K’ADDARA CE CHAPTER 2 BY MAMAN NUSAIBA
Marubuciyar
*AMEER DA AMEERA*
*ALJANAR JARUMAI*
*HAFSAT*
Yau ma gani dauke da sabon labari mai suna *K’ADDARA CE* Kada ku bari a baki labari wannan shima salon shi da,banne ne kudai sai kun karanta.
🔔📚
*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
Free page
3/4
Iman na shiga Gida da Sallamar ta ta shiga tana turo baki gaba kamar wadda aka yiwa lefi.. Maman ta Ta amsa Sallama Ta ce” a a sannu da zuwa Imanie na marhabin lale, sauke kayan mana! Sauke kayan Iman Ta yi ta k’araso kunsan Maman ta ta zau na, kud’in ta mik’a mata Ta ce” gashi Mama..
Amsa Tayi ta soma k’irga wa taga naira dubu Ashirin ne da d’ari biyar akai, kallon Iman Ta yi Ta ce” Iman ya naga d’ari biyar tahau ka? kardai kice min wani Saurayin ya baki? Kin san dai na hana ki amsar kud’in saurayi ko? dan kina talla bashi yake nuna cewa baki tarbiya ba, Iman na gargad’e ki ki rike mutumcin ki kada ki bari koda yatsa Namijin daba muharramin ki ba ya kama miki, karna kuskura naji ko na gani, hakan ta kasance ko a mafarki kina ji na ko! Yan zu fad’a min waye ya baki d’ari biyar Y’ar albarka Y’ar lele na… Mama ta k’arasa maganar ta cikin lallami….
Iman ta kuma turo baki gaba Ta ce” ke Mama dad’ina dake ba dama Mutum ya kawo kud’i sai kin ringa mishi fad’a, nima ai da hankali na bazan bari wani Namji ya tab’a jiki na ba har ya bani kud’i, Insha Allah bazan zubar da tarbiyar da kuka bani ba a ko wani hali na tsinci kaina.. Wannan d’arin biyar kin Manta jiya nace miki Abdul Malik Yaci WAGASHI bai biyani kud’in ba ya tafi to shine fa.. Mama dan Allah ki kwantar da hankalin ki Insha Allah bazan zubar da Mutumci na ba duk runtsi zan kama kaina koda bana gaban ku Insha Allah….
A jiyar zuciya Mama ta sauke Ta ce” Alhamdulillah Allah ya rabaki da sharrin Zamani, Allah yakare min ke a duk inda kike koda K’ADDARA CE zata raba mu… Murmishi Iman Ta yi Ta ce” yauwa Mama na Addu’a zaki ke min koda yau she, nima zanke yi duk lokacin da nayi Salla.. Mama Ta ce” to Iman shiga kiyi wanka kici abinci sai ki huta, idan zaki tafi sai ki dauk’i dubun biyar da aka ce kukai Makaranta.. To kawai Iman Ta ce” ta shiga dakin…..
****************************
A b’an garen Sultana ita ma ta shiga Gidan su ta tarar Maman ta ta gama girki tana wake-wake. Sultana Ta ce” Mamma sannu da Gida.. Murmishi Mamma Ta yi Ta ce” Yau wa Sultana sannu dai har an dawo kunsha rana ai.. Sultana Ta ce” eh Mamma akwai rana fa, Kud’in ta mik’a wa Momma ta amshi wake-waken ta k’arasa, Mamma na hanata amma sai da ta wanke , tukun ta dawo cikin d’akin ta zau na kusa Momma…
Kallon ta Mamma Ta yi Ta ce” to Sultana ake rike mutumcin kai dai karki bari samari su ribace ki,ki kama kanki kinji! Allah ya miki albarka tashi kici Abinci sai kiyi wanka ki huta kafin lokacin zuwa Islamiyya Ya yi…..
Sultana Ta ce” Insha Allah Mamma ina kiyaye dakokin Ubangiji Kuma Insha Allah zanci gaba da kiyaye wa.. Mamma Ta ce” to Allah ya k’ara kareki daga duk wani sharri shiga ki huta.. Sultana Ta ce” to Mamma nan ta shiga d’aki dan yin wanka…..
Misalin karfe 3: 40P.M. dai-dai , Iman tazo Gidan su Sultana suka wuce Islamaya. Suna tafiya suna hirar su gwanin burgewa har suka k’arasa Islamayar..
Suna shiga Aji Malamin su ya shigo babu bata lokaci aka soma daukar darasi.. Bayan an tashi su Iman suka kama hanyar dawowa Gida a hanya Abdul Malik ya tare su.. Yana fad’in Iman! Iman!! Iman!!! Dan Allah ki saurare ni mana please!
Wata Uwar harara Iman Ta aika wa Abdul Malik Ta ce” to meye lafiya kake kira na ko fad’an da mukayi a Kasuwa bai isheka ba Yan zu nayi tsukiya mu sake wani… Iman na maganar tana mishi gatsine…. Sultana Ta ce” haba Iman ke wai komai naki na fad’a ne! Mutum Yana binki ai sai ki tsaya kiji Abin da yake son fad’a miki, amma kin wani rufe shi da masifa ke wai fad’a baya isar kine? Zanga ranar da zakiyi hankali Wallahi, to ki tsaya kiji me zai miki fad’a miki banza kawai masifaffiya…
Turo baki Iman Ta yi Ta ce” ke ba dama mutum Ya yi magana sai kin ringa mishi fad’a, kamar wata Kaka ta.. Sultana Ta ce” Eh nayi fad’an ki tsaya ki saurare shi kin daiji Abin dana fad’a miki ,idan bazaki tsaya d’in bane saiki fad’a min naji… Iman kamar zatayi kuka take kallon Sultana ganin ba wasa yasa ta juya ta k’arasa wajan Abdul Malik Ta ce” gani tana aika mishi harara….
Shi kam Abdul Malik Tin da Iman Ta soma fad’a yake Kallon ta yana sakin murmishi, sosai ta bugershi da,tana fad’an nan…A jiyar zuciya ya sauke Jin Iman Ta ce” gata… kallon ta Ya yi Ya ce” am Iman gaskiya bazan, b’oye miki ba,Jiya bayan munyi fad’an nan dake ina koma wa Gida na kasa bacci…
Iman Ta katse mishi maganar da cewa Iyee to Wallahi ashir d’in ka kuruwa ta tafi k’arfin ka, ato kaci kanka ehee kai wai ma saboda wannan banzar maganar ne ka tsaida ni a hanya iyee?
Abdul Malik Ya yi murmishi sai yaji Iman Ta k’ara shiga ran shi Ya ce” a a fa Iman bafa haka nake nufi ba ,Ina nufi tunanin ki ya hanani bacci , har Gari ya waye ban rintsa ba, sai tunanin ki nake,maganar gaskiya Iman ina sonki ina kaunar ki, dan Allah karki ce baki sona kinji! Wallahi na miki Alk’awarin zan gyara hali na na dawo nutsatsen Namiji sai muyi Auren mu nida ke….
Iman ai tuni kunya ta kama ta da gudu tabar wajan Abdul Malik ta koma wajan Sultana tana dariya.. Sultana Ita ma na dariya Ta ce” ai dama nasan Abdul Malik yana sonki kawai tsoron masifar ki ne ya hana shi fad’a miki.. . Iman dai bata sake cewa komai ba bakin rashin kunya Yayi shuru, nan suka k’arasa Gida..
Shi kuwa Abdul Malik na ganin haka yasan Iman Ta amshi Soyayyar shi. Cikin farin ciki shima ya dawo gida…
***************************
*Garin kirika- samma*
Kirika-samma wani gari ne dake cikin Jahar Naija.. A bakin kofar wani Gida wata Budurwa ce na hango, Baka ce amma bak’in ta mai haske ne doguwa ce, mai kyaun diri da sura Masha Allah, Amma kana ganin ta zaka san wahala ce ta k’ara saka ta Ta koma bak’a sosai..
A gidin Bishiyar wani rimi take a zau ne, ga kayan wanki nan ba kad’an ba a gaban ta, wasu kuma ta shanya shi wasu tana wanke wa a cikin wata Babbar roba, A bayan ta wani tsoho ne zau ne ya jingina da bayan shi da Bishiyar, K’afar shi d’ayar a kumbure take….
Wata Y’ar Yarinya ce ta zo wajan su Ta ce” Anty Hanan ki amsa kud’in wankin ki inji Mommy na, Ta ce” wai kije ki taya ta aikin girki an jima Daddy na zaiyi bak’i..
Amsar kud’in Ta yi Tana murmishi mai had’e da hawaye Ta ce” to Islam kice mata daga an jima zanzo kinji! Islam Ta ce” to tukun ta tafi da gudu.. Hanan ta juya ta kalli Tsohon Ta ce” Baba ga kud’i yazo har ma naga da k’ari Ta yi min kud’in dubu talatin ne, Yan zu bari naje na siyo maka maganin na dubu shabiyar, sai na siyo mana kayan Abinci na mana girki,kaga yanzu su Saudat da Mahfuz sun kusa dawowa daga Makaranta, bari na bar wankin naje na dawo…..
Baba Ya ce” to Hanan kibi a hankali a dawo lafiya. to Ta ce” ta saka hijab d’in ta ta fita daga Gidan.. A hanya tana tafiya tana kukan halin rayuwar da suka tsunci kansu ita da K’anan ta da Baban ta…
Masu buk’atar littafin nan zaku Iya tuntub’a ta ta WhatsApp number ta +966599791573
zaki iya biyan kud’in ki ta wannan hanyar
0002482217 jaiz bank
Mu’utasim Ibrahim
Idan kuma katin waya ne zaki tura ta wannan number 08149194919
sai tura shedar ki ta h
wannan number +966599791573
MAMAN NUSAIBA CE✍🏻