K’ADDARA CE CHAPTER 4 BY MAMAN NUSAIBA
*WACECE HANAN?*
Hanan Y’a ce ga Malam Masa’ud. Malam Masa’ud Haifaffan garin *KIRIKA-SAMMA* dake cikin jahar Naija, su biyu Iyayen su ka haifa shida Yayar shi mai suna Rayya, haka suka taso cikin so da kaunar junan su shida Yayar shi. Lokacin da ta isa aure ta samu miji a nan cikin Garin, babu b’ata lokaci aka musu aure, Haihuwar ta d’aya Mijin ta ya tafi K’asar Saudiya.Sai da Yayi shekara biyu a K’asar Saudiya tukun ya biya mata kudin jirgi, ranar kasa bacci Tayi shima Masa’ud na taya Yayar tashi murna ganin zata koma k’asa mai Tsarki da zama ita da Mijin ta, cikin K’akanin lokaci aka gama mata komai. Ana gobe zata tafi sai da suka yi fad’a da Matar surukin ta, saboda Rayya irin masifaffiyar nan ce bata ragawa kowa a Unguwar su, idan Masa’ud na nuna mata Abin da take ba dai-dai bane, shima sai ta mishi tass wani lokacin ma har marin shi take..
Haka yake Hak’uri ya k’yale ta saboda Mutum ne mai sanyin hali, bashi da fad’a baya shiga harkar kowa, haka Allah Yayi shi.. Tinda Rayya ta tafi Saudiya bata tab’a zuwa Nigeria ba, a da lokaci zuwa lokaci tana aiko wa Masa’ud kud’i shida Iyayen su, kuma suna gaisawa sosai, Amma bayan Iyayen su sun rasu sai ta dena yiwa Masa’ud komai, ko waya ta dena kiran shi, idan ya kira number ta sai ace mai wayar a rufe take….
Hakan ba k’aramin tashin hankali Masa’ud ya shiga ba ganin Y’ar Uwar shi d’aya tak a Duniya amma ya kasa samun ta, har ciwo ya kwanta na tsayin kwana uku, haka ya shiga damuwa sosai, na rashin samun Rayya.. Daga k’arshe hak’ura Yayi ya cigaba da lamarin shi, ruwa yake turawa a kura yana bin Gida-Gida ya siyar da ruwan, da haka yake samun nacin Abinci Tinda bai san dangin su ba a garin, Iyayen su kawai ya sani bayan su baisan kowa daga dangin su ba.
Wata rana yana yawon Sana’ar tashi ne ya had’u da wata Budurwa kyakyawa da ita Murmishi ta mishi Ta ce” Sannu Malam Dan Allah ruwa zaka kawo zamu siya!.. Sai da ya lumshe idon shi jin zazzak’ar muryar Budurwar, Bud’e idon shi Yayi Ya ce” yauwa Y’an Mata to muje Gidan naku ko! Gaba Tayi yana binta a baya har suka je Gidan su. Suma Talakawa ne da alama ma Irin masu zuwa ne daga wata K’asar suyi d’an watanni su koma inda suka fito.. Ciki ta shiga ta kawo mishi d’ari biyar tana Murmishi Ta ce” to Mama na Ta ce” ka amshi wannan kullin kake kawo mana ruwa, idan ya k’are sai kayi magana a baka wani….
Cike da farin ciki Masa’ud ya amsa Yana washe baki Ya ce” to Y’an Mata na gode Insha Allah kullin zanke kawo wa, Yanzu muje a juye ruwan ko! To Ta ce” tayi gaba Ta kai shi har wajan randar su Babba mai tsayi, wadda ake kira da randar gwauro. Duka ruwan ya juye ya juyo zai tafi Gida sai yaga Budurwar nan a bakin k’ofa tana tsaye… Yana iso wa Ta ce” muje na rakaka . Masa’ud kam ji Yayi Yarinyar ta shiga ran shi lokaci guda, nan suka fita har bakin titi ta raka shi , suna ta hira kamar dama sun san juna, saida taga ya b’ace mata tukun ta koma Gidan su….
Shi kuwa Masa’ud Tinda ya koma Gida yake ta tunanin wannan Yarinyar daya gani , da k’yar Yayi bacci.. Yau ma yana kai ruwan ita ce ta raka shi har bakin titi ta dawo Gida.., Sannu a hankali shak’uwa mai karfi ta shiga tsakanin su, Sosai Masa’ud ke jin Yarinyar a zuciyar shi gashi ya kasa tambayar ta sunan ta, Amma yau Yasha alwashin zai tambayi sunan ta , kuma zai isar da sak’on dake cikin zuciyar shi , da haka ya bawa kanshi kwarin gwiwa ya nufi Gidan su…
Bayan ya zuba musu ruwan ta biyoshi kamar kullum, suna cikin tafiya ya tsaya Yana kallon ta, ita ma shi take kallo. Ta ce Yaya Masa’ud lafiya dai ko? Murmishi Yayi Yace” lafiya wai yama sunan ki ne? Dariya Tayi Tace” tab da wai baka san sunana ba ? Murmishi Yayi Ya ce” eh Wallahi ki fad’a min kiji! Tace” ni sunana Shafa’atu. Masa’ud Yace Masha Allah gaskiya sunan akwai dad’i. Dan Allah dama wata magana dake so muyi ! Allah yasa zaki amince da Abin da zan fada miki.
Shafa’atu Ta ce” karka damu ina jinka! ka fad’i duk Abin da yake ranka karka ji komai Yaya na.. Wani Sanyi Yaji sosai dan haka ya gyara tsayuwar shi Ya ce” Wallahi tin ranar da na soma ganin ki naji kin shiga raina, maganar gaskiya dai inason ki kuma so irin na aure, Allah yasa dai wani bai rigani ba! Rufe fuskar ta Shafa’atu Tayi tana murmishi, sai cen tukun Ta ce” nima ai na dad’e ina sonka dan haka na amince zan aure ka. Tana fad’in haka ta kwasa a guje ta shige Gidan su… Dariyar farin ciki Masa’ud Yayi Ya ce” Alhamdulillah Allah Abin godiya, ina sonki Shafa’atu na.. haka Ya koma Gida ranshi fal farin ciki ranar kusan kwana Yayi yana jera nafilfili na godiya ga Allah, yana rokon Allah ya zab’a musu Abin da yafi zama alkhairi a tsakanin su……
Cikin k’ankanin lokaci soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su, hakan Yasa Masa’ud turo wani mak’
otan su mai suna. Malam Kalamu wanda ya dauke shi tamkar Uba a gare shi.. Malam Kalamu yaje nema wa Masa’ud auren Shafa’atu. Da farko Maman ta k’in amince wa Tayi Ta ce” to su ba Yan Gari ba , taya zasu bada Y’ar su aure su tafi su bar ta. Da k’yar Baban Shafa’atu ya shayo kanta aka saka ranar bikin sati uku kacal. Sosai Malam Kalamu yaji dad’in wannan abu, haka ya koma Gida fuskar shi cike da farin ciki da anna shuwa. Da dare Masa’ud yazo wajan Malam Kalamu nan ya fad’a mishi komai. Sosai Yayi farin ciki nan ya dauko kud’in shi da yake tara wa ya bawa Malam Kalamu, Ya ce” a siyo duk Abin da ake buk’ata kafin lokacin auren yazo…..
Malam Kalamu ya lissafa kud’in yaga dubu dari biyu ne da dubu goma akai. Ya ce” to shikenan za’a siyo kayan lefe da duk Abin da ake buk’ata , amma ka aje wannan dubun goma ka dan yi d’inki ko? Cike da ladabi Masa’ud ya amsa ya tashi ya tafi.. lokaci nata tafiya haka ake ta shirye-shiryen biki an kai lefe duk Abin da ake buk’ata anka, komai dai dai-dai misali aka yishi……
Yau ce ranar da aka auren Masa’ud da Shafa’atu, ansha taro sosai Gidan Malam Kalamu ya cika da Y’an Uwan shi…Da dare aka kawo Amarya d’akin Mijin ta tasha lalle mai kyau. Ango ya shiga d’akin Amaryar shi. Sosai suke Amarcin su Masa’ud na k’okarin faran tawa Shafa’atu ita ma tana k’okarin mishi biyayya dai-dai Gwargwado…..
Auren su da wata shida ta samu ciki sosai Masa’ud Yayi murna nan ya soma tara kud’i yana asusu, haka yake ta kula da Shafa’atu babu Abin da take yi , duk da yana Talaka amma yana k’okarin sauke nauyin da Allah ya daura mishi… Cikin Shafa’atu na isa Haihuwa ta haifo Y’ar ta Mace kyakyawa mai kama da ita, murna wajan Masa’ud ba’a magana. Ranar suna Yarinyar taci sunan Hanan, Masa’ud Yayi wa Shafa’atu d’inkin fitowa daga d’aki kala uku, jaririya kuma ya siyo mata sunfi kala ashirin, shima ya siyo nashi kala biyu, sauran kud’in ya siyo musu kayan Abinci.. haka suka ringa kula da Hanan cikin so da kauna….
Hanan nada shekara goma Shafa’atu ta sake haifo Y’ar ta Mace mai kama da Masa’ud, itama tasha gata a wajan Iyayen nata, aka sha suna Yarinya taci sunan Saudat sunan Mahaifiyar Masa’ud ne aka saka mata.. Saudat dana shekara uku Shafa’atu ta sake haifo D’an ta Namiji, ai kuwa ranar Masa’ud yasha murna wannan karon ya samu Namiji,Yaro yaci sunan Mahfuz…. haka sukaci gaba da rayuwar su cike da kaunar junan su……..
Wata rana wadda ita ce wannan Gida zasu kira ta da bak’ar rana. Lokacin Mahfuz yana d’an wata shida, Maman Shafa’atu Tazo Ita da Baban ta Ta ce” ai ta had’a kayan ta zasu koma K’asar su.. Tashin hankali wanda ba’a sa maka ranar, fad’in tashin hankalin da Shafa’atu ta shiga b’ata baki ne, Ta ce ita fa baza tafi tabar Yaran ta ba.. Ai kuwa Maman ta Ta ce” dole ne mutafi kibar mishi Yaran shi .. Masa’ud ya durk’usa shida Shafa’atu suna rokon Mama da ta tafi tabar Shafa’atu anan.. Amma Ta ce” bata san zancen ba, kuma dole Ya saki Shafa’atu, ganin zata b’ata mata lokaci yasa ta kama Hannun ta taja ta har k’ofar Gida. Nan ta tsara Masa’ud Tace sai ya bata takardar Shafa’atu, shi kuma Masa’ud Yace” bazai iya sakin Matar shiba yana son ta, ai kuwa ta ringa sunfa masifa tana zagin shi…..
Da sauri Malam Kalamu yazo yana bata Hak’uri kar ta raba Uwa da Yaran ta, amma da yake bata da mutumci ko kallan shi bata yiba ta tura Shafa’atu cikin mota kuma Tace. Masa’ud ya bata takardar Y’ar ta, ko ta kaishi k’ara.. Malam Kalamu ne Yace wa Masa’ud ya saki Shafa’atu.. Haka yana ji Yana gani ya dauko takarda ya rubuta mata saki d’aya, ya bata.. Shafa’atu an kuka Ta ce” Masa’ud ka rike min Yara na Amana wata rana zan dawo gare ku. Masa’ud shima kuka yake Ya ce” zai rike mata amanar su..
Hanan na kuka tana kiran Maman ta, amma suka ja motar suka tafi daga k’ofar Gidan….
Hanan Tasha kuka lokacin gata k’arama ,haka suka hak’ura suka rumgumi K’addarar rashin Mahaifiyar su , tinda an raba su k’arfi da yaji.. Hanan taci gaba da ronon Mahfuz ,har ya kai Shekara biyu, basu da komai fitar da Baban nata yake yi ma yanzu baya iya wa saboda damuwa, nan da nan hawan jini ya kama shi, sosai Hanan ta shiga tashin hankali jin Baban ta na dauke da hawan jini, haka ta fara yin wankau tana ciyar da K’annuwan ta da Baban ta.. Ciwon k’afa ya kama Baba Hanan ta rasa inda zata saka kanta taji sanyi saboda damuwa, Allah ya taimake ta inda suka kawo mata wankau, nan suka dauke ta aikin Gida, idan taje Tayi aikin ta gama sai ta dawo Gida da Abinci dafaffe ta zubawa su Baba suci….
Haka rayuwar su taci gaba da tafiya cikin k’unci da damuwa. Ciwon k’afar Baba sai k’aruwa yake, ganin haka yasa Hanan
kaishi Asibiti, Aka auna shi suka rubuta mata magani mai tsada, sai da taje shagon siyan maganin ya fad’a mata ai dubu hamsin ne kud’in.. Sosai hankalin Hanan Yayi mugun tashi jin wannan Uban kud’in, ita ina zata same su? Nan ta fito da dubu goma ta bashi tana kuka ta durk’usa a gaban mai shagon..
Cikin kuka ta soma magana kamar haka: Dan Allah Abdul Majeed kaji k’aina! kaji tausayi na!, ka bani maganin idan aka bani kud’i na zanke kawo maka har na biya ka duka, ka taimake ni kaji! Wani tunani Abdul Majeed Yayi sai Yayi murmishi Ya ce” to shikenan Yan zu a nan ba maganin amma muje Gida sai na baki ki wuce… Ita kuwa Hanan ta dauka da gaske ta tashi tana share hawaye, ta ringa mishi godiya. Gaba Yayi tana binshi Har suka je Gidan shi, Ya ce” mata ta shigo ta Zau na sai ya duba shi a cikin d’akin da yake aje magungun nan shi. Ita Hanan da zuciya d’aya take binshi Har suka shiga wani d’aki dan girma, gefe guda duk kayan magugun nan ne a jere tsaf…
Kallon Hanan Yayi Ya ce bari na kawo miki lemu kisha naga kinsha rana. To kawai Hanan Ta ce” . Ya fita ya dauko lemon juice sai da ya bud’e ya zuba maganin bacci tukun ya kawo mata yana murmishin zai kwashi banza. Amsa Tayi ta mishi godiya ta d’an sha kad’an shima da k’yar ta hadiya sau d’aya saboda damuwa ta mata yawa.. shi kuma Abdul Majeed sai ya soma dube² a wajan kayan maganin nashi, sai da yaga baccin ya soma daukar ta ya dawo kusan ta Ya Zau na yana mata magana..
Hanan ko bacci kike ji ne? To kwanta ki huta idan na fiddo maganin zan tashe ki saiki tafi.. Hanan da take kamar Y’ar maye Ta ce”to nan ta kwanta ta k’udundune k’afar ta cikin babban hijab d’in ta… Sai da ya bari ta yi nisa a baccin ta ya cire mata hijab d’in, duk wani kayan jikin ta saida ya raba ta dasu, ya bar daga ita sai pant da bra, yau sai murna yake zai kwashi gara….
Dariya Yayi Ya ce” ai yau sai nayi yadda kike Yarinya komai naki Yayi min Wallahi, yana maganar yana hawa gadon, ya kai hannu zai rumgume ta ta bude idon ta.. A razane ta tashi zaro ido tayi ganin bata da kaya a jikin ta,aikuwa ta kwala ihu da sauri ta dauki zanin ta ta daura ta saka rigar ta da hijab d’in ta, Kuka sosai take zuciyar ta cike da tsoro.. Kallon Abdul Majeed Tayi Ta ce” Allah ya isa tsakani na dakai Azzalumi mugu macuci, Insha Allah kaima sai anyiwar Y’ar Ka Abin da kaso aikata wa akai na dan iska marar mutumci… Sai da ta zazzage tas tukun ta baro Gidan tana kuka hannun ta aka.. Tana zuwa Gida taga Baban ta har taji sauke yana zau ne, da sauri ta k’arasa wajan shi ta zube ta kusan ta tana kuka.. cikin damuwa Ya ce” Hanan meyasa faru ne?
Kwashe komai Tayi ta fad’a wa Baba tana kuka. Lallab’a ta Yayi tayi shuru nan ta mata nasiha sosai, a nan ne yake fad’a mata ai Mijin Matar da take aiki a Gidan su ne ya siyo mishi magani har na dubu dari, nan ya dauko ya nuna mata .. Wani kukan Hanan ta kuma sakawa tana godewa Maman Islam, tasan. Ita ce ta Mijin ta suka zo Gidan su…. Washe gari da taje ta ringa yi musu godiya, suka ce mata ba komai ai an zama d’aya. Haka sukaci gaba da rayuwar su tana kula da Baban ta da K’annuwan ta.. Yanzu Hanan tana da shekara 22 years , da haihuwa……
Yau dai Iman fushi take,ko customer d’in ta ma sunga cenji ,sosai suke mamakin ganin Iman, Yau bata kula kowa fuskar nan a had’e take kamar hadari, lokaci zuwa lokaci Tana share hawaye sai kuma ta kalli Sultana ,idan suka had’a ido sai ta banka mata harara.. Abdul Malik ne yazo wajan so fuskar shi dauke da k’ayataccen Murmishi irin na in kaya abar kaunar ka, k’araso wa Ya yi wajan su ya Zau na yana kallon Masoyiyar tashi… Cike da mamaki yake Kallon ta ganin, yadda tayi kicin-kicin da fuska, kuma Tana share hawaye…
Cike da Al’ajabi Ya ce” Imani na! Lafiya kike kuka haka? Waye ba lafiya? Wani ne yaci Abinci bai biya ba? Dan Allah kiyi min magana! Bana son ganin kukan ki kinji! Ai kuwa kamar jira take ta saki sabon kuka tana kallon Sultana, har shid’ewa take, saboda da farko kukan zuciya take hawayen fili, sai Yanzu da Abdul Malik Yayi magana taji kukan ya fito fili… Cike ta tashin hankali yake fad’in. Haba Iman wai yau d’in nan maiya sameki? Ki fad’a min waye ya tab’a min ke? Yau yaga yadda ake tasa Mutum a Kasuwar nan…..
Iman cikin kuka ta soma magana. Ba ita bata ta sani kuka, kuma tak’i kulani ko kallo na tak’i yi, Shikenan Yanzu bata sona ,waiyo Allah ni ka bata Hak’uri tamin magana, ka gani ko! Harara Ta takeyi fa Abdul Malik, kace tamin magana dan Allah! Ni Gida ma zan tafi Tinda bata kulani. Ita kuwa Sultana danne dariyar ta Tayi, so take yau ta share Iman, saboda ta gaji da masifar ta ita kowa ma bata bari ba, dole take taka mata birki, saboda ita ce tafi kowa kusanci da ita, dan haka zata yi k’okarin daura ta akan hanya, ta dena fad’an nan…
Abdul Malik Ya ce” Sultana dan Allah ki kula ta! Kinga fa kuka take saboda kinki kula ta, ki daure ki mata magana Sultana! Bana son ganin kukan ta…kuka Iman Ta kuma saki&nbs
p; Ta ce” ka gani baza ta min magana ba! Haka take min daga Tayi fushi, Gida zan tafi . Tana fad’in haka ta tashi hannun ta akai Tana rusa kuka kamar ance mata Mama ta rasu, ta kama hanyar Gida… Abdul Malik Ya ce” haba Sultana! Me yasa bazaki hak’ura ba? To wai ma menene ya had’a ku?
Sultana kallon hanyar da Iman tabi take yi, sai taji ta bata tausayi , kallon ta ta dawo ga Abdul Malik Ta ce” ka rabu da ita ai tasan Abun da tamin idan na dena fushin sai mu shirya gobe. Mutanen wajan suka ce gaskiya Sultana baki kyauta ba! Ai ya kamata kiyi Hak’uri tin ta baki Hak’uri, Yanzu gashi ta tafi ko Abinci bata siyar ba.. Shuru Sultana Tayi bata ce komai ba, duk jikin ta sai ya mata sanyi, haka ta siyar da Abincin har na Iman, tukun ta had’a kayan ta fito bakin titi, mai Nepep ta tare Ta shiga Tace ya kaita Unguwar su Iman….
Yana kai ta ta bashi kud’in shi , tukun ta shiga Gidan da Sallamar ta. Turus Ta tsaya ganin Iman kwance a bakin k’ofar Gida, da alama dai Gidan ba kowa. Da gudu ta k’araso inda Iman take a kwance kamar gawa, da sauri ta ciccib’o Iman Ta daura kanta à kan ciyar ta ta soma kiran sunan ta.. Iman! Iman !! Iman!!!ta fad’a a firgice jin bata numfashi.. A gigice take danna k’irjin Iman tana kuka. Ta ce” na shiga uku Iman daga wannan Abun kike neman Salwantar min da rayuwar ki, dan Allah Y’ar Uwa ta ki tashi! Karki barni ni kad’ai a Duniyar nan! Iman! !! Ta kuma fad’a da k’arfi…..
Ganin Abun bana k’arewa bane ta tashi à guje ta shiga cike, dakin ta bud’e ta dauko ruwa mai sanyi sosai, da gudu ta dawo wajan Iman.. Ruwan ta zuba mata duka à fuskar ta ,tana kiran sunan ta. Da k’arfi Iman taja numfashi tana saki sabon kuka, Bud’e idon ta Tayi ta dauke su akan Sultana, da sauri ta k’ankame Sultana tana fad’in. Y’ar Uwa ta kiyi Hak’uri ! Wallahi na dena jan kowa, bazan sake ba, bana son ganin kina fushi dani, kar kiyi fushi kinji Sulty na!
Da sauri Sultana Ta d’ago ta ruka rumgume juna. Sultana Ta ce” na dena fushi take Y’ar Uwa ta, saboda wannan maganar har kike suma Iman! Kodai ciwon kine ya tashi da kika zo Gida? Dan Allah ki dena min irin wannan! Wallahi kin bani tsoro sosai na dauka mutuwa suka yi, ashe suma ne…Iman Ta ce” na dena Aminiya kiyi Hak’uri ! Sultana Ta ce” Amma ciwon naki ne ya tashi ko? Shiyasa naga kin suma.. Iman Ta ce” tin kafin nazo Gida aka soma rike min k’afa ta da k’yar ns k’araso Gida, nidai nasan na fito daga cikin mota, to daga nan ban sake ina nake ba sai Yanzu da kika zo…
Sultana Ta ce” tashi muje ciki kisha maganin ki. Tashin ta Sultana tayi suka shiga ciki, drowar ta bud’e ta d’auko maganin ta bata tasha, kwantar da ita tayi ta cire mata hijab d’in ta, kayan ma ta cire mata tasa mata marar nauyi ta lullub’e ta da bargo, Abin Abinci ta dauko ta tashi ta zaune. Da kanta Ta ringa bata a baki har ta k’oshi, tukun ta dauk’e Abincin ta maida kitchen, ruwa ta dauko ta bata mai sanyi.. Lumshe ido Iman Tayi tana sauke ajiyar zuciya akai-akai, saida ta kusan minti sha biyar tukun ta dena sauke ajiyar zuciya…
Ganin haka yasa Sultana d’auko Alkur’ani mai girma ta bud’e ta soma karanta mata, surorin Alkur’ani. Iman tin tana rawar jiki har ta dena sai juya kanta da take yi, bakin ta rawar sanyi. Mik’e wa Sultana Tayi Ta lullub’e ta da wani bargon, ta dawo taci gaba da karatun ta, sai da taga Iman bata motsi alamar ta samu bacci tukun ta ake Alkur’anin tana share hawayen tausayin K’awar tata. Tashi Tayi ta fita waje, kayan tallar nasu ta wanke su duka, Tayi shara ta daura girki, shinkafa da wake dafa duka tayi , tana gama wa ta dawo d’akin ta yaye mata bargon d’ayan tabar mata d’aya ganin had’a jib’i.. kayan ta ta had’a ta fito zata tafi Gida, sai taga Mama ta shigo Gidan da Sallamar ta….
Amsa mata Tayi Ta ce” Mama sannu da zuwa. Mama na murmishi Ta ce” yauwa Sultana har kun dawo? Ina sauri nazo na daura Abinci kar Iman Ta dawo ban gama girki ba,ashe ma har kunzo, da Mamma d’in ki muka je Gidan haihuwa.. Sultana Ta sunkuyar da kanta kar Mama ta gane kuka take sai Ta ce” ayya Allah sarki nima na jima da zuwa, Iman ce jikin ta yau ciwon ya tashi sai d’azu ma Tayi bacci, shine nace bari na wuce nasan duk inda kike kina kusa… Cike da damuwa Mama Ta ce” Allah ya miki albarka kinji! Bari naje naga jikin nata, ki huta gajiya kinji!
Murmishi mai had’e da hawaye Sultana Tayi Ta ce” to Mama na tafi ,nan ta fita ita kuma Mama ta shiga ciki.. Sultana n’a tafiya tana tausaya wa Iman da wannan ciwon yake zo mata lokaci² , da wannan tunanin ta isa Gidan su…
*************************
Hanan ce ta fito zata tafi Gidan Maman Islam don yi mata aikin gida. Su Saudat ne suka fito a Tare ita da Mahfuz, Saudat Ta ce” Anty ki kai mu school d’in.. Hanan ta juyo Ta ce” to kuzo muje, Baba mun tafi ana Sallar Azuhar ko kusan ta zan dawo.. Baba Ya ce” to ku dawo lafiya Allah ya tsare ku a duk inda kika je, Allah ya muku albarka. Ameen suka ce tukun suka tafi. Har Makarantar su ta kai su tukun ta nufo Gidan Maman Islam. Tana sauri dan taso ta makara…
A bakin get d’in Gidan suka yi kusan karo da Baban Islam da Islam da alama shima Makarant
a zai kaita.. Hanan Ta ce” dan Allah kayi hak’uri Yaya Faris! Wallahi ina sauri ne ban ganka ba! Shi kuwa kafeta Yayi da ido kamar ya samu TV, sai murmushi yake zubawa. Hanan jin Yayi shuru ba amsa Yasa ta d’ago taga ko dai ya,tafi ne, Tana d’agowa taga ita yake Kallon, gaban tane Yayi fad’in rass, ganin Yadda yake Kallon ta bako k’iftawa, Ta ce” Yaya Faris!
Da sauri ya dawo daga Duniyar tunanin daya tafi, Ya ce am..Am ba komai ki shiga ai bata nan ma taje wajan aure, amma Ta ce” inkin zo ki wanke kayan su anan basai kinkai Gidan ku ba, kuma Ta ce” ki gyara d’akina da nata, san nan ki mata girki bayan La’asar zata dawo…Hanan kuwa mamaki ne ya kama ta jin yadda Faris ke magana kamar bashi ba. Ta ce” to shikenan zanyi bari na shiga ciki. To Ya ce” tukun ya fita ita kuma ta shiga ciki…..
Tana ciki ta soma aikin da yada kawo ta, gyaran Gidan ta soma yi ta wanke toilet d’in, tukun ta shiga d’akin Maman Islam Ta gyara mata fess, tana gama wa ta shiga na Islam shima ta shima ta gyara tukun ta nufi na Baban Islam. Wani daddadan kamshi ne ta shak’a sai da ta lumshe idon ta, a hankali ta shiga ta soma gyarawa, toilet d’in ya ta fara gyara wa tukun ta gyara d’akin, sosai d’akin ya burge ta ganin komai tsaf kamar d’akin Mace….
Tana gama komai sai ga Faris ya dawo daga aiki, sannu da zuwa ta mishi tukun ta kawo mishi ruwan. Kallon ta Yayi Ya ce”na gode Hanan. Ita dai bata ce komai ba , ta shige kitchen d’in ta k’arasa wanke kwannukan tukun ta soma shirin tafiya Gida. Fito wa Tayi Ta ce” na tafi Gida. Da sauri Faris Ya ce” to har zaki tafi baza ki tsaya ba sai tazo tukun! Hanan Ta ce” a a Yaya Faris su Saudat sun kusa taso wa daga school zan yi sauri naje na musu girki ne. Na gama komai sai gobe idan na dawo Insha Allah. Tana fad’in haka Tayi saurin barin parlon ta fita..
A jiyar zuciya Ya sauke Yana murmishi Ya ce” gaskiya Hanan kin sosai ina son Mace mai nutsuwa kamar Matata, ina sonki Hanan. Haka Ya ringa surutun shi har ya gama cin abincin ya shiga d’akin shi, wani sanyi Yaji ganin ta gyara mishi ko ina fess dashi, nan ya kwanta nan da nan bacci Yayi gaba da shi..
Hanan na zuwa Gida Tayi sauri ta gama girki kafin K’annuwan ta suzo. Ta gama kenan suka zo , wanka ta musu ta canja musu kayan su , Abincin ta zuba musu ta dauki kayan ta wanke su sai da ta gama komai tukun taci Abinci… Washe Gari kamar kullum ta kai su Saudat school tukun ta fice aikin ta. Yau ta samu Maman Islam a parlon zau ne, da murnar ta ta k’araso. Ta ce” Anty sannu ta zuwa an dawo lafiya?
Murmishi. Maman Islam Tayi Ta ce” yauwa Hanan ya kike ya jikin Baban ,da fatan yana samun sauk’i? Hanan Ta ce” eh Anty Alhamdulillah Baba ya samu sauk’i sosai.. Sai da suka taba Y’ar hira tukun Hanan ta tashi taje ta kama aikin ta. …Sai da ta gama gyaran Gidan tukun ta dawo kitchen suka fara girki da Maman Islam, suna gama wa Hanan Tace Gida zata tafi, Maman Islam Ta ce” ta Zauna tana son suyi magana sai Abban Islam yazo, to Tace ,nan ta zauna suka ringa hira…..
Sun jima suna hira sai ga Baban Islam yazo, sai da yaci Abinci ya koshi tukun ya dawo inda suke.. Ita kuwa Hanan ta k’agara taji maganar da zasuyi , saboda bata so take zama à inda Baban Islam yake duk sai ta kasa motsin kirki ma.. Maman Islam Ta ce” Hanan! Da sauri Hanan ta d’ago dara-daran fararen idanun ta ta sauke su akan Maman Islam, Ta ce ” Na’am Anty.. Shi kuwa Faris zuba mata n’a mujiya Yayi ganin yadda ta masa cikin tsoro…
Maman Islam Ta ce” Dama ina so muyi wata muhimmiyar magana ne dake Hanan, Allah yasa zaki amince da buk’atar mu nida Mijina! Hanan Ta ce” ai ki fad’i duk Abin da kikeso Anty ni kuma indai ina dashi zan miki matuk’ar bai sab’awa tarbiya da Addinina ba, kuma idan ina da Abin da kuke buk’ata a gareni zan muku shi , saboda kune dangi na! Allah ne gatan mu ,amma kune gatan mu, ki fad’i buk’atar ki Insha Allah zanyi k’okarin miki biyayya. Hanan Ta k’arasa maganar tana share hawaye…
Maman Islam Ta ce” to Alhamdulillah Masha Allah, nagode da wannan karramawar , jiya ne bayan na dawo da dare,sai Faris ya sameni da wata mai magana wadda tayi min dad’i har bacci na kasa saboda na k’agara kizo na fad’a miki. Cikin Tsoro Hanan ta kuma kallon Maman Islam Ta ce” Allah yasa ba wani lefin na mishi ba ni Hanan! Tayi maganar a raunane.. Sai da Maman Islam Tayi dariya ganin Yadda Hanan ta tsorata. Ta ce” ba lefin da kikayi ya sameni ne Ya ce” min shifa yaga kina da nutsuwa da hankali, ka kin burge shi dan haka Yace na fad’a miki zaki aure shi? Allah yasa dai wani bai riga Mijina ba! Idan akwai ki share shi ki auri Mijina muyi zaman mu nida ke,kinga nasan halin ki ,kema kinsan nawa duk da shi kishi da ban yake amma na san zamuyi zaman lafiya dake, da yaje ya kwaso min wadda bansan halin taba gara ke ya aure ki, nasan duk rintse bazaki nuna min wani hali marar kyau Ba….
A mugun firgice Hanan ta d’ago kanta har tana fad’o wa daga kan kujerar da take zau ne, Ta ce” An…Ant…Anty…
< br />
MAMAN NUSAIBA CE✍🏻