K’ADDARA CE CHAPTER 7 BY MAMAN NUSAIBA
_Nomal N300 ne_
_Vip N 500 ne post sau biyu kullin_
_*Domin k’arin bayani ku tintib’eni ta WhatsApp number na + 966599791573*_
🔔📚
*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
*⚜️©J.A.W📚🖌️*
بسم الله الرحمن الرحيم
Hanan ji tayi kamar ta saki zawo saboda tsananin tsoro daya cika mata zuciya dama gangar jiki, jin ya kuma had’a ta da jikin shi sai ta saddakar yau ai kawai Yaya Faris Fad’e zai mata.. Shi kuma gogan yana kallon ta bako k’iftawa so yake yaga iya gudun ruwan ta da k’arfin ta, shi yasa ya matse ta kamar wata Y’ar shi, Hannun shi ya cire daga bakin ta daya rufe mata…
Da sauri Hanan Ta matso hawaye Ta ce.” Yaya Faris please ka cikani! Wallahi kila ka karya min kafad’a wannan matsa haka kamar ka samu soban wasan ka! To nidai ka sakeni ko kuma Anty na zuwa nace mata ka rumgume ni kamar wata Baby Jaririya. Ta k’arshe maganar tana turo mishi bakin ta…..
Murmishi Yayi yana binta da namujiya , ji yake kamar ya maida ta ciki dan so da k’aunar da yake mata, sai dai ita tsoron shi ma takeyi, baisan yaushe zata dena jin tsoron shi ba a matsayin shi na Mijin da zata aura ba. Ajiyar zuciya ya sauke Ya ce.” To shikenan naji zan sakeki amma sai kin min alk’awarin bazaki k’ara jin tsoro na ba! Idan kuma naga tsoron na nan to Wallahi gobe sai naje wajan Baba ya daura mana aure in ta tsoro kuma, wai ma meye à jikina wanda in kika ganni kike tsoro na? Haba Hanny bana son kina jin tsorona nifa Mijin kine Insha Allah!
Kara turo baki Tayi tana k’unk’unen magana Ta ce.” Kaji wani sabon salo gemu a kafad’a! Tab ikon Allah ikon gaske wai kiran salla da usir kut! Wai hadda cewa nifa Mijin ki ne, kaji neman guri a wajan Yaya Faris hmm, to bazaa dena jin tsoron naka ba! Ni ai ba Matar ka bace da har kake rumgume ni saika bari inka aure ni kake tab’a ni ai ko! To saina dena zuwa Gidan naku ma ehee….
Duk maganar da take bata san tana fitowa fili ba, shi kam Faris tagumi Yayi yana kallon yadda bakin yake mutsowa in tana magana, dariya sosai yake yi ciki² saboda karta gane yaji, saida ta gama ne Ya ce.” Kai lalle Yarinyar nan ni kike fad’awa magana ko? To kin jawa kanki gobe saina je wajan Baba an saka bikin mu nan da wata d’aya, badai kina cemin bazata dena ba ko?
Da sauri ta rufe bakin ta tana zare ido jin Abin da yake fad’a Ta ce.” Waiyo Allah ni Yaya dan Allah kayi hak’uri karka je! Nifa gaskiya bazanyi auren cin amana ba, haka kawai ka wani mak’ale min, nidai karka je kaji!
Mik’ar da ita Yayi ya zaunar da ita a gefen shi, ya had’e rai Ya ce.” Ai baki isa ba Yarinya tinda kika fad’i haka dole gobe a saka ranar bikin mu nan da wata d’aya, badai kin renani ba to zanyi maganin wannan bakin naki da kullin sai kin turo min shi in muna magana! Yana gama Fad’ar haka ya mike tsaye zai bar falon……
Da sauri ta rike k’afar shi tana kuka Ta ce.” Haba Yaya nifa da wasa nake maka fa! Sai kace baka san wasa ba! Wallahi naji zan aure ka amma karka ce wannan shekarar , nasan in kaje Baba zai amince tinda ya riga daya baka ni, to meye na gaggawa kuam? Ka bari sai sabuwar shekara kaji! Wallahi bana son had’a ido da Anty gani nake kamar zata gane ka rumgume ni…..
Danne dariyar shi Yayi yana fad’in. Tab ban san wannan zancen ba kuma zuwa sai naje gobe zan tura Kawuna wajan Baba, gyarama ki sakeni naje na kira shi a waya na fad’a mishi yaje a saka. Ranar bikin mu gobe, dan haka kin kusa dawowa Gidan nan na har abada…….
Hannu ta daura akai ta saki wani marayan kuka sai Kallon shi take, shi kuma ya daure fuska dan kar taga ko wasa yake mata, cikin kuka Ta ce.” Wai da gaske zuwa zakayi Yaya? Tana k’iftace² kamar wani sabon kamu……
Hannun ta ya cire daga rik’on datawa k’afar shi Yayi saurin barin falon ya shiga d’akin Ilham ya kulle duk da yasan bazata biyoshi ba…..
Hanan kamar zatayi hauka ganin da gaske fa Yayan nata yake nan da wata d’aya ya zama Mijin ta, mik’ewa tayi taje da d’auki Abincin dake kula d’aya ta saka hijab d’in ta ta fita daga falon. Tafiya take tana kuka saboda tsoro da fargaba daya cika mata zuciya , inta tuna maganar auren nan, da ta kusa isa Gida sai ta share hawayen ta ta biya wani shago ta siyo musu kayan miya da mai , tana zuwa Gida bata bari Baba ya gane ba ta shige d’aki….
Tana nan zaune su Saudat suka shigo suna kiran ta, fitowa Tayi tana musu murmishin yak’e Ta ce” kun dawo ! Sannunku..
A tare suka ce eh Anty mun dawo kuma yunwa muke ji. Hanan ta kawo su wajan Baba suka zauna ta zuba musu Abincin gaba daya ta tura musu a gaba, sai da sukaci suka koshi sukayi saura, sai Tace” musu suje su wanke hannun su su kwanta su huta kafin lokacin zuwa Islamiyya Yayi” to suka ce suna shigewa d’akin…….
Ajiyar zuciya ta sauke ganin Baba ma ya koma bacci sauran Abincin ta had’a a kwano daya ta gyara zaman ta ta soma ci, tana gamawa ta dauke kwanukan ta wanke tukun itama ta dawo d’akin ta kwanta a kusan su Saudat, cike da tausayin Yaran ganin za’a rabasu………
Washe Gari kamar yadda Faris Yacewa Hanan haka kuwa ta gani, Kawun shi ne yazo wajan Baba aka saka ranar bikin wata d’aya kamar yadda Faris ya buk’ata, ai kuwa ranar kwana tayi batayi bacci ba tana kuka, har kusan Asuba kafin bacci Yayi gaba da ita…….
************************
A b’an garen Abdul Malik yana tafiya Gida ya nufa jiki a sanyaye yake driving duk ya rasa nutsuwar shi, sai numfashi yake sauke wa akai-akai, Unguwar _Quartier Jacque_ ya nufa iya damuwa yau yana cikin ta, wani Babban get ya nufa back hon Yayi aka walgale mishi kofa ya shiga ciki, yana gama packing ya fito daga motar ya nufi ciki.
Da Sallama ya shi kutsa kanshi cikin tafkaken falon , wata Hamshak’iyar Hajiya n’a gani zaune taci ado, kana ganin ta kasan hutu da jin dad’i sun zauna mata, Doguwa ce mai jiki dai-dai misali, wankan tarwad’a ce gata kyakyawar gaske , kana ganin ta zaka san ita ce Mahaifiyar Abdul Malik, gefen ta wata Budurwa ce tana kallon TV wadda bazata wuce shekara 17 ba da haihuwa..
Amsa mishi Sallama Tayi Tana fad’in. A a My Son lafiya na ganka jiki a sanyaye? Ko duk gajiyar ce?
Abdul Malik kamar zaiyi kuka yakeji ganin k’anwar shi saiya daure ya aro jarumta ya daura murmishin yak’e a kan fuskar shi Ya ce.” sannu da hutawa Mommy bafa komai kawai na gaji ne. Kallon k’awar shi Yayi Ya ce.” Ke tashi fice mana à nan !
Shuru Tayi kamar bada ita yake ba sai da ya kuma mata wata tsawar tukun ta mik’e tana fad’in. Kai Yaya kai bakaso in zaka bawa Mommy labari naji, to ai ba wani zan fad’a wa ba please kayi hak’uri kaji Yaya!
D’ago da idon shi Yayi Ya ce.” Asma ! Meyasa kika renani wai? Zaki fice ko saina make ki nan banza shashasha kawai…
Da gudu tabar falon tana saka kuka saboda film d’in da take kallo yazo wajan da takeso..
Mommy Ta ce.” Ina jinka ya akayi?
Sunkuyar da kai Abdul Malik Yayi yana jin kamar zuciyar shi zata fasa kirjin shi ta fito saboda da damuwa, da k’yar ya iya fad’in. Mommy Tace” wai bata sona saboda ni D’an masu kud’i ne, please Mommy ki taimake ni! Wallahi inban auri Iman ba zan iya rasa hankali na…
Cike da tashin hankali Mommy Tace.”wacece Iman kuma? Kuma waye Maihaifin ta da har ta dubi idon ka Tace” bata sonka?
Abdul Malik Ya bata labarin Iman da duk abubuwan da sukayi a baya har zuwa na yau data ce bata son shi saboda suna da kud’i…..
Ajiyar zuciya ta sauke Ta ce.” Lalle Yarinyar nan ita wani irin tsattsauran ra’ayi ne gareta da har bata son mai kudi? In banda shirme irin nata ina taji ana irin haka, to kayi hak’uri zata yarda ta aure ka kaji! Bana son ganin ka cikin damuwa, ku biyu kad’ai Allah ya bamu banaso wani abu ya sameku, kayi hak’uri zatq soka kaji!
Wani sanyi Yaji saiya matsa kusan Mommyn nashi ya kwanta a cinyar ta yana Jan numfashi, ita kuma tana shafa kanshi suka ci gaba da hira…..
************************
Hanan ce zaune ita da Ilham tazo Gidan su ganin kwana biyu bata zoba, sai da tazo ta ganta kwance ba lafiya, cikin tashin hankali take tambayar ta mai yasa meta ne? Tace” zazzab’i ne magani ta bata tasha tukun ta taimaka mata ta zauna daga kwanciyar datayi….
Ilham Ta ce.” Hanan dan Allah ki dena sakawa kanki damuwa akan wannan lamarin! _K’ADDARA CE_ fa tasa auren nan zai tabbata ! To ki kwantar da hankalin ki kinji ko!
Ajiyar zuciya ta sauke Ta ce.” To Anty zan dena amma Wallahi ni kunyar ki nake ji” wannan Abun kamar a mafarki nake ganin shi..
Karki damu K’anwata ai komai da kika gani a rayuwa ya sameka yo _K’ADDARA CE_ Dan haka ki dena tunanin komai K’anwata! To Hanan Ta ce” Amma duk ranta babu dad’i, haka sukaci gaba da hira har yamma tukun Ilham Ta mata Sallama ta tafi Gida. …..
Washe Gari Faris yazo ganin ta, wajan Baba ya fara zuwa suka gaisa tukun Baba Yace” mishi Hanan na d’aki, to Yace” san nan ya nufi d’akin da Sallama. …
D’ago da fararen idanun ta Tayi tana amsa mishi Sallamar. K’araso wa Yayi inda take Zau ne shima ya zauna yana binta kallo ganin yadda ta rame sosai a hankali Ya ce.” Hanny ya jikin ?
K’asa dakai Tayi tana wasa Y’an yatsunta, amsa mishi gaisuwar daga haka bata sake cewa komai ba.
Sake matsowa Yayi Ita ma ta matsa gefe tana banka mishi harara, dariya Yayi Ya ce.” Ki tsaya mana zanji ya jikin naki ne fa koda zazzab’i ko babu..
Hanan ta turo baki gaba tana murza ido ita ala dole tana hawaye, Ta ce.” Wai kai Yaya meye yasa dole saika taba jikina ne? Nifa bana jin dad’in hakan ka dena ba kyau, ka bari in ka aureni komai ma sai kayi..
Ihmm Faris Yace” yana mata wani shu’umin kallon mai narkar da zuciyar wanda akewa, kyale ta Yayi danya lura Yarinyar zata koma Mafad’aciyar ba arziki, sai ya jata da hira har ta saki jikin ta ta ringa bashi labari masu dad’i, shi kuma yana murmishi yana bata amsa inta tambaye shi.. ….
*************************
Su Sultan ne suka shigo Kasuwar Imam fuskar nan kamar Soja zaije filin daga, sun nufi wani rumfa zasu zauna Imam ya juya kamar daga sama yaga Imam ta shak’i wata katuwar mata tana surfa ruwan masifa, murmishin mugunta Yayi Yace” yar Mitsiyata yau saina rama Abun da kika min inba n….
Idan kin karanta ki daure kiyi comment sister 🤝🏻
_Taku har kullin ( Maman Nusaiba ce)_