KALLON KITSE CHAPTER 2
Www.bankinhausanovels.com.ng
bata daina dukan yaran mutane ba, harda cizo takeyi. Mal. Mamman yayi dariya, inna zata daina, yarinta ke damunta, amma kam Aisha akwai ta da fada, shiyasa nake sonta, saboda tsiwanta, ga iya lafazi kamar wata babba, koda yake tana tare da manya dole ta iya, yaci gaba, dama inna wata magana ce ta kawoni, mai muhimmanci, don Allah inna dama…..dama indo ce nake so, amma sam taki amince min, yanzu haka satina uku kenan ban sata a ido ba, nayi da ita ta fadamin dalilinta, amma taki shine nace bara na biyo ta wurinki, kila ta amince. Inna ta gyara zama sosai, ta kara gyarawa uwani kwanciya, dan tuni tayi barci, akafan innar, toh mal. Mamman gaskiya ne, kuma haka yayi kyau, in Allah ya yarda zanyi mata magana, kuma zan nemeka. Allah yasa Alheri a wannan batu, Allah kuma yasa damu za’ayi ameen.
Bayan tafiyarsa inna har daki tabi indo, indo tace ita bawai auren ne bata soba, ita bata so ta bar gidan, inna tace, wannan mai sauki ne, saiku zauna a boys quater, tunda ba kowa anan. Ahaka inna ta kwantar wa da indo hankali, har ta amince da maganan auren mal. Mamman.
Washe gari ta nemi mal. Mamman ta fada masa yadda sukayi, yaji dadi sosai dan dama gida haya yake zama, yanzu ya huta da biya, yayi godiya yace, saita taimaka ta tambayeta yadda takeso ayi, dan gaskiya inaso a daura kafin azumi. Inna tace hakane, yau fa saura kwana goma sha bakwai a fara, dan hka ninasa ranar nanda sati biyu, mal. Mamman ya washe baki yana godiya, inna ta kara da cewa kaje ka duba dakunan, ga makulli, Allah yasa an dace. Ya amsa yana godiya.
Abu anyi shi a saukake, dan haka komai yayi sha’awa, indo ta tare a dakinta, harma inna ta bata kyautan set din kujeru da gado, komai yayi acan-acan.
Jafar ana saura kwana biyu a zumi ya dawo gida, ba wacce ya sawa ido irin uwani, saboda acewarsa ta cika shagwaba, komai tayi, sai ya kusheta, tun da tazo gidan yau watanta kusan bakwai, amma bata daina kazanta ba, makaranta kuwa tana dai nata kokarin amma ba sosai ba, shiyasa yake yawan tsawata mata.
Ita kuwa data lura da hakan, indai tasan yana gida saita gudu can sashen indo, tayi zamanta.
Azumi na saura kwana daya ya kare jibi sallah, salaha da ‘ya’yanta suka dira sokoto, dama tuni mal. Mamman yaje ya tarbesu, ana sallar azahar suna shigowa, inna tasa indo ta shirya abinci kala biyu, ga fura kuma da sinasir, don haka yaran sunji dadi kwarai don suna son irin hurar inna. Salaha tace gaskiya inna kinyi dacen yarinya, ta maidake uwa.
Inna tace kinsan dama tun can ‘yar shagwaba ce shiyasa, hafsat da uwani da yake suna sa’annan juna, nan da nan suka shaku da junan su, suna wasa.
Washe gari zainab ma ta ison gidan tare da ‘ya’yanta baki dayan su, da yake shima mijn ya gina gida musamman saboda insun zo su zauna, shiyasa basu barin kowa. Alokancin ne suka hadu su uku ina nfin uwani, hafsat, da kuma fa’iza, duk da duk sun girmeta amma tafisu baki, ga tsiwa, amma ba karfi. Inda uwani ke sa’an cinzali shine, saboda tsiwarta, dolene ako da yaushe sai su rinka fada da hafsat dan itama ba kyalle bace, har gwara fa’iza dako tsokananta kayi ba ruwanta.
Ranar sallah bayan andawo idi, jafar ya shigo gidan, nan da nan yara sukaje gunsa suna fadin uncle barka da sallah. Saida ya bawa kowa, amma banda uwani, idonta yayi rau-rau zatayi kuka, ya daka mata tsawa, in kikayi min kuka saina gurje bakin nan naki. Salaha tace “haba jafaru ya zaka bawa kowa nasa banda ita, kuma kace kar tayi kuka? Inna tace ‘eh ai gara kitayani fadi, in gaya miki auta sam baison diyar nan tawa, zo uwani ki karba, ya shiga ya zauna tare, da fadin salaha don Allah dubi yarinyar nan kazamiyace wallahi, ki duba kiga hafsat da fa’iza anyi musu kitso, sannan kayan jikinsu komai tsab, ita fa? Dubeta kanta babu kitson kwarai sannan ta cire zaninta ta yar, dubi fuskarta ki gani, duk majina ina zan bata barka da sallah?
Inna tace babu ruwanka da ita, haka kawai yarinya karama batada ikon sakewa itada gidansu, kaidai sonkai kake nunawa, toh ta Allah ba takaba, ni wallahi na matsu ka koma makaranta mu huta, tunda kadawo ka ishemu da masifa, ko an gayama bana lura da yadda duk ka takura mata?
Salaha tace. Kaiko jafar ka bawa kanka lafiya, kaima kasan sai a hankali uwani zata daina behaving haka.
“kinsan Allah salaha, wannan yarinyar bazata dainaba, ai kazanta halittace…”
“bari kaga irin yaran nan sunfi kowa kwalliya insuka girma, yarinta ne ke damunta.
Ya mike tsaye yana fadin toh haka dai kukace , ai muna nan zamu gani.
Lokacin zainab ta shigo, uwani ta ruga aguje tanayi mata oyoyo aunty. Aiko saita fadi kasa, jafar da karfi yace Allah ya kara. Inna da sauri ta mike tunkan salaha takai harta dauko ta, da yake inna jikinta mai iri kyan nan ne, bazaka taba yarda takai hamsin da biyar ba, don kyan jikinta, batada kiba dai-dai take. Wurga wa jafar harara, batace komaiba, amma ta rungume uwani ta lallashi, shikuwa jafar mikewa yayi dan yasan ya batawa inna rai, ya fito waje yaci karo dasu bashir………..yadan saki ransa suna gaisawa, bashir ya dubeshi yace, yaya dai?
“mts…
Mtssss, wannan wanne irin abune kayi mana tsaki?
“wallahi yarinyar nan ce da nake baku labari,
shagwabarta sai karuwa takeyi, ni wallahi duk ta fice min a rai.
Safwan yace toh me ruwanka kaima da ita?
“ka gane yarinyar kazamiyace, sannan sam! Inna bata so taga haka, idonta ya rufe da son yariyar dayawa.
Toh kodai kishinta kakeyi, ta maye maka wurin, ai kaima haka kasan haka kake kai da har yanzu baka daina rumgume inna ba, saikace karamin yaro? Inji bashir.
“kasan Allah bata isa inyi kishi da itaba, danni nasan na fita a gun inna. Safwan ya girgiza kai yace “shiyasa a koda yaushe in ankiraka yaro ka rika jin haushi, yanzu dai kishin yarinyar ka keyi?.
Duka ya kaiwa safwan, suna dariya, “dan Allah kudaina fadan haka, kar wani yaji yayi min dariya.
Ahaka suke tafiya har suka kai inda zasu, wai gun budurwar safwan za a, sunyi sallama cike da yanga harira ta fito, ta gaidasu. Bashir kadai ya amsa jafar kam ko kallo bata ishe shiba, saida suka basu wuri shida bashir, yace kaiwai meyasa kakeyin hakane, duk sanda mukazo gun harirat sai ka nuna mata tsana a fili?
“na fadawa safwan ya rabu da yarinyar nan yaki, yarinya ba shape ba komai don Allah dubi yanda tabar kirjinta waje, sannan ta wani turosu, saikace dama tana dashi, gata nan sambal ba gaba ba baya, sai uban yanga, ni kasan bana son mace irin wannan, nafi son bul-bul, wadanda suka cika sosai…….
“kai jafar baka da dama.
“Allah kuwa abokina gaskiya na fada, me zaka shafa ajikin wacan yarinyar kaji, komai kyame, kamar sanda.
Bashir ya kwashe da dariya, kai nima fa bana son irin haka, saikaga wata dan tsabagen rashin shape saita tumbure….. .”
safwan ya katse masu hirar su daya bude motar ya shiga.
“wai dan Allah safwan da gaske auren yarinyar nan zakayi? Yayi ajiyar zuciya, toh gani nan dai, amma fa ta fara fita raina, har dai yau, yarinyar so tke wai….in….mts. Manta kawai ni nama fasa, ni wallahi nafasa.
“a’ah kar ka haukace mana, metace dakai?
“wai kasan ‘yar iskar yarinyar nan cemin tayi wai ni wane irin masoyi ne da ban iya soyayya ba? Kun san ma’anarta? Bana smoshing dinta irin su hug dinnan, can you believe that, matar da kake so ka aura ta nuna maitar ta afili, tun kafin ayi aure? Jafar dariya yasaka masa sosai, dan har ya tsuko yakai dundu, “dan iska, mahaukaci ka maidani kakemin dariya? Sai ka manta da wannan dama bata da komai sai yanga, banza gata ba gaba ba baya, abunda nagama fadawa bashir kenan, kaga ka hakura da neman auren nan, ka gama karatu tukunna.
“gaskiyane amma ai insha Allahu next year zamuyi graduating ba gara mutum ya samuba, kafin lokacin, shege ka manta saika kara almost one-helf year kafinan
ka zama cikekken likita bayan wanda zakayi yanzu.
Toh Allah ya nuna mana lokacin, (ameen)
haka rayuwa ta ci gaba da tafiya gashi uwani ta shiga aji daya na primary, da yake makarantar babu nusery 3, shi kuwa jafar ya zama cikaken likita, murna biyu agun inna, saika ga yadda take washe baki, ranar da taje ‘speach & prize given day’ na uwani an bata kyauta a ‘punctuality’ wato mai zuwa makaranta da wuri. Inna ta gyarata a ranar sosai, don ribon ta saka mata, tayi kyau sosai, su jafar suna abuja zasu zana jarabawa na gwajin zama cikakken likita, anan ne ya hadu da wani tsohon abokinsa, wanda sukayi secondary school tare, soja ne, ana ce masa captain lawal. Shigar da yayi shiya burge jafar, shikenan yaji shifa dolene yayi soja, kota halin kaka. Da yake mahaifin lawal mahmud tsohon soja ne, tare sukaje suka sameshi, dan su nemi shawararsa.
Mahmud usman tsohon soja da yayi mulki ta fanni iri-iri, yaji dadi kwarai da gaske, ya kuma kara nuna masa muhimmacin yin hakan, yace yaro gaskiya in zaka daure ana bukatan irin ku sosai ma,
saboda kana da digiri, sannan cikakken doctor, Allah yayi muku albarka, irin haka akeso, ai Allah ya taimaka, insha Allahu zan taimaka kayi sa’a N.D.A suna sayar da form, sai zasu rubuta jarabawar, saikuje ku siyo,za a taimaka.”
bai koma kebbi ba, saida yayi sati, don ya sami iri abokin da ra’ayin su ya zama daya, wato na mata.
Form din N.D.A kuwa sun saya har sun cika, sun maida.
Inna na zaune suna kallon film din hausa, ana waka, uwani ta mike sai rawa takeyi, ita kuwa inna harda yi mata tafi tana juyawa, sai sallamar jafar sukaji daga sama. Uwanikam taci gaba da rawarta, ya shiga saida ya zauna gab da inna ya dauki remote ya rage karan T.V din, sai a lokacin uwani ta nemi wuri ta zauna a jikin inna.
Yadaga murya sosai yace ke tashi daga gurin nan. Inna ta harare shi, kai bana son haka fa, daga shigowarka zaka soma ko? Ta zauna din kafarka ce?.+
Kenya mi lari yimbe don nyama yam hande wala fulfulde nah? Toh hande miwadi tainna kina bata yarinyar nan da yawa, shiyasa take iskanci data ga dama. Ta buge masa kafa tace “nafadama ba ruwanka da yarinyar nan tunda bakai takeyiwa ba, ya kalli uwani data shige jikin inna tana kallonsa, ya hade fuska tare da harararta.
Da sauri ta rufe idonta, sai a lokacin ya soma gaida inna.
Inna tace bana amsawa, tunda shigowa kayi, kasani gaba kana yimin fada, saikace ‘yarka.
Haba inna dan na fadi gaskiya?
Toh ayi hakuri ni albishir nazo miki dashi. Tayi fara’a tana duban shi.
Inna na sayi form na N.D.A a kaduna, makarantar sojoji zanje inyi.
Ta bata fuska auta makarntar sojoji kace?
Hakane inna kuma insha Allahu zan samu, dan ta hanyar wani tsohon soja mahaifin lawal abokina zai taimaka min…..”
kayi min shiru dan Allah ya maganar zamanka doctor? Inna ai wannan ba matsala bace, ina nan a matsayin likita, zanjene kawai na samu cos da trainina na sojoji, shikenan fa. Don Allah inna ki amince min, saboda inada ra’ayin zama likita, kuma soja.
Inna tace toh ni bazan hanaka ba dan yanada kyau yin hakan, amma jafaru shekara nawa zakayi?
Haba inna wane irin shekara? Wata tara ne fa zanyi.
Ta tsura masa ido nadan wani lokaci, sannan ta kara ajiyar zuciya, toh jafaru aure fa?. Yayi murmushi,
inna dama nasan abunda zai dameki kenan, amma inna ‘am still young shekarata fa ashrin da bakwai, yanzu bama cika ba. Zanyi aure inna ‘don’t worry’ da akwai sauran lokaci.
Toh Allah sa albarka auta, ya kuma kare min kai, yaushe zaka tafi? Saimun rubuta jarabawacikin watan, sai sunan ya fito a list, sannan zansa ranar tafiya, Allah ya nuna mana ya kuma bada sa’a.
Amin inna haka nake so ki karayi min addu’a, ta harareshi. Dama kasan kullum muna cikin addu’ar.
Indo ce ta shigo falon a’a saukar yaushe kato? Yayi murmushi da har hakoransa suka fito, wato indo bazaki daina kina da wannan suna bako? Kin san zan zama soja? Tayi dariy ba’a dai kake, wane irin soja kuma?
Allah zanjje N.D.A Insha Allahu.
“toh fa aure fa? Ka isa aure fa? Zanyi amma ba yanzu ba.
Indo tayi jim sannan tace Allah bada sa’a.
Ya fadada murmushinsa, “waiku da mutum ya taso sai afara maganar aure? Tayi dariya inda kauye kake, daka ajiye mata uku,
yace keni bana ra’ayin mata biyu balle uku, soja fa nace miki zan zama, cikekken soja kuwa mata daya yakeyi.
Dalla can inda bamu san inda gugar zanar takeba, sojoji nawa keda mata, har hudu ma?. Ya mike nidai daya zanyi. Ina kuma zaka abincin fa?
“yanzu zan dawo zan shiga gidan su safwan ne”
toh a dawo lfy, inna kinji jafaru inda yasa kai kuma? “bakiga nayi shiru ba? Halin sak! Dana mahaifinshi, shima in gaya miki ra’ayinsa daban yake dana mutane, akwai lokacin da ‘yan uwansa suka sashi gaba, wai sai yayi aure, da yake mun dade muna haihuwa yaran basa zama, dakyar zainab ta fara tsayawa, sai dai ya sake aure shi kuwa yayi musu mirsisi yaki yayi auren nan.
“hakane fa toh Allah bai daura masu sonyin auren bane, amma fa anya jafaru zai iya dauriyar mahaifinsa?
Toh zamu gani, Allah ya nuna mana, ke uwani tashi kidauko abinci kici. Indo tace nasan shigowar jafar yasa tayi shiru kamar bata dakin, shine kadai maganin rashin jinki.
“kai indo yanzu har wani rashin jine da uwani?
Inda shatu tana nan data baki labarin na jafar, dan ita tasan shi kamar yunwan cikinta.
“ai fa kam, koda bansan na yarintarsa ba, shima din akwai rigima.
Da result ya fito jafar ya zama cikekken likita, zai iya aiki a kowane asibiti, da yake shi likitan mata ne wato ‘Garnicoligist’. Inna kam farin ciki sosai tayi shi, ya soma neman aiki anan babban asibitin kebbi da wata private ‘godiya specialist hospital.’
a private din aka daukeshi, da yake shikam yanada kwazo, cikin lokaci kankani jama’a suka fara son aikinsa, hatta ma asibitin yaga canji, cikin ‘yan kwanakin nan daya zo asibitin. Sam baya wasa da aikinsa, lokacin aiki, aiki ne sai da daddare ne daga wannan sai gaiya ce shi party sai ranar da ba aiki, saiya wuce sokoto dan acewarsa matan sokoto sunfi wayewa.
*** *** ****
suna tare su dukansu, sun hadu a sokoto, safwan shikam anan sokoton yasami aiki, shikuma bashir a lagos yasamu, yana aiki awani kamfanin kawunsa. Bashir yace ni kana bani mamaki wani irin soja kuma? Bayan ka gama wahalan zama cikakken likita wurin shekara takwas, ka kwashe, shine yanzu kuma zaka kwa-kwalowa kanka sabon aiki?. Safwan ya shafa gashin kansa yace shifa na gani?
“ku bazaku gane, na riga na rubuta exams din anan N.D.A, ku kam is just for nine months, aiba wani da dewa zanyi ba.
Toh Allah ya taimaka (amin),
“inaso ma in fada muku nifa aure zanyi”. Inji safwan, kai dan Allah yaushe” gara ka bude mana kofa dan nima inaso inyi.” inji bashir.
“eh toh zai iya kai mext year zanyi”
“ashe zan rigaka, saboda ni na gida zanyi, “yar kawuna zan aura, anaso nanda wata biyar, jafar ya kalle shi kace dai zaba maka ita akayi?shine nace zaba maka akayi?
“wallahi ni kasan yare nake so, amma ya zanyi tunda mama tasa baki, sai kuma dan yarinyar tayi minne.
“shege ina fata kayi bankwana da shashanci, dan aure ba abun wasa bane.
“i will try and stop, amma kasan is not that easy”
“dama nasani, gashi dama ka koma lagos, kayi barna da hujja,
“a’a zan daina insha Allahu, suka kwashe da dariya, safwan yace, “da yake fadane abaki, akwai sauki. Amma dai baikai zuci ba.
Adai-dai wannan lokaci wayarsa ta soma ringing, yayi saurin dauka, “ya lawal kana lafiya? Daga can lawal ke fada masa jarabawarsa ta fito sunansa ya fito a list, jafar baisan lokacin da ya yar da wayan ba yana “yes-yes, Allah na gode maka, na samu school din abokai. Yasake daukar wayar, ina! Ta tsinke ya nemi lawal din, toh captain yaushe zan zo kenan? Saika taso next weak, saboda nan da nan za a fara training, the time is going.
“hakane, toh sai mun hadu. Ya dubi abokansa,
abokan zan wuce, dole inje in fara shiri, dama so nake na wuce jibi in Allah ya yarda.
Toh Allah kiyaye hanya sai munyi waya kenan?
“good luck, thanks. Yafada. Ya fita daga dakin. Bai jira komaiba ya wuce birni kebbi, ya fadawa inna, sunyi murna kwarai da gaske, ranar alhamis din kuwa ya wuce.
**** **** *****
a yau an wayi gari uwani tana aji uku na primary a lokacin jafar har ya zama second leauternal ya zama dai cikekken soja, abun gwanin sha’awa gashi cikekken likita ga shikuma soja dan haka jafar yake ji da kansa, yanzu haka a wari yake aiki da yake akwai sabbin sojoji a can, yana daga cikin layin wadanda akeji dasu, ya sami watanni a can, tun inna na damuwa harta barwa Allah, kudi kuwa tuni jafar ya samu, don yanzu haka gida aka bashi a can, akwai dan course din da zaiyi acan din kafin abashi captain yana tare da abokinsa lawal acan yasami wata yarinya ‘yar maiduguri wai ita zai aura, shikam lawal ba ruwansa dama shi rayuwarsa ta turawa ce, bai cika shiga harkar da ba tashi ba, akwai wani hutu na sati da ya samu ya tafi kebbi.
Ya samu uwani tana primary 4 headmastern makarantarsu ya bada shawaran abarta ta rubuta jarabawa na zuwa J.S 1.
inna sai murna take jafar dai baice komaiba, yana dai saurare, sai bayan isha’i, suna zaune yana cin abinci, inna tace, wai auta ina maganar da mukayi da kai ne?
“inna nifa yarinyar bata yimin ba.
Shin wai meke da munka dan nan, anya lafiya kalau? Kana neman shekaea talatin da biyar, amma ko tunanin aure bakayi?
“kai inna kidaina karamin shekaru iyaka fa talatin da uku….” ta katse shi, dan Allah gara can, kullum akayi magana saikace kai yaro ne, toh kada Allah yasa kayi auren, nikam bazan sake yi maka magana ba, kaje kayi abinda kaga dama, duk abokanka sunyi aure, yanzu kaida bakinka kacemin ‘ya’yan bashir biyu, safwan kuwa daya, wai me kake so ka maida kanka ne, kullum aka hada da yarinya sai kace batayi maka ba?
Ni wallahi na gaji da irin abunda ka keyi…..”
ya rike hanunta dole ta daina fadan ta dube shi, “inna zanyi aure kwanan nan, na sami matar da zan aura.” ta harare shi haka kace wancan zuwan ma da kayi, amma har yanzu shiru.
“inna abun da ya kawoni kenan, inaso aje a nema min auren yarinyar, inna ta washe baki yauwa ko kaifa auta, a ina take haka?
“uhm…uhm…’yar can warri ce, saidai su ‘yan asalin maiduguri ne, shuwa arab ce….”
eye? auta nikam banason irin auren nan na nesa….,” ya katseta inna aidai nanda maidu guri ba wani nisa….” itama ta tsinke shi, kai nifa nace ma bazan yarda da irin wannan auren ba, gaskiya haka kawai nan kebbi zuwa katsina ka rasa yarinyar da zaka aura sai ‘yar maiduguri, duk yanda aka bada labarin tsafinsu?
“ai inna ba duka a taru aka zama daya ba, don Allah inna kidaina fadin haka.
“eh gaskiya ne, indaina fadin gaskiya dan kana son tayar mana da hankali.
“a’a inna ba haka bane, nidai inna ban yarda da asiri ba, kinsan sai inka yarda da abu zai zama gaskiya, agareka. Allah kuwa inna ba wani matsafa bama a can iyayenta sukeba, anan warri suke baki dayansu.
Inna kam taki ta saurara masa tace sam bata yarda ba, haka kawai taji auren bai kwanta mata ba, haka suka rabu ya kasa shawo kanta.
Dakinsa ya wuce, ya rasa abunda keyi masa dadi a duniya. Shikam inba marliya ba, toh bazaiyi aure ba kenan. Adaren ko abinci yaki dauka, har saida indo ta tura uwani takai masa. Tayi sallama bataji ya amsa mata ba, saita ci gaba da kwada sallamar ya shaka ya bude labule da karfi, saida ta firgita yace cikeda masifa, ke wai meke damunki, kinyi sallama ba a amsa ba basai ki koma ba, ko baki san hakan ba? Tayi saurin juyawa zata koma, ya daka mata tsawa saida hanjin cikinta yayi rawa, saikace hantar cikinta zata fita, ta tsaya cak! Yace zonan. Ta ware idanun nan nata farare tas, ta soma tagiya a hankali, ta iso kusa da kofar, sai kuma ta tsaya, ya harare ta zaki kawo min abincin ko kuwa, da wasu idanuwa kamar na mujiya” ita dai idonta tasa akasa, ta isa ta shiga ta ajiye akan center table din dakin. Zata fice taji yakai mata ran kwashi akai, saida hantar cikinta ta kada.