JIRWAYE CHAPTER 5

JIRWAYE CHAPTER 5

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

“A dangerous plan, just this time

A stranger’s hand clutched in mine

I’ll take this chance, so call me blind

I’ve been waiting all my life……”. A hankula take ta bin wakar zaune a garden in da ke harabar gidan da suke zama ita da Yasmeenah. Qaton gida ne me ginin zamani wanda wani senator ya bawa Yasmeenah as tukwuicin hada sa da tayi da Laylah Jaan. Ita kuma Yasmeenah tace bazata koma gidan ba sai tare da Laylah. Gida ne qato mai compartments da yawa. Daga Laylah sai ita sai kuma masu aiki da ke zuwa suyi su tafi, sai mai gadi, driver da kuma yarinyar Yasmeenah wadda ta riga ta yi aure tana zama a portharcourt da ýaýanta biyu sai dai tazo hutu ta koma.

Zaman ta a garden din ba abunda take yi in ba tunani ba, tana kallon pictures din ta da Abdulmalik tana ta tunani. Gashi tunda ta dawo Nigeria about 3 months kenan amma koh a hanya basu taba koh da cin karo bane. Toh ina ma take wani fita bare har ta sa ran zata hadu dashi.

‘Maybe you made the wrong decision by turning him down’ Zuciyar ta ta fadi mata.

‘No! The decision was a right one’. Wata zuciyar ta fadi.

Cigaba da jin waqar ta tayi trying as much as possible ta kawar da tunanin sa daga zuciyarta amma kuma inaa. Muryar Yasmeenah kawai taji ta katse mata nazarinta.

“Earth to Laylah, tunanin me? Wannan matsiyacin kike tunani har yanzu koh?”. Ta fadi tana tabe baki. “Laylah I’ve told you, love ba namu bane, it’s too much luxury for us. It only ends up with you getting hurt. Love sucks sweedie. Cheer up, just consider your moments with him as a rebound shikenan”. Ta fadi tana shafa wa Laylah baya. Daga nan tace su tashi su shiga cikin gida ta shirya su fita shan iska.

Ba gardama Laylah ta tashi ta wuce daki ta fada wanka. Tana fitowa ta shirya cikin wani maroon colour Pakistani top da black jeggings ta rufe kanta da maroon turban cap. Tana gama shiri taji tana son tayi make up, haka ta zauna gaban vanity table ta dau kayan kwalliya ta dinga yi har ta gama. A hankula Yasmeenah ta tura kofar dakin ta ta shigo.

“Are you set?”. Ta tambaya.

“Yeah, i’ll be out in a jiffy”. Ta fadi da murmushi. Turare ta fesa kan ta dau car key dinta da other necessities ta fito. Lokacin guda kawai taji mood dinta ya sanja. She felt happy and alot more at ease with herself. Har wani murmushi ta dinga yi a hanyar ta na fita. Yasmeenah ta izza ta jingina Jikin mota tana jiran ta.

“I’ll drive”. Ta fadi tun kan Yasmeenah ta miqo hannu karban car key. Dariya kawai Yasmeenah tayi ta shiga mota ta zauna. Da suka zo fita Laylah har kyauta tayi wa mai gadi kan suka wuce. Waqa ta sa tana tuqi tana bin waqar tana rawa. Kasa shuru Yasmeenah tayi sai da ta mata tambaya.

“Jaan, what’s with the sudden mood change?”.

“No idea! I just have a feeling something good’s awaiting me. Scratch that something good’s awaiting us Yasmeenah”.

“Hmmmm”. Yasmeenah ta sa hannu a chin dinta kamar me nazari. “Something good”.

“Yeah. Something life changing, in a positive way”. Ta fadi suka dan cigaba da hira har suka isa national park and zoo. Sun gama siye siyen da zasu yi kenan zasu wuce su sama wuri su zauna sai ga Yasmeenah ta hadu da wata qawarta. A nan suka dan tsaya ana gaisuwa aka kuma fara dan taba hira. Can Laylah ta matsa dan gefe dun ta ansa waya, tana cikin magana a wayar ne wani dan yaro ya rugo bayan ta da gudu ya qanqame kafafun ta.

“I’ll get back to you Ameer”. Ta fadi ma P.A dinta wanda suke discussing wani sabon assignment da aka basu na organising din wani fundraiser event for orphans, handicaps and less privileged sannan ta kashe waya. Zata juyo taji an qanqame kafar ta da karfi. Sai da tayi da gaske ta iya Juyowa. Ido ta hada da wani dan yaro me matukar kyau wanda a shekaru bazai wuce 7 years ba. Tsananin kyau da sha’awa da yaron ya bata ya sa ta dan zuqunna. Ta buda baki zata yi magana kawai taji yaron ya kamata yayi hugging dinta tightly.

STORY CONTINUES BELOW

“Hey wh……”. Bata gama maganar ba ya rufe mata baki da dan karamin palm dinsa.

“We’re playing hide and seek. He’ll get me a new play station if I win”. Ya fadi mata yana murmushi “You’ll help me hide, won’t you”. Komi na yaron kamar mace, harta dan karamin voice dinsa, smile dinsa ga dimple inda yike da. Ga kuma gashi baqi wuluk me tarin yawa a kansa.

“But I have to go”. Ta fadi.

“Don’t say no, Pleaseeeeeeee mommy”. Ya fadi a shagwabe yana maraice mata kamar zai yi kuka. Ita kam duk ya gama sa zuciyar ta karaya tunda ya kirata mommy. Murmushi tayi ta riqe mai hannu suka wuce can wani lungu inda ba zaa yi noticing dinsu sosai ba. Farko zama suka yi shuru for about 5 minutes kan yaron ya fara mata magana.

“Can I see your phone please”. Ya tambaya ita kuma ta miqa mai. Password ya fara tambaya ita kuma ta sa finger print dinta kan ya ansa ya fara game. Can kuma ya miqa mata wayar ya tabe baki.

“It’s boring”. Miqa mai popcorn inda suka siya tayi ya karba yana dariya har qaton wawulon sa ya fito. “Let’s be friends”. Ya fadi yana miqo mata hannu. Karbar hannun tayi, tayi shaking dinsa.

“I’m Laylah and you young lad?”.

“I’m muhammad Fadeel but it’s safe to call me Chuchu”. Dariya tayi tana mamakin shegen wayon yaron.

“How old are you?”. Be yi magana ba sabida popcorn inda ya cika baki da, yatsu Bakwai kawai ya nuna mata ita kuma ta gyada kai alamar ta gane.

“How about you?” Ya tambaya da ya gama taunar. Ruwa ta miqa mai kan ta basa ansa.

“I’m 26”.

“You’re biiiiiiiiig”. Dariya tayi kawai. Yaron ya shiga ran ta sosai. Shuru suka kuma yi kan yace mata wai tayi musu hoto a wayan ta. Ciro wayar tayi ta fara daukar su selfies yana ta yin funny posts. Kwata kwata ta mance da zancen wata Yasmeenah sai da wayar ta ta fara ringing taga ita ke kira.

“Ina kuma kika shige kika barni”. Yasmeenah ta tambaya. Laylah ta kwatanta mata inda suka zauna. Kan ka ce mai sai ga Yasmeenah a gun. Buda baki tayi cike da mamaki da ta isa taga Laylah tare da dan yaro sai kashe hotuna suke ta yi abunsu basu ma lura da isowar ta ba.

“Yaron wa kika samo?”. Yasmeenah ta tambaya.

“Is she your mom?”. Fadeel ya tambaya yana kallon Yasmeenah “Can I call you grannie?”.

“Kai! Kiji yaro zai mai da ni tsohuwa. Call me Yasmeenah”. Ta fadi tana wasa da gashin kansa wanda ya taru sosai. Sake tambayar Laylah inda ta sama yaro tayi ita kuma ta kwashe komi ta fadi mata. Ita kam Yasmeenah lokaci guda tajo yaron ita ma ya shiga ran ta. Zama tayi ta sa shi a cinya tana ta mai wasa tace Laylah ta musu hoto tare.

Shikam Abdulmalik yana can daga zuwa ya ansa waya ya barwa Tariq amanar Fadeel amma kuma da ya gama wayar ya dawo sai ya izza babu Tariq bare Fadeel a inda ya bar su. Wayar Tariq din ya dinga kira amma kuma baa dagawa duk hankalinsa ya tashi. Tunani ya fara koh anyi kidnapping dan sa ne. Nawfal wanda suka bari a gida ya kira kai tsaye yana tambayar sa koh Tariq da Fadeel sun dawo gidan ne amma yace mai aah. Hankalinsa ya da da tashi ya ce wa Nawfal ya same sa da sauri a park din, yana tunanin kidnapping dinsu aka yi. Be zauna ba ya cigaba da Juyawa cikin park din yana neman su amma shuru har Nawfal ya isa.

Shima kam Tariq tsurewa yayi, daga an bar masa yaro, Fadeel ya matsa mai ya sa tsiwa wai sai sunyi playing hide and seek kuma in ya ci sai ya siya mai play station. Ba yadda ya iya, haka nan ya yarda saboda tsananin nacin Fadeel. 30 minutes kenan tunda Fadeel ya ruga wai dun ya buya amma shuru be gansa ba. Gashi ya mance wayar sa a mota bare ya ce zai dauko ya kira Abdulmalik yaji koh Fadeel na tare dashi. Kwata kwata tunanin ya je ya dauko wayar a mota be zo masa ba kawai yawo yike ta yi cikin park neman yaro. Ya san kashin sa ya bushe indai ya koma gun Abdulmalik ba tare da Fadeel ba. Sanin kowa ne yadda Abdulmalik ke matukar ji da dan nasa. Gudun kada wani abu ya same sa ne ya sa ya hana a sa shi a makaranta instead ake zuwa gida koya mai karatu. Tariq dai yayi ta yawo yana gumi.

Shikam Fadeel na can yana ta wasa da su Laylah, duk ya bi ya cika su da surutu. Suna ta cin dariya, duk dan yaron ya saci zuciyar su har lokacin ya wuce basu ankara ba kuma tunanin ce masa ya tafi gun iyayen sa be zo musu ba. Suna cikin hirar su da Fadeel, yana basu labarin elephant inda ya gani na fada da monkey lokacin da yaje India holiday, wai har elephant din ya nemi ya zaune cikin monkey din amma ya shiga ya raba su kawai suka ji an kwala ihun sunansa.

“Muhammad Fadeel!”. Koh da zasu wuce gida, Yasmeenah ta miqawa key din mota ta ce mata ta tuqa. Jikinta duk yayi sanyi. Lumshe idanu tayi ta settling sosai a seat din motar. Koh da ta rufe ido, vivid picture din abunda ta gani earlier ne ke ta yawo a kanta.+

Suna cikin hira ne wani wai assistant din mahaifin Fadeel ya hango su ya zo daukar yaron. Da gudu Fadeel ya miqe, ya manna wa Yasmeenah kiss a kumatu, ita ma Laylah ya juyo ya yi hugging dinta sannan ya manna mata kiss a both cheeks dinta.

“I owe you”. Ya fadi kan ya ruga. Juyawar da yayi ya ruga da gudu ne Laylah ta lura da rubutun da aka yi a bayan Tshirt dinsa……. *Fadeel Al-Haydar*. Koh da ya qarasa gun wanda yazo daukar sa, ta ga ya rada wa mutumin abu a kunne sai mutumin ya ciro pen da wani dan kamar complimentary card da aka basa ya bawa yaron. Juyowa Fadeel yayi ya dawo da gudu yana magana numfashin sa sama sama saboda gudun da yayi.

“Yo…your nu…mber”. Ya miqa mata dan card din da pen. Bata iya cewa komi ba kawai ta rubuta mai number dinta ta basa. Da gudu ya ruga akai akai yana Juyawa yana daga musu hannu har ya bace musu da gani. Qarar horn inda Yasmeenah ta saki wa wani me keke napep ne ya dawo da ita reality.

“Hmmm Yasmeenah”. Ta kira sunan a hankula.

“Yes bae”.

“Yanzu wancan yaron dan khalifa Al-Haydar ne?”.

“Do you need to question me again? Tun yaushe Google yayi confirming mana dan sa ne. Muhammad Fadeel Al-Haydar”.

“Fadeel yace da Babansa yazo park din. Kenan we were close to meeting khalifa Al-Haydar”.

“Ke fa wannan obsession din ya fara yawa. Dan Allah ki mance wannan Al-Haydar din. Ya sha karfinmu”. Shuru ta yi ta cigaba da nazari har ta ciro waya ta fara kallon hotunan ta da Fadeel. Yaron ya tsaya mata a rai sosai. Sannan kuma wannan mutumin da yazo ya dau yaron ta san ta taba ganin sa a wani gu amma kwata kwata ta rasa inda ta taba ganin sa gashi ta fadi wa Yasmeenah ta karyata ta, wai maybe deja vu ne kawai. A haka suka isa gida ba me cewa kowa komi. Laylah na Wucewa dakin ta ta fara shirin kwanciya kasancewar the next day a very busy day for her.

Haka rayuwa ya cigaba, Laylah nata aikin ta. Aside from sayar da jikinta, Laylah tana da cover business wanda take wa iyayenta karya dashi. Tana events planning and management wa mutane in suna da sha’ani especially kuma mutane na alfarma, masu naira. Daga nan kuma atimes take haduwa da manya mutane, kusoshin qasa.

Ranar da aka sa na fundraiser event din ya iso. Kowa ya so aikin da Laylah da team dinta suka yi. Yadda tayi planning event din ya burge kowa and Alhamdulillah masu kudi da yawa da politicians sun halacci tarun dun haka aka sama donations da yawa. Zuciyar ta fara bugu tayi sosai da sosai da taji an ambaci sunan Khalifa Al-Haydar, cewa be sama damar zuwa taron ba amma ya aika aminin sa Nawfal Muhammad Fadoul yayi representing dinsa. Daga kai da Laylah zata yi ta hadu da abun mamaki.1

Rufe idanunta tayi ta kuma budawa dun confirming koh what she was seeing was really a reality. Abdulmalik ne tsaye a gefen Nawfal suna ta gaisawa da mutane. Koh da ya dago idanunsa basu fada koh ina ba sai a kan Laylah. Nan suka tsaya suna ta kallon juna. Miqewa tayi jiki babu sauran karfi ta fara tafia. Kawai tuno last day dinsu tayi a Australia and all that ensued between them taji kunyar sa ta kamata. Gani take kamar bata kyauta mai and in ta tsaya a gun sanin yana kusa, da wuya ta iya controlling emotions dinta dan koh a lokacin da ta gansa, ji tayi kamar ta ruga da gudu tayi hugging dinsa, ta fadi mai how much she missed him. Ji kawai tayi an riqo mata hannu.

“Bamu gaisa ba zaki wuce. Haka kika tsane ni? Koh hello ba zaki iya tsayawa ki mun ba? Koh kina kunyar aga kina magana da driver ne”. Ta ji muryar that she had been longing to hear for weeks. Dogon ijiyar zuciya ta sauke kan ta juya tayi facing dinsa. Ta kai minti biyu duk ta rasa me zata ce mai kawai sai tayi following instincts dinta. Jawosa tayi jikinta tayi hugging dinsa lightly. A hankali ta sauke ijiyar zuciya, taji lokacin daya hankalinta ya kwanta. Kanshin cologne dinsa me dadi tayi ta shaqa taji kamar kar ta sake sa amma kuma da ta tuno islamically it’s not right tho wasu suna yi, ita ma tana cikin masu yi tunda ita har jiki take sayarwa bare kuma wani hug. Sai dai kuma bata san wani kalar mutum ne shi ba tho lifestyle dinsa clearly shows how social and western he is kuma gashi cikin mutane suke.

“I’ve missed you”. Tayi saurin zame jikinta daga nasa “Sorry if I was too forward, I was just overwhelmed by your presence”.

“Shhhhhh” ya sa mata yatsar sa a baki. “I’ve missed you more”. Ya fadi yana mata irin murmushin nan da ke hanata barcin dare. Wani sonsa ke da da shiga zuciyar ta. A da, she was living in oblivion, Kullum tana yaudarar kanta cewa ba sonsa take ba amma tun dan months inda suka yi basu ga juna ba ta tabbatar da lallai sonsa take, Sosaima kuwa ba kadan.

“Shine baka neme ni ba?”. Ta fadi tana dan bata rai.

“Ke fa kika nuna baki son na neme ki. Ba ajinki bane yawo da driver”.

“Ni nace maka haka?”. Ta fadi tana rolling idanu. Dariya yayi kan ya bata haquri a zuciyar sa kuma yana ta murna ne. What she just did ya tabbatar masa da cewa abunda yike feeling for her isn’t one sided, ita ma from all indications she feels something similar.

Sannu a hankali suka taka zuwa parking lot, inda Laylah tayi parking hadaddiyar motar ta me qirar BMW. Buda motar tayi suka shiga suka bar kofofin a bude sabo da tsananin zafi da motar yayi. Sun jima a zaune ba wanda ke cewa kowa komi sai dai su dan saci kallon juna. Ita ta fara buda baki ta yi breaking silence din.

“How has life been?”.

“Alhamdulillah”. Murmushi tayi kawai bata ce komi ba kuma. “Soooooo are we still buddies?”. Ta tambaya.

“Depends on you, in baki damu da zama friends da mere driver ba”.

“What if I don’t want friendship?”. Ya tambaya. Shuru tayi ta dade tana nazari kan ta buda baki tayi magana.

“I’m cool with it. Just say the word and I promise to disappear without a trace”.

“Oh really”. Ya juya ya Kalle ta da kyau yana daga mata gira. Lura yayi da expression din da ke fuskar ta, kamar ya sanja. “So as I was saying”, ya tsaya ya san gyara murya “What if I want something beyond friendship?”.

“Something like?”. Dariya yayi kawai be ce mata komi ba. Pen inda ke breast pocket dinsa ya ciro ya jawo hannunta ya rubuta number dinsa a kan tafin hannun. “Call me when you have the answer, and remember i’ll be cool with whatever your response is. Fi waqt akhar”. Ya fita ya rufe mata door din motar. Tana kallo ya wuce cikin hall inda ake fundraiser event din koh Juyowa ya sake kallon ta be yi ba. Kai kawai ta ije kan steering wheel din motar zuciyar ta na mata saqe saqe iri iri ga wani irin sonsa da ke da da shiga ran ta.

One thing she has noticed about Abdulmalik is that gashi dai talaka amma sai shegen attitude. Gashi da charisma and wani aura na power da yike da. Duk sanda zai yi magana, babu tsoro bare fargaban wani abu ya faru yike yi. Maganar ma in zai yi sai ya dau lokaci yana nazarin words inda zai furta, Yanga dai da jan aji akwai shi sosai a gun sa. In ba Abdulmalik ba, wana driver ne har ya kai yawa Laylah magana the way he just did. Murmushi kawai tayi, arrogance is a quality she had always adored in men. Rufo door din gefen ta tayi ta ja motar ta zuwa gida mind dinta too preoccupied with thoughts. Sai da ta kai gida tukun ta kira P.A dinta wanda ta bari a can gun event din.

Abdulmalik kuma tunda Tariq ya dawo dauke da Fadeel a kafadar sa suna wasa ya hau mai fada akan irin tsoron da suka basu. Shi dai Tariq be ce komi ba yayi ta bada haquri. Fadeel ne ya fara bawa mahaifin nasa labarin new friends inda ya hadu da. Tariq be ce komi ba sai da ya bari suka shiga cikin gida tukun ya nufi hanyar study din Abdulmalik inda ya same sa har ya shiga ya kama aiki a computer dinsa.

“Sir….”.

“Yes Tariq…. what’s the problem?”. Ya tambaya.

“Ummm ba wani serious abu bane”. Ya fadi yana sosa kai “dama…..”.

“Look Tariq I don’t have all day, dama me?”.

“The lady little master was talking about, it was her sir. Laylah, the lady from Australia”. Dago kai Abdulmalik yayi yana kallonsa.

“Laylah? You’re sure of that?”.

Throughout ranar Laylah ta rufe kan ta a cikin bedroom dinta ba abunda take in ba kallon palms in ta ba inda Abdulmalik ya rubuta number dinsa. Ba karya tana son sa amma tana gudun abun da zai biyo baya in ya gane koh ita wacece. Bata ganin zai yi accepting dinta a yadda take, bata so kuma ya fara tsanarta. Bata so kuma ta fara soyayya dashi daga baya su rabu dun tana gudun ya kawo maganar aure. Haka ranar ya gushe tana cikin daki tana ta tunanin, ta qulla wannan ta kunce wancan. A karshe ta miqe ta wuce wanka. Har saura kadan ta fara durzan hannu ta tuna da number din a haka ta koma bedroom ta dau karamin wayarta ta rubuta number din kan ta dawo ta fara wankan ta.2

Abdulmalik shuru shuru yana ta jiran response daga Laylah amma yaji shuru. Da ka gansa ka ga wanda ke cikin damuwa. Ya rasa ya akayi son wannan Laylah ya mamaye zuciyar sa har yike ganin dole ya mallaketa. Har ya fara tunanin bata matsayin mahaifiyar Fadeel ta hanyar auran ta indai zata amince. Gashi dan nasa tun randa ya hadu da ita a park ya kasa daina hirar ta. Kullum Laylah this, Laylah that, in yana yi wayancewa kawai Abdulmalik yike kamar be san ta ba ya ta sauraron yaron.

Zaune yike a study room dinsa da laptop dinsa a kunne a gabansa. Yana cikin aiki ne amma ya fada nazari, tsananin tunani har Nawfal ya shigo ya zauna gaban sa for about 15 minutes be sani ba har sai da Nawfal din ya dan tabo sa.

“Wai tunanin me kake ne haka?”.2

“When did you arrive?” Ya tambaya dan uwan nasa.

“Kusan 30 minutes fa amma baka ma sani ba hankalin ka na can kana ta tunani”. Ya fadi ya qure Abdulmalik da idanu sai kallon sa yike ta yi.

“Abdulmalik you love her”.

“It’s that obvious?”. Ya tambaya yana dariya “wallah Nawfal ban taba tunanin after Fati akwai macen da zata shiga zuciya na ba. Ji nike I can do anything to have Laylah”.

“A relationship based on lies? Abunda kake so kuyi kenan? Don’t you think it’s high time ta san koh kai wanene, it’s obvious ita ma neman ka take. Infact ba ita daya ba, Abdulmalik duniya ya kamata su san who the real khalifa Al-Haydar is. For how long?”.

Dogon numfashi Abdulmalik ya ja sannan ya sauke ijiyar zuciya kan ya kalli Nawfal “ka san meyasa nike boye identity na?”. Ya tambaye sa. Kai ya juya mai alamun aah be sani ba.

“Na dade ina tambayar ka ai”.

“I have my own reasons for hiding it from you all, harta Begum bata sani ba”. Sai da ya dukar da kansa qasa kan kuma sauke ijiyar zuciya ya fara ba Nawfal labarin yadda aka yi.

Let’s take a walk down to 8 years ago…….. on the night of 1st January.

A daren 1st January everywhere was blasting with celebration na shiga sabon shekara. Mohammed Mumtaz Al-Haydar yana cikin hotel room dinsa a babban hotel inda ya sauka a united Arab Emirates. Shiri yike dan zuwa wani new year dinner da wani business partner dinsa balarabe yayi organising. Masu aiki maza guda biyu ne a kansa wanda duk sanda zai yi tafia suna tare dashi. Daya na daure lace din takalmansa while daya yana daura mai tie. A haka Abdulmalik ya shigo da fara’ar sa ya izza Babansa.

“My king”. Mohammed ya fadi yana murmushi. Dama tun randa begum Sahar ta basa labarin daukar ciki ya fadi mata indai Allah ya basa yaro zaya basa suna Abdulmalik, his king, the king of khalif airlines and group of companies. In kuma mace ce she’ll be Malikah, his queen and the princess of khalif airlines and group of companies. Ita kuma begum Sahar ta fadi mai ta dade tana son sunan “Khalifatullah” dan haka in suka haifi dan su zata dinga kiransa da Khalifatullah.

“Har ka gama shiri?”. Ya tambaya dan nasa.

“Yes father. Mamu na jiranmu a qasa”. Ya fadi mai. Cikin hanzari Mohammed ya gama shiri ya riqe hannun dan sa suka sauka qasa inda Al-Mubaraq ke jiran su. Mohammed ya dau Al-Mubaraq tamkar qani, ba kowa bane ya san ba abunda ya hada su illa mutunci. Cikin fara’a Al-Mubaraq din ya gaida uban gidan sa da kuma dan sa sannan suka wuce.

STORY CONTINUES BELOW

A gun dinner din ne Mohammed Mumtaz Al-Haydar yayi making announcement cewar daga yanzu zai sauka daga kujerar CEO kuma insha Allah dan sa Abdulmalik khalifa Al-Haydar ne zai gaje sa, inda dan uwansa Ishaq wanda aka yi adopting dinsa tun suna yara ya nuna be yadda da decision din wan sa ba, ya zaa yi Abdulmalik ya zama magajin Mohammed bayan shi yana da rai . Washe gari da sassafe suka koma Nigeria a inda Mohammed Mumtaz Al-Haydar ya kuma qara kiran cabinets dinsa emergency meeting dan signing dim handing over documents din khalif airlines and group of companies to his son a nan ma Ishaq yazo rai a baci koh walwala babu. Ranar kowa ya halacci meeting din with the exception of Al-Mubaraq wanda shi dama an riga da an saba da fashin sa. Ganin babban matsayin sa a kampanin ya sa yike wasa da zuwa aiki duk yadda yaga dama.

A gun meeting din ne Mohammed ya bada umarni da a basa ruwa saboda glass inda ke gabansa ba ruwa, ya shanye. Wata ýar waitress ta taho tana tafia tana yanga ta miqa mai wani glass din ruwa. Ya karba yana mata murmushi ya shanye ruwan. Shan ruwan ke da wuya aka ga ya fara cije cije ya sa hannayen sa biyu a chest dinsa. Kan ka ce mai ya zuba a qasa jini na zuba ta baki, ta hanci. Abdulmalik da ke kusa dashi ya ruga da gudu ya riqo babansa. Shikam Ishaq yana tsaye yana kallon wan sa nata aman jini.1

“Go after that waitress! Now!”. Ya daka tsawa kan ya dau babansa aka ruga waje da shi da gudu. Koh da bodyguards din suka fita babu ita ba labarin sa. Nan aka wuce da Mohammed hospital inda aka ije sa a wani confidential room sannan aka hana a sanar da press dun baa son labarin ya isa jama’a. For 2 days aka hana kowa ganinsa sai rana na uku ya bada umarni akan a kira mai dan sa.

Abdulmalik na shiga ya kalli Babansa kawai hawaye suka kufce masa.

“Aah kai kuma, kada ka zama rago mana. Abunda mahaifiyar ka ta hane ka dashi tun kana yaro shine ka zo zaka yi dun bata kusa koh. Maza share hawayenka”. Ya fadi a hankula, muryar sa da kaji ka san yana cikin wani hali.

“Matso kusa”. Ya fadi yana nuna ma dan nasa gefen gado, yazo ya zauna. Yana zama mahaifin sa ya riqe masa hannu. “Take care of Sahar, she’ll be distraught at the news of my death”.

“Abba….,”. Abdulmalik ya kira sa yana kuka “please stop this, i’m trying to process your trip abroad”.

“Shhhhhh the poison has spread, it’s late. Mutuwa zanyi. Pray for me, that’s all I need right now”.

“Lokacina yazo Abdul. But before I go you should know this; kasan mutanen da zaka yi harka da, ba kowa da ke dariya da kai ne ya zama masoyin ka ba. Ba abunda dan Adam bazai yi ha dun dukiya. An kawar dani ne saboda handing over in business da nayi into your name, and I bet you’re the next target, dole ka kula. Don’t let the Al-Haydar empire fall into the wrong hands. Kaga 40 years ago, mahaifi na na a ranar da yayi handing over group of companies dinnan to my name, a ranar aka yi assassinating dinsa and yanzu gashi nima haka. Dan Allah ka kula, mahaifiyar ka ka kula da ita. Ba sai ta san abunda na fadi maka ba..,., she’ll worry unnecessarily. “. Ya tsaya tari ya riqe sa.

“Khalifa Al-Haydar should be…..a….a…. mys…..mystery t… to the world. Kada kayi trusting mutane blindly, kaga kawun ka kiri kiri ya nuna disapproval akan handing over the position of CEO to your name, na gida ma kenan suna ma bakin ciki. I know who is responsible for this, na san wake son kashe ni, kuma na san kanka zai dawo, plea….se son ka kula”. Ya kuma tsayawa tari. Abdulmalik kam sai kuka yike yana mai sannu yana tambayar sa sunan wanda ya mai wannan muguntar amma inaaa har rai yayi halin sa. Sai doctors kawai suka shigo suna basa haquri. Shi dai a ransa yana kyautata zaton adoptive brother din babansa ne zai aika ta wannan mummunar aikin tunda dama tun asali kawu Ishaq ya kasance mutum mara imanin a tsoron Allah.

Back to present……

“Tun daga ranar na fara boye identity na, na rage yarda da mutane, and tun daga ranar 8 years ago na fara undercover research a kan wanda ya kashe Abba. I’m close to getting the culprit kuma ina kyautata zaton shi koh su ke satan funds din company”. Ya fadi wa Nawfal lokacin idanunsa sun rikida sun koma jazur.

“Bu….but aka ce uncle died of a heart attack”.

“Abunda nace wa doctors su sa a death certificate dinsa kenan amma Mohammed Mumtaz Al-Haydar was poisoned to death. His death was planned most definitely by his brother, brother inda ya dauka ya maida shi mutum”. Nawfal ya shiga tashin hankali, mutuwar uncle dinsa, wan mahaifiyar sa sai ya dawo mai tamkar sabo. Tun yana yaro ya shaqu da kawun nasa wanda shi ya tsaya masu matsayin mahaifi lokacin da nasu mahaifin ya mutu suna yara. Bayan rusuwan mahaifin su da shekara biyu mahaifiyar nasu ta kwanta barci bata kuma tashi ba. Tun lokacin iyayen khalifa suka zama musu iyaye, Begum ta riqe su tsakanin ta da Allah da zuciya daya. Shi da kannensa mata guda 3.

“Yanzu what’s the next step?”. Ya tambayi Abdulmalik.

“Very soon, the world will get to know the true khalif Al-Haydar, for now dan Allah ka cigaba da misleading mutane”. Ya roqi dan uwan nasa. Nawfal be ce komi ba ya ja khalifa jikinsa yayi hugging dinsa.

“Koh rai na kace na cire na baka wallahi khalifa i’ll gladly give it to you. Halaccin da kuka mun da kai da iyayenka bazan taba mance wa ba”. Ya fadi yana kuka.

“Ya isa kan Begum tazo ta ganmu hankalinta ya tashi”.

Murmushi yayi ya share hawayensa. “Toh Laylah fa?”.

“Ita ma very soon zata gamu da Khalifa Al-Haydar inda ta dade tana nema”. Ya fadi yana wata ýar dariya “send an invite over to her, a private invitation. Sannan ka bada umarni a gyara the most expensive suite a Khalif empire for the meeting”.

“Man! What are you planning?”. Ya tambaya.

“It’s confidential. Wannan meeting din shi zai determining future dinmu, if I have a future with her or not. It means a lot to me”.

Ita kam Laylah tsawon kwana uku ba abunda take yi in ba tunani ba har dai finally tayi making up mind dinta. Waya ta dauko ta tura mai text.

*I finally have an answer, let’s have dinner together. It’s on me*. Ta tura.

Sai da ta jira reply dinsa kan ta tashi ta fada bandaki domin fara shiri.Abdulmalik ya riga ta isa restaurant din dun haka ya zauna shuru yana ta danne danne a wayar sa har ta iso. Kanshin turaren ta kawai ya isa ya sanar dashi da isowar ta. Dago kai yayi ya Kalle ta yana murmushi.+

“It’s safe to call you babe, isn’t it?”

“Not so fast mister”. Ta fadi tana dariya.

Zama tayi suka gaisa kan waiter yazo da menu suka yi selecting abunda zasu ci. Har suka kusa gama cin abinci bata dago zancen ba shikuma Abdulmalik duk he’s restless, ya qosa yaji response dinta.

“Sooo….”. Ya buda baki ya fara magana. Kallon shi kawai tayi ta dan yi murmushi. Abdulmalik akwai rashin haquri, tunda ta iso ta lura da cewa ya qagu yaji answer dinta.

“In tambaye ka mana”.

“Allah sa ina da ansar tambayar ki”.

“Wani irin so kake mun?”. Sai dai Abdulmalik ya dau lokacin sosai yana wasa da juice inda ke gabansa, yana ta juya juice din da straw inda ke ciki. “So na tsakani da Allah”.

“Hmmmmm Laylah how do I explain how I feel to you? Without you my heart is always anxious. A da nayi tunanin after loosing my wife bazan taba son wata ýa mace ba a duniya not until I met you, komi ya sanja. Na rasa yadda nike jin ki a zuciya na”. Sai da ya tsaya ya dan jan numfashi kan ya cigaba.

“I’m not saying all these to deceive you, koh kadan ban zo da yaudara ba. Subconsciously, my heart chose the path that leads to your heart, nayi nayi na danne zuciya na, nayi suppressing feeling din but i’m only human, I can only fight against destiny but never can I change it. Abu daya nike nema a wajen ki; amincewar ki, ni dai talaka ne, i’m not rich but I promise to treat you like a queen, sai kin zama abun kishi a cikin mata ýan uwan ki, under the sun I promise to be your shade, in the rain i’ll be your umbrella, i’ll be your best friend, your support system. I’ll be your soldier and fight all your battles, i’ll be a shoulder you can always lean on, duk madubin da ba fuskar ki ban kallo, duk abunda baki so bani so, duk wanda ya bata miki rai sai ya hadu da fushi na, ke kadai zaki zama tauraruwar da ke haskaka rayuwata and i promise the next lady i’ll love this way will be our daughter insha Allah……”. Be yi niyyar tsayawa amma hawayen da yaga tana zubdawa ya sa dole ya tsaya. Rarrashin ta ya fara tare da miqa mata hankie.1

“Did I say something wrong?” Ya tambaya “I’m sorry…..”.

“Shhhh”. Ta sa hannu a baki “You talk alot”. Ta saki ýar murmushi idanunta cike da kwalla.1

“It feels so good….. The feeling of being loved. Na mance when last nayi feeling that way”. Ta fadi mai tana goge hawayen da ke zuba a kan kumatunta. “I love you Abdulmalik, right from day one. Ban damu da class dinka ba, ban damu da rashin dukiyar ka ba, duk ba wannan bane a gabana amma sai dai I don’t see a future for us. Bana tunanin zaka iya zama dani, bana taba tunanin zan taba samun acceptance from you after knowing my true colours. And it’s a shame i’ll lose the love and companionship of someone like you amma wallahi ka san cewa ba dun baka da kudi bane nake qin ka. Har ga Allah ina son ka amma…..”. Bata kai da gamawa ba ta kuma fashewa da kuka. Be ce mata komi ba yayi shuru yana kallon ta kawai. Sai bayan kamar 10 minutes ya buda baki ya mata magana.

“What if I’m ready to accept you the way you are? Zaki yarda dani? Nifa Allah ban zo da wasa ba, so na gaske nike miki. Kinga dai ni ba yaro bane, bazan yaudare ki ba”.

Murmushin takaici ta saki kan ta basa ansa “Abdulmalik kenan, I doubt you’ll accept me after hearing everything”.

“How about you try me. Wallahi I won’t judge”. Sai da tayi dogon nazari kan ta basa reply.

STORY CONTINUES BELOW

“Shikenan, how about we meet this weekend. I promise zan fada maka komi, koh karya daya bazan sako a ciki ba. In kaji komi then you decide if you still love and will accept me me for who I am”. A haka suka rabu. Sai da ya tabbata ta daina kuka kan ya rakata inda tayi parking mota ta shiga. Tayi tayi ta rage mai hanya amma ya qi.

“Shikenan sai da safe”. Ta fadi da dan murmushin ta sannan ta shiga mota.

“Laylah”. Ya kira sunanta kan ta rufa qofa.

“Yes?”.

“Take care”. Murmushi kawai tayi tace mai “you too”. Zuciyar ta na saqe saqe iri iri ta tuqa mota har gida.

Tana shiga taji gidan da dan hayaniya tana ta mamakin baqin daren da suka yi kawai sai taji an fado jikinta.

“Auntie! Auntie”.

“Hey young lad! You’re all grown up”. Ta fadi tana wa dan yaron wasa da gashin kansa. Reyhaan ne jikan Yasmeenah. “When did you arrive? Where’s your mommy and Amaan?”. Ta fadi tana riqe da dan yaron dan shekara takwas a kafadar ta.

Da hanzari ta qarasa ciki tana kwala ihu “leeeeeeeeek”. Tayi ta kira da karfi. Tana hango ta ta fada jikinta tana kukan murna. Ta dade bata gan ýar uwan ta ta ba wadda ta zama tamkar babbar yaya gare ta. “Shine baki fadi mun zaku zo ba, where’s my new niece?”. Ta tambaya referring to baby inda leek ta haifa wata uku da suka gushe.

“I wanted to surprise you. Sorry”. Leek ta fadi tana riqe da kunnuwanta.

“Yara na sun girma”. Ta fadi tana kissing din Amaan kanin Reyhaan, wanda daga shi sai baby inda aka haifa. Murna ranar a gun Laylah da Yasmeenah baya misaltuwa. A cikin wannan murnar ne kuma sai ga me gadi ya shigo wai wani yazo neman Laylah.

“Ka shigo da shi waiting room”. Ta fadi wa me gadin kan ta wuce dakin ta ta samo dan veil ta rufe kanta ta fito waje. Koh da ta isa waiting room din sai ta sama wannan mutumin ne da yazo ya dauki Fadeel the other day a park. Nan da nan ta ganesa, suka gaisa fuskar ta a sake kan tayi wa masu aiki umarni da a kawo mai refreshments.

“Lafia kuwa da dare haka. Ya aka yi ma ka gane gidan”.

“I must say the Al-Haydar’s are well connected”. Ya fadi yana murmushi. Ita ma murmushin tayi bata ce komi ba tana mamakin ziyarar sa. Sai da ya dan zauna kan ya miqe ya bata wani dan invite.

“This is a personal invite from khalifa Al-Haydar”. Ya fadi “He wants to show his appreciation on behalf of our young master”. Ya fadi mata. Ita dai ji kawai tayi kamar a mafarki wai abun da ta dade tana nema yazo har gida cikin sauki ya same ta. Kwalban wine ya miqa mata sannan yayi mata sallama ya wuce. Yana Wucewa ta buda dan envelope inda invite in ke ciki. Card din farko ta fara dubawa…..

*Trade at Al-Haydar empire. Friday night, 8:00Pm sharp💋*

Second card din kuma kamar pass ne wanda a jikinsa akwai secret code da ba kowa ya sani ba. Fadawa tayi cikin lush leather seat inda ke waiting room din. Mutuwar zaune tayi dan jin kanta take kamar a dream. Har tsawon 20 minutes ta kasa komi sai da Yasmeenah taji shuru ta biyo ta. Koh da Yasmeenah ta shigo ta izza ta ansan envelope din kawai tayi ta duba abunda ke ciki ta sa ihu.

“Yarinya me goshi”. Ta fadi tana guda “In my 35 years of being in this business ban taba ganin yarinya me farin jini irin naki ba”. Ta fadi tana ta murna.

“Ai sai mu shiga ciki in fara shirya diyata, Khalifa Al-Haydar ya wuci wasan yara”.

“It’s such a pity mother”. Suka jiyo muryar leek “Tunda nayi hankali ba randa bana addua Allah ya kubutar daku daga wannan hanyar da kuka zabawar kanku amma a ina. Jibi yadda kike murna dan anyi mata tayin sayan jikinta”. Ta fadi cikin hawaye.1

“And you little sister….. is this the path you’ll tread on forever? Yaushe zaki gane wannan rayuwar bata kamace ki ba”. Ta fadi sautin kukan ta na qaruwa. “Bazan iya zama da ýaýana a nan ba. My mistake for coming home, ina tunanin koh in kika ga  jikokin ki zaki yi hankali amma inaa old habits never die…”.

“Kullum mamakin ki nike Yasmeenah, ni meyasa baki sa ni a wannan sana’ar ba? Amma kike sa yaran wasu?”.1

“Big sister….”. Laylah ta buda baki tayi magana amma ta kasa.

“Zan bar gidan nan, this night itself and wallahi bani kuma dawowa sai randa kika shirya barin sana’ar nan kuma kika kaini gidan ubana. Kin ce ba ta hanyar banza kika haife ni ba amma ubana fa? Meyasa ba zaa nuna mun shi ba? Meyasa koh sunansa ba zaa fadi mun ba?”. Suna ji suna gani leek ta ja ýaýanta wanda har sun fara barci suka wuce. Yasmeenah kam jiki a sanyaye ta wuce dakin ta, ita ma Laylah ta wuce nata dakin. Daren ranar kasa barci tayi.1

Shikam Abdulmalik tunda ya koma gida yike ta tunani, duk ya ji ya kasa barci dun haka ya dauko waya yayi dialling number din Laylah. Lokacin ita kuma har barci ya dan fara gaba da ita.

“Hello” ta ansa wayar in a groggy voice.

“Na tashe ki koh?”. Murmushi kawai tayi wanda ya yasa zuciyar sa jin wani sanyi. “I just wanted to hear your voice, now I can rest in peace”. Ya fadi.

“Sleep well”. Ta ce mai.

“You too…. I love you”. Ya fadi ya kuma ji ta saki wani murmushi. Shima murmushin yayi kan ya ije wayar.

Ita kam Yasmeenah tun daren ran lahadi da diyarta ta fadi mata maganganu ta bar gida bata kuma fita daga dakin ta ba. Ba karya maganar ya sosa mata zuciya, ya kuma fama mata tsohon miki wanda ta dade da tunanin koh ya warke. In banda kuka da tunani ba abunda take yi. Da kyar Laylah ta iya samu ta rarrashe ta after 3 days.

“She hates me koh?”. Yasmeenah ta tambaya Laylah tana kuka a jikinta.

“No! I’ve never witnessed a mother-daughter bond like that of you guys. It’s natural for her to act that way”. Laylah tayi ta rarrashin ta. “Amma Yasmeenah I also think it’s high time ki ansa mata tambayoyin ta. Allah na tuba baa san gawar fari ba…..”. Bata gama magana ba ta miqe zata fita daga dakin. Har ta kai kofa ta juyo ta kira sunan Yasmeenah.

“Yasmeenah”.

“Yes love”.

“Al-Haydar will be my last operation. I think it’s high time for change”. Ta fadi a hankula sannan ta juya ta wuce.

Laylah na fita ta kira leek tace mata dan Allah su hadu a wani park kusa da hotel inda tayi lodging. Suna haduwa Laylah ta fada jikinta tana kuka tana bata haquri da cewar dan Allah su sasanta da Yasmeenah dan tana cikin wani hali. Ta kuma fadi mata duk abunda ke tsakaninta da Abdulmalik da kuma decision dinta na barin prostitution. Leek tayi murna kwarai sannan ta ba Laylah karfin guiwar fadi wa Abdulmalik labarin ta, tsakaninta da Allah banda karya.

A haka har ranar friday ya iso, ba randa Abdulmalik baya kira dun yaji muryar ta kawai, ranar da Laylah zata hadu da Khalifa Al-Haydar sannan kuma ranar ta na karshe a karuwanci. Tunda ta tashi da safe ta shige wani dan daki inda ta dau wani Ghana must go ta buda. Riga ce da zani duk sun kode har sun fara hujewa dun tsananin ijiya, da wani dan dankwali irin na fulani. Kallon kayan tayi ta dauka ta sa a jikinta sannan ta zo ta qura wa mirror kallo. Rayurwata a da kawai ta fara tunowa tana kuka sosai. Yanzu koh duniya zata nade bazata iya komawa yadda take da ba, the innocent and naive ýar Baba.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

 Hmmmm labari ya fara daukar dumi. Ku biyo a next chapter where the real drama begins. Many secrets will be unraveled.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *