KALLON KITSE CHAPTER 12

 KALLON KITSE CHAPTER 12

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yayi tambayar cike da sha’awarta, dan yadda ya lura duk ta fita hayyacinta, daga can bayansu yaji inna na cewa, “me kuma ya kawoka kicin?”

da sauri ya juya inna ina wuni? Ya gaisheta, tare da barin wurin, “inna kin fita ne tun dazu na shigo ina sallama ashe tana kicin taki amsawa”

toh aini banji ba.” uwani ta fada.

Inna taji da gangan taki amsawa.”

toh ai kaji tace bataji ba, tunda ba kunne daya kuke dashi ba, ina zaka sani? Yayi murmushi, “toh ki kawo min abincina, bai jira amsarta ba ya wuce dakinsa.

Mirsisi tayi, saida inna tace, “ki dauka ki kai masa mana ‘yar inna.” ta dauka acikin sanda ta isa dakinsa, tana isa ta ajiye a bakin kofar, ta ruga cikin gidan. Ya kalleta, murmushi yayi, ya karasa dashi cikin dakin.

Washe gari ya shigo gaida inna, take ce masa, “tunda kasa aka daura ma aure da uwani, nima inada nawa sharrudan, na farko inaso saina shirya bana so kayi maganar tare warta har saini karan kaina nayi tunanin hakan, sannan zata ci gaba da zuwa makarantarta.

Yace, “na amince inna, a lokacin uwani ta shigo idonsa akan kugunta, ‘yan kayan data sane ya fito mata da surarta, yayi ajiyar zuciya, amma idonsa na kanta, gun inna ta nufa ta zauna. “ina kwana uncle? Ya amsa aciki, tayi kamar bata lura da yadda yanayinsa ba a ranta tace kai ka sani, kar ma ka amsa mana.”

taci gaba, “inna inaso inje gidan amarya balaraba, nida lawisa.”

“toh saikin dawo, ko kallon inda jafaru yake bata yiba, ta shige dakinsu.

Jafar ya cewa inna zai fita sai ya dawo.

Uwani ta fito, ta rataya dan karamin gyalenta, wanda ta saba sawa, ji tayi an jawota, jafaru ne.

Bai saketa ba har saida ya kaita, cikin dakinsa, “ke ina zaki? Gabanta faduwa yakeyi kamar zai fado, ta tsorace sosai, bata iya ce masa komaiba, da ganin ya kulle kofar dakin da key, “bakiji abinda nace bane?

Uncle dan Allah kayi hakuri.”

bazanyi ba, inaso inja miki kunne, ki sani yanzu bakida ikon kanki, saida iznina, yanzu kin zama matar aure.”

“yi hakuri.” ta kara fadi, “wai miyasa in kina gaban inna kin fiye rashin kunya, dakin bar wurin saiki zama kamar wata salaha? Toh bazai yuwu ba, kada ki sake ki fita gidan nan, sai da iznina.” ya matso inda take, da yake idonta na kasa, sam bata san yana gab da itaba, sai jin kamshin turarensa tayi cikin hancinta, da sauri ta daga idonta ta dubeshi.

Shikuwa yayi kamar bai san irin tashin hankali day gani a idonta ba, yasa hannunsa na dama akan bango, dai-dai kafadarta, yayi magana kasa-kasa, “Baby ina sonki, ki soni dan Allah.”

da sauri ta girgiza kanta, a’a ni bana sonka! Ya hade fuskarsa, idonsa kuwa sun canza kala, bugun gabanta ya karu, har shima yana jin faduwar gabanta, “kin san Allah dole ne ki soni, dan ni abun sone.”

da sauri tace “ga wasu matan ba, amma bani ba.” duk tsoronsa data keji bai hanata magana ba, “toh zamu gani nida ke wa zai sauko.”

zan fita, ta fada tare da zuwa bakin kofa, ya jeho mata makulli,

“zaki shiga hannuna ne yarinya, sai yadda nayi dake, sannan ina kara ja miki kunne ki rika neman izinina kafin ki fita, kin gane ko?

Ta bude kofar har sai da ta fita tukunna, sannan ta kalleshi tace, “inba a nema bafa me zakayi… .” kafin kace kwabo harya biyota, a guje ta isa cikin gida, tana kiran inna, a zaure ya tsaya yana dariya, “yarinya sai tsoro, amma kuma tsiwa ya mata yawa.

Haka yayi hutunsa na sati daya sannan ya koma kaduna, marliya dai tana nan a tunaninta tunda yaki sakinta, toh ba shakka yana sonta, kawai yana sone ya nuna mata kuskurenta dan haka ta dauki aniyar ganar dashi irin son data ke masa. Yana zaune a falo yana waya da bashir, can itama ta leko tana kallonsa yayi mata kyau sosai a ido dama suna shiri saita je ta rungumeshi.

Yau kwanansa biyar da dawowa daga tafiya amma bata ganshi ba, sai yau….” ya tsinka mata tunani data ji yace amarya lafiyarta lau, kasan mene bashir? Wallahi na matsu in sami yarinyar nan a hannuna, kona tashi yin wani abu, saina kasa dan ina shakkar inna, sam inna bata goyi baya naba, sai abunda yarinyar nan ta fada, shine dai-dai a gun inna na rasa dalili……”

marliya ce ta katse masa maganar da yakeyi, tayi tsugunne gabansa, tare da dafashi, “aure kayi doctor? Na shiga uku na lalace ni marliya na shiga uku, gaskiya bazan yadda ba, wulakancin ya isheni haka, yau saika fadamin matsayina a gunka.” nan da nan idanunsa suka sauya kala, yana dubanta, so kie kisan matsayinki? Da sauri ta amsa “eh! Inaso na sani.”

“toh shikenan dama akwai littafi kusa dashi, yayi rubutu ya mika mata. Ihu tayi, “ka sakeni, bakince in nuna miki matsayinki ba? Toh shine na nuna miki.” ya riko kunnuwanta duka biyu ya murde, “wannan saki daya ne, saura na biyu, dan haka inaso ki zama mai fita daga harkata, kuma kika sakeyi min maganar nan saki niyu zai biyo baya, dama kin daina.

Ya tureta, ta fadi kasa tana kuka mai tsimar da zuciya, duk taji tausayin kanta, ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, bakin cikinta daya datayi masa magana, amma bazata sake ba, ta fada a ranta, “wannan wace irin rayuwa ne ta shiga haka? Bata da ikon fadan magana saita samu matsala?Bata da ikon fadan magana saita samu matsala? Shin anya malamanta sunyi aiki ne akan ya sota? Ko kuwa ne dai sunyi ne akan ya mulketa?

Kuka taci gaba dayi, a fili tace, badai zan tafi ba, so yake intafi, amma bazan tafi ba ina nan har abadan abada.”

toh rayuwa kenan, Allah ya shiryamu Ameen.

A kebbi kuwa, uwani ba abunda ya dameta, tabi ta kara kyau, har yanzu ba wanda yasan tanada aure, hatta aminiyartata lawisa.

Hamza kuwa a kullum kara soyayya suke tsakaninsu, anata tunanin tunda inna tace zata raba auren toh basaita rabu da hamza ba, tunda ko an raba auren shi take so.

Ana cikin haka sukayi midMterm ta roki inna tana so taje gusau. Inna ta amince, dan yau jumma’a da wuri ta shirya ta wuce.

Hafsat kuwa murna take sosai, dama sun dan jima basu hadu ba, bayan sun baje dakin su hafsat, take zolayarta matar uncle.”

kinga bana so.

Haka ne baki so, amma haka magnar take, kinzama tashi yanzu sai yadda yayi dake wallahi.”

“uhm! Dole ne ma ya sakeni, in auri wanda nake so,

lallai uwani bakida ido, kin manta wai uncle dan inna ne, ya kamata kiyi a hankali, inba dai so kike kiyi butulci ba.

Ke hafsa kinsan ba yadda zanyi inki jinin inna ba, saboda a rayuwa ba abunda zance da ita sai addu’a.

Amma abunda na lura dashi, sam inna bata son wannan auren….ke baki saniba, inya shigo gari kullum tana kaffa-kaffa dani, ko meyasa kuma saitayi ta jamin kunne akan indaina zuwa gunsa, ko abinci zan kai masa saita ce, in ajiye a bakin kofarsa in dawo tana jira na.

“hum inna tana nema ta kareki daga sharrin namiji, kinsan fa komai na iya faruwa, gashi bawai gama makaranta kikayi ba, shiyasa takeyin haka.

Toh ai shiyasa nima nake kara tsanarshi, hardai lokacin daya bar inna cikin tashin hankali….” kofa ake bugawa, waye? Inji hafsat, “ke bude min kofa kinji ko? Da sauri suka bude kofar dan sun gano muryar mami ce (zainab).

“toh ‘yan iyayi menene nawani kulle kofa? Ai saiku fito ga uncle dinku can yazo.” da gudu hafsat tabar dakin, ita kuwa uwani mutuwar tsaye tayi, bata motsa ba a inda take, “waya fada masa ina garin nan? Ta fada a ranta, gashi bata fada masa batun zuwanta ba….hafsat ta katse mata tunani, “bazaki je kiyiwa mai gida barka da isowa ba ko? Ta fadi hakan cike da zolaya, hawaye ne ya fara zubar mata, “hafsat ya zanyi? Allah zai dukeni, ban fada masa zanzo nan ba, kuma ya gargadeni.”

toh ke ya akayi baki fada masa ba?

“ni meye ruwana dashi dazan fada masa? Ta share kwallanta, “nifa bazani gaidashi ba.

Akan wane dalili? Sharewa kawai zakiyi kije ki gaidashi.”

kinsan ba zani…..”

aiko dole kije.” muryar mami zainab ne data ke bakin kofa, mami kiyi hakuri Allah zai dukeni.

Ta riko hannunta, “zo muje ba abunda zai miki.” suka isa falon. Yana zaune rike da mujalla a hannunsa, ya dago ya dubeta, da gani yasan ta shiga wani hali, “uncle sannu da zuwa.” bai amsa mata ba, idonsa na kanta. Ta kara yi masa kyau sosai, anya zai iya hakura da yarinyar nan kuwa? Gaskiya bazi iya bin sharrudan da inna ta jera masa ba, yana ganin ya samu wannan tsaleliyar yarinyar.

Zainab ta tsinka masa tunani, “bakaji ana gaida kai bane?

“naji yaya kinsan fa zuwa tayi bata fada minba.

“au kai kuwa ai ba a tare ba, tana gun inna fa har yanzu.”

“hakane, ya fada, amma ai dasai ta bugo ta fadamin, badan kin fadamin ba da ban saniba yay?

Toh ai batada waya.”

“ba yadda za ai in bata waya yaya tunda guduna ma takeyi.”

kai kuwa kasan yarinya ce sai a hankali.”

mata nawa akayiwa yadda akayi mata? Kawai shagwaba ce, inna ta riga ta batata dayawa.” ita kam ma tuni ta koma daki, suke falo yake fadawa zainab, saida yaci abinci, sannan yace zai fita ya dawo.

Da yamma likis jafar ya shigo falo, sam basu ji shigowarsa ba, uwani na daga bakin kofa tana bada labarin wata yarinya data hau icce a makaranta ta fado, sai jin muryarsa tayi a kanta salamu alaikum.” ai kuwa tuni ta kece a guje, da sauri yace “daughter hafsat kenan.” haka yake kiransu, “kama min ita.”

caraf hafsat ta rike hannunta da sauri, ya isa gun ya riketa, ya hadata da bangon wurin yana fadin yauwa daughter na gode maki, so ina zakije ne ‘yar surutu?

Gabanta faduwa yakeyi, “bakisan kinmin laifi bane?

Niba laifin danayi.” ta fadi hakan, “ni kike fadawa haka? Toh zanyi maganinki, dama kinga ina kyaleki ne.”

tayi saurin kulle idonta, dan a zatonta dukanta zaiyi, ji tayi bakinsa akan nata kissing dinta yakeyi ba sassauci, tun tana juye-juye har dan dole ta hakura, saida ya tsosa yadda ransa ke so, sannan yadan saki bakinta, data turo yawu ta zubda, nifa uncle bana son irin wannan abunda kake yimin.”

kara matseta yayi, “karya kikey, kina so.” zai kara kai bakinsa, yaji muryar zainab, “haba jafaru kayi mata a hankali mana, baka ga yadda take bane? Yayi saurin janyewa daga gunta, “yaya ina wuni? Ya fada yana dubanta, ita kuwa uwani kuka takeyi a guje ta shige ciki, sai dakin hafsat.

Tana isa ta dadawa hafsat dundu a bayanta, itakam dariya takeyi mata, saida ta gama kukan sannan,

saida ta gama kukan, sannan ta shiga tayi wanka, ta fito tayi sallar mangariba.

Sunyi shirin barci mami zainab ta shigo dakin ta mikawa uwani waya, a kunya ce ta amsa, saida zainab ta fita sannan ta kara a kunnenta, ta lura a kunne take,

“Hello” ta fada da murya mai sanyi, har ransa yaji muryarta, yana jin yadda tayi maganar….ta tsunka masa tunani da kara cewa “Hello”

yakike? Ya fada da kasaita, bata amsa masa ba “inaso gobe ki shirya mu shiga kaduna..” bata bari ya gama magana ba, tace, nifa ba inda zani wani irin kaduna kuma? Wana sani a garin…

“ke ina wasa dake ko? Ya tambaya, murguda baki tayi saikace yana kallonta,

nagaya miki ki shirya zan shigo gobe mu wuce.”

abunda bazaiyu ba kenan.” ta fada, da sauri ta kashe wayar, da sauri ta kaiwa zainab wayarta, “har kun gama?

Eh mami mun gama.” ta fice cike da kunyarta, tana isa daki tayi zaune tana tunani, hafsat ta matso kusa da ita, “ya akayine ‘yar uwa? Hawaye ne ya cika a fuskarta, wai kinji uncle, wai in shirya mutafi kaduna gobe, anya uncle yana da hankali? Hafsat dariya ta saki sosai harda hawaye.

Ita kuma kuka ta saka mata dama tanada niyar yin hakan, dole hafsat ta daina dariyar ta soma lallashi, “ke wasa fa yake miki danya gano weakpint dinki ne shine yake tsokanarki.

“da gaske?

“ni inda uncle yake bala’in burgeni uwani, shi yana bala’in iya soyayya, don Allah fadamin dayake, kissing dinki da dazu me kikaji?

Uwani ta marairaive fuskarta, “haba hafsat wannan shi ake kira soyayya? Na dole fa yayi min, me kike tsammani zanji, tunda baso nakeyi ba.

“keadai fadi gaskiya ‘yar uwa.” duka ta kai mata ta kauce, nifa bana son wannan hirar, ta kwanta, hafsat ta dameta da surutunta, karshe ta kyaleta.

Washe gari tunda safe jafar ya shigo gidan, ya fadawa zainab bukatarsa nason tafiya da uwani, anya haka zai faru jafaru?

Kai wai miyasa bakada hakuri ne wai?

Haba yaya kinsan fa nayi hakuri, munkai wata kusan takwas fa da aure yaya, kuma ai yaya ba wani abu zanyi mata ba.”

“hum dama nasan halinka jafaru, kaifa in kana son abu ka iya naci, toh ai saikayi mata magana inta yadda toh kasan ni ba ruwana, kaida inna ne inta ji labari.”

“don Allah kisa baki yaya.”

“kwana nawa zata yi?

Kwana uku.” ajiyar zuciya tayi, “nidai na fadama babu ruwana idan inna taji.”

na yadda yaya yimin magana da ita, inaso mu wuce da wuri, kada rana yayi min, inada evening ne a yau din nan.” a kicin ta samesu suna fere dankali, uwani jafar na magana yana falo, dama hijabi ne a jikinta, dan haka ai tsaye falo ta nufa.

Idonsa a kanta, tadan russuna, ucle ina kwana?

“lafiya. Ya fada, kin shirya mu wuce?” yayi saurin tambayarta cike da isa, miyau ta hadiye da sauri, “ina zamu? Ta fadi hakan cike da tashin hankalin.

“bana ce ki shirya kaduna zamu ba? Nan da nan hawaye ya soma zubo mata, uncle kayi hakuri, amma bazani ba wallahi.”

“nima kiyi hakuri, amma ina bukatar matata, wai bazaki tausaya minba ne? Kinsan hakkin da ke kanki kuwa?

Kin san irin zunubin da kike kwasa kuwa? (Kuji fa shi bai duba nashi zunubin ba yana duban na wani lolz)

kuka ta keyi sosai, tana magiyar ita bazata ba, data lura hakan bazai fisheta ba, saita ce, “toh da kake fadan wani hakki, ai na sha fada maka, niba zan iya dakaiba kafi karfi na, sannan ai na fada maka bana sonka!”

dariya ya saki, wanda ke cike da nuna kasaita, baki sona? To wa kike so? Da sauri tace “hamza!!.

Waye kuma hamza? Baka sanshiba, amma kowa yasan shi, kuma kowa yasan irin soyayyar da mukeyi dashi.”

kina nufi harda auren naki kina tadi da wani? Tambayar ta fado mata a bazata, ta kuma ga bacin ransa a fili, dan haka ta nemi kara masa bacin ran, saita danyi murmushin karfin hali, tana dubansa tace “eh! Mana ai inna tace raba auren nan zatayi.” bata ankara ba, saiji tayi ya rike mata bakinta da yatsan sa biyu, dan tsabagen zafi bata san sanda gwiwarta suka kai kasa ba, “ni kike fadawa magana?

Hawaye kawai ke ambaliya a fuskarta, yaci gaba, “na fada miki dole ne ki soni yadda nake sonki, sannan dole ne zama dani, ban hana in na mutu ba, sannan da kike bugun gaba da cewa, inna zata raba aurena dake, hala igiyar a hannunta yake?

Zainab ta shigo falon, tana fadin “subhanallahi jafaru so kake kaji mata ciwo? Wai meyasa kake son gwada mata karfine? Da sauri ya saketa, ita kuma kuka takeyi sosai, nan da nan bakinta yayi sumbul ya kumbura, zainab ta rungumeta, toh gaskiya tunda haka ne, na fasa baka ita, nasan inba ma kusa abunda zakayi mata saiya fi wannan.”

“yaya bakiji irin bakaken maganan data ke fadamin bane.”

“amma shine zaka ji mata ciwo? Ran mami ya baci, ya lura da hakan, “toh yaya ayi hakuri, amma ai ita taja ma kanta.”

haka ma zakace ko? So kake gobe na nemi alfarma gun inna taki kenan ka kyauta” ta riko hannun uwani datayi kuka harta galabaita, zo muje na fasa bada aron naki.”

da sauri ya mike daga zaman da yake yi, yaya kada kiyi min haka, kin riga da kinsa min rai.”

toh ka cire ran dan ba yadda za ayi in baka ita kaje kaji mata ciwo akan banza, aiyin soja ba hauka bane,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *