KALLON KITSE CHAPTER 5

KALLON KITSE CHAPTER 5

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Haba yaya ya zakice haka? Kinsan yanda nake son marliya kuwa? Wallahi bazanyi aure ba in har kuka hanani aure marliya.

Salaha tayi tsaki, mts! Kai har so ka sani? Bayan ance ma mutanen nan ba ‘yan mutunci bane?. Kuka ya saki, baiji bai gani, nan da nan jikinsu yayi sanyi, tare suka hada baki, “kai hakuri mun daina, kaje ka aurenta, amma ashe soja na kuka? Ko ko shagwaba ce ta tashi? Toh inna bata nan, dan haka akama kai”.

Ya kirne fuska, “ni wallahi dama nine babba, komai sai a danne ni ace nine karami.

“eh mana ko kai ba karami bane? Amma ai sai taurin kai da Allah yayi ma, toh Allah yasa ayi lafiya.

Ya washe baki, nagode dan Allah karku fadawa inna.

“um bazamu fada ba, amma kasani komai daren-dadewa gaskiy zata bayyana, mudai ‘yan kallo ne”

nagode bari inje in sayo muku abinci tunda kunce yunwa kukeji.

“daka kyauta, ka siyo mana amala ma ya ishemu, da sauri ya fice, su kuwa sai tausaya masa sukeyi.

Haka akata shirye-shiryen aure, har gashi gobe daurin aure, a ranar uwani suka iso tare da iyayensu zainab. Washe gari aka daura aure, har a wannan rana basusa ido kan amaryarsu ba, saida yamma akace, a shirya aje akwai wani wasa da za ayi.

Da suka isa ko kallo basu ishi mutane ba, suka sami wuri suka zauna, dan sun san baza a basuba.

Suna zaune akazo aka wuce da amarya, abun mamaki basu yadda da hakanba, har saida suka kalla an bata fili tana wata irin rawa kamar maciji, shikuwa gogan yanata tare ta dan karta fadi, wai inta fadi za’a ci shi tara.

Iya kuwa su goggo ansha kallo, kayan abinci saidai sukaga an wuce dashi, badai abasu ba, harma sun saba, dan haka zasu zo da ruwan shansu a mota, tun suna fadawa jafaru, har suka sa idonsu ayima su tafi gida, dan sun gaji. Su uwani kam abun yabasu sha’awa, itada su hafsat, tunda su ina ruwansu, basu san maabunda ke faruwa ba, dan alokacin sunada shekaru goma sha daya da sauransu.

Sai karfe sha biyu suka bar wurin, suka koma gida, kowa da abinda ke ransa. Suna sauka suka soma bayanin abinda ke cikin zuciyarsu, goggo tace “anya yarinyar nan bata girme ma jafar ba? Zainab tace, “kedai bari goggo, ai wannan ba yarinya bace, daga ganinta takai shekara arba’in, wallahi tayi sa’a da salaha.

Salaha tace, “anya bata girme ni ba?.

Suka kwashe da dariya, tun abun na basu haushi, har ya soma basu dariya, wannan dare basu kwanta ba sai hira sukeyi, dan haka yasa sukai kusan makara.

Tun da safe suka shirya, suna jiran mota, dan mota uku ta wuce irin su goggo da jirgi zasu, dansu zasu karbi amaryarsu.

Da kyar da sudin goshi aka basu ita, shima saida sukace, sukam in baza a basu ba zasu wuce, dan bazasu kara kwana a wannan garin ba.

Karfe biyar ta wuce suka isa sokoto, dama mutane na jiransu, dan haka karfe bakwai suna gidan inna.

Abunda inna ta gani a idon yarinyar nan jikinta yayi sanyi, dan tasan ba karamin gamo danta yayi ba.

Ajiyar zuciya ta rinkayi, dan abun ya tayar mata da hankali matuka, duk da ta nemi ta boye da muwarta, amma saida ‘ya’yanta suka gane, janta sukayi zuwa shashen indo, batasan sanda hawaye suka fito mataba, zainab ce ta gani itama saita soma kukan.

Salaha itake bada hakuri.

Inna tace, “shine baku bugo kuka fadamin ba?. Sai a lokacin suka kwashe komai suka fada mata. “toh shikenan tunda haka ya zabarwa kansa, Allah ya kare shi daga sharrinsu, ya kuma bada zuri’a daiyiba.”

Amin, suka ce baki dayansu. A lokacin sukaji sallamar jafar din, sai sukai sauri sakin fuskarsu, ya shigo ya isa, ya rungume inna yace, “inna nayi missing dinki.”. Ta tallabo fuskarsa, “kana cin abinci kuwa auta?.

Ya hadiye miyau da karfi yace, “rabona da abinci inna, har na manta.

“haba jafar so kake kayiwa kanka lahani?

Salaha ma za dauko abinci, ga makulli, zaki ganshi na shiryashi daban-daban, na kune nace a ajeshi daban, inasu uwani? Na gansu yanzu suka iso, Allah na gode maka, Allah shiyi muku albarka.

“Amin. Suka amsa baki dayansu.

Haka amarya ta tare a wani gida na Alh. Yunusa, daya ce a ara masa su dan zauna, da yake guest house ne, komai akwai aciki, dan haka basu da matsala.

Da daddare akayi dinner inka gansu wurin sun sha kwalliya da dinkin wani bakin lace, da zainab ta dinka musu, su uku tace, sune ‘yan matan dake tasowa, sunyi kyau sosai sai kace ‘yan uku , duk inda suke toh tare zaka gansu, dama gasu gwanayen rawa, sunyi rawa sosai, kamar bazasu dainaba. Ali jita aka kira dan haka ranan ba karamin naira aka saki ba, ba a tashiba, sai karfe dayan dare.

Amarya na daki, abokai sukayi ta barkwanci, basu tafi ba saida wajajen karfe biyun dare.

Amarya kuma ko digon kwalla babu a idonta, tana tare da jamila tace, “mikomin hodar nan, dan anzo da ita.” ta mike ta nufi bandaki tasa dan ruwa aciki, sannan ta matsa, wai inji bokan laya ce, zaijita tamkar wadda ba a taba saduwa da itaba, wato budurwa daga leda, tayi murmushi tace “jafar na kamaka sai abunda nace shine zai zama dole, dole in rabaka da duk wanda zai rabani dakai.” ta fito tace da jamila, ta wuce hakan zasu hadu gobe .Tana tsakiyar gado night gount ce ajikinta, duk ilahirin jikinta awaje, dataji shigowarsa saita mike zaune, tana murmushi. Shima murmushin yakeyi, ya isa gunta, ya zauna, “amarya kinsha kamshi, ya ya hidima? Ta wangale baki tana murmushi. Wani dadi yaji ya buge hancinsa, baisan komeye bane, bai kuma ya isa ya tamaya ba, dan yana tsoro kada a hanashi abunda yayi niyya. Ya shafa gefen fuskarta, “zo muje muyi alwala, muyi sallah, ko kinyi isha?

Kwanciya tayi tana shagwaba. Shikam ya mike ya shiga toilet yayi wanka tareda alwalla yazo yayi sallah, sannan yafita ya dauko leda, kaji ne aciki da madara mai sanyi, ya dauko plate ya juye. Ai tana ganin kaza ta mike zaune, ta dawo kasa, yace dama bakiyi barci ba?. Ta rangada ido, tace ina naga barci wannan yunwa da nakeji? suka ci, suka sha, sai da sukayi dam, sun hau gado, a yau yayi mamakin marliya yanda ta kauda kunya baki daya ta rinka nuna masa soyayya, abunda yafi bashi mamaki shine, yadda zata juya da namiji wurin kwanciya, indai dadi ne yaji kam, dan ya sami abunda yake nema, amma bashine da namiji na farko daya kasance da ita ba, har aka kira sallar asuba idonsa biyu, abun ya daure masa kai ya rasa abunda yakeyi masa dadi, yanzu dama marliya ba virging bace taketa nuke-nuke sai kace ta kirki?

Dayaje masallaci ya dawo ya isketa sai bacci takeyi, ya tunama jiya bata bari sukayi nafila ba suka kwanta, yadan janye zanin data rufa da shi, ta dube shi cike da takaici tace, “nifa ba a tadani daga barci, sai in ni na tashi da kaina!.

Abunda ya bashi mamaki kenan, baice mata komaiba, sai ya tsinci kansa dace mata Allah baki hakuri, dama na cene kitashi kiyi sallah.

Tace haba jafar bayan wahalar dani dakayi jiya? Takaici ne ya kara kamashi, ya bata wahala kodai ta bashi wahala? A fuskar sa sam bai nuna mata ranshi ya baciba, saima ya sami wuri ya zauna yace “haba dan Allah kiyi hakuri, ki tashi kiyi sallah mana, bakisan wasa da sallah ba kyau ba? Ta ware ido sosai tace, bazan iyayi yanzu ba, sai anjima.

Tashi yayi yana murmushi, “Allah yabawa gimbiya hakuri asha bacci lafiya.

Yasa kai ya fita kitchen ya shiga, ya hada tea mai kauri yana sha.

Daya gama sai ya dawo ya kwanta, abun mamaki ta shiga yi mishi susar kadangare, can ta shiga tube kaya, me zaiyi? Shima saiya fara maida martani. Wajajen karfe biyu saura, suka tashi shima kofa sukaji ana kwankwasa musu, da sauri ya mike ya shiga bandaki yayi wanka ya saka wata blue sky shadda, yayi kyau a idonta, ta rinka sumbatarsa, shikam abun yana bashi mamaki, ya akayi marliya ta iya irin wannan soyayyar? Ya fita ya bude kofar, su uwani ce da hafsat, ya hararesu, “ku haka akeyi, kuyi ta buga ma mutane kofa da karfi, zaku karya kofar ne?

Hafsat tace, “dama inna ce tace mu kawo abinci, yanzu zuwanmu na uku kenan, munzo tun safe baku bude ba.

Ya dubi uwani ke bakisan halina bane? Da ai saiki gaya mata, ba a buga kofa, ku aje abincin ku tafi, ba shikenan ba?

Daga can bayansu suka tsinkayi muryar marliya tana cewa, ” toh ai saika bari su shigo ciki ko?.

Ya basu hanya suka shiga, idon marliya akan uwani ta tsaya tace, “wannan kanwarka ce ko?.

Yadan dubeta kasa-kasa, “eh hakane ya akayi kika san haka?

“kuna kama.”

“wace kama?.

“yanayi da juna kukeyi.” yayi murmushi, “wancan itace hafsat ‘yata ce, ita ce ‘yar yaya zainab, ta biyun kin gane yaya zainab?

O.k na ganeta, nikam dan Allah dauko plate ka dibar mana abinci, dama yunwa nakeji.” da sauri ya shiga kitchen ya hada musu abinci, dankali da miya ne da kwai sai kayan tea.

Sun sami kamar sati biyu a kebbi shima suka takure don ta nuna masa ita bata son zaman wannan garin, yace da ita aiba nan zasu zaunaba, hutunsa kawai yake jira, tunda dama kaduna zai koma da zama. Da kyar sukayi sati uku, kamar ance gobe zasu wuce warri, da daddare sukaje yiwa inna bankwana, tunda sukaje yau ta fito, wai ita rana takeji, garin ya cika rana.

Ita kuma inna bata fasa sa abinci akai ba, koba komai tasan jafar na bukata.

Suna zaune bamai cewa komai, sai shi jafar din da yake ta shagwabarsa, ita kuwa gimbiyar ta juya musu baya, tana taunar cingam, tana kallon t.v, duk ta tsargu, har dai yadda ta gani a idon inna sam bata ra ayinta, a ranta tace, “nafiki iko da shi dai, kuma wannan zai zama na karshe keda ganin danki. Tayi murmushin mugunta.

Uwani ta kawo mata ruwa, tun kafin ta ajiye tace, “nifa bazan sha ruwa ba, ke maida.

Hatta jafar saida abin ya masa zafi, shidai baya ganin laifinta.

Daya lura zaman ba dadi, sai yace inna, zasu wuce.

Zumbur ta mike tana gun-guni, dama ta matsu su tafi, sai yayi kamar baiji ba, suka kama hanya suka fita.

Inna ajiyar zuciya tayi tace, “Allah wadarn naka ya lalace.” uwani ta shigo tace, “inna ke kadai kike magana?”.

“uhm ni kadai kuwa, waccan ‘yar barikin na kewa addu’a, Allah ya shiryeta.” uwani tace metayi makine?

“bazaki ganeba uwani, ke yarinya ce, Allah ya shiryeta, ya shiryamin ku baki dayanku amin”,

yau watansu uku da komawa kaduna, har an kara masa girma, ya kai matsayin captain, duk yadda kaga jafar naji da kansa,

Duk yadda kaga jafar naji da kansa, yana huci kamar kumurci, da yadda baya wasa da yaransa, inya shigo gida dole ya ajiye wannan abu gefe, zama yake tamkar karamin yaro a gaban marliya, idan yadawo aiki na wannan wunin toh bazai fita ba, ko emergency aka kirashi, da yake yana aiki anan 44 dake cikin garin kaduna, wani lokaci kuma suna zuwa jeji training, marliya bata aikin komai a gidan ‘yan aiki ne da ita su uku, kowacce da aikin data keyi, sai kuma cook da yake girkin abinci, hatta abinci bataci da kanta indai jafar yana gida, shike bata abaki, toh balle ta dauko masa abinda zaiyi amfani dashi, duk abunda ta keyi, shima baisan dalilin da yake yi mata shiba, amma abun na bala’in damunsa, ba yadda za ayi, kuma ya fadawa wani, a rayuwarsa bai taba tunanin zai bautawa ‘ya mace ba, shi abun ma ya daure masa kai, da in ya zauna a office tunani kawai ke damunsa, shi wai meke damunsa ne? Ya tambayi kansa, duk karfin halinsa da kuma jarumtakarsa, amma ace mace ke juya shi, yadda ranta keso, wai meke damunsa, shin wai so haukane? Ya kara tambayar kansa, duk abunda tace baya musawa, sai kace uwarshi, yanzu haka watansa biyar kenan rabonsa da kebbi, kullum saiya ta yiwa inna karya, aiki ne yayi masa yawa, koyayi shirin karya dokar marliya, sai yaji bai iyawa, duk yawanci fadansu bai wuce in yace zaije kebbi ba.

Duk bakar zuciya da aka sanshi dashi, saidai yayiwa na waje, amma badai marliya ba, duk abun duniya ya ishe shi, tun a wannan lokacin shi kanshi yasan ya canza, inya koma gida bayada hutu, shi yasan yana son mata, amma yau yaga wadda ta fishi, domin sai su kwana suna making love da marliya, amma bazai isheta ba,

shi abun har mamaki yake bashi, inda shiba soja bane, da yake cikin excrse ba da tuni ya rube.

Yau ya iso gida gabansa na faduwa, saboda jiya yace da ita a kebbi zaiyi weekend dinsa to batace komaiba, amma ya shirya yadda zai bullowa matsalar, ya shiga falo ya iske an shirya abinci akan tebur, ya duba ko ina amma baiji motsinta ba, daki ya shiga ya sameta kwance, wai batada lafiya, nan da nan hankalinsa ya tashi, ya isa bakin gadon datake kwance, ya tsugunna ya riko hanunta, “ya akayi ne sweety, na dawo kina kwance?

Ta ya tsina fuska tare da ture hanunsa, tun safe nake amai banjin dadin jikina, “dauko min abinci in dan ci.” ya mike da sauri ya nufi tebur din abinci,ya febo mata, ga mamakinsa ta cinye shi tas, ta dube shi tace “doctor, dama haka take kiranshi wataran, ya amsa sweety, dubani meke damuna?

Tayi kwance rashe-rashe, ya dan kalli idonta, ba abinda ke damunta, lafiyarta kalau, yayi jim yace, inaga stress ne ke damunki, amma ga fleden kisha, zaki sami sauki.”

ta karba ta rike, sai kuma ta wurga masa a jikinsa, tace “bazan shaba, kaje ka hadomin kazar danasa a gasamin tana cikin micro wave”.

Ya mike a sanyaye yaje ya dauko, cikin ransa abace yake yayi bakikirin, amma a zahiri fuskarsa babu alamun haka. Saida ya zauna ya bata ta cinye shi tas, sannan tace “ya aza mata ruwa tayi wanka. Daga karshe wankan ma shi yayi mata shi, ya shiryata, sannan ya sami kansa yace, “zaije yayi sallar mangariba”.

Yawanci saboda aikinta a gida yake sallah shidda, baya taba barin jam’in sallah ya wuce shi, amma yanzu ya zama gwani.

Abun mamaki sai gashi jafar yayi sallah a kaduna, abunda bai taba faruwa ba komai dare dole ya kasance da inna, tare suke farin cikinsu.

Anyi sallah da kwana salaha ta dira gidan jafar anan kaduna, daga kebbi take, tunda suka iso basuga marliya ba, kuma tana nan aciki, sam salaha batayi mamaki ba, saboda tasan haka zai faru.

Tun a kebbi take shirin abunda zata fadawa jafar na tsiya, amma abun mamaki data ganshi, saita kasa furya koda kalma dayane, yabi ya lalace, kamaninsa duk ya canza ta rasa da wacce kalma zata fara yi masa magana, ya dubeta sosai ya wangale baki, “yaya salaha”. Ya karaso yana dariya, yana cikin kaki (kayan sojoji) ya cire hular da yake kansa yana yi mata barka da zuwa.

Da kyar ta maida kwallar dake idonta ta amsa gaisuwarsa, sun danyi hira kadan, yana wasa da fa’iz dan salaha data haifa, inasu faisal, ba a zo dasu bane?.

Ta kalleshi murya shake “jafar baka tambayeni inna ba? Ya danyi shiru bai mata magana ba, amma yasan bazai iyaba, saboda kunyar salaha dayaji, “ai nasan tana nan lafiya yaya”.

Tamike toh bari in wuce, dama na biyo ne in gaidaka tunda kai kafi karfin hakan nan da abuja baki da hanci.” murmushi yayi kawai, baice komai ba, abun ya daure wa salaha kai, hatta dan barkwancin nan dayake tsakanin su baiyi mata ba, saida suka fita a falon take ce mishi, “anya lafiyarka kalau jafaru? Ya amsa cike da fara’a “llafiya lau yaya, me kika gani hala?. Ta juya kanta menene ma bangani ba, Allah ya sauwake.” yana kallo ta wuce bai iya cewa komaiba. Duk cikin zuciyarsa ba dada, yakeji.

Bayan ta wuce ya shigo gidan ya iske marliya tana tsaye, tana shan kamshi, da sauri ya isa gunta yanayi mata magana, “yana ga ranki a bace, me akayi maki sweety?.

Ya rike hanunta ta janye ta nemi wuri ta zauna, ta saki kuka,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *