KALLON KITSE CHAPTER 7

KALLON KITSE CHAPTER 7

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

inna gashi nikam na koshi, dazun nan naci abinci.”

“yauwa na tuna uwani akwai wani kaya da salaha, dauko in gani.” da sauri ta mike, suna ina inna? Ta tambaya, “suna cikin wadrope din kayan ki.” ta dauko, kayane kala uku shaddabiyu da lace daya a dunke suke, “uhm wannan dinkuna da salaha keyi muku kamar abunda za a sawa ‘yar tsana?.

“gaskiya inna dinkunan sunyi kyau, tasan irin wadanda nakeso, dama ni bana son manyan kaya.”

“eh mana, nasan kyace haka, kinfi so kisa kaya duk ilahirin suranki a fili ko?

“toh inna ba inasa abaya ba, in zan fita aibaki ganiba.”

“na lura da hakan, amma ai ba koda yaushe bane.

Inna yanzu fa su ake yayi, ko bakiso nima inyi yayi?

“inaso uwani amma a lura da kama kai, kinsan ita ‘ya mace anfi so a ganta da kamun kai sosai.”

tace, hakane inna, zan kula bari inje in gwada ko zasuyi min.” ta shiga daki, inna tabita da ido, a lokacin indo ta shigo.

Uwani ta shigo tana juyi, “inna ya kika gani? Inna ta tabe baki, sunyi kyau.” indo ta kalleta tana dariya, “wannan wane iri dinki ne kuma, ya matseki uwani, ke dan Allah yayi miki wannan cikan kirji haka, ina ke ina wadan nan kayan? Ki kai a buda maki su.” a shagwabe take magana, inna kin ganta ko?

Nidai haka nakeson kayana.”

nima dai haka nace wannan kaya kamar na….” uwani ta katseta da, inna ni dan Allah kudaina cewa haka.” ta rinka buga kafa a kasa cike da shagwaba, indo dariya ta rinkayi, “lalai duk wanda zai daukeki gun inna nan taki, saiya yi da gaske, shagwabar taki kullum karuwa ta ke.”

“inna kin ganta ko, babba batada magana saina a rabamu.”

ki kyaleta kinji ba inda zaki.

Habawa yarinya dole ki bar inna taki watarana.” haka zaman nasu yake a kullum gwanin sha’awa.

Uwani haka ta zama kamar gwal gun inna, a koda yaushe suna tare, hatta nanda makota inna zata shiga, toh tare zasu shige shi, in tana nan.

Uwani dai ta zama babbar budurwa, dan komai nata ya fito ya batse, batada jiki sosai, amma akwai cikar kirji, sai kunya da Allah yayi mata.

Tana shiga na english wears, saidai bata taba bari ta fitar da tsaraicinta a waje ba, dan tana aza hijabi ko abaya, ta rufe shigarta ruf!

Makarantar da take zuwama suna sa hijab dan islamic school ce, tanada kawaye, amma tafi shiri da lawisa, itama lawisa anan kebbi take zama iyayenta, saidai gidansu babban gidane, irin gidan nan ne da duk ‘yan wa da dan kani, saidai kowa da sashensa. Sun shaku da lawisa sosai, tun suna j.s one suka hadu, gashi yanzu zasu shiga s.s 2, lokaci kenan ba wuya!

Tare suka shigo da lawisa suka iske anyi baki a gidan, dan haka cikin daki suka wuce, inna ta kirata, uwani baki ga su hafsat bane?.” ta fito a guje, “ina take inna?

“bata waje? Kila tana gun indo.”

da gudu suka karasa dan dama su hafsat ma sun saba da lawisa, suna isa suka fada kanta suna ihu, indo tace, “wadannan yara ba kwa  girma, kullum haka kuke.” ta fice ta barmusu dakin, “yan iska.” inji hafsat, waya fa nake kuka tsinka min.”

“dawa kike wayar?

“zakuji ne, meye na sauri na baka na zuba? Za a kara bugowa, sai kuyi guesing.” uwani ta kwashe da wata uwar dariya, “kaddai wannan katon mutum daya nace makin ne?

“kedai shine, amma yanzu fa badama dan inayi dashi.” lawisa tace kina nufin kina sonsa?

Hafsat ta rangwada ido, “eh ina sonsa.” guda uwani tayi,

“Allah ya kawomu hafsat za a zama matar aure!.”

hafsat tabita suka fara zagaye dakin suna dariya, “kedai ce matar aure, saboda zaki rigani yin aure.”

“wazan aura? Nida ko son bansaniba, ke kuwa tun yanzu kin fara shi, wai su fa’iza fa.” (diyar zainab kenan wanda suke sa’a daya)

tana nan zuwa, amma sai hutu, nima da kyar mama ta bari nazo, ran lahadi zamu koma.”

toh Allah kaimu.”

***** **** **** *****+

jafar kuwa, ya sami shekaru hudu rabonsa da kebbi, suna sheka soyayya da yake hankalinsa ya dan kwanta, har kiba yayi.

Ita kuwa gimbiyar tasa harda teba tayi don kiba, gashi kibar sam batayi mata kyau ba, don dama ta kwana biyu, a kalla yanzu zata kai shekara arba’in da biyu.

Ana cikin haka da yake jamila ta dawo zama dasu, tunba yau ba, itama tayi kiba sosai abinta, duk abunda taga dama shi takeyi, samari kuwa ba irin wanda basa shigowa, shidai baya magana, amma abun naci masa tuwo a kwarya, dan tun abun nadamunsa har ya cire shi a ransa.

Rannan suna zaune a falo shida gimbiyar tasa, sai take ce mishi, tana so tayi tafiya zuwa maiduguri, ya kalleta baice mata komaiba, dama in zatayi tafiya, aiba neman izni takeyiba, saidai ta shirya ta tafi abunta, ta narke a jikinsa, “doctor bakace komaiba.” yaja hancisa kamar mai mura yace, ba damuwa, Allah kaimu.”

haka kuwa akayi, washe gari ta wuce da mota ta tafi, don tana tunani inzata dawo ta biya wani kauye wurin sabon malaminta, acan gun shanshani take dama kowacce zuwa tayi dole yayi amfani da ita sau ashirin da bakwai, dan haka aikinta ya gada, awannan zuwa ta nemi sassauci

akan ita ta gaji da wannan, dan haka shanshani ya amince, amma da sharadin zata rage kwanciya da mijinta. Tace,Tace, wannan ai mai sauki ne, tana iya hanashi, yace ba damuwa sannan kuma zata rinkayin hayaki da daddare, amma zata ringa shiga da bakaken kaya a duk lokacin da zatayi hayakin, ta amince da haka, data tafi gun dayan bokanta, shi kuma cewa, yayi intana so ta rike jafar sosai, saita rinka bashi hadin kai gurin kwanciya, sannan ya bata wasu layu huda biyu, yace ta rinka sawa a kasan filo duk in zasu kwanta,.

Daga nan ta wuce bauchi gun malaminta na can, shima haka din yace da ita, ta rinka saduwa da mijinta sosai, danshi kuma yanada sha’awar mata sosai. Tun anan ta zama comfuse ta rasa nawa zata dauka, dan dai tafi yadda da aikin shanshani, toh amma ita kuma tanaso ta rinka kasan cewa da mijinta, don dai itama ba baya ba wajen sha’awar da namiji, tun a mota ta yanke daukar shawarar malaman biyu da zancen su ya zama daya, ba tare da ta nemi shawarar shanshani ba.

Jafar shi dama Allah yayi shi da sha’awar mace, dan haka dama sun saba in gimbiyar bata nan, saiya kasance da jamila, suyi yadda ransu keso, in gaskiyane tsafi meyasa basu fadamata ba, ko suma sun gaji da la lurarta ne? Dan sau dayawa zatayi aiki, amma bata bada cikakken kudi, sun san kuma tana samu, dan hakane suka barta duhu? Oho Allah ya ganar da ita gaskiya amin.

Ta iso gida ta iske jamila sanye da da wando, wanda ake kira pencil jeans, da riga ‘yar karama, tana zaune suna hira da jafar. Ranta ya baci sosai, sam! Basu san da shigowarta ba, wucewa daki tayi da yake ta gabansu zata wuce, sai a lokacin suka ankara suka mike buzut! Suna yi mata oyoyo, bata tsaya tanka musu ba, ta wuce daki. Dama ako da yaushe tayi tafiya, toh haka zata rinka samunsu acike da nishadi, ta rasa dalili, duk da bata zargin wani abu na faruwa a tsakaninsu, tunda tasan jafar baya iya kasancewa da kowacce ‘ya mace sai ita.

Jafar ya bita daki duk ya sukurkuce, ta banka masa harara, “nikam bana son yadda kuke zama da jamila kuna hira, dubi yadda kukayi, kuna cike da nishadi, wai meke tsakaninku ne haka?.”

“haba sweety me tsakanin mu kuwa? Kawarki ce fa? Ki tambayeta mana.” yana magana ya tausa mata kafadarta, nan fa sha’awa ta birgizo mata, suka hau gado, shikenan ta manta.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, abun mamaki a yau jafar ya tashi da wani azababben ciwon kai, da kyar ya tashi sallar asubahi. Ya tsinci kansa da wasu irin tunani, na ban mamaki, toh wai ya akayi baya jin labarin su inna? A yau yai mafarkinta, tana ce masa “auta ba zaka dawo gida ba mu ganka?.”

shi ya manta yaushe rabon da yaji muryar mahaifiyarsa, meke damunsa? Sai a lokacin ya fara tunawa da ‘yan uwansa, a ranar sukuku ya wuni, sam ba walwala a tare dashi, meke damunsa, da har zai guji mahaifiyarsa?

Daya fita gun aiki ma sam bai saki ransa ba, daya dawo gida kuwa ya share kowa. Suna zaune a falo koda ya shigo, bai kalli inda sukeba, ya shiga daki. Abun yabawa marliya mamaki, taya zaya shigo yaki gaidata, harma ya wuce ko kallo basu ishe shiba? Ta bishi dakinsu tana wani yatsuna fuska.

“ya ya ka shigo mana gida haka, fuska ba annuri? Bana hana irin haka ba?.” kallonta ya rinkayi kamar ma ba dashi take magana ba, karo na farko kenan tun aurensu da zata nuna mata laifi bai nuna mata abun ya dameshiba. Ta karaso gunsa ba dakai nake magana bane jafar?.”

idonsa sunyi jajir ya dubeta saida jikinta yayi sanyi, sam bata taba ganin fuskarsa ta zama haka ba, sai yau, yace “banaso a dameni, banjin dadi.” haka kawai ya fada ya kwanta, data lura kamar da gaske baida lafiyan, yasa taja jiki ta zauna a gefensa akan gado, ta kai hannunta kan goshinsa, “amma jikinka ba zafi?. Yace, “nadai fada maki banda lafiya inaso in huta.”

haka tabar dakin, tana tunani. Jamila ta lura da hankalinta ba a jikinta yake ba, dan haka itama tabar mata falon, ta rika tunanin meke faruwane, koda yake lafiyane bai dashi, dan haka ta cire damuwa a tare da ita.

Sun sami kamar kwana hudu kullum haka yake fita, kuma ya dawo ya shige dakinsa, ya kwanta. Wani soyayya da kasancewa da marliya babu, toh dama ita tana fita taje ta wala a waje, dan haka abun bai fara damunta ba, ansami sati daya abun duniya ya ishi jafar, wannan wane irin rayuwa yakeyi hakane?

Meke damunsa ne, ace yadau dogon lokaci ba tare da yaje yaga iyayensa ba? Anya zai gama da duniya lafiya kuwa? Tambayar kansa yakeyi, alokacin yana zaune a falonsu, yana kallo, duk da hankalinsa ba kan t.v yakeba, marliya ta shigo cike da kasaita, zata shiga dakinsu, saiji tayi daga sama kamar a mafarki, ke daga ina kika fito?

Bata yarda da maganan dataji wai da gaskene ba, dan haka, sai taci gaba da tafiya zuwa bakin kofar dakin. Ta kumaji ance badake nake magana ba ne, ko bakiji abunda nace ba?.” ta juyo cike da mamaki “dani kake?  “toh dawa nake, koba ke kadaice mutum anan ba da zan iyawa magana ba?.”

gabanta ya fadi, “meke shirin faruwane da ita? Kaddai asirinta ne keson tonuwa? Koda yake mallam yace mata yanada tsananin kishi, kaddai ya ganta a hamdala motel?

Na da nan tayi ta maza tasha jinin jikinta tace, yaushe kafara kula da rashina acikin gidan nan,Yaushe ka fara kula da rashina a gidan nan, hala yau ne ka fara….. .”

ya katseta cikin tsawa yace, “ke! Kar ki gayamin maganar banza, inba hakaba zaki gane kurenki, ina tambayarki kina so ki maidani dan iska.” nan da nan hankalinta ya tashi, fuskarsa ta koma kamar yadda ta fara ganinsa rana ta farko da suka hadu a shopping mall, sam ba annuri a fuskar sa, yaci gaba da cewa kada ki sake kaimin wannan lokacin baki gida, inba hakaba zaki gane kurenki, inba iskanci ba, yanzu karfe goma saura zaki dawomin gida, har kinada gots din ki rika gaya min magana? Toh kiyi hankali nafada miki.”

waje ya nufa, fita yayi ya bar gidan baki daya, ita kuwa baki sake, haka ta tsaya tana kallonsa,

yau meke faruwa ne? Dole ta nemi shanshani, ya za ayi haka ta faru, ta kuma sake tunani, o.k ai dama malam hussaini ya fada mata, mijinta zai kasance mai bala’in kishi, tayi dariya ta karasa daki, nikam nasan bai isa ba, toh amma ai bai taba nuna mata wannan fushinba, ta gani a kwayar idonsa, dam babu wasa.

Tayi tsaki “mts…. Zai gane kurenshi ne, zai dawo ya sameni.”

jafar bai dawo ba sai wuraren karfe daya da rabi na dare. Tana zaune a falo, duk hankalinta a tashe yake, ya shigo duk yanayinsa ya canja. Ta tsaya tana harararsa, baima san tanayi ba, ya wuce zai shiga daki, saita shiga gabansa, tayi tsaye, “kai ina zaka haka? Ta fada cike da isa. Ya kalleta daga samanta har kasanta, baice mata komaiba, mamaki ne ta bashi? Oho! Sai kuma ta yatsine fuskarta, tana kallonsa ido cikin ido tace, “warin me nakeji? Kaddai giya ka shawo?.” kallonta kawai yakeyi. Can ta dan matso gunsa, tana sunsunarshi, warin giyarce da gaske, harara ta kuma wurga masa, mai cike da tsiwa, “kai bakajin abinda nace ne, ko kai kur…ma..ne.”tureta yayi ya shige daki abinsa, ya rufe kofar da karfi, ta nan inda ta fadi, yanzu kam hankalinta ya soma tashi, wai meke faruwa ne? Ta tambayi kanta, karda aikine ya fara lalacewa, toh meya kawo haka? Ta kara tambayar kanta.

Inko hakane, ta shiga uku! Taje ta murda kofar dakin, gam take, yasa key ya rufe, falo ta kwana ranar, dan bataso jamila tasan abunda ke faruwa.

Washe gari bata farka ba sai wajajen goma saura, abun mamaki jafar ya fice daga gidan shida baya barin gida indai bata ce, ya fita ba. Ta iske jamila a kicin, “a’a yadai naganki a falone ‘yar uwa?.”+

wannan shafin ya samu matsala

Ammi ki taimakeni, am in big trouble dan bazan iya rabuwa da jafar ba, har karshen rayuwata!.”

magajiya ta riko hanunta, “toh ki kara komawa gun su shanshani mana, kila kuskure aka samu ta wurinsu.”

“ammi bazan kara zuwa ba, saboda komai ya lalace, inaso dai ki kaini wani wurin inda za ayi min aiki cikin gaggawa.” ajiyar zuciya tayi tace, “wuri biyu na sani, zan kuma kaiki, ki kwantar da hankalinki, za ayi nasara.”

“toh jamila fa, ya za ayi da ita?

Sai munje gun malaman su zasu san abunda yafi.” ko kalaci batayi ba suka fita.

Boka na farko da suka samu yace musu, jafar kam bazata sameshi yadda ta kesoba, dan yana neman tsari sosai ajikinsa, amma kuma bayada niyar rabuwa da ita, “saidai dolene zakiyi hakurin zama dashi, dan yanzu bayada damuwa daya wuce ta mahaifiyarsa, daya bari kila inya ganta zai iya sauka, amma da duk kika nemi hanashi ganinta, toh ba karamin tashin hankali zaki gani ba, shawarar da zan baki, shine kije gun master na shanshani shi zai iya taimaka miki, kila kiyi nasara.

Na biyun kuwa tayar mata da hankali yayi yace. Jafar bazai kara sauraranta ba, tsanane zai shiga tsakaninsu. Hankalin marliya ya tashi sosai ta rasa inane zata sa kanta. A rayuwarta bata taba tsammanin zata shiga cikin kuncin rayuwa irin wannan lokacin ba, mamaki take yadda da namiji yake nema ya gagareta cukin kankanin lokaci, ta tuna saidai ta tarwatsawa namiji lissafi badai shi yayi da itaba, haka zata juyasu son ranta, tasha wulakanta namiji, ta daburce akan rabuwa da ita, amma gashi yau namiji na neman ya daburce mata. Oh! Ita Allah dama bata hadu da jafar ba.

Ta sami kwana biyu bata cikin nutsuwa sosai, magajiya kuma tana cikin lallashinta a kullum, saita nuna mata ta cire wa ranta son jafar yayi yawa shiyasa take wahala, tasha tunasar da ita cewa, tun farkon haduwarta da jafar take cikin tashin hankali, mezai sa bazata manta dashiba, taci gaba da rayuwarta yadda ta saba a da, tun daga lokacin duk taji ta tsani mahaifiyar tata, dan dai itace silar lalacewar rayuwarta, sannan kuma itace ta koya mata wannan tarbiya ta rashi ganin girman na sama da ita, duk wani abu data ke lallashinta a yanzu ba burgeta yake yiba, don dai ta riga ta bata mata rayuwa.

Ita kanta magajiya ta lura da yanda ‘yarta keyi mata wani irin kallo wanda ke fassara mata ‘yar na tsananta, dan hakane ta janye.

A ran kwana na uku tana kwance tana tunanin yadda zata shawo kan jafar, sai Allah yasa ta tuna yadda jafar keda biyayya, dan yanada displine ta mike da sauri ta sami magajiya a falo, tareda wani mutum, dama a kullum aikin kenan, daga wannan namiji ya fita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *