KAINUWA CHAPTER 7

KAINUWA

CHAPTER 7

Turab yana shiga ya bud”e kofar d”akinsa yasa kai zai shiga kenan yaji muryar Garzali yace “Ranka ya dade ana nemanka.”+

Juyowa yai yace ” wa?”
Garzali yai kasa dakai, Abu Turab ya kalleshi yace “Umma ce?”

“Tuba nake ranka ya dade.”
Idanu Turab ya rufe, Garzali ya tsugunna da sauri yace ” Tuba nakeyi.”
Abu Turab ya juya har yakai kofa sannan ya tsaya yace ” ka fada mata komai?”
Garzali yace ” a”a bansan waye ya sanar da ita xuwan mu can ba, ina shigowa ta turo inxo, tambayata tai me ya faru a inda mukaje…..”

Katsetshi yai yace ” tambayar da maka itace ka fada mata komai?”
Garzali yace ” nadai sanar da ita kunan dakai amma bansanar da ita wani abu ba daga wannan.”
Takawa yai ya cigaba da tafiyarsa fuskarsa a d”aure.

Xama yai irin zaman daya sabayi a gaban ta, wato lankwashe kafa, kansa na kasa kallansa tai cikin kulawa tace ” muga hannun.”

D”agowa yai ya mata murmushi yace ” Umma karfa ki damu ba wani abu bane nine bansani ba na taba ruwan zafi sannan a lokacin aka samun zuma a gun.”

Ido ta kuramai cikin kulawa da tausayi tace ” Turab ba sai ka dage ba wajen b”oyemin gaskiya ba dan hankalina ya kwanta, banaji ko yaro ne yaji xancen nan naka zai yarda.”

Kallanta yai yace ” Umma.”

Yanda ya kirata yasa bata amsa ba sai kallesa datai.
Ajiyar zuciya yai yace ” Umma ina neman alfarma a gunki.”
Idanunta na kansa bata dauke ba haka kuma batace komai ba ya cigaba ” abu d”aya nakeso kimin, dan Allah Umma ki rage damuwa dani.”

Cikin tsananin mamaki ta kalleshi sai dai yanayin yanda yai maganar yasa ta kasa magana.

Idanunsa yadan rufe kadan sannan yace ” gidan sarauta muke, sarautar ma inda makiyanmu sukai yawa, na tabbata a gidan nan kaf daga ciki har waje in har mukace muna neman wanda yake kaunarmu dari bisa dari banaji zamu samu mutane goma cikaku, in muka dauke bayin dake karkashin mu, yanayin yanda muke rayuwarmu ni dake dole ne sai mun sadaukar da rayuwarmu dolene mu sha wahala in har munasan zama cikin kwanciyar hankali, sa damuwata a ranki da kuma shiga wani hali in har abu ya sameni ina ganin babbar matsala ce, saboda dole wani sa”in zan nemi b”oye miki wani abun saboda gudun shiga wani yanayi da kikeyi.”

Kallansa tai jikinta yayi mugun sanyi, tanasan sanar dashi abinda ya samu yayanta sai dai a yanda tasan Turab tana ganin in har yasan abinda ya faru dasu to fa lalai tana ganin xai cire wani farinciki a ransa ne ya juya rayuwarsa zuwa d”aukan fansa wanda ita kuma tana san farincikin danta dukda kuwa tasha alwashin hukunta wanda yama yayanta hakan.

Kallanta yai ganin yanayin datake ciki yasa ya runste idanunsa da karfi sannan ya mike yai hanyar fita.

Jiyai tace ” shikenan Abu Turab.”
Tsayawa yai sannan a hankali ya juyo ya kalleta, ta mai murmushin yake sannan tace ” hankalinka ya kwanta?”
Kallanta yai cikin wani yanayi, sannan a hankali ya taka inda take zaune ya tsugunna gabanta yace “Umma do u trust me?”

Kallansa tai tace ” me kenan?”
Dariya yad”anyi kadan yace ” nufina kin yarda dani?”
Kai ta d”aga mai, ya dan murmusa yace ” shikadai nake bukata, yardarki gareni, in har kin yarda dani inaso ki yarda xan kula dake bazan bari wani abu kuma ya samen ba sai dai abinda Allah ya kaddara.”

STORY CONTINUES BELOW
Kai ta jinjina mai tace ” nagode Abu Turab, sannan insha Allah ba abinda zai sameka.”

Mikewa yai ya mata sallama zai fita.
Mairo wacce ta kawoma Basira gwaza wacce mahaifiyarta ta dafata ta fere ta sa ma kula, taxo shiga taji yana cema Basira do u trust me? Wanda hakan yasa ta koma ta tsaya.
Jin alamun fitowarsa yasa ta juya da sauri zatai waje garin sauri kafafunta suka harde, baya tai luu kamar zata fadi.
Cikin hanzari ya karaso ya tareta.
Idanunta ne suka sauka akan nasa, kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ya saketa dan sam ya manta ashefa batasan yana gani ba.

Jikake tim ta fadi a kasa, sosai taji xafin faduwar saboda sam bata zaci zai saketa ba, kallansa tai kamar tai kuka dan bakin ciki.

Hannu yasa yace ” sannu faduwa kikai?kina ina?”

Haushi ya kamata ta mike ta matso inda yake tace ” yaya fadamin gaskiya, da saninka ka sakeni ko?”

Gefen inda take ya kalla yace ” me kike nufi?”

Sake baki tai cikin salon shagwaba tace ” inba haka ba tayaya ka taimaken kuma zaka sakeni?”

Murmushi yai dan tabbas yaga faduwar datai yasan taji zafi yace ” au so kike in rike ki?”
Kallansa tai tace ” yaushe nace haka?”

Iska yadan furzar yace” lalai Mairo da alama aure kikeso.”
Ya juya da sandarsa ya fara tafiya.

Takaici ma ya hanata magana, aure takeso? Me yake nufi da hakan?

Kallansa tai ta baya a hankali tace ” na tabbata mun fa hada ido dashi.”

Tana neman amsar tambayarta taji muryar.

Lantana taji tana cewa ” Mairo? Me kike anan a tsaye?”

Juyowa tai ta kalleta idanunta sun dan ciciko, kusa da ita taxo ta ajiye kula tace ” kiba Umma.”
Ta juya da sauri tai waje.

Abu Turab kam b”angarensa ya nufa yana bud”e gate, bayinsa suka taho da sauri suka karasa bud”e mai kofa.
Ciki ya shiga, yana zama Garzali ya mikomai abu a bakar leda.

Yace “Ranka ya dade gashi an aiko a kawoma.”

Yace “Magajiya?”
Garzali yace ” a”a wlh bansan waye ba kawai kawowa akai, dana tambaya inji waye sai wacce ta kawo ta juya da gudu.”
Ya gane Khadija ce, bai sa hannu ya amsa ba yace ” ajiye anan kwanciya nake sanyi.”

Ajiye wa yai ya mike a hankali yai waje.
Yana fita ya kalli ledar, shiru yai yana tuno fuskarta, fuskar daya dade yana san gani duk yanda yaso ya yage ta a ransa ya kasa, dan karamin tsaki yaja sannan ya sa hannayensa kan goshinsa.
Khadija kam bayan ta aikamai da magani gida ta tafi ta shige dakinsu ta fada gado ta kwanta, kuka kawai takeyi tana jin xafin abinda akama Turab.

Duk yanda mahaifiyarta tai akan ta bude kofar taki, ko abinci kinci tai.
*********

Yau kwanan Basira ne, ta shirya tsaf ta nufi bangaren Mai Martaba.
Bayan sun kwanta ne ya kalleta yace ” Basira.”

Kallansa tai ba tare da ta amsa ba, yacigaba ” me kike tunani game da auren Turab?”

Kallan mamaki tamai tace “aure? Takawa ka manta Abdulmajid baiyi aure ba?”

Kallanta yai yace ” na sani sarai sai dai inatunanin auran sa zai sa matsayinsa da kimarsa ta karu a gun mutane sannan inasan nemarmasa matar da zata taimakeshi yanda ko ansan yana gani ba wani wanda ya isa ya nemi cutar dashi.”

Kallansa tai tace “ban gane ba?”

Yace ” me kike tunani game da hadin aure da “yar sarkin kano?”

Kallansa tai tace ” Bilkisu?”
Kai ya daga mata alamar eh.
Kallansa tai jiki a sanyaye tace ” amma kana ganin za”a bashi? Na farko shi makaho ne a idan duniya sannan Bilkisu ita kadaice mace a gun Sarki Muktar wato sarkin kano, ni nafi mai sha”awar mairo “yar gidan Barde.”

Kallanta yai yace ” Na fahimceki sai dai ina so ki sani Abu Turab ba mijin mace d”aya bane sannan yana bukatar mace kamar Bilkisu saboda taimakamai wajen hawa mulki.”

Da sauri ta mike zaune cikin tsananin tashin hankali tace ” me? Mulki?”

Kallanta yai ya daga mata kai.

Idanu ta zaro cikin tsananin mamaki, yace ” Bilkisu ita Magajiya takesan aurama Abdulmajid in har ya aureta ba makawa sai ya hau mulki, bakya tunanin abinda zai faru da rayuwar ku ke da Abu Turab kn har Abdulmajid ya hau mulki?”

Kallansa tai duk tama rasa ta cewa dan ta tsorata da zancen.

Ya kalleta yace ” Abu Turab shi kadai ne wanda ko bayan raina na tabbata bazai wulakanta ahalina ba, bazai wulakanta mutanena ba, bazai rushe rayuwar dana gina a kasa ta ba.”
Kai kawai tashiga girgizawa tana tsoron abinda zai faru da wannan sabon lamarin…….
Kallansa tai cikin tashin hankali tace ” mai kake nufi da kalamanka? Nasani ka fini iko da Abu Turab sai dai ina rokonka kabar maganar nan a kan gadon nan, ni zan manta munyi wannan maganar dakai.”+

Jitai yace ” kin taba jin inda akai magana bayan wanda aka fadama maganar yaji sannan yace zai manta maganar? Ai magana ana manta tane in batada mahimmanci.”

Kallansa tai tace ” dan Allah kabar maganar nan, nafisan Turab ya auri Mairo ya bar gidan nan dan samun farincikin rayuwarsa.”

“In kuma kaddararsa ce mulkin fa?” Jin maganar tai batai zata ba, Kallansa tai batace komai ba.
Shima bai tanka mata ba ya kwanta tare da juya bayansa.
Ta dade a zaune tana kallansa kafin ta kwanta.
Idanunsa a bud”e suke tunani yakeyi ” bazai iya sanar da ita su Magajiya sune sanadiyyar makantar Abu Turab ba saboda bayasan ya sanya mata damuwa da kuma shiga wani yanayi najin wannan zancen.

Ba shakka shikanshi jin wannan zance ya daga mai hankali matuka, kamar wasa d”azu da rana Khadija yar gidan Hisham ta samu barde da sakon Lami akan dan Allah tanasan Mai Martaba ya ziyarceta dan akwai magana mai mahimmanci da takesan sanar dashi.
Ganin yanayin aikin dake gabansa yasa ya aika Barde akan yaje yaji menene.
Zuwan Barde ya taradda ita cikin mugun hali, tana kwance ko mikewa bata iyayi, ba kowa a gunta d”akin banda wari ma ba abinda yakeyi wai a hakan ma zuwan Khadija ne ta gyara mata d”azu.
Barde ya kalleta tare da dubata, ya d”ora da cewa “amma ya akai ke kad”ai anan?”

Tana kwance sai numfarfashi takeyi tace ” Barde.”

Kallanta yai cikin tausayawa yace ” Mai Martaba wani uzuri ya rikeshi shine yace inzo inji menene, bai san jikin naki haka yakoma ba.”2

Hawayene suka gangaro mata tace ” Barde ni tawa ta kare dan banaji ko gobe zan kai a duniya, dan Allah ka nemarmin yafiya agun Abu Turab, Basira da Mai Martaba.”

Kallan mamaki ya mata yace ” ban gane ba.”
Hawayene suka kara kwaranyu mata tace ” nice sanadiyyar makantar Abu Turab dan kuwa nice na je gun malami aka makantar dashi, kwanakin nan ko bacci na fara ganin yaro nakeyi ba ido yana tsaye a gabana, na tabbata laifin danai ne yake bibiyata, na sani alhakinsa ne ma ya kwantar dani haka, “ya”yana da “yan uwana da nake komai dan faran ta musu rai duk sun gujeni…..”

Kuka ne yaci karfinta wanda yasa ta kasa karasawa, jikin Barde ne ya mutu mamaki da tsoron wannan al”amari yasa ya taho daga gidanta ba tare da ya gamajin kalamanta ba.

Idanu mai martaba yadan runtse a ransa yace ” bazan taba yafe musu ba.”
Babban bakin cikinsa shine a matsayinsa na sarki bashida hujjar hukuntasu, na farko bashida kwakwarar shaida sannan inma yana tunanin Lami zata zamarmai shaida ya tabbata Magajiya juya abin zatai kanta ko za”ai me bazata taba cewa itace sila ba.

Ba shakka sanya Abu Turab a mukamin Sarki ita kadai ce hanyar da zai sa ya hukuntasu ta ruwan sanyi wanda yafi na zafi kuna.

Dolene Abu Turab ya auri Bilkisu dan kuwa wannan shine mataki na farko na cinma burinsa.

Basira ma bacci ya gagareta ta rasa abinda ke mata dadi, itakam ba wata “yar sarki datake so Mairo takeso ta bashi ko dan farincikin sa na nan gaba.

***********

Washegari da safe Abu Turab ya tafi garden din mahaifinsa wanda a yanzu shike zama agun dan kebencewa daga hayaniya, yana zuwa gun ne a duk lokacin da yake bukatar yin dogon nazari game da wani abu.

STORY CONTINUES BELOW
A zaune yake akan kujera ta karfe dake gun, shukoki kala kala ne a gun, wanda ya kayata gun, kansa ya kwantar a kan saman kujerar ya lumshe idanuwansa tare da dora hannunsa daya kone akan goshinsa.

Kana ganinsa kaga mai bacci, shigowa tai a hankali gun, tafiyarta takeyi mai sanyi tana tafe tana duba inda yake, cak ta tsaya a yayin data han goshi akan kujera, tunda ya fito ta biyoshi, sannan matsayinta yasa fadawan dake gadin kofar shiga gun basu hanata shiga ba.

Murmushi ne ya bayyana a fuskarta ganin yanda ya ke, ta dauka bacci yakeyi hakan yasa ta tako a hankali tazo inda yake.
Ta bayan kujerar ta tsaya ya zamana tana tsaye saman inda ya kwantar da kansa.

Hannunsa ta kalla gun yayi jaa har yanzu amma bai duri ruwa ba.

Kallansa takeyi tanajin wani sanyi na ratsa dukkan sansan jikinta.
Jin kamar mutum na kusa dashi yasa ya bud”e idanunsa a hankali.
A hankali ya kara maida idanunsa ya lumshe dan ya tabbata mafarki yakeyi, ba wanda ya taba biyoshi gun sannan in ma ana biyoshi mai zai kawo Khadija nan?

Idanunta ne suka ciciko a hankali tace ” yanzu fa bazai ganni ba ko?”
Idanunsa ya kara budewa ya daurasu a kanta, itama kallansa tai.
Da sauri ya mike zaune ya dan maze yace “akwai mutum anan ne?”

Khadija batace komai ba, jin yayi shiru yasa a ranta tace ” da alama bai san dani ba.”
Dawowa tai ta gabansa ta tsugunna tare da tagumi kallansa kawai takeyi, ba shakka su Magajiya da Mahaifinta sun bata mata rai sosai wannan wace irin muguntace?

Abu Turab yana ganinta amma sai yai kamar bai ganta ba.
Sunfi minti talatin a haka kafin daga bisani ya mike rike da sandarsa.
Yace ” na dauka nayi magana akan wanene anan ko? Ko dan bana gani an dauka bana jin motsi da numfashin mutum?”

Idanu Khadija ta zaro itama ta mike tsaye, juyawa taga yayi zai tafi da sauri ta sa hannu ta rike rigarshi ta baya.
Tsayawa yai va tare da ya juyo ba, yace ” wanene?”

Shiru tai batace komai ba, rigarsa ya fizge ya fara tafiya da sauri ta sa hannu batasani ba ta riko hannunsa.
Tsayawa yai sai dai wannan karan ya juyo.
Hannunta ta kalla da sauri ta sakeshi tace ” Yaya nice.”
Fuskarsa a d”aure yace “kece wa?”

A hankali tace ” Khadija ce.”
Gani tai ya sake juyawa zai tafi.
Gabansa tasha da sauri, shikuma yai kamar bai ganta ba ya taho ya dauka in ya taho zata matsa ita kuma bata taba tunanin zai zo daf haka ba.
Jikinsu ne ya hadu da juna wanda tsoro yasa ta rike rigarsa tai baya da sauri, shi kuma rike rigarsa datai yasa ya fada kanta suka fadi tare?

Idanunta ta rufe saboda tsananin kunya, shikam kallanta yai sosai dan bai taba kallanta daf da daf ba sai yau.

Idanunta a rufe tace ” Ya ka d”agani!” Cikin shagwaba tai maganar kallanta yai yace ” da wayace ki yarda ni?”

Tace ” ni kuma? Yaushe?”
Mikewa yai tare da sa hannu ya d”agota hannu tasa ta rufe fuskarta.
Juyawa taga yayi zai tafi sai alokacin ma abin yazo mata to ma in taji kunyarsa inama ya gani?

Daurewa tai tace “Yaya kayi hakuri.”
Yace “game da me kenan?”
Tana tsaye a bayansa tace “game da komai ma.”
” niban fahimci hakurin da kike bani ba ai.”

Hawaye ne suka fara zubo mata, cikin kuka tace ” na konewar da kai wanda su Umma Babba suka ja ma.”

Fuskarsa a had”e yace ” wannan kuma menene naki a ciki? Meye naki na bada hakuri?”

Kallansa tai ta baya tace ” taya zaka ce haka Yaya?”
Cikin bacin rai ya Juyo ya kalleta yace ” kukan me kike kuma?”
Cikin kuka tace ” ni kaina so nake hawayen su tsaya.”
Dan karamin tsaki yaja yace ” abinda ya kamata kuma nakesan naji kin ban hakuri akai da alama ma bakisan shi ba, bana bukatar kukan ki ba kuma na neman ban hakurin ki.”
Juyawa yai kamar zai tafi.
Rigarsa ta sake rikesa amma hanzu hannun rigar ta rike, a hankali ta furta “Yaya kayi hakuri tafiyar danai ba tare da nama sallama ba.”

Jikinsa ne yai sanyi, bai juyo ba, ta kara share hawayenta zatai magana ya juyo cikin bacin rai yace ” kinsan kwana nawa nai ina jiranki? Awanni nawa nai ina nemanki? Lokuta nawa na bata ina tunanin dawowarki? Zaki tafi menene inkincemin zaki tafi? Hanaki zanyi? Ko dan Kinga na dogara da zuwanki a koda yaushe? Sai dai inaso ki sani na dade da mantawa da ke da jiranki.”

Juyawa yai ya fara tafiya, tsugunnawa tai kawai tasa kuka.

“Ba laifina bane yaya, ba laifina bane nikaina banso tafiya ba, ba laifina bane.”
Abinda kawai take fada kenan.
Yana jinta yai waje shikanshi kukanta har jikinsa yake ji.
Yana fita ya jingina da jikin kofa ya dade a haka kafin ya sa sandarsa ya fara tafiya.

********

Mairo ce zaune tana wanke wanke tanayi tana “yar karamar mita dan itakam ta tsani abinda ake mata, mahaifiyarta su biyu ne, kishiyar babarta sam bata sa nata “ya”yan aiki amma ita kullum ita ake sawa aiki kuma tanayi ba a gode mata sai tai magana mahaifiyarta tace batada hakuri.

Sa”arta ta gani ta gun kishiyar mahaifiyarta ta kalleta tace ” nikam Karima wai nikam sai yaushe zaku biyani kudin wata?”

Karima ta kalleta tace ” kudin wani watan kuma?”
Mairo ta harareta tace ” na albashin aiki da kuka daukoni mana.”
Karima tace ” ban gane ba”
Mairo cikin masifa tace ” nifa bazan laminci wannan rainin hankalin ba ehe, sai kace wata “yar aikinku?”

Muryar maman Karima taji a bayanta tace ” to bazasuyi ba kedin meye aikinki? Tunda kinki aure?”
Mairo tai dariya tace ” dan ma dai bani kadai bace banyi auran ba.”

Karima tace ” da wa kike?”
Mairo tace ” wanda ya tsargu, haka kawai tunda mai taya mu aiki tai tafiya kullum ni nake aiki ni ba “yar aiki ba bakuma baiwa ba?”

Jitai an dada mata duka a bayanta ta juyo da nufin masifa, mahaifiyarta ta tagani, ta kalleta tace ” Mairo bana hanaki ba?”

Turo baki tai batace komai.
Garzali ne ya biyoshi suka nufi fada dan yanzu aka aiko akan yaje saboda Abdulmajid zai sanar da binciken dayai.
Bayan sun zauna ne Abdulmajid ya dawo tsakiya sannan yace ” Ranka ya dade na gama bincike.”
Galadima ne yace ” to munajinka.”
Abdulmajid yai d”an gyaran murya sannan yace ” bincike ya nuna mana cewa ba kowa bane ya jawo wannan abin ba sai mahaifiyarsa.”

Jin wannan zance yasa mutane suka fara kananan magan magan, Abu Turab kam wani murmushi ya saki kansa na kasa a ransa yace ” they take the bait.”

Kallan Abdulmajid kowa yai, Mai Martaba ya kalleshi yace ” meye hujjarka na fadar haka?”
Abdulmajid ya gyara zama yace ” Mahaifiyarsa tanasan asan shi wanene, ma”ana asan shidin d”an sarki ne, sannan tayi hakan ne dan mutane su farga susan akwai wani magajin sarkin bayan ni.”

Mai Martaba yace ” wannan ita kadai ce hujjarka?”
Kai ya girgiza alamar a”a yace ” tayi abu kala biyu, na farko in har yasa mutane zasu sanshi saboda kayansa da kuma yanayin dokinsa, na biyu kuma ba wanda zaiyi zarginta sai dai kowa yai zargin Magajiya, kunga ta jefi tsintsu biyu da dutse d”aya.”

AbuTurab ya d”ago kai yace ” Bravo! Ba shakka wannan ma abin dubawa ne.”
Mamaki hakan yaba Abdulmajid ya dauka abin zai tadamai hankali.
Barde ne ya katse mai tunaninsa da cewa ” shaidu fa?”

Abdulmajid ya juya yace ” shigo.”
Nan wani bawa ya shigo wanda kowa ya sani bawa ne wanda ke kula da al”amuran Magajiya na waje bana ciki ba.

Daga can bakin kofa ya zube ya gaidasu, Abdulmajid yace ” wannan bawan bawa ne ga Magajiya shi Mahaifiyar Abu Turab tai amfani gun aika mai da kaya dan gudun kar a gane itace.”

To fa? Nan kowa yad”an fara magana kasa kasa.
Abdulmajid ya kalleshi yace ” sanar damu abinda ka sani.”
Muryarsa na rawa alamar tsoro da dana sani yace ” tuba nake ranka ya dade amma abinda Yarima mai jiran gado ya fada haka yake, ranar nazo wucewa Baiwarta wato Lantana ta mikon kaya tace ” dan Allah sauri nake dan mikama Abu Turab, basai ka shiga ba kawai ka bada a kofar shiga ka wuce.”
Salati mutane suka fara dayawa sun gamsu dan sunsan ba yanda za”ai bawa yazo gaban mai martaba ya gilla karya haka.

Abu Turab yai murmushi sannan yace ” Ammm ina Mai bada shaidar nan?”
Bawan yace ganinan Yarima.”
Abu Turab yace ” ka tabbata duk abinda ka fada gaskiya ne?”
Yace ” hakan yake Ranka ya dade, ina ni ina karya gaban Takawa.”

Abu Turab yace ” haka ne, sai dai nima ina rokon a bani dama namai tambaya.”
Mai Martaba yace ” inajinka.”

Abu Turab yace ” inaso ka bani amsar tambaya ta cikin sauri ba tare da kaja min lokaci ba, inaso daga na tambayeka ka sanar dani amsa.”
Kai ya daga.
Abu Turab yace ” A ina kuka had”u?”
“Gaban Turakar Magajiya.”
“Hmm kenan can ta bika saboda tana san ta aikeka?”
Muryarsa ce tadan sarke yace ” banida masaniya akan wannan.”
Yace ” me yasa daka kawo kayan baka ce inji Lantana ba bayan a iya sanina wanda ya kawo kayan ance ya sanar da wanda ya aikosho?”
Inin na ya fara cikin tsoro yace ” hmm hmm nima sauri nake hmm shi yasa…..”

Abu Turab ya karseshi da cewa ” ok na gane, saurin da kakeyi ne ya hanaka sanarwa ko?”
Da sauri yace haka ne.
Abu Turab yace ” kenan bayi nane sukai karya tunda sun sanar dani an fada musu wanda ya aiko da kayan?”

Bawan yai shiru, Abu Turab yace ” na fahimceka, yanzu tambaya d”aya zan maka, dakai da Lantana wanene yafi wani matsayi a gidan nan?”
Cikin rashin fahimtar zancensa yace ” na fita.”
Abu Turab yace ” Good! Ka fita matsayi meya saka ka yarda ta aikeka?”

STORY CONTINUES BELOW
Gaban Bawan ne ya fadi ya fara inda inda “hmm dama….”
Katseshi Abu Turab yai yace ” dama me?”
Shiru yai dan ya rasa bakin magana, Abu Turab yace ” bari na aika a kira Lantana da alama kunada wata ala”aka da ita wanda ba wanda ya sani, dan hakan ne kadai zai sa mu fahimci dalilinka na zuwa aikenta.”

Hankalinsa ne ya tashi da sauri yace ” wlh ba haka bane ni banma taba magana da ita ba, ina dai gani suna zuwa gun Magajiya amma wlh ko sau d”aya bamu taba magana da ita ba…..”1

Shiru yai jin ya kauce hanya a zancen sa.
Abu Turab yace ” to fa yanzu wace maganar zamu yadda da ita?”
Galadima a harzuke yace ” wannan shaidar bamu yarda da ita ba dan ta nuna itadin bakin ganga ce.”

Idanu Abdulmajid ya runtse dan bakin ciki.
Wani mugun kallo ya bugama Abu Turab, nan mutane suka fara kananan maganganu, lalai dama ance makaho yanada tasa baiwar da alama Abu Turab akwai kwakwalwa, ganin ne dai da Allah ya d”auke mai.

Kallansa Mai Martaba yai cikin jin dadi, Abdulmajid yace ” inada wata shaidar.”
Mai Martaba yace ” muna jinka.”
Wanda ya kawoma Abu Turab doki ne ya shigo, bayan yayi gaisuwa Abdulmajid ya kalleshi yace ” sanar damu abinda ya faru.”

Nan yace shidai an aikeshi ne yakai doki bangaren Abu Turab.
Abu Turab ne ya katse Abdulmajid wanda ke shirin magana yace ” tabbas muryarka ce naji a lokacin, sai dai tunda ba gani nake ba bazan san kaidin bawan wanene ba.”
Kansa na kasa yace ” bawan Magajiya ne.”
Murmushi Abu Turab yai yace ” kenan duk bayin Magajiya ta nemo?”

Abdulmajid ya bugamai kallo baice komai ba, Abu Turab yace ” amma ni mai ka sanar dani a lokacin? Wa kacemin ya aiko ka?”

D”agowa yai yad”an kalli Abu Turab, gabansa ne ya fadi, duk da yasan baya gani amma baisan me yasa ba sai yaga kamar yana kallansa, kwarjini Turab yamai dama gashi duk cikinshi ya gama rud”ewa a waje dan kuwa yaji duk abinda ya faru da d”aya bawan.

Shiru yai baice komai ba, Barde yace ” zancen banza kenan, tayaya ana tambayarsa ya kasa bada amsa.”
Mai Martaba ne yai gyaran murya yace ” Kana da wata shaidar? Dan wannan shaidar naga farar kura ce.”

Abdulmajid kasa yai dakai a hankali yace ” tuba nake ranka ya dade banida wata.”

Mai Martaba ya kalli Abu Turab yace ” kaifa? Kanada ta cewa?”

Abu Turab yace ” ina neman alfarma akan mai martaba ya yafema wanda ya aikata wannan laifin gudun samun babbar matsala garin bincike, dan na tabbata duk wanda ya aikata hakan tabbas bazai yarda a gane shi bane.”
Mai Martaba yace ” zanyi tunani, amma wad”an nan bayin da sukai shaidar karya inaso a kullemin su.”
Da wannan fada ta tashi, kowa yana yaba kwazon Abu Turab.
Hisham kam da Abdulmajid a cike suka isa gun Magajiya, bayan taji komai ta kalli Abdulmajid bai yi auni ba yaji ta wanka mai mari.

Tashin hankali, d”agowa yai cikin tashin hankali dan tunda aka haifeshi ba”a taba dukansa ba sai yau, Magajiya ta kalleshi tace ” wannan shine shirmanka na cewa in barma zaka d”au mataki da kanka? Wannan shine abinda kwakwalwarka kawai zata iya karantama?”

Hisham wanda yaji dukan kamar a fuskarsa ya daure yace ” kiyi hakuri Magajiya.”

Kallan Abdulmajid tai tace ” ku bani guri.”

Nan suka mike jiki a sanyaye, Hisham na fita yai “yar karamar kwafa a ransa yace ” wlh wannan marin bashinshi kika co kikira d”ana ya hau mulki zakisan kin mareshi.”
**********

Bayan sati d”aya.

Abu Turab zaune a gun mahaifiyarsa yanacin abinci sai dai zuciyarsa nata tunanin tun randa yaga khadija bai sake ganinta ba har yau, ko dai ta koma inda ta tafi da ne?

Yana neman amsar tambayarsa yaji sallamar Mairo.
Amsawa yai va tareda ya juyo ba.
Gefensa ta karasa ta gaisheshi sannan tace ” Yaya ina Umma?”
Yace “Mairo tana ciki, kwana biyu?”
Murmushi tai tace ” na da”uka ko daina zuwa nai bazaka nemanba bare ka tambayen dalili.”

Juyowa yai yace ” tanan kika b”ulo?”
Tace “Ba haka bane yaya gaskiya ce ai na fada.”
Yace ” hmm, ina saurayin naki? Ki fada mai fa in har yanasan in ba da ke sai yazo ya kwashi gaisuws.”
Fuska ta had”e tace “ni bansanshi ba.”

Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa wanda har hakwaransa suka fito, daidai nan Basira ta fito, kallansa tai cikin jin dadi tana ganin yanda yake tsokanar Mairo, kana ganinsu kasan suna cikin farin ciki, lalai dolene ta tilastamai auren Mairo.

Yana gama cin abinci yanashan ruwa Garzali ya sanar dashi nemansa da Sabi”u yake.

Mikewa yai ya sa hannu zai dauki sandarsa, da sauri Mairo ta d”auke sandar ta b”oye tana dariya.
Yace ” Mairo nasan kece, mikomin in fita, in kuma baki ban ba zan fita a haka duk abinda ya samen kece.”

Da sauri ta mikomai tace ” yahkuri yaya.”
Amsa yai ya fita baice komai ba.
Kallo ta bishi dashi tanajin wani abu na ratsa ta.

*********
A waje yaga Sabi”u yiyai kamar zai wuceshi, Sabi”u yace ” ganinan mutumina.”
Ya karasa maganar tare da dafashi.
Abu Turab yace ” Badai aiko ka akai ba ko?”
Yace ” Mai Martaba ne yace inzo dakai.”
Fuskarsa a hade yace ” dama nasan bazaka kazo dan radin kanka ba.”

Sabi”u yace ” Abu turab kaikasan dalilina, kana gani yanda nake sha fada agun Mahaifina na bayasan in ware ga wanda nakeso saboda gudun nan gaba.”

Abu Turab yai murmushi yace ” da gaskiyarsa, tunda yasan Abdulmajid ne next emperor kaga kuwa yana tsoron kar Abdulmajid ya hukuntaka na shakuwa dani.”

Sabi”u yai tsaki yace ” in kuma kaine fa?”
Tsaki Abu Turab yai yace ” zaka fara ko?”

Sabi”u yace “Allah sau dubu kafi Abdulmajid matsalar ido ce kadai kuma…….”
Abu Turab ya katseshi yace ” muje dan Allah.”
*********
Sun isa gun hutawar Mai Martaba inda yake zaune rike da wasu takardu yana dubawa, bayan sun gaisheshi ne Mai Martaba ya kalli sabi”u hakan yasa ya mike yai baya dasu.

Shiru ne ya biyo baya kafin Mai martaba ya kalli Turab yace ” Abu Turab!”

Yanda ya kira sunansa ne yasa Abu turab kallan mahaifin nasa.
Cigaba yai da cewa “Inaso gobe Asabar dakai da Sabi”u ku ziyarci masarautar Kano.”

Kallansa yai cikin mamaki, sai dai baice komai ba.
Mai Martaba yace ” Zakuje Masarautar ne da nufin ziyara sai dai inaso ka samu keb”ewa da Bilkisu “yar Sarkin garin.”

Cikin mamaki yace ” ban gane ba Abba.”
Mai Martaba yace ” Inaso duk yanda zakai kayi dumin sace zuciyarta.”
Mamaki ne yasa Abu Turab ya kasa magana.
Mai Martaba yace ” Umarnine na baka ba shawara ba, inaso ka kwana a garin kamar kwana biyu, a wannan lokacin ka tabbatar Bilkisu ta aminta dakai.”

Kansa na kasa yace ” bazan tambayi dalili ba dan nasan ba kirana kai a matsayi uba ba, ka kira ni ne a matsayin Sarki, zanyi abinda kace sai dai inada tambaya, a makaho xan je mata?”

Sarki yace ” wannan na bar maka hukuncin domin ni Sarki ne wanda baisan d”ansa yana gani ba.”1

Nagode, kawai abinda yace kenan ya mike.
Suna fita daga gun ya tsaya cak, jiyake kamar zuciyarsa zata fashe.
Sabi”u ka dafashi yace “me yasa baka musa mai ba?”

Yace ” ta ina zan musamai bayan Umarnin Sarki ne bana uba ba?”

Sabi”u ya kalleshi cikin tausayi yace ” amma nifa hadin auren ya birgeni, Bilkisu itakadai ce gun Sarkin kano aurenka da ita zai karama matsayi da kuma daraja agun mutane.”1

Abu Turab murmusawa kawai yai baice komai ba, Sabi”u ya kalleshi yace “yanzu ya zakai?”
Juyowa yai saitinsa yace ” Sabi”u nasan bazan samu abinda zuciya ta takeso ba dan haka banga wani damuwa ba akan auren wata, ban dauki auren nan wani abun ba banda biyayya da kuma raba gado da wata ba.”

Dariya ce ta kama Sabi”u yace ” raba gado?lalai Turab bakada kyau, taya zaka dauki auren “yar sarki akan raba gado?”
Tsaki yad”an ja yace ” to fadamim, soyayya ce?aminta ce?yan uwan taka ce? Ko kuwa shakuwa ce?”

Dariya Sabi”u ya sakeyi baice komai ba.1

********

Acan gidan Waziri kuwa Hisham kuwa tunda Khadija ta dawo zazzabi ya rufe ta yau sati d”aya kenan tana fama da zazzabi da ciwon kai.
7
Wannan kenan
B”angaren Mahaifiyarsa ya nufa, tana zaune gefenta kuma Lantana ce, daga bayanta kuma a tsaye Mairo ce take mata kitso, jiki a sanyaye yai sallama.
Dukansu suka amsa nan ya karasa ya zauna a kasa tare da lankwashe kafafunsa.
Basira ta kalleshi sai dai batace komai ba, d”agowa yai yace ” Umma gobe zani Kano.”
Gabanta ne ya fadi dan kuwa tasan me zaije yi kanon.
Sam ta manta da Mairo dan kuwa hankalinta ya tashi, ta kalleshi tace ” ka amince da ganin yarinyar ne ko kuwa har auren?”

Idanu Mairo ta zaro cikin tsananin tashin hankali, kallan Abu Turab kawai tayi, shima jin kalaman Basira yasa ya d”ago ya kalli Mairo.
Ganin yanda idanunta sukai yasa ya kalli Basira kansa na kasa yace “Mairo bamu guri.”

Jin haka yasa Basira ta juyo da sauri ta kalleta, ganin yanda kwallq ta ciciko mata yasa tace ” Lantana shiga da ita d”aki

Mikewa Lantana tai ta ja ta ciki, suna shiga ta zube a kasa tare da hade kanta da gwiwarta, ba kuka take ba sai dai yanda takeji a ranta tabbas taso ace ma kukan takeyi.

Tana iya jiyo muryar Basira sama sama tana cewa ” Abu Turab nifa wannan hadin auren bai kwantamin ba, nafisan ka auri Mairo ko dan samun nutsuwarka da kuma kwanciyar hankalinka.”
Dan murmusawa yai yace ” Umma kinaso ne na karya umarnin Sarki ko me? Abba ya kiranine a matsayin Sarki bawai a matsayin Uba ba, sannan maganar Mairo nicewa tai tana sona ko kuwa nice nace ina santa?”
Shikam yasan tana sansa sai dai yayi hakan ne dan sa Umma ta saduda, ya cigaba da cewa ” itama ta kanon xan dai jene kawai inbi Umarnin da aka bani amma tana “yar sarki guda d”aya tilo mai zatai dani? Makaho?”
Basira cikin bacin rai tace ” Da farko amsarka xan ba, na tabbata kai kanka kasan Mairo tana sanka, sannan kaima nasan haka, sannan na biyu shi mai martaba cewa yai kaje a Makaho?”

Gaban Mairo ne ya fadi, Lantana jin haka ta taso fa sauri daga inda take a d”akin tace ” tashi ki shiga can ciki.”
Mairo ta kalleta tama kasa magana mikewa tai a hankali ganin yanda ta tsaya kamar me shirin faduwa yasa Lantana ta riketa, ji sukai Abu Turab yace ” yace inje a duk yanda naso, nima haryanzu ban tantance a me zanje mata ba.”
Jitai kanta yayi wani irin sarawa, cikin rawar murya ta kalli Lantana tace ” meke faruwa?”

Lantana ta kamata suka fara tafiya, sai data kaita canciki sannan ta kalleta tace ” ba abinda ya faru nikaina bansan me suke nufi ba.”

Mairo ta kalleta tace ” amma dai ba kina nufin in yarda da kalamanki ba ko?”
A makaho xakaje mata? Ta maimaita maganar da Basira tai sannan tacigaba da cewa ” me hakan yake nufi? Duk wanda qwaqwalwarsa take aiki na tabbata xai gane magana ce aka yita mai ma”ana biyu, a makaho zakaje mata?ko da ido?”
Lantana ta kalleta cikin tsoro, Mairo ta mike ta tsaya gaban Lantana tace ” zan gyara tambayar dana miki d”azu, Yaya yana gani?”

Idanu Lantana ta runtse batace komai ba, Mairo tace ” zan kara gyara tambaya ta, Lantana meyasa yake pretending din baya gani?”

Lantana ta girgiza kai tace ” nima bansan komai ba, da sauri tabar d”akin tare da janyo kofa.”

Mairo tai shiru tana tunani, me yasa yaya yana gani yake nuna baya gani? Wani irin abu ne yau takeji haka? Abubuwan da sukai ta faruwa dashi yana yari ta tuna, kai ta girgiza tace bazai yiwu ace pretending yakeyi tun da ba sai dai in warkewa yai.”

A can bangarensu Basira kuwa, kallansa tai tace ” Abu Turab harga Allah zaka cemin baka san Mairo tana sanka ba?”
Kallanta yai yace ” Umma!”
Tace ” ni mahaifiyarka ce nasan abinda zai taimakeka gun samun farincikinka, Mairo zata kula dakai, zata taimakeka ni aguna ita kadaice zata dawoma da farincikinka.”

Idanu ya runste yace ” nifa Mairo kanwa tace ban taba tunanin zaman aure da ita ba.”
Jiyai tace ” sai ka fara yanzu.”
Mamaki ne ya kamashi yace ” Umma nawa nake? Shekarata kwatakwata nawa? Taya zakumin zancen auren mata ba d”aya ba har biyu a rana d”aya wanda kuma duk cikinsu ba alakar soyayya dake tsakaninmu?”
Basira tace ” Ba takura maka zanyi ba sai dai inaso ka duba ra”ayina ka kuma ba shawarata lokaci mai yawa.”
Sunyi shiru kafin tace ” tashi kaje.”

Mikewa yai ya fita, d”akinsa ya shiga ya kwanta akan gado yana kallan sama.

Mairo ce ta fito kana ganinta kasan tana cikin wani yanayi, Basira ta kalleta tace ” Mairo jeki gida zansa a karasa min kitson.”
Kai ta girgiza alamar a”a tace ” a”a Umma bari na karasa miki.”
Basira tace ” jike Mairo, ninace kije ai.”
Jakarta kawai ta d”auka ta mata sallama tai waje.
Tafiya kawai takeyi amma zuciyarta fal take da tunani kala kala tama rasa ta inda zata samo amsoshin tambayoyin.

Jitai an fizgo hannunta, a tsorace ta juyo, janta kawai taga yayi soron kusa da gun ya sata a ciki.
Hannunta ta shiga fizgewa ta hada cewa ” Malam meye hakan? Sakarmin hannu ko?”
Baisake ta ba ya d”ora da cewa ” da dan rashin mutunci kina ganina kika wuce ni?”
Kallansa tai cikin takaici tace ” Malam sakeni dan Allah, ni ba muharamarka ba zaka wani dinga rikeni? In magana zakamin kamin da baki.”
Murmushi taga ya saki yace ” Karki damu saura kiris ki zama matata dan na kula shi kadai ne yanya mafi sauki da zan daidaita miki sahu.”

Kallansa tai cikin takaici tace ” in zama matarka? To ko nidin baiwa ce banaji kamada damar yanke hukunci akaina bare kuma…..”
Katseta yai tare da sakin hannunta yace ” kin dai san nidin waye kin kuma san matsayina a garin nan, ko Mahaifinki bai isa in yanke hukunci ya canza min ba.”
Dan karamin tsaki taja sannan ta kalleshi ido cikin ido tace ” Abdulmajid kake ko wa?”1

Idanu ya zaro ya kafeta dasu, tacigaba ” Zan maka kashaidi xa gargadi na farko kuma na karshe, in har zamuyi magana dakai ka kiyayi min abubuwa guda biyu, na farko kada ka kuskura ka kara rikeni ko ka taba ni ko da kuwa hijab din jikina ne, na biyu kuma kada ka kuskura ka dinga sako iyayena in muna magana, ni yanzu banda lokacin ka abinda ke gabana yafi karfin na tsaya ina bata lokacina.”
Matsawa tai da nufin wucewa, fizgota yai da karfi ya bugata jikin bango yace ” ke harkin isa ina magana kina magana, har kina da matsayin da zaki kira sunana gatse gatse har kice zakimin gargadi?”
Ajiyar zuciya tai tace ” in kaji haushi inji sammaci.”
Tana gama fadar haka ta ture hannunsa tai waje.
Kallan bayanta yai cikin kuluwa yace ” mu zuba mu gani, ina tausaya miki in kika shigo hannuna, auranki kuma ya zama dole a gareni.”
Yanajin haushin yanda baya iya yanke mata hukunci duk wulakanci da zatamai.

Itakam ranta a bace tai gaba, tana kokarin fita taga wata kamar Khadija ta wuce, binta tai da kallo cikin mamaki da san tabbatar da abinda zuciyarta ke zargi.
Khadija kam bata kula da ita ba dan ba lafiya ce ta isheta ba yanzun ma daliline ya shigo da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *