JIRWAYE CHAPTER 8
Www.bankinhausanovels.com.ng
And?”. Khalifa ya tambaya da yaji tayi shuru in banda jan majina da hawaye ba abunda take yi.+
“Kashe gari da safe, Yasmeenah ta bani kudi eighty thousand na tura gida dun Ummati ta samu ta rage crisis inda family dinmu ke ciki a lokacin. Koh da na tura mata kudin, rashin lafiyar Abba kadai ya cinye dubu hamsin a cikin kudin kan aka zo aka yi bailing din ya Suraj out of prison, da kyar suka anshi dubu ashirin. Sauran dubu goman kuma bazai isa registration din Auta ba, bazai isa Ummati ta kama hayan gida ba tunda ya Suraj ya sayar da gidanmu, ga rashin kudin kula da buqatun su,……”. Ta kuma tsayawa kan after some time ta cigaba.
“Dun haka, a few days after I sent the money to them, Yasmeenah tayi wani baqo wanda a lokacin babban ma’aikacin government ne. Zuwan baqon nan ne ya wayar mun da kai, har na san asalin sana’ar Yasmeenah. She’s a pimp, connecting ýan mata take yi da manyan mutane a biya ta kudi. Dun haka ranar baqon yazo a sama me budurwa kyakyawa that’ll entertain him for the weekend sai ya ganni…..”. Ta fadi murya na rawa.
“He offered me a hundred and fifty thousand naira, I was desperate, I needed the money and afterall there was nothing left of me, tunda I’ve already lost the one thing I’ve always been urged to safeguard, na zama baqar ashana. Out of desperation nayi taking offer din, ya biyani kudina na tura gida na biya wa iyayena buqatun su. And since from that day, sunana ya tashi daga Badejo to Laylah Jaan…… The heartthrob of the whole city, the heart desire of every man. Slowly nayi ta kashe wa ýan mata kasuwa dun duk wanda yazo sai yace shima sai ya dandani zumar Laylah Jaan. It became like a competition to the men, kowa na so ace shi ya fi biyana kudi masu yawa da yayi amfani da ni”.
Dogon numfashi khalifa ya ja, koh kallon ta ya kasa ya buda baki ya tambaye ta “And your parents? Kika ce musu kina samun kudi a ina?”.
“Karya nayi musu, nasan baza su taba jin dadi sanin diyar su ta zama karuwa, me siyar da jikinta dun samun biyan buqatun ta ba dun haka nace musu na sama aiki da wata hajia me kirki kuma ta sani a makaranta sannan zata dinga tura musu kudin da zai ishe su kula da kansu har na gama karatu na fara aiki. A haka na koma makaranta, da kudin karuwanci, nayi sponsoring Auta, da kudin karuwanci, na kai ya Suraj rehabilitation har ya gyaru ya koma karatu, da kudin karuwanci, na kai Abba na kashen waje da dama, da kudin karuwanci, Ummati tayi hajji da umrah, da kudin karuwanci. Da kudin karuwanci na ginawa iyayena gidan da duk Girei ba irin sa. Da kudin karuwanci na ba the people that mean the world to me all the happiness they deserve in the world”. Ta zube qasa tana kuka kamar ran ta zai fita.1
“I sacrificed my love, my body, my conscience just to make them happy. Na sabawa mahallici na just to keep them happy. Na rufe jikina da zuciya ta da Jirwaye just to place food on their table and happy smiles on their faces”. Ya so ya tambaye ta ya rabuwar su da Mahmoud ya kasance amma ganin irin kukan da take yi ya sa shi karaya.2
“You need some rest”. Abunda kawai ya iya fadi mata kenan kan ya bar dakin ya koma living room din suite din ya zauna shuru cikin utter darkness. He was just trying to digest all she told him, yana ta nazarin rayuwa, circumstances and how cruel some people can be and most of all, ba abunda ya mai zafi kamar yadda har da hannun ýar Uwar sa a cikin bacewar rayuwar Laylah.6
Khalifa ya dade a gun zaune shuru yana nazari iri iri, kwata kwata be yi tunanin haka meeting dinsu zai yi turning out ba. Yanzu her story has thrown his heart in confusion, be ma san me yike so ba kuma, ya kasa tunanin da kyau. Can towards subh ya leqa ya sama Laylah a kwance ta ci kuka har barci ya kwashe ta a qasa. Da har kamar zai daga ta ya maida kan gado sai kuma ya sanja mind dinsa kawai ya dau tuxedo dinsa da ya jefar kan gado the previous night ya nufi exit din Suite din. Without second thoughts ya fita daga Suite din. Yana isa lobby din ya anshi car key dinsa ya fi ce. Kwata kwata be damu da koh karfe nawa bane yayi ta driving recklessly a empty streets din Abuja.
STORY CONTINUES BELOW
Badejo kam on the other hand ba ita ta tashi ba sai minutes past 9 the next morning. Koh da ta dudduba bata ga alamar sa ba there and then she got the message. Without being told, ta riga ta san response dinsa.
‘No responsible guy would want to associate with a whore afterall’. Ta fadi a zuci kan ta daga wayarta tayi dialling number din Yasmeenah.
“Send the chauffer”. Ta fadiwa Yasmeenah. Koh gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta katse wayar kan ta shiga bathroom to tend to her early morning business. Fitowar yayi daidai da lokacin da driver ya kirata cewar ya isa gaban Al-Haydar empire. Jacket dinta tazo dauka ta ga bundle na kudi, American dollars da ya ije mata. Hawaye masu dumi ne suka sauka daga fuskar ta kan ta dau jacket din ta wuce, leaving the money lying there. Wato shikenan Abdulmalik koh ta ce khalifa shima karuwa ya dauke ta, da har zai ije mata kudi. Toh bata son kudinsa, a da tayi kwadayin cin kudin khalifa Al-Haydar amma yanzu, sanin the real face behind the name has turned down her vibe. A hankula, cike da takama, with her head held up high ta fito daga suit din tana taku dai dai har ta isa parking lot din hotel din inda driver ke jiran ta.
Suna isa gida, bata tsaya ko ina ba sai dakin ta, ta tube kayan jikinta ta fada ban daki. Ta dade sosai a ciki ba abunda take yi in ba rusa kuka ba har sai da Yasmeenah ta yi knocking door din ta ji koh lafia taji ta shuru.
“I’ll be out in a sec”. Ta fadi kan ta miqe daga qasa inda ta zauna comfortably tana ta sharar kuka. For the second time, she has lost her key to happiness….. For the second time in life, she has lost true love all kudos to the path fate and circumstances lead her to.3
Wanka tayi kan ta fito ta izza Yasmeenah zaune bakin gado tana jiran fitowar ta.
“Wannan da kika dade a wanka haka, it seems khalifa Al-Haydar had a wonderful night”. Yasmeenah ta fadi with a hint of mischief in her tone.
“He sure did”. Laylah ta ansa ta fuska ba walwala. Daga nan ba wanda ya kuma cewa komi. Yasmeenah tayi busying kanta da phone dinta while Laylah took her time to doll up. Mai kawai ta shafa, ta fesa body spray kan ta nufi closet ta nemi wani free gown ta sanya. Kusancin da ke tsakanin Yasmeenah da Laylah ya sa ta sensing something wrong amma kuma bata yi pressing issue dinba dun haka kawai ta fita ta nufi downstairs. Kitchen ta wuce direct ta fara mixing batter zata hadawa Laylah breakfast of one of her fave meals. Tana gama frying pancakes din tayi arranging dinsu neatly a plate kan ta dora a kan tray wanda ke dauke da mug na tea already, ta buda fridge ta dauko dressings for pancake din kan ta wuce dakin Laylah da abincin.
“Come eat”. Laylah ta so objecting amma Yasmeenah bata bata room for that ba “Come on, I made it with so much love”. Tayi convincing dinta. Koh da ta fara cin abinci, Yasmeenah na lura da yadda ta ke ta wasa da pancakes din kawai her mind far off in a trance.
“Something went wrong?”. Ta tambaya amma shuru “It’s okay if you don’t wanna talk about it, I’d just go to my room”. Ta miqe heading for the door.
“Abdulmalik is khalifa Al-Haydar……. Khalifa Al-Haydar is Abdulmalik”. Maganar ta ya sa Yasmeenah Mutuwar tsaye. Ta dade in shock kan ta juyo ta kuma tambayar Laylah, just for confirmation.
“Who is who?”.
“Abdulmalik, the guy I’m crazily in love with. Turns out the poor driver, the single father of one is none but the mysterious khalifa Al-Haydar. khalifa Al-Haydar inda nayi shekaru ina targeting”. Ta fadi kan ta kuma fashewa da wani kuka me ratsa zuci. Da gudu Yasmeenah ta qarasa kan gado ta riqo ta, ta sa kanta a shoulder dinta tana ta shafa mata gashi a hankula, in a soothing way. Sai da kukan ya ragu kan ta kwashe duk yadda suka yi tas ta fadiwa Yasmeenah.
“You think I did the right thing?”. Ta tambaya.
“Right now I’m so proud of you baby”. Yasmeenah ta fadi tana kissing hair dinta “And I’m very certain zai dawo, he loves you. Just give him some space, he needs time to digest all you told him, to clear off his mind. Kin ji, just cheer up. Mu zubawa sarautar subhanahu wata’alah ido”. Ranar dai haka Laylah ta wuni kuka Yasmeenah kuma nata faman bata haquri daga karshe dai tayi making up mind dinta to call the only person that can cheer Laylah up dun haka daukar wayar Laylah kawai ta yi ta fara dialling number din, ana dagawa ta sawa Laylah wayar a kunne ta fita ta basu waje.
Ýar uwa kenan, rabin jiki. Cikin few minutes Auta tayi abunda Yasmeenah ta wuni tana yi ta kasa. Kan kace mai Laylah nata dariya da fara’a, koh da suka gama wayar mood dinta yayi improving sosai. A haka dai kwanaki suka fara gushewa ba khalifa Al-Haydar ba labarin sa. shi be kira ba, be kuma neme ta ba.
Cikin ýan few days dinnan, life lost meaning to Laylah. Kullum bata da aikin da ya wuci zama cikin daki tayi ta tunani. Daga baya da ta gaji da zaman daki sai ta fara fita in the evenings zuwa park for long walks. Koh events planning business dinta bata wani kula da, komi ta bar wa Ameer PA dinta ya dinga kula da business din, sai dai ya kawo mata feedback.
Kamar wasa, aka yi two months Laylah bata ji daga khalifa Al-Haydar ba dun haka ta yi making up mind dinta to take the right step. Ranar da dare ta shiga dakin Yasmeenah dun suyi magana. A hankula ta tura kofar ta sama Yasmeenah zaune a armchair inda ke dakin tana karatu. Murmushi tayi mata kan ta qarasa ta zauna kusa da ita a dayan armchair din. Shuru shuru bata ce komi ba dun haka Yasmeenah ta cigaba da karatun ta.
“I’m leaving”. Maganar ta ya sa Yasmeenah sakin novel inda take karantawa ta dago tana kallon ta. “Hey! Not forever”. Ta fadi tana wata ýar dariya “For sometime, I want the world to forget about Laylah Jaan, just to clear off my mind and stay off the social circle for a while”.
“How long are are we talking about here?”.
“I don’t know; months, one year, 2 years, 5 years. I just don’t know. All I know is zan dawo”.
“Kema barina zakiyi Laylah, leek left and you’re leaving too. Duk duniya ban da irinku”. Kawai ta fashe da kuka.
“Hey, wallahi zan dawo. Kullum zan dinga kiranki, i’m not leaving the world, yola zan koma for a while. You can stop by anytime you miss me”. Ta fadi. Yasmeenah kawai jawo ta tayi jikinta tayi embracing dinta affectionately.
“I am proud of you Laylah”. Ta fadi mata. Koh da Laylah ta miqe zata koma dakin ta sai ta isa bakin kofa ta tsaya.
“Yasmeenah”.
“Na’am”.
“It’ll be good if you go home too you know, atleast su san kina raye”. Ta fadi kawai ta juya ta wuce. Kashe gari da sassafe suka tashi Yasmeenah ta mata rakiya zuwa airport. Sai da taga tashin jirgin su kan ta koma gida zuciyarta fal da tunani. Maganar da Laylah ta fadi mata the previous night ne kawai ke ta mata yawo a kai. Hakika ya kamata ta nemi gida. Tana isa gida dakin ta ta wuce directly ta buda wani drawer ta ciro wani dan envelop wanda yike dauke da details din family dinta da suka rage. About 3 years ago ta sa aka mata investigation amma tunda aka kawo rashin courage ya hanata buda envelop din. Koh da ta ciro envelop din, ta dade tana nazari on whether or not to open it kan tayi making up mind dinta to just open it. Tana budawa contact din farko ta fara dialling, contact din ýar Uwar ta Gumsu.
“Hello…”. Shuru Yasmeenah ta kasa magana.
“Hellooo….”. Aka qara fadi a background tana jin haniya kaman na yara suna argument.
“Yasmeen! Dan Allah kuyi shuru in ji magana”. Ta ji ta fadi kan ta kuma cewa hello amma shuru Yasmeenah ta kasa magana sai wasu hawaye masu sanyi da ke sauka kan kumatunta.
“Yasmeenah….. is that you? Ke ce?”. Ta tambaya amma kuma sai Yasmeenah ta yi saurin katse wayar. Gaba daya ma ta kashe wayar ta kwanta tana kuka. She has never felt so lonely and vulnerable in her life.