KAWUNA CHAPTER 8 KARSHE

KAWUNA





CHAPTER 8. KARSHE




A hankali ta ɗago da idanuwanta ta sauke su a kan Hammad, Wanda Shi ɗin ma ita yake kallo da alamun nazarinta yake, wani iriyar kwarjini taji yayi ma ta a hankali ta ce ” Tabbas na san komai da komai amma mainene dalilinka na son sanin malamanta?” Ta watsa masa tambayar kanta tsaye, murmushin gefen baki Hammad yayi kafin ya nisa tamkar ba zaiyi magana ba, can kuma sai ya ce ” kin shirya faɗamin inda suke ko sai na tona asirinku ku duka?” Ya ida maganarsa ransa a ɓace, jin yadda yayi maganar ma kawai ya isa ya hautsinar da hanjin cikinta ya kuma isheta sanin a kowani lokaci in ba ta yi wasa ba zai iya mangareta, haɗiyar miyau tayi mai zafi kafin ta ce ” Hammad!” Ta kirasa a raunane, mai amsata ba sa’anan bai da niyyar amsatan don haka ta ci gaba da maganarta ” shiga hanƴar Nenne ba abu bane mai sauƙi,wallahi Hajia da kake gani ta wuce tunaninka da saninka, duk wani iya makirci, shaiɗanci, rashin mutunci da rashin imani inka shiga tsabgarta babu ɗaya da ba zata aikata a kan koma waye ba!. Ina guje maka shiga tarkon ta don a yanzun ma ba barin ka tayi ba, ina ga kuma ta ankara da kanay mata kutse cikin lamuranta? A yanzun haka bazan maka ƙarya ba kaine mutum mafi tsana wajen Nenne ta ƙosa taga bayanka, ka kuwa san sau nawa tana ƴunƙurin son kawar dakai a doron duniyar nan? Wallahi yafi a ƙirga! Dan Allah dan Annabi Hammad karka jefa Rayuwarka cikin hatsari, Malamanta ma bazasu baka goyon baya ba hasalima zasu sanar ma ta da ƙudirin daka zo masu da shi a kanta.” Asma’u ta faɗi ma sa hakan a zatonta da tunaninta hakan data faɗa ɗin zai sanƴa Hammad janƴe ƙudirinsa na son ziyartar malaman Nenne. Amma sai dai mu ce Asma’u ta makaro, dalili kuwa Hammad ya riga ya gama yanke hukuncin ganin malaman Nenne, malaman dake ma ta aiki har take cin duniyarta babu tsinke, ya ci alwashin duk runtsi duk wahala sai ya ga bayan Hajia Nenne, yayi rantsuwa da mahaliccinsa matuƙar yana raye sai ya rusa dukkanin farin cikinta, jin daɗinta sai kuma ya kwace dukkanin dukiyar da ta mallaka ta hanƴar maguɗi. Sa’annan bazai barta ita da ahalinta su wuce hakanan ba tareda sun ɗanɗana hukunci ba, a yanzun baya tunanin akwai wani wanda zai iya dakatar da shi wajen cimma burinsa a kan kawar da muggan halayyar Nenne da duk wani wanda yake da sa hannu a kan hakan. Shiru yayi yana ɗan nazari kafin ya nisa ya ce ” ba shawara na kira ki bani ba, hakanan kuma ban ce da ke ina buƙatar shawara daga wajenki ba, na kiraki ne don ki sanar dani inda malaman bokayen yayarki suke, ba shawara nake baki ba umarni nake baki, wallahi tallahi in kika ƙi sanar dani billahil azeeem abin da zan miki zaki gwammaci mutuwarki sama da komi a rayuwarki. Ina mai daɗa tambayarki a karo na ƙarshe, ina Bokayen yayarki suke?!” Ya ida maganarsa a tsawace wanda har yayi nasarar tsoratar da Asma’un, gani tayi ya riƙiɗe ma ta ya zama wani daban fuskar nan ta sa a mauɗe tamkar Mala’ikan mutuwa. Tsananin tsoronsa ne yayi azamar dabaibaye ilahirin gaɓɓan jikinta, burinta ɗaya ta samu tabar gabansa kuma ba tada damar yin hakan har sai ta sanar da shi gaskia, bata ji zata iya sanar masa da gaskiar don yayarta bata cancanci hakan daga gareta ba. “Kayi haƙuri bazan iya sanar da kai komi a kan wannan al’amarin ba, yayata bata cancanci hakan daga gareni ba ya kamata a ce ni mai rufa mata asiri ce duk runtsi duk wahala” Asma’u ta faɗi hakan a ɗan tsorace don bata san abin da zaije ya kawo ba, a yadda taga Hammad ɗin ya fusata babu abin da bazai iya aikatawa ba amma ya ta iya? rufin asirin yayarta ya fiye ma ta komai a duniya, duk da tasan halin yayarta ta ba abu bane mai kyau amma tanay ma ta addu’an samin shiriya wajen Ubangiji kamar yadda ita ya shirye ta a yanzun. ” Ina ganin ba zaki ba da haɗin kai cikin ruwan sanƴi ba, tunda kin nuna ke ɗin mai taurin kai ne bari na nuna miki nawa iriyar taurin kan.” Ya ida maganarsa a zafafe, lokaci guda kuma ya miƙe ya tako daidai inda take a zaune kafin ya ce ” tunda kin zaɓi na bi dake tahanƴar tursasawa bari zan yi yadda kike son” ya faɗi hakan lokaci guda yana cire wani ƙaramar bindiga daga cikin aljihun wandonsa. A tsorace Asma’u ta soma bin hannunsa da ke riƙe da bindigar da kallo jikinta babu inda baya shirin soma rawa, tun fil’azal Asma’u na da masifar tsoro abu kaɗan zai tsoratar da ita, muƙut da kyar ta iya haɗiyar miyau daidai nan kuma Hammad ya ɗaga bindigar ya saita sa daidai goshinta kafin ya soma magana cikin ɓacin rai ” Wallahi tallahi ko ki sanar dani abin da na tambayeki ko a yanzun ba anjima ba ki ziyarci lahira! Zan kashe ki na kashe banza babu wanda ya isa yamin hukunci, ina mai baki dama ta ƙarshe ki sanar dani ko wallahi na raba lumfashinki da gangar jikinki!” Ya faɗi a tsawace wanda har hakan yaso tsoratar da Asma’u har take shirin sakin fitsari a wando. Bakinta na karkarwa ta soma magana ” ka .. ka…. Kayi haƙuri zan sanar maka komai da komai, sai dai don Allah kamin alfarma guda ɗaya karka sanarwa Nenne cewa ni ce na tona asirinta don Allah don annabi” ɗan shiru tayi tana jiran ji ko zai amsata, amma sai taji yayi banza da ita kuma bai da shirin cema ta komai ga kuma dukkanin alamu bai da shirin sauke wannan bindigar a samar goshinta. ” Hammad, malamanta su uku ne ɗaya a Jos yake ɗaya a Maiduguri ɗaya kuma a minna (Niger State) wlh tallahi na maka rantsuwar musulmai Hajia Nenne bata taɓa zuwa dani wajen ko guda a cikinsu ba, hasalima bata zuwa da kowa ita kaɗai ke zuwa kuma a motar haya! Sai dai na sani a Jos, Maiduguri, da Minna suke, amma ban san a wacce unguwa ko jiha suke da zama ba, akwai teacher wanda naga kamar cikin su duka tafi aminta da shi sa’anan tafi yarjewa aikinsa!” Ta ida maganarta tana mai satan kallon Hammad, shi kuwa nazarin maganarta ya shiga yi, nisawa yayi don ya hango iyakar gaskiar ta take sanar da shi. ” Shi teacher ɗin ya sunansa sa’anan wani gari shi yake a cikin gari ukun?” lumfashi ta sauke kaɗan kafin ta ce ” Hajia bata bari muna sanin komai dangane da malamanta, ban san dalilinta ba don dukan su bata saving lambansu da sunayensu sai dai malam Jos, Malam Maiduguri sai kuma shi Teacher, wlh ban San sunansu ba Amma teacher a Minna yake” gyaɗa kai yayi kafin ya sauke bindigar a samar goshinta wani dogon lumfashi Asma’u ta sauke wanda har taso baiwa Hammad dariya amma sai ya gimtse, kallonta yayi yana hango tsantsar firgici a tattare da ita ” kin yi ƙoƙari, a gaskiya yayarki na da matuƙar dabara amma karki damu aikin da zaki min next shine….” ɗan tsagaita wa yayi da maganarsa ganin yadda Asma’un ke zaro idanuwa, ɗan guntun murmushi kawai yayi, Asma’u kuwa cewa take a cikin zuciyarta ” ohni Allah, wannan mutumin ina yake son jefa rayuwata ne?” Katse tunaninta yayi ta hanƴar cewa ” karki damu aikin ba mai wahala bane, kawai abin da nake so dake shine ki san yadda zakiyi ki samarmin lamban Teacher yau ɗin nan, zan baki awa biyu tal rashin cikamin aiki zai saka ki fuskanci mummunar hukunci wallahi” ganin yadda yayi maganar babu alamun wasa a tattare da shi ya sanƴata jin zata iyayin koma mainene ya sanƴata dan hakanan da ranta da Lafiyarta ta na kuma ji tana gani a raba ta da lumfashinta. ” In sha Allah zan turama” ta faɗa a raunane duk da tasan ba lalle bane Hajiar ta bata wayar na ta ba, amma hausawa sunce mai naima baya fidda ran samu. “Very good, zaki iya tafiya sai na jiki, and don’t try acting up anything stupid” ya faɗa kansa tsaye, da sauri da sauri ta shiga gyaɗa ma sa kai kurum don burinta bai wuci tabar gaban Hammad completely ba (gaba ɗaya). ” Now go!” Ya faɗa ciki-ciki, da sauri ta miƙe har tana harɗewa da hanzari tabar cikin falon jikinta duk a sanƴaƴe.

Story continues below


Kyalkyacewa kawai ta shiga yi da dariya har da su riƙe ciki, shi ko katseke ya zauna yana kallon yadda take kwasar dariya abinta ranta a kwance, zai iya cewa dariya yana matuƙar ƙara ma ta kyau da haiba, sam sam baya gajia da kallonta in tana dariya. Sosai take burgesa kuma take sake samun wani matsayi na daban a cikin ƙogon zuciyarsa. ” Oh ni Allah Baffa’am! Ashe zaka iya acting film, kai Allah ina ma Ali Nuhu zai ga wannan acting ɗin na ka da kai a yanzun, da kuwa babu abin da zai hana sa fara yi maka directing film” ta Ida maganarta tana mai sake fashewa da wani dariyar wannan karon har tana durƙusa wa a ƙasa tsabagen dariya. Girgiza kai Hammad yayi kafin ya ce ” Senorita Allah ya shirya min ke!” Far da idanuwa Abee tayi kafin ta ce ” yauwa gwara yau da Allah ya saka ka kirani da wannan sunan, plss Baffah mai ma’anar Senorita?” Dariya yayi kaɗan kafin ya ce ” kina so ki san ma’anar sunan ne?” Da sauri ta girgiza ma sa kai ta ce
” ai saboda Ina son sanin ma’anar ne ya saka na tambayeka Baffah” tayi maganar a shagwaɓe wanda har sai da Hammad ya ji tsigar jikinsa na tashi, da sauri ya kawar da idanuwansa a kanta, kafin ya shiga kawar da maganar ta hanyar cewa ” matsoraciya kawai, ina kafa fitowa kikayi da Ma’u tazo? kinje kin ɓuya sai da ta tafi sa’annan ake ganin ƙeyarki harda su sheƙewa da dariya, umm umm Dota fa” ya Ida maganarsa yana mai dariya ƙasa-ƙasa ita ɗin ma dariya tayi kafin ta ce ” chap, Baffah ai naji tsoron Allah naji tsoron su Asma’u yanzun abune mai sauqi ta ganeni fa, duk da babu tabon a fuskana” dariya kawai Hammad Yayi ba tare da ya sake cewa da ita uffan ba.
*************************************************
Cikin sanɗa ta idasa shiga cikin ɗakin Hajia Nenne, a hankali ta shiga bin ɗakin da kallo a kuma sa’i guda taji alamun tafiyar ruwa a cikin ban ɗaki(toilet) alamar mutum na cikin banɗakin. Guntun murmushi ta saki mai ƙunshe da ma’anoni daban daban wanda ita kaɗai tabar wa kanta sanin ma’anar da murmushin na ta ke ɗauke da shi, hango wayar Nennen da tayi a kan Centre table dake tsakiyar ɗakin shi ya sanƴata saurin ƙara sowa gaban table ɗin, a hanzarce ta ɗauki wayar ta fita a ɗakin da sauri gudun kar Hajiar ta fito ta isketa tana taɓa mata wayar salularta, ɗakinta ta koma kafin ta buɗe wayar ta sanƴa password wanda take da yaƙinin cewa shi ɗin ne password ɗin wayar, ganin wayar ta buɗe ne ya sanƴata sakin murmushin samun nasara, da sauri ta shiga contacts ta ciro lambar Teacher Har da lambar sauran malaman ta kofe a cikin wayarta sa’anan ta yi saurin fitowa ta mayarwa Nennen wayar nata ta ko ci sa’a bata fito ban ɗakin ba, har ta a jiye wayar tana shirin barin wajen taji Muryar Nenne a samar kunnenta wanda hakan ba ƙaramin tsoratar da ita yayi ba ” Ma’u, mai kike da wayata?” a hankali tamkar mara gaskia ta juyo tana kallon Nenne wacce ita ɗin ma Asma’un take bi da kallo, kallo irin na tuhuma ɗin nan. murmushi Asma’u ta lalubo ta yafawa Samar fuskarta kafin ta ce ” am…am like Babu abin da nake da wayarki, na dai ɗauka zan kira wayata ce na rasa inda na wurga wayar tun ɗazun nake naimar wayar ban gani ba shine na ce bari nazo na dau wayarki na kira” ta ƙarasa maganarta cike da ƙarfin gwiwa, sauke lumfashi Nenne tayi kafin ta ce ” kin tabbata wayar ki ce baki gani ba?” Da sauri ta girgiza kai alamar eh, ɗan nazarinta Hajiar tayi na wasu daƙiƙu kafin ta ce ” hmmm, ko kin jefa shi cikin kaya and waima ke da kika ce min sai nan da 2wks zaki dawo mai ya dawowar dake yau ko sanar da ni baki yi ba?” Hajiar ta idasa maganarta lokaci guda kuma tana buɗe wadrope ɗin ta dake maƙale da kayayyaki masu matuƙar yawa, hannu ta sa ta dau wani dakakkiar leshi wanda a kalla zai kai kimanin Naira dubu 70. “Da kinsan tuggun da a ke haɗa miki da baki zauna kina tambayata dalilin dawowata ba tare da na sanar miki ba” Asma’u ta raya hakan a cikin zuciyarta. “Mai kika ce?” Hajia Nenne ta katse ma ta tunaninta lokaci ɗaya kuma tana kafe Ma’un da kallo, a ɗan tsorace Asma’u ta kallo yayarta kardai tayi suɓutar baki ne? Abin da ta faɗa a zuciyarta kar dai ya fito fili ne? ” Ma..mai kikaji na faɗi?” Harara Hajiar ta sakar ma ta kafin ta ce ” anƴa Lafiyarki kuwa ? Kina abu kamar baki da gaskia” far Asma’u tayi da idanuwanta kafin tayi saurin maido da hankalinta jikinta gudun kar Hajiar ta fara ɗano jirginta. ” Wallahi lafiya nake kawai dai na ce ne kamar bakya kewata, ko ki ce U missed me” girgiza kai Nenne tayi daidai nan kuma ta ciro sarƙar gwal ta a jiye kan gado kafin ta zauna gefen gadon, ba tare da ta kallo Asma’un ba ta ce ” naji koma dai mainene ya kamata a ce kin sanar da ni zuwanki, ki Kula next time kin ji ba? Kema kin san dole nayi kewarki i missed u a lot” Hajia Nenne ta Ida maganarta, tanay ma Asma’un nuni da tazo wajenta, ba ɓata lokaci ta isa gaban Hajiar inda suka runguma juna kafin Nenne ta ce ” toh maza jeki huta, gobe da safe mayi magana” gyaɗa kai kurum tayi jiki a sanƴaye tabar ɗakin tana mai tunanin abin da zai je ya komo, ta rasa sukunin zuciya tana wasuwasin abin da tayi wa yayarta dai dai ne ko a kasin hakan? Sam Yayarta bata iya dogon fushi da ita ba, In tayi wuta tayi tsawon fushi da ita shine kwana 3 daga nan zata maida komai ba komai ba. “Does she really deserve this from me?(Anƴa ta cancanci hakan kuwa daga gareni?)” Shine Tambayar data watsar wa kwanƴarta, amma ya ta iya her life is at stake ( rayuwarta na garari) dole ta sanƴata yin hakan.

Story continues below


Kyalkyacewa kawai ta shiga yi da dariya har da su riƙe ciki, shi ko katseke ya zauna yana kallon yadda take kwasar dariya abinta ranta a kwance, zai iya cewa dariya yana matuƙar ƙara ma ta kyau da haiba, sam sam baya gajia da kallonta in tana dariya. Sosai take burgesa kuma take sake samun wani matsayi na daban a cikin ƙogon zuciyarsa. ” Oh ni Allah Baffa’am! Ashe zaka iya acting film, kai Allah ina ma Ali Nuhu zai ga wannan acting ɗin na ka da kai a yanzun, da kuwa babu abin da zai hana sa fara yi maka directing film” ta Ida maganarta tana mai sake fashewa da wani dariyar wannan karon har tana durƙusa wa a ƙasa tsabagen dariya. Girgiza kai Hammad yayi kafin ya ce ” Senorita Allah ya shirya min ke!” Far da idanuwa Abee tayi kafin ta ce ” yauwa gwara yau da Allah ya saka ka kirani da wannan sunan, plss Baffah mai ma’anar Senorita?” Dariya yayi kaɗan kafin ya ce ” kina so ki san ma’anar sunan ne?” Da sauri ta girgiza ma sa kai ta ce
” ai saboda Ina son sanin ma’anar ne ya saka na tambayeka Baffah” tayi maganar a shagwaɓe wanda har sai da Hammad ya ji tsigar jikinsa na tashi, da sauri ya kawar da idanuwansa a kanta, kafin ya shiga kawar da maganar ta hanyar cewa ” matsoraciya kawai, ina kafa fitowa kikayi da Ma’u tazo? kinje kin ɓuya sai da ta tafi sa’annan ake ganin ƙeyarki harda su sheƙewa da dariya, umm umm Dota fa” ya Ida maganarsa yana mai dariya ƙasa-ƙasa ita ɗin ma dariya tayi kafin ta ce ” chap, Baffah ai naji tsoron Allah naji tsoron su Asma’u yanzun abune mai sauqi ta ganeni fa, duk da babu tabon a fuskana” dariya kawai Hammad Yayi ba tare da ya sake cewa da ita uffan ba.
*************************************************
Cikin sanɗa ta idasa shiga cikin ɗakin Hajia Nenne, a hankali ta shiga bin ɗakin da kallo a kuma sa’i guda taji alamun tafiyar ruwa a cikin ban ɗaki(toilet) alamar mutum na cikin banɗakin. Guntun murmushi ta saki mai ƙunshe da ma’anoni daban daban wanda ita kaɗai tabar wa kanta sanin ma’anar da murmushin na ta ke ɗauke da shi, hango wayar Nennen da tayi a kan Centre table dake tsakiyar ɗakin shi ya sanƴata saurin ƙara sowa gaban table ɗin, a hanzarce ta ɗauki wayar ta fita a ɗakin da sauri gudun kar Hajiar ta fito ta isketa tana taɓa mata wayar salularta, ɗakinta ta koma kafin ta buɗe wayar ta sanƴa password wanda take da yaƙinin cewa shi ɗin ne password ɗin wayar, ganin wayar ta buɗe ne ya sanƴata sakin murmushin samun nasara, da sauri ta shiga contacts ta ciro lambar Teacher Har da lambar sauran malaman ta kofe a cikin wayarta sa’anan ta yi saurin fitowa ta mayarwa Nennen wayar nata ta ko ci sa’a bata fito ban ɗakin ba, har ta a jiye wayar tana shirin barin wajen taji Muryar Nenne a samar kunnenta wanda hakan ba ƙaramin tsoratar da ita yayi ba ” Ma’u, mai kike da wayata?” a hankali tamkar mara gaskia ta juyo tana kallon Nenne wacce ita ɗin ma Asma’un take bi da kallo, kallo irin na tuhuma ɗin nan. murmushi Asma’u ta lalubo ta yafawa Samar fuskarta kafin ta ce ” am…am like Babu abin da nake da wayarki, na dai ɗauka zan kira wayata ce na rasa inda na wurga wayar tun ɗazun nake naimar wayar ban gani ba shine na ce bari nazo na dau wayarki na kira” ta ƙarasa maganarta cike da ƙarfin gwiwa, sauke lumfashi Nenne tayi kafin ta ce ” kin tabbata wayar ki ce baki gani ba?” Da sauri ta girgiza kai alamar eh, ɗan nazarinta Hajiar tayi na wasu daƙiƙu kafin ta ce ” hmmm, ko kin jefa shi cikin kaya and waima ke da kika ce min sai nan da 2wks zaki dawo mai ya dawowar dake yau ko sanar da ni baki yi ba?” Hajiar ta idasa maganarta lokaci guda kuma tana buɗe wadrope ɗin ta dake maƙale da kayayyaki masu matuƙar yawa, hannu ta sa ta dau wani dakakkiar leshi wanda a kalla zai kai kimanin Naira dubu 70. “Da kinsan tuggun da a ke haɗa miki da baki zauna kina tambayata dalilin dawowata ba tare da na sanar miki ba” Asma’u ta raya hakan a cikin zuciyarta. “Mai kika ce?” Hajia Nenne ta katse ma ta tunaninta lokaci ɗaya kuma tana kafe Ma’un da kallo, a ɗan tsorace Asma’u ta kallo yayarta kardai tayi suɓutar baki ne? Abin da ta faɗa a zuciyarta kar dai ya fito fili ne? ” Ma..mai kikaji na faɗi?” Harara Hajiar ta sakar ma ta kafin ta ce ” anƴa Lafiyarki kuwa ? Kina abu kamar baki da gaskia” far Asma’u tayi da idanuwanta kafin tayi saurin maido da hankalinta jikinta gudun kar Hajiar ta fara ɗano jirginta. ” Wallahi lafiya nake kawai dai na ce ne kamar bakya kewata, ko ki ce U missed me” girgiza kai Nenne tayi daidai nan kuma ta ciro sarƙar gwal ta a jiye kan gado kafin ta zauna gefen gadon, ba tare da ta kallo Asma’un ba ta ce ” naji koma dai mainene ya kamata a ce kin sanar da ni zuwanki, ki Kula next time kin ji ba? Kema kin san dole nayi kewarki i missed u a lot” Hajia Nenne ta Ida maganarta, tanay ma Asma’un nuni da tazo wajenta, ba ɓata lokaci ta isa gaban Hajiar inda suka runguma juna kafin Nenne ta ce ” toh maza jeki huta, gobe da safe mayi magana” gyaɗa kai kurum tayi jiki a sanƴaye tabar ɗakin tana mai tunanin abin da zai je ya komo, ta rasa sukunin zuciya tana wasuwasin abin da tayi wa yayarta dai dai ne ko a kasin hakan? Sam Yayarta bata iya dogon fushi da ita ba, In tayi wuta tayi tsawon fushi da ita shine kwana 3 daga nan zata maida komai ba komai ba. “Does she really deserve this from me?(Anƴa ta cancanci hakan kuwa daga gareni?)” Shine Tambayar data watsar wa kwanƴarta, amma ya ta iya her life is at stake ( rayuwarta na garari) dole ta sanƴata yin hakan.

Story continues below


************************************************
” Kika ce ina ne garin na ku?” a hanzarce Abee ta ce ” onicha ne Hajia” gyaɗa kai Nenne tayi tana ƙare wa Abeen kallo wacce ta gama sanar ma ta da cewa Mahaifiyarta babu lafiya rai wurin Allah, shine ta ce a sanar ma ta tana son ganinta bata san ko Wannan ciwon shine ajalinta ba.
” Owk, kya shirya gobe kije nabaki kwana 4 kawai ki dawo, don akwai aiki jaa a gabanki kar su miki yawa” gyaɗa kai kurum Abee tayi fuskarta ɗauke da jin daɗi ba tay tunanin Hajiar zata barta taje haka cikin ruwan sanƴi ba, duk ɗaukar ta zata iya cewa ɗaya daga cikin drivers ɗin gidan sukai ta amma sai Ubangiji ya ɗaura ta a kan Hajiar har tabarta ma tayi kwana 4, murmushin samun nasara Abee ta riƙa saki wanda har sai da Hajiar ta lura da hakan ” murmushin mai kike haka?” Da sauri Abee ta kallota ta ce ” Hajia murmushin Jin daɗi, murmushin samun nasara!” Kallonta Nenne tayi tace ” nasara kuma? Wace irin nasara?” Murmushin gefen baki Abee tayi ta ce ” nasarar zuwa onicha gurin mahaifiyata ban tsamman zaki barni ba shiyasaka nake ta murmushi na samu nasarar barina da kikai” gyaɗa Hajiar tayi tana kuma taɓe baki ” humm hakane, In banda abinki Abeedah wake wasa da lamuran mahaifiyarsa? Uwa fa uwa ce dole mukula da ita Allah bawa taki mahaifiyar lafiya da nisan kwana”.

” Ko baki faɗa ba mahaifiyata Allah zai ƙare ta da lafiya sa’annan zai ara mata tsawon rai ta dawo gareki ta fanshe zalincin da kika mata very soon!” Abee ta faɗi a cikin zuciyarta amma a fili sai ta ce ” hakane Hajia Nagode sosai Allah kara lafiya” a taqaice ta ce ” Ameen” dai dai nan kuma Asma’u ta kunno kai cikin falon, sanƴe take cikin riga da wando sun matuƙar amsar jikinta kanta babu ɗankwali tayi parking gashinta da rimbom ya sauko har gadon bayanta, kunnenta saqale da earpiece lokaci guda kuma tana daddanan waya. Murmushi Abee tayi don Asma’u na burgeta da salon iya ɗaukar wankanta sam sam matar bata tunanin ta girma takai 40’s kullum cikin yin abu take tamkar ƴar 20’s, bata bari shekarunta sun ruɗeta ta daina kwalisa ba kullum cikin gayu zaka isketa, yanayin jikinta kuma ba lalle bane ka yarda takai shekaru kusan 40 da en kai sosai jikinta ke ɓoye shekarunta. Zama tayi kan kujerar da ke fuskantar Nenne kafin ta shiga amsa gaisuwar da Abee ke yi ma ta sama sama don har yanzun haushin yarinyar take ji, haushin bata muƙamin da Nenne tayi ta haneta ita. Abee kuwa Bama tasan tana yi ba don hakane ma ta miƙe tawa Hajiar Sai anjima ta koma ɗakinta ta soma shirin tafiya.

**********************************************
Wuraren 10:30am Abee tawa Hajia sallama driver ya kaita tasha, Hajia Nenne harda yi mata shatara na arziqi ita dai Abee banda dariya babu abin da yake wa Hajiar a cikin zuciyarta, “oh In da a ce kin san duk a kanki nake tafiyar nan da na lahira sai ya fini Jin daɗi” kafin ta tafin tajewa Hajiar sallama inda take cewa ” Hajia ni zan tafi ki jirayi dawowata!” Ta faɗa maganar a gatse a kuma habaice, Hajiar kam bata ɗau maganar a bakin komai ba don bata kawo komai cikin zuciyarta ba.

A tasha Hammad yazo ya ɗauke ta suka nufi hanƴar yola, tafiya suke suna hira jefi jefi wanda ƙarfin hirar ma Abee ce don Hammad kam ba wani magana yake ba ita ɗin ce dai uwar surutu keta zuba kamar radio, tana basa labarin yadda sukay da Hajia Nenne.

Ƙarfe 12:45pm daidai suka isa garin Yola, can unguwar da su Mancy ke zaune suka nufa. Kallon board ɗin dake ɗauke da sunan layin Abee tayi a hankali ta karanto sunar unguwar ” wuro yanka” mutsuke manƴan idanuwanta tayi ta ce ” Baffah anguwar yanka mutane a ke ne?” Ta faɗa bilhakki da gaskiyarta, dariya sosai tabaiwa Hammad Wanda Har Sai da ya ɗara sosai har Abee ta saki baki tana ƙare wa kekkyawar fuskarsa dake fidda dariya kallo sosai take mamakin mai yake yiwa dariya haka? ko da akwai abin da ta faɗa na ban dariya ne a cikin maganar na ta? Muryarsa ta tsinkayo yana faɗin “oh Allah Senorita!, don Allah karki kasheni kafin lokaci na, yanzun waye ne ya ce miki yanka mutane a keyi cikin unguwar?” narai tayi da fuskarta ta ce ” toh baka ji sunan unguwar bane wai wuro yanka, yanka fa kamar yanka abu haka suke nufi fa kenan” ta basa amsa, murmushi yayi yana jinjina wauta irin na Abee. ” Toh ba yanka suke yi ba kinji ko?” gyaɗa kai tayi tace ” toh mai suke yi kenan?”
“Sunan unguwar ce kawai haka” daidai nan kuma Abee taga yayi horn a ƙofar wani hamshaqin gida, gidan da zata iya rantsewa kaf layin babu mai kyansa Sa’annan kallo ɗaya za ka wa gidan ka tabbatar sabon gidane fil, ƙare wa gidan kallo kawai Abee ta shiga yi ba ma kamar Sa’adda mai gadi ya wangale masu gate ɗin gidan, baki da hanci da ido Abee ta buɗe kawai tana ƙare wa halittar gidan ido, har Hammad Yayi parking Abee bata lura ba, girgiza kai Hammad Yayi kafin ya ce ” Daughter a rufe bakin hakanan ko?” daidai nan ta dawo cikin hayyacinta cikin jin kunya ta sanƴa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta.

Story continues below


**************

Ihu suka saki a tare suna rungumar junansu, ganin Mancy dake saukowa daga matakalen bene dake cikin falon ya sanƴa Abee janƴe jikinta cikin na Farhana, rugawa tayi a guje ta haihaƙowa Mancy tamkar zata maida ta ciki, ihu take tana ” Mancy nayi kewanki waiyoo Mancy wlh I missed you so much” murmushi Mancy tayi tana mai jin daɗin ganin ƴarta a hankali Mancy ta ce ” oh ni Haleematu ƴar Faɗi, yaddani zakiyi dai ko Abee?” Mancy ta faɗa fuskarta ƙunshe da murmushi, sumbatar fuskar Mncy Abee tayi kafin ta janƴe daga jikin Mancyn ta ce ” kai Allah Mancy wlh nayi kewanki ina Abbi da Harees?” Ta tambaya lokaci guda tana waige -waigen naimo inda suke. ” Suna masallaci” Farhana ta bata amsa, kallonta Abee tayi ta ce ” ke ƴar nan, wai mai Mancy ke baki haka? naga kinyi tuɓurɓur ne, iyye mai sirrin?” Abee ta faɗa tana ɗagin girarta, girgiza kai Mancy tayi ta ce ” Abeen Abbi har yanzun dai ana nan da hali ba’a canza ba?” Mancy ta faɗa cike da tsokana, cuno ƙaramin bakinta waje tayi ta ce ” haba Mancy, Allah ni gani nayi ƴar taki ta zama duma-duma” dariya Mancy da Farhana Kawai sukai, sosai sukayi missing barkwancin Abeen. Abee Kam zagaye gidan kawai ta shiga yi tana yaba kyawu da tsaruwar gidan, zuciyarta kuwa na tsunduma wa Hammad addu’o’in gamawa da duniya lafiya, har da ma sa addu’ar samun mata tagari mai son shi da ƙaunarsa, amma sai taji tamkar zuciyarta na kwaɓarta a kan hakan mai kenan? ba ta da amsa kam. Sosai suka yi hira da ƴan uwanta barin ma da Abbi ya dawo cire kunƴa Abee tayi ta rungume Abbinta don babu karya wlh tayi matuƙar kewan tsohonta, raba dare sukayi suna hira anan Mancy ke sanar mata su Baffa Rufa’i da Baffah Yusuf da iyalansu sunzo sunyi masu wuni, nan kuma Mancy ke sanar ma ta Hammad Yaron autan su Daddy ne, yaran Baffah Rufa’i uku Hydar, Aliya da Fatima sai matarsa Hajia Rukayya, Baffah yusuf kuma Yaransa biyar, Abubakar (takoran Daddy) Sulaiman, Hidayah, Zaituna, da Zeenat sai matarsa Hajia Ramlatu. Sosai Abee tayi mamaki kenan dama Hammad causin ɗin mahaifiyarta ce na ƙut da ƙut? Farhana ta ce ” Wallahi Adda Abee suna da kirki sosai, musamman Zeenat aurenta ma saura sati Uku ta ce min” jinjina kai Abee tayi ta ce ” lalle I can’t wait to see them, Kuma dukan su ne suka zo?” Farhana ta ce ” a’a, Zeenat da mamanta da babanta sai matar kaka Rufa’i da yaranta biyu, Fatima da Hydar Aliya tana Egpt da aure” jin jina kai Abee tayi ta ce ” kai dangi daɗi wallahi!”
**************

Kwanan su ɗaya a yola, suka shirya tafiya Minna ita da Hammad sosai Mancy da Abbi suka musu fatan dacewa kafin suka wuce airport don ta jirgi zasu bi, Abee kuwa anso yin ƙauyenci a cikin jirgi abinka da sabon shiga.

1:30pm daidai suka yiwa garin Minna dirar tsinke, a hotel suka sauka Hammad ya kama musu ɗakuna biyu na shi daya na ta ɗaya, bayan sun ci abinci sunyi salla sun huta Hammad ya shigo ɗakinta da sallama a bakinsa, zaune take tana latsa wayar hannunta ganinsa ya sanƴata a jiye wayar tana masa murmushi ta masa iso, zama yayi ya ce ” duk cikin gajiar ne? Na ga anata murmushi ba’a son Magana?” Dariya Abee tayi ta ce ” babu sam fa” jinjina kai yayi kafin ya ce ” nayi waya da malamin ya ce muzo mu same sa around 11:30pm,” kallon sa Abee tayi ta ce ” Baffah, mai ka ce da shi haka?” Murmushin gefen baki yayi ya ce ” aiki nake so zai min” murmushi Abee tayi ta ce ” oh oh nagane toh Allah kaimu lokacin”. Hira suka ɗan shiga yi kafin Hammad ya miƙe ya Koma na sa ɗakin don kwantawa ya ɗan samu baccin koda awa uku ne, Abee kuwa Vedio call ta kirasu Mancy suna yi abinsu cike da so da ƙaunar junan su, gashi ribar haƙurinsu na riskarsu ai komi a duniya akwai lokacinsa. 

*******************
Jugum jugum suka zauna kowa na jiran fitowar likita daga cikin ɗakin, Mommy kam babu abin da take furtawa sai sunayen Allah fatan ta Allah ya sauke ƴarta lafiya, yanzun awansu biyar kenan zaune suna jiran ji daga likita amma shiru basu da ma alamar fitowa yanzun, Hafiz kam zufa duk ya gama gauraye jikinsa babu abin da yake nanatawa a cikin zuciyarsa face Allah ya sauki Suhailat lafiya, uƙubar naƙudar da tayi kawai ya isa mutum zubar ma ta da kwalla, kwanaki har uku Suhailat ta jera tana fama da walalliyar naƙuda. Iya tsinuwa Salman babu tsinewar da bai sha ba a hannunta. 

Fitowar likita daga cikin ɗakin ne ya sanƴasu miƙewa da sauri har suna tuntuɓe, rige rigen tambayar likitan halinda Suhailat ke ciki kawai suka shiga yi. 
“Likita ya jikin nata?” Suka faɗi a tare, ganin tsanin tashin hankali shimfiɗe a samar fuskokinsu ya sanƴasa faɗin ” Alhamdulullah” daga haka bai sake cewa uffan ba yayi wucewarsa, ya barsu tsaye suna binsa da kallo har ya ɓace ganinsu. 

Likitan baifi mintuna 10 ba ya sake dawowa wannan karan da ɗan sauri saurinsa. Sun ɗebe kusan mintuna 50 kafin Allah ya sauki Suhailat lafiya inda Allah ya nufeta da samun tagwaye (twins) duk mata masu tsananin kama da ita, amma sai dai kana naka Allah na nashi, tunda Suhailat ta haifesu lumfashinta ya tsaya cak! bata lumfashi sam sam kuma babu alamar lumfashin a tattare da ita. Nurse ɗin ce ta kallo likitan a tsorace ta ce ” sir tarasu? Bata lumfashi?” Tsayawa kawai likitan yayi yana ƙare mata kallo sam-sam babu alamar lumfashi a tattare da ita!…….🙄



************************************************
11:30pm 

shiru sukai babu mai iya cewa da ɗan uwansa uffan, mamakin dake shimfiɗe a samar fuskarsu kawai ya isa sanar maka yanayin da suke ciki. Abee ce tayi ƙarfin halin motsa bakinta ta ce ” Baffa’ah!, Yanzun fisabililahi ta ina za mu iya kutsawa cikin dajin nan? dare ne fa yanzun, In muka haɗu da abin da yafi ƙarfin mu ya za mu yi Please? gaskia Malamin nan bai kyauta mana ba tunda har yasan gidan tsafin na sa can cikin dajin aljanune mai ya saka zai ce mu zo cikin dare fisabilillah fa?, Sha biyun dare a ke naima yanzun. kai Allah In da ranka ka sha Kallo”. Ta ida maganarta rai a ɗan ɓace, tafukan hannayensa biyu ya buɗe ya cusa fuskarsa a ciki lokaci guda kuma yana furzar da huci, lumfasawa yayi ya ce ” nima dai mamakin da nake yi kenan, dajin nan ba zamu iya shiganta ba”. “Hmmm” kawai Abee ta furta don haushi da taƙaici ke lulluɓeta, ta rasa dalili ta rasa wannan lamarin na matan duniyar nan, ta kuma rasa dalilin da yasaka yanzun ko wata mace a rayuwar nan ɗaɗai ku ne kawai a ciki basa yawon bin malamai.  Shin wai basu da wayau ne komai? Su ɗin malaman ba halittun Allah bane? Mai ya saka bazamu zauna mu roƙi Allah ya biya mana buƙatunmu ba sai dai muje can wurin wani malam wai shine zai biya maka buƙata, taya?! shi ɗin waliyyin Allah ne? ko malami zai maka aiki kuma aikin yayi wallahi na wasu ɗan lokuta ne don tabbas watan watarana sai ya karye, kuma Malaman nan ba su da aikin da ya wuce su ta sakaki kina asarar kuɗi kina kawo masu su kuma suna sakawa a aljihun su, anjima su miki aiki, aiki ya yi amma ta hanyar tsafi in kuma kika tashi magana sai kice addu’a malam yamin, addu’ar mai? Addu’ar tsafi da asiri shine addu’a? Wallahi gwara mu tuba mu koma ga Allah, mu riƙa tunawa akwai ranar ƙiyama ranar tsayuwa a fadar Allah, ranar da babu mai iya ƙwatarka sai aikinka, boka ko Malaman da kika bi suka biya miki buqatunki wallahi babu mai zuwa taimakonki, suma suna can suna ji da na su, mufarka mata daga nannauyar baccin da muka afka! Wallahi boka ko malam basu isa su canza abin da Allah ya nufa zai faru da ke ba. ” Bari na kirasa muji mai zai ce”  maganarsa ta katse ma ta tunaninta, gyaɗa ma sa kai kurum tayi ba tare da ta ce masa ƙala ba. 

“Hello, malam gamu a gefen dajin zuwa gurin naka” 
Malam ya ce ” toh toh, nasan dare yayi baza ku iya shigowa ba kam, gurin da hatsari bari na turo a zo a tafi daku” ya basa amsa a taƙaice Lokaci guda kuma yana katse kiran. Lumshe idanuwansa yayi ya ce ” Daughter ya ce zai turo azo  a tafi damu”  taɓe baki tayi ta ce ” Baffa’ah, Allah nake roƙo ya shirya duk wani ko wata dake zuwa gaban malami don biyan buƙata, Allah ya nuna musu hanƴa mai kyau ya fidda su cikin duhun kai da suke ciki. Har yaushe zaka zauna kana saɓawa Allah kana haɗa Ubangijinka da wani ƙato gardi? Shirka fa kenan yawancin mata keyi ba tareda sun sani ba! oh Allah kasa mufi ƙarfin zuƙatan mu, Allah karka jarrabce mu da abin da zai sanƴa mu kwace wa addininka”. Shiru kawai Hammad Yayi yana kallon Abee, kallonta yake cike da so da sha’awa. sha’awar yadda take magana cikin nutsuwa da ilimi, tunani yake yi tunanin shin har yanzun ana samun mata kamar ta? shin har yanzun akwai matan dake tunani da hangen nesa kamar Abeen sa?. Babu namijin da zai duba Abeedah yaƙi muradin zamarta matarsa, In kyau ne ko ilimi ko wayewa kake naima wajen mace, zai iya bugan ƙirji ya ce dukkanin abubuwan da ya lissafo ɗin nan babu wanda Abee bata da shi. A kallum godiya yake yiwa Ubangijinsa da ya hana faruwar auren Abee da Salman, baya tunanin zai iya rayuwa da wata macen da ta wuce Abeeda, ya sani sarai love at first side ya mata. shi a daa kallon mace ma ba iyawa ya yi ba, ballantana aje ga yaji wai yana sonta ya kasa bacci saboda mace, zai iya cewa lalle lalle Abee ita ce mace ta farko da ta ciri wannan tutar a cikin zuciyarsa, kuma yana fata kamar yadda yake sonta itama ta so shi. 

Story continues below


” Baffah ina ta magana kayi shiru sai kallona kake ta yi”. 

Abee ta ida maganarta lokaci guda kuma tana dawo da Hammad duniyar tunanin da ya afka. Lallausar murmushi kawai ya sakar ma ta kafin ya ce ” ummm, mai kike ta cewa ne haka?” kasaƙe Abee ta tsaya kawai tana kallonsa cike da mamaki, mamaki take yanzun duk uwar maganganun da ta riƙa yayyafosu tamkar a kunna radio sam Hammad Zai ce bai ji ta ba? Toh wai ma tsareta da ya yi da idanuwansa yana kallonta tamkar yana kallon wani serious film a TV, kallon na mainene?. Katse mata nata tunanin yayi shima In da ya ce ” ummm kallon fa na mainene Daughter?” Ya Ida maganarsa yana ɗaga mata girarsa ɗaya yana kuma sakar mata murmushin nan nasa dake matuƙar tafiyar mata da imaninta. “Umm umm Baffah nikam ba kallonka nake ba” ta faɗi a shagwaɓe, shima shagwaɓe fuskarsa ya yi ya ce ” Umm umm ki faɗi gaskia dai, kina kallewa Mancy ƙani” ya faɗa yana mai kwaikwayon muryata, dariya dukkaninsu sukai a lokaci ɗaya. 

Wani ɗan yaro da bazai wuci shekaru 10-12, ya zo gaban motar nasu hannunsa riƙe da wani ƙanƙanuwar tourch light wanda haskensa ma ba wani na zo a gani bane, kwankwasa ƙofar motar yayi wanda hakan ya sanƴasu tsayawa cak daga dariyar da suke yi  Hammad ya buɗe motar ganin yaro ƙarami ya sanƴasa cewa ” ɗan samari lafiya dai?” Yaron ya ɗan yi murmushi kafin ya ce ” lafiya ƙalau, Baba Malam ne ya ce nazo na tafi daku can wajensa” shiru Hammad da Abee suka yi suna ƙare wa yaron kallo, mamaki shimfiɗe ɓaro ɓaro a samar fuskarsu. Taya wannan ƙaramin yaron ya iya fitowa daga cikin wannan ƙololuwar dajin? taya? Su da su ka girmewa yaron ma sun kasa koda fita cikin motar bare a kai ga shiga cikin dajin amma wai wannan ɗan ƙanƙanin yaron shi a ka aiko ya tafi da su anƴa kuwa babu wani abu a ƙasa?. Abee ce tayi ƙarfin halin cewa ” toh kai ba ka tsoro ne ɗan samari?, sha biyu na dare fa yayi” wani kalan murmushi suka ga ya saki wanda sun gaza fassara mai ma’anar murmushin ” karku damu ku dai sauko mu tafi, kar garin naiman ƙiba a samo rama.” Yaron ya faɗa maganar a dunƙule, Abee ta so tambayarsa mai yake nufi da hakan amma sai ta kame bakinta tayi shiru, don tunanin da zuciyarta ke yi ma ta na cewa wannan ɗin ba mutum bane face aljani atoh in ba aljani bane taya fisabilillah yaro ɗan shekaru 10 zai iya kutsawa cikin dajin nan babba ya fito shi ɗaya?. A hankali suka fita yaron ya yi gaba ya ce ” ku biyo ni kawai a baya, karku bari na ɓace ma ku”. Gyaɗa kai kurum suka yi a tare, Abeedah kuwa sai faman tsinewa Nenne ta ke yi a cikin zuciyarta. 

Lallausar hannunsa ta ji a cikin na ta, da sauri ta ɗago su ka haɗa ido da sauri su ka lumshe idanuwansa a tare, Abee kuwa wani iriyar baƙon yana yi ta ji yana ziyartar ƙwanƴarta. Tafiya suke tamkar zasu ta shi sama, yaron kam na sa tafiyar kam ba’a magana, tafiya suke yi tamkar zasu ƙasar misra. Abee ƙafafuwanta har ciwo ya soma yi mata amma ya ta iya? babu,  dole hakanan za ta haƙura ta jure har Allah ya kaisu gurin malamin tsubbun lafiya. Tafiyar kimanin awa 1 da rabi sukayi kafin Allah ya saka suka isa wajen Teacher lafiya, Abeedah kam takalminta har tsinkewa yayi ƙayoyi dayawa suka caccaki ƙafafuwanta, sun wahala sosai kafin Allah ya kaisu gidan Teacher lafiya, wani ƙaramin bukka ne ma gidan amma ga mamakinsu mutane sunfi sama da 20 jere reras a bakin ƙofar bukkar da alamu dai layi suke kowa na jiran lokacin shingansa ya yi, abin yayi mugun ɗaurewa Abeedah kai wai mai mutane ke tunani ne a duniya haka? Shin dama akwai wani wanda zai iya mallaka ma abu ko ya biya maka buƙatunka sama da Ubangijin taliƙai? Ita abin da ma yafi bata mamaki shine yawan mutanen dake gurin rabin su mata ne mutane 3 ne kawai taga maza, tayaya fisabilillah mata baza su fi yawa a cikin jahannama ba? kuma fa duk wannan abun da suke don su mallaki ɗa namiji ne fa! Annabi ya yi gaskia da ya ce sa’adda ya leƙa wutar jahannama mafi yawan mutanen dake a cikinta mata ne! Allah ya saka mufi ƙarfin zuƙatan mu ameen. 

********************************************* 

“Surayyah, na faɗa miki zuciyana da gangan jikina babu wanda suke muradin gani a wannan lokacin face Suhailat, ki taimakamin dan girman Allah ki kawo min Suhailat wala’allah In ta yafe min Allah yayi min sassaucin abin da ke damuna”. Share ƙwallan idanuwanta ta yi kafin ta ce muryarta a raunane ” Salman!, kwana uku kenan ina mitan zuwa gidansu Suhailat amma mai gadin gidan baya bari ina shiga, ni kaina yafiyarta nake naima”. Hawayen da suka gama taruwa a cikin kwayar idanuwansa ne yayi azamar fara sauka a gefen fuskarsa, ga shi nan dai kwance da ransa amma ba zai iya taɓuka ma kansa komai ba, wannan wani irin rayuwa ce? Mai ya saka duniya zata juya masa baya a yau? Yau duk kwalisar nan ta sa da ji da kai duk babu su, ya tabbata hakkin Abeedah da Suhailat ne ke bibiyarsa tabbatas sakamakon abin da ya aikata musu ne Allah ya juyar ma sa da rayuwarsa a daƙiƙu da ba su wuci 20 ba, baya so sam yana tuna abin da ya faru da shi a watan baya da ya wuce, watan daya yi sanadin zamanto warsa a haka, ciwo ya ci jikinsa kuma ya tabbatar bayi da ranar warkewa. Runtsa idanuwansa ya yi ba dan ya na so ba ya soma tunanin abin da ya faru da shi har rayuwarsa ta koma haka. 

Story continues below


Flash back
Tun bayan rabuwansa da Suhailat da ya dawo ya iske mahaifiyarta ta tafi da ita bai sake bi ta kanta ba, hasalima takardar saki ya aika ma ta In da ya sake ta saki biyu. sosai Suhailat tayi matuƙar yin farin ciki da hakan ya kasance tsakaninsu, don har ga Allah bata da muradin sake komawa cikin gidan Salman, ƙunci da baƙin cikin da ya laftawa rayuwarta a baya kawai ya isheta, baƙin cikinta ɗaya yaron cikinta zai tashi babu kulawar uba a tattare da shi sa’anan zai yi baƙin ciki da ita tunda ita ce ta zaɓa ma sa mahaifi mazina ci, tun abin na damunta har ta cire hakan a cikin zuciyarta ta fallalawa Allah lamuranta. 

tun bayan ya saki Suhailat suka buɗe wani shafin na rayuwa shi da Surayyah, ciki ko harda auren Surayyah da ya yi. 

rayuwa suke yi cike da so da ƙauna tamkar zasu cinye juna. 

Surayyah gaba ɗaya Salman ya sanƴa a ka juyar ma ta da mahaifarta don sam sam Salman bai ƙaunar haihuwa. (baka kaunar haihuwar naga a ka haifeka ai😡mutanen da basu kaunar haihuwa wlh suna bani mamaki, humm Allah dai ya kawo mana sauqin muwafaƙa Ameen) . 

Ita kuwa Surayyah so ya rufe ma ta idanuwanta nan da nan ba tare da wani tunani ba ta yarda a ka juyar ma ta da mahaifarta. Rayuwa suke na jin dadi sosai kafin komai ya zo ya tsaya musu cak! 

Ranar wata litinin da misalin ƙarfe 3:30pm na rana, ya kasance cikin ranaƙun da Salman zai sanar wa duniya baya ƙaunar ranar, don tabbas da ana mai da hannun agogo baya da babu abin da zai hana sa mayarwa ya gyara komai, amma ina komai Allah ya riga ya gama tsarawa!. Ranar ce tayi sanadiyar daƙule farin cikin sa a rayuwa, a ranar ya yi na damar aikata abubuwa masu yawa a cikin rayuwarsa a ranar littin yasan bawa ba komai bane wajen Allah face ƙaramin ƙwaro, wanda a lokaci guda in Ubangiji na so zai daƙule rayuwar bawa a daƙiƙu da ba za su wuci 1 tak ba!. 

A ranar ya gasgata zina ba ɗabi’a mai kyau ba ce, kuma a ranar ya gama aminta zina yana karya garkuwar ɗan adam, a ranar yasan ma’aikin Allah ya yi gaskia da ya ce muguji zina saboda zina na kawar da imani!

MUGUJI ZINA JAMA’A:Zina tana cikin manyan laifuffuka Wanda dukkan shariun da Allah ta’ala ya saukar sun hadu akan haramcin zina,
Al kur’ani mai girma da sunnar Annabi SAW,da dukkan malamai sun hadu akan haramcin zina,kofofin zina guda biyar ne 
1-kallo zuwaga abinda Allah ya haramta
2-Shigar batsa 
3- Kalaman batsa
4-Kebancewa da matar da ba muharrma ba,
5-Shaawa mai karfi babu aure .
Allah taala yace: Mai zina ba zaiyi zina ba yayin da yake zina,sai an cire masa imani.
Abdullah Dan mas’ud ya ce : Duk al’ummar da take zina ,ta jawo wa kanta fushin Allah,da halaka.
Musulunci yayi umarni da tsare abubuwa biyar:
Addini, dukiya, rayuka, hankali, mutunci, nasaba.
Amma zina ita kadai tana rusa wadannan duka.
Hukuncin mazinaci mai aure, kissa ta hanyar jifa, Mara aure bulala dari da daurin shekara.
Ana tabbatar da zina ta hanya uku :sheda guda hudu, mutum yayi ikirari da kansa, samun mace da ciki,babu aure, koh subha.
ALLAH YA KAREMU AMEEN. 

      ” Ban fahimce abin da kike faɗa ba Hajia, kimin bayani kin  sanƴani cikin duhu.” Murmushin yaƙe ta yi kafin ta girgiza kanta ta ce ” ina ce dai Hausa na maka Salman, ba wani yaren ba?, Sarai ka fahimce abin da nake nufi, Toh inma fahimtar ce baka fahimta ba bari nayi maka gwari gwari yadda zaka gane, cewa nayi Likita ya shaidamin ina ɗauke da cutar nan dake karya garkuwan jiki wato HIV/AIDS!” Tari ne ya yi azamar turnuke sa, a lokaci guda ya soma tari tamkar zai Fidda hanjin cikinsa. Hajia ce ta yi saurin kawo masa dauki inda ta mika masa ruwa,  da kyar tarin ya tsaya amma hankalinsa gaba daya baya tare da shi, mai hakan ke nufi kenan? Shi ma yana dauke da cutar HIVAIDS kenan? “Inaa bazai yiwu ba!” Ya furta da ƙarfi lokaci guda yana fici fici da idanuwansa tamkar wanda ke shirin shiɗewa. Da kallo kawai Hajiar tabi sa da shi kafin kuma ta ja dogon tsaki ta ce ” yoo mai nene bazai yiwu ba kenan? Cuta ce na sanar maka ina ɗauke da shi, hakan kuma ya isa ya sanar maka cewa kaima kana ɗauke da kwayar cutar. Toh mainene bazai yiwu ba ?” Ta ida maganarta tana kafe Salman ɗin da duk yake a firgice hankalinsa kwata kwata baya jikinsa, ” Amma bazan iya yafe miki ba Hindatu! Kin san kina ɗauke da wannan mugun ciwon tun farko shine baki sanar min ba? Haba haba mana!! Wannan wacce iriyar mugunta ce kika min haka?” Ga mamakinsa tuntsure wa ta yi da dariya kafin ta ce ” kwantar da hankalinka Salman, ni kaina ban san ina da cutar ba sai kwanannan kuma cutar bawani jimawa yayi a jikin nawa ba ko wata biyu bai kai ba, ina kasan da wa na kwana qarshe? Toh mugun ashe yana dauke da cutar ban sani ba, karka kuskura kaga laifina don dama duk mai sabon Allah qarshensa babu kyau, ina matar aure na kasance mazinaciya! Na ci amanar mijina! Na kwanta shimfiɗa ɗaya  da yaron gidansa, kai cona kai co da rayuwa irin nawa ko don hakkin mijina Allah bazai barni haka ba dole na girbi abin da na shuka!” bai iya cewa da ita ƙala ba, ya miƙe yabar mata cikin gidanta gaba ɗaya, zuciyarsa da ruhinsa cike da nadama kala kala. Bai gama tsinkewa da lamarin ba sa’annan bai gama gasgata lamarin ba kai tsaye har sai da likita ya shaida masa tabbas shima yana dauke da ciwon HIV/AIDS, Allah ne kaɗai ya san iriyar halinda ya tsinci kansa a ciki. Bai taba jin kyamar zina ba sai a yau, ji yake yi duk duniya in har akwai abin da yafi tsana a cikin rayuwarsa toh ya bi bayan zina, a yau ji yayi ya tsani zina da duk wani rai da ke aikata zina a duniya, ya yi Allah wadai da rayuwarsa yabi ye sharrin zuciyarsa ya aikata babban sabo shaidan ya yi masa kidan ganga ya hau ya zauna. 

Story continues below


Ko da ya sanarwa Surrayah ba karamin rudewa tayi ba, itama gwajin farko a ka tabbatar da tana dauke da ciwon tayi kuka har ta gode Allah, likitan ne ya rika tausarsu ya ce karsu damu zaa daura su a kan magani yanzun mafi yawan mutanen dake dauke da cutar sukan surviving. 

Tashin hankalin Salman bai gama sanƴa rana ba har sai ranar da bahagon mummunan labari ya riskesa, anan yayi shahada ya sanarwa Ubangiji don ya sani sarai hakkin Suhailat da Abee ne ke bibiyar rayuwarsa. A ranar litinin ishirin ga watan Disamba shekara ta dubu biyu da sha takwas ne yayi daidai da dakatar da Salman da a kayi daga jami’ar Bayero (BUK) a bisa dalilin da shi kansa bai san mai ya aikata ba! Kawai takardar sallama kawai ya riske, yayi tambayar duniya a kan a sanar masa abin da ya aikata amma fafur kowa ya ce babu takardar sammacin daga wajen gwamnati ne ba daga su ba, bai gama dawowa daga cikin tension ɗin rasa aikinsa ba uban gidansa da suke kasuwanci tare yayi masa koran wulaƙanci, Hajia Hindatu ta sanarwa mijinta duk abin da ya faru iya baƙin ciki wannan bawan Allan yayi sa don baiga hujjan da zai sanƴa matarsa da yaron gidansa cin amanarsa ba, a take ya sake ta saki biyu ya ce ta tattara tabar masa a gida, iya kuka Hindatu tayi sa har hawayenta suka kafe cak! A hanyarta na komawa garinsu sukai hatsari babu wanda ya rayu a cikin motar face direban motar. Alhaji Tafida da haɗin bakinsa ya sanƴa a ka sallami Salman daga aikin gwamnati kuma ko ina ne nan gaba bazai iya samun aikin gwamnati ba, sa’annan ya koresa daga kasuwancin da suke. Wannan lamari yayi matuƙar dagulewa Salman rayuwarsa, daga nan lafiya yayi bankwana a jikinsa, tunani shine ya zamana abokinsa safe, rana, dare a haka tunanin yayi masa yawa kuma nan ne silar kamuwarsa da hawanjini. A ranar talata ne jikin nasa yayi masa tsanani gashi dukkanin  dukiyarsa da ya mallaka babu su don Alhaji Tafida freezing account ɗin sa duka ya sanƴa a kayi, babu abin da Salman ya tsira da shi face motarsa da gidansa da yake ciki. 

A ranar talata ciwon ya ci jikinsa sosai don magungunansa duk sun qare abincin gelen ba samu yake yi ba, Surrayah kam ganin halin ha’ula’in da suke ciki ya sanƴata fitirewa lalle lalle sai Salman ya sake ta amma yaƙi, nan ta kwashe kayanta ta koma Maiduguri garinsu, koran kare iyayenta suka mata suka ce babu su babu ita, ta rasa mafita ta rasa madafa dolenta ta hakura ta juyo ta dawo Kano wajen mijinta. A ranar data dawon ta iske jikin Salman ɗin sai Allah,  baya iya tashi baya iya yin komai alamu sun riga sun gama nunawa mutuwar ɓarin jiki ya Kamasa, tun ranar Salman bai sake iya tashi ba nan yake kashi fitsari da komai, tun Surrayah na dauriya itama har jikin nata ya soma tsanani, Salman ne ya shiga rokonta ta je tabawa Suhailat hakuri wala’allah Ubangiji ya sassauta masa. 

” Shikenan Surayyah, duk ranar da Allah ya saka kika haɗu da Suhailat ko Abeedah ki rokamin yafiyarsu nikam Nawa ya riga ya ƙare a duniyar, Allah nake roko ya shirya duk wani mai hali irin nawa Allah ya nisanci ƴan bayana da faɗawa mummunar ɗabi’ata, ki roƙamin yafiyar su don……………..”  Bai iya gama furta sauran maganganun dake ƙunshe a maƙoshinsa ba wani abu ya tsaya masa rak a ƙirji, tari kawai yake yi ta hanci da baki yana fidda farin kumfa, idanuwansa na kakkafewa duniyar na juya masa, lumfashi yake so ya fitar amma baya iyawa, motsa wa yake so yayi da jikinsa amma jikinsa yaƙi basa haɗin kai, ihu kawai ya iya saki a daidai sa’adda ya furzar da lumfashinsa na ƙarshe a doron duniya!. 

Surayyah kam tuni ta rufta a guje taje kiran mutane don kawo musu ɗauki, koda isowarsu Salman ya riga ya gama kwanakin da Allah ya ɗebe ma sa a duniya, wani ne a cikinsu yayi ƙarfin halin rufe wa Salman idanuwansa dake a kafe yana kallon sama, a hankali ya dubi Surrayyah da jikinta ke famar rawa ya ce ” kiyi hakuri Allah yayi masa rasuwa!.” Ji tayi a lokacin duniyarta ta tsaya mata cak!, Ta kasa ma yin tunanin komai, ta kasa kuka ta naimi hawaye a cikin idanuwanta ta rasa. kuka take son yi amma ta gaza, sai a yau take gasgata lalle kuka ma rahma ne. Tsirarun mutane suka sallaci gawar Salman aka kaisa gidansa na gaskiya. Gidan ya ragi Surrayah Kawai wacce har yanzu hankalinta kam baya cikin jikinta. 

Story continues below


*******************************************
Da kyar da taimakon Allah, a ka samu lumfashinta ya dawo daidai. Allurar bacci likitan yayi mata kafin ya fita a ka barta don ta huta, sosai Mommy da Abban Suhailat da Hafeez sukayi murnar ganin yaran Suhailat, sai dai baƙin cikinsu ɗaya yaran zasu taso cikin rashin kulawar uba. 

Awowi uku taɗebe tana bacci kafin ta farka, bakinta ɗauke da kalimatuh shahada ta buɗe idanuwanta. Ɗakin take bi da kallo tana tuna abin da ya faru, saurin dafa cikinta tayi tajisa wayam hakan ya sanƴata saurin waigawa nan ta ga gadon jarirai da saurinta ta miƙe har tana tuge drip ɗin hannunta. Da saurinta ta ƙaraso gaban gadon da jariren ƴaƴanta ke a kwance, hawayen farin ciki ne yayi azamar soma sauka a kan fuskarta, saurin ɗaukan su tayi tana hawaye ta rungumesu wani iriyar ƙaunarsu taji yana ziyarar ilahirin gabɓan jikinta. Sumbatarsu kawai ta shiga yi tana antaya musu adduo’i kala-kala, a haka likita ya shigo ya risketa, murmushi yayi kafin ya ce ” maman twins an farka kenan?” Yayi maganar fuskarsa dauke da murmushi,sai a sannan hankalinta ya dawo jikinta kallon likitan tayi tana girgiza masa kai alamar eh, Hafeez ne da Mommy suka shigo cikin dakin dukkanin su fuskokinsu dauke da murna. Ya jiki suka soma yi mata ta amsa musu da sauqi, likita ya duba ta kafin ya fita yabarsu.

” Ya Hafeez ka musu khutba?” Murmushi yayi ya ce ” a’a baki ganin mahaifinsu keda wannan hakkin?” Yanayin da yaga ta shiga ya sanƴasa tsananin dana sanin faɗin wannan maganar, cikin fushi ta ce ” in bazaka Yi ma su ba ai babu dole ba sai ka ce ga mai musu ba” ta faɗa rai ɓace, “ke Suhailat na kwaɓeki mai haka?” Mommy ta faɗa a fusace, Suhailat bata sake cewa komai ba ta koma ta kwanta abinta ranta nayi mata susa. 

Kwanan su biyu a ka sallamesu suka koma gida, nan Suhailat ta soma wankan jego, kuma a ranar a ka sanar masu mutuwar Salman Suhailat kam addu’a kawai tayi masa toh in ma bata masa addu’ar ba mai zata masa tunda babu shi a duniyar yanzun?. Ranar da suka ciki sati ranar a kayi suna in da yaran suka ci sunansu Abeedah da Sumayyah(takorar Mommy) inda a ka sakaye sunan nasu L2l Abee da L2l Summy. (Allah raya su a kan Sunnah Ameen) 

*********************************************** 

Basu suka shiga cikin bukkar Malam teacher ba sai wajajen 1:30am na dare, da shigansu yayi masu nuni da wajen zama. Zaune yake kan wata ƙatuwar daddumar fatar rago, tsoho ne wanda a ƙalla zai kai kimanin shekaru 65 a duniya. ƙare masa kallo Abee ta shiga yi na wasu daƙiƙu, baƙine sosai na bugawa a jarida idanunsa manƴa manƴa kamar na Mayu! (Cewar Abee😂) daka gansa zaka hango tsantsan kamanninsa da nupawa, gefemun fuskarsa fari fat tamkar farin takarda. 

Nazarin ɗakin Abee ta shiga yi babu abinda da akwai a ciki face jerin kwarya kala kala, da wasu abubuwan da tunda take a cikin nahiyar ta bata taɓa ganinsu ko saninsu ba, gabansa kuma wani ƙatuwar casbaha ce (tasbi) wanda a kalla zai kai rolls dubu ɗaya a ciki, gefensa kuma wani ƙwarya ne cike da jini!. 

” Barkanku da zuwa!” Suka tsinkayo gardin muryarsa mara amo da sauti na yi masu lale marhabun, a sa’i guda dukkanin su suka ɗago suna kallonsa, da sauri Abee ta saukar da kanta ƙasa don har ga Allah idanunsa ba ƙaramin tsoratar da ita sukayi ba. 

“Barka malam, mun same ka lafiya?” 

“Eh ina lafiya, mai ye ke tafe daku? Duk da ansanarmin abin da ke tafe dakun, mai kuke buƙata nayi mata?” Da ido suka kallo junansu don mamakin abin da ya faɗa, kenan ya san a kan wa suka zo yayi masu aiki kenan? cire idanunsa yayi a kan nata kafin ya kai dubansa ga Malam teacher Wanda ya kafe su da mula-mulan idanunsa, a hankali Hammad ya ce ” Malam….” Tsawan da ya daka wa Hammad ɗin shi yayi azamar maida kalamansa cikin ransa, Abee kam har ta ruɗe. ” Nayi maka kama da malamai ne bawan Allah? Ta wani dalili zaka kirani da malam? kace min boka! Don ni ɗin boka ne mai amfani da shaiɗanu da aljanu, karka kuskura ka kuma dangantani da malamai magadan annabawa!” Ƙuri Hammaf yayi ya na nazarin bokan, ashe yana sane yake take sani ? Allah kyauta ya furta a ƙasar maƙoshinsa. 

Story continues below


” Ka gafar ce ni, boka so muke ka kwance asirin da Hajia ta sanƴa kayi wa mijinta don Alla……..h” nan ma Hammad Bai ƙarasa ba bokan ya gunduma mai ashar! ” Ka kikayi lafuzanka, na sanar maku ni da shaiɗanu da aljanu nake mu’amala, a kan wani dalili ne zaku haɗani da Ubangiji? In shi kuke son ya biya muku buƙatar ku mai ya saka ba kuyi zamanku ba? Sai ku roƙesa ya karya maku sihirin, na kwanɓeku na ƙarshe karku kuskura ku sake haɗani da Ubangiji” ras ras Abee taji zuciyarta na buguwa “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” shine abin da Abeedah ke nanatawa a cikin zuciyarta, yau kuma a wace nahiyar duniya suka tsinci kansu? hasbunallahu oh Allah! mai mutane suka mayar da duniya ne wai? Shin basa tunanin ƙiyama ne? Yaumul hisab? Basa tunanin ranar tsallake siraɗi? Wannan wani kalan bahagon tunani ne da kaucewa addini? Bokan nan babu shakka shi ɗin ya kasance cikin mutanen dake shirka, ya kasance cikin mutanen da suke haɗa Allah da waninsa.

Hammad Kam nadamar zuwansa nan yake, zuciyarsa ma ta fara raunana da tunani kala kala, shin Allah zai yafe masu takowa da sukayi suka zo wajen boka mai shirka? Allah yaga zuciyansu basu tako zuwa gidan boka don ya biya musu bukatunsuba, sun zo ne don ya wargaza asirin da yayi.

” Ina jin ku, nawa zaku biyani in karya aikin? Kasan mu a ƙa’idar aikinmu bamu da amana!, Bama riƙe amana samsam hhhhhh kuɗin ma yanzun da Hajiar zata buƙaci na faɗi mata waye yamata wannan ɗanƴen aikin in ta cike bujena da bugun Abuja tsaf zan sanar mata.” Abee kam kame bakinta tayi kawai don gani ma take in tana Magana da bokan tamkar zunubi take kwasa, Hammad ya ce ” ka faɗi ko nawa kake so zamu baka” dariya sosai bokan ya fashe da shi sa’annan ya ce ” aikin dayawa suke, asirin kuma kala kala nayi mata, zaku bani naira miliyan 3 yanzun inna kammala aikin zaku cikamin Naira miliyan 4 kun amince?”. 

Abee ji tayi haƙurinta na ƙarewa, juriya take tayi amma hakan na naiman gazawa, zuciyarta tafarfasa kawai yake so take kawai ta masa rashin mutunci, wannan muguntar har ina? mai da imani ne zai ce a basa zunzurutun kuɗaɗe har nairan miliyan 7? A kan wani dalili? Sune suka saka a yi aikin asirin komai?. Jin lallausar hannun Hammad tayi a cikin nata riƙe hannunta yayi gam, yana murza hannun na ta a hankali, hakan kuma ba ƙaramin samar mata da natsuwa yayi ba, a hankali taji zuciyarta na lafawa kaɗan kaɗan.

” Babu damuwa zamu biyaka” kallon Hammad boka yayi na wasu daƙiƙu kafin ya ce ” toh inji dumus!” Ya faɗa yana faɗaɗa murmushin fuskarsa, jajayen haƙoransa da suka fentu da goro ya bayyana, zaro wayansa Hammad yayi ya ce ” bari na ma transfer mai account number?” Ba tsoro balle tsoron Allah, boka ya karanto masa account lamba a mintina 4 Hammad ya mass transfer ɗin miliyan 2 da rabi, ya roƙi bokan a kan zai cika sauran zuwa gobe.

” kafin nayi wa mutum aikin asiri ko tsafi, sai na shimfiɗa ma sa sharadɗu in ka ga zaka iya bi zan maka aiki in ka ga bazaka iya bi ba, babu tilas zan bari ka janƴe. A haka Hajia Nenne tazo min don na biya mata buƙatarta yau kimanin shekaru 15 kenan muke tare da ita, gashi kuma yau zan karya mata amana! Toh mai laifina babu? Tsarin aikin nawa ne haka.” Shiru yayi can kuma ya ci gaba da cewa 

” A cikin sharuddan dana gindaya mata sun ka san ce kamar haka:
Na ɗaya dole ne ta daina haɗa shimfiɗa tare da mijinta, na biyu dole sai aljanu biyu sun kusanceta, na uku dole sai ta riƙa yankawa aljanu shanu guda biyar ana basu jinin suna sha duk ƙarshen wata, in tayi wannan ababen toh ilai sun ce su kuma zasu cika mata buƙatarta zata samu abin da take so. Hakan kuwa a kayi duk sharuddan ta bisu, sai muka wa mijin nata aiki muka cire masa sha’awarta a cikin ransa muka cire masa sha’awar duk wata ƴa mace ma a duniya. Aikinta na farko da muka yi mata shine sanƴa ƙiyayyyar ƴarsa Haleematu a cikin zuciyarsa, muka rabasa da ƴan uwansa muka mallaka wa Hajia shi sai yadda tayi da shi kawai zai bi, komai yazo mana cikin sauƙi don Hajiar tana bada haɗin kai a duk abin da a ka umarceta tayi.” Shiru ya sake yi kafin ya ce 

” Zan muku aikin karya asirin duka, amma matuƙar na karya asirin nan toh zai koma kan ita Hajiar ne, wanda cikin ɗayan biyu dole a yi ɗaya a ciki ko Hajiar ta haukace, ko ta samu naƙasa dole a cikin biyu sai ɗaya ya faru da ita, mai kuka ce?” 

Story continues below


Abee kam taɓe baki tayi a zuciyarta tana tunanin toh mai a ciki in Hajiar ta haukace ko ta samu naƙasa? Ita lokacin da take raba ƴaƴan da uba ai bata san zafin dake cikin hakan ba ko?. 

” Muddin komai zai daidaita mun amince”. Hammad ya basa amsa a taƙaice. 

Wani ƴar ƙaramar ƙwarya boka ya fidda ya a jiye gefe, kana ya ciro wani ƙaramin zare a cikin aljihunsa ya sanƴa a cikin wannan kwaryan nan da nan su Abee suka hango kwayar ya cika taf da ruwa, nan bokan ya soma magana cikin wani yare na daban wanda Abee zata rantse tunda take a rayuwarta bata taɓa jin yare makamancin haka ba, wannan sai dai Yaren aljanu kam. 

Ya ɗau kimanin mintuna talatin yana magana kamar bugagge mahaukaci, kafin ya nisa ya daina maganar ya ɗago ya kallo Hammad da Abee wanda kamar haɗin kai dukkanin su addu’ar naiman tsari kawai suke yi a cikin zuciyarsu.

“Ku matso nan, wa kuke hange a cikin ruwan kwaryar nan?”. Hammad da Abee suka matso suna kai dubansu ga kwaryar, fuskar daddy ne ya bayyano a ciki, a tare suka furta “Daddy!” 

“Yauwa, toh komai yazo ƙarshe, ku koma aikin ku zaku ga biyan buƙata nan da sati ɗaya cur!, Ku miƙe Ku tafi!” Ya basu umarni, a hankali suka miƙe Hammad yayi masa godiya suka fito, dare kam ya riga ya gama latsawa hakanan suka kutsa cikin dajin nan da taimakon wannan karamin yaron suka iso har gaban motar suka shiga suka soma tafiya don barin layin gaba ɗaya.

” Baffah, wannan wacce iriyar musiba da bala’ee ne?”. Shiru Hammad yayi kamar bazai amsa ba can kuma ya ce ” lahira akwai kallo my dear” 

************************************************
A gurguje please! 

7days later

A cikin kwanakin nan abubuwa dayawa sun faru da daɗi ba daɗi, ciki har da dawowar Daddy daga india. Abee da Hammad kuwa tun washegarin ranar suka dawo Adamawa, sun biya Yola suka sanarwa Mancy duk abin da ya faru sosai tayi jimamin al’amarin kuma ta roƙi Allah ya kawo masu mafita. 

Daddy zaune yana shan juice a cikin glass cup, hankalinsa gaba ɗaya na a kan kallon Aljaseera yana kallon labaran da a ke a wannan lokacin. Hajia Nenne ce ta shigo sanƴe cikin kayan alfarma jikinta babu inda baya fidda ƙamshi, cike da rangwaɗa tazo ta zauna kusa da Daddy. 

” Alhaji Barka da wannan lokacin” 

“Barkan mu dai” ya bata amsa a taƙaice don tunda ya dawo India yau kwanansa 6 kenan gaba ɗaya in ya ga Hajia Nenne sai yaji yana matuƙar jin haushinta, ji yake tamkar ya miƙe ya bubbugeta haka yake ji, yanzun ma ko kallonta bai iya yayi ba don bai son abin da zai baƙanta ransa. 

Shiru Nenne tayi tana nazarin Alhajin, kwana biyun nan duk ta gaza gane kansa sam baya sakar mata fuska kamar daa wai mai yake faruwa?, Ji kawai yayi a daidai wannan lokacin baayi da muradi bayi da buri da ya wuci ya ga ƴarsa, ji yayi lokaci guda a sa’i ɗaya yana kewanta yana burin sanƴata a cikin idanunsa. Tamkar wanda a ka tsikara ya kallo Hajia Ya ce ” Khadija ina Haleematu?!” Ya nayin yadda ya kirata da yanayin yadda ya tambayeta sunar ɗiyarsa da a ƙalla yau za’a kai kimanin shekaru 20 rabon da taji Alhaji ya furta sunan Haleematu a cikin gidan, cike da ruɗu da firgici ta ɗago kanta tana kallon Alhajin don gasgata lalle shi ɗin ne dai yayi maganar, kansa dake matuƙar sara masa taga yariƙe ta mau yana furta sunan Haleematu. 

Iya birki cewa Hajiar ta gama birkita, faɗi ya ke ” ina Haleematu, Haleematu ina kika shiga fito na ce kizo Daddy na naimanki!” daidai nan Hammad ya kunno kai cikin falon, ganin halinda Daddy ke ciki ya sanƴasa saurin isowa wajen Daddyn. 

” Daddy lafiya? Mai yake damunka?” Ɗan waigowa Hammad yayi yana kai dubansa ga Nanne, wacce a wannan lokacin zufa ya riga ya gama fesowa a gabɓan jikinta, tsoronta ɗaya kar Hammad yaji sunan da Daddy ke furta wa, wai mai ke faruwa ne? tana da son ƙarin bayani mai hakan ke nufi? Hankalin DADDY ya dawo jikinsa ne ko mai wa? Inaaa bazaaiyu ba wallahi bazai taɓa yiwuwa ba, don boka ya tabbatar mata da asirin da yayi mata bazai taɓa kuncewa ba toh uwar mai ya saka Alhajin don iskanci yake kiran sunan matacciyar ƴarsa? Bata son iskanci fa! 

Story continues below


” Hammad ina Haleematu? Inaji a jikina tamkar nayi shekaru dubu ban sanƴata a kwayar idanuna ba, ina ta shiga ne Hammad?” Wani irin ajiyar zuciya Hammad ya saukar, lokaci guda kuma yana furta Alhamdulillah don da dukkanin alamu Allah ya taimake su bokan ya karya sihirin jikin Daddy, tunda gashi yau Daaddy da kansa ke kiran sunan ƴarsa wanda a daa sam sam baya ma zancenta kuma ya hani kowa yin zancenta a cikin gidan. 

” Daddy dan Allah don’t stress yourself, Haleematu tanan ai kana son ganinta ne?” da sauri kamar yaro Daddy ya shiga girgiza masa kai alamar eh, kallon gefen Nenne Hammad ya sake yi amma wannan karon ta wutsiyar idanu yake dubanta, nazarin halinda take ciki yake, ɓaro ɓaro mutum zai karanci tsantsar tsoro da firgici a tattare da ita jikinta ya mutu murus ta ma rasa abin da ya kamata tayi, tananan zaune kamar wacce a ka dasa ta a wajen shekara da shekaru ta kasa koda kwakkwarar motsi!.

A hankali Hammad ya miƙe ya fita gaba ɗaya a cikin falon ba tareda ya sake cewa uffan ba, dama sun riga sun gama tsara yadda zasu bi da wannan ranar komai kuma is going according to plan, Hajia Nenne Yau ƙarshen muguntanta ya zo ƙarshe, dama hausawa sunce ƙarshen alewa ƙasa kuma a juri zuwa rafi dai!. 

Jikinta har kerma yake lokacin da tamiƙe don barin falon, so take kawai ta isa sashenta so kawai take ta ɗau wayarta ta kira Teacher ta sanar masa halinda yau kuma ta tashi ta taras a cikin gidan, wai yau Daddy ne ke kiran sunan Haleematu a kan wani dalili? Toh koma dai wani ɗan banzan ne ya soma yi mata kutse cikin lamuranta zata bin ciko sa kuma zata mugun saɓa masa, zata raba sa da lumfashinsa kankat a cikin duniya sai ya ɗanɗani azaba mai matukar yawa, da ita duk ma waye ke zancen da ita!

” Ke khadija Ina zaki?” Ta tsinkayo muryar Daddy daga sama, waigowa tayi da sauri ta sauke dubanta a kansa, if har she is not mistaken zata iya cewa babu abin da take hangowa a samar fuskar Daddy face tsananin ƙiyayyarta shimfiɗe lakaɗan a samar fuskarsa. Jikinta ne taji yayi lakwas yayi la’asar.

Zata buɗi baki tayi magana kenan, suka tsinkayo muryar Hammad yana sallama, Daddy ne kawai ya amsa masa. Shigowa yayi ya zauna kusa da Daddy kafin ya fara magana ” Daddy, Alhamdulillah dukkanin godiya sun tabbata ga ubangijin taliƙai” 

Kallonsa Daddy yayi ya ce ” haka ne Moallahidi komai dukkanin yabo ya tabbata ga mahaliccinmu” murmushi Hammad yayi, kafin ya kallo Hajia Nenne ya ce ” ki zauna Hajia akwai maganar da zamuyi” Hammad ya furta kansa tsaye lokaci guda kuma yana jin maganar na sa bambamrakwai don bai saba yin dogon magana haka da Hajiar ba. 

” Maganar uwar ubanka zan zauna muyi?” Hajiar ta faɗa a cikin zuciyarta, amma a fili sai ta samu guri ta zauna tana jiran jin bayani ko Allah zai bata haske ta ɗan san maike faruwa!

” DADDY! kana da baƙi” Hammad ya faɗi lokaci guda yana kallon Daddyn, murmushi Daddy yayi kafin ya ce ” toh su waye baƙin?” 

” Yanzu zasu shigo Daddy, Bismillanku” ya furta a tsanake, ido baki hanci duka Hajia Nenne ta buɗe tana baza jinta da ganinta don gano su waye baƙin. 

Mutanen data ga suna shigowa ne ya sanƴa tunaninta da lumfashinta tsayawa na wasu mintuna, duniyar ta taji yana juya ma ta wai mai ke faruwa? mai take gani haka wai? Kar dai Hammad kamun kura yayi mata?.

Baffah Yusuf ne da Baffah Rufa’i da matayensu da ƴaƴa suka bayyana cikin falon, kallonsu Daddy yake yi kallon nan dake ƙunshe da ma’anoni daban daban, ji yake a jikinsa kamar sun shekara dubu bai gansu ba, ji yayi tamkar ya mance su da jimawa. Ƙwaƙwalwarsa ne ta shiga yi masa mubaya’a yana tuna mu’amalar su, mai kenan ya a kayi suka rabu!? Ina suka shiga tsawon shekarun nan? Ina Haleematun sa kuma? So yake yayi tunani amma da zarar ya zurfafa tunaninsa sai yaji kansa na ɗaurewa tamau yana sara masa.

” Rufa’ee, Yusuf? Ina kuka shiga tsawon shekarun nan? mai ya saka kuka tafi kuka barni? Mai ya sanƴa kuka nesanta kanku da Ni? Ina Haleematu? Ina ji kamar bata tare dani da jimawa dan Allah ku fadi min mai ya faru dani? Ina son tuno da abubuwa dayawa amma bani iyawa, kaina saramin yake!”

Story continues below


” Hammad ina Haleematu? Inaji a jikina tamkar nayi shekaru dubu ban sanƴata a kwayar idanuna ba, ina ta shiga ne Hammad?” Wani irin ajiyar zuciya Hammad ya saukar, lokaci guda kuma yana furta Alhamdulillah don da dukkanin alamu Allah ya taimake su bokan ya karya sihirin jikin Daddy, tunda gashi yau Daaddy da kansa ke kiran sunan ƴarsa wanda a daa sam sam baya ma zancenta kuma ya hani kowa yin zancenta a cikin gidan. 

” Daddy dan Allah don’t stress yourself, Haleematu tanan ai kana son ganinta ne?” da sauri kamar yaro Daddy ya shiga girgiza masa kai alamar eh, kallon gefen Nenne Hammad ya sake yi amma wannan karon ta wutsiyar idanu yake dubanta, nazarin halinda take ciki yake, ɓaro ɓaro mutum zai karanci tsantsar tsoro da firgici a tattare da ita jikinta ya mutu murus ta ma rasa abin da ya kamata tayi, tananan zaune kamar wacce a ka dasa ta a wajen shekara da shekaru ta kasa koda kwakkwarar motsi!.

A hankali Hammad ya miƙe ya fita gaba ɗaya a cikin falon ba tareda ya sake cewa uffan ba, dama sun riga sun gama tsara yadda zasu bi da wannan ranar komai kuma is going according to plan, Hajia Nenne Yau ƙarshen muguntanta ya zo ƙarshe, dama hausawa sunce ƙarshen alewa ƙasa kuma a juri zuwa rafi dai!. 

Jikinta har kerma yake lokacin da tamiƙe don barin falon, so take kawai ta isa sashenta so kawai take ta ɗau wayarta ta kira Teacher ta sanar masa halinda yau kuma ta tashi ta taras a cikin gidan, wai yau Daddy ne ke kiran sunan Haleematu a kan wani dalili? Toh koma dai wani ɗan banzan ne ya soma yi mata kutse cikin lamuranta zata bin ciko sa kuma zata mugun saɓa masa, zata raba sa da lumfashinsa kankat a cikin duniya sai ya ɗanɗani azaba mai matukar yawa, da ita duk ma waye ke zancen da ita!

” Ke khadija Ina zaki?” Ta tsinkayo muryar Daddy daga sama, waigowa tayi da sauri ta sauke dubanta a kansa, if har she is not mistaken zata iya cewa babu abin da take hangowa a samar fuskar Daddy face tsananin ƙiyayyarta shimfiɗe lakaɗan a samar fuskarsa. Jikinta ne taji yayi lakwas yayi la’asar.

Zata buɗi baki tayi magana kenan, suka tsinkayo muryar Hammad yana sallama, Daddy ne kawai ya amsa masa. Shigowa yayi ya zauna kusa da Daddy kafin ya fara magana ” Daddy, Alhamdulillah dukkanin godiya sun tabbata ga ubangijin taliƙai” 

Kallonsa Daddy yayi ya ce ” haka ne Moallahidi komai dukkanin yabo ya tabbata ga mahaliccinmu” murmushi Hammad yayi, kafin ya kallo Hajia Nenne ya ce ” ki zauna Hajia akwai maganar da zamuyi” Hammad ya furta kansa tsaye lokaci guda kuma yana jin maganar na sa bambamrakwai don bai saba yin dogon magana haka da Hajiar ba. 

” Maganar uwar ubanka zan zauna muyi?” Hajiar ta faɗa a cikin zuciyarta, amma a fili sai ta samu guri ta zauna tana jiran jin bayani ko Allah zai bata haske ta ɗan san maike faruwa!

” DADDY! kana da baƙi” Hammad ya faɗi lokaci guda yana kallon Daddyn, murmushi Daddy yayi kafin ya ce ” toh su waye baƙin?” 

” Yanzu zasu shigo Daddy, Bismillanku” ya furta a tsanake, ido baki hanci duka Hajia Nenne ta buɗe tana baza jinta da ganinta don gano su waye baƙin. 

Mutanen data ga suna shigowa ne ya sanƴa tunaninta da lumfashinta tsayawa na wasu mintuna, duniyar ta taji yana juya ma ta wai mai ke faruwa? mai take gani haka wai? Kar dai Hammad kamun kura yayi mata?.

Baffah Yusuf ne da Baffah Rufa’i da matayensu da ƴaƴa suka bayyana cikin falon, kallonsu Daddy yake yi kallon nan dake ƙunshe da ma’anoni daban daban, ji yake a jikinsa kamar sun shekara dubu bai gansu ba, ji yayi tamkar ya mance su da jimawa. Ƙwaƙwalwarsa ne ta shiga yi masa mubaya’a yana tuna mu’amalar su, mai kenan ya a kayi suka rabu!? Ina suka shiga tsawon shekarun nan? Ina Haleematun sa kuma? So yake yayi tunani amma da zarar ya zurfafa tunaninsa sai yaji kansa na ɗaurewa tamau yana sara masa.

” Rufa’ee, Yusuf? Ina kuka shiga tsawon shekarun nan? mai ya saka kuka tafi kuka barni? Mai ya sanƴa kuka nesanta kanku da Ni? Ina Haleematu? Ina ji kamar bata tare dani da jimawa dan Allah ku fadi min mai ya faru dani? Ina son tuno da abubuwa dayawa amma bani iyawa, kaina saramin yake!”

Ganin Haleematu tsaye da ranta a cikin falon Daddy ba ƙaramin girgiza ƙwaƙwalwar Hajia Nenne tayi ba, wai waye da wannan ɗanƴen aikin waye yayi mata zagon ƙasa haka? dama Haleematu bata mutu ba? Ƙarya a ka mata a ka sanar mata da Haleematun ta mutu sun kasheta? Kodai mafarki take yi?. Da sauri Hajia Nenne ta shiga mintsilin jikinta ko wai zata farka daga baccin da take ciki sa’annan taga komai cikin mafarki ne ya faru ba a fili ba! Da a yau ba gobe ba zata sallami Abee a aiki sa’annan ta saka a juyar da hankalin Hammad ya dawo mahaukaci. 

Amma da dukkanin alamu ba mafarkin take yi ba komai dake faruwa a zahiri ne, ji tayi ƙafafuwanta suna gaza ɗaukarta zuciyarta na barazanar bugawa, ilahirin jikinta babu inda bai shiga karkarwa ba, jinta da ganinta taji yana ɓacewa, bata iya jin abin da kowa ke faɗi a cikin falon idanuwanta sun kafe cak!, Cikin sakannin da basu wuci 2 ba ta faɗi a ƙasa warwas don ƙafafuwanta sun gaza ɗaukar ta, lumfashinta ne ya tsaya callin cak bata fidda lumfashi, kamar haɗin baki Daddy ma kafin suyi aune ya faɗi warwas a ƙasa, don ganin fuskar Haleematu da yayi tunaninsa ya dawo jikinsa abubuwan da ya aikata mata ya shiga kunno masa a kai, ya kasa jurewa ya kasa sanin dalilinsa na aikata wa ƴarsa tilo wannan lamurran, mai ya sanƴasa korarta a cikin gidansa wani laifi ta aikata masa haka ya riƙa musguna mata ? Anƴa shi ɗin ya cancanci zamtowa uba? Anƴa Faɗi (mahaifiyar Mancy) a duk inda yake a yanzu zata iya yafe masa a kan abin da ya aikatawa ƴarsu? Baya jin Faɗimatu zata taɓa yafe masa, “innalilahi wa’inna ilaihir raji’un”. Shine abin da Daddy ya iya furtawa dalilin kansa da yayi matuƙar juya masa idanuwansa suka kafe daganan ya faɗi ƙasa warwas ba tare da ya sake sanin halinda yake ciki ba a raye ko a mace!?. 

Da gudu Mancy ta ƙaraso gaban Daddy, durƙusawa tayi tana kai hannunta kan ƙirjinsa, dogon lumfashi ta sauke don jin bugun zuciyarsa da alama yana lumfashi. 

Hammad da Baffah Yusuf ne suka ɗau Daddy a ka fita da shi don kaisa asibiti, babu wanda yabi ta kan Hajia Nenne wacce ke kwance bata koda ƙwakƙwarar motsi. Abeedah tabi su Hammad, falon ya rage daga Mancy sai Matayen Baffaninta da yaransu, a hankali Mancy ta ƙaraso gaban Hajia Nenne so take ta taimaka mata don bai kamata a banzatar da ita hakanan ba, kai hannunta tayi daidai saitin ƙirjin Hajiar taji sam ƙirjin Hajiar bai buguwa a hankali ta shiga ƙarewa Hajiar Kallo, matar da tayi sanadiyyar rabata da ahalinta na tsawon shekaru 22, matar data haddasa ƙiyayyarta a cikin zuciyar mahaifinta itace silar daƙulewar rayuwarta ta ƙarasa ƴan matancin ta Babu uwa babu uba babu dangin uwa babu dangin uba. “HALEEMATU!” ta tsinkayo muryar wata na kiran sunanta, hakan ya sanƴa Mancy waigowa don ganin waye, duk da jimawar da sukay basu haɗu ba bata jin zata iya mance fuskarta komin jimawar rashin haɗuwan su kam. 

“Asma’u!” Mancy ta faɗi a fili, Asma’u wanda shigowarta kenan cikin sashen ta ƙaraso wajen Mancy cike da mamaki da ruɗu. 

” Haleemat, dama kina raye baki mutu ba?” Miƙewa Mancy tayi a zaunen da take kusa da Hajia, kafin ta Kallo Asma’u wacce ta ƙureta da kallo kawai tana mamaki sosai, ” a’a ban mutu ba Ma’u, inanan da raina harda yarana su uku” wangale baki Asma’u tayi ta ce ” yara kuma? Har kin haihu ma?! Allah mai iko ina kika shiga tsawon shekarun nan? mai ya sanƴa baki dawo ba? ni a ka ce min kin mutu dana dawo daga US lokacin. Kai abun da mamaki!” Asma’u ta faɗa, murmushi Mancy tayi kafin ta ce ” ba abun mamaki bane, ki taimaka ki kira wani ya taimaka a fidda Hajia a kaita asibiti tana da buƙatar taimakon gaggawa” Mancy ta ida maganarta ta nai wa Asma’un nuni da yatsar hannunta inda Hajia ke a kwance. Har ga Allah Asma’u bata lura da Hajia ba don mamakin ganin Haleematu ya sanƴa ta kasa ganin komai ma. Da sauri ta fito ta kira masu aikin gidan a ka fiddo Hajiar a kai asibity da ita.
************************************** 

A hankali ya shiga buɗe idanuwansa lokaci guda kuma bakinsa na furta sunayen Allah, sauke idanunsa yayi caraf a kan kekkyawar fuskarta. Kanta ne a kwance a gefen gadon da yake kwance, hannunta ta sakala kan nasa a haka bacci ya sureta. 

Story continues below


Ƙare ma ta kallo kawai ya shiga yi, bai san lokacinda hawaye ya soma zuba a samar kuncinsa ba, tausayin kansa da na ƴarsa kawai zuciyarsa keyi ya rasa sukunin zuciya baya tunanin Haleemat zata iya yafe masa abin da ya aikata gare ta. Shekaru kusan 22 rabonsa da ƴar cikinsa, ƴarsa tallin tal, mai wai ya shiga kansa ne haka da har ya iya korar ƴarsa da kansa don kawai taƙi auren zaɓin da yayi mata? Baya manta irin cuzguna war da yayi mata a baya, anƴa shikam bai butulcewa Allah ba kuwa? bayan shekaru aru aru da har ya fidda ran samun rabon ɗan cikinsa, Allah ya duba masa ya basa Haleemat amma ya kasa sauke hakkinsa a kanta? Ya kasa kiwata abin da Allah ya basa shin ta hakan zai godewa Allah kenan?. 

” Abbaaah!” Haleematu ta katse masa tunaninsa a sa’adda ta kirasa, kasa janƴe idanunsa yayi a kanta ji yake in har ya ɗauke kallonsa a kanta toh kuwa zata ɓace masa. Da sauri Mancy ta miƙar da kanta a kan gadon tana kai dubanta ga mahaifinta, hawaye taga yana faman tsere a bisa kuncin nasa hakan ba ƙaramin tayarwa da Mancy hankali yayi ba da sauri ta miƙe tana faɗin ” Abbaah, Abbaah mai ya saka kake hawaye? ko dai jikin ne? Bari na kira likita yazo ya duba ka kaji Abba kadaina hawayen haka don Allah.” Mancy ta ida maganarta muryarta a sanƴaƴe lokaci guda kuma tana share hawayen da ya soma zirya a bisa kuncinta, da sauri Daddy ya kama hannunta yana ɗan furzarda huci yana kuma murza hannun Mancy a hankali ba kuma tare da ya janƴe idanunsa a kanta ba, kallonta kawai yake kamar zai cinƴeta a hankali cikin muryar marasa lafiya ya ce 

“Ɓingel am!” 

Ya furta a hankali, kallonsa Mancy tayi tana jin wani irin daɗi na ziyartarta. oh Allah yaushe rabon data ji wannan sunan a bakin mahaifinta? shi ne kaɗai a duniya yake kiranta da wannan sunan wallahi tayi kewan mahaifinta, Hajia Nenne bata kyauta mata ba data rabata da mahaifinta wanda tafi qauna sama da komai a cikin rayuwarta, sosai take bala’een ƙaunarsa amma anyi mata katangar ƙarfe da shi. 

Share hawayenta tayi tana murmushi ta ce ” Na’aam Abbaah Na’am” murmushi Daddy yayi kafin ya ce 

“Joɗu (zauna)” da sauri Mancy ta koma ta zauna tana ƙarewa dattijon mahaifinta kallo. 

” Ɓingel, na sani ban cancanci ki yafe min ba amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafewa Abbaah, Abbah ya tuba Ɓingel. Ban san mai ya sanƴani aikata miki hakan ba amma inaso kisani wasu lokutan ba da son raina nake aikata miki wasu abubuwa dayawa ba, wasu lokutan inna miki abu har kuka nake yi in na kaɗaice ni kaɗai, amma hakan kuma bazai sanƴani gobe ma na nuna miki hantara da ƙyashi ba wallahi bansan mai ya saka in har na ganki sai naji haushi na ziyartar zuciyata ba matuƙar ban miki rashin mutunci ba zuciyana baya iya samun sukuni, a yafayam Ɓingel am useni (ki yafemin ƴata don Allah).” 

Daddy ya ida maganarsa lokaci guda kuka yaci ƙarfinsa, Mancy dama tun tuni ta soma gunjin kukanta, ta sani sarai aikin asiri ne ke ɗawainiya da mahaifinta a lokacin shi ya sanƴa ya aikata mata dukkanin abin da yayi ɗin a baya, sam sam dama tun fil’azal bata riƙesa a zuciya ba don tasan ba yin kansa bane tursa sa shi  a ke. 

Daddy kuka Mancy kuka, an rasa mai lallashin wani. 

Da sallamansu suka idasa shigowa cikin ɗakin, ganinsu a wannan yanayin ba ƙaramin tayar musu da hankali yayi ba, kallon junansu sukayi a lokaci ɗaya kafin kuma suka hanzarta idasa zuwa wajensu. 

Abee tayi saurin rungumar Mancy ta baya, Hammad kuma ya zagaya wajen Daddy yana mai taimaka masa don ya miƙe. 

” MANCY, kibar kukan haka don Allah”. 

Abee ta furta a hankali, goge hawayenta ta shiga yi tana saakarwa Abeen murmushi, Daaddy kam kallon Abeedah kawai yake yi baya koda ƙyaftawa kamannin ƴarsa da jikarsa har yaɓaci yadda kasan fuskar Mancyn a ka cire a ka sanƴawa Abeen haka kamanninsu yake. 

Story continues below


“Abeedah!” Daddy ya furta a hankali, ɗagowa Abee tayi tana kallon Kakanta. babu abin da take iya hangowa cikin ƙwayar idanunsa face tsantsan So da ƙaunarta shimfide cikin idanunsa. 

A hankali ya buɗe mata hannayensa alamar ta taho garesa, aikam tamkar jiransa take dama ya bata damar yin hakan, da hanzarinta ta shige cikin jikinsa ba tare da tasan dalilin komai ba taji ta fashe da kuka, kuka take yi mai tsuma ran duk mai sauraro. 

Cikin sigar lallashi Daddy ya shiga yin petting bayan Abee a hankali har kukanta ya soma raguwa, Hammad kuwa narai narai ya koma don jin kukan nata yake yi har cikin ransa. Suna a haka Abbi da Farhana da Harees da Baffah Rufa’ee suka shigo cikin ɗakin, har wannan lokaci kuma Abee na a rungume a ƙirjin kakanta idanuwanta a rufe tana runtsa hawayenta. 

Kai dubansa yayi wajen su Abbi, a hankali kuma ya shiga ɗaga Abee daga cikin jikinsa yana ƙarewa Abbi kallo, Abbin ma Daddyn yake kallo. Mancy ce tayi murmushi kafin ta ce ” Abbaah, ga mahaifinsu Abeedah, wa’ancan kuma ƙannen Abeedah ne”. Mancy ta ida maganarta tana mai nuni wajajen da su Farhana ke a tsaye suna kallon kakansu. 

” Usman!” Daddyn ya kirawo Abbi,  ɗan murmushi Abbi yayi yana mai ƙarasowa kusa da Daddy, “Naam Abbaah, ya jikin ka kasamu sauqi sosai? Allah ƙara maka lafiya Abba”. Murmushi Daddy yayi ya ce ” Ameen Usman, Allah yayi muku albarka dukkaninku ya raya maku zuri’arku ya sanƴa tabbatacciyar salama a tsakanin ku duka” a tare dukkanin su suka amsa da Ameen, nan su Farhana suka shiga gaida Daddy ya amsa musu fuska a sake yana mai tambayar sunayensu suka amsa mai ya shiga sanƴa musu albarka. A haka likita ya shigo ya iskesu kowa na murna yau dai Mancy taji ta sakayau abin da yake binne cikin ranta a yau ta haƙosa burinta ya cika, yau gata cikin daginta kowa na murna da farin cikin ganin juna, murmushi Mancy ta ɗan yi kafin ta furta a hankali ” ya Ubangijin annabi Muhammadu, na roƙeka ka dawwamar da farin ciki a cikin zuri’ata ya Allah”. ” Ameen Adda Halee” ta tsinkayo muryar Hammad murmushi tayi tana mai jinjinawa Hammad ɗin, don tabbas in banda don shi da duk hakan bazai kasance ba. 

Likitan ne ya ce su fita su bar Daddyn ya huta, don ya masa allura bacci ba ya kuma buƙatar hayaniya don gudun tashin hawan jininsa. 

*********************************************** 

2days later (Bayan kwana biyu) 

A cikin kwana biyun Daddy ya samu cikakkiyar lafiya sosai, kullum kuma yana tare da ƴarsa a koda yaushe kuma bata da buri face sanƴasa cikin annashuwa sam bata barinsa yana shiga damuwa da zarar ta fahimci yana son fara tunane tunane take jansa da hira, hira zata zauna ta masa na ban dariya hakanan Daddy zai ta razgar dariya har ya gode Allah. Ko da likita ya zo ya auna BP ɗin Daddyn sosai ya ga BP ɗin ya sauko hakan kuwa ya sanƴa likitan basu sallama haɗe da basu sharudɗa a kan a daina barin Daddyn yana shiga damuwa. 

Da dawowan su gidan ƴan uwa suka soma cike gidan, abin da a shekarun baya sam basu da ƴancin zuwa gidan ɗan uwansu. sosai kowa ke murnar dawowar Mancy, ƴan ƙauyen Mayo belwa da Mambila ma duk sunzo ganin Mancy, Abee har mamakin yawan ƴan uwansu ma take, dama suma a she suna da ƴan uwa har haka? Kyawawa asalin fulanin usul,  masu ji da kyau da ilimi? Oh Allah ina ma yau Suhailat da Salman da mutanen unguwansu na a kusa su zo suga yau suma suna cikin ƴan uwansu, suma suna da asali kamar kowani ɗan adam. Hmmm shi yasaka sam sam babu kyau kana yanke wa mutum hukunci kai tsaye ba tare da kayi bincike ba, ji yadda a daa kowa ke hantarar iyayenta a na cewa zaman dadiro suke ba su da asali daga sama suka faɗo, yau a ce zasu san cewa Alhaji Abubakar Gidaddo Dala wannan fitaccen ɗan kasuwan, shine Mahaifin Mancy kakan Abeedah surukin Abbi, wani kalar tabarmar kunƴa zasu naɗe? Burinta a yanzu bai wuci Salman ya san ita ɗin mai asali ce, kuma ƴar babbar  gida ce ita ɗin, ya fasa aurenta don bata da asali ai kam gashi yau ta samo asalinta, danginta masu cikakkiyar asaline yanzu kam gori da habaici sunƙare musu cak don suma yanzun masu cikakkiyar asali ne.
*************************************^*****
(Ina labarin Nenne ne wai? Bari mu waiwayota) 

Story continues below


Da isarsu asibiti, a kayi saurin amsarta a ka wuce da ita Emergency room, Asma’u kam sai kuka take tayi ta rasa mai ke yi mata daɗi ita kam a yanzu. Bata san abin da ya faru sosai ba don ba ta gurin sa’adda komai ya faru amma da dukkanin alamu tana mai ji a jikinta yau ƙaryar su ya ƙare asirin komai ya gama tonuwa, tunda ga Haleemat ta dawo ai kuma bakin alƙalami ya riga ya gama bushewa, sauransu kaɗan ne kawai. 

” Asma’u bari naje asbitin da a ka kai Daddy pls, in ta farka ki kira ki sanar mini Allah ya bata lafiya” Mancy ta faɗa a taƙaice, kallonta Asma’u tayi kaɗan a ranta tana mamakin hali irin na Mancy, shin  har yanzu ana samun masu hali irin na Haleemat kuwa? Wallahi inda ita ce a matsin Haleemat babu abin da zai sanƴata sake kusanci da Hajia Nenne, mutum da yayi sanadin raba ka da farin cikin ka har yaushe zaka zo ka tsaya masa a kai don kawai bai da lafiya? Tab gaskiya ta jinjina ma Mancy ita kam bata ji zata iya hakan, ilai kam har addu’ar mutuwa ma ƙila tayiwa Hajiar. 

” Shikenan Haleemat, Zan sanar mikin mun gode” murmushin yaƙe Mancy tayi kafin ta ce ” karki damu babu komai, yiwa kaine ai Allah ƙara afuwa” Mancy ta faɗa tana mai juyawa don barin asibitin. Da kallo kawai Asma’u tabi Mancy har ta ɓacewa ganinta.

” Asma’u mai likitan ya ce na damun Yayah?” Dogon lumfashi Asma’u taja kafin ta ce ” ai har yanzun basu fito ba ma Faruuk”  jinjina kai yayi ya ce  ” Allah bata lafiya, amma wai mai ya faru haka?” Ɗago da idanunta tayi tana duban Faruk kafin ta ce ” aww ashe kana office lokacin da komai ya faru ko?” Gyaɗa mata kai yayi alamar eh, ” oh Haleemat ce ta dawo, wannan inƴamurar kuma a she ƴar Haleemat ce, toh ina ganin shock ɗin ganin Haleematun ne ya sanƴa Hajia faɗuwa ƙasa warwas” tunda ta soma maganar ya kafe ta da idanunsa baya koda ƙyaftawa, mamaki yake sosai da jin abin da take faɗi. 

” Wacce Haleemat kike magana ke kuwa Ma’u?” A hasale dama cike take da shi fam ta kallosa ta ce 

” Wacce Haleemat ɗin ka sani hala? bayan ƴar Alhaji?! ” Ta faɗi rai a ɓace,  don abin da ya dameta ma kawai ya isheta bata bukatar ya sake ƙara mata wani tension ɗin na daban. 

“Haleemat?! Haleematu dai ƴar Alhaji?” Ya ida maganarsa da a yarin tambaya a kai. ballo masa harara Ma’u tayi kafin ta ce 

” a’a kamanta ƴar Hajjaju dai” 

ta basa amsa a daƙile, kallonta yayi yana mamakin ta ita kuma mai ya dame ta haka?. 

“Kinga malama kifito fili ki sanarmin abin da ke faruwa, stop beating around the bush”  ya bata amsa fuskarsa a ɗaure tamau, ta fi kowa sanin halin Faruk sarai yanzun nan in batayi wasa ba  har ta bari ransa ya ɓaci sai ya mangareta a wurin babu ruwansa, don haka ta  haɗiyi fushinta ta shiga sanar masa duk abin da ta sani. 

Shiru yayi jikinsa duk ya fara mutuwa murus, mai kenan? Mai yake shirin faruwa ne hala haka? Oh Allah kardai yau ce ranar tonuwar asirinsu?. 

Bai kaiga yin tunani na gaba ba likita da fitowan sa kenan daga cikin  ɗakin Emergency ya katse masa tunaninsa. 

” Excuse me, Please see me in my office now ( Ku iske ni a offishi na yanzun nan)” ya basu umarni.

******** 

  ” Am sorry to say, munyi iya yin mu don ganin mun ceci matar nan daga stroke but abin yafi ƙarfinmu” 
a sukwane suka kallo likitan a tare, bakinsu na karkarwa kamar haɗin baki suka ce ” stroke kuma Dr?” Jinjina musu kai yayi kafin ya ce ” Yes, ina mai baƙin cikin  sanar muku patient ɗin ku ta samu mutuwar ɓarin jiki ( paralyse), faɗuwar da tayi ya janƴo mata hakan and a bisa bin ciken mu zuciyarata na barazanar bugawa but in sha Allah zamu san abin yi yanzun dai zamu ɗaurata a kan magani” 

Story continues below


” Likita shin zata iya warware wa? I mean will she be back to normal?”. Faruk ya tambaya likitan cike da damuwa, gyara zaman gilashin fuskarsa yayi kafin ya ce ” there is hope, mutane da dama sukan yi sa’ar warkewa in an musu aiki but ba’a aikin anan ƙasar sai dai kamar ƙasar india, US, Paris da dai sauransu. Hopefully in a kayi aikin she will be back to normal” 

Shiru sukai kamar basu da lakka a jiki, duk jikinsu a sanƴaƴe, yanzun mai abin yi?. 

************* 

Bayan fitowarsu daga office ɗin likitan Asma’u ta dubesa ta ce ” mai mafita wai?” 

” Mu fitar da ita kawai waje, a yi mata aikin bari na koma office na duba wasu abubuwan ma cire kuɗi cikin secret folk bank” gyada masa kai kurum Asama’u tayi. 

*************
4hours ago

Ƙwaƙwalwarsa ne ya tsaya cak, ya ma rasa ta ina zai fara tunanin mai ya kamata yayi, taya hakan ya faru? Dafe kansa yayi don juyawar da yaji yana yi masa. 

” How? Taya account ɗin zai zamana empty babu kuɗi ko kwandala a cikin sa” babu ma abin da yafi basa mamaki tamkar ganin hatta account ɗin Hajia Nenne asalin account ɗin ta ma babu ko kwandala a cikinsa da dukkanin alamu freezing na account ɗin a kayi, shin waye da wannan ɗanyen aikin mai ke faruwa wai?” 

***************** 

Kyalƙecewa tayi da dariya harda riƙe ciki, ta ce” Baffa wallahi dama ance ƙarshen tiƙa tiƙa tik, rana dubu na ɓarawo rana ɗaya tal na mai kaya!, Yau ƙarshen Nenne da ƴan uwanta yazo gangare, don Allah ji fuskar Faruk kamar zai yi kuka” nan ma ta kuma fashewa da wani sabon dariyan tana ƙara kallon Faruk daga cikin system don suna monitoring dukkanin motsinsa. 

” Daughter baki da dama” . Mancy da shigowarta kenan cikin falon sanƴe da kayan alfarma ta dube su ta ce ” ha’a duniyar ce halan tayi maku daɗi dariyan mai kuke haka?” Ta faɗa tana mai faɗaɗa fara’ar fuskarta. 

” Hmm wallahi Faruk mukewa dariya fa” Abee ta bata amsa, ” a kan wani dalili zakuyi masa dariya?”
” Mancy, freezing account ɗin ƙungiyar su mukai kaf muka mai da komai cikin asusun Daddy, hatta account ɗin Hajiar ma munyi freezing mun mai da komai cikin asusun Company na Daddy” jinjina kai Mancy tayi kafin ta ce 

” Allah maku albarka, kuma ya baku ƴaƴan da zasu muku abin da kuka mana fin namu, thank you har ban da bakin yi muku godiya” 

“Awwn Mancy, karki saka ni kuka mana  Ameen Ameen” Abee ta faɗi a shagwabe sa’annan tana share kwallan da suka tarun mata a kwayar ido. 

Rungumeta Mancy tayi tana petting bayanta Hammad kuma na gefe yana kallonsu, ji yayi sun matuƙar burgesa ƙaunarsu na ta kunno cikin ruhinsa. 

************************ 

1 week later ( a gurguje plsssss) 

Cikin satin abubuwa dayawa sun faru, ciki harda tsanantar  ciwon Hajia Nenne,  ya kai ya kawo yanzun magana ma da kyar take yinsa, bata iya motsa ko ina a jikinta tana a kwance ne kawai amma mara banta da gawa shine lumfashi kawai. 

Sosai jikinta ya tsananta, nan take fitsari da komai wari kawai shi zai fara maka lale marhabun inka tunkarota, Asma’u da faruk da Mancy ne kawai ke zuwa wajenta. Abin duniya ya taru yayi mata yawa zuwa wannan lokacin HajiaNenne tayi matuƙar yin nadamar abubuwa dayawa data aikata a cikin rayuwarta, yau dai yarinƴar data so rabawa da duniya itace a kanta a tsaye tana bata taimako, babu hantara babu kyara haka Mancy zata wanketa ta sauya mata kaya, abin da ƴan uwanta suka gaza yi mata kenan Asma’u kam har toshe hancinta take yi wasu lokutan don kawai tijara irin nata.

Story continues below


Roƙon duniya Mancy ta shiga yiwa Daddy a kan ya taimaka ya bar Hajia ta dawo cikin gidan, amma Daddy fafur ya ƙi , hakan bai sanƴa mancy daina yi masa mita ba daga ƙarshe dai ya amince ya bar Hajiar ta dawo, amma kuma yace babu shi babu ita don har takardar saki ya bata. 

Wannan saki ba ƙaramin sake dagule rayuwar Mancy yayi ba, wannan shine samu da rashi a lokaci ɗaya. 

**************

Zaune suke su duga a babban falon Daddy, Babu wanda baya a ciki, Hajia Nenne ce ƙarshen shigowa ita da Mancy wacce ta gungoro Hajiar kan keken guragu, kallo ɗaya tak Daddy yayi musu ya ɗauke kansa, in banda bai son ɓacin ran ƴarsa da babu abin da zai hana sa yiwa Hajia Nenne korar kare sai ya wulakanta ta fiye da tunanin mai karatu,amma taci sa’ar Mancy don da yaga ÿarsa cikin damuwa gwara yayi mata koma mai nene in har bai fi karfinsa ba, duk abin da yafaru a baya ÿan uwansa sun sanar masa iriyar cin kashin da hajiar ke yi masu komai da komai har kudinsa  da take sanƴasa asara har ƙungiyar data buɗe babu abin da ba a sanar masa ba. 

Yayi bakin ciki iya bakin ciki, yau ina ma Yape (mahaifiyar Daddy) Na da rai taga abin da Hajia ta aikata wa danginta, sun riketa da zuciya ɗaya ita kuwa ta watsa musu ƙasa a ido, ta mayar da alkairan da suka mata da sharri iri iri. Yayi shiru ne ya bar ta amma ba wai don ya yafe mata ba sai dai ya barta da Allah ranar qiyama Allah zai bi masa hakkinsa shi da ƴarsa. 

Abee kam tun tana mamaki da haushin taimakon da Mancy kewa Hajia Har ta daina, ta tabbata halin Mancyn ne haka batada riƙo sam a zuciyarta, tana da kyan hali da yafiya da maida komai ba komai ba. Ita kam bata tunani wallahi zata iya wannan qarfin halin na Mancy da ita ne a matsayin Mancy da tuni an shafe tahirinta a cikin gidan.

A gefe Mancy ta tsayar da keken Hajiar kana ta samu guri kusa da matar baffah Yusuf ta zauna. 

Hammad ne ya buɗe taron da addu’a kafin Daddy ya soma Magana.

” Alhamdulillah, dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin taliƙai, yau ina yi maku lale marhaban da haɗuwar mu duka a guri guda, ina sake baiwa dukkanin ku haƙuri ku samu wani wuri a cikin zuciyoyinku ku yafe min, ni ɗin na sakance mai laifi a gareku hakan kuma ya samo asaline ta dalilin muguwar mata da Allah ya haɗani da ita, ta shiga ta fita ta rabani da dukkanin ku” daga nan Daddy yayi shiru saboda ɗacin da zuciyarsa ke yi masa, Hajia Nenne kuwa hawayen nadama da baƙin cikin hali irin nata ne ya soma gangarowa a bisa kuncinta, gashi dai tana jin duk abin da suke faɗi amma bata da damar iya yi musu magana ko motsa jikinta taje ta basu haƙuri ta naimi afuwarsu. Ita kam ta sani nata yazo ƙarshe yanzu kam, a yanzu zata fara girbe abin da ta shuka kafin kuma ta koma ga mahaliccinta tasani ita ɗin abin a kƴamata ne, duniyarta bata amfana mata komai ba hasali ma tabi ruɗin shaiɗan ta ɓata duniyarta da lahiranta bata tunanin Allah zai yafe mata tarin abubuwan data aikata. Daddy ne ya ci gaba da magana 

” Kamar yadda kuka sani, alaƙar auratayya ya ƙare a tsakanina da wannan azzalumar matar!, Bana tunanin zan iya yafe miki khadija, don ke ɗin kin cika muguwa azzaluma mai raba zumunci, kije gaki ga duniya Allah kam bazai barki a haka ba koda hakkin marainiyar Allah kawai ya isa duniyarki tayi shawagi, kin ci sa’a Haleemat ta roƙamiki banda haka da kin ɗanɗani azaba da uƙuba da wallahi sai na koya miki hankalin da kika rasa a baya, ƴan bayanki babu wanda zai sake marmarin yin iriyar halayyarki, zan barki a cikin gidana don darajar da ƴata ke da shi a cikin idanuwana amma zaki tattara ki koma BQ shine kawai alfarmar dazan iya miki,” 

Daddy ya faɗi ransa duk a zafafe, Abee ta kallo Hammad Shima ya kalleta kafin suka kai dubansu ga Mancy wacce ke famar gogewa Hajia kwallan dake tururuwar zubuwa a samar kuncinta. 

Story continues below


” Sai magana na gaba” Daddy ya daɗa katse tunaninsu, nan suka maida hankulansu a kansa. 

” Ina mai shaida muku kuma ina so ku zama shaidu, ni Abubakar Gidaddo na mallakawa Ƴata rabin dukiyata, sa’annan na mallakawa ƙannena da mijin ƴata sauran rabin dukiyar nawa su cigaba da juya komai, zan dawo gida in zauna in huta hakanan na damƙamuku amanar komai a hannunku” tsananin mamaki ne bayyane a fuskokin dukkanin jama’un dake cikin falon, Baffah Rufa’i da Baffah Yusuf da Abbi bakinsu ya kasa rufuwa tsabagen mamaki, Mancy kam tama kasa cewa komai.

Hajia Nenne kuwa ji tayi zazzabi na shirin rufeta, yau dai duk mayincinta na son mallake dukiyar Daddy ya tsaya cak, yau a gabanta Alhaji ya mallakawa ƴarsa da a da can ɗin ma don bata son ta mallaki dukiyar Alhajin iya ɗayane ya sanƴata aikata komai yau dai tana ji tana gani Daddyn ya mallaka mata. Oh duniya juyi juyi

” Sai kuma wata alfarma da nake so kamin Usman” da sauri Abbi ya kallo Daddyn, alfarma kuma shi ko mai yake da shi haka da Daddyn zai naimi alfarma a wajensa?. 

” Alhaji alfarma kuma? faɗi komainene matukar baifi ƙarfina ba ni mai yi maka ne” murmushi Daddy yayi kafin ya ce ” Alfarma ɗaya nake naima a wajenka, don Allah Ina so kabani auren ƴarka wa yarona Hammad!” 

Maganar ce ta riski kunnuwan kowa a cikin falon bambamrakwai, babu ma kamar Abee da Hammad zaro idanuwa sukayi duka a tare, kowa da abin da zuciyarsa ke kissa masa. Hammad kam baiyi tsammanin naiman auren Abee da yake shirin yi zai zo masa cikin sauƙi ba amma da Allah ya tashi sauƙaƙa masa komai sai ya kawo masa hanƴa mafi rinjaye gashi Daddy ya tambayar masa auren Abee ba tareda ya sanarwa kowa ƙudirinsaba, oh Allah ji yake tamkar an tsundumasa cikin aljanna. 

A gefen Abee kuwa, tarasa wani irin yanayi take a ciki farin ciki ko baƙin ciki? Ta sani sarai ta jima da lulawa duniyar ƙaunar Hammad da jimawa, kullum addu’an ta bai wuci Hammad ya sota ba takwankwacin yadda take ƙaunarsa, ta riga ta gama sadakarwa ita ɗin tana matukar son Hammad kuma bata tunanin zata iya rayuwa ba tareda shi ba, baƙin cikinta ɗaya a ce yau duk ita kaɗai ke kiɗinta da rawanta a ce Hammad Sam baya sonta son ƴan uwanta ka Kawai yake yi mata da babu wanda zai kaita baƙin ciki. 

Asma’u kuwa Hawaye ne kawai taji ya soma gangaro mata a  saman kuncinta, yau kam ta gama tabbatarwa Hammad ba mallakinta bane ita ke haukanta ita kaɗai. 

Hajia Nenne kam ba’a magana tama rasa tunanin da ya kamata tayi. 

” Daddy, ai ba sai ka naimi alfarman auren Abee a waje na ba yadda ka isa da Haleemat nima hakanan ka isa da ni, umarni kawai zaka bani ni kuma nabi, kana da ikon baiwa Abeedah aure ga kowa a sadda ka so, na yarda na amince na baiwa Hammad auren Abeedah!” 

Daɗi sosai da murna kowa ya shiga yi, nan Alhaji yayi wa Abbi godia Babu kuma ɓata lokaci a ka sanƴa auren Abee da Hammad sati biyu rak masu zuwa. 

******************^*******
A gurguje Please! 

” Amarya ba kya laifi ko kin kashe masu gida” dariya Abee ta fashe da shi kafin ta ce ” kinga Hayfa bana son iskanci, ban Kira na sanar miki ba don kimin shaqiyanci eheee” Hayfa ma dariyar tayi kafin ta ce 

” Wallahi Abee lamarin ya bani mamaki, amma Alhamdulillah ta dalilin zuwanki aiki kin gano asalinki wlh na yi matukar taya ki murna” 

Murmushi Abee tayi ta ce 
” Kibari kawai ƙawata, abun ba’a magana sai godiyan ubangiji, ina Suhailat wai?” Jim Hayfah tayi kafin ta ce ” hmm Suhailat tanan da tagwayen ƴaƴanta mata, jia ma ta zo mana yawon arba’in tana ta tambayarki nace nima bansan inda kike ba, amma baki san wani abuba Suhailat da Salman sun rabu sa’annan Salman Allah yayi masa rasuwa yau wata biyu kenan” jin kalmar mutuwa ba ƙaramin girgiza Abee yayi ba bakinta na karkarwa ta ce ” mutuwa kuma? Salman ya mutu? Bai da lafiya ne mai ya faru?” dogon lumfashi Hayfa ta shiga kafin ta shiga baiwa Abee labarin dukkanin abubuwan da suka faru daga farko har ƙarshe, sai a yau Abee tasan lalle itama tana da zuciyar tausayi sosai Suhailat ta bata tausayi kuma taji a ranta ta yafe mata dukkanin abin da ya shiga tsakanin su, sosai taji mutuwar Sir Salman kuma har cikin ranta taji ta yafe masa toh in bata yafe masa ba mai zata yi? Duniyar ma kwata kwata nawa take? 

Story continues below


” Allah sarki Hayfa, Wallahi naji mutuwar bawan Allan nan ubangiji ya jiƙansa ya haskaka kabarinsa, kice wa Suhailat ina gaisheta kuma na yafe mata dukkanin abin da ta aikata a gareni” sosai Hayfa taji dadin kalaman Abee don haka ta shiga yi mata godia, sai dai taki sanar mata Suhailat tayi mata takora a ganinta yafi da cewa taji a bakin Suhailat ɗin, sun ɗan taɓa hira kafin suka yi sallama suka rabu. 

” Ke wai Abee ba cewa nayi kizo Zaitun ta ƙarasa miki dilkan jikin bane?” Asma’u ta faɗa tana sakarwa Abeen hararan wasa, dariya Abee tayi don yanzun suna matuƙar ɗasawa da Asama’u duk ta dawo salaha abinta babu ruwanta da ƙananun maganganu yanzun sosai ta tuba kuma ta naimi yafiyar kowa, sa’annan ta soma cirewa kanta son Hammad Don tasan a yanzun kam yayi mata nisa. 

” Aa Anty Ma’uu, Hayfa ce tayo kirana ki bari nayi wanka sai nazo ta ƙarasa min” Abee ta faɗi fuskarta a sake. 

Tun ranar da a ka sanƴa auren su da Hammad Abee ke gudun haɗuwa da shi, duk inda tasan zasu haɗu kaucewa wurin take don kunyarsa take sosai, Hammad tun yana batsarwa har abin ya soma damunsa don Sai yake tunanin kodai Abeen bata son shi ne?. 

**+************** 

Yau ya ragi sati ɗaya cur auren Hammad da Abee, shiri sosai dangi da abokan arziqi ke yiwa bikin, gidan Alhaji ya cika dam da ƴan uwa da abokan arziki, Mancy har ƴan unguwansu na kano ta gayyata kuma suka zo yawancin su don ganin gulma kowa yayi mamakin sanin cewa wai Mancy da iyalanta na da asali. Auren ƴan gata Alhaji ke shiryawa jikarsa da ɗansa babu abin da bai sanƴawa Abee a kayan ɗaki ba gida sukutum ya danƙa musu a can Abuja don Hammad zai koma can da gudanar da kasuwancin Daddy, kayan lefe kam ba’a magana babu abin da ba’a sanƴa mata ba auren ƴan gata kam.

” Hajia kiyi ƙoƙari ki sha wannan maganin in sha Allah zazzabin zai ragu kinji ba?” Mancy dake shafa goshin Hajia Nenne a hankula ta faɗiwa Hajiar. Girgiza kai kurum Nenne tayi azaba na cin jikinta ita kaɗai tasan halinda take ciki, ita kaɗai da Allah suka san iriyar azabar datake fuskanta a yanzun kam har roƙawa kanta mutuwa take, so take kawai tabar duniyar ko zata huta da wannan azaban, don yanzun jikinta yayi mugun tsanani kowa gudunta yake inka cire Mancy da sam bata ƙyararta yaran Mancyn ma sosai sukan zo duba jikinta,  zuwa yanzun ta gama sakankancewa kanta bata wa kanta adalci ba yau wacce ta muzgunawan itace ke a kanta ita ce kawai ke kula da ita babu ƙyara babu tsangwama, bata tunanin zata iya yafewa kanta a kan hakan. 

” Kinji Hajia ki daure ki sha, kinga bayan bikinsu Abee nake son a fita dake zuwa ƙasar waje amiki aiki zaki samu sauki kinji” zuwa yanzun kam jikin Nenne ya gama saki, da kyar ta iya budan baki ta ce ” Haleemat, bani da bakin baki hakuri kuma banaso ki yafemin abin da na aikata miki na fison kibari Allah yayi min azaba kwatankwacin yadda nayi miki, karki wahalar da kanki a kaina Haleemat don ni ba tashi zanyi ba ki adana kudin kimin sadaka in na mutu!” Hajia ta faɗi a raunane, cike da tausayi Mancy ta ce ” Dan Allah ki daina kiran mutuwa, shifa cuta ba mutuwa bane Nenne am, zaki samu sauqi in sha Allah ki rayu sosai har ki goya ƴaƴan jikokinki (su Abeedah)” murmushi kawai Hajiar tayi bata sake cewa uffan ba. 

****************
A na saura kwana uku biki, Hayfah da Suhailat suka diro a garin Adamawa, sosai Abee tayi murnar ganinsu musamman ma Suhailat daka tsalle Abee tayi ta rungumeta tana mata barka da zuwa fuskanta fal farin ciki, sosai Suhailat tayi mamaki don batayi tunanin Abee zata amsheta haka ba. 

Koda suka je gaida Mancy Suhailat ji tayi kamar ta nutse ƙasa don kunƴa, amma ko a fuska Mancy bata nuna mata komi ba hasalima murna take sosai da zuwanta. Abee kam kane kane tayi da yaran Suhailat tanajin qaunarsu har cikin ranta.

Story continues below


” Ke Suhailat kiban kyautan su don Allah” dariya Hayfah da Suhailat suka yi kafin Suhailat ta ce ” toh na baki halak malak” 

” Shi ya saka nake ƙaunarki qawas, ya sunan su,?” Abee ta tambaya fuskanta sake tana wa yaran wasa. 

” Abeedah da Summayyah, takorarki da takorar Mommy suke”. Cak Abee ta dakata daga wasan da take yiwa yaran ta kallo Suhailat ta ce ” kina nufin kinmin takora Suhay?” Jinjina kai Suhailat tayi ta ce ” eh kin cancanci fin haka Abeedah, don Allah zaki iya yafe min abubuwan danayi miki!?” Hawayen farin ciki ne suka shiga ziryar a kuncin Abee, ji tayi qaunar Suhailat yana linkuwa a cikin zuciyarta, rungume Suhailat ɗin Abee tayi suna kula a tare, Hayfa tausayinsu duk ya rufeta. 

” Nagode Suhailat, Wallahi naji daɗi fiye da tunaninki. Na yafe miki dama can ban riƙeki a rai ba” 

*********** 

Sosai Suhailat da Hayfah suka shiga tsara yanda bikin zai kasance waleema kawai suka ce zasu yi, Hammad ya basu komai da komai duk da har yau Abee ta hanesa kallanta.

A ranar juma’a  talatin ga watan mayu shekara na dubu biyu da sha tara aka ɗaura auren  Muhammad Mahmud Gidaddo da Abeedah Usman Dambatta  a kan sadaki naira dubu ɗari, sosai taron bikinsu yayi jama’u daban daban manƴan mutane kama daga gwamnoni sarakuna duk sun sami damar halattar daurin auren. 

” Iyye ayiiiiriiiii, ta zama ta zama ɗauko hula, ta zama ta zama ɗauko wando” Suhailat da Hayfa suka shiga yi mata waqa, a hankali Abee ta waigo tana qarewa aminan ƙawayenta kallo. 

Ma sha Allah na furta a hankali. 

Sosai Abeedah tayi kyau cikin doguwar riga na wedding gown milk colour anyi mata ɗauri da golden head sosai kayan suka amshi jikinta,  fuskarta ƙunshe da make up wanda yayi azamar tona asirin kyawunta hannunta da ƙafanta sun sha zanen ɓakin fulawa da ja abinka da farar mace sai ya matukar yi mata kyau da haska fatarta, tsayawa misalta muku yadda tayi kyau ɓata lokaci ne sai mu kwana muna abu ɗaya. 

Rungume juna sukayi duka su ukun, kafin Farhana ta shigo itama cikin nata kwalliyan tayi kyau sosai sai zuba ƙamshi take. 

“Ango da abokansa sun ce a yo musu kiran Amarya!” Farhana ta Ida maganarta tana dariya, suma dariya sukayi kafin suka amsa mata da toh. 

Duk inda suka kutsa cikin gidan sai an sami ƴan uwa da zasu gaisar haka har suka isa harabar waje inda Hammad yake da abokansa, Abee kam ƙirjinta ne ya shiga dukan tara tara don rabonta da Hammad wlh har ta manta. 

Can na hango muku Hammad, yaci ado cikin babban riga gezna fari tas an masa aiki da brown zere, iya kyau Hammad yayi don har kyan nasa ma ba’a magana.
Tunda ya hangosu ya tsura mata ido, kallonta ya ke yi tamkar yau ya fara ganinta, tayi masa kyau iya kyau a cikin ransa ya riƙa godewa Allah da ya mallaka masa Abeedah Usman a matsayin matarsa ta sunna. 

Bai lura sam da isowarsu ba sai maganar suhailat ne ya dawor da shi duniyar da ya afka. 

” Lalala Ango ka sha qamshi” murmsushi yayi yana sake kai dubansa ga Abee wacce kanta ke a durƙushe tana kallon ƙasa, Abokan Hammad su uku suka shiga gaisawa da su. 

Hotuna sukayi kala kala, su Farhana da Harees da Mancy da sauran ƴan uwa duk suka firfito a ka sha hotuna kamar ba gobe. 

************ 

Story continues below


Misalin ƙarfe 4:30 a ka soma shirin kai amarya gidanta, sosai a ka mata nasiha Abee harda kukanta hakanan tanaji tana kallo a ka ɗauketa a ka sanƴata a mota don kaita nata gidan.

Straight airport suka nufa, Daddy ya bada private jet nasa don kai amarya, a cewarsa tafiyar mota duk sungulla ne. 

Basu wani jima ba suka iso garin Abuja, a gidanta dake can Asokoro a ka Kaita, gidane nagani na faɗa tsayawa misalta kyawun gidan ɓata lokaci ne, kayan alfarma na ƴan gayu babu wanda ba a jerewa Abee ba.

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Story continues below

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Asma’u ce ta dubi su Hayfah dake a zaune suna hira sama sama da Abee, ita kuwa Abee tana zaune gefen gadonta ta riƙe l2l Abee tanay mata wasa, L2l sumy kuma na bacci a gefe. 

” Ƙawayen Amarya yau zamu juya ko sai gobe?” Abee ce tayi saurin cewa ” Haba Anty Ma’u don Allah ku bari gobe yau ai yamma yayi” Suhailat ce tayi dariya kafin ta ce ” so kike wannan Angon naki ya zo ya kore mu ko?” Ta ida maganarta tana dariya, cuno baki Abee tayi kafin ta ce ” ina Farhana ne wai?” 

” Tana falo tana kallo, kin san halinta da rashin son shiga jama’a ai” Hayfah ta amsa mata. Dariya kawai Abee tayi don ta san za’a rina,Farhana sam bata da son magana da shiga mutane ita kuma haka Allah yayi ta. 

******************
Wa she gari. 

” Hajiya ya jikin naki? Bari na haɗa miki ko tea ne ki samu ki sha” Mancy ta ida maganarta lokaci ɗaya tana haɗa wa Hajia Nenne tea. 

Jin jikin Hajiar tayi zafi rau tamkar ana gasa biredi a jikin nata, uwa uba gawani ƙarni da jikinta ke fiddawa warin yawu da fitsari da kashin da take a gadon duk ya haɗu yayi wa jikinta zaman dirshen. Mancy kanta jurewa kawai take yi amma abin ya fi ƙarfinta, yanzu tunanin yadda zatayi a fidda Hajiar waje kawai take yi don samun lafiyarta.

” Haleemaat…..” Ta jiyo Hajiar na kiran sunanta a hankali, matsowa Mancy tayi kusa da Nenne ta na amsa wa da ” Na’am Hajia” magana Nenne keyi amma Mancy bata iya jiyo komai, don haka ne ta saita kunnenta ta matso da shi daidai bakin Hajiar don jin mai take faɗi: 

” Haleemat, ko bayan raina ban yarda ki yafe min ba Haleemat ban cancanci yafiyarki ba, kibari Allah ya hukunta ni zanfi jin dadi a kan ki yafemin, ki bari na ɗanɗani abin da na shuka da hannuna ki bari hakkinki ya kamani, don Allah ki roƙamin yafiyar Alhaji kice masa na tuba na koma ga Allah ya yafemin ko zan sami ragwanci wajen Ubangiji, don Allah Haleematu ki riƙe min ƙannena amana wallahi basu miki laifi ba duk nine na sanƴa musu karan tsanar ki, Haleemaat ki ya………..” Shaƙuwar da ya turnuƙeta lokaci guda shi yayi sanadiyar dakatar da zancen da take yiwa Mancy, sosai take shaƙuwa lokaci guda kuma tana tari tana fidda kumfa ta baki idanuwanta na faman kafewa zufa babu inda baya giftowa a sassan jikinta. Ruɗewa Mancy tayi sosai nan ta ɗau maganin Hajiar ta shiga bata abaki amma babu abin da ya iya ya shiga cikin bakinta komai zubowa kawai yake. Ganin halin ha’ula’in da Hajiar take ya sanƴa Mancy mikewa a sukwane don kiran taimako azo a kai Hajiar asibiti, mutanen biki nanan kowa na shirin ko mawa inda ya fito ganin Mncy a ruɗe ya sanƴa su miƙewa suka bi bayanta, amma kafin su zo Hajia Nenne Allah ya riga ya amshi abarsa. (Shike nan fa rayuwar kenan, in ka zo duniyar dole wataran kabarsa, shi ya sanƴa Annabi ya ce muyi aiki masu kyau da zasu iya bamu aljanna don more rayuwar ƙiyama Allah sa mudace ameen, kun ga dai yadda karshen Hajia Nenne ya ƙare yau duk wani ji da kanta duk wani tsafi da asirin da take yi yau dai ta koma inda ba’a dawowa). 

Story continues below


Mancy ji tayi duniyar tayi mata zafi mutuwar Nenne ya shiga ranta da ruhinta, a yau ta gasgata bawa ba komi bane wajen Ubangiji face ƙaramin ƙwaro a sakanni da basu wuci 1 ba Allah babu yadda ba zai iya yiwa bawansa ba.

**************
Ko da mutuwar Hajia ya riski su Abee sun tausaya mata sa’anan sun roƙa mata samun rahmar Ubangiji, Asma’u kam tayi kuka har ta gode Allah. Ko da suka iso Adamawa anriga ansallaci gawar Hajia Nenne an kuma kaita makwancinta, fafur Daddy yaqi a yi zaman makoki a gidansa hakanan kowa ya haƙura kowa kuma ya kama gabansa. 

Bayan kwana 3 da rasuwar Hajiar Mancy ta sanƴa a kayi sadakar uku, a ranar kuma Abee da Hammad suka koma Abuja, Suhailat da Hayfa ma suka koma Kano cike da kewan juna, sai dai Abee tayi musu alkawarin zuwa bikin Hayfah wanda za’ayi nan da wata  ɗaya mai zuwa.

********************************************* 

A gurguje 🥵

Five month later.

A cikin watannin da suka shuɗe abubuwa dayawa sun faru, wala na daɗi ko mara daɗi wala farin ciki ko baƙin ciki. A cikin watannin da suka shuɗen ne a kayi auren Hayfah da mijinta Hamis in da suke Lagos da zama, a cikin shuɗewar watannin ne kuma a kayi auren Suhailat da Hafeez Wanda a yanzun haka suna ƙasan England da zama, inda suke baja kolin soyayyarsu ita da mijinta Hafeez don tuni Suhailat ɗin ta koya wa kanta son Hafeez ɗin ta , ta yarda ta amince shi ɗin masoyinta ne mai ƙaunarta fisabilillah sosai Hafeez Ke nunawa Suhailat so da ƙauna ita da yaranta sam sam baya son abin da zai taɓasu.

Ƙawancen Abee da Suhailat da Hayfah kam sai dai muce Alhamdulillah don sosai suke daraja ƙawancen nasu, harta mazajensu sai da suka haɗasu abokanta ka duk da nisan da sukayi wa juna bai hanesu kasan cewa da juna kusan koda yaushe suna kan vd call ko conference call.

Soyayyar Abee da Hammad kam masu karatu ba’a iya cewa komai sai son barka don son juna suke tamkar zasu haɗiye juna tsabar so da kulawa, a ranar da Hammad ya furtawa Abee kalman so da yadda yake son ta har kuka sai da Abee tayi, itama a ranar ta sanar masa iriyar son da take masa, a ranar suka aminta da juna suka kasance cikin lema ɗaya a kuma ranar Hammad ya jiyarda Abee zumar So, a ranar kuma yaji soyayyar Abee ya linku a kan wanda yake yi mata don ita ɗin ta kasance cikin mata masu kare mutuncinsu, tabasa kyautar da kowani ɗa namiji ke burin matarsa ta sunna ta basa shi a daren farkonsu, ya shaida lalle Abee tana ɗaya daga cikin matayen da Allah yayi musu baiwa, ita ɗin daban ce a cikin jerin mata. Sosai suke mutuntawa junansu ɗaya baya son ganin ɗaya cikin damuwa sam Sam they are always there for each other.

********************* 

gudu gudu take yi shi kuma yana binta a baya suna zagayen falon, hannunta riƙe da remote da dukkanin alamu dai remote ɗin ya biyo ta zai amsa amma taƙi basa tana wana sa. Dariya sosai take yi duk da cikin dake jikinta bai hanata wannan gudun ba, don dai cikin nata ƙarami ne ba babba ba, duk da a yanzu cikin nata watansa 6 zaka ɗauka yana wata 4 ne don Abee sam bata da girman ciki. 

” Senorita Allah kibar gudun nan haka, karki jijjigami ni unborn” tsayawa Abee tayi cak tana dariya kafin tayiwa Hammad gwalo ta ce ” Hayattiey Allah bani baka wannan remote ɗin sai ka je ka siyamin fura da nono mai sanƴi” ta ida maganarta tana lumshe ido, ” toh kiban remote ɗin Senorita am yanzun za’a gama match in Sai naje Na siyo miki” make kafaɗa Abee tayi ta ce sam sai dai ya je ya siya mata fura. 

Ganin zai cafkota ya sanƴata rugawa a guje tayi cikin ɗaki tana dariya, mara mata baya yayi shima yana dariya yana mamakin yarintar Abee. 

Kan gado ya isketa don haka shima ya haye kan gadon amma mai? Yana hawa ta soma wurga masa pillow, nan da nan suka shiga jefewa juna pillow suna kyalƙetar dariya cike da so da ƙaunar junansu. Mirginota Hammad yayi ta faɗo kan ƙirjinsa ƙura Mata sexy eyes ɗinsa yayi dake tafiyar mata da imaninta, cuno baki tayi waje tana faɗin ” Hayattiey kallon fa?” Lumshe idanuwansa yayi a hankali ya haɗe bakinsu waje ɗaya, ya soma kai mata hot kisses sosai saƙonsa ke shigar Abee babu ɓata lokaci ta basa haɗin kai kan kace kobo, tuni salon nasu ya canza sosai Hammad ya shiga sarrafata cikin kwarewa itama ta basa haɗin kai kafin kace tak, tuni masoyan biyu suka luluƙa duniyar ma’aurata. 

Story continues below


(A daidai nan kuma na tattara inawa inawa na barmusu ɗakin sum sum 🏃‍♀️🏃‍♀️don fayyace ko ganin tarayyar ma’aurata babu kyau sam. Abee da Hammad a kashe juna da love lafiya 😍🤣🤣🙈)

*************** 

10yrs later

Rayuwa juyi juyi, rayuwa kuma mai tafiya da shuɗewa sosai. Yau da gobe sai Allah kuma komai ubangiji ya gama tsarawa bayinsa duk abin da zai faru da a rayuwar bawa har ya koma ga mahaliccinsa.

A cikin shekarun nan abubuwa dayawa sun faru, ciki harda auren Asma’u da a kayi da abokin kasuwancin Daddy don Daddy Shima yanzun ya yafe masu ya kuma jasu a jikinsa sosai, a haka abokinsa ya nuna yana son auren Asma’u babu bata lokaci akayi auren duk da mutumin zai kai kimanin shekaru 75 amma kuɗi da kwanciyar hankali sun mamaye shekarunsa, matan sa biyu da yara 4 ta farko tana da uku ta biyu tana da ɗaya sai Asma’u data shigo ana uku, can Germany suke zaune ita da mijinta inda yanzun yaranta biyu duk maza kuma tagwaye.

A cikin shekarun ne kuma Farhana tayi aure inda take auren yaron sarkin Gombe, yanzun haka ciki gareta suna can moroco ita da mijinta anan yake aiki. 

Mancy kuma da Abbi sun koma makka da zama kasantuwar kasuwancin Abbi da ya riƙesa a can, sukan dawo Nigeria duk ƙarshen shekara.

Daddy ma yayi aure da matarsa mai kirki Hajja Nafee wacce keda kimanin shemaru 55 a duniya, mijinta ya rasu ya da jimawa inda ya barta da yara uku marayu, a makka suka haɗu da Mancy suka saba sosai don ita Hajja Nafee aikatau tazo yi anan makkan, sosai Mancy ke mutunta matar tanay mata kallo tamkar mahaifiyarta, zuwan Daddy makka yazo wa Mancy ziyara ta kwaɗai ta masa auren Hajja Nafee, ta nuna masa sam zaman sa a haka bazai yu ba. Don samarwa da ƴarsa farin ciki ya sanƴasa amincewa babu ɓata lokaci aka daura auren Daddy da Hajja Nafee suka dawo Nigeria. Sosai Abee sukay murna da auren Daddy Suma a kai a kai sukan ziyarci adamawa.

Ƴar Abee ɗaya har yanzu kuma bata sake haihuwa ba, ƴarta kekkyawa mai kama da mahaifinta sak. sunanta Haleematu sadia takorar Mancy amma suna kiranta da Shuraiha, yarinƴa mai farin jini ƴar kubul kuɓul da ita ga wayon tsiya. 

Farin ciki kam ya samu sosai a cikin zuri’ar su Abee, mijinta na qaunarta har bata iyama fasalta iriyar son da yake mata, ga jin daɗi dake ratsata ta ko’ina bata da damuwar komai a ranta, sosai mijinta ke bata gudun mawa don a kalla yanzun Abee tana da gidajen mai guda biyu tana da gidajen gona, school na koyar da ɗinki da saqa da su humra, sabulun gyaran jiki etc Hammad ya buɗe mata anan garin Abuja take ɗaukan mata dayawa tana koya masu.

Mancy ma ba a barta a baya ba don harta ƴan unguwannin su da suka zauna dasu a Kano sai da Mancy taje tayi musu alkairi, sosai tabaiwa ko wacce mace jari ta gina islamiya da masallaci duk a cikin unguwar, sukam sam basu da bakin godewa wannan baiwar Allah face Allah ya saka mata da aljanna ya biya mata buƙatunta, sam da ana samun mutane masu hali irin na Mancy da munsamu cigaba sosai cikin al’umma. Ita ɗin macece mara riƙo sam sam gata da tausayi da zuciyar taimako. ( Allah qara miki lafiya da tsawon kwana Mancy)

Alhaji Faruk ma yayi aure inda yake zaune da matarsa Aliya anan gidan Daddy an ware masu part na musamman shi da matarsa. 

Abbi ma ya naimo ƴan uwansa yana musu alkaire kaala kala fatan sa dai Allah ya cigaba da haɗa kan zuri’ar sa gaba ɗaya ameen
************************* 

” Mancyn yara ke ɗin nan ƴar aljanna ce” murmushi Mancy tayi kana ta miƙawa Abbi tuffa (Apple) data gama gyara masa, fuskarta ɗauke da murmushi ta ce ” Allah ya amsa bakinka Abbin yara” murmushi Abbi yayi yana jin son matarsa har cikin ransa, shi kam yayi sa’ar mata duniya da lahira. 

” In sha Allah Mancyn Yara, Aljannar ki a ƙarƙashin ƙafana yake nikam Babu abin da zai sanƴani ƙin miƘar miki ki shige aljannah” dariya sosai Mancy tayi ta ce ” Ameen Abbi, ɗazun Harees ke cemin zasu samu hutun shekara ya ce min zai tafi Nigeria yayi wata biyu kafin ya zo Makka” gyaɗa kai Abbi yayi kafin ya ce ” Allah ya nuna mana Ameen” 

Story continues below


Mancy kam yanzun bata da sauran damuwa a tattare da rayuwarta sosai ta samu farin ciki yanzun kam kullum tana maƙale da ƴan uwanta, yaran Baffaninta ba’a share shekara suke zuwa su ziyarce ta, ƴaƴanta duka ta aurar suma kusan koda yaushe suna sunturin zuwa ganinta, ita kam yanzun mai ya rage mata a duniya? Babu sam yanzun ya rageta naiman lahiranta Kawai.

************** 

” Mommy da gaske su Abee da summy da Najma (ƴar hayfah) wai zasu zo Abuja next week? Yeeee daɗi my friends are coming” dariya Abee tayi tana kallon ƴarta kafin ta ce ” sure baby am, duk suna tafe next week we gonna have fun!” Abee ta faɗi da fara’arta, nan da nan Shuraiha ta miƙe tana tsallen murna, Abee kuwa tsareta da idanuwa kawai tayi tana al’ajabin wai yau ita ɗin ma uwa ce? Yau ita ma da nata gudan jinin a duniya oh Allah. ” Allah yayi wa rayuwarki albarka Shuraiha” 

” Ameen ya Allah, Matata” ta tsinkayo Muryar Hammad Na amsa addu’ar da tayiwa ƴarta. 

Da sauri ta miƙe taje ta rungumi mijinta da dawowarsa kenan daga aiki. ” Hayytiee welcome back” murmushi yayi kafin ya sunbaci bakinta ya ce ” thank u Maman babyna” Shuraiha ce ta zo da gudu ta rungumi Daddyn ta tanay masa Barka da dawowa, da kyar Abee ta samu Shuraiha ta bar Hammad yaje ya kimtsa. 

*****************
12:30am 

Coffee ta gama haɗawa Hammad bayan ta kwantar da Shuraiha a ɗakinta, kitchen ta koma ta haɗawa mijinta Coffe kafin ta shigo ta iskesa yana faman danne danne a system. 

” Hayattiee your coffee is ready” Abee ta faɗi masa, ƙamshin turarenta duk yabi ya turnuƙe ƙofofin hancinsa da sauri yaɗago yana kai dubansa gareta, sanƴe take cikin wani haɗaɗɗiyar night gown kayan yayi matuƙar fidda surar jikinta, sosai tayi masa kyau hakan ya sanƴasa a jiye system ɗinsa a gefe ya buɗe mata hannayensa alamar ta taho garesa, babu musu Abee ta je ta shige jikin mijinta tana sakin lumfashi, sumbatar goshinta yayi kafin ya raɗa mata a kunne ” i love u very very much oum Shuraiha,” ƙara narkewa tayi a jikinsa tana mai faɗi masa ” i love u to Abu Shuraiha, I deeply love u Baffa’am!” 
daga nan Hammad yayi saurin haɗe bakinsu guri guda ya shiga sarrafasu cike da kwarewa, kafin ƙiftawar ido salon na su ya soma canzawa nan Hammad ya mirgino dasu tsakiyan gado a hankali kuma ya kashe bed side Lamb duhu ya mamaye ɗakin, dukkaninsu sun yi loosing control burin kowa bai wuci su lula duniyar ma’aurata ba, a hankali Hammad ya ce cikin muryarsa dake nuni da tsananin sha’awa ” yau zamu samarwa Shuraiha l2l broda in sha Allah, Senorita kinji?” Cikin ƙosawa Abee ta gyaɗa masa kai, lokaci guda kuma tana manne jikinta cikin nasa, daganan salon ya canza suka tafi duniyar da ma’aurata kawai ka iya zuwa susha daɗi da lada. 

(A hankali kuma na kwashi ƙafafuwana  da birona na fito a cikin ɗakin nasu na kulle a hankali don barin ma’auratan su kashe juna da love😂) 

Alhamdulilah, anan kuma na kawo qarshen wannan littafin nawa 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *