KE NAKESO CHAPTER 5

KE NAKESO





CHAPTER 5






Bayan sun kammala karyawa ne. Abdul-Aali ya-cewa Mai-jidda. “Anjima zan kai Hamamatu gidan Sister dinta da ta haihu, zan ajiye su Ramla gidan Abba, za ki je ne, ko ki na gida?” +

Ta yi shiru tana tunanin, idan suka watse, gidan zai mata shiru, don haka ta-ce. “Ba damuwa zan shirya, sai ka bar mu gidan Abban”.

Suna fita gidan yar Hamamatu, suka fara zuwa ma mai haihuwa, dukan su suka shiga har da Abdul-Aali yayi mata gaisuwa. Zulfa’a tana da fara’a, kasancewar ta kan hadu da Mai-jidda a sunan yaran kanwarta, ko wata hidima, ba ta gwada mata wani canji ba.

Suka gaisa kamar koyaushe, yayin da Hamamatu take ta jin haushin yarta, wai yaya za ta washe baki, ta yi ta yiwa kishiyarta dariya.

Da suka zo tafiya ne. Mai-jidda ta bude jakarta ta fito da ledan zani, ta ba ta. “Ga wannan ba yawa ayi goyo. Allah kuma ya raya cikin addinin musulunci.”

“A’a haba Anty Hauwa, kuma sai ki shiga dawainiya haka? Ki bar shi kawai, don Allah.”

“A’a kar mu yi haka don Allah, ki karba, ai na riga na yi niyya.”

“To shi kenan. Allah ya amfana. Allah ya bar zumunci.”

“Ameen-Ameen. Mu za mu wuce kar Dadin su Mimie ya yi ta jiran mu.”

Nan ta rike hannun Mimie ta daga Ramla a hannu. Hamamatu ta bi-ta da kallo. Suna fita, ta hau yiwa Zulfa’a bala’i.

“Haba ke kin faye daukar abu da zafi, tana da kirki sosai, ki ga yadda take da yaranki fa.”

“Duk kinibibi ne, bari na fada miki, ke kuma dole ki fadi haka, tunda har zani aka kawo miki.”

“Akan ba ni da su ko meye? Ke dadina dake rashin son gaskiya.”

Ba abinda yake damun Hamamatu, illa yanzu haka Mai-jidda za ta je ta kame a gaban motar Abdul-Aali suna tafiya, suna hirar soyayya. Tamkar ta cewa Zulfa’a ta fasa wunin, don gaba daya ta kasa daina tunanin Abdul-Aali da Mai-jidda. 2

Sai da yamma ya dauko Hamama, suka taho gidan Abba, nan suka samu su Ramla sun sha kyau, saboda Mai-jidda zama ta yi ta rangada masu kitso, ta aika aka sayo mata Ribbons ta jera masu a kai.

“Mami kin ga kitson mu. Anty Hauwa tayi mana, kuma ba zafi”.

Ganin Abdul-Aali a wurin, ba ta son ta nuna haushinta ta-ce. “Lallai kun ji dadinku, sannu Anty Hauwa, kun ce mata thank you?”

STORY CONTINUES BELOW


Nan Mimie ta kama baki, cikin alamar tuna abu. “La na manta, thank you Anty Hauwa.”

Abdul-Aali ko dadi ne fal! A ransa ganin an samu canji tsakanin jiya da yau.

Mama ma farin-ciki ne ya cika zuciyarta, saboda ganin komai ya daidaita, sannan Danta yana cikin farin ciki. Daga gani dai, hala Hauwa ta sassauto ne. 8

*******

Tana zaune a falonta da dare ne, ta ga wayar Abdul-Aali, don haka ta daga. “Ki sameni a falo.” Ya fada a takaice. Mayafi ta daura kan kayan barcinta, sannan ta shiga falon nasa, ta samu yana kallon labaru, don haka a kasa ta zauna nesa kadan da kafafun sa.

“Gani”.

Mika mata wani kit ya yi da jarida, ta duba ta ga kayan yankan farce ne, da gyara kafa.

Ta dube shi, don neman karin bayani. “Bude mana, ko sai na gwada miki? Farce na sun fito, so na ke yi ki dan gyara min.” 16

Wani kallo tayi masa, wanda ita kanta ba ta san iya ma’anar sa ba. “Ni zan yanke maka farce? Na fada maka fa, kar ka yi tunanin ko zan zama wata (Ideal wife) gareka, ka jira wacce ta saba maka, ta yanke maka.” 5

“Ke nace ki yanke, ko kina da matsala?”

Cikin sanyin jiki ta matsa kusa da jakar, ta shimfida jaridar, sannan ta mika masa hannu alamar ya ba ta hannunsa. Fuskarta a murtuke ta fara masa gyaran farcen yana kallonta yana murmushi, ga hannayenta da suka faye laushi, tamkar ba ta aikin komai. Yana kallo har ta gama yanke na hannu cikin natsuwa da kula take aikin. 2

Bai ankara ba, yana cikin kallonta ne ya ji zafi har cikin kwakwalwarsa, saboda yanke matsa babban yatsar kafa da ta yi cikin kuskure, nan da nan kuwa jini ya hau bulbula, da sauri ta mike ta dauko Tissue ta danne wurin, tana fadin “Wai, sorry don Allah ka yi hakuri.”

“Ba wanin nan, dama ba ki so yankan ba, da gangan ki ka yi ko?”

Ta tsume nan da nan, ta bar bare-baren da take yi na ganin jini a kafarsa. “Da da gangan ne, ai da guntule yatsar ma zan yi, ai dama na ce maka ban iya ba.”

“Yatsata za ki guntule?”

“Eh”.

“Bismillah.” Ya fada hade da mika mata dayan ma. “Bayan yanka kadan ma kin fi-ni rudewa da ganin jinin, shegen tsoron tsiya, a hakan ne za ki guntule yatsa?”

“Ka kawo mana ka gani, kuma na gama kenan, daga yau ka rinka yankan farcenka da kanka”.

“Ai aiki ya sameki, don kuwa ni ba abinda na ke yi, hatta wanka yi min ake yi, idan za ki koya to”. 2

“Sai ka ce wani yaro karami, sai na tsaya yi maka komai? Lallai ma ka na da aiki ja gabanka”.

“Shi kenan, ashe za a bar ki a baya kuwa. Don kin ganni. Ni Dan gata ne, sai abin da na ke so, za ayi min, idan kuwa ba kya min, to ni ma za ki sha mamaki.”

“Kamar na damu.” Ta fada hade da juya idanu.

Ta mike za ta tafi ya-ce. “Yau a dakina za mu kwana.”

Ji ta yi kamar ta karbi rezar ta gutsure yatsar da gaske, don ya soma ba ta haushi. “Abdul-Aali sai da safe.”

Bakin gyalenta ya rike ya-ce. “Ke haka ki ke son mu rabu, gobe kuma Hamama ce a nan. Kin san jibi fa za mu koma, ko kin fi son na yi ta tunaninki, na kasa aiki?”

“Allah ya bada sa’a. Na fada maka jiya ma kuskure ne, kuma ya daina faruwa, sannan ai ba mu zauna mun yi magana da Mamin Mimie akan yawan kwanaki ba”.

“Ke kuma haka kawai ki ke neman fushin Allah a kanki ko?”

Jin maganarsa, sai ta koma gefensa ta zauna. “To, ka yi hakuri, ba haka bane nufi na.”

“To meye ne nufinki?”

STORY CONTINUES BELOW


“Kawai dai, kayi min bazata ne, shi ya sa. Amma ni ban ce maka dama ina so ba”.

“Oh, sai kin so ne, za ki farantawa mijinki rai? Shi kenan tashi ki tafi.”

Jikinta ya yi sanyi kuma bayan ya fadi haka, ya saki gyalenta cikin jin haushi. Ta bar falon ba tare da ta sake kallon inda yake ba.

Ya rasa me ya sa Jidda take masa wasa da hankali, jiya sai ya rantse ba ta da wanda take so irin sa, ganin yadda ta saki jikinta da shi, amma yau tun da safe ta wani canza, sai ka ce Hawainiya sarkin canjin launi.

Ya san duk kora kunya take yi, amma kuma hakan ba karamin bata masa rai ya yi ba, su yara kanana ne da za ta tsaya tana masa wasa? Ya so ya bi bayanta. Amma bacin rai, ya hana shi, sai dai ya mutu akan ya je, dole ta gane kuskurenta. 1

Ko da ta koma daki, banda juyi, ba abin da take yi ta kasa barci, haka nan ta ji rashin dadin abin da ta yiwa Abdul-Aali, ta san lallaba ta yake yi, amma kuma ita ba za ta iya ba. Sai dai ba abinda take ji a kunnenta, irin tambayar da yayi mata ko ta fi son fushin Allah a kanta?

Don haka ta mike ta kashe wutan dakinta, ta koma sashinsa, ta samu ya kashe wutan falon, don haka ta san yana cikin daki.

A hankali ta kwankwasa kofar dakin, ya taso yana tunanin ko waye? Bude kofarsa, sai ya ganta a tsaye kanta ba Dan-kwali, ta sako gashin ta, ta gefen wuyanta.

Sannan gyalen dazu yana yafe iya kafadunta, sabanin dazu da ta rufe kanta da shi, sai wani sansanyar kamshi da take yi. Amma ya daure ya maida kofar zai rufe. 1

Da sauri ta sa hannu ta tare, idanunta sun yi narai-narai! Ta-ce. “Ka yi hakuri, Abdul-Aali.” A hankali ta sa hannu ta rike hannun sa. Ajiyar zuciya yayi, ya ja ta jikinsa ya turo kofar. 2

**********

Tana goge-gogen Side dinta ne. Hamamatu ta shigo, hakan ya sa ta mamaki, saboda tun zuwansu ba ta shigo Side din nata ba, sai yanzu. “Mamin Mimie? Ina kwana?”

“Lafiya kalau.”

“Bismillah! Ki zauna mana”.

A bakin hannun kujera ta zauna, tana karewa falon kallo kafin ta-ce. “Na ga har kin yanke iya kwanakin da ki ke so mu diba, ko tukuna ba ki gama diba ba?”

Kan Mai-jidda ya kulle, amma ta yi murmushi ta-ce “Kwanaki?”

“Eh mana, ko jiya ba ke ki ka yankewa sweety farce ba? Na ga dai cewa ya yi mu yi shawara akan kwanakin da ya dace mu yi.”

“Gani na yi ya kirani, shi ya sa na je, saboda dacewar hakan, a zatona ke ki ka fada masa hakan yayi miki”.

Hamama ta hadiye wani abu, wato namiji ma sai a bar shi, bayan ya-ce su yi shawara. Shi ne har da kiran Hauwa. Daman ya san meye a ransa kenan. “Da shi muka yi za mu yi shawara ko da ke?”

“Yanzu dai magana ta kare, ki yi hakuri, ke me ki ke ganin ya fi? Kwanaki nawa suka yi miki?”

“Tunda kin yi kwana biyu, shi kenan, da yamma sai na karba, kwana bibbiyu kenan.”

“To shi kenan, hakan ya yi.” Mai-jidda ta fada. Hamama na fita, ta bi-ta da kallo, tana murmushi. Abdul-Aali kenan. Sarkin hada wuri.

Ranar ita kadai ta wuni a gidan kasancewar Hamama ta kwashi yaran sun tafi gidansu. Hakan ya sa bayan ta gama abinci, ta shiga daki don rama barci.

Ranar da za su tafi ne. Ta ji wani iri, don da safe ya shigo ya sameta. “Jidda, ni ban ga amfanin zamanki ke kadai ba anan, ki shirya mu tafi kawai.”

Tayi shiru kafin ta-ce. “Kai ba ka san ance wai gida biyu , maganin gobara ba? Ni na fi son zama nan kusa da Mama da su Umma, ka ga idan an kwana biyu, zan dubo Muhammad, amma idan na yi nisa fa?”

STORY CONTINUES BELOW


Kallonta yakeyi kaman yayi yaya da rashinta da zai yi a ganganshi “Muhammad ne dai damuwar ko? Ina ce sun kusa yin hutu?”

“Eh sun kusa.”

“To shi kenan. Ki zauna cikin shirinki, yana hutu duka za mu koma can.”

Za ta yi magana ya-ce. “Kar ki fara.” Riketa ya yi a jikinsa, sannan ya-ce. “Ba na son gardama.”

“Allah ya kai mu lafiya, shi kenan?”

“Yauwa, ko ke fa? Ameen. Jiya na je wurin su Umma, suna gaisheki”.

Ta daga idanu ta dube shi cikin tuhuma, har yanzu bai sake rikon da yayi mata ba. “Shi ne ba ka fada min za ka je ba, mu tafi tare, na zauna gidan nan ni kadai, ba abin da na ke yi.”

“Idan nace ki min rakiya, ki na yi ne? uhmm?”

“Kai ma ka san da zan je, ka fadi wurin zuwan mana ka gani.”

Dariya yayi, ya sumbaci saman goshinta sannan ya-ce. “Zo mu tafi Breakfast. Hamama na jiran mu.” Lokacin ne ya saketa daga jikinsa.

Mayafinta ta dauka, sannan ta bi bayansa zuwa bangaren sa. Anan suka sameta ta gama cika, saboda ta kusa minti ashirin tana jiran fitowarsu, daga bari ya yi mata magana su ci abinci, shi kenan.

Haka suka gama cin abincin, ba wata kwakkwarar hira. Sai yara ke ta shirmen su. Lokaci-lokaci Mai-jidda na hada ido da Abdul-Aali, amma sai ta kawar da kai. A karo na uku ne ya sakar mata da murmushi.



Daidai kuwa a kan idanun Hamama, ranta ya baci. Haka ta hakura da abincin da ta bata lokaci tana hadawa. Mai-jidda dai ta ji wani iri, da yaran suka tafi. Sai gidan yayi mata shiru sosai. 2

*************

Ranar Asabar kawai, sai ga Walida da mijinta sun zo Kano, suna shigowa ta kira Mai-jidda a waya. “Haba don Allah?”

“Kawai abin da za ayi, ku je gidan Abba zan yi waya. Kasim kanin Abdul-Aali sai ya kawo ku.”

“To shi kenan.”

Tana ajiye waya. Kasim ta nema ta fada masa, saboda Sulaiman ya tafi Kaduna. Nan ta hau shirya kayan tarbarsu, masu saukin yi, kamar su zobo mai dadi irin wanda take hadawa a Dutse, don ta san Walida da son zobonta, musamman take sawa ta tafi masu da shi wurin aiki.

Ta fito da sauran samosan da ta saya, ta soya masu, sannan ta dan kara da wani abin da ba a rasa ba, ta kammala komai. Dai ga su Walida, sai da ta sa mayafinta ta bude masu falon Abdul-Aali. Can ta yi masu masauki.

“Kai Uncle ka kyauta min yau din nan raina fari kal!”

“Ko? To lallai ya yi kyau, tun ba yau ba ta matsa min, ita dai tun tafiyarki ba ki je ba, tana son ganin ki”.

“To mun gode kwarai. Yaya mutanen gidan, duk suna lafiya ko?”

“Lafiya kalau. Alhamdulillahi.”

Nan ya tafi ya bar Walida, bayan sun ci abubuwan da Mai-jidda ta tanadar masu. Mai-jidda ta-ce. “Ba ki san yadda ki ka taimaken ba yau, da ki ka zo, gidan nan shiru ba kowa”.

“Haba ni nace ko saboda hutu ma hala na samu Injiniya?”.

“Ran Talata suka koma, kin san yanayin aikin nasu da matsi.”

“Ayya! Lallai ke kadai a cikin gidan nan? To wai me ya sa ba ki tafi ba ke?”

Mai-jidda ta yatsina fuska. “Ban gane ba, ki na bata fuska, kar ki ce min har yanzu ki na wahalar da Abdul-Aali bawan Allah?”

“Kin daina tayani tsanarsa ma kenan?” 3

“A yanzu kam kuma ai za mu wuce gona da iri, idan mun tsani Mai-gida guda, maganar gaskiya dai Mai-jidda.”

STORY CONTINUES BELOW


“Don Allah ki bar maganar Abdul-Aali, damuwarsa sai shi, nan wai so yake yi idan na dauko Muhammad mu koma Portharcourt, ni da zai bar mu, mu yi zaman mu anan, ba komai na ke yi ba.

Zan rinka kai shi makaranta da kaina, na dauko shi, tunda anan yake barin motarsa. Can yana amfani da ta Mamin Mimie ne.”

Walida ta zare idanu ta-ce. “Shi kuma mijin sai ki yi yaya da shi. Ko ba shi a lissafinki ma kwata-kwata?”

“Ke wa yake ta shi, ki na ga zuwan shin nan ma, ya takura min ga matarsa da har yanzu take daukar abubuwa da zafi, don ma an dan samu sauki kadan. 2

Dan yayi mana nasiha zuwan su. Gaba daya na fi son na yi zamana anan hankali na a kwance, wai tsumma a randa. Ya fiye min.”

“Oh daman ya auro ki, don ya sa miki idanu ne?”

“Ni na rasa ma me ya sa mutane suke wani zafafa wannan abin, aure dai na yi shi, ba shi kenan ba”.

“Ai ba daga auren bane sauke hakkin auren fa? Bare ke da ki ke da abokiyar zama, dole sai kin dage kan ki dasa wuri a zuciyar mijinki, domin kuwa kin riga kin samu suna rayuwarsu.

Zai yi wuya kan ki saba da yadda ake masa, ki bar ganin wai don yana sonki. Wallahi a ja ajin a hankali, kada ga-rin neman kiba, a samo rama “.

Jidda murmushi tayi. “Ni na fada masa, kar ma ya tsammanci komai daga gareni, har ya fara cewa shi ba haka matarsa take masa ba”.

“You see! Which means Yana so ki gyara, kuma idan ki ka bari ku ka yi nisa a haka, ba ki dau gyara ba, to Wallahi kan ki gyarota, sai kin yi da gaske.”

Mai-jidda ta jinjina kai, yanzu kam yaya ta iya ta riga ta aure shi. “Haka ne kam.”

“Yaya su Yaya Maryam?”

“Suna nan lafiya, jiya aka kawo min A’isha da Nabil ma wuni”. Nan suka sha hirar su, sai da dare Mai-gidanta ya zo daukarta, za su wuce gidan yarsa.

********

Tana zaune kamar kullum. Yau ma ya kirata a waya, ta daga, gaba daya sai ta ji ta tsargu, musamman yadda suka tattauna da Walida, ta ba ta shawarwari, daga yanayin amsar wayar tata yau. Abdul-Aali ya ji bambanci, don da tamkar wuta haka take Allah-Allah take ya gama magana, ta ajiye. Amma yau cikin kwanciyar hankali take masa magana.

“Jidda, yau na ji wani nishadi ki ke ciki me ya faru?”

“Wa, ni din ce?”

“Eh mana, tunda muka fara magana, ba ki nemi fada ba, dole da wani abin.”

“Don ni ce Sarkin masifa, sai na yi ta fada koyaushe, abin naka ma na ga har da sharri ciki”.

Dariya ya yi sannan ya-ce. “Mai hali dai, baya barin halinsa”.

“Hmm! Kai dai ka fada kai tsaye, ka na tunzurani, sai kuma ka ce ni ce marar hakurin”.

“To na ji ki yi hakuri, ban labarin me ya sa ki farin-ciki yau?”

“Walida ta zo min, muka wuni, sai dazu suka tafi ita da Mai-gidanta”.

“Allah Sarki. Yaya take? Wai na ji dadin zuwan tan nan, ko ba komai na san ita ‘yar gari ce, tunda ta fara sa matata yi min fara’a.”

“Da ba ka ganin fara’ata ne?”

“Wai wani kallon idan an yi min. Tamkar zai kifar da Kano gaba daya, ke dai ba a cewa komai. An cuci na dawa”. 4

Dariya ta yi a karo kadan da za ta iya tunawa, tun fara nemanta da Abdul-Aali ta-ce. “Dadin Mimie kenan, na ji tunda haka ka daukeni. Daman ina son na ma maganar zuwa na Dutse Next week.

Idan na je, sai na jira hutun Muhammad, tunda nan zaman haka ya min shiru da yawa.”

“To ba komai, zan yi Making arrangements Insha-Allah. Kin ga amfanin tahowarki ko? Da yanzu ki na da abokin hira.”

Murmushi ta yi sannan ta-ce. “Bayan zan je na ga Ummata, ina ruwana da kai.”

“Haka ki ka ce ko? Ba zan ce miki komai ba.”

“Ka gayar min da Mimie da Ramla”.

“Banda Mamin su?”

“Ka iya hada fada, ba ka jira na karasa ba, za kayi min fassara, ka gaisheta ita ma. Dan hadin rigima”.

Yana dariya. “Ga ta nan ma, ko za ku gaisa?”

Gaban Mai-jidda ya fadi, daman Hamama tana wurin yake waya da ita? “Abdul-Aali dama tana wurin ka ke magana?”

“A’a yanzu ta shigo.”

“Sai da safe to.”

“Tsaya. Jidda kar ki kashe wayar. Yaya muna hira za ki kashe min waya?”

“Yaya zan yi magana da kai, bayan tana nan?” Ta fada hade da rage murya, tamkar tana wurin ita ma.

“Zolayarki na ke yi, kin faye kishi. Menene, don ta ji hirar mu?”

“Wannan sirrin mu ne, akan me ya sa za ta ji, ni na ji nata ne? Sannan ni ba na kishin ka. Maganar abin da ya dace ne da wanda bai dace ba”.

“Jidda Sarkin fada, to Allah ya ba mu alkhairi, bari na shiga, kafin na yi wani laifin.”

Mai-jidda ta kashe wayar cikin jin haushi, har ma Allah-Allah wato yake yi ya gama waya da ita, ai daman ba ta iya magana ba, matarsa ta fita iya komai. 21

****
Tafiyarta Dutse, ya sa ta ji dadi kwarai, ta ji dadin ganin Ummanta, wanda ta yi kewa sosai, haka Muhammad tun isarta ya makale mata. +

Duk inda za ta yana biye yana ba ta labari kala-kala. Ta samu fushin Baba ya ragu. Amma sai da yayi mata fadan abin da ta yi, na tahowa yin aiki ba tare da izinin mijinta ba.

“Umma ki na ji Baba, har yau fadan bai kare ba.”

“Ai dai gwamma yayi miki, da hankalinki ace kin yi haka, me za ki fadawa su A’isha da suke tasowa. Ya min daidai ai, da ya dauke ki ba sallama. Gobe kya kara tsallake umarninsa.”

“Yanzu dai Umma ya wuce, ku yi hakuri.”

“A haukan naki ne za mu kau da kai mu yi hakuri, yanzun me ya hana ki tafiya? Wancan karon kin ce aiki, to yanzu kuma ban ga zaman me ki ke yi ba.”

“Umma fa daman, idan Muhammad ya yi hutu, zai zo ya dauke mu mu tafi can”.

“To, na sanki ne ai sarai, sai ki bijiro da wani abu daban.”

Mai-jidda ta san idan Umma ta fara, ba tsayawa don haka ta-ce. “Yaya labarin auren Yaya Abbakar ne?”

“Au bai gaya miki bane a waya? Ai an riga an kai goro kam, yanzu zancen lefe yaketa fama, ya kaiwa Maryamu wasu kudade ma, don ta shiga masa kasuwa.”

“Lallai ma Yaya Abbakar shi ne ya yi shiru, ko labari babu, ko ba komai ni ma ai sai na bada tawa gudumawar.

Umma ba ga irinta ba. Kano kawai na tafi, amma abubuwa na faruwa, ba kwa fada min, idan na tafi wata uwa duniya kuma, sai ta Allah kenan.” 1

Umma ba ta ba ta amsa ba, don tana ganin bata lokaci ne.

Sai da ta huta son ranta, sannan ta shirya ta tafi gidan Yaya Hamza, tana ta murnar haduwa da Anty Fauziyya, sai dai tana shiga gidan.

Jikinta ya mutu, don ganin halin da Anty Fauziyya ta ke ciki. Fuskarta a kumbure, alamun ta sha kuka. Mai-jidda ta-ce, Wai, Yayanta ya kwafsa kenan.

“Anty Fauziyya, lafiya na gan ki haka?”

Kuka ta kara fashewa da shi, don daman ranta ya gama kufula, saboda rashin sanin wanda za ta fadawa kukanta, to amma Mai-jidda kusan abokiyar shawararta ce, don kullum idan dayansu na da matsala, to dayan yake samu.

“Banda Hamza ne…”

“Me ya faru kuma, har yanzu maganar ce?”

“Ai ke kam, yanzu ma komai ya lalace, yau baram-baram muka yi kan ya fita. Kamar ni wannan abin baya damuna, ke kanki kin san irin damuwar da na ke ciki game da rashin haihuwar nan, amma idan ya tashi tamkar ni ba na son na haihu, haka yake min.”

STORY CONTINUES BELOW


“To, amma kuma da abin nan fa bai dame shi ba, na rasa me ya sa yanzu zai daga hankalin sa? Sannan komai fa yin Allah ne, abinda ki na samun cikin. Miscarriage ne matsalarki, kuma da za ki kula da shan magunguna, komai zai daidaita Insha-Allahu.”

“Ai yanzu ba kan wannan bane, last month mun je asibiti, a kai min gwaje-gwaje. To shi kenan sai Likita ya-ce wai (Infection) ke jawo min bari. (Miscarriage) dina.

Dole na kiyaye abubuwan da suke kawo kamuwa da cutar (Infection), na yi maganinsa, sannan mu ci gaba da gwadawa har Allah ya sa mu dace”. 1

Mai-jidda ta dubi Anty Fauziyya cike da tausayi. “To ba ga shi an samu abin da yake jawowa ba. Ai Alhamulillah! Daman farkon samun sauki, to gano cuta ne. To meye matsalar anan?”

Anty Fauziyya ta goge hawayen fuskarta. “Mai-jidda kin san yadda na ke da tsoron kishiya a rayuwata?”

Kwarai Mai-jidda ta sani, don wataran abin Anty Fauziyya har dariya yake ba ta.

“Eh, yanzu kuma da ni ki ke yi kenan.”

“Ba haka bane, maganar gaskiya ce, to wannan dalilin ya sa duk inda na ji labarin wani abu da zai sa na rike mijina na kara daraja a idanunsa , to nan na ke bazama, don na fi kauri ta wannan wurin, hakan ya sa ba kalar maganin matan da ba na amfani da shi.

In takaice miki zance dai. Hamza na ganin ajiyata komai ya banbame, domin kuwa ya kaiwa Doctor, nan Likita ya-ce, to ai wannan abubuwan da na ke ta amfani da su, su suka jawo min Infection.” 14

Mai-jidda ta jinjina maganar. “Tun daga mota ya fara min masifa, ta inda yake shiga, ba ta nan yake fita ba, ni kuma shi ne da safe raina ya baci, na rama maganganun da ya fada.

Don Allah duk ba don shi na ke ta faman wannan saye-sayen magungunan ba? Yanzu wai haushina yake ji, saboda ni na hana mu samun haihuwa.”

“Hmmm! Anty Fauziyya kar ki ce wai na bi bayan Yaya Hamza, amma ni tun ba yau ba na sha fada maku, wannan kayan duk shirme ne.

Ba wai nace kar ki yi gyara bane, amma dai ki rinka sanin inda za ki saya, ki kuma lura da hannun wa ki ka saya, saboda akwai marasa kyau.

Sannan ni na rasa me yake damun mata yanzu, duk inda mace ta ji abin mallake miji ko shi menene, sai ta karba ta afa, ko ta cusa ba tare da ta san da me aka yi shi ba. 7

Ko yaya aka yi shi. Sannan yaya lafiyar sa a jikinta, ko kuwa me zai mata nan gaba. Yanzu dai kawai abunyi shine ki natsu ki jira, idan ya huce kadan sai ki bashi hakuri. 2

Ke kuma sai ki koma aikin nature. Tunda gaki ga komai da zaki bukata cikin ingancin lafiya a kitchen dinki.’

“Sai kinga asarar kudina da ya min gaba daya ya juye komai a dustbin, harda wanda na saya dubu ashirin.” 4

Maijidda dai da kyar ta gimtse dariyarta.

Anty Fauziyya ta buga uban tagumi. “Yanzu ni na rasa me yake min dadi? Sai kin ga yadda ya bar gidan nan, ba mu taba fada irin na yau ba. Ga shi ga-rin neman kiba, na samo rama.”

“Kar ki da mu. Insha-Allahu. It’s not late, idan ya dawo, ki lallaba shi, ki ba shi hakuri ki nuna masa nadamarki. Ki ci gaba da zuwa asibiti kuma har Allah ya ba ki lafiya, ai ba a cire rai a rahamar Allah. Insha-Allahu za mu daga yaron Yaya Hamza da Anty Fauziyyan mu”.

“Na gode kwarai Mai-jidda.”

Sai da Mai-jidda ta tabbata hankalin Anty Fauziyya ya kwanta, sannan ta-ce za ta koma gida. Bayan kwana biyu da suka yi waya, ta ji muryarta wasai! “Iye, an gyaro ta kenan. Dama ai mun san fushin masoyi, hutu ne.”.

“Hmm! Ke dai bari, ba irin kashedin da bai min ba akan wannan harkar. Ai ni ma na hakura, ba dole ba. Ace da Iya Inna In-ji ‘ya’yan mayya.”

“To ya yi kyau. Ki gaishe shi.”

STORY CONTINUES BELOW


“Zai ji, ki gaida Muhammad da su Umma.”

*****

Muhammad na kammala jarrabawarsa. Mai-jidda ta hada kayansa, suka koma Kano, saboda Abdul-Aali ya fada mata yana tahowa karshen sati. Gidan Mama ya makale, saboda ya fi gane can.

Tarba sosai ta shiryawa Mai-gidan, tun shigowar sa yake mata kallon yabawa, saboda adon da ta yi. Da dare ta kawo masa Tea ne a Parlo ta samu wuri ta zauna a gefen sa. “Kun kammala shirin ku dai duka ko?”

“Eh, ba abinda ya rage. Sai dai kwanaki nawa za mu yi?”

“Kin gan ki da neman magana ko? Ina ruwanki da kwanakin da za ku yi, ke dai ki dauki duk abinda ku ke bukata.”

Shiru ta yi tana tunani, ita ba ta son zuwa ta zauna a can gaba daya, ba wanda ta sani. “Tunanin me ki ke yi?”

“Kawai dai ni ina tunanin zaman namu ne gaba daya a can da zan fi so ka bar mu anan”.

“Ina ce dai mun gama magana, kafin tafiyata, yanzu kuma me yayi saura?”

“Wai ina tunanin ko za ka dan canza shawara ne.” Ta fada gami da dan karya wuya. 4

Wani kallo ya mata kasa-kasa, “Ke ba ki san yadda na ke ji ba, idan ba kya tare da ni ko?”

Mai-jidda a take ta ji wannan balli-ballin ya dawo cikin kirjinta. “Dadin Mimie kenan, da, da ba na nan, mutuwa ka yi?”

“Dan-uwan hakan ne ai, yanzu ko daidai na ke jin kaina.” Kafin ta amsa masa ne. Wayarsa ta dau ruri, don haka ya daga.

Ji kawai ta yi ya-ce. “Na’am sweety. Yaya ki ke da yaran?’

Kut! Wato ita ce ba daman ta kira waya, amma shi za a kira shi, idan yana tare da ita ko? Sannan shi kuma har da wani amsa mata, tamkar shi kadai ne a falon. Haushin da ta ji ne, ya sa ba ta tsaya sauraron sauran zancen ba. Ta mike za ta bar falon.

Ji ta yi ya riko hannunta, yayi mata nuni da ta zauna. Tabdi! Lallai ma, haka ta daure ta jira, ya gama magana da Hamamatu, saboda ba ta son masa gardama, yana kashe wayar ya-ce. “Ina za ki je da?” 4

“Wace irin tamabaya ce haka? Dama wato da gaske, idan ka na can ma haka ka ke waya da ni a gabanta ko?”

Abdul-Aali ya yi murmushi ya-ce. “Ke fitinarki ma ta daban ce, don na yi magana a gabanki, sai me?”

“A’a ni dai gaskiya ba na so, idan har za ka yi magana da ni, ban bukatar kowa ya ji mu, ina ce waya na kira, aka ce min ba a kiranka, sai dai kai ka kira?”

“Jidda, kenan. Na ji zan daina waya dake a gaban kowa, shi kenan?”

“Ba shi kenan ba, haka ni ma idan ka na tare da ni, lokacina, lokacina ne, ba na son a bawa kowa, sai dai idan lalura ce ta taso, to. Kuma batun gaskiya ne ai, ba wani abu ba.” 4

“To ranki shi dade.”

Jidda ta juya idanunta, cikin wani salo.

“Tunda ki na Mood din Ideal wife, sai ai min tausa.” fuskarsa kunshe da murmushin tsokana.

“Dadin Mimie, don Allah ka bar wasa, sai da safe.”

“Ke dadi na dake, sai ki yi ta noke-noke, bayan kuma ni na san komai. Anjima kadan za ki zo ki na buga min kofa.” Ya fada yana wannan murmushinsa na daban din. 2

Kunya ta kamata, ta yi kasa da kai, bakinta mutuwa ya yi murus! Ai tunda ta yi kuskure, ta ja wa kanta abin magana a gun Abdul-Aali ta shiga uku. Haka ta fara masa tausa, kamar yadda ya bukata, idanunsa a lumshe. Sai ya dan bude, ya dubeta ya yi murmushi. 2

******

Sai washegari suka je gaida su Abba. Nan ne suka taho da Muhammad, yana ganin sa kuwa, ya makale masa, ya sha labari kala-kala, tare da tambayar su Mimie. “Zan kai ka gunsu, za ka je ai?”

STORY CONTINUES BELOW


“Zan je, yaushe za ka kai ni? Mamana ta-ce da nisa”.

“Gobe Insha-Allahu. Maman ka ta taba zuwa ne?” Ya fada yana kallon Mai-jidda.

“Kai Muhammad surutun ya isa haka, ka bar Uncle Abdul-Aali ya huta.”

“Mama labari fa muke yi”.

“Ki rabu da shi, ba ruwanki, mun saki a maganar mu ne? Ba ka ban labari ba, grade nawa ka samu a School ma?”

Nan Muhammad ya yi ta zuba, tare suka ci abinci, wajen karfe takwas ya gaji, ya kwanta.

Isar su PH. Abdul-Aali yayi masu shatar mota zuwa gida, suna isa. Su Ramla ne suka taryi Dadin su, da gudu suna masa sannu da zuwa, kafin Hamama ta fito, kai tsaye ta wuce jikinsa tana masa sannu da zuwa. Mai-jidda aka bari da kau da kai.

Sai da suka gama sannu da zuwa, sannan Abdul-Aali ya sa yaron gidan sa ya shigo masu da kayansu ciki. Kamar yadda ya fada, gidan wadatacce ne.

Tsarin gidajen, dakuna uku ne da babban falo guda, sai kicin. Dakuna biyu, suna da (Toilet) a cikinsu, yayin da (Toilet) daya kuma yake wajen daya dakin.

Mai-gidan ne ya nuna mata dakinta, don haka ta shigar da kaya, tun sannu da dawowa Hamama ba ta sake ce mata komai ba. Nan falo Muhammad ya tsaya da su Mimie suka samu wasa. Mai-jidda ta karewa dakin kallo gefen kujerar dakin, ta ajiye akwatinsu, gadon babu bedsheet.

Allah ya so ta, ta yi guzurin komai, saboda rashin sanin yadda za ta samu wurin. Tana shimfida gadon, ta shiga ta watsa ruwa, ta ajiye duk abinda za ta bukata na bandaki a bandakin. Cikin shigar atamfa ta fito falon nan ta samu yaran, kamar tashin murya take ji a ciki, sai dai ba ta bada hankalinta kan hakan ba.

“Wane irin abu ne, za ki ce ba ki yi abinci ba? Sai ka ce ba ki san yau za mu taho ba?”

“Sweety kai ma ka san yadda ba na jin dadi yau da ciwon kai na tashi…”

“Amma dai ki na ganin irin dawainiyar da Jiddah ta yi zuwanmu Kano ko?”

Ran Hamama ya sosu don me ya sa zai yi ta koda matar sa a gabanta.”To ai sweety ita lafiyarta kalau lokacin, haba ka tausaya min mana”

“Wannan rashin hankali ne kuma ba zan amince da shi ba, gwamma kin sani.” Ya zari makullin mota ya fito cikin zafin rai, ganin Jiddah a falon ya sa ya sauke numfashi saboda bacin ransa ya ragu.

Cikin su ya zauna ya daga Ramla ya-ce “Wa zai raka Daddy yawo?”

Dukan su suka daga hannu, “To shi kenan Mimie dauko maku takalman ku da huluna sai ku zo mu tafi.” Ya dubi Jidda ya-ce “ke ma shirya ki zo mu je.”

Mai-jidda ta dube shi yanzu isowarsu kuma ina za su je? “Fita kuma?”

“Za mu je neman abinci, Hamama ba ta ji dadi ba don haka gidan ba abinci.” ya fada yana sosa kai.

Jin haka ya sa ta mike ta je ta shirya, sai dai da suka zo fita ne sai ba ta ga Hamama ba ta-ce “Ina Mamin mimie?”

“Jikin ya motsa so, nace ta kwanta mu je mu dawo yanzu.”

“Dadin Mimie, ku je da yaran kawai ba dadi duk mu watse mu bar ta ba lafiya, idan yaso sai ka taho mana da abincin.”

Dubanta ya yi kawai ya rasa abin cewa, don haka ya kwashi su Muhammad suka tafi niyyarsa da Jidda ta je ko ruwa ba zai sayowa Hamamatu ba sai ta ci halinta.

Haka ya jido masu kayan cima iri iri suka zauna a falon shi suka ci kayansu, sai can Hamama ta fito fuska a murtuke, Mai-jidda tana mata sannu ba ko kunya ta sa baki ta amsa.

Abdul-Aali ya kalleta, ya san ba ciwon da take yi kawai shirme ne irin nata, don tun kan ya tafi dauko Mai-jidda ta tada hankali wai ita kam ba ta son ta zo mata gida. 6

“Gidan nan, gida na ne, kuma duk matar da na ke aure, ni na ke da ikon a kanta, wajibi ta bi duk yadda na ke so, saboda haka ki kwantar da hankalinki. Jidda za ta taho kuma. (I want you to be nice to her.)”

Shi ne ita kuma ta zabi tayi masa haka. Ya rasa me yake damun mata, idan sun tashi yin wani abin, ba su ko tunani, yanzu da haka za ta durawa yaran nan tarkace, duk don kar ta bawa kishiya abinci. Ya ja tsaki a fili.

****

Tana gyarawa Muhammad kwanciyar sa ne. Abdul-Aali ya shigo dakin yi mata sai da safe.

“Har ya yi barci?”

“Wai yau yadda suka sha wasan nan, ai dole ya yi barci da wuri. Ramla duk ta riga su ma.”

“Ina ruwan Muhammad.” Ya fada tare da shafa kansa. “Ba abin da ku ke bukata ko?”

“A’a tukun na dai, sai dai ko daga baya Yanzu kam Alhamdulillahi”.

“To shi kenan mu kwana lafiya.” Ya fada tare da shafa fuskarta.

A sanyaye ta amsa. “Allah ya tashe mu.”

Ya rasa me ya sa yake jin Jidda har haka a ransa, ba wani sabo ya yi da ita sosai ba, amma koyaushe ya kalleta, wani natsuwa yake samu a tare da shi. A dole ya koma dakinsa, domin dakin da yara suke amfani da shi. Nan Hamama ta tattara ta koma, ita wai a dole ba za ta hada shimfida da Mai-jidda ba, zuwa ya yi ya yi kwanciyarsa. 4

Kwanansu uku a gidan, amma Hamama ba ta canza zani ba, don haka Abdul-Aali ya sameta ya bi-ta da nasiha, tunda dai ya ga fushin nasa, bai sa ta sassauto ba.

Ta nuna dai yayi mata afuwa. Amma har cikin ranta daga shi, har matarsa haushi suke ba ta, ko da ta fada masa haka. Ransa kal! Ya shiga, saboda Jidda tana jiransa. 2

Tana fitowa daga bandaki ne, ta ji wayarta na kara, hakan ya sa ta duba, ta ga ko waye. Hankalinta ne ya tashi. Ganin sunan kan Screen din. 1

Har bari ta ji ta soma yi. Amma ta ki ta daga. Daidai lokacin Abdul-Aali ya shigo dakin, ta yi saurin daga wayar ta yi Rejecting. Sannan ta kasheta gaba ki daya.

Yake ta yi, wanda ya fi kuka ciwo, yau lafiya karfe goma da rabi Dan Kano zai kira wayarta. Bayan sun daina waya, tun ran daurin aurenta? Anya ba gamo ta yi ba kuwa?

“Jidda, lafiya na gan ki haka? Me ya sameki?”

Da sauri ta damki bakin gado ta zauna, tana maida numfashi ta-ce masa. “Babu komai.” Yau me Abdul-Aali zai yi tunani, idan ya ga wani yana kiranta a wannan lokacin, anya ba zai zargi ko haka take yi ba daman can?

Jin hannayensa da ta yi a kafadunta ne, ya sa ta razana ta dago idanu, tana dubansa. “Jidda jikin ki rawa fa yake yi, are you sure, babu wani abu?”

Da kyar ta hadiye yawu, sannan ta-ce. “Lafiya kalau. Sai da safe”.

Nan da nan ta kudundune a gefen gadon, ganin haka bai matsa mata ba. Ya kwanta a bayanta hade da jawota jikinsa, ya sumbaci wuyanta
Abin da Mai-jidda ta kula da shi. Shi ne, Abdul-Aali mutum ne da sam baya wasa da lamarin abincinsa, sannan yana da matukar jan yaran a jikinsa, don kullum bayan Magariba shi da kansa yake masu karatu. Hakan ya bawa Mai-jidda sha’awa sosai. +

Tun zuwansu, ya fi so su hadu, ayi hira kafin lokacin shiga, amma Hamama sai ta fara dauke wuta, ko kuwa ta yi ta masa hirar da ta san ya fi rinjaya a kanta.

Ganin haka Mai-jidda ta fara bada excuse, ko ta-ce ta gaji za ta shiga da wuri ko kuwa kanta na mata ciwo. A haka dai har ta daina zaman wannan hirar.

Hakan kuwa ya fi yiwa Hamama dadi. Duk randa dayansu ba ta da girki, to tana fama da al’amarin yara, har su yi barci, ita ma ta shiga.

********

Suna zaune a falon Abdul-Aali ne a Weekend. Sai ga Sam yaron gidan yana knocking wai oga ya yi baki. Mai-jidda ta yi mamaki kasancewar bai sanar da su da zauwan baki ba.

Har ta mike za ta bar falon, ganin Abdul-Aali ya fita wurin bakin, sai kuma ta hango bakin ta window, wannan wasu irin baki ne? Mata a gidan Abdul-Aali, ta juya ta ga Hamama na zaune, ba ta ce komai ba, don haka ta-ce hala ta san su ne.

Da yamma suna zaune a falon. Hamama na yanke farce, yayin da Mai-jidda take duba wani littafi, rufewa ta yi ta-ce. “Mamin Mimie, ni kuwa ban gane bakin Dadin Mimie da suka zo da safe ba?.

“Oh, Francisca ce, daga ofis din su suke.”

Mai-jidda kanta ya daure. “Me zai kawo ‘yan ofis gida kuma, duk wani aiki ba zai kare ba, har sai Weekend sun biyo shi gida?”

“Wani lokacin wasu al’amuransu suke nema na taimako, kin san sweety kuma, nan da nan zai sa a masu.”

Tabdi! Wannan wace irin rayuwa ce? Ita Hamamatu ta fi ba ta mamaki ma da ta ga ko a jikinta, bayan ta san har gida ake zuwa a kira mijinta, sannan ya fita gun ‘yan matan ofis. Lallai ita kam ba za ta yarda da wannan shirmen ba. Haka kawai! Ta ci-gaba da aikinta ba tare da ta ce komai ba. 1

Ranar litinin da safe ta tashi da wuri, ta kammala aikin Breakfast ta shiga daki ta hau shiri. Abdul-Aali ya shigo ya ganta cikin shirin fita. “Ah, Jidda yaya na gan ki haka?”

Ta juyo ta dube shi cikin murmushi ta-ce. “Wa, ni ce? Kar ka damu, ofis zan je”.

Ya bude idanu. “Ofis kuma?”

“Eh wurin aikinka, ka ga ba mu samun isasshen time da kai a Weekend ba, hakan ya sa na yi tunanin may be, idan muka fita tare, zan karasa fahimtar ko kai waye ne, saboda zamantakewar mu ta dore”. Ta fada hade da daura agogon hannunta. 2

“Na yaba da gesture dinki na son gyara zamantakewarki da ni, amma ofis kam, ai wurin aiki ne. Yaya za ayi…”

Pin din shaylarta ta makala “Right, haka gida ma wurin iyali ne, me ya sa za ka kawo ‘yan ofis gida, su cinye mana lokacin mu?” ta karasa tana masa kallon tuhuma.

“Ok, in na fahimceki, kin gwada manufarki, ba kya so a zo wurina daga ofis, ko kuwa dai don mata ki ka gani shi ya sa?”

“Ko ma wa na gani, ai gida ba wurin aikin bane, idan ka tafi, ka yi yadda ka ke so, amma haka kawai wasu mata masu dangalallun siket su kama hanya su wani biyoka har gida, wai lamarin aiki? Ba maza ne a ofis din?” 4

Tana fada a tsume. Abdul-Aali kuwa ya sa dariya ya-ce. “Wallahi duk kishin Hamama, kin damata, kin shanye, ba ta taba cewa komai ba, amma ke… Sai a hankali.”

“Ai laifinta na gani, da ta yi magana tun farko da ba a biyoka har gida ba. Don haka ni ma yau ofis zan je.”

Ta fita daga dakin da jakarta, ya bi-ta da kallo. Lamarin Jidda baya daina ba shi mamaki. Tana wargaza masa kwakwalwa, nan ya fito ya sameta a falon ta gama dakewa. Hamama ta dubesu da neman karin bayani. Mai-jidda ta-ce. “Dadin Mimie ba ka fadawa Mamin Mimie za mu fita ba? Mamin Mimie rabu da shi, ya manta.”

STORY CONTINUES BELOW


“Uhmm! Za mu je da Mai-jidda, ta ga wurin aikina, direban ofis zai kawo ta gida.” ya fada tamkar dole yayi bayani.

Hamama ta ‘kula akan me ya sa za a kai ta yawon ofis? Ita yaushe ya taba kai ta ofis dinsa?

“Amma Sweety…” Maijida ba ta jira, ta ji me za ta fada ba ma, ta yi waje abin ta, ita mata na ba ta mamaki. Yaya za ayi wai ba za ki yi kishin mijinki a waje ba, sai ya auro wata, ki zage wai ke ga mai kishi? A mota ta yi zamanta, yana fitowa, ya shiga mota.

“Jidda, ke ‘yar rigima ce Wallahi.”

“Don Allah tsakanin ka da Allah. Yaya za ayi na ga ana sintiri wurin mijina, hankali na ya kwanta? Idan Mamin Mimie tayi maka koma meye ne, ni ba zan damu ba, saboda matarka ce, amma haka kawai ka hau washe baki, don wai wasu kattin mata?”

“Ke ba ki dariya da wani ne, sai ni?”

“Kai ma ka san an wuce nan, wanda ya kama ayi shi daidai gwargwado, ana yi, amma kai fa, tamkar daya mai blun kayan nan, za ta shige jikin ka take yi.”

Wani dadi ya ji a ransa, ya kai mata sumba. “Ina sonki da yawa Jidda, na ji dadi na, ashe ke ma haka ki ke so-na?”

“Don kawai, ina kishinka, ai ba shi bane so.” 5

“Hmm! Na ji.” Sai da suka je ofis din, ta ga har inda yake aiki tukun, sannan hankalinta ya kwanta ta-ce. “Zan koma na bar ka ka yi aiki, kuma Wallahi ko kallon wata ka yi, ni da kai yau.” 9

“To ranki shi dade.” Ya fada yana dariya. Nan ya hadata da mai mayar da ita gida. Tana tafe dadi fal! A ranta da ta dau mataki, gobe ba mai kara zuwan masu gida.

Wuraren azahar ya kirata, wai yana jin yin hira. “Ka fasa aikin yau din kenan.”

“Babu, aikin da tun tafiyarki, kin tafi da concentration dina, banda ke ba abin da na ke son gani.”

“Dadin Mimie kenan, kar ka wani dora min laifi. Idan za ka yi aikin ka, ka yi.”

“Ke ba kya son na dawo gida yanzu?”

“Ni aiki na ke yi a kicin yanzu, idan na gama kuma za mu yi karatu da yara, idan mun gama kuma zan yi barci. Idan na tashi kuma na mikawa Maman Mimie ragamar gidan. Which includes you, saboda haka ka yi zaman ka a ofis.”

“Ni dai ba ni da gata, haka kawai ayi ta wahalar da ni, ba a sani a lissafi”.

Kashe wayar ta yi tana dariya, don ta kula yau a cikin (Mood) yanayin wasa yake. Tana kashewa ta hau tunanin yadda a hankali Abdul-Aali ya rikide kamar ba shi ba. Bayan sakin fuska da walwala da son yara da son kyautatawa, sai take mamakin yadda da duk ba ta ganin wannan a tare da shi.

A yanzu kuwa ba ta ma son tuno iya soyayyarsa, saboda tsikar jikinta tashi yake yi. Ashe za ta iya son Abdul-Aali? Ashe gaskiya su Yaya Maryam suke fada mata tana son shi tuntuni? 2

To amma kuma kusan hakan take ji game da Dan Kano a baya, an taba son mutum biyu lokaci guda? Me ya kai ta tunanin Dan Kano? Haka nan ta ji tsigar jikinta ta tashi, a daidai lokacin da (Pressure Cooker), ya saki kara.

Can falo ta jiyo fada. Da sauri ta fita don rabiya, don baya wuce Muhammad da Mimie, ga son wasa, amma da zaran an hadu, to sai an taba.

Bayan ta kammala ayyukanta ne. Ta kira su Mama suka gaisa, haka nan ta kira Umma. Zaman su dai ba laifi tsakaninta da Hamama, kasancewar ba mai shiga sabgar wani, randa rikicinta ya tashi kuwa. 2

Ta fi sauke fushinta kan Mai-gidan. Abu guda da ya fi damun Mai-jidda. Shi ne yadda sam ta ki ta sake da Muhammad, komai ya yi a gidan. Sai ta yi magana.

Hakan ya sa sai su zauna ko a falo, ko kuwa ta sa shi ya huta a daki. Abdul-Aali kuwa da ya kula da rashin sakewar da Muhammad ke yi, sai ya ja shi jiki, su fita tare su yi sallah tare.

STORY CONTINUES BELOW


Wannan ya kara sawa Mai-jidda ganin kimarsa da darajarsa, don haka ba ta wasa da duk wasu al’amuransa.

Ana shirin komawa makaranta ne, ta samu Abdul-Aali da batun makarantar Muhammad. Shi ya gwada mata yana so su zauna anan da su Mimie.

Saboda su shaku ne, ita kuma ta-ce ta fi son su koma Kano. Ganin ta dage kan maganar, ransa ya dan sosu, ya kyaleta ba tare da ya-ce komai ba.

Ran Juma’a ya-ce, su shirya zai maida su Kano, ta ji dadi. Amma ganin yadda ya bata rai, ta san ya yi ne kawai, don abin da take so kenan, ba wai hakan ya kwanta masa a rai ba. Ita dai kam haka kawai ba za a takurawa Danta ba, idan gidan Dadinsu Mimie ne, shi kuma Baffansa ne.

Ba bare ba, don haka ta danne zuciyarta, gwamma ta yi zamanta a Kano ta kula da yaronta, tana bangarenta duk lokacin da suka zo su zo a marmarce, kafin lokacin barin su PH din ya yi gaba daya.

************

Yana ajiye su. Kwanan sa biyu, ya gaida iyayensa, ya yi wasu harkokinsa, sannan ya koma. Gaba daya sai ta samu kanta da jin wani iri da rashin walwalarsa.

Ta yiwa Muhammad rajista a wata makarantar dake kusa da su, ta kudi ce mai kyau, kullum ita take kai shi, ta kuma dauko shi idan an tashi.

Hankalinsu kwance. Idan Weekend ya yi ta kai shi wurin su Mama, yayi masu Weekend, a haka ta sa shi a Islamiyya.

Ranar laraba da yamma Mukhtar ya kawo matarsa. Mai-jidda ta-ce. “Ai Mukhtaar na fara tunanin anya kuwa? Har zan sa ka a kwandon shara, ka ci albarkacin Kamila.”

“Hmm! Anty Hauwa ba za ki gane bane, sai dai a hankali ke kam, kin san tana Service dinta a Damaturu so, zaman nata on and off, sai yanzu na samu aka dawo da ita nan, ni kaina ban ganta sosai ba.”

“Hmm! To ya yi kyau. Kamila kin ji mijinki ya yi kwas a iya bada Excuse.”

Kamila ta yi murmushi. Nan Mai-jidda ta cika masu gabansu da kayan cima iri-iri. Ita dai Kamila faram-faram din Mai-jidda kawai ke burgeta, tana da son mutane.

“Da Yaya Abdul-Aali ya ce, duk kun koma PH”.

“Kai ka rabu da ni, na dawo nan ka ji mutane su yi ta zaman keji? Ka ga nan na sakata na ga ‘Yan-uwa son raina. Ga shi yanzu na ga Kamila”.

“Kin yiwa Anty Hamama wayo kenan.”

“Suna can da yara ko da muka yi waya da su Mimie, su ma wai ba su jin dadi.”

“Hakan ya fi, ko ba komai za mu rinka ganin Yaya Abdul akai-akai, tunda an ajiye gimbiya a nan.”

Mai-jidda ta yi murmushi. Mukhtaar bai san darun da ake tabkawa bane, tun da ya ajiye su bai zo ba, sannan waya idan ya bugo to bukatunsu kawai yake tambaya ko kuwa ya ji lafiyarsu, babu wata doguwar zance.

Ita ma ba ta damu ba, duk da tun tahowarta ta fahimci, kamar tana dauke da ciki, don ba ta ga al’adarta ba, ga wani barci da take yawan yi na safe.

Ba ta fada masa ba, duk randa ya zo, sai ta fada masa. Wani ikon Allah, ba ta tashi fara laulayi ba, sai da ta yi PT, ta tabbatar da shigar ciki. Shi kenan zazzabi ya-ce salamu-alaikum, ga amai kamar me. Makaranta ma Kasim ne ke kai Muhammad.

Tana kwance lamo a falo, sai ga su Mama sun yi sallama, ta gyara jikinta, sannan ta bude kofa, ta yi farin cikin ganin su kwarai.

Bayan sun gaisa Abba ya-ce. “Hauwa yaya ki na kwance ba lafiya, ba za ki sanar da mu ba?”

“Abba, na ga da sauki shi ya sa.”

“A’a an taba wasa da lafiyar jiki ne? Sai da Kasim yake fada mana wai ai kwana biyu shi yake zuwa ya kai Muhammad makaranta, saboda ki na kwance.”

STORY CONTINUES BELOW


Nan Mama ta karbe. “To kin je asibiti ne?”

Kanta na kasa ba ta-ce komai ba, nan ne Mama ta fahimci ko menene, sa ta tayi a gaba ta-ce “Ki shirya gobe sai ku koma gida Insha-Allahu. Amma mutum ya kwanta ciwo shi kadai a gida?”

Ita duk ciwonta bai dameta ba, irin yadda Abdul-Aali ya yi banza da ita, ita ba kiran wayarsa take yi ba, bare ta kira ta ji dalili, shi kuma ya dau zafi ya sa ta a gefe, tunda ba ta damu da shi ba.

A wurin Mama ya samu labarin ciwon nata, sai ga wayarsa da dare ta daga suka gaisa. “Yaya jikin naki? Mama ta-ce ba ki ji dadi ba.”

“Eh, da sauki Alhamdulillahi! Ina gidan Abba ma”.

“Uhmm! Allah ya kara lafiya”.

Kawai ya ce, ya kashe wayar Mai-jidda, ba ta san sanda ta sa kuka ba, ace wai ba ta da lafiya iya kulawar da Abdul-Aali zai nuna a gareta kenan?

Gwamma da ta taho Kano ya nuna mata halinsa na gaskiya, wato mugunta, da tana can ai ba za ta gane hakan ba. Ita kuma ta ki ta fada masa ciki ne da ita, ta san Mama ma ba ta fada ba.

*******

Washegari ta fito wanka kenan da yamma, sai ganin sa ta yi a dakin, ya ba ta mamaki kwarai, don ba ta yi tsammani ba.

“Dadin Mimie!”

“Jiddah. Yaya na ga kin tsaya ko zuwan ma kar nayi, tunda kin zabi ki gujeni?”

Murmushi ta fara yi ba ta san yaushe hawaye ya tabo gefen idanunta ba, don haka ta dan share da bakin Towel din da yake kafadarta. “Ni ban guje ka ba. Allah ma ya gani.”

“Mikewa ya yi ya riko hannunta, ya zaunar da ita a bakin gado. “Yaya jikin naki? Kin ga yadda ki ka yi haske kuwa?

Ki na da jini a jikinki? Kin je asibiti kuwa? Me Likita ya-ce? Ni fa ba na son wasa da lafiya. Yaya za ki zauna har sai su Mama sun ce ki taho nan, alhali ki na fama da ciwo?”

Kallon sa kawai take yi, idanunta cike da hawaye, can kuma ta-ce. “Ina da jini na a jiki na, ban je asibiti ba da farko.

Saboda ba na zuwa asibiti bane, sannan wa zan fadawa damuwata bayan ka share ni, ka daina damuwa da ni ko waya, sai a tsume ka ke min?”

Shiru yayi sannan ya nisa. “Ki yi hakuri raina ne ya baci, na sha fada miki ba na son taurin kai. Kuma ba abinda na ke so irin ki kasance a tare da ni… Amma tsaya tukun, wane irin ciwo ne, ba na zuwa asibiti ba?”

Idanu ta bude masa tana murmushi, nan take ya dago zancen, da sauri ya kai mata sumba cikin jin dadi. “Da gaske ki ke yi Jidda?”

“Eh, bayan na dawo nan na je asibiti, sun sake tabbatar min, wata biyu kenan.” 2

Wani farin ciki ne ya rufe shi, har ya kasa ce mata wani abu. Ta cire hannunta a nasa ta-ce. “Bari na shirya, har kasa jiki na ya bushe, ban shafa mai ba.”

Kallonta yake yi cike da abubuwa a idanunsa. “Ki shirya ki zo mu tafi yawo.”

“Yawo kuma ni da ba ni da lafiya, Ina za mu je?”

“Ke dai ki shirya ki fito, idan kuma so ki ke yi mu zauna anan, shi kenan sai na sa key a kofa.” 1

Nan take ta dago manufarsa, yau ta shige su. Abdul-Aali zai jawo mata magana, yanzu ta shirya ta bi-shi, sannan su dawo bayan kuma Mama za ta gane?

To amma idan ya kulle kofa, kuma shi kenan ta tabbata a daki babu fita. Tana gama kimtsawa ta-ce. “Yaya ka ke son na yi? Mama ta san ba na jin karfin jiki na, wane unguwa za ka ce za mu je?”

“Idan ba ki fito ba, na rantse zan sa key, don ba zan iya hakuri ba.” 2

Haka ta sungumi mayafi tana ji, ya kerawa Mama karya wai zai kai ta asibiti a sake duba ta, don ya ga kamar ba ta da jini sosai. 3

Mama ko ba ta ce komai ba, baya ga a dawo lafiya.

“Idan ba ta sani ba, kai za ka zo ka koma ka bar ni, ni na ke zaune da ita ka sani jin kunya kawai.”

“Laifin waye? Wa ya-ce ki gudu ki bar ni, bayan kin san yadda na ke jinki a raina.”

*********

Za ta mike ya kara janyota jikinsa. “Wa ya-ce miki ki tashi?”

“Yanzu kam idan muka yi dare, ce mata za ka yi PH ka kai ni asibitin ko meye?” 4

“Wa ya-ce miki za ki koma? Ai ta riga ta sani, saboda haka kawai ki yi zamanki da tushe, sai gobe zan mai dake.”

Sai ga Mai-jidda har da kuka tana rokon Abdul-Aali ya maidata gidan Abba, amma haka ya share ta ya more abinsa. 3

A tsume ta zauna, a falo ta-ce. “Yanzu kam sai dai ka kwaso min kayana, ka ce na warke, don ni kam ba zan koma ba da wane ido zan kalli Mama Fisabilillahi?” 1

“Ki tashi na mai dake, anan din da wa za ki zauna, ki na ganin yadda ba ki iya yin komai.”

“Na kusa na warke ai.”

Ajiyar zuciya ya yi, ya zauna kusa da ita. “Ke da mijinki, koma ina ki ka je, ba mai miki magana, don haka ki kwantar da hankalinki, ki zo mu tafi, ni kin ga tafiya zan yi na fi son, kuma na san cewa na bar ki cikin kulawa.

Idan da son samu ne, ni da kaina na zo na kula dake, amma kin ga hakan ba zai yiwu ba for now. Amma na kusa daukar hutu Insha-Allahu, kafin nan ki daure, ki zauna da su Maman, ok, kin ji?”

“Idan za ka zo nan gaba, ka fada min, sai na taho kafin isowarka, ba wai ka saceni ka mayar da ni ba.”

“Na ji Gimbiya, za mu tafi ko kuma da saura? Don ni kam zan iya.” 4

Ta buge shi a kafadarsa, sannan ta mike suka tafi. Ranta dadi fal! Saboda Abdul-Aali ya bar fushi, daga ranar kuwa ya makalewa waya, idan suna hira kamar ya tsago ta cikin wayar haka yake ji, haka ita ma Jidda ba ta gajiya da jin muryarsa. Tunda ta samu karfin jikinta, suka tattara suka koma gidanta. Sai ta dauki A’ishan Yaya Maryam, don ta tayata zama a gidanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *