K’ADDARA CE CHAPTER 8 BY MAMAN NUSAIBA
Inda su Iman suke Imam ya soma k’okarin nufa, Sultan ne Ya ankara da barin Imam gurin da sauri ya janyo shi da karfi yana fad’in. Kai Malam! Ina zakaje ne haka? Naga kuma kana nufar cen inda Y’an Mata suka taru, ko kasan wata a cikin suke?
Imam cikin jin haushi ya tsaya Ya ce.” To ina ruwan ka ! Ai nace maka saina rama abun da waccen marassa tarbiyar tayi min, shine Yanzu na ganta zanje na rama ka hanani.
Sultan Ya ce.” Wai kai Imam meye yake damun kanka ne? Ayi Mutum sai bak’ar zuciya haba da Allah! To Wallahi inma kaje ka taro Aljannun wacce Yarinyar ni dai babu ruwana, kana gani dai ranar yadda ta maka saida wani yazo ya kwace ka, shine dan b’atan basira kake neman komawa ko? To kazo ma Yanzun nan Daddy ya kira Ya ce.” Mu koma Gida tinda mun daura kayan da mukazo siya, kuma kaga Alhaji Aliyu mai atamfa d’in ma baizo ba! Dama au Sallama ce mukazo yi masa to tinda baya nan mu koma muje mu had’a kayan mu mutafi Gida kana jina dai ko!
Imam ko k’ala baice ba ya juya suka koma ,motar su suka hau suka koma hôtel d’in da suka kama, babu b’ata lokaci suka had’a komai nasu suka fito zuwa Airport, basufi minti goma ba jirgin _TEEGO_ ya sauka , Sultan shiya shiga musu da kayan su ciki saboda Imam ya had’e girar sama data k’asa , shi ala dole fushi yakewa Sultan daya hana shi yaci mutumcin Iman yaga waye Uban ta a cikin garin Kwatano, shiyasa da sukazo yaki kulashi yana ta had’e rai…..
Sultan Ya dawo inda yake Ya ce.” Malam saika tashi mutafi ko in kuma anan zaka zauna saika fad’a min naji! Idan kuma har Yanzu fushin ne kake yi to koma cen kasuwar ka yi duk Abun da kakeso , Mutum sai shegen wulak’anta Talaka dan kawai ka fishi arziki, to kayi duk Abun kaga ya dace rayuwa ce nidai iya bakin k’okari na ina yi a kanka Allah ya gani, dan Allah Aboki kake sawa zuciyar ka ruwan sanyi! Yanzu kai ba abun kunya bane kake fad’a da Mace? Kuma Macen ma Yarinya Y’ar k’arama wadda bata fi shekara 15 zuws 16! To ka tashi mutafi nace in kuma ba haka ba in kira Daddy na fad’a mishi komai shashasha kawai mai banzar zuciya. Sultan Ya k’arasa maganar yana k’okarin fiddo wayar shi ya kira Daddy…..
Wani Tuk’uK’in bakin ciki ne ya rufe Imam jin Yace” mishi mai banzar zuciya , kallon shi Yayi Ya ce.” Ni kake cewa mai banzar zuciya Sultan? Akan Y’ar Talakawa mai talla a titi marar tarbiya! Shine ka Zab’e ta a kaina ko? To Wallahi nayi alk’awari koba Yanzu ba duk ranar dana sake haduwa da ita saina kakkarya ta, saina mata rashin mutumcin dako wani akace ta zaga bazata tsaya a wajan ba, badai na gane fuskar su ba har ita dayar tinda a dalilin ta sobar ta taci Mutumci na , dukkan su saina nuna musu ruwa ba sa’an kwando bane Wallahi! Saina wulak’anta su naga waye Uban su dame suke tak’ama ne da har suka min haka! Yana fad’in haka ya tashi fuuu ya bar wajan ya shiga cikin jirgin…..
Sultan girgiza kai kawai Yayi, yana mamakin Zuciya irin ta Imam Ya ce.” Allah ya shirye ka Imam Allah yasa ka gane Annabi ( S.A.W) ya faku, kai inba hauka bama meye da wani b’ata rai a wannan Abun? Naga dai marin mata Y’ar Uwa kayi ta rama mata, to meye à ciki? Insha Allah wata rana sai wannan Yaran daka ke son wulak’anta wa sun taimake ka.. Wayar shi ya maida aljihu ya shiga ciki shima, babu jimawa jirgin su ya d’aga zuwa K’asa _TEEGO_……
A ban garan su Iman kuwa tinda ta shak’i wata Budurwa suka kama dambe, da k’yar aka rabu su shima sai da wannan Tsohon ya mata magana tukun ta saki ta. Kallon ta Iman Tayi Ta ce.” Wallahi kinci darajar Baba Tsoho da sai na koya miki hankali a Kasuwar nan! Kuma ki fita harka ta inba haka ba zakiga yadda zanyi wajijin kura dake a kasuwar nan! Ni bana shiga harkar Mutum amma inka shiga gonata to saina keta maka rigar Mutumci, Jaka aladiya jahila kawai wandda bata san mahimmancin kanta ba bare Addinin ta .. Iman sai huci take tana idon ta Yayi jajur saboda masifa nacin ranta, dama neman soban yi take sai ga shi wannan Budurwar ta shiga gonar ta.. …..
Sultana kamar zatayi kuka saboda wannan karan ma a dalilin tane Iman take hawa kamar fulawa Ta ce.” Haba Iman kike hak’uri da Mutune mana! Ki k’yale ta kawai aiko Yanzu jikin ta ya gaya mata keba sobar yinta bace kinji! Bana so kina fad’an nan a kasuwa Wallahi…..
Iman Ta wugawa Sultana Harara Ta juya ta kalli sobar fad’an nata Ta ce.” Ke! Daga rana irin ta yau inna sake ganin ki a wajan mu saina tsone wannan idon naki da kika zubamin su! To Wallahi ahir d’inki nafi karfin ki koda wasa kika kuskura naji labarin kin zauna anan zakiga mai zan miki! Marar kunya gyara a koma makaranta , wannan kan naki ya d’auki Hadisi da K’awa’idi da Alkur’ani, sauran littatafan Addini dan na kula baki da ilimin su……..
Iman Ta kuma cewa kallini da kyau ta juya ta zagata ta tukun taci gaba da cewa. Dan kin ganmu muna talla bashi ke nuni da cewa mu bamu da kamun kai ba, ko bamu da Ilimin Addini kamar ke ba, to wannan kan da kike ganin shi da
bakin nan, Iman Ta nuna kanta da hannu da bakin Ta ce.” Cike yake da Hadisai da Surorin Alkur’ani mai girma dan Uban Babarki ! To ki fice mana anan ko na karya miki hannu. Tana fad’in haka ta nufeta……
Da sauri Sultana Ta janyo ta ta rumgume ta tana fashewa da kuka Ta ce.” Yanzu ke Iman ban isa na fad’a miki magana kiji ba? Nace ki k’yale ta amma kin ki sai masifa kike meye haka?
Hankalin Iman ne ya tashi ganin Sultana na kuka, itama rumgume ta Tayi tana fad’in. Kiyi Hak’uri Sultana! Bazan iya jure naga ana cin miki Mutumci nayi shuru ba , Shikenan ki dena kukan na dena Wallahi bana son ganin kukan ki Y’ar Uwa ta!
Baba Tsoho ne yake Kallon su cike da burgewa Ya ce.” Kai iko sai mai duka wannan shak’uwa taku ko ciki d’aya kuka fito ai sai haka. Da hannu Yayi Sultana alama da suzo, kama hanun Iman Ta yi suka k’araso wajan Baba Tsoho. …..
Kallon su Yayi Ya ce.” Wai to meye ma ya gama ku da Indo ne?
Sultana ce ta soma magana kamar haka:
Baba Indo ce tazo inda muke zaune muna jin wa’azin da Malaman Sunnah sukayi kamayya wanda akayi shi a garin Kaduna, Wani Malami Yace.” Ace kana Musulmi amma baka iya karanta Fatiha a dai-dai ba ai kaci baya, ko kuma kana Musulmi kake tsallake Salla kamar kayi Azuhar bazayi La’asar ba zakayi Isha’i amma baza kayi Salla Asuba ba, ko kuma kake aikata aikin sab’on Allah kana sane amma ka kasa tuba, ko kake aikata zina alhalin kasan haramun ne kuma kaki yin taubatan nasuha, ko kuma son zuciya ya maka yawa, duk masu irin wannan halayen indai basu tuba ba suka cikin masifa da bala’i musamman ma wanda basa Salla ko basa cika Salla, Duk wannan lefukan dana zanau idan ka tuba Allah zai yafe maka amma fa indai Allah kana Musulmi baka Salla to kana cikin tashin hankali saima ka shiga k’abarin ka…
Sai muka kunna d’ayan wa’azin sai Malamin yake magana akan tarbiya kamar haka:
Ya ce.” Indai ka kuskura ka auri Mace marar tarbiya to kana cikin jarabawa, ko ka kake mu’amala da wanda bashi da tarbiya to in baka yi sanadin shiriyar ba to shi zai lalata maka taka tarbiyar, Y’an mata masu zuwa Makaranta, ko masu talla ko masu zuwa aiki office aiki, ku kula da tarbiyar da Iyayen ku suka baku ,kada son kudi ya kaiku ya baro, yanzu Duniya ta lalace Yanzu saita biya Saurayi ya lalata mata rayuwa saboda taki maida hankali tayi karatu sai jarabawa tazo taje Tace” ya mata shi kuma ya nemi saiyayi zina da ita tukun zai mata , ita kuma dake mahaukaciya ce saita yarda, ko Y’an Mata masu talla Mutum zaike miki juye ke kuma kina jin dad’i, idan yaga kina yarda ki zauna kusa dashi zai soma nuna miki kud’i idan ke mai son kud’i ce saiki yarda shi kuma Yayi zina dake ya lalata miki tarbiya, sai kuma daga baya kizo kina cewa sharrin shedan ne, to dan haka kuke rike mutumcin ku , da Mazan da Matan…….
Sultana Ta ce.” Baba wannan shine fa da mika gama ji sai nace , mu dama muna ta kame kanmu Insha Allah baza mu bawa iyayen mu kunya ba, Allah ma ya raba da zuwa d’akin Saurayi ko masu yin juye, shine kafin na k’arasa maganar Indo ta soma cewa.
Ai muna ce mata tana zuwa d’akin Saurayin ta da yake mata juye, nidai bance mata komai ba lokacin Iman tazo kawo maka Abinci ta dawo ne t’a soma zagina tana cewa ai dama da ita muke , shiyasa muka kunna Wa’azin dan muci mata mutumci ne ai , shine fa Iman ranta ya b’aci ganin ban rama ba tana zagina da fad’a min magana, sai ta tashi taci kwalar ta suka kama fad’a wannan shine fa ya had’a su fad’a, kuma da gasken zuwa take d’akin Saurayin ta, sau nawa ana kamasu, Sallar ma bata cikawa , idan munci muje muyi Salla sai tace wai ai ba kab’ari d’aya za’a binne muba, ita in taje Gida da had’a suka sai tayi gobe…..
Baba Tsoho yaja numfashi Ya ce.” Kuyi hak’uri! ku rabu da ita , indai rayuwa ce Duniya zata koya mata Hankali, Yanzu kuje ku tafi Gida tinda kun siyar Abincin……
Iman Ta mike tana sauke ajiyar zuciya akai-akai Tace.” Baba ka fad’a mata karta sake shiga harkar mu nida Y’ar Uwa ta, inba haka ba zan bata mamaki!
Murmishi Baba Tsoho Yayi Ya ce.” Insha Allah zab gargad’e ta kuje Gida sai gobe kuma in muna da rabon ganin ta. To sukace nan suka koma wajan kayansu, t’attrape komai sukayi suka fita a kasuwar zuwa bakin hanyar neman Abun haka.
Suna nan tsaye Abdul Malik yazo ya tsaya Ya ce.” Kuzo n’a kaiku Gida Sultana.
Hararar shi Iman tayi tana cuno baki kama sai wani bud’e kofar hanci take. Dariya Yayi Ya ce.” To duk ni akewa haka My heart ?
Sultana itama murmishi Tayi ganin yadda Iman tayi zatayi magana Iman taja ya ki ta tura ta motar wanda ta tsaida, kallon Direban Tayi Ta ce.” Malam kama muje. To kawai yace” mata yaja suka bar Abdul Malik maki a sake yana mamakin hali irin na Iman, motar ya juya ya bisu a baya ……
Idan kin karanta ki daure kiyi comment sister 🤝🏻
_Taku har kullin Maman Nusaiba ce_