin dadewa fate will bring them back to each other.
Wata ranar sati, Abdulmalik na cikin study dinsa yana aiki daga nan ya fara lulawa duniyar tunanin sai ji yayi ana kwala mai kira ana jan hannun rigarsa.
“ABBA! ABBA!”, Fadeel ya dinga ihu dama ga muryan nasa very sharp.
“Wai me? Dawo da kai gidan nan laifi ne Fadeel?”. Ya tambaye dan nasa dun tun randa Fadeel ya dawo gidan Abdulmalik ya rasa sukuni, daga Fadeel yayi fitinar yana son kaza sai yayi na yana son wani abun. Gashi da shegen tsiwa da tonan fada. Da ace ba a gida ake zuwa koya me karatu ba da an sha fama dun da sai ya dinga neman fada a makaranta.
“You promised to take me out today rememberrrrrr”. Ya fadi da wani irin grin da ke nuna wawulon bakin sa. Sanin halin yaron nasa ya sa ya miqe ba gardama.
“Go tell your nanny to dress you up, i’ll be downstairs waiting”. Sai da Fadeel ya tsaya yana imitating wai irin rawar Michael Jackson kan ya wuce dakinsa shiri. Abdulmalik kam dariya kawai ta tsaya yana ta yi.
Koh da suka isa national park and zoo be san meyasa zuciyar sa ta dinga wani irin bugu ba, kaman wani abu na shirin faruwa, something great, something amazing.
▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪
Hi hi hi hi hi me ke shirin faruwa ne. Who likes little Fadeel, I definitely like him, he reminds me of my childhood😁😁😁. Sai mun hadu a next chapter.