KAINUWA CHAPTER 5

KAINUWA CHAPTER 5

Itama Magajiya a daren ta shirya taje ta samu mai martaba da nata sharad’in, yayi mamaki kwarai dajin wannan zancen, ya kalleta harzaiyi magana sai ya fasa yace ” shikenan ya amince, hakan datai ya nuna masa lalai ba zaman amana take dashi ba haka kuma ta nuna d’ansa ba nata bane.” Magajiya ta juya kai bata ce komai ba dan itakam a yanzu abu d’aya kawai ta sani wato ta tabbatar ta d’aura d’anta a mulki ba komai ba. Haka mai martaba ya rubuta mata a takarda ya kalleta cikin takaici sannan yace “na dauka na sanar dake d’ana yana da lalura?”+ Bata amsa mai ba ta dai amshi takardar hannunsa sannan tai murmushi tace ” ba wai rashin yarda ne ko rashin san d’anka bane yasani yin haka sai dai nayi haka ne saboda kauda matsala dazata iya afkuwa nan gaba, me zai faru idan nan gaba ka tara ‘ya’ya anzo ana takara da kishi akan mulki? Amma kaga in har mun riga mun tsaida babban d’a a matsayin magajinka banaji wata babbar matsala zata faru.” Kallan yai cikin mamaki duk da dai maganarta ba karya bane sai dai yana ganin sankai da san mulkinta ne yasata yin haka, yafi kowa saninta ya san abinda take tunani, tana tsoro kar nan gaba yaron ya warke in fara tunanin sashi a mulki. Sallama tamai ta fita. ************ Washegari wajen sha biyun rana aka turo da mota dazata daukesu. Kofar gidan sarauta aka bud’e, Abu Turab ya kurama kofar ido yana kallo, gannin tsari da girman gidan yasa ya shiga kalle kalle, mamaki yakeyi duk wannan katan gidan na mahaifinsa ne? Basira ce ta tabashi, ya juyo ya kalleta hararar sa tai sannan ta nuna mai sandarsa, da sauri yai kasa da kansa sannan ya d’auki sandar. Sun sauka Lantana ta kama hannunsa suka nufi b’angaren da wata baiwa tazo dan nuna musu. Ba b’angaren ta na da bane wannan yafi girma saboda an warema Abu Turab nasa bangaren. Haka akai ta zuwa ana gaidasu wasu gaisuwa sukazo, wasu kuwa gulma sukazo, wasu kuwa so suke suga lalurar da yaron ke dashi. Kafin kace me? Zance ya baza gidan akan Abu Turab makaho ne. Abdulmajid kam yana gun Magajiya tana kara huremai kunne akan karya kuskura ya bari yaron nan ya rainashi, dan nan gaba baisan mai zai zamar masa ba. Sun dade a d’akin kafin tace ya tashi ya koma bangarensa. Abdulmajid nada tsananin kishi, jin akwai wani d’a bayanshi a gun Mai Martaba yasa ransa ya bace, kallan masu kula dashi yai yace ” muje in ga kanin nawa.” Haka ya taho dan ya matso yaga kanin nasa da sam baya farin cikin kasancewarsa, sannan yanasan yagani in da gaske baya ganin. ******* Abu Turab na xaune aka dinga shigowa da kaya, sai dai ba dama ya nuna yana gani, kansa ya kawar gefe yana wasa da hannunsa, sun ajiye kaya dayawa daga na sawa, takalma da sauransu, sannan suka gaidashi. Juyowa yai inda suke ya amsa tare da cewa “su waye?” “Mai Martaba ne ya aikomu mukawoma kayan sawa, sannan ga abinci kala kala ya sa a girkama, yace a sanar dakai xai turo anjima a kaika gunsa.” STORY CONTINUES BELOW  Abdulmajid wanda ke tsaye dan ya shigo kenan yaga ana shiga da kaya yasa ya bisu, wani mugun kishi da tsanar yaron ne ya turnukeshi. Abi Turab ya saki fuska yace ” nagode kwarai.” Wasu kaya aka ajiye a kusa dashi, sannan wanda ya ajiye yace “wannan zaka sa in zakaje gunsa dan a fada yakesan nunaka.” Kai ya daga alamar to, sannan suka juya suka fita. Abdulmajid ya juya ya juya ya kalli bawansa yace ” akwai almakashi?” Mamaki ya kamashi sai dai batare da ya tambaya ba yace “akwai amma sai gun soro.” Yace ” yi gudu maza ka amson.” Nan ya fita da gudu. Shiga ciki yai ya tsaya a gaban Abu Turab, Lantana ta gaisheshi. Kallanta yai sannan yace ” bamu guri.” Hanyar waje ta nufa gabanta na faduwa, shi kuma Abu Turab ya mike ya mika mai hannu dan su gaisa duk da ba saitinshi ya mika ba, sannan yace ” sunana Abu Turab.” Dariya Abdulmajid yai yace ” ta ina zamu gaisa bayan ba gani kake ba? Sannan ni yayanka ne baka gani rusunawa ya kamata kayi?” Abu Turab ya dan kalleshi kad’an sannan ya juya kai baice komai ba. Shigowar bawansa ne yasa ya juyo ya mikamai hannu yasamai almakashin, rigar da aka kawo dan ya saka ya dago ya sa almakashin ya yanka bayanta takai har wajen wuya sannan ya ajiye ya kalli Abu Turab yace ” ungo kayanka saka ni ne wanda zan rakaka gun Mai martaba.” Abu Turab yana kalan mai yai sai dai ba yanda zaiyi, ya kalli Abdulmajid yace “amma karar me naji?” Kallansa yai a wulakance yace “abu na cire a rigata.” Abu Turab ya runtse ido, yana tunanin yanda zaiyi, in ya nuna ya sani alama ce ta yana gani kenan. Haka ya amshi kayan ya kankama a jikinsa bayan yasan duk bayansa a waje yake. Abu Turab ya kalleshi yace ” Amma ance turowa za’ai inje ai.” Abdulmajid ya kalli Bawansa yace “ga wanda aka aiko nan, sannan cewa akai in kaika.” Fitowa yai rike da sandarsa, Abdulmajid na gaba shikuma yana baya, masu kula da Abdulmajid na bayansu. Tunda suka fito ake kallansa ana dariya, lalai wannan ba makanta bane kadai a kansa akwai alama ta hauka. Shikanshi Abdulmajid sai dariya yakeyi sam baisan abin zai kayatar dashi haka ba, shidai kawai yayi ne saboda yasa amai dariya a fada bai dauka tun a hanua za’a fara ba. Sai da sukaje kofar shiga fadar, ya kalleshi yace “shiga.” Abu Turab idanunsa suka kada sukai jaa, jiyake kamar ya sa ihu, mahaifiyarsa ya tuno da kuma kashaidinta akan idanunsa. Haryaje shiga ya tsaya Shi mamakinsa mai ya mai? Daga zuwansa ko awa biyu cikakke baiyiba ace harzai mai haka? To shi mai yayi? Daga bakin kofa akace ” Bawan Allah ya akai?” Abu Turab ya juya zai bargun da gudu, nan fa akaga bayansa. Barde cikin mamaki dan dashi akaje daukosu yasan yaran ya kalleshi yace “Ba…….” Shiru yai ganin yanda rigarsa ta baya take. Dariya aka shiga guntsewa ganin kayansa kowa ya tabbatar d’an sarki ne. Abu Turab duk ya rikice garin gudu ya fadi a kasa, hannayensa ne suka kurje, jiyai idanunsa sun ciciko, fadan mahaifiyarsa na ragonta ya tuna hakan yasa ya hadiye kukan ya mike jiki a sanyaye ya daina gudu, sandarsa ya rike kam yana tafe. Yana fitowa daga fadar, Lantana ta taho da gudu dan labari ya kaimusu ga Abdulmajid can da Abu Turab suna tafe zuwa fada amma shi Abu Turab rigarsa ta baya a yage take sosai. Lantana tunda ta ganshi hawaye yake zubo mata, yaron daya taso a kauyen kayau hankalinsa a kwance yau gashi daga dawowarsa gidan mahaifinsa an maidashi shashasha. Hannunsa ta kama ta rufa mata babban kyallen data d’auko tana hawaye. Kallanta yai sai dai jiyake kamar taimaka mai tai wajen yin kukan dashi yakesan yi. Basira kam tun da aka fada mata take zaune ko motsi ta kasa yi, hannayenta kawai ta matse kam. Abu Turab na shigowa ta shige d’aki da sauri, bayan ta ya kalla ya bita da gudu. Yana kokarin shiga yaga ta rufo kofa. Zama yai a bakin kofar. Hakoransa ne suka shiga kadawa, sanyi ya fara kamashi. Yana nan a zaune bacci ya daukeshi, wani zazzafan zazzabi ne ya kamashi. ******* Magajiya kam jin abinda ya faru yasa ta cikin wani farinciki ba shakka lalai d’a dole ya gaji ubansa, bayan Hisham ga ta ai dolene Abdulmajid yai gadon makirci Da kissa. Dadi ne ya kamata sai murmushi take. Jin wannan labari yasa Hisham cikin farin ciki, shida Magajiya sunyi dariya sosai sun kuma yaba kwazon d’an nasu da alama in ya girma abinda zaiyi ba wanda zai iya tunani. Hisham sai kara wasa Magajiya yake yanacewa “ai kwakwalwa da kwazonta ne ya gado yo dama kaza bazatai gudu d’anta yai rarrafe ba….” Dadi sai kara kamata yake. Da alama basai ta taimaki d’an nata ba, komawa zatai ta zauna ta dinga ganin yanda Abu Turab zai kasance gun Abdulmajid…….. nαcє hmmmmmmmm…. Lantana ce ta zo ta daukeshi tai b’angarenshi dashi, akan gado ta kwantar dashi har lokacin bata daina zubar da hawaye ba, bargo yaja ya luluba ita kuma ta mike ta fito.+ A tsaye ta taradda Basira, kusa da ita taje ta tsaya ba tare da tace komai ba. Basira ta juyo tace ” yana ina?” “nakaishi d’aki.” ta fad’a tare da kara share kwalla, Basira ta had’iyi wani yawo na takaici sannan tace ” ki amso mai magani yasha.” Tace to, sannan ta juya ta fita. ********* Mai Martaba kam ana la’asar ya kalli Barde yace ” a aika a kira Abu Turab.” Barde ya kalleshi jiki a sanyaye yace ” Takawa kayi min afuwa amma ina ganin ka bari sai zuwa wata rana sannan a nunashi a fada.” a hankali yai maganar. Mai Martaba yasan halin Barde tunda ya fadi haka da alama akwai wani kwakwaran dalili, hakan yasa bai sake magana ba. Ana tashi daga fada ya tambayi Barde abinda ke faruwa. Barde ya nisa yace ” bansan nikaina takamaimai menene ba sai dai naganshi ya taho gunka sai kuma ya juya.” Cikin mamaki Mai Martaba yace ” ban gane ba?” Nan Barde ya sanar dashi abinda ya gani. Hankalin Mai Martaba ne ya tashi sosai nan ya juya afusace yai bangaren d’an nasa. Bai jira Zagi ya isar da zuwansa ba ya fada ciki da sauri. D’akinsa ya nufa ya bud’e, a dukunkune ya ganshi cikin bargo, da sauri ya karasa gunsa ya d’agoshi. Jikinsa zafi rau wanda hakan ya kara tadamai hankali, ya kalli Abu Turab wanda idanunsa sai lumshewa suke, yace ” Menene? Waye ya tabaminkai? Har yajama zazzabi?” Kai Abu turab ya girgiza alamar bakowa. Fuskarsa yace ” bayin dana aiko da kayanka sune suka baka yagagge ko akwai wani abun?” Abu Turab jiyai wani kuka yazo mai, baisan sanda yasa kuka ba, kuka ya shigayi sosai. Mai Martaba ya rungumeshi tsam a jikinsa hankalinsa a tashe. Abu Turab ya dade yana kukan sannan ya share hawayensa cikin murya mai raunin gaske yace ” kayi hakuri na tadama hankali daga zuwana.” D’ago dashi yai ya kalleshi yace ” ni zan baka hakuri na rashin kula da abinda ke faruwa dakai.” Abu Turab ya share kwalla baice komai ba. Yana zaune kusa dashi har bacci ya dauke d’an nasa sannan ya mike ya fito. Bangaren Basira ya shiga, zaune ya ganta tana cin abinci. Sai daya zauna sannan ya kalleta yace ” Abu Turab yaci abinci ne?” Murmushi tai tace “in bashida lafiya bayacin abinci dan ko yaci zai dawo dashi.” Ya kalleta ya kalli yanda takecin abinci yace ” Basira mai ya sameshi? Ance ya sa kaya bayan rigar a yage.” Abincin hannunta ta ajiye dan dama ci kawai takeyi, ta kalleshi tace ” bansan me ya faru ba nima na dai san bashida lafiya.” Ido ya kura mata, tai saurin kauda kanta gefe, yace ” wanene yamai haka? Na tabbata kinsani.” STORY CONTINUES BELOW  Ta dan kalleshi kadan tace ” shi bai fadama ba?” Yace “yace bakowa.” Murmushi tai najin dadin yanda dan nata yace bakowa, tace ” tunda yacema bakowa hakan ne, koma ba hakan bane alama ce ta bayasan kasani.” Shiru yai, sannan ya kalleta yace ” komai yayi daidai? Na gida nake nufi.” Kai ta d’aga tace ” komai yayi daidai sai dai inaso ka bani dama na wani abu.” . Ya kalleta bai ce komai ba. Tacigaba da cewa ” so nake Lantana ta koma gun Abu Turab sannan inaso ka taimaken akan barinta ita kadai ta kula dashi banasan abashi bayi dayawa.” Mamaki ya kamashi yace ” me kike fada haka! D’an nawa da bashida lafiya kikeso invar lantana kadai ta kula dashi?” Tace” rokon ka nake akan hakan inya tasa lokacin sai ta dawo nan, ya saba da ita da ita kadai yakejin dadin zama.” Shiru yai baice komai ba, ita kuwa tana tsoron kar a turamai mutane ya zama harda mutanen Magajiya kada kuma tsautsayi yasa ya nuna yana gani tunda dai yaro ne. Ta kalleshi tace ” sannan yana san karatun boko.” Mai Martaba yai murmushi yace ” akwai mai koyama Abdulmajid da ‘ya’yan kanina da na galadima karatu a cikin gida, inyaso sai ya dinga zuwa.” Tai murmushi tace ” nagode Takawa.” Kallanta ya sakeyi yace “amma kina ganin zai iya karatu cikin yara masu gani shida yake makaho?” Tace ” zai iya, kuma hakan zaisa su fuskanci juna da ‘yan uwansa.” Kai ya jinjina alamar gamsuwa. ******** Washegari. Da gudu ta shigo bangaren Magajiya, tana zuwa cikin zumudi tace ” Umma ina kanin Ya Abdulmajid d’in?” Abdulmajid ya maka mata harara yace ” khadija me yasa bakida hankali ne? Ba na hanaki yima mutane gudu ba? Kina mace?” Baki ta murguda kadan sannan ta kalli Magajiya ta shagwabe fuska tana neman yin kuka. Tace “Umma kinga Ya Abdulmajid ko?” Abdulmajid haushi ya kara kamashi, yace “banace karki kara cemin Ya Abdulmajid ba?” Kuka ta saka sosai, Magajiya ta janyota jikinta tana lalashi. Abdulmajid ya kalli Magajiya yace “Umma duk ke kika b’ata yarinyarnan.” Khadija ta d’ago daga jikin magajiya tace “Umma ina kanin ya…..” Sai kuma tai shiru. Magajiya tai dariya yace “Abdulmajid kadaina zafafa mata.” Itakam ganin anki fada mata yasa tai waje da sauri. Baiwar bangaren Magajiya ta samu tace “kaini gun yaron dayazo jiya.” Nan ta dauketa tai bangaren Basira da ita. Ta nuna mata bangaren yaron. Da sauri tai ciki, Lantana ta gani a zaune tana ninke kaya, cikin zumudi tace ” sannu, ina yayan da aka kawo jiya?” Lantana ta mata kallan mamaki ganin bata santa ba. Abu Turab ne ya fito daga d’aki bai kula da wani a gun ba yace ” Lantana dan bani ruwa.” Jiyai anzo an rungumeshi kam. A tsorace ya kalli kasansa. Yarinya ce karama ya gani, cikin mamaki ya tureta yace ” waye hakan?” ya fada kamar bai ganta ba. Khadija tai dariya tace ” nice nan ‘yar gidan waziri, kaine yayan dayazo jiya ko?” Kallanta yai kadan ya kauda kai yace ” ni bansanki ba.” Dariya tai batace komai ba, itakam tun jiya ta matso ta ganshi. Hannunsa ta kama tace “ai kai zaka dinga wasa dani ko? Bakaman ya Abdulmajid ba ko?” Shiru yai baice mata komai ba, ta kara rike hannunsa tace ” sunan ka Ya Turab ko?” A hankali yace eh. Dadi ya kamata tace ” zanje gun karatu sai nazo gobe. Nan tai waje da sauri. Baisan sanda yadanyi murmushi ba. Lantana ta kalleshi tana dariya tace ” tunda kazo gidan nan sai yanzu naga fara’arka.” Ya kalleta yace ” bani ruwa kishi nakeji.” Tai dariya ta mike, jikinsa ba karfi hakan yasa ya zauna. ********** Jin labarin fara karatunsa agun Mai Martaba yasa Barde shima ya gurfana gaban Mai Martaba yace ” Takawa nima inasan abani izini in dawo da yarinyata cikin gida dan daukar darasi.” Mai Martaba yace “ba da kace tanayi a waje ba?” Barde yace ” wlh Takawa yarinyar tawa ce kasan na fadama bataji sam, kullum ta fita makaranta sai an kawo kararta, ina ganin in anan take zatafi samun nutsuwa tunda ba wanda ta isa tsokana ganin darajar mutanen da zatai karatun dasu.” Mai Martaba yadan murmusa yace ” shikenan ka kawota, Mairo sunanta ko?”1 Barde yace “eh Takawa, ina godiya Allah yaja kwana.” ********* Da yamma suka shirya ita da d’anta dan zuwa gaida Magajiya. Duk inda sukai kallansu ake ana ‘yan gulmace gulmace har suka isa b’angaren Magajiya. Tana kilisarta itada d’anta, bayan an neman musu izini nan suka shiga,ta kama hannun Abu Turab sakamakon sakeshi da Lantana tai da zasi shiga. Abu Turab ya sauke idansa akan hamshakiyar matar dake zaune ta kafe kofar da sazu shigo da ido. Kallanta yai sannan ya kalli d’an nata dake gefe sai kuma yai kasa dakai. Magajiya kam ta kafeshi da ido tunda suka shigo har suka isa suka zauna. Ta rasa me yasa tana ganinshi taji gabanta yayi wani wawan fad’uwa, Basira ta kalla sai dai yanzu taga alamar ba tsoro da gidadanci a idanunta kamar waccan zuwan nata na da. Zama sukai,Magajiya ta kara kallan yaron a ranta tace ” sak Mai Martaba lalai naji dadi da Yakumbo ta taimaka wajen nakasa idan nan.” Gaisheta Basira tai, i Bata amsa ba ta maida idanta gun yaron, ya d’ago suka hada ido da sauri ya kalli gefe yace “Barka da Yamma.” Tabbas tasan sun hada ido sai dai dayake zuciyarta na farin ciki da kasancewarsa makaho yasa ta kasa dogon nazari akan haka. Abdulmajid kam ya had’e rai da alama bashida niyyar gaida Basira. Sai da Magajiya tace “Yarima baka gansu bane?” “Barka.” Abinda ya fada ma Basira kenan. Murmushi tai ta kalli Abu Turab tace ” Yarima bakaga yayanka bane?” Wannan kalma ta ba Magajiya da Abdulmajid mamaki, yarima? Haryaushe yazo?kuma ma a gabansu?” Abi Turab bai kalleshi ba yace “Barkanka dai Yarima.” Magajiya zatai magana, Basira tai saurin cewa ” haba Abu Turab sai kace ba yayanka ba? Ai kai basai ka kirashi Yarima ba ko Magajiya?” Ta karasa maganar tana kallan Magajiya. Magajiya ta juya ido a ranta tace ” lalai wai so kike ki nunamin kin kile ko me?” Murmushi ta saki sannan tace ” hakane abinda kika fada sai dai kinsan tsintaciyar mage bata mage.” Basira cikin mamaki tace “bangane ba?” Magajiya tai wani nishi na kasaita tace ” Dafatan muhallinku an sa komai da komai? Dan ina nan ina fama da al’amuran cikin gida ban samu naje ba.” Basira ta daure tace ” komai yayi.” Shiru suka d’anyi Magajiya na kallan yaran, can tace ” naji ance ka fita riga a yage jiya? Meke faruwa? Ko dayake laifinki ne kinsan yaran makaho ne bai kamata ki barshi shi kadai ba.” Basira ta kalleta kadan batai magana ba,BU turab yai saurin cewa ” Laifinane dan batasan ma nafita ba.” Magajiya a hasale tace ” kada ka kuskura in inamagana da mahaifiyarka kasamin baki, ko kaga Abdulmajid na haka? Wannan alama kake nunawa na kataso a wani gun daba Gidan sarauta ba.” Basira ta kalleshi tace ” kada ka sake, sannan yi maza ka bata hakuri.” Shiru Abu Turab yai wanda hakan yasa Basira tai dana sanin cewa ya bada hakuri, tasan halin d’anta sarai inhar tace yai abu ya tsuke baki to fa lalai bazaiyi ba. STORY CONTINUES BELOW  Magajiya ta kalleshi tana jiran ya bata hakuri sai dai jitai yayi gum. Abdulmajid ya kalleshi yace “bakaji me aka ceba?cewa akai ka bada hakuri.” Abu Turab aya dan juyar dakai saitin Abdulmajid yace ” bansan laifin me nai ba.” Wannan kalma tasa ta basu mamaki sosai, a zuciye Abdulmajid yace “bakasan me kai ba? To me ya damemu? Kayi laifi dan haka bada hakuri ya zama dole.” Kasa ya maida kansa yai shiru, Basira tadan tabo hannunshi nan ma shiru, Magajiya tai wata dariya kadan ta takaici tace ” kai? Nice magajiya gimbiyar sarki, sannan nice a matsayin mahaifiyarka babba dole ne kabi abinda nakeso ka kuma guji abinda banaso.” Abu Turab baiyi magana ba, Basira ta kwallama lantana kira tace ” Lantana samo bulala.” Lantana ta kalli Uban gidan nata cikin tausayawa sai dai ya zatayi? Haka ta fita ta samu bulala na bishiyar maina. Basira ta kalleshi yace mike, Abu Turab ba musu ya mike, ya d’aga kasan wandonsa dan yasa nan zata daka, zata fara dukansa Magajiya tace ” Basira meye hakan? Dan d’ana yamin laifi ai hakkinane in hukuntashi bake ba.” Basira ta tsaya sai dai a ranta tana addu’a Allah yasa kar tace ita zata hukuntashi. Magajiya ta kalli Abu Turab tace “yi zamanka kaji d’ana.” tai maganar fuskarta a sake. Gani tai Abu Turab yaki komawa ya zauna, kallan mamaki tamai gani tai kansa na kasa kusa da mahaifiyarsa. Ya saba da hakan inyai laifi sai tace dakanta ya zauna. Basira ta kalleshi tace ” zauna mana.” nan ya koma ya zauna, ba shakka wannan abun ya kuna ran Magajiya ya kuma kona ran d’anta, sai dai bata nuna ba har suka tafi, tana tunanin lalai dole ta saita d’an nan. ********** Yau satinsu biyu a gidan, sam Abu Turab baya fita saboda gudun kar wani abu ya faru a gane idansa na gani, sam bayasan gidan, sai dai jefi jefi Khadija na zuwa gunsa tai tamai zuba, shi mamakinsa ma ko mahaifinsa baya gani dan tun daga wannan ranar bai sake sashi a ido ba. Yau ce ranar dazai fara zuwa makaranta da safe yai wanka yasa kaya, Lantana ta kawomai abinci yaci sannan suka fita, Basira ta mai fada sosai kafin su wuce makarantar. Sun kusa isa makarantar sukaji ance Lantana, nan ta juya jin muryar kawarta. Kallan Abu Turab tai tace ” dan Allah bari in mata magana.” Murmushi yai yace ” jeki, ba can bane?” Tace nan ne. Sandarsa yasa a gaba ya fara tafiya yana d’an kale kale kadan kadan. Yaje zai shiga yaji an bangajeshi dakarfi wanda sai daya sashi ya fad’i. Hannunsa ya kalla yaga ya kurje, ya d’ago dan ganin waye, sai dai ga mamakinsa gani yai ta mike tana neman kara mai. Hannu yasa da karfi ya fizgota. Mairo ta juyo suka had’a ido, da sauri ya kauda kansa wato yarinyar nan ce ta rannan? Itama ido ta kuramai tace “la kaine makahon nan ko?” Abu Turab yace ” meyasa bakida hankali? Bakiga bigeni kikai ba? Kike neman gudu baki ban hakuri ba?” Dariya tazo mata ta toshe baki, jakar buhun dake hannunta wanda ya rike gam ta zare ta rike da hannunta, yana kallanta a ransa yace ” wannan ba karamar fitinaniya bace.” Waige waige ta shiga yi nan taga khadija ta nufosu. Alama ta mata da hannu akan tayi sauri, itakam ganin yayanta ne agun yasa takara sa sauri, tana zuwa kusa dagun zatai magana Mairo ta mata alama datai shiru. Mamaki ya kamata ta karaso, alama ta mata da hannu akan ta rike mata jakarta, nan khadija ta rike tana san ganin me zatai. Duk wannan abun da suke Abu Turab na kallansu shi dariya ma abin yake bashi lalai yarinta da ciwo, inba haka ba ko baya gani tana san tacemai bazai fahimci me takeyi ba? Khadija na amsa ta shige ciki da gudu. Da kallo ta bita, can tace ” Ya Turab haka zamuyi ta zama anan?” Murmushi yama Khadija yace “cilar da jakar ki shiga muje.” Nan ta yarda jakar sukai ciki. Suna shiga suka zauna gu d’aya dayake lokacin da ne, akan tabirma suka zauna, can gefe kuma Abdulmajid ne zaune akan wata daduma mai kyau ya hard’e kafafu. Khadija na zaune kusa da Abu Turab. Mairo tazo ta baya ta tab’ata tace ” jakata fa?” Tace tana waje. Waje kuma?yarmin kikai? Khadija tace eh yayane yace in yar. Baki ta murgud’ama Abu Turab tace “yayan naki da ba gani yake ba?” Abu Turab ya kalli inda Khadija take, Mairo ta kalleshi tace ” ni anya baka gani kuwa?” Abu Turab ya juya kansa bai tanka ta ba, ta harareshi tare da murgud’a baki ta mike tai waje. ********* Sosai yaji dadin yanda yake fahimtar karatun, dan daga anyi tambaya sai yaga yasan amsar, sai dai ba damar ya fada indai ba tambayarsa akai ba, saboda umarnine na mahaifiyarsa. Abdulmajid in yaji ya bada amsa daidai sai yai dariya a ransa yace duk kokarinka dai baka isa yin rubutu ba saboda rashin ido, yana tsananin jin haushi yanda Khadija ke zama inda yake, sam ma tadaina kulashi iyakacinta dashi gaisuwa. Wata shakuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Khadija da Abu Turab ko makaranta zata ita take zuwa ta rike hannunsa su tafi, in an tashi kuma sai ta rakashi sannan take tafiya. Mairo kuwa da Abu Turab banda fada ba abinda ke had’asu, rigimarta tayi yawa da sam ko kusa dashi bayasan tazo, haka kawai indai taganshi azaune sai ta tsokaneshi. Abdulmajid kam na tsananin kishin Abu Turab ganin yanda ko Mahaifinsu ke nuna mai kulawa da kuma yanda mutane ke sanshi, yasa san ya tsaneshi farincikinsa yaga yamai sharri, sai dai duk sharrin da yakemai cikin ikon Allah sai komai ya warware. _Wannan kenan_ Haka rayuwa ta kasance musu sosai Abu Turab ke kokarin ganin ba wanda yasan yana gani, sannan baya shiga gun mutane saboda tsaro, Mahaifiyarsa tana kara tarbiyantar dashi da nunamai abinda ya dace da wanda bai dace ba. Baya zuwa gun Magajiya akai akai, sannan in yaje gaisheta ma yana zuwa yake cewa zai tafi in kuwa ta hanashi tahowa haka zai zauna gum, sosai ya fahimci matar fuska biyu gareta. Haka ya taso cikin tarbiyya mai tsauri, haka ya taso cikin sanin halayen mutanen gidan, ya kuma fahimci lalai mahaifiyarsa gata tamai, ko daga yanda mutane suke mai kallan tsana sun dauka baya gani, sharrin da ake mai da kuma nuna halin ko in kula akansa. Mutum d’ayace yake zama da ita yaji dadi, daga mahaifiyarsa da Lantana sai kuwa Khadija. Ganin irin tsananin shakuwar da ta shiga tsakanin Turab da Khadija yasa hankalin Magajiya ya fara tashi, ga yanda take tsananin san yarinyar, Hisham tasa aka kira ta umarceshi akan ya maida Khadija kano gun ‘yan uwan mahaifiyarta, a lokacin Khadija nada shekara 10, sai tazo gidan sau nawa amma ko b’angaren Magajiya wani sa’in harta fita bazata ba, Hisham ma ya aminta da hakan dan kuwa shikansa abin ya fara damunsa jin komai a gida zancenta kenan Ya Turab. + A ranar da za’a tafi da ita ma tazo gun yayan nata tana ta sashi magana, dan dama kaf gidan ita kadai ce mai sashi yai ta magana, suna cikin hirarsu aka turo tazo Mamanta na nemanta, mikewa tai cikin sauri dan ko d’ankwalinta bata d’aura ba kawai ta sa hijab dinta ta fita, hartaje kofa Turab yace ” Khadija.” Juyowa tai cikin fara’a, murmushi ya mata ya kalleta yace ” karfa kiyi gudu ki tafi a hankali kije ki dawo.” Itama murmushi tamai tace ” yanzu zan dawo Yaya, in na dawo zan cigaba da baka labarin.” Kai ya d’aga mata alamar to, kusa da shi ta dawo da sauri ta kura mai ido, kallanta yai tare da saurin d’auke ido, tace “wani sa’in sai inga kamar kana gani.” Fuska ya d’an hade yace ” zaki fara ko?” Dariya tai tace “karka damu yaya a kullum in nai sallah addu’ar da nakeyi kad’ai kenan ‘Allah ya baka lafiya ka dinga gani.’ Fuska ya saki yace “dafatan ba ita kadai kikeyi ba? Addu’ar nake nufi.” Mikewa tai da sauri ta fara tafiya, hannu yasa ya riko hijab dinta ta fizge da karfi sai dataje kofa tace ” ita kadai nakeyi.” Tai saurin tai waje. Dariya yad’anyi tare da girgiza kai, ba shakka Khadija itace take d’ebe mai kewan zaman kad’aici, dan ko sharri akamai ko aka b’atamai rai inyazo ya zauna a d’aki shiru ita ce ke zuwa gunsa, bazatace komai ba sai dai zata zauna kusa dashi harsai taji ya fara mata magana, ya rasa menene dalilin dayasa mahaifiyarsa ma zancenta kenan akan ya rage kula Khadija, ko Lantana ma wani sa’in sai yaji tace ” Uban gidana ka rage sa Khadija a ranka.” Bai tab’a tambayar dalili ba dan kuwa yasan ba mai fadamai, kuma yana tunanin dan tana ‘yar yayan Magajiya ne yasa ake fadamai haka. A can kuwa Khadija na zuwa aka sa ta amota, mamaki ya kamata ta kalli Mamanta tace ” ima zamu?” Rufo kofar motar Hisham yai sannan ya kalleta ta yace ” ki koma kano gun kanwar Mamanki ki zauna acan, kiyi karatu, inkinyi hankali nida kaina zanzo d’aukanki.” Ihu ta saka tace “itakam bataso abarta anan, gub Ya Turab.” Tana ihu tana kuka aka ja mota akai gaba, kuka take sosai harda shesheka, sai dai Mahaifiyarta kawai ta jawota jikinta ta kwantar. Tana kuka har bacci ya d’auketa, bata farka ba sai da akai parking a kofar gidan. Da kuka ta shiga gidan. ******* Haka rayuwa ta kasance tun Turab na jiran Khadija kwana d’aya, biyu ba labari, nan ya fara tunanin ko batada lafiya ne. Satar jiki yai ranar datai kwana hud’u ya fito, tunani ya fara ta inane ma inda zaije shidai ba yawo yake ba, ga gidan katon gaske, yana tsaye yana tunani yaji anzo tabayansa ance woo da karfi akai wanda sai daya d’an tsoratashi ya juyo da sauri ganin Mairo ce ya had’e rai tare da dauke ido daga kanta, hannu takai kamar zata dakeshi ta makamai harara tace a hankali ” nima ba farincikin ganinka nake ba.” Fuskarsa a had’e yace ” kinga Khadija?” STORY CONTINUES BELOW  Bakibta tab’e tace ” khadija?” Sai kuma tasamai dariya tace ” niban ganta ba.” Kallanta yad’anyi kamar ya tambayeta inda zaije yaganta sai kuma ya fasa, Mairo tace “la ga Yayanta nan zuwa ka tambayeshi.” Juyawa yai da sandarsa zai koma, jiyai Abdulmajid yace ” Abu Turab.” Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, Abdulmajid ya karaso inda yake, ya mai wani kallo na sama da kasa yace ” kana d’an sarki menene dalilin fitowarka kai kadai?” Abu Turab ya kalli gefensa baice komai ba, Abdulmajid yacigaba” in har kanada ido ma ba wani abin amma kana makaho ka dinga yawo kai kadai?” Ba kalmar daya tsana irin a dinga cemai makahon nan, Mairo dake tsaye ta kalli Abdulmajid dan dama ba kunya gareta ba tace ” yau naga ikon Allah, wani inyaji kana fadar haka daukama zaiyi ka damu dashi.” Abdulmajid ya maka mata wani mugun kallo yace ” ke kuma uban waye ya sa bakinki?” Tab’e baki tai tace ” wai da….” A hankali tai maganar, sai dai yajita, juyowa yai ya kalleta yace ” wlh kika batamin rai bakeba har ubanki sai na sa an hukunta.” Baki ta murguda kadan tace “badai nawa uba….” Abu Turab yai saurin daka mata tsawa yace “ke Mairo!” Idanu ta zaro dan sosau ta tsorata, yace wuce ki tafi gida. Kallansa tai batace komai ba tai gaba, yauce rana ta farko da taji bazata iya maida murtani ba akan fadan da aka mata. Tana tafiya Abu Turab ya juya zai tafi, kafa Abdulmajid yasa mai ya kifa kuwa tim. Kasa duk ta shiga bakinsa, Abdulmajid ya matso da sauri ya kama hannunsa yace ” tashi sannu, kaga irinta ko? Yanzu dan Allah yasa ina nan ne da bamai d’agaka.” Mamaki ya kama Abu Turab, sai dai ya daure ya mike ya kade jikinsa baice komai ba ya juya zai tafi. Abdulmajid yace ” Khadija fa? Badai cemin zakai ita ka fito nema ba.” Abu Turab baice komai ba. Abdulmajid yasa dariya ya dawo gabansa yace ” duk amintar ku bata fadama zatai tafiya ba?” Abu Turab yad’an juyo inda yake, Abdulmajid ya dan dafashi yace “yaro man kaza.” Baijira mai zaice ba ya juya ya tafi. Jikin Turab ne yai wani mugun sanyi a hankali ya dinga tafiya har ya isa b’angarensa dan yanzu an fitomai da kofa daga b’angaren Basira. Yana shiga yaga Mahaifiyarsa a tsaye a tsakar gida, ga bayinta da nashi duk a tsatsaye. Da alama fada take musu, jin bude kofa da shigowarsa yasa duk suka kuramai ido. Wani mugun kallo tamai ta kallesu tace ” ku bamu gu.” Nan kowa ya juya ya fita, Lantana kam jiki a sanyaye ta fita dan tasan Ubangidanta yayi laifi. Basira tana matsowa ta wanka mai mari. Hannu yasa a gun bai d’agoba kansa na kasa, cikin kuluwa tace ” gidan ubanwa kaje? Sau nawa ina cema karka fita kai kadai?” Kansa na kasa yai gum da baki. Ta kalleshi dan tasan bazai magana ba, ita kanta tayi dana sanin marin nasa sai dai itakam tana tsoron abinda za’amai in aka ganshi shi kadai, balle yanzu dataga gefen kuncinsa kasa ta tabbata wani abun ne ya faru. Juyawa tai a harzuke tai waje. Abu Turab ya tsugunna a gun idanunsa suka ciciko, ga jin khadija tayi tafiya, ga bakincikin Abdulmajid, gashi ya b’atawa mahaifiyarsa rai. Lantana ce ta dawo ta d’agashi ta shiga dashi ciki, a wannan ranar kam Abu Turab sai daya zubda hawaye. *********** Tundaga wannan rana komai na rayuwarsa ya canza, magana wannan sai ya zamarmai dole yake yi, kullum yana b’angarensa, rayuwarsa ta koma ta da, sai dai ko makarantarsu ko kuwa inya fita gaida Mai Martaba ko Magajiya. A makaranta ne dai Mairo take dan mai magana bayan ita kuwa kaf ajin daga gaisuwa ba abinda ke hadasu da kowa. Tun randa ya ma Mairo tsawa kuwa ta rage rainashi, sai tausayinsa ma data darayi, gashi yanzu ya canza kullum fuskarnan tasa ba fara’a. A kwana a tashi ba yuwa yau gashi Abu Turab ya cika shekara 22. Yau an tashi a gidan Sarki anata shirye shirye sakamakon hawan Sallah na karama da za’ai. Zaune yake a d’aki ya saka kayan da aka aikomai inji Magajiya wai ya saka, tunda ake hawan sallah Abdulmajid ne kadai yakeyi, amma wannan sallar wai ta aikomai da kaya akan shima zaije hawa. Murmushi ya saki sannan ya d’aga kayan sama ya tabbata akwai wani makirci da aka shirya mai. Yana nan azaune yaji ana kwankwasa mai kofa. Mikewa yai ya tako yazo ya bud’e. Mahaifiyarsa ce hakan yasa ya matsa mata ta shiga ciki. Zama tai a bakin gado sannan tace ” akacemin an aikoma da kayan hawa?” Kai ya d’an jinjina yace ” gasu can.” Kallan kayan tai sannan tace ” Turab amma dai…..” Murmushi ya mata yace ” zanje.” Kallan mamaki tamai tace ” baka tunanin so take a mutanen gari su fahimcu baka gani? Ko kuma wani abun sukama dokin kaje ya yarda kai mutane su gane baka iya doki ba? Sannan su fahimci makantarka?” Idanunsa ya d’an rufe kadan sannan yace ” Umma.” D’agowa tai ta kalleshi yace ” har sai zuwa yaushe ne zan nunama mutane ina gani?” Kallansa tai tace ” Abu Turab!” Yacigaba ” Wani irin tsoro ne damu da haryanzu bamu cireshi a ranmu ba? Kina tunanin wannan tsoron namu akwai inda zai kaimu?” bai jira amsarta ba ya cigaba “a’a, wannan tsoron haka zai cigaba da dawammar damu a inda muke ba tare da mun tsinana komai ba? Na sha wahala tun ina yaro har zuwa wannan lokacin, har sai yaushe ne zamu kwaci ‘yan cinmu? Har sai yaushene zaki bari d’an da kika sha wahala akansa zai sama miki farin ciki?” Kallansa take yi cikin tausayawa da tsananin kauna. Hannayenta ya kama yace ” na gaji da wannan tsoron, nifa namiji ne, jinin mahaifina haka kuma d’a gareki, haka kikeso incigaba da zama? Ana nuna ked’in ba kowa bace balle ni? Bayan kuma ni nasan ked’in mace ce wacce kaf duniya a gurina banga kamarta ba?” Idanunta ne suka dan tara ruwa kadan, kai ya girgiza mata yace ” tun ina d’an yaro kika haneni da ragonta da kuka, Umma kina tunanin Mai Martaba shine zai kwatar mana ‘yancin mu?” Kallan mamaki tamai, kai ya girgiza yace ” ko kad’an in har kina tunanin wannan ki cire a ranki, Mai Martaba sarki ne, sarkin mutane masu dumbun yawa wanda yake mulkarsu sai dai ba sarki bane a tsakanin matansa, Magajiya bazata taba barinsa yai yanda yakeso ba akan matansa, yaci ace a shekaru goman nan kin fahimci haka.” Murmushi tai sannan tace “nasan da haka Abu Turab sai dai ina tsoron karmu lakutowa kanmu abinda gaba bazamu iya magani ba.” Dariya yai sai dai mai dan sanyi, wanda rabon dayai dariya haka ya dade yace ” ina Umma na ne wacce take tsaidani in nai laifi? Ina Umma nane wacce take hanani kuka? Ina Umma nane wacce ke marina duk sanda na b’ata mata rai?” Harara ta makamai tace ” da alama girma ya fara kama wannan Umman taka.” _Nikaina sai da na saki wata bazawarar dariya….Lol_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *