KASHE FITILA CHAPTER 2 BY BATUUL MAMMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun daga wannan rana Awaisu yake wasan buya da Harisu. Duk inda yasan zasu hadu su kebe guduwa yake yi. Ranar da zai koma Abuja ma kamar ana korarsa don sauri. Haka ya tafi tasha kafin Harisu ya dawo daga shagonsa inda ya ajiye masa kayan amfani kamar su madara da ganyen shayi da yake son bashi guzurin tafiya.+
Baiyi sati da komawa ba Alh Mudi ya dawo daga Kano. Wata rana da yamma ya tura karamin dansa ya kirawo Awaisu. Da ya zo ne ya tabbatar masa da Gimbi ta sanar dasu abin da ke tsakaninsu. Karshe yace yana so ya sanar da yayansa cewa su same shi a Kano shi da Saminu idan har da gaske yana sonta da aure suyi magana.
“Ban yarda da bata lokaci ana soyayya ba indai akwai halin yin auren gara ayi kowa ya huta.”
Gaban Awaisu ya fadi jin Alh Mudi ya ambaci ganin yayansa da Saminu. To da wane idon zai kallesu ma. Shi dai Alh Mudi bai san me yake faruwa ba. Albarkacin Saminu yake ganin lallai Awaisu ma mutumin kirki ne kamar yadda ya kula a dan zaman da yayi dasu.
Bai sami damar komawa gida ba sai bayan sati biyar ana hutun Good Friday da Easter Monday. Haka ya tafi jiki babu kwari saboda rashin sanin yadda zai tunkari dan uwansa da maganar auren Gimbi. Gashi Alh Mudi yace su same shi a gidansa na Kano. A son ransa ayi bikin bayan sallah karama tare da na babban dansa wanda suke a Kanon tare da babarsu uwargidan Alhaji.
*****
Kwanansa biyu da dawowa ya rasa abin da ke masa dadi kuma ya kasa fadawa kowa. Maamu tayi fadan da magiya duka yaki cewa komai. Gashi yana matukar son Gimbi baya fatan rasata.
Da daddare yana kwance a dakinsa Harisu ya shigo. Ya tashi zaune amma ya kasa cewa komai.
Harisu yayi murmushi yana kallonsa. Sai da ya zauna a gefen katifar dakin ya soma magana.
“Yanzu ni kake gudu saboda ka soma aiki a Abuja kayi kudi ko. Kana ganin kafi karfinmu.”
Awaisu ya zaro ido a razane “Yaya me ya kawo wannan zancen kuma? Wallahi ba haka bane. Allah Ya kiyaye. Bana fatan abin da zai kawo min tunani makamancin haka”
Harisu ya daure fuska “haka kawai za ka fara guduna ne idan ba kana tsoron a ganka tare da talaka irina ba.”
Idanun Awaisu tuni suka yi ja saboda rashin jindadin kalaman yayansa. Shi da ya dauki Harisu uba yaushe ma irin wannan tunanin zai zo masa. “Wata matsalar ce daban Yaya” Ya fada a raunane.
Harisu yayi dariya a zuci domin ya samu Awaisu ya fada tarkon da yayi masa na son jin damuwarsa.
“Ina jinka, menene matsalar da take hanaka walwala a gidan nan?”
Babu amfani cigaba da boyewar shiyasa ya fada masa maganar da yaji sunyi da Saminu da kuma wadda suka yi da Alh Mudi.
Wani dogon numfashi Harisu ya ja. Ya jima yana tunani kafin ya soma magana cikin nutsuwa.
“Kai ba yaro bane da zan ce baka san abin da kake yi ba. Sannan ka wuce ayi maka auren dole. Duk yadda nake son ka auri Mardiya ba ni zan zauna maka da ita ba. Saboda haka nagode da ka fada min da wuri kafin ayi auren muji kunya. Zanyi kokarin fahimtar da Saminu. Kuskurena ne da ban fara maganar da kai ba na fada masa”
Ko bai fada ba yasan ransa a bace yake kawai ya danne ne “Kayi hakuri Yaya. Itama Gimbi tana da kyawawan halaye idan ka ganta …..”
Bai karasa ba Harisu ya mike batare da yace komai ba yayi hanyar fita. Tunaninsa bai wuce yadda zai fita kunyar Saminu ba. Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba yace “ka shirya muje Kanon gobe kafin lokacin komawarka aiki.”
*****
“Zancen banza kai, ina Awaisu ina ‘yar masu kudi. Ko kuwa so yake ya janyo ace yayi auren jari? To ma a ina yake tunanin ajiyeta idan anyi auren. Yaushe ma ya fara aikin da zai jajibo aure irin wannan”
Maamu ce take ta fada bayan Harisu ya sanar da ita da Baaba batun tafiyarsu Kano neman aure. Haka tayi ta fada yana bata hakuri da nuna mata magana kawai zasu je yi ba auren za’a daura ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ranar da suka isa Kano Saminu jiki a sanyaye ya tarbesu. Wannan ya dagawa Harisu hankali ko har Alh Mudi ya sanar dashi komai. Baya son abin da zai taba alakarsu ko kadan. Shi Awaisu dama ya kasa kallonsa ma. Tunda suka zo yake sunkuyar da kai.
Bayan sun dan huta ne suka zauna tattaunawa. A nan Saminu ya dubi Harisu “Alh Mudi yazo gidan nan da kansa akan yana son na bawa dansa auren Mardiya. Sanin cewa munyi magana da kai nace na bayar da ita ga Awaisu. Shine yayi min wani bayanin daban da ban gama fahimta ba “
A kunyace Harisu ya fada masa abin da ke faruwa. “Kayi hakuri abokina, bani da masaniya akan hakan. Da tun farko bazan bijiro da maganar hadasu ba”
Awaisu duk sai yaji babu dadi. Yanzu da Alh Mudi baizo nemawa dansa ba shikenan ya bata zumuncin abokan.
Muryar Saminu ce ta katse masa tunani “Babu komai, ai kaga yadda Allah Yake nuna ikonSa. Sai muje gidan ka fada masa ka bada auren Mardiya ga Fawaz a matsayin waliyinta tunda bani da dan uwa namiji. Shi kuma Awaisu sai na nema masa auren Gimbi”
Sai a lokacin Harisu yayi murmushi hankalinsa ya kwanta ganin Saminu bai dauki abin da zafi ba.
Washegari kuwa suka dunguma sai gidan Alh Mudi aka daidaita magana. Sallah karama da sati biyu aka sha bikin Awaisu da Gimbi. Ganin cewa bai samu muhallin kirki ba Alh Mudi ya bashi gida da sunan Gimbi a Abuja inda zasu fara zama kafin ya sami nasa. Ita kuma Mardiya suka tare a Kaduna ina Fawaz yake aiki.
*****
*Bayan shekara 12*
Cikin shekarun da suka gabata Awaisu ya sami budi sosai. Domin har gida ya gina kato a Abuja yana shirin tarewa. Inda Allah Ya kara taimakonsa shine kasuwanci da yake yi. Duk da yana aiki ga rashin lokaci haka ya sami yara biyu ‘ya’yan kawunan sa da ya budewa shago suke sayarda atamfa da shadda. Abu kamar wasa sai da ya hada shaguna hudu a jere a Wuse market. Ga kwazonsa a wurin aiki yasa ya sami mukamin manaja a bankin.
Gidan Harisu kuwa yasha gyara sosai har mota ya saya masa sannan ya kara masa jari. Zamansu gwanin sha’awa.
Tsakaninsu da Gimbi babu wata matsala. Dayake itama aikin bankin take yi bata da lokaci na zuwa Fika sosai. Yaransu hudu babban ciki Haris, sai Daula mai sunan babar Gimbi, Amir mai sunan Alh Mudi da kuma auta Sa’ad suna kiransa Mu’allim. *****
A gajiye Awaisu ya shigo bayan isha yaran suna ta murnar dawowarsa daga Fika. Sai da ya gama dasu ya wuce dakinsa. Sauri yake yi idanunsa su gane masa matar da yake jin bazai taba iya hadata da kowa ba saboda irin son da yake yi mata ga kuma albishir a bakinsa.
Taci kwalliya tayi kyau sosai tazo ta tarbe shi tana murmushi “Ashe ka shigo maimakon ka kira kafin ku karaso na hada maka ruwan wanka”
Ya shafi gefen fuskarta yana murmushi “kada ki damu, zo ki zauna kiji albishir din da nazo miki dashi har biyu. Dayan ina hanya akayi min waya aka fada min”
Kaskon turaren wutan da yake gefen gado ta dauke sannan ta dawo ta zauna kusa dashi yana rungume da ita yayi ajiyar zuciya.
“Gimbina Allah Ya yarda. Visa dinku ta fito”
Ta dago kai da sauri cikin farinciki “wace visa kuma?”
“Dama na boye miki ne sai komai ya tabbata. Na biya muku Hajji ke da Yaya Harisu, Baaba da Maamu. Sai Yaya Zakiyya tunda su Anti Baraka da Ummu mazansu sun kaisu. Kinga za ta tayaki kula dasu Baaba. Albishir na biyu kuma kuna dawowa nake so mu tare a Apo. To babban abin jindadin shine dasu Maamu zamu tare”
Shiru yaji Gimbi taki dagowa bare tayi magana. Ko da ya dago kanta hawaye take yi sosai. Wani sonta ne yake shigarsa domin yasan kukan farinciki take yi. Rungumeta yayi yana shafa bayanta.
“Dama nasan zakiyi murna sosai Gimbina. Shiyasa ban fada miki batun tafiya Hajjin ba sai da na gama. Tunda kinga ni naje har sau biyu kuma last year munyi umara tare dake. Shiyasa bazan bi ku ba. ” ya cigaba da cewa “Kuma fa yadda naso har da Baaba zamu tare. Sai dai lalurar idonta yasa Yaya yaki yarda. Shine na hakura ba don naso ba. Burina ya cika zan dawo da Maamu kusa in kula da ita. Itama taji dadin arzikin da Allah Ya bani. Ta dade tana jin nauyin su Baaba da Yaya Harisu. Duk da naso hadawa da Baaba hakan bai samu ba. Amma zan dauko Rumana. Gimbina da ina da yadda zanyi fa wallahi Yaya Harisu ya dena fita neman kudi. Komai ni zanyi masa”
Can kasan makoshi tace “uhmm hakane.” Domin ji take yi ya cikata da surutu mara kan gado.
Mikewa yayi ya shiga bandaki domin yayi wanka ko zaiji saukin gajiya.1
Yana shiga Gimbi ta fice ta tafi dakinta ta rufe kofar da mukulli. Gadonta ta hau ta saki kuka cikin tashin hankali. Ko da wasa bata taba kaunar zama da uwarmiji ko dangin miji ba. Can daga nesa dai yayi musu kyauta suna kauye ba sai sun rabesu ba.
“Tabdi, akwai matsala. Matar da ko Hausar kirki bata iya ba sai anyi magana tayi ta yankare hakora tana murmushi. Shine don kana jin ka fara kudi zaka dauko min su ka kawosu ko neman izini na bakayi ba. Da sake Awaisu….bana cikin matan da za’a hada da uwarmiji ace mu zauna lafiya gida daya”
Dankwalinta tayi jifa dashi ta rasa me yake mata dadi. Ita fa shi kadai take so ba danginsa ba. Duk halaccin da tayi masa ta aureshi talaka ko gidan zama bashi dashi. Shine yanzu arzikin nasa kuma sai sun raba tare da wadda bata nan lokacin da suke nema. Ta hana kanta sukuni tana fita aiki duk domin ta taimaka masa. Ba don kada ace tayi sharri ba ma sai tace gabadaya gidan Harisu wari yake yi mata idan taje Fika. Shiyasa bata son zama idan taje.
Gani tayi kukan bazai kaita ko ina ba ta yanke shawarar washegari zata kira Mama ta fada mata. Dole ma a dauki mataki don ba bauta tazo yiwa kowa ba.+
Shirin bacci tayi sannan ta koma dakin nasa. Kwance ta same shi akan abin sallah da gani sallah ya idar bacci ya dauke shi.
Tausayinsa kuma taji, ya mayar da kansa tamkar agogo. Bashi da hutu kwatakwata duk domin ya farantawa su Maamu. Tsaki taja a fili tana tunanin yadda zata bullowa lamarin da ya tunkaro ta.
“Saboda zan kawo mahaifiyata gidana shine kike tsaki haka Gimbi?”
Muguwar faduwar gaba taji. Shi kuwa ya mike tsaye yana kallonta rai a bace. Bakinta yana dan rawa tace “haba my dear, kada kayi min mummunar fahimta mana. Dazu da kanka ka gani ina murna harda kukan…”
“Kukan bakinciki ba. Da farko har ga Allah nayi zaton dadi kika ji ganin yadda na damu da yanayin da mahaifiyata take ciki. Bata da wurin da zata kira gidanta. Sai da nayi wanka na biyo bayanki naji kina kuka sosai a dakinki.”
Rasa bakin magana tayi shi kuwa ya cigaba da magana cikin kunar rai “Duk duniya bayan Maamu babu wanda ya cancanci kyautatawa daga gareni kamar Yaya Harisu. Ban taba boye miki asalina ba. Amma abin mamaki kina nuna bacin ranki akan kyautatawar da zanyiwa wanda suka zama jigon rayuwata. Idan bazaki iya zama dasu ba sai na auri wadda zata iya”
Tun da ya fara magana bata tanka shi ba sai yanzu da ya ambaci kishiya.
“Kayi kadan kace zaka auro wata ka ajiye a gidan nan. Ko ka manta cewa nawa ne. Suna na ne a jikin takardun gidan”
“Dadin abin nima ina da nawa. “
Ta turo baki cike da tsiwa. Tsiwar da a da take bashi sha’awa idan tayi “Haka nan zaka kare rayuwarka kana yiwa wani kato bauta. Sai shegen aure da tara iyali. Kai kuma an barka da siyan shinkafa da ragon suna”
Shiru yayi har sai da ta gama maganarta tukunna sannan ya tako gabanta fuskarsa babu annuri ko kadan. Ja ta rinka yi da baya yana binta
“Yaya Harisun ne kato Gimbi?” Ya fada a hankali amma kana jin muryarsa har wani rawa take yi saboda bacin rai.
Duk da a tsorace take amma ta kule da yadda yake zare mata ido akan ‘yan uwansa.
“Karya nayi ba katon bane? Ko baiyi biyunka ba”
Bata karasa magana ba taji ya gwabje mata baki. Nan take jini ya soma zuba saboda fashewar lebenta na kasa.
Cikin kuka tace “Awaisu ni ka fasawa baki?”
“Idan baki fita daga dakin nan ba sai nayi miki abin da yafi wannan.”
Murya ta soma dagawa tana kuka “babu inda zani, gidana ne ba naka na. Idan kaji haushi ka fita ka koma naka”
Fitar yayi zuciyarsa tana tafasa. Wai akan iyayensa da bashi da tamkarsu shine Gimbi take yi masa abin da bai taba tunanin zata aikata ba. Lallai ba’a shaidar mutum. Yasan halinta na kyankyami da ji da kai. Shiyasa yake mamakin irin son da take masa farkon haduwarsu. Falo yaje ya samu yaransa uku sunyi bacci sai Haris da yake karasa homework. Tashinsu yayi daga su sai kayan baccin jikinsu suka fice.
Motarsa ya bude suka shiga suna tambayarsa inda zasu je. Bai basu amsa ba ya rinka dannawa mai gadi horn. Yana budewa ya fita a guje.
Karar horn din ce ta fito da Gimbi. Tsoronta kada da gaske ya fita daga gidan. Sai dai abin mamaki ba shi babu yaran.
Nan fa hankalinta ya kara tashi. Mai aikinsu Laminde ta shure da kafa tana bacci itama a falon ta tambayeta ina su Daula
“Hajiya gasu nan suna hamok. Jiransu nake yi su karasa aje a kwanta.”
Ta galla mata harara “ina kika gansu. Aikin banza babu abin da kika iya sai bacci”
Waje ta fita inda mai gadi ya tabbatar mata da yaran Alhajin ya fita. Haka ta rinka kiran wayarsa yaki dauka. Karshe ma kashewa yayi yana kallon yaransa suna bacci a makeken gadon dakinsa. Gidansa na Apo ya tafi dasu. ******
Da sassafe yaji ana buga gate ya leka ta taga. Maigadinsa ya gani yana ta washe baki ya budewa Gimbi gate ta shigo. Ko rufe kofar motarta batayi ba ta fito ta shiga gidan cikin sauri.
A falo ya sameta yace kada ta tasar masa yara.
“Wane irin wulakanci ne zaka daukar min yara cikin dare”
“A iya sanina lokacin da muka tare a gidan nan ke kadai kika shigo sai akwatunan kayanki. To mene ne na bacin rai don na kwashe yaran da jinin Maamu yake yawo a jikinsu”
“Wai duk saboda maganar jiya da bata taka kara ta karya ba kake min wannan cin kashin harda fasa min baki”
Ya tabe baki “ina jin baki san girman uwa bane”
Neman sulhu take yi domin tun aurensu basu taba samun sabani irin haka ba. Kwantar da murya tayi ta soma magana “Duk laifinka ne, ta yaya zaka shirya kawo Maamu batare da neman izinina ba? Nima fa ina da hakki akan ka. Kuma abu irin wannan sai ka fara shawara dani kaji nawa view din”
“Neman izininki? Wai dama haka kike ne ko kuwa sabon salo ne kika fito dashi kawai don baki son dangina. Ba fa tun yau na san kina nuna musu kyama ba. Sharewa kawai nake yi saboda babu wanda ya taba korafi cikinsu.”
“Kaga ni ba rigima nazo muyi ba. Maganar fahimta nazo da ita. Idan kana so ka ginawa Maamu sabon gida a Fika is up to you. Amma batun mu zauna tare is out of the question. Zama da suruka baya taba haifar da alkhairi”
Duk yadda yake son ta a daidai wannan lokacin yayi nadamar aurenta. Rasa bakin magana yayi yace mata kawai ta fita idan ta gama. Ganin wankin hula zai kaita dare ta ja motarta ta tafi gidansu. Tana kuka ta zayyanawa Mama abin da ya hadasu. Mama ta dubeta sosai ta girgiza kai.
“Idan kika kure Awaisu ya sakoki zaki gane kudi da gata aikin banza ne idan aka rabaka da iyalinka. Ke da ya kamata ki nuna masa kinfi kowa farinciki shine zaki bata masa rai akan mahaifiyarsa. To yayi miki adalci ma da bai hadoki da takarda ba. Shashashar kawai. Idan ma zugaki akeyi ki sani aljannarki tana karkashin kafar mijinki. Shi kuma tasa tana tare da mahaifiyarsa. Kada ki zama mace mai kashewa mijinta fitilar rayuwarsa Gimbi. Uwa haske ce, uwa rahamace. Da kika shiga matsala ai gaki a gabana.”
“Mama yanzu goyon bayansa kike yi”
“Ki kiyayeni Gimbi. Kuma ki wuce yadda kika bata mishi rai ki bashi hakuri ku sasanta. Idan Alhaji yaji maganar nan ki kuka da kanki. Kinsan halinsa sarai. Bar ganin yana sonki hakan bazai hana ya saba miki ba”
Dukar da kai tayi ta gama jin fadan Mama ta tashi ta koma sabon gidan.
Amir ne ya fada mata baban nasu yana daki ta shiga da sallama. Kafin ya amsa ta durkusa gwiwoyi a kasa a gabansa tana kuka. Kamar ya basar sai dai Gimbi matsayinta daban a zuciyarsa.
Tasowa yayi yazo gabanta. Cikin kuka da nuna nadama ta rinka bashi hakuri da nuna masa ta gane kuskurenta. Kukan da tayi tana ajiyar zuciya yasa dolensa ya hakura tare da yi mata nasiha. Cikin dan kankanin lokaci ta shawo kansa suka daidaita.
*****
Zaune suke cikin daki su biyu ta dubi kanwar Mama wadda take binta bayan ta bata labari.
“Anti Bebi wannan ita ce matsalar da ta tunkaro ni. Kuma Mama ta bashi goyon baya”
“Ki bar komai a hannuna ‘yata. Indai ina raye babu wanda ya isa ya takura miki. Tun da dadewa nace kizo muje a mallaka miki shi a tafin hannuki kika ki yarda ke dadi miji. Yau ga irin abin da nake ta hango miki ya faru. Ke ko babu boka babu malam yayi kadan kinji ko. Shi din me? Mijina na uku ma duk taurin kansa sai da ya koma albashinsa ma a hannuna yake balle wani Awaisu.”
Kalmar karshe ta sosawa Gimbi rai sai dai biyan bukata yafi dogon buri.A kwanakin da suka biyo baya Gimbi ladabi take yiwa Awaisu sosai. Tsakanisu tamkar wani abu bai faru ba. Tarewarsu a sabon gidan da ake jiran sai bayan babbar sallah idan sun dawo daga hajji kuwa tuni ta rushe. Kusan duk abin da suke bukata daga tsohon gidan sun gama kwashewa.+
Gimbi ta gyara dakin da Maamu zata zauna tamkar wata amarya. Dayake komai sabo ne idan ka shiga kamar kada ka fita. Dakin Daula da taci burin gyaransa ma saboda tilon ‘yarta sai da ta matsawa Awaisu aka karo wani gadon a matsayin na Rumana.
Karshe ta yiwa Maamu da Rumana dinki kala biyar biyar ta kawowa Awaisu.
Shayi yake sha yana duba wasu takardu ta kawo ledoji manya biyu ta ajiye tare da durkusawa a gabansa.
“My dear ga tawa ‘yar gudunmawar”
Daya daga cikin ledojin ya bude. Kaya ya gani a dinke duka super holland har biyar. Ya kalleta da alamar tambaya. Rausayar da kai tayi tana kifta idanu alamun zata yi kuka.
“Nasan babu wani abu da zanyi ya wanke wautar da nayi maka kwanakin baya. Amma don Allah ina mai sake neman afuwarka. Na tsorata ne da jin labaran zama da surukai har naso bata aurena akan labaran wasu da nake ji”
Tayar da ita yayi sannan ya matsa yadda zata iya zama kusa dashi. Ya kama hannunta ya rike.
“Bazanyi miki alkawarin cewa kullum cikin zaman lafiya zamu kasance ba idan Maamu tazo. Amma ina so ki sani ba wai don ita ta haifeni ba, Maamuna bata da rigima ko kadan. Mace ce wadda yanayin kaddarar rayuwa ta sanya mata mugun hakuri da kawaici. Ina jin ba domin Baaba ba da a sangarce ma zan tashi saboda tsabar hakuri irin nata. Tabbas banji dadin abin da kika yi ba amma na hakura. Da kinsan yadda nake mafarkin zama inuwa daya da ita nasan baza kiyi waccan maganar ba tun farko”
Sake bashi hakuri tayi tana kuka da alkawarin gyara kuskurenta ta hanyar bin Maamu sau da kafa. *****
“Anti Bebi lokacin tafiyarmu sai kara matsowa yake fa. Ni wallahi bana son yin tafiyar da mutanen nan. Dukkaninsu babu wata alamar wayewa. Muje airport su janyo a rinka kallona”
Dariya sosai Anti Bebi tayi sannan ta soma magana da shakakkiyar muryarta wadda tsabar gayu da make murya wurin janyo hankalin maza ta koma haka
“Ki samu ya barki muje wurin da nake fada miki. Kuma kiyi a hankali kada uwarki taji labari. Kinsan dai ba shiri muke da ita ba”
Gimbi ta tsuke baki jin an zagar mata uwa. Ita kanta bata fiye shiga sabgar Antin tasu ba sai da wannan abin ya faru. Yadda Anti Bebi da Mama basa kama a fuska haka suka bambanta a hali. Yanzu haka aurenta na shida kenan. Abin mamaki masu kudi take aure suyi ta mata bauta. Sai ta tara abin da ta tara ta nemi sanadin da zasu saketa. Mama ta gaji da fada da nasihar ta tsame hannunta daga lamuran kanwar ta ta.
“Shi kuma mijin naki ki barni da shege, idan Wangesi na tsangaya ya fara aiki akansa ina fada miki sai juya alkalami yafi miki wahala akan yadda zaki rinka juya shi son ranki. Shi din banza…”
Mikewa Gimbi tayi tana rataya jaka rai a bace. Anti Bebi tace “Me aka yi kuma zaki tafi muna magana”
“Haba Anti, zamana a nan kin zagar min uwa kin koma kan mijina. Ina sonsu bazan jure zaginsu da kike yi ba”
Dukan cinya tayi irin na matan da suka ga jiya suka ga yau.
“Karyar banza, Amina dai zan yarda kina sonta tunda ita ta haifeki. Amma indai Awaisu ne karya kike yi Gimbi. Duk matar da take son mutum take kin iyayensa ko ‘ya’yansa na wani auren kallon munafuka nake yi mata. So da ya amsa sunansa shine ki rungumi duk abin da mijinki ya nuna yana so ki taya shi ririta shi”
Ganin Antin tana ya6a mata magana ta fice ko sallama babu. Dama can ba wai tana ganin mutumcinta bane. Tun suna yara sun san tayi kaurin suna a dangi saboda fitinarta. Yanzu ma dole ce ta kawota. Zata nemarwa kanta mafita.
*****
Bayan kwana biyu Awaisu yake sanar da ita cewa nan da sati uku su Maamu zasu taho Abuja domin ta nan zasu tashi. Kuma an kusa fara dibar alhazai. Sanan za’a taho da Rumana tun yanzu domin taya Laminde zama da su Haris da kuma sabawa ita ma da gidan. Da murnarta ta dauko takarda tana yi masa list na abubuwan da take so a karo musu na kayan abinci da kayan masarufi domin tarbar baki. Yadda take yi masa dole duk wani sauran zargi da bacin rai da yake ransa ya kawar dashi.
Bayan ya fita a gigice ta kira Anti Bebi har ta manta abin da ya faru tsakaninsu. Ita kuwa tana ganin kiran taki dauka. Sai da ta kira yafi sau biyar sannan ta amsa tana magana da kyar wai ita a dole anyi mata ba daidai ba.
Gimbi bata yi fushi ba ta fada mata yadda suka yi da Awaisu. Anti Bebi tace idan zata iya ta je ta sameta a gida washegari su tafi wani kauye a Nasarawa state inda Wangesi na tsangaya yake.
Da daddare kuwa ta karantawa Awaisu karya da gaskiya saboda kada ya ga bata dawo gida da wuri ba daga bankin da take aiki. Shi kuwa sanin yanayin aikinsu bai kawo komai a ransa ba sai addua da yayi mata.
Washegari tana zuwa wurin aiki tayi karyar ciwon ciki ta samu manaja ya yarje mata komawa gida. Daga nan bata zame ko ina ba sai gidan Anti Bebi. Ko zama batayi ba suka kama hanya. Dreban Anti Bebin ne ya kaisu. Tayi mamaki sosai yadda taji suna hirar malamin tsibbun tare dashi. Ashe shine ya hadasu ma.
*****
Wangesi ya bata layu da guraye da zata saka a cikin gidan wanda su Maamu suna zuwa zata ji ta tsani gidan saboda zafin da zaiyi mata. Saboda yarda da shirkarsa da yayi har alkawarin dawo mata da kudinta yayi idan Maamu ta iya kwana uku a gidan batare da ta matsa a mayar da ita Fika ba.
Gimbi murna ba’a cewa komai. Tana zuwa gida tayi duk yadda yace ayi da kayan da ya bata ta zauna jiran lokaci.
Ranar da zasu zo ta kama asabar. Tun kafin asuba ta farka ta shiga kitchen tana ta dafa kayan tarbar baki. Laminde ma a nan ta sameta. Awaisu kuwa zuciyarsa fes ganin ta sake tana nuna masa ta fishi murnar zuwansu.
Dama dreba ya tura aka dauko su. Motar na shigowa yaran suka fita a guje suna murnar ganinsu. Haris tamkar ya shige cikin Harisu don murna. Ba karamin son kawun nasa yake yi ba. Maamu ce karshen fitowa daga motar. Kafar dama ta fara saukewa cikin sanyin muryarta tace “Bismillah tawakkaltu alallah”.Awaisu da yaransa duk da murnarsu suka koma cikin gidan tare da su Baaba. Maamu ce karshen shigowa. Ta tsaya a waje ta karewa gidan kallo. Yau danta wanda ko rabin fuloti bai mallaka ba shekarun baya da suka wuce shi ne da dankakaren gida irin wannan. Addua tayi sosai ta neman tsari da kariya gareshi da zuri’arsa da kuma sanya albarka ga samunsa. Sai da ta gama ta shigo ciki. Nan ta tarar da su Baaba Hure suna ta kalle kallen gida su ma suna yabawa.+
Kayan abinci Gimbi da Laminde suka rinka fitowa dasu suna jerawa a tsakiyar katon kafet din falon. Sai da ta gama sannan tazo ta durkusa har kasa tana gaishesu tana satar kallon fuskar Maamu. Wangesi dai yace gidan zafi zaiyi mata da kanta zata nemi a mayar da ita inda ta fito. Wani murmushi tayi sannan ta cigaba da tambayar Rumana yaya mutan gida.
Da yake Maamu banda amsa gaisuwa da kalmomi kadan ita ba Hausa ta iya ba shiyasa bata shiga hirarsu sosai. Baaba ma yau da gobe tasa Hausarta sai a hankali, ta iya amma sai ka zata ba bahaushiya ke magana ba. Haka Rumana da Zakiyya su duk da sun dan iya amma ba kamar Awaisu mai auren bahaushiya da kuma Harisu dan kasuwa ba. Bolanci yafi kama bakinsu. Hirar dai aka ake yinta wani abin sai kaci dariya. Idan kaga Gimbi a tsakiyarsu sai ka rantse ko goyo suka nema zata yi musu. Shiyasa basu taba korafi akan ta ba. A ganinsu yanayin aiki ne yake sawa bata zuwa Fika sosai.
Dakin da aka tanadarwa Maamu nan Baaba tayi masauki tare da Zakiyya. Gado ne kato wanda zai ishi mutum hudu ma. Ba karamin kashe kudi Awaisu yayi ba. Harda tv ya saka mata da fridge. Baaba da aka soke zuwanta Abujan itama yayi shirin sake gyara mata nata dakin kafin su dawo daga Hajji.
Ranar a wurinsu ya yini shi da Harisu. Da safe zai tafi aiki ya bar sallahu cewa drebansa zai dawo sai ya kai Harisu kasuwa ya ga shagon nasa.
Kwananusu biyu babu wata matsala da ta taso. Ranar laraba Awaisu zai tafi aiki Gimbi take sanar dashi ta dauki hutu na tafiya Hajji. Ya nuna mata jindadinsa tunda ga baki dama a gidan. Bayan fitarsa bai dade ba Anti Bebi tazo. Da yake safiya ce babu wanda yasan tazo ta shige dakin Gimbi. Mayafinta ta cire wanda ya bayyana siraran kitson da akayi mata da karin gashi. Dama ita da wuya tasa dankwali. Dan mayafi ne guntu shara shara kullum take fama dashi.
“Ke kuma sai naji ki shiru babu wani jawabi game da bakinki?”
Gimbi ta tabe baki “hmmm Anti wannan anya ba kudina yaci ba. Kullum naje dakin sai tayi ta murmushi babu alamun ta soma gajiya da gidan. Ita fa fuskarta kullum a sake kamar mara lafiya. Har tunani nake ko aljanun nan ne masu sa dariya basuyi mata kamu sosai ba aka tsaya a murmushi”
Dariya sosai Anti Bebi tayi “Shegiya Gimbi, ashe kema baki da mutumci, yarinya tayi gadon uwa. Kuma ina mai tabbatar miki indai zakiyi yadda nake yi to babu wanda ya isa ya taka ki”
Gimbi shiru tayi. Idan da Mama zata ji abin da take yi yanzu Allah kadai Yasan fadan da zatayi mata. Balle kuma Alhajinsu da ya dauki son duniya ya dorawa Awaisu. Shi a ganinsa ba karamin dace yayi da surukai ba.
Sai bayan azahar Anti Bebi ta dauki mayafinta
“Tashi muje na ga bakin naki sai na wuce daga can. Idan anyi sati babu chanji da kaina zan koma wurin Wangesi”
*****
A falo suka tarar dasu harda su Haris sun dawo sun tsaya basu labarin makarantarsu.
Anti Bebi kallo daya tayi musu taji babu wanda yayi mata a cikinsu. Duk da cewa zata yi sa’ar Ummu kulsum ‘yar Baaba Hure ta uku domin ita ce autarsu Mama amma daga tsaye ta dan dago musu hannu
“sannunku”
Zakiyya ta amsa mata tana yi mata wani irin kallo. Wannan mata duk inda ta fito akwai rashin kamun kai a tattare da ita. Labaran da akeyi a tashar NTA Hausa shine ya dauki hankalin Baaba Hure ga Rumana ta biyewa su Amir suna ta hayaniya. Remote din tv ta dauka zata karo sautin yadda zata ji jawabin mai kawo rahoton. Tana cikin dannawa Anti Bebi ta kwashe da dariya
“Mhmmm ashe harda su kaza a cin danko. ‘Yata kinyi sa’a su o’o hannu baya gani ya kyale. To gaskiya a dage a sayo musu computer”
Baaba Hure ji tayi kamar an zuba mata ruwan zafi saboda yadda zuciyarta ta harzuka. Bata bukatar wani bayani tasan cewa da ita wannan bakuwar take. Ajiye remote din tayi jikinta babu kwari tana jiran amsar da Gimbi zata bayar sai ji tayi tace
“Waya ga dan wake a hotal”
Zakiyya da Maamu sai dan murmushi sukeyi. Ita Zakiyya duk da tana dan jin Hausa ko kadan bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba balle kuma Maamu.
Baaba Hure ganin haka itama sai ta biye musu tana murmushin. A iya saninta Gimbi bata san cewa ita asalin bahaushiya bace. Kuma yanayin da Hausarta ke fita da wuya ace tana gane karin magana indai ba yarenta bane. Gara ta nuna musu itama bata ji ko don ta ga iya gudun ruwansu. A lokaci daya kuma tausayim Maamu ya cika mata zuciya. Ashe Gimbi ba son Allah da Annabi take yi musu ba. Indai hakane kuwa akwai matsala wannan zaman da zata yi a gidan.
Da yamma da Harisu da Awaiau suka shigo. Baaba taso ta sanar da Harisu abin da taji sai kuma tayi tunanin kada ta zama uwa mai sa ido. Daga faruwar abu daya bai kamata ta yanke hukunci akan cewa Gimbi ba mutuniyar arziki bace. Hakan yasa ta fasa cewa komai.
*****
Bayan kwana hudu aka kirasu sune diba na biyu. Awaisu da drebansa sukayi mota biyu aka kaisu Airport. Basu dawo ba sai da jirginsu ya tashi.
Madina suka fara wucewa. Tun a hanya Gimbi ta soma zazzabi mai zafi da amai. Suna isa aibiti aka kaita likita yace taci wani abu ya bata mata ciki. Duk rashin kirkin da taso gwada musu sai ta koma abar tausayi suna jinyarta. Kwanakin Madina kaf bata ji dadinsu ba. Haka suka je Makkah can ma bata da wani kuzari. Wannan Hajjin dai bata ji dadinsa ba kwata kwata. Daga zazzabi ya warke sai mura mai zafi da ciwon wuya. Haka sukayi kwana talatin suka dawo da ita duk ta fige sai mugun nufi a zuciya.
*****
Sai da sukayi sati da dawowa sannan suka koma Fika aka bar Maamu da Rumana. Gimbi ce ta samar mata makaranta wadda bata da nisa sosai da gidansu. Makaranta ce mai tsada mai kyau don kawai ta burge Awaisu.
Da taga hankalinsa a kwance yake da abubuwan da take yi ta koma gidan Anti Bebi tana korafin rashin aikin maganin Wangesi.
“Kwantar da hankalinki naje na same shi. Yace wannan magani ranar da suka je gidan wani abu ya bata sihirin da yake ciki.” Wata leda ta dauko ta mikawa Gimbi.
“Ga wannan yace ki dafawa mijinki abinci dashi. Daga ranar a hankali duk wani so da kulawa da yake yiwa uwar tasa zai fara fita daga zuciyarsa. Sai kiyi amfani da wannan damar ki gasa mata aya a hannu. Da kanta zata kwashi kafarta ta gudu gashi an daure bakin”
Karba tayi jindadi ya bayyana a fuskarta
“Ina fata wannan karon a dace. Idan ba haka ba kuma zanyi maganinta da kaina. Shiru shirunta irin na munafukai shi nafi tsana. Kinsan irinsu abin tsoro ne. Ga wannan yarinyar da suka zo tare mai cin tsiya. Ina tsammanin horon yunwa zan fara yi musu a gidan”Ranar laraba da daddare Gimbi da kanta tayi girki sabanin yadda ta saba saboda yanayin aikinta Laminde ce take yi. Maganin da aka karbo mata ta juye shi tas a miyar Awaisu ta kara maggi.+
Da ya dawo dakin Maamu ya fara zuwa ya gaisheta tare da zama zai fara hira ta dube shi duk da alamun gajiya a tare dashi
“Ka tashi kaje kaci abinci ka huta na yafe hirar nan”
“Maamu ni sai kiyi ta korata. Da Yaya Harisu ne ai sai kin gama sauraronsa”
“Sannu baban kishi. Yanzu dai ka tashi, ka ga matarka itama ba zama take yi ba. Dan lokacin naku kuma bazan so na hanata sakewa ba. Ni ban zo gidan nan don takura muku ba. Abokan hirar nawa ma abinci suka tafi ci. Yanzu zaka ga sun dawo”
Tashi yayi rike da coat dinsa a hannu yace zai dawo bayan yaci abinci yayi wanka. Har ya fita tana cewa ta yafe hirar yau.
Wanka yayi Gimbi ta biyo shi da abincinsa daki wai falon hayaniya tayi yawa. A haka tana yi masa hira ya cinye tuwon da ta zuba masa harda neman kari. Dadi ya kamata kuwa. Yanzu abin da ya rage kawai shine ta fara gwada aikin maganin.
*****
Washegari saboda fitarsu aiki da zuwan yara makaranta tun asuba suke tashi ranakun aiki. Kitchen ta shiga ta aunowa Laminde shinkafa sannan ta fito da kazar da ta tafasa tun dare.
“Kiyi min jallof din shinkafa taji alayyahu da busasshen kifi. Wannan kazar kuma pepper chicken nake so kiyi. Kiyi komai cikin sauri kinsan Abbansu Daula baya son jira.”
Laminde ta gyada kai “To Hajiya, amma shinkafar bazata ishemu har su Hajiya Babba ba da ‘yan makaranta”
Gimbi ta koma store din da yake cikin kitchen din ta dawo rike da wata karmasasshiyar doya. “Shinkafar ki dafa mana ni da yara da babansu. Wannan doyar kuma fate zaki yi muku ke da sauran mutan gidan”
Laminde ta kalli doyar ta kalli uwargijiyarta. Ita dai tunda take a gidan ba’a taba yi mata wulakanci akan abinci ba. Wani lokacin ma ita Gimbi take barwa zabin abincin da za’a dafa. Kasa shiru tayi ta dan rausayar da kai tana kara kallon doyar da ta bushe
“Wai Hajiya nace ba, uhmm ita Hajiya Babba nake nufi ki karo shinkafar saboda ita”
Daure fuska Gimbi tayi “sunanta Maamu ba Hajiya Babba ba. Wannan so kike yi wani yayi zaton ni da ita uwargida da amarya ne. Anyway, itama faten zaki zuba mata naji ance tana son doya. Ga langa can da na karbo wurin Mama. Kinsan mutanen da suna son komai irin na zamaninsu. Shine na nace har sai da Mama ta bani cikin nata tun na aure. A ciki zaki rinka zuba mata abinci. Kuma kiyi sauri tare zamu fita zan aike ki”
Kasa hadiyar yawu Laminde tayi domin tsananin mamaki. Langa ce da gaske ga kuma doya da akace ta zuba mata. Ko ita da take aiki yau tasan anso wulakanta ta bare uwarmiji. Magana take son yi amma sam bakinta ya kasa hada kalma ko daya. Tana ji Gimbi tace ita zata yi musu nasu girkin wanda suke tafiya dashi wurin aiki yaran kuma suje dashi makaranta. Ita kuma tace tayi sauri tayi faten kada su makara.
*****
Rumana cikin sauri ta gama shirinta tsaf saboda bata so a jirata. Tun fara zuwa makarantarta kwanaki biyu da suka wuce tare suke fita da yaran gidan da Gimbi. Dreba ne yake kaisu makaranta ya wuce da ita wurin aiki. Tunda a banki take shiyasa suke yin sammako sosai.
Ko da ta fito falo Mu’allim ne kawai Gimbi take bashi abinci a baki yana ta rigima shi bacci yake ji. Har kasa ta durkusa ta gaisheta sannan ta nufi dinning table inda kayan tea suke zata hada.
“Dakata Rumana me zakiyi a nan?”
Murmushi tayi ta kirata yadda yaran gidan suke kiranta “Mummy tea zan sha kafin su Haris su fito”
“Kinga daga yau ki rinka zuwa wurin Laminde ki sha tea din a can.”
Bata ji komai a ranta ba tayi hanyar kitchen. Sake dakatar da ita Gimbi tayi “Kiyi sauri kisha ki fito kada ki makara”
Dayake bata san sunan dreban ba sai tace “Mai kaimu makarantar har yazo ne? Bari na fadawa su Amir suyi sauri su ma”
“A’a kina jina ko Rumana, makarantarku ba wani nisa gareta ba. Ki rinka shiryawa da wuri kina tafiya. Tafiyar da mukeyi da ke tasa ina makara kwana biyu. Gashi ba’a gama abinci ba. Idan kin dawo sai ki ci. Tea din ma ruwan zafin aka juye a girkin sai an dafa wani”
Sai a lokacin Rumana taji wani iri a ranta.
“To Mummy bari na tafi, sai kun dawo”
Gimbi harda murmushi “yauwa Rumanan Abba. Allah Ya kiyaye kinji.”
Rumana ta dan tsaya jim ko zata bata kudi tunda sai hudu da rabi suke tasowa. Gimbi ta fahimci dalilin tsayuwar ta dan sake fuska “ko akwai wani abu ne Rumana?”
“A’a babu komai. Na tafi”
Fita tayi tana tafiya a hankali. Allah Yasa makarantar a bakin titi take kuma babu wuyar ganewa. Tafiyar minti shabiyar zata kaita idan tayi sauri. Iyayenta ne suka fado mata a rai taji kamar ta fashe da kuka. Bata san yadda zata fassara abin da Gimbi tayi mata ba. Tayi kamar minti biyar tana tafiya taji mota ta tsaya a gefenta. Horn da akayi yasa ta kalli motar. Mace ta gani tasha lullubi sai wata yarinya mai uniform irin nata. Da ta sake kallonta ta tuna ajinsu daya duk da bata san sunanta ba. Gaishe da matar tayi cikin hausarta.
“Shigo mu karasa kin fito cikin sanyin nan ko rigar sanyi babu. Kada kiji tsoro ga Yusra ajinku daya tace min”
Bayan motar ta shiga ta sake gaisheta sannan Yusra ta juyo “Sunanki Ummu Ruman Abali ko”
Rumana ta gyada kai tana murmushi. Hira uwa da ‘yar suka cigaba da yi har suka iso kofar makarantar.
“Umma baki bani kudin break ba fa”
“Yusra bana son wannan kashe kudin da kike son koya. Ga abinci nan a jakarki”
Yusra ta sake kwantar da kai “Umma ko hamsin ce saboda siyan ruwa”
Dari biyu maman ta mika mata “gashi ku raba da Rumana idan kun fito. Allah Ya bada sa’a”
Rumana tayi mata godiya suka jera cikin makaranta tare da Yusra wadda take yi mata tambayoyi akan makarantar da ta baro. Da haka ta manta da bacin ran da ta fito dashi.
*****
Duk sun gama shiri sun fito Awaisu ya tambayi ina Rumana. Gimbi tace
“Ta tafi, wai makarantar babu nisa zata rinka tafiya da kanta.”
Bai ce komai ba suka fice saboda ya leka Maamu tana bacci.
Bata farka ba sai karfe tara da kusan rabi. Sabanin yadda ta saba ganin tray din abincinta na safe yau babu komai a wurin sai wata langa da cokali makale a hannunta. Bata kula ba ta shiga bandaki tayi wanka. Sai da ta gama shirinta ta zauna shiru Laminde bata kawo abinci ba. Fita tayi falon taji gidan tsit alamun ita kadai ce. Komawa dakin tayi tana tunanin ina Laminde taje haka. Dama ita take tayata hira kafin yaran su dawo daga makaranta. Langar ta sake kallo bayan ta koma sai ta bude. Faten doya taci karo dashi yayi wani baki ya cure wuri guda saboda rashin wadatar mai. Haka aka yi shi kandas sai kan sauran kifin da Gimbi tayi musu abinci. Mayarwa tayi ta rufe zuciyarta tana karyata cewa wannan abincin nata ne. A