KAWUNA CHAPTER 3

KAWUNA




CHAPTER 3





Shiru Abee tayi tana sauraren Suhailat ɗin can kuma ta nisa ta ce “naji Nagode Suhailat,ina so ki sani Sir Salman ni yake so! kuma ni yake shirin aura! shawarar da zan iya baki shine tun wuri ki saduda ki fallalawa Allah lamuranki kidaina biye ma malaman nan dan ko annabi bai san gaibuba ballantana su ,a kan kiso wanda bai son ki ko da ya aure ki bazai darajaki ba gwamma ki aura wanda yake son ki koda ke baki son sa hakan zaifi kawo zaman lafia ,shawara ce nake baki a matsayina na ƙawarki ”

Abeedah ta ida maganar tana mai jan dogon lumfashi haɗida miƙewa tana tattara inata-inata da nufin tafiya gida.Suhailat kuwa baki ta buɗe fangam tsananin mamakin Abee ya gama rufe ta wlh ko a mafarki tayi mafarkin cewa Abee zata iya auren wanda tasan cewa tana matuƙar so,tsaf zata ƙaryata mafarkin dan tasan waye Ƙawarta Abeedah, ta kuma san halinta bata san takamaiman abin da ya sauya Abee farat ɗaya haka ba ,SO babu abin da bazai iya sa mutum ya aikata ba dama ance so gamon jini ne da zarar ka faɗa tarkon SO shikenan kuma wasu harta iyayensu zasu iya rigima dasu duk dai a kan SO! toh ita wacece da Abee bazata iya shurewa ba ?abin da har yau bata samo amsar shi ba shine Abee na son Sir Salman ko kuwa kawai ta aure sa ne dan yana son ta ?………….

Maganar Abee ya saka tunaninta katsewa.

“Ni kinga tafiyata in kinso kizo gidan namu gben in kinƙi kuma kiyi zamanki yau dai saura sati ɗaya kacal bikin ,na barki lfy”

Ta ƙarasa maganar tana mai ficewa daga cikin ɗakin, Suhailat kuwa da idanu kawai ta bita .

Shiru Suhailat tayi tana tunanin wannan al’amarin wai shin mai ya kamata tayi ne dan ganin an fasa bikin Abee da Salman ne ? zuciyarta gab take da bugawa wlh muddin bata mallaki Salman ba! gashi bata son cutar da Abee dan tana mutuwar ƙaunarta toh mai ya kamata tayi cikin ruwan sanƴi ba tareda ta cutar da Abeen a kowani siga ba? Ita dai ta gama rantsuwa da Allah a kan bazata taɓa barin a ɗaura auren Abee da Salman ba dole sai an soke wannan auren indai tana lumfashi a doron ƙasa auren su bazai taɓa yuwa ba,wannan alƙawari ne ta ɗauka sai dai duk su biyun su rasa Salman …………………

Maganar Momy ne dake ta faman kwala mata kira ya saka tunaninta katsewa.

“Na’am Momy ganinan zuwa”

Ta ida maganar tana cuno baki tana magana ciki ciki
“Ni wlh wannan yaah Hafizz ɗin da takurawa yake dole ne ya ganni ?yabi yata takurawa mutane shi a dole sai na so shi toh baza’a so shi ɗin ba!……….

Maganarta ce ya maƙale a maƙoshinta takasa amayo da sauran sakamakon ganin sa zaune ya zuba mata oily eyes ɗin sa da alamu ya gama jin duk abin da take faɗi ko baiji komai ba tasan yaji na ƙarshe .

Harara Momy ta wurgo mata sa’annan ta ce “kina kyautawa ai Suhailat rayuwa ce kiyi yadda kike so da ita is all yours ”

Momy ta Ida maganarta tana mai miƙewa dan barin falon ranta na matuƙar tafarfasa ,ƴarta na naiman zubar mata da ƙimarta da kuma darajarta a bainin dangi ,zata iya rantsewa da Hafizz ya linka Salman kyawu da kyan hali da ɗabi’a a kota wani fanni a rayuwa, Suhailat ta gaza gane hakan Son maso wani ya rufe mata ido ,Hafizz kota ina ya gama haɗewa kekkyawane a jin farko dogon matashi ma’abocin ilhama, kwarjini da cikar zati fari tas da shi daka gansa zaka san cewa hutu ya gama samun tabbatacciyar mazauni a jikinsa ɗan asalin ƙasar Lebanon ne dan su Suhailat en can ƙasar Lebanon ne kakanninsu duk ƴan can ne sune dai da iyayen su a ka haifa anan ƙasar Nigeria , Suhailat mahaifinta ɗan garin Katsina ne mahaifiyarta ce keda jinsi da ƙasar lebon duk da cewa itama anan ƙasar a ka haifeta Momy da mahaifin Hafiz uwa ɗaya uba ɗaya suke .

Story continues below


“Hummm Sisterly angel!”

Hafiz ya katse Suhailat ɗin daga guntun tunanin data afka , cikin ko in kula ta ce “Ya akayi?” 

Murmushin dake fiddo da tsananin kyawunsa yayi kafin ya ce “Yau naga Abeedah ta koma gida da wuri kodai angon ne ya ce ta dawo da wurwuri haka?” 

A kufle Suhailat ta ce “mai ya hana ka tsayawa ka tambayeta ?” 

Suhailat ta ida maganar tana juyawa dan shigewa cikin ɗaki abin da ke damunta kawai ya isheta yanzun nan ta biye ma wannan Hafizz ɗin babu abin da zata yi. 

*************************************
A gurguje plssss🙏(we have alot to see nan gaba .Novel ɗin ko rabin wasan ba’a fara ba gwara muta yi a gurguje dan mukama zaran lbrn ) 

Dukkanin abin da a ka sa wa lokaci dole watan watarana sai lokacin nan yayi .Yau saura kwana biyu kacal a ɗaura auren Sir Salman da Abeedah an kawo kayan laife da duk abubuwan da ya kamata fatan dai Allah ya kaisu ranar da za’a shaida ɗaurin auren su .

Sir Salman zaune cikin motarsa yana ta zuba uban ƙamshi jiran Abee yake wacce ya aika kiranta dan duk wayoyinta a kashe suke . 

Knocking ɗin windon motar yaji hakan ya sashi zuge glass ɗin windon, kekkyawar fuskarta ya bayyana a kan fuskarsa murmushi ya sakin mata haɗida buɗe mata murfin motar ta shiga . 

ABEEDAH ! amare tayi kyau sosai fatan jikinta sai sheƙi da yalƙi yake tayi ɓulɓul abinta gwanin ban sha’awa jikinta na fidda wani sihirtaccen ƙamshi mai daɗin gaske taƙara haske sosai har wani yellow yellow take yi.Hannayenta da ƙafafuwanta sun sha zanen fulawa baƙi da jaa wanda yayi matuƙar yi mata kyau abinka da farar mace zanen fulawa na matuƙar yi masu kyau! 

Hannunta Sir Salman ya kama dukkaninsu sai da suka tsinci kansu a cikin wani irin  yanayi barin ma Abee wacce bata saba da hakan ba ,kusantota sosai Sir Salman yayi har suna shaƙar numfashin junan su Abee kam jikinta ne ya shiga rawa ganin yana shirin haɗe bakinsu waje ɗaya kiciniyar kwatan kanta ta shiga yi shikuwa Sir Salman sai faman shige  mata jiki yake yana shaƙar ƙamshin jikinta Abee kam jikinta taji yafara mutuwa tanata mutsi mutsin hanasa haɗe bakinsu waje ɗaya ganin bata da niyyar basa haɗin kai ya sa shi janƴe jikinsa daga nata ya na jan tsaki ya ce “ke dalla gafara mai ban sani ba ?kina wani min yanga kina nuna baki son taɓaki da nake ,ki sani ni son ki nake! Inda nayi niyyan yaudarar ki da tuntuni na yaudare ki toh ni son ki nake auren ki zanyi ” 

Ya ƙarasa maganarsa yana kallo Abeen wacce keta faman sauke ajiyar zuciya ,sam kwata kwata Abee bata jin daɗin irin abubuwan da yake mata ,kawai dai tana danne zuciyarta ne bata cimasa mutunci don tana son sa. Bazata manta ba ranar da a ka samu su rana yake tambayarta wai mainene size ɗin bra ɗin ta da pant ɗin ta ? Abin ya matuƙar bata kunƴa dan a speaker tasa shi ranar suna waya Mancy da Farhana suna zaune nesa da ita amma ta tabbata sunji waskewa kawai sukayi.

“Jeki toh dama nazo ganinki ne kawai tunda kin hana kuma shikenan mu kwana lafiya” 

Ya ƙarasa maganar yana juya mata baya .Kafe sa da idanuwanta Abee tayi tana mamakin ƙarfin hali irin na Salman shi sam baka iya masa ,toh so yake ta sake jikinta da shi yayi yadda yake so tun kafin ayi auren ko mai yake nufi?

“Sir Salman kwallon ɗan iska ne kawai dai ya iya takunsa ne shi yasa bazaki taɓa sanin wannan halin nasa ba” 

Maganar Surayyah ta faɗo mata saurin kallon sa tayi shin ta gasgata maganar Surayyah ne ?kodai kawai dan yaga ita zai aura yasa yake mata haka?dan taga yawancin samarin yanzun haka suke ma emmatan su!……….. 

  “Baki ji mai nace bane?”
Maganarsa ya kuma katseta daga tunaninta. 

Saurin buɗe murfin motar tayi ta fita abinta jikinta duk amace .Shi kuwa Sir Salman ɗauka yayi in ya mata haka zata basa haƙuri ta sake masa jiki koda ɗan romancing ɗin ta yayi dan tagama tada masa sha’awarsa yanzun dole sai dai yaje wajen Surayyah dan yasan ita kaɗai zata iya gamsar dashi a wannan lokacin. 

Story continues below


*************************************
“Wai ke Abeeda shin kashe kanki kike so kiyi ne?Kina jin dai abin da Malamin can ya ce.Ya ce  tabbas akwai rabo tsakanina da Sir Salman! Duk wanda ya yi k’ok’arin raba wannan rabon zai mutu! Me yasa ba za ki saduda ki hak’ura da auran Sir Salman ba, Abeedah?” 

   Suhailat ta’ida maganarta tana mai kafe Abeedah da kwala-kwalan idanuwanta. A lokaci guda kuma tana jiran fitowar amsarta a bakinta, wacce hankalinta gaba d’aya yana ga Suhailat d’in. 

   Sauke ajiyar zuciya Abeeda ta yi ,ta ce:  “Haka Allah ya k’addara lamuransa a gare mu, dan haka su waye ne mu da har za mu yi kutse cikin lamuran ubangiji? Ina ganin ki fidda zantukar wannan Malamin daga cikin kwakwalwarki dan shi ai ba Allan musuru bane da zai san gaibu! Da ace akwai aure tsakaninki da Sir Salman da a yau da ya rage saura kwana biyu kacal a d’aura auren mu ,da dake za’ayi ba ni ABEEDAH ba!” 

Abeedah ta sauke maganarta cikin wata irin natsuwa, tare da dafe kanta tana ya mutsa fuska. Kafin Suhailat ta kuma samin bakin magana,ta d’ora da cewa”kinga yin hak’uri da manta Sir Salman cikin rayuwarki ,shine sauk’in lamuranki Suhailat .And lastly ki daina yarda da duk wani abu da malaman duba zasu fad’a maki dan ba suda ilimin komai face wanda Allah ya nufe su da sani.” 

Abeedah ta sauke maganarta,tana mai kafe k’awarta da idanuwanta,dan son sanin yana yin yadda Suhailat zata amshi amsar tambayar data bata,wanda kuma Suhailat d’in da kanta ta buk’aci hakan. 

Shuru kaman mai nazari Suhailat tayi tana mai waswasi da zuciyanta,bata so sam ta gasgata abin da zuciyanta ke ayyana mata game da Abeedar,ni sawa sosai Suhailat tayi,murmushi d’auke a fuskan nata, ta kuma jefo ma Abeedar tambayar dake matuk’ar cin ranta ,ta ce “Yaushe Zuciyarki ta kamu da son Sir Salman? Kina son Sir Salman ne Abeedah?” 

Kallon kallo suka shiga jefe kawunan su da shi,ko wacce da abinda zuciyanta ke ‘kissa mata, maganar gaskia in Abeedah ta bud’e baki tace bata son Sir Salman tayi ‘karya,hakan kuma idan tace tana son nasa ,ta san har cikin zuciyarta ba tama k’awarta adalci ba,ta yaudara amintakar su da abotarsu,ba kuma tama Suhailat adalci ba,Amman harga Allah tana mugun son Sir Salman ba tasan lokacinda ta fara son Sir Salman ba kawai tashi tayi farat d’aya taji ni’imtacciyar Son sa har cikin sassan ga6o6in jikinta bata tsanmanin cewa zata iya rayuwa ba tareda Sir Salman ba,dan tana masa wata kaliyar so tsaftacciya. 

   Shin mai ya kamata ta gaya ma Suhailat?eh tana Son Sir Salman komai? ! 

   Ta sama zuciyarta na jefo mata wannan tambayoyin data gaza sanin amsoshin su,muryar Suhailat taji tana cewa”kin yi shuru baki ban amsata ba Abeedah ” 

Suhailat ta ida maganar tana mai kamo hannayen Abeedan daya sha zanen fulawa bak’i da jaaa wanda ya zaunu d’as akan fatar hannayen nata,sai shek’i da kyau suke fiddawa, had’e hannayen Abeedan cikin nata Suhailat tayi sannan ta d’a goda kanta ta kafe Abeedan data tsaya kallan yana yin da Suhailat ta sark’e hannayensu a tare,ta san mai hakan ke nufi,ta san dalilin da yasa Suhailat d’in aikata hakan,wannan yana d’aya daga cikin abinda suke matuk’ar girmamawa acikin tarayyar abotarsu,hakan na nufin Suhailat na son ta fad’a mata iyakar gaskiyar ta,bata son ta 6oye mata komai ,ko kuma ta mata k’arya,tasan tabbas sark’e hannayen juna da Suhailat ta musu na nuni a kan cewa lallai lallai tabbas ta fad’i abin da ke cikin zuciyanta.had’e idanuwansu waje d’aya Suhailat tayi suna kallan juna ido cikin ido dan gano iyakar gaskiyar kowa a kwayar idanuwansu,Abeedah ba zata iya jurar wannan kallan ba,ta san k’ilan zuciyarta ta k’aryata abinda take son fad’i,ta san bai zama dole ta fad’i gaskia ba,amman fad’in gaskiyar a wannan lokacin yafi,gwara ta sauke wannan hakkin ta fita daga cikin hakkin Suhailat d’in.Tsintar bakinta tayi yana fad’in:”da ban son sa da bazan aminta da auran sa ba!” 

Abeedah ta ida maganarta tana mai saurin cire idanuwanta tare da kaudasu gefe,dan bata son ganin yana yin da Aminiyar tata zata tsinta kanta a ciki ,gwalalo may’an idanuwanta waje Suhailat tayi a lokaci d’aya kuma harufan bakinta suka sama damar furta:”What!” 

  Muryarta na karkarwa ta kuma cewa
“Kina son sa fa kika ce?taya?when?how?aina?a wani lokaci?ina sha kin aminta da auren sane dan ke ya nuna yana so bani ba?ashe dama chan ha’inta ta kikeyi?dama kina son sa kika barni cikin duhun daren tsammanin baki ƙaunarsa?I was fool to believe that Ashe ?kin manta cewa ba malami d’aya ko biyu bane suka shaida mana cewa lalle akwai rabo tsakanina da Sir salman BA ko?wanda yayi k’ok’arin rabawa zai iya mutuwa ?have u forgotten all this?uhummm tell me? Mutuwa kike so kiyi komai Abeedah?!” 

  Ta ida maganar cikin sigar lallashi tana mai kafe Abeedar da kallo! 

  “Pls let me be Suhailat,in har ba zaki amince ki yarda da ikon ubangiji ba pls allow me and free me,Aure dai yau saura kwana biyu rak a d’aura shi tsakanina da Sir Salman,in kuma hakan na nufin ranar mutuwa ta ,ba komai am ready to die,bana tsoron mutuwar,kuma is better for u kiyi saurin farkawa daga zantukan wa’innan malaman duban dan wani zubin babu abinda suke fad’a in banda k’arya ke ko annabi bai san gaibu ba! ,bare kuma wa’inda suke rayuwa a duniyan domin shi, dan haka zancen akwai rabo tsakaninku wanda ya raba kuma zai mutu wannan kuma chan ta shafe ku free me pls!” 

Daga haka Abeedaa ta mik’e tabar d’akin fuuuuu kaman zata tashi sama,cike da mamakin Abeedah Suhailat tabi bayan ta da kallo,ta san Abeedah da shegen zafin zuciyan bala’i shi yasa ma tun d’azun take raunana zantukanta dan bata son 6ata zuciyar Abeedan.Nisawa Suhailat tayi sannan tace”tirk’ashi! Any’a zata iya barwa Abeedah sir Salman kuwa? Any’a zata iya sadaukar da soyayyar Sir Salman kuwa? Mutumin da take mutuwar son sa take k’aunarsa fiye da yadda take k’aunar kanta? Tana son Abeeda tsaftacciyar so wanda babu hassada a cikin sa,shi yasa ta hak’ura tanaji tana kallo a kasa auren Sir Salman da Abeedah wanda a yanzun saura kwana biyu rak Abeedah ta zama mallakin Sir Salman,tanaji tana kallo Abeedah zata aure mata rabin rayuwarta wanda dominsa take rayuwa?kuma an haliccesa domin ita ne ba domin kowa ba? A daa ta kwantarda hankalinta kan auran Sir Salman da Abeedah dan a tunaninta maganar malaman nan zasu tabbata ,yanzun kuwa gani take kaman abin bazai yuba yau fa kwana biyu kawai yarage  a ɗaura auren su. 

  Tirk’ashi dole tasan abinyi kafun akai ga d’aura auren Sir Salman da Abeedah,dole ta fallasa wannan sirrin da Abeedar take 6oyema Sir Salman wanda har a yau daya rage 2days bikin su bata fad’i masa ba,kuma ta rok’eta  a kan karta fad’awa Sir Salman wannan Sirrin nata wanda ta 6oye masa shi kad’ai kawai,ta kuma kulle duk wani hany’a dazai sa Sir Salman gano wannan Sirrin! 

  Murmushi tayi ta raya a fili “Dole in dakatar da wannan auren naku Abeedah da Salman,dole Sir Salman yasan wannan sirrin naki da baki son ya sani Abeedah,ki gafarce ni a yau zan karya alk’awarin dana d’aukar maki tunda kema kika 6oyemun son dakike ma wanda kika san nake mutuwar so a rayuwata “! 

  Daga haka ta saki wani lallausan murmushi mai cike da ma’anoni  dayawa a ciki!  Ta mik’e ta d’au inata inata ta kutsa cikin jama’an dake kai kawo cikin gidan (mutanen biki) tabar gidan gaba d’aya ba tareda ta sake naiman Abeedan ba,burinta kawai ta ganta gaban Sir Salman ta warware masa zare da abawa! Ta fiddasa a duhun da yake ciki a kan matar da zai aura! Ya ka mata ta sanar da shi wacece matar da yake son aura! Dole ta nausar da shi hakan dan kuwa faɗa masa wannan sirrin shine kawai zai sa Sir Salman fasa auren Abeedar.

    Gidan cike yake Maƙil da mutane ƴan unguwa wanda rabin su ba don Allah suka zo ba, leƙen asirine kawai ya kawo su,  ƙawayen Abeedah rabin su sun hallaro, mutane sai kai da kawo kawai suke. anata aikin abincin waleemah wanda za ayi gobe idan Allah ya kaimu. 

  Kamar wanda a ka jefo daga sama ya shigo cikin gidan yana ɗaga murya yana surutai ,hankulan kowa dake cikin gidan ya koma kansa ana kallon sa cike da mamaki. 

   “Abee wannan hargoguwar faaa ?kamar ana faɗa ko?” Hayfah ta wurgoma Abee tambayar,wacce itama a dai dai wannan lokacin ta kasa kunnuwanta dan jin maike faruwa. 

  “Kunga kaman muryan Sir Salman nake ji faa?” Abee ta ida maganar tana mai miƙewa zumbur da zummar barin ɗakin ,ƙawayenta dake cikin ɗakin suka mara mata baya da sauri saurin su suka ƙarasa tsakar gidan . 

  Tsayawa cak Abee tayi tana ƙare masa kallo cike da mamakinsa ,kafesa da idanuwanta tayi sa’annan ta kasa kunnuwanta tana mai sauraren kalaman dake fitowa daga bakinsa ,kunnuwanta basu gama shaida abin da yake faɗi ba har sai da ta tsinkayo muryarsa yana faɗin “Allah ya kiyaye,Allah ya sutura na aura yarinƴar da ba’a san asalinta ba! wacce ake zargin ma iyayenta zaman dadiro suke yi a haka suka haifeki saboda kaf unguwar ku babu wanda ya bada shaidar cewa ansan asalin ku  rana tsaka a ka ganku kunzo kun yada zango cikin unguwa .Toh wlh bazata saɓuba bazan aura shegiya ba  mara asali ,a yau da’a ce ƙawarki bata zo ta sanar dani wacece ke ba ,da na cutar da kaina na cutar da ƴaƴana saboda haka Abeedah Usman na fasa Auren ki !” 

  Sir Salman ya ida maganarsa yana mai kuma jin zafin Abeedar har cikin ransa. 

Abee kuwa duk cikin maganganunsa babu wanda yafi firgitata da ɗaga hankalinta kaman inda ya ce  *Abeedah Usman na fasa auren ki*! 
Sosai Wannan maganar take barazanar bugar da zuciyarta da tsayar da numfashinta
Babu abin da keta yawo a cikin kwakwalwarta face wannan maganar, wanda hakan yasa tayi baya tana  shirin zubewa ƙasa, da sauri ƙawayenta suka riƙota, fuskokin su cike da mamakin maganganun Sir Salman . 
Ta kasa dauke idanunta daga kallonsa yayinda take jin komai kamar a mafarki, domin sanin irin soyayyar da Salman ke mata bazai saka don kawai ance batada asali yace ya fasa aurenta ba. Dangantata da Suhailat tayi da shegiya kuma zata barta ne ga Allah, don tasan tabbas zai saka mata. 

tsinkayo muryarsa ta kuma yi yana mai ci gaba da cewa “Bazan auri mara tushe ba ,a fiddomin da kayayyakina gaba ɗaya ,duk abin da a kasan an taɓamun a cikin lefen  a mayarmun komi da komai na fasa auran bazan auri shegiya ba”.

  Jan jikinta tayi daga riƙon da ƙawayenta suka yi mata ta ɗan tako kaɗan zuwa tsakar gidan, waigowa tayi ta kallo inda Mancy ke zaune hawaye tagani yana zarya  bisa ga kumatun mahaifiyarsu wani abu taji ya caki ƙirjinta “Mancy kuka?Salman yasa Mancy zubarda tsadadden hawayenta?” Ta raya hakan a cikin zuciyarta nan danan zuciyarta ta shiga tafarfasa duk inda ta waiga babu abin da take gani face gulmanmaki da ƴan unguwarsu suka shiga yi a kan su ,Suhailat tagama da ita bata taɓa tsammanin cewa Suhailat zata iya aikata mata haka ba kai ɗan Adam abin tsoro ne . 

Share gumin dake keto  mata asaman kai tayi ,kafin ta haɗiye wani zazzafar yawu lokaci guda kuma ta haɗe rai tamau ta dawo asalin Abeedar ta ,wannan mai zafin ran da rashin fara’a ,hankulan kowa ya koma kanta harta shi Salman ɗin sai da ya ɗan tsorata da ganin yanayin da Abeen ta rikiɗe tadawo lokaci ɗaya, cikin zafin rai ta kutsa cikin langalangar tsakar gidan su da gudu gudu ta ƙarasa shiga cikin falonsu uwar ɗakan su Abbi ta buɗe ta shiga, inda a ka ajiye akwatunan  da sauran kayan lefen ta nufa cikin azama ta shiga saukoda akwatunan ɗaya bayan ɗaya, har ta diresu tas a tsakiyar ɗakin kafin ta shiga jan akwatunan tana fiddosu falo sai data tabbatar ta fiddo da komai data san mallakinsa ne sa’anan ta shiga fito dasu tsakar gidan tana jefa akwatunan a ƙasa ,hankulan kowa ya tashi musamman Mancy tasan halin ƴarta tsaf inkana son ganin tashin hankali toh kace da ita bata da asali In ranka yayi dubu toh Abee saita mugun ɓata shi . 

Story continues below


  Wurgo akwatunan kawai takeyi waje ,babu abin da kake ji face ƙarar wurgin akwatuna sai da ta tabbatar ta wurgo da komai tas a tsakar gidan ,sa’anan tafito ranta na ƙuna ta ƙaraso daf da Sir Salman ,wanda ya shafa’a da ƙare mata kallo dan bai taɓa ganin Abee ta fusata irin haka ba ,nunasa da yatsanta da tayine ya dawo dashi daga tunanin daya faɗa cikin kakkausar muryata ta soma magana “koda bani da asali ni ƴar mutunci ce kuma ƴar halak ,iyayena da aure suka haifemu kaf ɗin mu ,kasani in kace iyayena zaman dadiro suke yi kaima zaman dadiro ka keyi da ƴar wasu!” 

Abeee ta ƙarasa maganar tana banko mai wata uwar harara kafin ta ci gaba da cewa “kana mamakin yadda a kayi na sani  ko?hhhhh toh ba abin mamaki bane yadda ka ce  nima ƙawata ce taje ta fayyace maka sirrina ,kaima haka zalika karuwarka da ƙafafunta ta kwaso tazo ta sanar dani mummunar ɗabi’arka, a wannan lokacin ina zata hassada ce kawai take yi maybe tana cikin matan dake fola maka,tirr da hali irin naka wlh gwamma da Allah ya ƙaddara ka ce ka fasa auren nawa ,dan Allah ba azzalumin bawan sa bane yasan am very pure shiyasa ya ƙaddaro rabuwar mu ,dan bazan taɓa auren fasiƙi mazinaci ba ,Allah ya rakata ki gona ka sunguma kayayyakinka ka fice mana a gida mugu azzalumi fasiƙi mazinaci”. 

  Abee ta ƙarasa maganarta cikin fushi tana mai da ɗa ƙundumama Sir Salman ashar dan ya mugun ɓata mata rai har sai da Mancy da kanta ta taso ta zo ta janyeta a wajen kafin ta sarara mai. 

  Shi kuwa gogan naku tsananin mamakin yadda a kayi tasan da wannan sirrin nasa kawai ya tsaya yi ,shin a yaushe ma Surayyah tazo ta sanarwa Abeen bai sani ba haka ? Ganin mutane sun fara mai ƙusƙus ana nuna sa da baki, yasa shi saurin soma sunkutar akwatunan yana fita dasu ransa a matuƙar ɓace ,Kwashe kayan yayi tas ba tareda sake kallon ko damuwa da jama’ar dake  wajen ba, ya tattara komai nasa ya zuba a mota, Motarsa yaja yabar unguwar ransa a matukar jagule. 

*************************************** 

  Kuka take tayi kamar ranta zai fita Allah na kallo har cikin ranta take mugun son Sir Salman ,tana son sa tana ƙaunarsa ,a kan sa tafara sanin mainene So ,shine First love ɗinta bata taɓa son wani ɗa namiji kwatankwacin yadda ta so Sir Salman ba,Allah na kallo ɗazun ma da tayi mai rashin mutunci danne zuciyarta tayi ,ta ingiza zuciyarta shi yasa ta sama damar mai da masa martani, wlh tana son Sir Salman bata tunanin cewa daidai da rana ɗaya tak zata iya rayuwa ba tareda shi ba,*hasbunallahu walni’eemal wakil* kawai take ta faman nanatawa a cikin zuciyarta ,sosai addu’ar ke sanyaya zuciyarta ,Hayfah da Mancy da sauran ƙawayenta ne zagaye a kanta suna bata baki , ringing ɗin wayar Hayfah ne ya ɗan katsesu, bakin Hayfar har yana wani karkarwa wajen faɗin sunanta Suhailat! ta faɗa sunan fuskarta ɗauke da mamaki ,jin sunan Suhailat da Haifa ta ambato yasa Abee da sauran ƙawayenta da Mancy saurin waigowa suna kallon Hayfar ,wacce a daidai Lokacin ta ɗaga kiran Suhailat ɗin tasa wayan a speaker,sautin ƙelƙetan dariyarta ne yayi azamar dabaibaye speakar wayan sai data yi ma ishi kafin ta tsagaita cikin sigar maganar dariya ta ce “hummm Hayfatu! Ykk ya shirye shiryen biki? Ƙelƙecewa ta kuma yi da dariya sa’annan ta ci gaba da cewa “ko nace ya jimamin fasa bikin ƙawar tamu?Allah Akbar nasan yanzun haka My Abee tana kuka ko?ouch sorry Abeee kar kiga laifina, wlh nayi hakan ne for ur own good, ke kinsan abin da ke tsakanina da Sir Salman ,kin sani sarai toh mai yasa zan bari ki hallaka kanki ki mutu a banza?,wlh kema kinsan ina sonki Abee bazan taɓa bari wani abu ya cutar dake ba,nasan kina mamakin ta yadda a kayi Sir Salman ya tsaya ya saurareni ko? hhhhh toh zan faɗa maki ,kin tuna jia da muka rabu ko sallama ban maki ba na kama hanyata na tafi ryt ?,toh babu inda na zarce sai a offishin Sir Salman Amma fa Kam nasha wahala kafin ya yarda ya tsaya ya saurareni  ,nafara zayyane masa lbrn ki da sirrinki na rashin Asalinki ,har ana tunanin ma zaman dadiro iyayenki suke ta sanadin haka ma suka haifeki ,na ci gaba da ce mai Sir yarinƴar da kake so ka aura ko wani ɗan adam a duniya yana son ya aura wacce take da asali ,wacce aka haifa ta hanyar aure ba hanƴar alfasha ba ,Abee da kake kallo ba ta aure a ka sameta ba shi yasa a kullum kake ganinta a wancan lokacin cikin fushi da ƙunar rai ,kai kuma a sanadiyyar hakan ka fara sausaya mata daga tausayi ka riƙiɗe da fara son ta.Kayi tunani mai kyau Malam shin ƴar halak ya dace ka samama ƴaƴanka ko kuma shegia mara asali?kar ka manta da cewa duk daren daɗewa fa ko kun ɓoyema yaranku society baza su ɓoye masu ba ,in one way or the order yaran nan zasu zo su fahimci asalin mamansu, toh a lokacin wa gari ya waya?dakai fa zasuyi kuka bcx U Are the one who choose her as their mother …….” 

Story continues below


   Tsagaita tayi da maganarta sa’annan ta ja dogon numfashi kafin ta ci gaba da cewa “sosai nasan kalamaina  suka ratsashi ,a wannan lokacin bai nunamun cewa yaji maganar tawaba ,dan ma a lokacin korata yayi a office ɗin harda kirana monster! but guess what ?hhhhh ban tashi sanin cewa maganar tawa tayi tasiri a kan sa  ba har sai yau da ya kawo kayan lefenki gidanmu !Abee duka kayayyakin lefenki yazo ya diresu a gidan mu ya roƙeni dana amince na aure sa jibi ,dan yace tabbas baza’a fasa ɗaurin aurensa   ba ,yanzun rana itayau in sha Allahu za’a  ɗaura mana aure duk da iyayena sunƙi yarda but babu yadda suka iya dani dole su bari a ɗaura auren ,dan haka kuta yamu murna da fatan Allah yama auren mu albarka tareda zuriya ɗayaba kema Abee Allah ya baki miji nagari bye” 

Daga haka kawai suka ji ƙit alamun ta kashe wayar. 

  Kallon kallo kawai suka shiga yima junansu a cikin ɗakin ,Abee in hankalinta yayi dubu toh ya gama tashi ,aduoi kawai take ta nanatawa a zuciyarta dan batason zuciya ya ɗebeta tazo ta aikata abin da zata yi dana sani a kai ,”Suhailat ,Suhailat ,Suhailat! “Ta riƙa nanata sunan Suhailat yafi a ƙirga .
A wani fannin bata ganin aibun Suhailat ,dan dama tuni an sheda masu Suhailat itace matar Salman, mai yasa ma tun farko ta bari soyayyar Sir Salman ya rinjayeta ,yanzun ya zatayi?taya zata fara cire son sa a cikin zuciyarta?taya zata iya rayuwa ba tareda shi ba? ,Tana buƙatar wannan amsar ,tana son zuciyarta ta amsa mata wannan tambayoyin ,in ba haka ba gab take da kamuwa da ciwon zuciya (heart diseases). 

*********************+*************** 

  Kan kace kobo tuni mutane sun watse ,dama su ba dangi ba bare a ce ansamu wa’inda zasu kwana, ƴan unguwane kawai dama da ƙawayen amayar da maƙota ,suka hallaro taya murnar bikin wasu dan Allah suka zo wasu kuma dan ɗauko gulma wanda a yau kam sun samu in sun sama dama ma zasu iya bugawa har a jarida abin buƙata ya samu.

Bayan kwana biyu 

  Yau take jummaat babbar rana a yau 12 ga watan rabiyul Auwal shekara ta dubu ɗaya da ɗari huɗu da arba’in da ɗaya ,bayan hijirar fiyayyen halitta (1441 AH) a ka ɗaura auren Suhailat Yusuf Maitama da Salman Ibrahim ɗambatta ,a kan sadaki naira dubu 50 sai fatan Allah ya basu zaman lfy da zuriya ɗaya ba .Yau take Sallah a wajen Suhailat dan har azumi Bakwai tayi alƙawarin yi dan Allah ya gama cika mata burinta ,a yau ta mallaki abin ƙaunarta cikin ruwan sanƴi ba tareda tasha wani wahala ba ,bakinta har kunne tsaban farin ciki.(Allahu yasa ki daure a haka #Suhailat)
***************************************

  Abee kuwa koda zancen auren Suhailat da Salman  ya riske kunnuwanta ji take ina ma a ce mutum yana roƙon mutuwa kawai zata zo ta ɗaukesa, a kwana biyun nan kacal kawai duk ta fige ta rame har tafara wani duhu duhu ,bata cin abinci ruwa kawai take sha Mancy da Abbi da ƙannenta kai harta da moƙotansu sun yi mata lallashin duniyan nan amma a tafau taƙi sauraren koda mutum ɗaya ,rufe kanta takeyi a ɗaki ta disgi kukanta son ranta ,dan Allah na kallo wlh ita kanta tasan tana mugun son wannan lekcaran son da bata da yaƙinin cewa zata sake yiwa wani ɗa namiji a duniya .Yauma anyi juyin duniyar nan koda ruwan a samu tasha tunda safe ,rana har dare taci wani abun fafur taƙiya ,bayan Abbi ya dawo  daga aiki ya shiga har ɗakinsu da kansa ya kirawo ta suka fito a tare duk idanuwannan nata sunyi luhu luhu tsaban kuka ,wuri tasamu ta zauna Abbi ma yazauna Mancy a gefensa Farhana da Haris ma suna zaune can gefen Abee ,lallashinta Abbi ya shigayi dan ganin taci abincin dayasa Mancy ta ɗebo mata tasa a gabanta ,amma fafur Abee taƙiya daga ƙarshe ma dataga sun takuramata kawai sai ta fasa wani uban tsawa daya gigita dukan su ,cikin ɗaga murya tamkar wacce bata cikin hayyacinta ta soma magana “ku kuka cucemu ,ku kuka zaluncemu!,kune manƴa manƴan wa’inda kuka cucemu! tun ina yarinƴa na tashi a cikin ƙunci ,dalilin dayasa na tashi mai zafin rai da zafin zuciya kenan,ba ku  kukasa na koyo wannan halayyan ba ?Mancy ke bakida zafin rai kaima Abbi bakada zafin rai! ni kun haifeni mai zafin rai saboda baƙin cikin mutane tun ina yarinƴa a ke cemun banida ASALI iyayena ba’asan daga inda suke ba ,da’an ganmu ansan mu ba zubin en ƙasar nan bane shiyasa a keta ƙyarar mu ana zargin wani irin zama kukeyi a tsakanin ku ?ku kuka jazamun gashi yanzun zanyi aure ina mugun son mutumin nan but halinku yasa a ka fasa aurena ya fasa aurena a gaban ɗunbin jama’a ,ana saura kwana biyu tak a ɗaura mana aure yazo ya kwashe komi nasa ya ce ya fasa auren ,a yau yau ɗin nan  daya kamata a ce dani a ka ɗaura mai aure rashin asalina yasa aka daura masa aure da ƙawata aminiyata” 

  Abee tana maganar tana haki tsaban ruɗu da tashin hankali bama tasan tana dannoma iyayenta wannan maganganun ba zuciya ta ɗebeta sheɗan na kuma ingiza ta “ku faɗamun ku suwaye ne ? Shin zaman Allah da Annabi kukeyi? zaman aure ku keyi ko kuwa zaman da ake zargin ku kuna yi?……………. 

   Tas taji Mancy ta wanke ta da mari wanda sanadin hakan yasa tayi saurin haɗiyar sauran kalamanta ,tana dafe kuncinta, cikin zafin rai ta ɗago ta kallo Mancyn wacce ke binta da kallon mamaki cikin ƙunar zuciya ta ce “saboda na faɗa gaskia ?so kike mu ci gaba da kwasar baƙin ciki?baƙin cikinku ya kashemu? Ku faɗa idan har kunsan kunada asali ! Ku suwaye ,wani irin zama kukeyi ?da aure kuka same…………. 

  Nan ma Mancy ɓata bari ta kai ayaba ta kuma ɗaga hannunta da zummar sauke su a saman fuskar Abeen ,dan tana tsammanin Abee bata cikin hankalinta Abbi ne yayi saurin riƙe hannun Mancyn ,waigowa Mancy tayi ta kallo Abbi shi kuma sai ya girgiza mata kansa kafin ya ce “kada ki manta Haleemah duk abin da kayi ma iyayenka kai ma za’a yi maka ,wannan abin da muka shukane muke girbewa ki barta tayi mana abin da zata mana son ranta ,domin muma haka muka ma namu iyayen ,shiyasa Abee take rama musu a yanzun!” 

Jikin Mancy ne yayi sanƴi kawai ta fashe da kuka mai tsuma rai ,duk da haka Abee bata sadudaba ta ci gaba da yaɓama iyayenta baƙaƙen maganganu ,daga ƙarshe ma kitchen ta wuce ta ɗauko petur ta fito ta shigo cikin falon ,ta tsaya a gaban iyayen nata dake ƙare mata kallon mamaki ,cikin ƙunar zuciya ta ce “wallahi wallahi ko ku gaya mana asalinmu, ko kuma dukkanmu na ƙonamu a cikin ɗakinan ,kunsan inada zafin ran da baku kaɗai ba ma duka unguwar nan zan iya ƙonawa ,saboda an ɓatamun rai da bazan taɓa iya haƙuri ba!” 

  Numfashi Abbi ya sauke kafin ya ce “kiyi haƙuri ba sai kinkai da ƙonamu bama ,zaki san ko ke wacece domin lokaci yayi da zaki san komu suwaye ne! Ki kwantar da hankalinki ,kiyi haƙuri kije ki mayarda wannan petur ɗin ……. 

  “Abbi bafa zan mayar ba har sai kun faɗa mana mu su waye ne ?” 

  Mancy kuwa saurin rungumar Abee tayi ,tasan dolene ƴarta ta naimi sanin asalinta ,tunda a dalilin hakan ne yasa a ka fasa aurenta Allah kadai yasan wani kalan ƙunci take fuskanta a cikin zuciyarta . 

  “Mancy ki sake ni ,nace ki sake ni ,babu abin da zaku faɗa mun ko ku yimun har sai kun faɗa mun asalinmu ,wani irin zama kuke ?” 

  Sakin ta Mancy tayi sa’annan ta shiga ƙarema Abeen kallo ,kallo ɗaya zaka mata ka fuskanci cewa danne zuciyarta kawai take tana yaɓama iyayenta maganganu ,basu kai har cikin zuciyarta ba. 

Saka hannu Mancy tayi ta kwace galan ɗin petur ɗin ,ta ajiye gefe kafin ta ce “zan gaya maki komu suwaye Amma sai kinci abinci ” 

“Mancy bazaki gane irin zafin rai da nake da shi bane bazaki gane irin ƙunar……….. 

Maganar Mancy ya katse ta daga ƙarasa maganarta ta ce “koma dai menene inason kici abinci kafin In gaya maku Asalinku” 

Cikin ɗaga murya ta ce “nagaya maki bazan ci ba har sai kin faɗa mun asalinmu” 

Wai yau ƴar data  haifa ita ke ƴaɓa mata maganganu son ranta?ƙare ma Abeen kallo tas Mancy tayi, kafin ta girgiza kanta tana mai tunowa itamafa kusan hakan ta yima iyayenta. 

  Jan hannun Abeen tayi ta zaunar da ita, ta jawo su Farhana wanda suka ɓingire da kuka ganin halinda yayarsu take ciki ,suma ta zaunar dasu ku sa da Abeen, kafin itama ta zauna a tsakiyar su Abbi ya zauna a gefen su . 

Dogon numfashi Mancy ta saki kafin ta soma basu Labarin Asalinsu kaman haka : 

  “Ni ɗin nan da kuke gani ƴar gidan..


   Dogon numfashi Mancy ta saki kafin ta soma basu labarin asalinsu kamar haka: 

   “Ni ɗinnan da kuke gani ƴar gidan Alhaji Abubakar Gidado mai Dala ce” 

  Baki sake Farhana da Abeee suka shiga kallon Mancy, fuskokinsu cike da mamakin maganar Mahaifiyarsu . 

   Bakin Farhana na karkarwa ta ce “Mancy ke ƴar gidan Alhaji Abubakar Gidado mai Dala fa kikace?wannan babban ɗan kasuwan?babu inda ba’a san da shi a faɗin duniyar nan, ina tunawa da current affairs din mu na makaranta, shine mutum na 5 da yafi kowa kudi a africa. Babban mai kudi ne, Kamfanoninsa sunfi a kirga, su kamfanin taliyane, makaroni, shinkafa, magie, indomie etc. Babu wani wanda za’a ce bai san Alhaji Abubakar Gidado Dala ba” 

   Jinjina kai Mancy tayi, tana sakin murmushin da yafi kuka ciwo kafin ta ci gaba da cewa “tabbas shi nake nufi, kun ganni nan ?nice ƴarsa guda ɗaya tilo, kin san ana cewa ba shida ƴa ryt?toh ni ƴarsa ce, shi ya haifeni, ni jininsa ce.” 

    A razane Abee da Farhana suka ɗago suna kallon mancy, Haris kuwa yayi ƙanƙantar da zai iya fahimtar abin da  Mancy ke Fada, abin ya mugun ɗaure masu kai Mancy jinin Alhaji Gidado mai Dala ce?” Shine tambayar da ko waccen su zuciyarta ke ƙissawa. 

  Murmushin yaƙe Mancy tayi sa’annan ta ce “kingani ?kina mamaki ko?, toh ni ƴar Alhaji Abubakar Gidado Dala ce kuma labarin nan da zan baku a yanzun labarine mai tsawon gaske, amma kafin nace komai tunda na gaya maki wanene mahaifina kici abinci toh” 

  Mancy ta ƙarasa maganarta tana kallon Abee wacce tsananin mamakin abin da Mancy ta faɗa yasa ta kasa motsawa, girgiza kai tayi kafin ta ce “Mancy ya za’ayi kice ke ƴar wannan mutumin ce ?mutum mai daraja da ƙima wanda kusan Mutanen duniya ta san shi ,sa’annan ke ki dinga rayuwa a irin wannan gidan!?” 

   Abeee ta ida maganar cike da mugun mamaki ,nisawa Mancy tayi kafin ta ce “kin taɓa ganin fuskarsa?, Girgiza kai Abee tayi alamun a’a bata taɓa ganin sa ba. Mancy ta ci gaba da cewa “da kin taɓa ganin fuskarsa da bazaki taɓa mamaki ba a yanzun dan na gaya maki mahaifina ne,domin fuskata fuskarsa,babu abin da ban ɗauko na shi ba sai farin mahaifiyata.” 

   Shiru Abee tayi tana nazarin wani abu kafin ta ɗago ta ce “Mancy wannan maganar ko gaskia kika gaya mun ?” 

  Mancy ta ce “ga Abbin ki nan tambayesa” 

  Da sauri Abee ta waigo ga Abbin ta, shi kuma sai ya ɗora da cewa “mu iyayenki ne zamu miki ƙarya?abin da ta gaya miki haka ɗin ne shine mahaifinta ,shi ya haifeta kuma sanadiyata ne ta rabu da shi , sanadiyyar soyayyar da muka yi a tsakanin mu.Tunda an gaya maki kici abinci za’a baki labarin in full”. 

   Abbi ya Ida maganarsa yana nuna mata abincin dake gabanta ,ba dan ran Abee ya so ba taja plate ɗin abincin ta soma ci don kawai a ƙarasa bata labarin. 

   Mancy kuma ta mike dan kawowa Abbi nasa abincin, Haris kuwa tuni bacci ya sace shi, Farhana kuwa zaman Jugum tayi, dama ita bata fiye yawan magana ba kamar Mancy. 

  ***************************************
  Sunan Mancy ta kira bayan ta kammala cin abincin,”Mancy ni fa wallahi na matsu ki bani labarin, ya za’ayi kice ke ƴar gidan mai Dala ce ?har yanzun ina mamaki!.” 

   Murmushi sosai Mancy ta yi  sa’annan ta shafa saman kan Abeen kafin ta ce “toh Alhamdulilah, Abee bari na ɗauko miki tahirin rayuwata wanda ya soma kamar haka: 

Story continues below


   Alhaji Abubakar Gidado mai Dala (mahaifina)su huɗu ne wajen iyayensu, Alhaji Abubakar Gidado shine babba sai mai bi masa Alhaji Rufa’i Gidado , Alhaji Yusuf Gidado sai ɗan autan su Alhaji Mahmud Gidado.Dukkanin su ƴan kasuwa ne kuɗin nasu ma a wajen baban su suka gado(inherit),Fulanin mayo belwa ne su (Adamawa state). 

  Mahaifina tunda ya yi aure Allah bai ba shi  haihuwa ba, ƙannensa kuwa da suka yi aure lokaci ɗaya duk sun sama rabo, shi kuwa Allah bai ba sa ba, tunda ya auri uwar gidansa Hajia Shafa’atu shuru shuru har tsawon shekaru 7 ba ta  haihu ba, ya ƙara aure har mata uku suma shuru babu wacce ta haihu, har takai ta kawo ma mata suna kawo masa kansu ya aure su dan kawai su zo su sama abin duniya su sa ya sake su then su kama gaban su, dan duk wacce zai saka sai ya cika ta da alheri. 

  Shi kuma ganin haka sai ya haƙura bai sake ƙara aure ba, bayan ya saki wa’ancan matayen nasa, ya zauna daga shi sai uwargidansa.Kwatsam ana zaman lafiya Hajia Shafa’atu ta tada jijiyoyin wuya a kan dole Alhaji Abubakar sai  ya sake ta dan ta gaji hakanan, babu irin lallashin duniya da bai mata ba amma sam taƙi ta ce a tafau ita dai ya sake ta ,ta gaji itama tana son taga ta haifa yara, In kuma yana so ta ci gaba da zama toh yaje asibiti a duba sa, yana kuka yana lallashin ta, yasan Allah bai ba shi haihuwa ba kuma yaƙi zuwa asibiti a duba sa saboda yana tsoron kar a gaya mai a ce bazai haihu ba .Ganin haka sai kawai ya sake ta……… 

  Ranar da ya saki uwargidansa a ranar suka tafi ganin ƴan uwan baban sa a can rugar mambila, akwai wani ƙanin kakansu a can rugar da ya rasu suka tafi gaisuwa. 

   A kan hanƴar su ta tafiya, sunzo daidai mambila suka ga wani bafullatani ya riƙe hannun wata yarinƴa yana ta dukan ta, kana ganin su zaka san cewa irin Fulanin nan ne na cikin daji masu zama a cikin duwatsuna, yarinƴar ma kana ganinta zaka san bata wuci shekaru 10 zuwa 11 ba, ganin wannan al’amarin sai ya basu mamaki gashi dama wurin babu titi can cikin daji ne, suma sai da suka a jiye motar su suka soma takawa a ƙasa. 

    Da hanzarin su suka ƙarasa wajen wannan bafullatani, cikin ɗaga murya Mahaifina ya ce “ha’ah mai yasa kake dukan ta?” 

  Tsayawa ɗan fillo yayi yana ƙare masu kallo daga sama har ƙasa kafun cikin Hausar sa ta ƴan fulani ya ce “dun Allah dun annabi ku ƴan mafiya (ma tafiya)ne?” 

  Kallon sa sosai suka yi lamarin sa ya soma basu mamaki. Har Alhaji Mahmud zai yi magana sai Mahaifina ya dakatar da shi sa’annan ya ce “eh matafiya ne mu” 

  Cikin jin daɗin amsar Mahaifina ɗan fillo  ya ce “yowa tazo gidan shauki,wannan yarinƴar zan siryar muku da ita,bata jin Hausa nine nake jin Hausa!” 

  Cikin mamaki Mahaifina ya ce “toh kai mai yasa kake son siyarda ita?” 

Ɗan jim ɗan fillo yayi kafin ya nisa ya ce 
  “Annoba she ita a rugar mu, ta zame mana annoba idan bamu rabu da ita ba toh annoba bazai taɓa kyale mu ba” 

  Kallon yarinƴar Mahaifina yayi sosai kafin ya maida kallonsa wajen ɗan fillo ya ce “toh nawa zan baka ka sayar mun da ita?” 

  Ɗan fillo cikin ƙaguwa ya ce “Ni na baku shauta (kyauta) ma ku tafi da ita, har abada kuje ku fille mata kanta” 

  Ita ko ƴar fillo sai mutsitsike idanu take tana share hawayen dukan da ɗan fillo ya yi mata . 

  Mahaifina kuwa lamarin su ya mugun basa mamaki, hakanan kawai yaji zuciyarsa tana ingiza shi a kan ya tafi da yarinƴar, dan haka ya ciro dubu biyar ya miƙa ma ɗan fillo cikin daburcewa ɗan fillo ya amsa kuɗin yana washe jajayen haƙoransa ya ce “har da kuɗi?toh miyetti” 

  Da hanzarinsa ya juya dan barin wajen, yau kam sun rabu da annoba.Da sauri mahaifina ya dakatar da shi ya ce “a wace ruga kuke?”
Ɗan jim yayi kafin ya ce “mai ya sha kake tambayata washe ruga nake?” 

Ya ida maganarsa cikin gurɓatacciyar Hausar sa. Waigawa Mahaifina yayi ya kalli yarinƴar da ganinta zaka san tabbas tana da wayau. 

  “Jeka toh kawai” mahaifina ya bama ɗan fillon izinin tafiya aiko harda haɗawa da gudunsa. 

  Bayan tafiyar sa Alhaji ya dubi wannan kekkyawar bafullatanar ya ce “minyaha ko?(muje ko?)”
Maƙale kafaɗa tayi alamun a’a ba zata ba, da kyar da lallashi ta yarda ta bisu suka shiga Mota. 

Kawu Mahmud shike tuƙin motar,mahaifina da yar fillo suka shiga gidan baya suka kama hanya, duk da hanyar da kyar mota ke shiga , hakanan suka riƙa kutsawa ciki. 

  Kallon ƴar fillo mahaifina yayi sa’annan ya ce “noi indema?(yaah sunanki?). Cikin siririyar muryarta ta ce “inde’am Faɗi (sunana Faɗi)” gyaɗa kai mahaifina yayi sai ya ce mata “moi on ɗo fiyete?(wayene wannan da yake dukan ki?)”. 

Share hawayenta tayi kafin ta ce “Baffa am on (Kawu nane)”
Alhaji ya jinjina kai ya ce cikin yaren fulatancin “toh mai yasa yake dukan ki?” Shiru tayi kamar ba zata amsa ba can kuma sai ta fashe da kuka, mahaifina ya ce tayi shiru ta faɗa masa dalili inba haka ba kuma zai mai da ta can rugar tasu.
Cikin rawar muryarta ta ce “dan Allah karka mayar dani zan gaya ma,baba’am on mayi hecitikeƴa be daɗa am  (Baba nane ya mutu shekaran jia,shi da mahaifiyata) dama ni kaɗai suka haifa, bayan sun mutu ranar sadakar bakwai sai naji kawu nai na suka haɗu suna cewa zasu kashe ni,toh shine da suka fito sai suka ce zasu tafi su ɗauke ni suje su kashe ni,toh da suka ankara da cewa naji su ,Ni kuma sai nayi ƙoƙarin guduwa,Baffah Barkindo kuma ya ganni ya kamani yana ta dukana har ya fito dani bakin Titi a kan zai siyarwa matafiya ni suje can su fille kaina.Sai kuma Allah cikin ikonsa waddi on (ya kawoku)duk da bana jin Yaren da kuke yi amma naji a zuciyata taimakona kuke son yi…

Shiru Alhaji Abubakar ya yi ya na mamakin wauta irin ta ƴan fulani, kafin ya nisa ya ce “Mahmud ni wallahi idan a ka ce mun fulanin jeji basu da hankali gani nake yi kamar ƙaryane, sai yanzun na tabbatar lallai fulanin cikin jeji ba su da hankali” 

Mahaifina ya ƙarasa maganarsa yana mai jin tausayin Faɗi har cikin ransa, Baffah Mahmud ya ce “nonnon on kam(hakane kam”. 

Kallon Faɗi Mahaifina ya sake yi sa’annan cikin yaren fulani ya ce “Mahaifin na ki mai kuɗi ne hala?” 

Murmushi tayi kaɗan ta ce “babana shine wanda yafi kowa yawan shanu a rugar,saboda shi mutum ne mai kiwo, yana da sa’an kiwo sosai a rayuwarsa”. 

Jinjina kai Baffa da Mahaifina su ka yi daga nan kuma babu wanda ya sake cewa uffan har suka shigo cikin garin mambila. 

Straight gidan mahaifiyarsu suka wuce,bayan ta musu tarba mai kyau mahaifina ya miƙa mata Faɗi sa’annan ya labar ta mata dukkanin labarin Faɗi, sosai Yape (haka suke kiran mahaifiyarsu) ta tausaya wa Faɗi harda ɗan kukanta ta ce “yarinƴa kekkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa, shine a ke son kashe ta?toh daga yau Faɗi ta zama ƴata daman Allah bai taɓa bani ƴa mace ba yau kam Ubangiji ya amshi addu’ata ya mallaka min Faɗi” 

Murmushi suka yi dukkaninsu harda Faɗi, Alhaji Abubakar ya nisa ya ce “Toh Yape mi sahima Faɗi (na baki kyautar Faɗi).” 

Cikin jin daɗi Yape ta masa godia tana janƴo Faɗi cikin jikinta. 

Mahaifina ya ce “Faɗi wani ruga kuke?” 

Ɗagoda kanta tayi kafin ta ce “rugar Arɗo muke a can cikin ƙauyukan Mambila, ƙauyene matsaƙaici wanda duk tarin mutanen dake ciki ƴan uwan junane (laƴol gotel)”.
************************************* 

Bayan wata shida (6months latter) 

Sosai Faɗi ta goge ta dawo ƴar gida Yape na matuƙar nuna mata so da kulawa ta maye mata gurbin uwa da uba, Alhaji Abubakar kuwa yana leƙowa cikin Mambila duk ƙarshen wata dan shi a Yola yake da zama shida ƙannensa duka, Lesson teacher daga can birni ya ɗaukowa Faɗi ana ko ya mata arabi da boko, sosai kuwa ta maida hankalinta wajen karatunta.

Wani zuwa da mahaifina yayi ƙauyen ya sama Yape ya ce da ita “shi fa ya sama matar aure” 

Cikin ɗauki Yape da dama ta gaji da zaman sa haka babu mata ta ce “Alhamdulilah minyetti Allah(mungode Allah ) waye ne surukar ta wa kuma yanzun?” 

Ɗan murmushi ya yi ya ce “Ƴar ki ce Yape Faɗi” 

Cikin mamaki Yape ta ce “Faɗi? Ya za’ayi ka auri yarinƴa da ba ta wuce shekaru 11 ba?” 

Ta ida maganarta cike da mamakin Abubakar, sosa kansa kaɗan ya yi kafin ya ce “Yape kin mance al’adar Fulani ne musamman na ƙauye? Faɗi ke mai ya sa ba’a miki aure ba?” 

Ya ida maganarsa yana mai kafe Faɗi wacce duk kunƴa ya gama rufe ta, ta ce “aini cewa a kayi baƙin aljani gare ni, duk wanda ya aure ni mutuwa zai yi, shi ya sa ba’a mun aure ba.” 

Ta baiwa Mahaifin nawa amsar tambayarsa. Sosai abin ya basu mamaki Yape ta ce “caf Allah ya kyauta, wasu suna abu tamkar jahilai,karki damu ɓingel’am (ƴa ta) Allah zai kawo maki miji na gari kin ji?” 

Gyaɗa Kai kurum Faɗi ta yi ta ce “ngde Yape” 

******************************* 

Daga wannan ranar Alhaji ya saka Faɗi a Islamiya da boko, still in ta dawo ana ɗora mata da lesson, dan ta fi gane karatun,ana kula da karatunta sosai, Yape ta tsaya sosai a kan karatun islamiyar ta yadda za ta kula da ibadar ta,etc. Da’aka ga ta fara ganewa har ta kai shekara 1 a Islamiya ta kai kimanin izu 30 a Alkur’ani,ta na da matuƙar ƙoƙari sosai. 

A lokacin kuma shekarunta 12 ne, tana primary 6 a lokacin.Bayan ta zana common intarance a ka ɗaura auren ta da Alhaji Abubakar, shi kuma Alhaji a wannan lokacin haka ya zauna ba shi da mata, saboda ya rigada ya gayawa mahaifiyarsa shi ba zai sake auren wata ba, in ba Faɗi ba shi ya haƙura da aure, shi son yarinƴar yake. 

***********************************
Bayan shekaru 3 da auren na su wani abu na tarayyar aure bai taɓa shiga tsakaninsu ba, hasali ma Faɗi ta yi ƙanƙartar fahimtar mai a ke yi a rayuwar aure, Alhaji kuwa sai bai matsa mata ba. 

Wata rana mahaifina ya ta shi da tsananin buƙata, daa ya yi wa kansa alƙawarin bazai taɓa kusantar Faɗi ba har sai ta kai shekaru goma 18 a duniya dan a wannan lokacin shekarun Faɗi goma sha biyar, a haka dai ya sama dama ya kusance ta, duk da cewa ta yi matuƙar wahala hakan bai saka ta yin fushi da mijinta ba, dan Faɗi macece mai sanƴin rai gata da ladabi da biyayya, a kuma ranar ta sama shigar ciki. 

Tunda ga wannan lokacin Alhaji ya soma kusantar Faɗi, kuma tana iya bakin ƙoƙarinta dan ganin ta biyawa mijinta buƙatarsa, bata gajia sam wajen faranta masa shi kuwa kullum cikin sanƴa mata albarka yake.

Sosai Faɗi cikin wasu watanni ta goge jikinta yayi ɓulɓul ga wani uban haske da fatar jikinta ya ƙara. Ita dai kusan kullum sai taji motsi a cikin cikinta, tayi ta kuka ta na cewa “ƙilama baƙin aljanin ne (da’aka ce tana da shi) a cikin cikinta, addu’a kawai ta dage ta na yi kullum da shan ruwan zamzam, da dai ta gaji kunsan bafullatani da kunƴa, ta rasa wanda zata faɗiwa.Har takai ta kawo ma in ta zauna a wuri sai tayi shiru, ga shi ita cikin nata bamai laulayi ba, ƙiba tayi sosai dan lokacin cikin na ta yakai kimanin wata 4 amma babu wanda ya lura dan a wannan lokacin burma burman kaya a ke sakawa ba wai ɗamammuba. 

Yape taje ta samu ta ce da ita “Yape ina ganin fa akwai aljani a cikin cikinta”. 

Cikin tsoro Yape ta ce “Aljani?!”.
Faɗi ta ce “Yape ai motsi na ke ji sosai a cikin nawa” 

“Motsi?!” Yape ta tambaye ta cike da mamaki Faɗi ta ce “eh motsi sosai Yape”
Haƙuri ta bata kafin Yape ta kira Alhaji ta sanar masa a matuƙar tsorace “Buba (haka ta ke kiran ɗan nata) Faɗi fa ta ce tana jin motsi a cikin cikinta” 

A tsorace shima ya dawo a ka kaita asibity a kayi mata scanning likitan ya ce “kai wannan ai ciki gare ta har na tsawon wata 4…….” 

Tun kafin likitan ya ƙara sa Maganarsa Alhaji ya faɗa ƙasa ya yi sujjada ya na mai godia ga mahaliccinsa. 

Doctor ya yi masu albishir da Faɗi tana da cikin ƴa mace .

Sosai kowa yayi farin ciki da wannan cikin, mutane na faɗin “Allah maji rokon bayinsa, Abubakar ma za’a haifa masa ɗansa na kansa, Alhamdulillah Allah ya saukeki lafiya Faɗi”Shine yawancin Addu’ar da mafi yawan mutane ke yiwa Faɗi, kan kace komai tuni aka fara tattalin cikin, komai yi mata ake, babu wani abu da zata buƙata ba’a kawo mata shi ba. 

  Haka kwanaki suka riƙa tafiya har Allah cikin ikonsa ya sauki Faɗi lfy, ta haifo santaleliyar ƴarta mace mai kama da mahaifinta sak hasken mahaifiyarta kawai ta ɗauko, Farin ciki gurin Alhaji Abubakar ba’a bada lbrnsa sai dai wanda ya gani kawai, sosai ya ɗauki son duniya ya ɗaura a kan ƴarsa yana matuƙar jin son ta har cikin sassan jikinsa, Ranar suna yarinƴa taci sunan mahaifiyar Faɗi wato *Haleematul Sadiya*, Alhaji sosai ya yi ɓarnar dukiyarsa a wannan taron sunan, fatan dai Allah ya raya masa Haleematun sa cikin addinin Islama. 

************************************** 

   “Hummm Suhailat ina jiye miki ranar nadama, ranar da zakiyi kuka da idanuwanki ranar da zakiyi kaicho da zaɓin ki, ina mai shawartarki ƴata ki guji ranar nadama wanda nayi imani wannan ranar zata zo miki wallahil azeem Suhailat ranar nadama zai zo ya iske ki” 

  Momy ta ida maganarta tana mai zubawa Suhailat ɗin idanuwanta, wacce taci ado cikin kayan amare fuskarta rufe ruf da alkebba. Ɗagoda maƴan idanuwanta ta yi ta sauke su a kan fuskar Momy sa’annan ta nisa ta ce “Momy albarkan ki kawai nake naima, ki mun fatan alkairi ki riƙa mun addu’an samun zaman lfy da samun zuri’a ɗayaba shikenan zai wadatar dani” 

“Hummm” kawai Momy ta faɗa a taƙaice kafin tama ƴan uwanta da suka rako Suhailat ɗin dan samun nasihar mahaifiyarta, signal alamun su tafi da ita. 

***********************+*++*********
Bayan shekara ɗaya da haihuwar Haleematu wacce a ke kira da (diddi) dan sakaye sunan mahaifiyar Faɗi yasa kowa ke kiran haleematu da *Diddi*, Diddi nada shekara ɗaya a duniya Faɗi ta samu shigar ciki sai dai wannan karan cikin bai zauna ba cikin na wata biyu ya zube, toh tunda ga wannan lokacin ciki ya daina zama a mahaifar Faɗi tana samun ciki zai zube, a haka har ta samu shigar wani cikin na huɗu kenan sai dai anci sa’a wannan karan cikin ya zauna sai dai an hanata aikin komai daidai da ɗaukan kofi an hanata bata wani dogon motsi, cikin na da wata bakwai ta haifesa inda ta haifi bakwaini, cikin sosai yazo mata da tangarɗa, Faɗi da ɗanta suka rasu a ranar da ta haifo cikin duniya. 

  Innalillahi wainna ilaihir rajiun Faɗi maku irin mugun tashin hankalin da Alhaji da zuri’ar sa suka shiga ɓata lokaci ne musamman Alhaji sai da a ka haɗa masa da rubutu dan mutuwar matarsa ya yi matuƙar ɗimauta shi, Diddi a lokacin tana da shekaru 4 a duniya. 

   ************************************* 

   Suhailat zaune a tsakiyar gadon babban ɗakinta, kanta sun kuye lulluɓinta ya gama rufe ko ina a jikinta, ƙamshin turarensa ya doki hancinta, dogon lumfashi ta sauke sa’annan a hankali taji yana yaye mata lulluɓinta, kekkyawar fuskarta ya bayyana, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da murmushin a hankali ya furta “Matata” wani kalan daɗi ne ya ziyarci Suhailat a nata tunanin Sir Salman ya fara son ta dama malamanta sun faɗa mata komun daren daɗewa zai dawo ya so ta fin yadda ya so Abee, hannunsa ya ɗora a saman kanta kafin ya ce “muje muyi alwala muyi salla raka’a biyu dan gode wa Ubangijin mu” murmushi sosai Suhailat tayi har side dimple ɗin ta na gefen hagunta ya bayyana. 

   Salla su kayi raka’a biyu sa’annan Sir Salman ya mata tambayoyi kuma ta amsa masa su daidai, aduaa yayi masu na samun zaman lfy sannan suka soma hira sama sama daga ƙarshe kuma Sir Salman ya sunguma matarsa sukai gado dan raya sunnan manzon Allah.

   Tun Suhailat na ihu tana kwala kiran sunan Momy da Abee har muryarta yazo ya dishe ta matuƙar sha wahala a hannun Sir Salman a wannan daren sai da ta maida ta cikakkiyar mace. 

   Wa shegari da kyar Suhailat ta iya ta shi ta tsaftace jikinta, duk jikinta ya mutu murus mugun haushin Sir Salman kawai take ji musamman in ta tuno muguwar azabar daya ɗan ɗana mata ga shi ya tsallake ya barta ko ya tai maka mata ya sata a ruwan zafi yaƙi kansa kawai ya tsaftace yayi ficewar sa a ɗakin, kallon agogon dake manne a bangon ɗakinta tayi 11am guntun tsaki taja a hankali ta shiga jan jikinta ƙasanta na mugun mata zafi da kyar ta shiga bayin ta haɗa ruwan ɗumi ta shiga tafi mintuna arba’in a ciki kafin ta fito ta shirya cikin wata haɗaɗiyar ɗinkin doguwar riga, tayi kyau sosai ta feshe jikinta da turaruka masu ƙamshin gaske, gyara ɗakin tayi ta kunna turaren wuta kafin ta fito ta nufa falo.

  Zaro idanuwanta waje tayi ganinsa zaune ita kuma tana kwance a ƙirjinsa tana shafa sajen fuskarsa, shi kuma yana mata raɗa a kunnenta, ihun da Suhailat ta kwaɗa shi ya dawo dasu cikin hayyacinsu, jikin Suhailat babu inda baya rawa muryarta na karkarwa ta shiga nuna su da yatsanta, tama gaza sanin abin da ya kamata ta faɗi cikin tsoro sosai ta ce “Sir……………


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *