JIRWAYE CHAPTER 6

JIRWAYE CHAPTER 6

            Www.bankinhausanovels.com.ng 

A haka barci ya kwashe Laylah. Jin shuru ya sa Yasmeenah bin sahun ta, ta san a duk lokacin da Laylah ke da meeting da client tana zuwa gun ta shiri amma kuma sai wannan karan taga sabanin haka so sai kawai ta bi. Tana isa ta izza Laylah ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa.

+

“Hey baby, wake up. It’s past 3 already”. Ta fadi tana shafa mata lallausar gashin ta. A hankula Laylah ta buda ido ta dan wa Yasmeenah murmushi. Ce mata taje tayi sallah Yasmeenah tayi sannan in ta gama ta same ta a dakin ta. Hakan aka yi. Tana idda sallah ta wuce daki ta sama Yasmeenah na ta hada ruwan wanka. Dago kai tayi ta ga Laylah ta zauna shuru ta qura wa hotunan da ke bangon dakin kallo, hotunan Yasmeenah ne da leek, tun tana karama har zuwa girman ta. Wani hoton kuma na leek ne da yaran ta. Murmushi Yasmeenah tayi kan tayi magana

“Special gyara zan miki yau, irin namu na ýan Borno”. (Shout out all my Borno folks🙌🙌).3

Dariya kawai Laylah tayi bata ce komi ba, hankalinta na kan hotunan. “Yasmeenah”. Ta kirata a hankula.

“Yes love”.

“I’ve known you for about 10 years now, amma koh so daya ban taba jin kin ambaci gida ba. You hardly talk about your relatives, all I know is ke shuwa ce from Borno nothing more, nothing…….”.

Bata gama magana ba Yasmeenah ta katse ta “Time for your bath, the water’s ready”. Ta fadi tana jan hanci alaman tana riqe hawaye. Laylah bata kuma pressing issue dinba ta tube shuru ta shiga qaton bathroom din ta zauna cikin bathtub wanda cike yike da ruwan turaren which was made out of sandalwood da jasmine flower. A haka ta zauna shuru ba mai cewa kowa komi, Yasmeenah ta dauko wani scented shampoo din ta wanke mata kai kan ta fito after spending about 30 minutes a bathtub din. Towel ta daura sannan ta daura wani karami a ka sannan ta fito ta zauna shuru a bakin gado. Yasmeenah ta fito ta kawo mata turaruka wanda zata bi jikinta dasu, dakin duk ya dau kanshi. Sai da ta gama shafa jiki kan ta koma vanity table,  Yasmeenah ta zo da hair dryer zata busar da gashin ta.

“I’ve never come across a lady as pretty and graceful as you are”. Yasmeenah ta fadi a hankula.

“Come on, duk da tsufar ki kin fa fi ni kyau. Kinga yadda maza ke kallon ki in muka fita kuwa”. Laylah ta ansa ta.

Sai da tayi dariya sosai kan ta buda baki tayi magana “I’m made for just one man”. Ta fadi kan ta tsaya ta goge hawaye. “Dazu you were asking about relatives, ina da ýan uwa amma almost 40 years kenan rabona dasu, rabona da gida since I was 15”. Ta fadi wa Laylah wadda ta zare ido cike da mamaki.

“Baki taba missing dinsu ba?”.

“I have, always. Da su nike kwana ba tashi a raina”. Shuru Laylah tayi cike da mamaki, Tabbas Yasmeenah ta dade tana kunshe da bakin ciki a ran ta wanda ta qi fitowa ta fadi wa kowa. Duk kusancin ta da Laylah ba sa ta taba opening up to her ba.

“As for Leek….. I swear Laylah she has a father. Me rufin asiri, dan gidan kirki”. Ta fadi mata.

“Toh ki fadi mata shi mana”.

“Ban san Inda zan nemo shi ba Laylah, be taba damuwa da mu ba. Ban tunanin zai iya tunawa da ni bare wata diyar sa”. Ta fadi hawaye suka kufce mata.

“Ba so na yike ba bare ita, gudan jinin sa. For 35 years I’ve been preserving myself for him, koh so daya ban taba siyar da jikina ba, I know that doesn’t make me a saint amma you can bear me witness Laylah, bana abunda ya wuce hada ýan mata da maza masu kudi. Leek kam iya gwargwado na bata tarbiyya, ban bari ta baci ba. Na mata aure…..”. Ta fadi tana ta kuka. Laylah ta juyo tana ta bata haquri. Sai da hawayen suka tsaya sannan ta cigaba da drying ma Laylah hair dinta.

“And I’m happy for you, zaki bar wannan rayuwar. You’ll start a new life. I’m very proud of you Laylah, ba kowa ce mace zata iya sacrificing abunda kika yi sacrificing ba, you’re a lady like no other. May you be happy always.”. Laylah ita ma kuka mara sound ta fara.

STORY CONTINUES BELOW

“So what are your plans?”.

“In na dawo gobe, zan fadi wa Abdulmalik gaba daya tarihi na. If he accepts me for who I am, zamuyi aure. I’ll be the best mother to his son. Zan tuba, i’ll finally go for pilgrimage, dama na dau alwashin bazan taba ziyartar gari me tsarki dabaibaye da Jirwaye ba, i’ll go for cleansing. Sannan zan raba dukiya na into 2, half zan ba Abdulmalik to start up something, to secure our future…… If there’s ever one. Dayan kason kuma zan cigaba da juyawa”. Yasmeenah ta ji dadin plans din Laylah sannan ta mata fatan alkhairi.

Ana gama busar da kan aka yi styling dinsa da kyau, lokacin ana neman karfe 7 kuma dama already P.A din khalifa Al-Haydar ya fadi mata cewa 7:30 on the dot driver zai zo ya dauke ta saboda boss ba mutum bane me son a bata mai lokaci. Sai da tayi isha ta sa kaya. Wani killer lingerie ne da Yasmeenah ta siyo mata, sabbi pul, red colour ta sanya. Sun mata kyau sun fito da curves dinta. A saman su ta sa wani black dress, dogon straight dress ne haka wanda ya dan kama jikinta yayi mata kyau sosai. Takalmin kafar ta shima black, gashi kafar ya sha anklet. Idanu kam sun sha kohl, lips dinta kuma ta zuba wani uban killer blood red lipstick. Ba kwalliya fuskar tam daga kohl sai lipstick inda ta sa amma ta fito tayi matukar kyau sosai. Jacket inda ta daura a sama shima black ne sai red clutch inda ta riqe a hannu. Sai 7:40 pm ta sauko, tana taku a hankula ga Kanshin turaren ta na tashi a ta ko wani angle.

Tana fitowa, driver ya sauko daga wata Shegiyar Mercedes Benz wanda ke da customised plate din Al-Haydar a jiki ya buda mata kofa yana gaidata. A hankula ta ansa sannan ta shiga gidan baya ya mayar da kofa ya rufe shima ya shiga nasa bangaren ya rufe ya fara jan motar. Saboda boredom ta ciro wayarta tana ta daukar selfie daga baya ta koma buga game sai dai gaba daya hankalinta ba akan game in yike ba. Ji tayi gaban ta na wani mugun faduwa, sai kace yau ta fara haduwa da manyan maza masu kudi, duk ji tayi she’s nervous. Bata san meyasa a duk sanda the name khalifa Al-Haydar is mentioned take jin wani faduwar gaba, without even meeting him, he’s already intimidating her, ina ga in an hadu. Cike da wannan nazarin suka isa Al-Haydar empire. Bata ma ankara an isa ba sai da driver ya buda mata kofa.

Sai da ta ja numfashi tayi wani dan guntun addua a zuci kan ta sauko motar tana murmushi ta shiga cikin makeken hotel din, wanda daya ne daga cikin businesses din Al-Haydar. Kuma yana hotels irin haka, masu girma kusan guda 5 a Nigeria banda wanda suke kasashen waje. Tana shiga lobby din ta isa counter da fara’ar ta.

“Yes ma’am, how may I help you”. Receptionist din ta tambaye ta cike da fara’a.

“A meeting with khalifa Al-Haydar”. Ta ansa.

“Any invitation?”. Ta tambaye ta. Ba tare da tace komi ba ta buda dan clutch dinta ta ciro wannan invite din da aka kawo mata ta miqa. Da receptionist din ta karba ta duba sai ta tambaye ta password.

Matsowa dan kusa da ita Laylah tayi ta rada mata ‘The heart of lucifer’. Murmushi matar tayi sannan ta miqa mata wani dan card a ciki wanda instruction ne a ciki sannan ta yi kira a waya sanar da Khalifa Al-Haydar da isowar baquwar sa. Bayan ta gama wayar kuma ta kirawo wani wanda kamar shima aiki yike a hotel din. Bata ce mai komi ba,  kawai password inda Laylah ta fadi mata ita ma ta fadi mai yayi coding saqonta. Sai cewa yayi Laylah ta biyo sa.

Tafiya suke har suka isa staircase amma sai taga basu dau stairs dinba neither did they take the elevator. Ita dai shuru tana binsa har aka isa wani qofa wanda biometric thumbprint dinsa yayi using ya buda qofar. Qofar na budewa suka shiga suka cigaba da tafia, har suka isa wani underground staircase.

Ita dai Laylah tana ta ganin ikon Allah, irin wanan security din duk for one man, saboda tsananin kudi, aji da matsayi. Bata ce komi ba har sai da suka sauka stairs din suka iso wani hall, daga nan yace ta yi tafi in ta kai end din hall din tayi taking left turn. Murmushi yayi sannan ya mata sallama ya juya. A hankula ta cigaba da tafia har ta isa left turn din, tana koh yin left turn din ta iso saitin wani qofa wanda aka rubuta “Confidential suite….. Khalifa Al-Haydar” a jiki. Tana cikin nazarinta ta ji muryan robot Jikin wani machine na magana.

“Welcome to the Confidential suite Laylah Jaan…..”. Baki ta bude cike da nazarin yadda aka yi machine din ya san sunanta. A zuciyar ta tana tsoron kada ta shiga ciki ta yi kauyanci. Bata gama yi nazarin ba ta kuma jin machine dun na magana.

“Once upon a time a poor woodcutter  wandered deep into the forest in search of wood to cut but came across a den of 40 thieves which he entered using the password……..?”

“Open sesame”. Ta fadi password din. Tana fadi kofar kofar ya buda.

“Welcome to khalifa Al-Haydar’s world”. Machine din ya kuma fadi. Wani sanyi sosai suite din ke yi ga Kanshin da ke tashi da wani dan soft music na the weekend na tashi a aha kula, ga ko ina duhu ba wani haske, candles ne aka kunna ba masu yawa ba.

“Hello… Laylah…. I am honey”. Ta ji an fadi. Wani irin ijiyar zuci ta ije tsananin tsoron da ya kamata. Tana juyawa taga wani robot ne a gefen ta tana magana. “Come this way, khalifa awaits you”.  Ta fadi, tana tafe Laylah na biye da ita har suka isa wani balcony shima ba wani haske sosai amma da dan wutan da ke illuminating a balcony din she could figure a man standing, sanye yike da suit ya juya musu baya, yana kallon dan glass window inda wajen window din man made garden ne, har da wani dan moon na karya a sama tunda ginin underground structure ne.

“You can leave now honey”. Ta ji ya fadi ba tare ya juyo ba. That voice, she knows the voice somewhere, amma a ina.

“Do have a great night boss”.

“I sure will honey”. Ya kuma fadi kan ya juyo.

“Hello Laylah…… Jaan”.Hello Laylah….. Jaan”. Tabbas koh a mafarki taji wanan voice din zata gane. Yadda yike kiran sunan. Abdulmalik ne, amma Abdulmalik? Me zai kawo sa wannan gun wanda shigar sa ma wani shegen wahala ne. Kai! Anya ba son sa da ya mata yawa a zuci bane yike sa take jin muryar kowa ma kamar nasa.

“We finally meet”. Ya kuma fadi. Wannan karon duk fluorescent light na suite din suka kunnu. Ido hudu tayi da mutumin da bata taba tunani zata gani ba. Abdulmalik. Wai me ke faruwa da ita ne? Wai dama haka soyayya yike? Harta fuskar mutane sanja wa yike ya zama mata na Abdulmalik. A hankula ta dan muntsili kanta just to confirm koh mafarki take.

“This is reality sweetheart, ba mafarki bane”. Ya fadi da irin wannan dariyar nasa.

“A…Ab….. Abd….ul m….alik”. Ta kira sunansa cikin in’ina duk ta rude, ta rasa me zata yi, ina zata sa kanta. Me ke faruwa da ita ne. Ita fa khalifa Al-Haydar tazo gani, ya kuma take ganin Abdulmalik, gashi yayi shigar masu kudi, duk ya sanja, ya qara wani murjewa yayi kyau.

“Ab….Abdul… malik”. Ta kuma kiran sunansa.

“Khalifa….. just khalifa. Khalifa Al-Haydar”. Ya fadi ya saki wata irin dariya, irin wanda mugaye ke yi a movies. Cikin tsananin rudu kawai ta juya zata wuce amma ta rasa ta wani qofa zata ma bi.

“Laaa karde ace tafiya zakiyi. Keda aka ce kin dade kina nema na”. Ya kuma fashewa da dariya. Juyowa yayi ta kallesa idanu cike da kwalla.

“Dan Allah ka daina. Abdulmalik me kake yi a nan”.

“Au kuka kike? Ai bama ki fara kuka ba yarinya”. Ya fadi wannan karon fuska a dake. Ita dai Laylah ta rude duk ta rasa abun yi. Sai da tayi tsayuwa kamar na minti 15 kafin ya matso kusa da ita ya miqa mata glass din ruwa sannan ya riqo hannunta zuwa ga dinner table inda aka hada masu, specially for 2. Sai da ya tabbata ta zauna tukun shima ya wuce ya zauna. Ba tare da ya ce mata komi ba yayi serving din kansa ya fara cin abinci. Ita dai Laylah ta rasa abun yi, mafarki take koh idanunta a bude suke ta kasa ganewa. Suite din shuru tsit ba motsin komi in ba na cutlery din khalifa ba yana cin abinci. Ruwa ta kuma zuba wa tayi refilling din glass dinta, kan kace me ta shanye ruwan, khalifa na satar kallon ta ta gefen ido amma be ce komi ba har sai da ya gama cin abinci. Bayan ya gama ya tambaye ta koh ita bata jin yunwa. A ina zata ji yunwa bayan tana cikin wani hali.

Da ta tabbatar me da cewa bazata ci ba sai ya tashi ya ce ta biyo sa, wani makeken living room suka shiga inda suka izza honey, sai da ya mata Bismillah ta zauna sannan ya nufi Inda robot din yike ya dannan sleep button kan ya dawo ya zauna a sofa me kallon wanda ta zauna.

“So ready to talk?”. Ya tambaye ta.

“Abd……”. Bata karasa maganar ta ba ya katse ta.

“Khalifa, you can call me that. And before you start ina so ki san tun farkon haduwar mu na san koh ke wacece”. Mamaki ne sosai ya rufe ta, wato yasan koh ita wacece amma ya cigaba da mata wasa da hankali. “Tun da muka hadu a airport, nazo na kuma ganin ki a park naji kawai ina so na san koh ke wacece dun haka na sa aka mun bincike a kanki, at first ban so na yarda ba, cewa Laylah da na sani ita ce Laylah Jaan, Nigeria’s top call girl. Amma hoton da detective dina ta turo mun yayi clearing doubt dina a kan komi”. Ya fadi fuskar sa ba alamar fara’a koh kadan.

“Toh amma me…..”.

“Shhhhh” ya fadi hannunsa a kan labbansa. “Bani son tambaya, today I’ll be  the questioner and zaki bani answer. The truth, I want nothing but the truth. In kin karya kema kinsan ina da hanyar finding out. In muka gama tattaunawar mu, zan baki damar ki mun duk tambayar da kike so amma ba yanzu ba”. Ya fadi ba alamar dariya koh wasa a fuskar sa.

Hankie ya miqo mata ta goge hawayen da ke sauka kan kumatunta. Kukan ta na matukar raunana zuciyar sa amma koh kadan be bari ta fahimci hakan ba.

“It all started 12 years ago, lokacin I was just 14 years old…… na farko dai ni ýar asalin jihar yola ce, fulanin yola. Can aka haife ni, can na taso a wani dan kauye before I found myself in Abuja…….”.

STORY CONTINUES BELOW

Jama’a lokacin da aka dade ana jira ya isa…… mu shiga labarin can baya mu gano koh wacece Laylah.

Cikin garin Girei ýan mata biyu ne ke rugowa da gudu, hijaban su a daure, sun riqe hannu suna ta sheqa gudu. Babbar bazata wuci shekara sha hudu ba ita kuma karama kwata kwata bata fin shekara goma. Basu tsakaita gudun ba har da suka shawo kwanan layin gidansu. Suka shiga gida da sallama suna ta faman nishi kamar wasu wanda suka yi aikin karfi.

“In ce ba na hana ku gudu cikin gari ba. Haba dan Allah, mata ne fa ku”. Wata mata wadda ba tsohuwa ba ta fito daga daki tana musu fada. Ta gama fadar kenan sun shiga ciki ba da dadewa ba sai ga Hanne, ýar yarinya wadda ita ma bazata wuci shekara 15 ba ta shigo gidan tana kuka. Tun kan ta buda baki ta fara magana, Rabi ta riga ta san abunda ya shigo da ita. Wato dalilin da ya sa suka shigo gida da gudu kenan koh kamar ana koran su.

“Badejo! Hidayatu!”. Ta kwalla musu kira. Kira take shuru shuru sunqi fitowa har sai da ta dau icce ta bi su har cikin Uwar daka inda suka shige suka boye. Da gudu suka fito suna ihu, mamansu na tambayan su abunda suka wa Hanne. Ashe gyadar da take talla suka tsare ta suka ci har na naira dari alhalin basu da kudin biya, a karshe kuma garin bin su da gudu dun ansar kudin ta tayi tuntube gyadar ta zube a qasa gaba daya.

“Kuma sai Daada ta buge ni in na koma gida haka nan”. Hanne ta fadi cikin hawaye. Rabi duk ta ma rasa abun yi gashi ba wasu kudaden kirki bane hannunta, naira dari da ashirin ce ta rage mata sama da qasa kuma a ciki zata sayi iccen da zata karasa girkin rana. Tana rafka musu icce a jiki tana ba Hanne haquri amma yarinya tayi qememe ta qi tafia wai alambaran sai an biya ta naira dariya hudu da talatin dinta tunda su suka jawo mata bari. Cikin tsananin takaici Rabi tayi ta rafkan yara da icce. Ana wannan drama din ne babban danta Suraj ya yo sallama ya shiga ciki tare da abokin sa Mahmoud, yaron headmaster. Da gudu suka ruga su biyu kwato su Badejo suna bada haquri.

“Ummati me suka kuma yi?”. Suraj ya tambayi mahaifiyar sa ita kuma ta kwashe komi ta fadi masa. Mahmoud da yike ta sauraron abunda ya faru ya ciro wallet dinsa daga aljihun wando ya ciro naira dari biyar sabuwa pul ya miqawa Hanne wadda ta ansa cikin gaggawa ta fita gidan tana fara’a, koh sallama bata wa Rabi ba.

Su kam ýan mata kamar wanda kwai ya fashe musu a ciki suka miqe sub sub kamar wasu maras gaskia suka wuce ciki. Ita Badejo cike da kunya saboda saurayinta yazo ya izza Ummati na bugun ta. Duk cikin gari  Girei ba wanda be san Badejo da Mahmoud dinta ba. Tun tana yarinya ýar karama ta ke liqe mai har zuwa ga yanzu da ta girma.

“Miskila toh ai sai ki fito ana jiranki”. Rabi tayi mata magana kan ta fito waje suka gaisawa sosai da Mahmoud din. Dama a gida an riga an amince, jira kawai ake ta zana waec a tattara ayi musu aure.

A kunya ce ta fito, tayi wanka ta sanja kaya zuwa wani atamfa riga da skirt me kyau, ta sa dan hijaab dinta madaidaici. A soron gidansu ta izza shi yana zaune, sallamarta yasa ya Suraj mike wa ya dan basu wuri. Mahmoud dan saurayine, dan shekara 18. Babansa shine headmaster din primary school din garinsu, yaro me kyau ga tattali da maida hankali a kan karatu da addini. Abokantansu da Suraj ya fara ne tun suna shekara 5 har ya zuwa wannan lokacin shiyasa koh da ya nuna interest a kanwar sa aka basa damar tsayawa zance da ita.

“Ba ki ji Badejo na”. Abunda ya fara ce mata kenan. Fuska a maraice ta kallesa tace

“Auta ce fa ta so cin gyadar gashi ba sauran kudi hannun mu”. Sanin kusanci da shaquwa da ke tsakaninta da ýar Uwar ta ta yasa be ce komi ba kuma yayi murmushi kawai.

“Toh shikenan, zan baki kudi ki riqe a hannu ki, koh da zakiyi sha’awar cin wani abu sai ki saya”. Ya ciro naira dari biyar sabuwa pul ya miqo mata sai ta qi ansa.

“Ya Mahmoud….”. Bata gama ba ya katse ta.

“Auuu yau dan na kira Laylah ta Badejo shine bazata kirani Majnu din ta ba?”. Ya tambaya yana fushin karya.

“Aah bafa haka bane….. Yawwa kama tuna mun kace zaka siya mun wanan sabon movie din na Amitabh Bachchan”.

“Yanzu ba zance film muke ba, ki anshi wanan kudin tukun. Yau wani babban mutum ya kawo gyarar motar sa garejin mu, kuma ya mana ihsani sosai. Karki damu ki ansa kinji”. Ya kuma miqa mata ta sa hannu ta ansa tana godia.

Tsananin son kallon finafinan India ne yasa tun randa Badejo ta kalli wani tsohon film nasu me taken “Laylah Majnu”, ta laqawa kanta suna Laylah shikuma ya Mahmoud dinta Majnu. Soyayyar da ke tsakanin wannan biyu kam Hmmmm baa cewa komi ne.

Hira suka dan taba kan ya miqe yace zai koma gareji dama ya so ganin ta ne da ranar. Ya mata alkawarin cewa da dare zai zo ya kawo mata film din. Ta mai addua da fatan alkhairi kan ta wuce ta shige gida. Shigar ta ke da wuya Ummati ta taro ta.

“Me aka samu yau?”. Ta tambaya. Dari biyar inda ya bata ta nuna mata gami da mata bayanin abunda ya sa ya bata kudin.2

“Ayiriri”. Rabi ta saki guda “Tabbas haihuwar ýa mace riba babba, bare ma diya me tsananin kyau irin Badejo na”. Ta karbe kudin tana daurawa a habar zanin ta. “Wannan kudin zan hada da sauran ne ayi ta siyayyar gara dashi, kada auran ki yazo mu sha kunya”.

Badejo dai ba wai ta taso bane gida na tsananin talauci, mahaifin ta Malam Othman wanda aka fi kira da Barkindo clerk ne a local government office din garinsu, kuma iya gwargwado yana kokarin kula da iyalinsa, gashi baya wasa da karatun yaransa, yana matukar masu kwadayin su sama isasshen karatu barin ma Suraj wanda yike namiji, shi zaya riqe gidan a nan gaba.Kamar yadda yayi alkwari, da yamma da Mahmoud zai wuce gida sai da ya biya ta gidan su Badejo ya kai mata movie inda yace zai kai mata da kuma ýan kayan kwalama. Nan ma suka kuma taba dan hira kan ya mata sai da safe ya wuce. Rashin wuta ya hana Badejo kallon film din dun haka Washe gari ana tashi makaranta bata tsaya tsokana da iya shege ta jawo hannun Auta suka kama hanyar gida. A hanya ne suka ga wani dan dattijo da gemu suka ta mai dariya wai gemun sa kamar na bunsuru.+

Suna cikin dariya Auta ta tambayi yayarta “Amma Adda”.

“Na’am ya aka yi?”.

“Yanzu ace ke ce da wannan gemun” ta fadi ta tuntsure da dariya “me zana dinga ce miki”.

Sai da Badejo ta jima gun tunani kan ta bata answer “Sai ki kirani Hamma Bunsuru”. Ta fadi suka tuntsure da dariya “Amma kuma Auta, da ace kina da bindi irin na saniyar Malam Jauro fa?”.

Auta bata gama tunani ba Badejo ta bata ansa “Da na kiraki Auta Saniya”. Auta kam ta sha kunu, ta hade rai wai ita bazata yarda ba. Nan fa ta kama bin yayar nata da gudu, suna gudu cikin gari suna dariya, basu da matsala a rayuwar su. Irin so da shaquwar da ke tsakanin Badejo da Auta har daure kan mutane yike atimes, gasu dai zaka ga daya ta girmi daya da dan ne sa amma kuma a kaf kauyen Badejo bata da wata qawa, ýar uwar shawara wadda ta wuce ýar Uwar ta. Yadda kasan a manne aka haife su dan koh aike tare suke zuwa, duk wanda kam ya taba ta sai ya gamu da bacin ran ýar Uwar ta dun koh a makaranta ne in zaa hukunta Auta dun ta yi wani laifi Badejo ke Karbar hukuncin indai tana kusa. Indai har Auta ta nuna tana son abu, Badejo na kokarin ganin ta ne ma mata shi, bata son ganin ýar Uwar nata cikin bakin ciki kwata kwata. Gashi ita kuma Auta karamar yarinya ce wadda bata san babu ba, ita kawai a duk lokacin da ta so abu a bata shi. Alhamdulillah dai mahaifin su iya gwargwado yana da na rufin asiri kuma irin tsananin son da yike wa yaransa, duk abunda suka nema gunsa yana kokarin yaga ya basu. Inda malam Barkindo suka sha bamban kenan da Uwar dakinsa Rabi, shi mutum ne shuru shuru mara hayaniya, magana ma be cika son yi ba, ita kam Rabi irin matan nan ne masu jaraba, sha yanzu magani yanzu, kwata kwata bata son rainin hankali. Dalilin haka ne yasa yaran duk suka fi kusanci da mahaifin su wanda shi a Kullum yike lallaba su yana bin su a hankula koh da laifi suka yi dun shi a nasa tunanin duka baya gyara yaro, wai! Banda Uwar gida Rabi ita da yaro yayi laifi muciya ne, tabarya, icce koh duk abunda hannunta ya fada zata dauka tayi ta rafkan yaro dashi har sai maqota sun kawo ceto. 

Basu bar gudu ba sai da suka sha kwanan layin su sannan. Sanin halin mahaifiyar su ma ya tsagaitar da gudun nasu. Suka shiga suna wakar ayye mama, ayye mama. Suna shiga suka sama iyayen su zaune kan tabarma.

“Sannunku da gida”. Suka gaisar da iyayen su. Rabi ce kawai ta dago ta ansa, bata bar fifitan da take wa babansu ba, ga kwanon hura gabansa koh tabawa be yi ba. Ita dai Badejo cike da mamaki, Meya dawo da Abban su gida da wuri haka yau, shi da sai bayan sallan asr yike dawowa gida. Ita kam Auta ba ruwanta, ta kutsa Jikin Babanta ta jawo kwanon huran ta fara kai hari, Rabi zata hanata yace ba komi a bar mata ta sha.

“Abba ka dawo da wuri yau”. Badejo ta tambaya. Murmushi kawai yayi ya Kalle ta ya ce ta matso ta zauna kusa dashi.

“Mamana ban jin dadi ne sosai yau dinnan”. Koh malam Barkindo be fadi ba da ka gani zaka san cewa a cikin yaransa Badejo ce favourite dinsa dan koh kadan be cika son ganin Rabi na hukunta ta ba in tayi ba daidai ba. Har zuwa yamma malam Barkindo na zaune da ýan matansa biyu suna ta mai hira har zuwa lokacin da aka gama abincin dare, dama al’adar su ce cin abinci gu daya dun haka Rabi ta kawo abincin inda suke a tsakar gida kan ta shiga ta kirawo Suraj.

Suna cikin cin abinci ne Badejo ta lura Babansu baya wani cin kirki. “Abba baka ci”. Ta fadi rai a hade.

“Bani da appetite ne mamana”. Yayi mata murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

“Toh bari na dinga baka a baki, Oya buda baki”. Ta fadi tana dariya. A haka ta lallaba shi, in tayi loma daya shima ta basa har suka gama cin abinci. Sun gama kowa ya wanke hannu zai yi hanyar sa malam ya dakatar dasu.

“Aah ku dawo muyi magana”. Ya fadi masu. Bayan sun dawo sun zauna sai da ya yi ta musu nasiha akan neman Ilimi,  haquri, iya zaman duniya da kuma tawakkali. “Yau an yi kora a office dinmu, an rage clerks kuma unfortunately ina cikin daya daga cikin mutanen da aka kora”. Ya fadi musu. Gun yayi shuru, ba me cewa komi sai Auta kawai ta saki ihu.

“Wayyo Allah! Wayyo Allah na! Shikenan Abba zamu talauce koh, zamu daina zuwa makaranta, mu fara talla irin su Hanne”. Ta fadi tana kuka sosai.

“Aah Hidayatu, insha Allah baza muga wannan ranar ba. Da izinin rabbi dukan ku zaku sama Ilimi, boko da addini iya gwargwado. Abunda zamuci bazai gagara ba insha Allah, zan nema wani aiki. For now dai dole a dan sama sauyi tunda bansan randa zan sama wani aikin ba”. Ya rarrashe ýaýansa, ita koh Rabi tana can gefe tana faman share hawaye da habar zanin ta. Ya zasu yi yanzu, gashi a ranar kan malam ya dawo taje Asibiti aka tabbatar mata da tana dauke da juna biyu, kusan wata uku ma. Wannan wana irin qaddara ce.

Abu kamar wasa haka malam Barkindo yayi watanni a gida ba aiki, dan guntun savings dinsa duk suka gama qarewa a kudin makarantar yara, da kuma kudin awo a karshe ma Rabi tazo ta haihu through CS, yarinyar tazo ba rai. Aka biya wa Suraj kudin zana wani waec dan na farko be yi kyau ba. Mahmoud na kokari iya gwargwado gun taimaka wa su Badejo da dan kudin da yike samu from part time job inda yike yi as a mechanic, a haka yazo ya sama admission a can Bayero university. Badejo ta sha kuka, tunda ya sama admission mahaifin sa yace ai maganar aure a dakatar ya gama karatu tukun. Da kyar ya samu ya rarrashe ta da yi mata alkawarin  bazai taba mancewa da ita ba, kuma insha Allah in ya gama zai dawo ya aure ta. Ita ma ta mai Alkawari bazata saurari ko wani saurayi ba, komin yaya zata jira dawowar sa.

A lokacin da admission ya fito, harda sunan Suraj dun haka malam Barkindo ya siyar da katuwar saniyar sa dun biya mai kudin registration. Murna gun su baya misaltuwa, dan su ya sama admission, zai yi karatu me inganci ya samu ya rufa musu asiri nan gaba. Suraj ya sha waazi da kuma addu’o’i. A lokacin rayuwa ta riga ta musu wuya matuka, su Badejo ma an cire su daga dan makarantar private inda suke zuwa an maida su ta government. Ci wuya, sutura wuya dun sai malam Barkindo ya fita yayi kwadago yike samun dan canjin da zai bada na cefane. A da Rabi na daya daga cikin matan da suka fi kowa sa sutura a kaf garin Girei, bare kayan danki a daki, abun baa magana amma wai ita ce yanzu rayuwa ta juyawa baya, kayan kaf duk an siyar, dan duk lokacin da Suraj ya bukaci kudi koh in karshen wata yayi zaa tura mai kudin abinci, dole ne ta siyar da wani kwanonta na jere koh atamfa, in ba haka ba basu da hanyar samu. Kusan shekara biyu Suraj na makaranta kawai wataran suna zaune suna shan iska da yamma sai gashi ya fado gidan, police biyu na rirrike da shi, duk ya rame ya yi baqi yayi wani iri.

Rabi ce ta fara miqewa da gudu tana zunduma Salati “Innalillahi Suraj! Kai ne haka, me ya faru”. Shuru be ce komi ba. Malam ne ya matso suka wuce zaure dun suyi magana. Daga can kuma ya dawo gida yana kwalla ihun ina Suraj din.

“Suraj! Dama abunda muka aike ka makaranta yi kenan, ashe kai mutumin banza ne ban sani ba, rayuwar da ka zaba wa kanka kenan, da hankalin ka da irin tarbiyyar da muka baka, muka yi trusting dinka. Duk savings dinmu mun kashe a kanka, saboda kayi karatu ka zama mutum, ka share mana hawaye. Umman ka kaf kayan dakin ta ta siyar, atamfafofin ta duka dan dai kayi karatu, ýan uwanka dole muka maida su government school dun dai kawai mu baka kulawa iya gwargwado, amma kaje ka shiga shaye shaye Suraj, har ya kai ga kunyi fada harda sare sare an koreka a makaranta. Ka bani kunya Suraj, ka tozarta ni. A hakan ne zaa ce haihuwar da namiji riba? Wallahi da na sani da na fi maida kula ga wannan ýan matan”. Ya fadi yana nuna su Badejo wanda duk kuka suke. Rabi tama kasa cewa komi sai hawaye kawai ke kwarara daga idanunta.

Basu ankara ba kawai sai ganin malam suka yi ya zube a qasa. Da gudu suka nufo sa, suna ihun a kawo agaji. Cikin kankanin lokaci makota aka taru, wani makocin su wanda ke da abun hawa ne ya dau malam har zuwa Asibiti government na garin.

Suna koh zuwa doctors suka shiga gwaje gwaje. Baa wani dade ba wata nurse ta fito da prescription din magunguna da allurai wai a jai a siya maza maza a kawo. Nan Rabi ta kuma rudewa, a wulakance prescription inda aka bata sai ta kashe dubu biyar, ina zata samu, ita da ta tashi yau koh naira dari na kanta bata dashi.

“Allah sarki malam, Allah jikan ka. Ni ina zan sama wannan kudaden”. Ta dinga fadi tana kuka. Wani mutum ne da ya kawo matar sa haihuwa yaga irin kukan da take yi ya tausaya mata ya karbi prescription din ya je ya siyo magungunan ya kawo mata ya hada mata da naira dubu biyu yana bata haquri. Zubewa tayi a qasa tana mai godia, tana Allah sauke me dakinsa lafia.

Nurse ta dawo ta anshi kayan ta koma ciki. Sai da aka yi kusan 2 hours kan doctor ya fito yi mata bayani. News inda doctor yayi breaking mata ya mugun razanata. Wai stroke ya ja malam, rendering one side of his body useless. Nan Nan ta kife a qasa ta yi ta kuka tana Suraj ya jawo mata tashin hankali, ita yanzu da wanne zata ji, ciyar da gidan koh da sayan magani. Sai da malam yayi wata daya cur a Asibiti kan aka mai sallama. Tun daga wannan ranar rayuwa ta sauya musu.

Wai ba zaki fito ki dau wannan Alalan ba”. Rabi ta fadi tana hararar Badejo.

“Ni gaskia Ummati ba zani talla ba, kefa kika ce bayi da kyau. Kina ji satin da ya wuce karime ta haihu ba aure kuma sanadin talla ta yo cikin”.

“Dallah rufe mun baki, mutuniyar banza”.

Malam da ke kwance bisa tabarma a gefe ya buda baki yana kokarin magana “R…ra….bi”. Yana magana miyau na bin gefen fuskar sa, Wayyo ciwo “ki ra….r….rabu da i….ta bata son ta…”. Be ma kai ga gama magana ba Rabi ta watso mai wani kallo tana jaraba.

“Dallah can rufe mun baki, in bata je ba waye zai je? In bar wankaun da nike yi ne na dinga fita tallan koh kai zaka tashi ka tafi tallan. Dan rainin hankali, sai anyi magana kace Allah zai hore, shekara biyu kenan baka da aiki sai kwanciya gu daya kudin magani ni ce, na abinci ni ce. Mutuwar ka ki kayi na huta”.

Badejo cikin hawaye tace wa mahaifiyar ta ya isa zata tallan. Ta wuce ciki ta dau hijaab dinta dogo mai tsafta ta saka, Auta na ganin ta sa hijaab ita ma ta dau nata ta saka, qafar Addan ta qafar ta. Badejo tayi tayi a kan cewa Auta ta zauna ta kammala assignment dinta amma ta qi. Ita Badejo dama tun Shekarar da ya wuce ta daina zuwa makaranta dan rashin kudi dan kuma ta taimaka wa Ummati wadda ke aikin wankau, da sana’ar suke ci, su sha, a siyawa malam magani.

Suna fitowa mahaifin su ya shiga zubda hawaye, wai yaransa ne yau wanda yike so kamar me zasu talla. Koh a mafarki be taba tunanin ganin irin wannan ranar ba. A zuciyarsa yayi tir da haihuwar na miji. Duk kudin sa yayi wasting akan wancan shashashan gashi yanzu shaye shaye a gun Suraj ba komi ba, da aka koresa daga makaranta ya dawo gida, at first yana yi aka boye amma yanzu kaf garin ba wanda be san halin da yike ciki ba, duk ya zama wani iri, daga shaye shaye sai fada da yawon banza kawai ya iya. Mahaifiyar sa ta ne ma ta dafa kuma ta basa ya ci, in ta ije kudi ma ya gani ya dauka ya je yayi shaye shaye da su.

Su kam tunda suka je bakin kasuwa suka zauna tare da wasu ýan mata wanda su ma talla suke ake ta tsokanar su, wai me ya sama yaran gwal, aka gansu da tallan alala. Su dai basu tanka ba suka zauna shuru. Suna kallo kusan ko wace yarinya ta siyar da kayan tallan ta amma su koh Rabi basu yi ba. Da samari sun zo sai suce zasu musu juye, su kuma su tashi su bi. Baya wuce ayi amfani dasu a biya su daidai kudin kayan tallan su su kai gida dun gudun fada daga iyayen su mata. Toh ýan uwa ina amfanin wannan rayuwa? A tura yara talla sannan ace lallai lallai sai sun sayar da gaba daya kayan da aka basu, ai dole a tunzura yaro ya bi hanyar da bata dace ba. Talauci ba hauka bane, and hawking isn’t always the option. Akwai hanyoyin nema kudi iri iri ba lallai sai tallan ba kuma in ya kama dole sai tallan sai ayi sa cikin tsoran Allah, amma yanzu yarinya zata fita talla sai kaji ana tillasta mata akan dole sai tayi ado, tallan abinci ta fita koh na jiki? Ai dole ma maza su tare yarinya su mata zancen banza.

Badejo na cikin tunanin ta taji muryar wani kusa da ita. “Me alala nawa ne?”.

“Naira ashirin ce”. Ta ansa shi.

“Aah wai gaba daya Alalan nike tambaya”. Badejo ta dago ta kallesa cikin mamaki, me zai yi da dukan alalan?.

“Naira dariya uku da sittin ne”. Auta ta ansa mai.

“Toh tashi muje in baki kudin”. Ya fadi yana murmushi.

“Aah, gaskia bazan iya bin ka ba. Kaje ka dauko kudin”.

“Haba ýan mata, minti nawa ne zaki biyo ni na baki kudin ki, mu dan huta ki dawo”.

“Dan Allah ka wuce, alalan ma na fasa sayar maka”. Ta fadi rai a hade.

“Kaji ýar iska, ni zaki wa jan aji? Waye be san halin ku ba ýan talla. Karuwar banza da wofi”. Ya ja tsaki ya wuce. Badejo ta ije kai a qasa tana kuka. In ba dan kaddara ba ina ita ina talla har wani namiji ya fadi mata zancen banza. Wai ita ce yau aka kira da sunan karuwa.

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin nan tayi wa kanta alwashin sai ta nemi kudi, sai ta zama mutum, sai ta share hawayen iyayenta da ýan uwan ta ta cire su daga wannan qangin rayuwa da suka shiga. Har yamma dai cinikin da su Badejo suka yi koh naira dari biyu be kai ba. A haka nan suka miqe da suka ji ana kiran maghreb suka nufa hanyar gida suna kuka, dan sunsan yau suna da rabon cin bugu daga hannun Ummati kuma ita mai iya hana su abinci ne, gashi tunda karfe sha daya da suka fita talla basu ci wani abun kirki ba illa alala kwara daidaya da tace su ciki in suka ji yunwa, basu isa su qara ba tunda a kirge yike. A haka suka riqi hannun juna suna kuka har suka zo wuce wa ta wata masjid.

“Ýan mata lafia?”. Suka ji an musu magana cikin wata murya me sanyi. Juyo da zasu yi suka ka ga wani mutum ne, ba wai tsoho ba haka. “Kuna tafia kuna kuka, lafia?”. Ya kuma tambaya. Badejo bata tsaya basa ansa ba ta jawo hannun ýar Uwar ta tana ce mata su tafi, shima be wuci ya musu maganar banza ba, ya nemi ya kwana da ita.

Ita kam Auta tayi kememe ta tsaya tana kuka ta fada mai abunda ya faru. Shikuma ga bisa dukkan alamu sun basa tausayi dan haka yayi nuni da hannu ma wasu almajirai da ke tsaitsaye yace ta raba musu alalan shi zai saya. Ya tambaye ta nawa ne kudin ta tace mai naira dari biyu da tamanin ne. Sa hannu yayi cikin aljihun wandon sa ya ciro naira dubu daya miqaqqa ya miqo mata yace gashi. Suna ta murna, Auta na tsalle suna mai godia. Shikuma yana musu murmushi yace su daina tafia suna kuka ya juya ya wuce. Sai Badejo ce ta kwalla mai kira.

“Bawan Allah”. Ta kira sa ya juyo ya nuna kansa da dan yatsa.

“Ni?” Ya tambaya.

“Ehhh baka ansa sanjin ka ba”.

“Na bar muku”.

“Aah. Ummati zata yi fada”.

“Sadaqah ne, fisabilillah”. Ya fadi sai tayi shuru. Auta kam na gefe tana ta daga mai hannu, tana waving mai.

“Ya sunanka”. Auta ta tambaya.

“Bawan Allah”. Ya ansa mata kan ya juya ya wuce cikin masallaci.

Suka cigaba da tafiya suna jin dadi. Auta na cewa wannan bawan Allah akwai sa da kyau, ina ma yace yana son ta.

“Ke baki ga zai iya haifan mu ba”. Badejo ta fadi.

“Kai Adda”. Auta ta fadi tana tabe baki.

“Kuma daga ganin sa dan gidan masu kudi ne, ba irin mu suke bi ba. Kuma ni banso Auta na ta auri tsoho”. Suka tuntsure da dariya “mun dade ba muyi tsere ba”. Badejo ta hankada Auta ta ruga da gudu ita kuma ta ruga a guje tana bin ta. Duk a kan idon wannan mutumin, yana kallon su yana dariya, basu da matsala. Suna komawa gida suka nuna wa Ummati kudin suka fadi mata duk yadda aka yi. Ta rungumo su tana kuka tana sa musu albarka da basu bi wancan dan iskan mutumin ba, shikuma bawan Allah da ya taimaka masu tana mai addua da fatan alkhairi a rayuwa.

Suna zaune suna cin tuwon dare ne suka ji sallama. Suka ansa sai ga zainaba ta shigo gidan da fara’a. Tsam Badejo ta miqe ta ruga da gudu ta rungumo ta suna tsalle suna kukan murna.

“Ashe zan kuma ganin ki zainaba”. Badejo ta fadi “kika tafi kika mance ni, jubi yadda kika yi kyau kika murje abun ki”. Badejo ta fadi cikin murna. Sai da Ummati ta tuna mata bata ba baquwar nata gun zama ba da ruwa. Da gudu ta ruga randa ta kawo mata ruwan randa me sanyi sannan ta jayo kwanon tuwon ta ta ije tsakaninsu tace ta sa hannu su ci. Kaf garin Girei, apart from Auta Badejo bata da wata qawar da ta wuci zainaba, tare suka taso tun suna yara, sai shekara biyu da suka wuce bayan rusuwan mahaifin zainaba mahaifiyar ta ta tura ta aikin gida can birnin tarayya, Abuja.

“Naji abunda ya sama Abba, dazu Daada ke fadi mun”. Hmmm kawai Badejo tace ta kai loman tuwo bakin sa.

“Abun sai godia kawai zainaba, wai yanzu ni ce da zuwa talla”.

“Talla kuma?”. Zainaba ta fada cike da mamaki. Lallai gari ya wa iyalin malam Barkindo zafi. “Kinga fa rashin son tallan nan ne ya sa Daada aika ni aikin gida, ya fi mutunci. Kuma Alhamdulillah ba laifi suna kula dani. Ci da sha da sutura suna bani, gashi yanzu suna so su sani a boko”. Ta fadi wa kawarta.

“Ehhh! Harda boko”. Badejo ta fadi cikin mamaki “kinga fa ni yanzu mates dina zasu zana jarabawar fita daga secondary, amma gani a gida daga aikin wankau sai tallan alala kuma wallahi ina so nayi karatun nan sosai”.

Kai zainaba ta gyada kan tayi magana “kinsan wani abu ne, naga auntie nada ciki kuma tana zancen nema me raino, wanda zata dinga bin ta office tana mata raino inta haihu. Zan mata waya gobe da safe in ta yarda in zan dawo sai mu je tare in ya so ma koh aikin gidan ne a wani gu ta sama miki in bata son rainon”.

“Da gaske qawata, kai Aikam da na ji dadi. Wallahi ya fiye mun talla”.

“Sosaima, in ya so ma in ta ji dadin ki a iya mai da ki boko”. Badejo murna a gun ta baya misaltuwa, at least zata taimaka wa iyayenta. Kudin da zaa dinga biyan ta zaya fi wanda take samu gun talla, bare Abujan nan da ake magana garin masu kudi. Sai dai in ta tuno abu daya sai taji ba dadi, ya zata tafi ta bar rabin jikinta, Auta.

Aikam kashegari, just as promised zainaba ta kirawo auntyn ta wadda take wa aiki, dama tun zuwan ta suka siya mata waya ýar karama wanda zasu dinga communicating da ita koh da basu gida. Bayan sun gaisa ta yi mata bayani sai tace mata ba komi duk da nan da wata uku zata haihu a kawo Badejo ta saba da gidan kan lokacin haihuwa yazo. Ranar murna a gun su baa cewa komi.

A kwana a tashi har ranar tafiyar su ya iso, Badejo ta hado ýan kayakin ta, har lokacin Auta bata daina kukan zata bita ba, bazata iya rayuwa ba ita ba amma Badejo ta bata hakuri kan cewa saboda su sama a more better future yasa zata bar gida taje tana bautan gidan wani, ya fi musu rufin asiri kuma ya fi musu rayuwar talla. Sannan ta sa Rabi yi mata alkawarin bazata ta dora wa Auta talla ba tunda ita ba wani wayo ne da ita ba. Rabi ta ciro dan rubabben wayarta, Nokia ce ýar karama ta ba Badejo yadda zasu dinga communicating.

“In ya so sai na dinga zuwa shagon yahuza me chaji ina kiranki koh na anshi na Hamman ku”. Ta fadi da tana miqawa Badejo wayar. “Dan Allah ne sunan Daada ki kula da kanki, ki kula Badejo. Karki watsa mana qasa a ido kamar dan uwan ki, ki tsare mutuncin ki, abunda ya kaiki can kiyi. Ba ruwanki da dauke dauke, in an baki Alhamdulillah in baa bada ba still Alhamdulillah. Muma muna nan muna miki addua da fatan alkhairi”. Ummati tayi ta mata nasiha. Shikam malam tunda ya kwanta yike ta zubda hawaye. Ba irin rayuwar da ya so yaransa suyi ba kenan. Wai Badejon sa ce yau zata gidan wani bauta, me sunan Daadar sa wadda a duniya ba wadda yike so kamar ta.

A haka dai suka gama sallaman, wan zainaba ya kai su tasha ya sa su a motar Abuja. Ya da da musu nasiha da addua. Har suka isa Abuja Badejo zuciyar ta cike yike da tunane tunane iri iri. Bata san meyasa gaban ta ke wani mugun fadi ba. Tana tsoron sabuwar rayuwar da zata fara da ta isa Abuja. Addua kawai tayi ta a zuci har suka isa tasha suka sauka, already auntie ta riga ta aika driver already dauko su.

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Toh ga Badejo tayi landing a birnin tarayya, garin manya. Garinsu khalifa Al-Haydar da su senator Junaidu😁😁😁. Bara muji ya labarin zai tashi daga nan. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *