KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 1 BY ayshay bee

KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 1 BY ayshay bee

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

              11th September, 2016

                 2:30 Am midnight

   Talatainin Dare lokaci ne na hutu da natsuwa. Lokaci ne da Al’umma suke kwanciya bacci domin sauke gajiya. Wadanda ko ba baccin suke ba zaka same su suna Bautar Allah ne ko kuma kallo, karatu ds. Koma dai mai Dan Adam yake a cikin natsuwa ya ke yinta a wannan lokacin in ka cire Shaidanun mutane wadanda suka dauki duniya gidan dadi kaman ba za a mutu ba. Duk abinda suka ga dama yi suke yi musamman sabon Allah da ya hada da shaye shaye da bin gidajen karuwai da na raye raye. Irin wadannan mutanen ne suka maida tsakar dare lokacin yin masha’an su, wasu ma abin nasu a boye ne dan kagansu da rana cikin mutunci da kamala zaka rantse sharri ake musu, Allah ya shirye mu ya kare mana zuri’a Ameen Ameen.+

Sulaiman Gidado matashin saurayi ne mai jini a jika. yana da kimanin shekaru Ashirin da shida a duniya. kyakyawa ne burin Ko wata ya mace dake rayuwa a doron kasa. duk da dai ance abinci wani gubar wani amma duk budurwar mai lafiyan da taga Sule wallah sai ta dara. Fari ne tas da ka ganshi kaga dan hutun da naira ta samu zama a wurin. Yana da dogon hanci Sak bafulatanin usuli, idon shi ko manyan ne farare tas mai ruda yan mata masu kwarjini da takama da Kansu, hakan na kara taimaka mishi wurin Yaudaran yan matan kwarai dagaske. Komai na Sule is perfect in ka cire wasu bangaren daga cikin halayenshi, dama ance mutum Tara yake bai cika goma ba… In ko ka ganshi a fili zaka rantse da Allah ba zai aika ta halayen shi daya Zame mai sirrin boye ba amma ina Musa a baki ne Fir’auna a zuci.

Zaune ya ke a Nicon Abuja tare da New catch in da yayi ko kuma ince new target wurin birthday in wata frnd inta. Yayi Nisa a wurin bin clubs, shaye shaye da kuma bin mata. Sai dai ba kowacce mace ya ke bi sai wacce ta amsa sunan ta mace mai ji da kai, zai nuna miki soyayya kaman da gaske yake sai ya samu abinda yake so zai wurgar da kwallon mangaro ya huta da kuda wai in angama shan abun sha wullar da kwalba ake dan bata da amfani.

Rungume yake da budurwar ita kuma sai wani kara narkewa take a jikin shi kaman wata mage. Flash in camera ke ta haske cikin hall in. A daidai wanan lokacin motan polisawa suka wa wurin diran mikiya, ba kanana polisawa bane Aa manya ne masu rank in Inspectors, ASP da DSP.

Cikin Hall in suka karasa da bindigogi a hannun su.

Suna shiga wurin yayi shiru yanda kasan ba wurin kidan ke tashi ba, ganewan da suka yi ba kanana nan polices bane da suka raina ma wayau ya sa su shiga hankalin su.

“Here is him” Wani inspector ne ya fada yana pointing Sulaiman dake rungume da Leelah budurwar tashi.

Wurin shi ko suka nufa hade da mika mai ankwa “You are under arrest”

Sororo ya tsaya yana kallon su domin rashin sanin laifin da ya aika ta musu “I don’t Understand Sir”

“Don’t argue with us Mr Sulaiman Gidado, You will know Everything after we get to the police Station” Wani DSP ya fada yana mishi shu’umin murmushi

“Okay I will follow you guys, but I think you don’t need this thing” Sulaiman in ya fada yana musu kallon sama da kasa

“Fine let’s Go”

         

               10:00 Am na safe

                 Birnin Zazzau

  Ahmad deedat ne zaune yana research akan conference in da zai je Abuja kasancewar shi lecturer a jami’ar Ahmadu Bello University dake Zaria.

     

   Wayar shi dake kusa dashi ne ta hau ruri. MUSA ne ya fito baro baro a gaban screen in. wani irin faduwan gaba yaji domin ya San ganin kiran Musa a gare shi ba alheri bane, sai da yayi bismillah sannan ya dauka.

“Ahmad, kayi mamakin ganin kiran na ko?” Musan ya fada yana dariya alamun cikin farin ciki yake.

Gaban Deedat ne ya kara fadi sanin cewa dariyan musan ba alkhairi bane a gun sa “Ina jinka ya akayi?”

“Ka kunna TV, tashar NTA yanzun nan za kaga sakon da nake son isar maka” Kwashewa da dariya yayi Wanda da kaji Kasan na mugunta ne sannan yayi ending call in

Innalilahi wa’inailaihi raji’un Deedat ke ambato a fili, Remote in TV ya dauko ya kunna sannan ya kai Tashar NTA.

Smugglers in cocaine aka kama a Airport, sai dai sunce sako ne su ake basu in suka kawo a biya su kudinsu, Sannan sun tona asirin ogan nasu har ma polices sun kamo shi a club in dare a Nicon Abuja, Wani Dan National Drug Law Enforcement Agency ( NDLEA ) ke bayyanin wa yan jaridan da suka sa shi a gaba.

Presently ogan na hannu Polices sannan EFFC sun fara bincike akan shi, sunan shi Sulaiman Gidado. Wani Dan jarida ke magana sannan karan hade da nuno hoton Sulaiman in.

Dafe kai Deedat yayi gami da kiran sunan Allah, “Sulaiman cocaine? Sannan club in dare? Anya ba sharri aka mai ba? kodai Musa ne? Kai ba zai yuwu ba karya ne” ya fada hade da girgiza kai

Hayaniyan da ya ji yana tashi daga cikin gidan su ne ya katse mai tunanin abin ban alajabin da ya ke ciki. Da sauri ya nufa cikin gidan.

A tsaitsaye ya iske su wasu na sallalalami wasu kam kuka ma suke, abin ka da mata hamza ne kadai Babban Namiji a gun.

Zahra ce a tsaye jikinta sai karkarwa yake basu ankara ba sai gani suka yi ta zube a kasa, A rude su kayi kanta dan daman jimamin ita suke tayawa.

Hamza ne yayi karfin halin dauko ruwa Deedat ya shafa mata sannan aka samu ta farfado amman ba natsuwa a jikinta, ko ina  na jikinta rawa yake, a hankali Deedat ke mata addu’oi tana amsawa sannan fa ta Dan samu natsuwa.  Bacci su ka samu tayi Wanda daga gani kasan ba na lafiya bane.

“Ni Gsky abin nan ya daure min kai anya Ya Deedat ba sharri bane?” Hamza ya tambaya

“Ni ma ban Sani amma Sulaiman in da na Sani hakan ba halin shi bane ko kadan” Deedat ya fada cikin tsantsan mamaki

“Ya Deedat ba abokin ka bane, Gsky a ganina kawai sharri aka mai” Wannan karan Ummi ce tayi maganan

Mai Jidda da Nanah kam har yanzu sheshekar kuka su ke. “Dan Allah Ku bar kukan ya isa haka, kukan Ku ba zai fidda shi ba” Ammah ta fada cike da  lallashi.

Mami kam mamakine ya hana ta magana Suleiman in da ta sanni natsatse, mai addini ga hankali da tarbiyya. Ba dai kama ko kadan, Allah ya sa ba da gaskr bane. Nima dai nace Ameen…

                  12th September, 2016

                Birnin Tarayya Abuja

    4:00 pm na maraice Deedat su ka tashi daga taron da ya je a cikin Abujan, Hotel in daya sauka ya koma, wanka yayi bayan yayi Sallah, ko ta kan Abinci bai yi ba ya dauki keyn mota ya fita.

  Abatcha Barrack dake Asokoro ya nufa kai tsaye Wurin dan’uwan shi Captain Aliyu Wanda ya sanar wa zuwan shi tun da safe.

Cikin Girmama juna suka gaisa, in kaga yanda Deedat ke wa Aliyu za ka rantse shekaru daywa kawai ya bashi amma shekara Uku kawai ya bashi, Aliyun mutum ne mai kwarjini da kima a idon mutane. Aliy kenan mazan fama.1

House boy in shi ya kira Daniel, kallo daya ya mi shi ya dauke kai hade da fadin “I have a guest, attend to him”

Abinci kusan kala uku, Fruits da drinks Daniel ya cika wa Deedat gaban shi dashi domin ko Aliyun Mutum ne da bai wasa da cikin shi ko kadan.

“Bismillah Malaman jami’a, gidana ai ba bakonka bane ai ka Sani”

Murmushi Deedat in yayi sannan ya fara cin Abincin.

“Ashe kuma abinda ya faru da abokinka kenan?”

“Ehmm wlh ni har yanzu abin daure min kai yake, gani nake sharri ne”

“Ko daya, ba sharri a ciki dagaske ne, kawai dai baka San halin shi bane”

“Kai Ya Aliyu? Sulaiman din gaskiya da mamaki”

Murmushi Aliyun yayi sannan yace “Shiyasa nace maka baka San halin shi ba, Abokantakan naku a Zaria da Kaduna kadai ya tsaya, hasalima zaka dauka mutum daban ne na can da kuma na cikin Abujan, Nasan waye Sulaiman shi yake ganin ban San shi ba. Na kyale shi ne kawai domin yayi nisa ba zai taba jin kira ba Rana irin na yau ya bayyana wa duniya waye shi, dazu na je na gan shi and yana kokarin Denying kuma shi ne the worst abinda zai yi, Wlh mutanen nan sunfi shi taurin Kai.”

“Tabdijam, Gaskiya abin akwai daure kai a ciki, Yanzu ya Aliy miye abin yi?

” Ba abin yi Deedat sai jiran hukuncin Ubangiji, Wlh kaf Naija banga me amso Sulaiman ba, can akwai business insu daya hada su ya sa su kayi kulla kullan da suka tona mai asiri.Zahrau ce tsugunne gaban iyayenta Abba, Baffa, Mami da Amma suna mata Nasiha akan Zaman aure. +

  Zaune kawai take ba wai Dan kwakwal warta na daukan wa’azin da suke mata ba illa tashin hankali da bala’in da take ganin iyayen nata sun jefa ta a ciki Wanda su a ganin su gata suka mata.

  “Allah ya miki Albarka, tashi kije ana jiranki” Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta, Anty Zainab da Anty Rukayya ne rike da ita sai kuma Maijidda da Ummiy dake biye dasu tare da wasu yan uwa, Sai guda ke ta tashi duk farin ciki ke fuskan yan kai amaryar inka cire maijidda da Amina da su ke ta kuka. Anty Zainab ke ta musu fada akan zasu tada ma amaryar hankali, Mutane da yawa ganin su rabuwa da Amaryar ya sa su kuka sai dai su suna mata kukan takaicin gidan da zata ne, gidan da su ka kira bakin gida Wanda su ke da tabbacin ba komai a ciki sai tsangwama, Wahala, mugunta da dai duk wani abin takaicin rayuwa.

   “Anya su Abbah sun San abin da suka hada kuwa?” Ummiy ke tambayan kanta a karo na ba adadi, ta so ba Fatima bace zata fada wannan gida at least da ace ita ce ko maijidda ba shakka za su iya kwato yan cinsu amma Zahrau duk cikin su tafi su tsoro da sa abu a rai. “Bakomai ai in ya sa mata ciwon zuciya ta mutu kowa ya huta”

A haka suka isa motan da aka tanada domin amaryar, Hamza ne ke tukin sai Ummiy a gaba, Amaryar da Maijidda da Anty Zainab a baya. A hankali motan ke tafiya, mota daya a gaban su daya a bayan su, duk dai close families ne a cikin. A jere motocin suka fita birnin zazzauOne week later+

                  19th September, 2016

  Ba irin fadi tashin da Iyayen Sulaiman basu yi a fiddo shi ba amma a banza. Maganar Aliyu ce dai ta tabbata daya ce kaf fadin kasar nan ba mai iya fiddo shi.

  A bangaren Zahrau ko ikon Allah ne kadai ya kaita izuwa wannan lokacin, duk ta rame, abinci ma sai anyi dagaske ake samu ta ci kadan, in ko aka matsa mata dayawa da ta gama ci za ta amayo shi, Zazzabi ko dashi take kwana ta ke wuni har an daina irga ledan ruwan da a ka sa mata.

Ganin abin na ta bana Kare bane, anyi fadan har an gaji, ya sa aka koma yi mata wa’azin yarda da kaddara, ana binta da lallami kawai, ba Wanda bai ji da Zahrau kaf fadin gidan in aka cire mutum daya da shi gaba daya harkar su ne ma bai Shiga balle ya damu dasu, A fadar su Zahrau yar Amana ce a wurin su so dole taga gata.

                  20th September, 2016

                            Abuja

  Sulaiman ne zaune a dan dakin da aka ajiye shi. Duniya ta mishi zafi, bai taba tunanin irin haka zata taba faruwa dashi ba. Yayi dana Sanin rayuwar da ya tsabar wa kanshi wanda ya boye wa Yan’uwan shi da duk wani na kusa dashi, shi ya San da sa baki a kama shin da aka yi amma tun farko shi ya ja wa kanshi. A yanzu ya fi takaicin halin da ya sa iyayen shi da kuma Zahrau wanda ba wai an fada mishi bane amma ya San irin halin da za ta Shiga. Ya San irin Son da ta ke mishi shi ma kuma hakan ne domin kaf duniya ita kadai ce macen da ya taba wa soyayyar gaskiya. Ya San bai mata adalci ita da iyayen shi ba, he wish za a bashi dama yaje ya roki su gafara.

Yau gabadaya wani iri ya ke jin shi tunda ya tashi, Sati daya kenan banda ruwa ba abinda yake iya kai wa cikin shi. Kaman kullum Abinci da suka sa ba bashi da ko kallo bai ishe shi ba aka kawo mai, Yunwa yake ji kaman ya mutu da sauri ya jawo abinci ya fara kai bakin shi. Sai da ya cinye Abincin tas sannan yaji cikin shi ya fara wani irin mahaukacin murda, tun yana daurewa har ya kasa, wani irin kara ya Saki Wanda ya jawo hankalin police in da ke wurin. Da farko sun dauka iskanci ne amma ganin yanda ya ke ihun a gigice yana neman dauki ya sa suka kira Emergency aka tafi dashi asibiti.

  Ba karamin galabaita yayi ba kafin a karasa, da gudu aka wuce dashi A&E. Sama sama ya ke hango Leelah da Samira (Last yarinyar da ya yaudara)

  “Sulaiman kenan ka dauka ka ci bulus, ka gama shan abin sha ka yadda kwalba ko, to kayi kuskure dan baka San wacece Samira balle mutanen da take hulda da su, Leelah kuma Aminiya tace  muka hada baki domin ganin mun kawo karshen ka” Wani irin mahaukaciyar dariya ta sheke da

Leelahn ce ta kalle shi yana ta kokarin tashi ya zauna, ture shi tayi ya koma kwance “kwanta mana yanda poison in zai bi jikinka da kyau ka tafi kowa ma ya huta”1

Bin su yake da ido kawai dan yawun bakin shi ma ya kafe balle ya iya magana.

“Da polices, da likitoci kai manyan kasan nan gaba daya ba ta inda bamu da hanyan samun abinda muke so akan ka, So Sman a huta lafiya sai munzo ko”  tare su ka fada suna daga mai kira sannan suka fita su ka bar dakin.

Sunan Allah Sulaiman ke kira jin wani abu dake tasowa a cikin nashi sai time in munafukan doctors in da aka hada baki su ka shigo, daga musu hannu yayi alamun kar su taba shi, Abu daya kawai yake ta fadi “Dan Allah Ku rokan min gafara wurin Iyaye na da Zahrau”

Wani irin Amai ya fara yana kiran Sunan Allah, Kafin kace kabo har yace ga garinku… Kulli Nafsin za’ikatul Maut daman kowa nashi ya ke jira.2

Gawan shi ma da kyar aka bada, aka mai Sallah sannan aka kai shi gidan shi na gaskiya.

A gidan su Zahrau ko ba karamin tsinkewa su kayi da Al’amarin ba barin ma Deedat da yake aboki a wurin shi. Zahrau lokacin da labarin Mutuwan ya iske ta ba karamin kidima tayi sai ma ta nemi kukan ta rasa, lokacin ta yadda lallai kukan ma rahama ne. Ta rasa Abdulrahman sannan a karo na biyu ta kara rasa Sulaiman ita kan bata da Sa’an Soyayya a rayuwa. Ta bawa yan gidan nasu mamaki domin yanda suka yi zaton zata karbi labarin mutuwan Sulaiman ba haka tayi. Juriya tayi ba Kadan ba ta fawwala wa Allah komai, Ko yaushe cikin mishi addu’a ta ke dan wasu halayen nashi ma sai bayan rasuwan shi su ke ta fito, Kai jama’a Allah yasa mu dace kawai. Har sauka tayi a matsayin sadaukarwa gareahi Allah ya kai ladan cikin kabarin shi. Tana dai kokarin Danne komai amma kai da ka ganta kasan tana cikin damuwa duk tayi baki ta rame abinka da farar mace. Allah ya sa mu dace kawai.

                  One  month later

Shirye Shiryen bikin Captain Aliyu ake wadan za ayi karshen shekara, ending December kenan. Sosai da Sosai ake shirya wa bikin Dan last bikin da aka yi a gidan shi ne na Anty Zainab Wanda yanzu haka take da ya’ya’ Uku, Babban su na da shekara Tara.

  Farida Ibrahim Kabir diya ce ga Wani Babban Dan kasuwan da ake damawa dashi a harkar Siyasa na jahar Kaduna garin gwamna.

  Sun hadu ne da Aliyu a bikin wani Abokin shi, ita kuma kawar Amarya. Babanta Mutum ne Wanda bai yadda mu’amala ta hadashi da Talaka ba ko da wasa hakan ya sa tun wuri ya gargadi ya’ya’nshi a kan hakan.

Ko da Faridan ta zo mishi da labarin Sojan hannu biyu ya karba ganin cewa Matashin Saurayine Wanda kudi ke shigo mai ta kowani hanya amma ya so samun fin hakan. Sai dai ance wai da babu gara ba dadi.1

Three Weeks to bikin kusan an gama komai sai jiran lokacin biki, anyi organising events kala kala daga both side na amarya da angon, haka anko ma kala kala an fiddo su.

Su Zahrau yan mata sai murna da rawan jiki ake, amma asali ba wai auren bane a gabansu, A’a barin gidan da zai yi gaba daya har Weekend ba zai dinga zuwa ba ke sasu farin ciki domin ganin shi kadai ba abin alkhairi bane a wurin su “Allah ya sa daidai dashi ce wacce zata gasa shi” Ummiy tana fada tana tabe baki, Maijidda ce ta katse zancen da cewa “ke a ganinki Ummiy akwai macen da zata iya gasa sojan nan, tabdi ” “Haba Hauwa kulu Maijidda sai dai in Soyayyan bai kama shi ma wlh” Zahrau ke fadi hade da girgiza kai tana murmushi.

  Dukkansu shiru su kayi, tausayin yar’uwar su na ratsa su, sun San ko shakka babu tana tuno masoyanta da ta rasa ne. Nanah ce ta katse shirun “haba Ku ko yayanku ne fa amma kullum mugun fata kawai kuke mai, Allah ba kyau.” Ummiy ce ta daga mata hannun cike da tsiwa “Wai ke Nanah Dan baki San waye wannan mutumin bane shiyasa ki ke kare mai kina ganin jiya fa dan muna murnar ganin Hamza yaushe rabon da a hadu ya fara zaginmu, mu dolayen ina ne, mahaukata, wawaye da baza mu taba girma ba, Fisabililahi kuma a gaban wannan Abokin na shi, yanzu fa ba da bane”

“Ni ko banga laifin Abokin ba, hana shi ma fa yake” Nanah ta fada tana murmushi

“Tabdi jam, Wlh na ciki na ciki asalima dariya yake mana in ana mana fada” Maijidda ke magana tana hararan Nanah

“Hmmm Ku barta, ni na ganota ai ba kuga yanda take acting a gaban shi bane” Zahrau ke tsokanarta. “Aa fa Zahra banda sharri” Nanah ta fada tana murmushin da daga gani kasan har zuciya ne.

  Yau aka shirya kai kayan lefe Kaduna gidan su farida. Anty Zainab, Anty Rukayya, Ammah da wasu yan’uwa ne suka tafi kadunan.

  An karbe su hannu bibiyu cikin mutunci da kamala. Sai dai me kamar yanda Al’ada ya gada su Anty Zainab ne suka mike domin fara bude akwatunan lefen. Kanwar Dad ce ta katse su da fadin “A’a ba sai kun bude ba ma, Baban  Faridan ma ya bada Sakon yana so an daga bikin don kawai shirye shiryen da ba a karasa ba.

Wai tashin hankali ba a sa mishi rana ba su Ammah kadai ba har mahaifiyar Farida sai da ta Shiga firgici. ” Nace ba mu gane ba dai naga kaman abinda kike fada ba maganar mu bace” Anty Rukayya ce tayi karfin halin maganan.

“Ni dai yar sako ce” Matar ta fada hade da juya Kai.

Yan kawo lefen duka jikin su yayi sanyi, shakka babu sun San akwai makarkashiya a abin.

Mahaifiyar Farida ko in ranta yayi dubu ya baci, ba tun yau ba dangin mijinta ke mata irin abubuwan nan amma yau sun kai ta makura. Sun dauka kudi shine rayuwa shi yasa duk abinda Dan’uwan nasu ya fada to daidai ne. Bakaramin kunyata ta suka aka yi ba ko dan yan’uwan ta da suka zo amsan lefen kuma  tabbacin ya San ba za ta taba amincewa ba shiyasa bai yi shawara da ita ba, yanzu haka wani mai kudi ya samo.

“Ku tashi mu tafi ko” Ammah ta fada saboda ita ba ta ga amfanin zaman ba.

“To sai anjiman Ku, mun kuma gode da irin wannan karrama war” Anty Zainab ta fada cikin habaici

Hararta Ammah ta yi sannan ta mata Alaman ta zo ta wuce.

“Ai daman kun da akwatinan kawai” wannan karan ma matar ce ta kara maganan.

Tsabagen kunya mahaifiyar faridan kasa magana tayi, kuma abin haushin wa’inda su ka girmeta na wurin amma ko a jikinsu.

“Haba ke ko, auren yarki fa suka zo nema ai da mutunci” Daya daga cikin dangin Maman ta fada a hasale

“Ai daya ke su  ma ba zasu rasa Namiji kuma kayi ayi maka ne abin” Anty Rukayya ce ke magna an cikin zafi. Sannan Anty Zainab ta kara da cewa “kuma mata nawa ne a gari”

Abin dai fada koma musu sai da mahaifiyar faridan da dangin ta suka basu hakuri sannan fa Ammah ta sa su suka kwaso akwatunan su ka wuce.Birnin  Zazzau+

Daga Abbah, Baffah har Mami ba Wanda ranshi bai yi mugun baci jin irin cin mutuncin da aka musu.

  Ammah ta so boye zancen ta fada musu zancen daga bikin da suka nema kawai amma kafin ta ce uffan ma Anty Zainab ta sanar musu duk abinda ya faru ba abinda ta rage.

  A zuciye Abbah ya nemi a hada mi shi family meeting har ko da Aliyun da tun da ya ga bikin ya karaso ya ke Zaria da Aminin shi Umar.

  Cikin mintuna kalilan aka hadu gaba daya, haka kawai Aliyun gaban shi ke fadi yana jin kaman zaman Dan shi aka yi. Baffah ne ya katse mai tunanin na shi “Kai Aliyu gidan kanana nan mutane kaje neman aure ne, ba kayi bincike ba halan”

  Das das gaban shi ke fadi “Baffah lafiya me ya faru ne?”

“Me ya faru kake tambayan mutane, sakarkaru zaka mai damu ma kenan” A hassalce Abbah ke magana Dan lamarin ba karamin bata mi shi rai yayi ba.

Mami ce ta kalleshi sai keta zufa ya ke “Haba Aliyu da hankalin ka da Tunaninka, ko an gaya maka saboda Soyayya kadai ake aure” Umar da ke zaune kusa dashi kanshi a kasa ta cigaba wa magana “Kai kuma Umar kana ina ya je irin wannan gidan neman aure”

A hankali ya amsa mata “Mami a iya sanin da mu ka wa Farida mace kamilaliyya mai addini sai dai kuma in akwai boyayyen abu wanda Allah bai bamu ikon sanin shi ba” Kusancin shi da Aliyu ne tun suna kanana ya sa suka dauke shi tamkar Dan gidan haka kuma ko abu ya taso kan Aliyun to wurin shi suke samun Karin bayani.

“Kuna da labarin neman daga auren da shi mahaifin faridan yayi” Baffah ya fada yana kallon su dukansu biyun.

A firgice duk suka dago su ka kalli Baffahn gani suke kaman kunnuwan nasu basu jiye musu da kyau ba.

“Ba daku ake magana bane wai” Abbah ya fada yana musu kallon sama da kasa.

“Aa wlh Abbah ko kadan ba mu da masaniya a kai hasalima yanzu naji daga wurin ku” Aliyu ya amsa mai cike da girmamawa.

   Mami ce ta karbe zancen

“To bayan Zancen daga auren ma, har da rashin mutunci aka zabga wa iyayenka da yayyinka ga Zainab da Ammah nan duk a gaban su aka yi komai”

Inalilahi Wa’ina’ilaihi raji’un kawai Aliyu ya ke ambato a cikin zuciya domin labarin ba karamin gigita shi yayi ba.

“Ba akanka muka fara aurar da Ya’ya’ ba haka kuma ba akan ka zamu bari ba. Ga Muhammad ga Zainab ba tarzoman da ya taso a nasu sai naka?” Abbah ke maganan yana girgiza kai.

“Don haka ba zamu daga aure ba saura sati biyu biki, Don haka kaje ka nemo matan da zan aura maka aure da ita zuwa wannan lokacin ko kuma in zaba maka duk wacce naga dama”

  Da sauri ya dago kanshi yana kallon Abbah, da kyar ya iya bude bakin shi domin magana “Abbah ina zan samo mata a kwana Goma Sha biyar?”

“Wannan ya rage ruwanka kuma, tashi ku bamu wuri.”

  Sadaf sadaf su ka tashi su ka bar falon. Tun daga lokacin Aliyu ya rasa natsuwan Dan ma Umar na tare dashi, Ya San halin Abbah mutum ne mai zuciya kuma baya magana biyu, tunda har ya furta a gaban kowa to ba makawa ya San sai yayi abinda ya fada din. Tsabagen takaici ma kasa kiran Faridan yayi domin jin ainihin abinda ke faruwa sai Umar ne ya kira ta.

                          Kaduna

  Kwance take a rigingine tana kallon silin a zahiri amma zuciya da ruhinta tuni suka cika da fargaba hade da Shiga matsanaiciyar damuwa ganin abun ta ke kamar a mafarki wai Dad dinta ya raba ta Aliyu a bisa wani dalili nashi Wanda har yanzu ba Wanda ya Sani daga ita har mom. Ba abinda ke kara tada mata hankali sai irin abinda taji ance kanwar Dad ta wa yan’uwan Aliyun, Tana Son Aliyu Soyayya ba na wasa ba bata San da wani baki zata iya bashi hakuri balle kuma ta daga ido ta kalle shi. A takaice dai ranar wuni tayi tana kuka da kyar mom ta rarrashe ta.

  Sau biyu wayar nata na ringing amma ba ta ma yi attempting duba wa balle ta dauka. A karo na Uku wayan nata ta ya kara daukan ruri, sai lokacin ta dauka wayan ganin Umar ne ya sa fargaban ta ta ke ji karuwa, sai da tayi bismillah kafin ta dauka game da yin sallama.

“Wa’alaiki Salam Sister hope dai kina lfy”

A hankali ta bude bakinta “lafiya brother” kawai ta iya cewa tayi shiru

“Sister mun ji abinda ke faruwa daga shine na kira inji me ye ainihin abinda ke faruwan”

“Wlh brother in nace maka ga abinda ke faruwa nayi karya, Dad in dai ya birkice ya ki zancen mun rasa gane kanshi gaba daya wlh. Dan Allah ka ba mine hakurin abinda aka wa su Anty Zainab wlh ba laifina bane and mom ta wa Wani Aminin Dad inma magana in Sha Allah komai zai dai dai ta.”

“Ba wani abu Sister just keep praying, Allah ya zaba mana abinda ya fi alkhairi”

“Ameen brother mine in fa”

“He is frustrated call him later”

“Shknn, Dan Allah ka bashi hakuri”

“Karki damu, kinsan halin mutumin naki da ya sauko shi da kanshi ma zai neme ki”

“Tam brother nagode, sai anjima ko”

 

                           Zaria

  Zuwa yanzu gaba daya gidan sun samu labarin abinda ya faru. Sai dai har yanzu Abbah yana nan kan bakanshi na ba zai daga auren ba. Tausayin Aliyun ya sa Baffah da Babban Yaya su ka yi tattaki har Kaduna wurin mahaifin Farida…

Yan  matan gidan ne zaune a falon suna tattauna abinda ya farun, duk rashin jituwan su da yayannasu bai hana su jin bakin cikin abinda ya faru ba. Maijidda ce ta kalli Ummi da ke ta fama danna waya tana murmushi “Halan da likita kike chatting, wannan  murmushin ba haka nan kawai ba” Ummiyn ce ta amsa ma ta Dan da ma ta San ba kyaleta za tai ba “Ya son ranki, Wani abin ma sai Next Year Officially Mrs Kabir Saraki Kanon dabo za ta yi diba” nuna kanta tayi tana blushing. “Ehmm fa Ummiy abi dai da Addu’a ga biki saura 2 weeks da kwanaki ance an fasa balle ke da ya rage kusan wata Tara” Nanah ke maganan tana hararta. Kaman jiran ta take ta gama maganan ta karbe da fadin “Ehm ehm dai Nana Aisha bari wannan maganan, shima Wanda kike maganan ai mai damu yayi low class to ga yan high class nan sun Nuna mi shi nasu halin though na ji wai yarinyar na son shi babanta ya kawo matsalan still na ji mai haushi kinsan wai ance hannunka ba zai taba rubewa ka cire ka yar ba to ya zamuyi tun da Allah ya hada mu da iri”  “ke dai bari” Maijidda ta fada hade da mika wa Ummiy hannu suka tafa. Nanah kallo ta ke bin su dashi cike da mamaki in all her life bata taba ganin masu kushe yan’uwan su irin su ba “nikam Kuna bani mamaki gsky abin na Ku ma na lura kara yawa yake”.  ” baki San waye mutumin nan ba” a tare su ka fada in aka cire Zahrau da ke gefe tana saurarensu. Itan daman ba mai yawan surutu bace sai kuma abin ya kara hadewa da abinda ya faru da ita month back.December  2016+

  Abbah ne ke magana rai a bace, bai taba jin an mi shi raini wayau na karshe ba irin yau, an mai da shi karamin Mutum mara kima da daraja duk a sanadiyar Neman aure, kaman an rasa diyar aure a duniya sai yar wadanda ba su San kima, mutunci da darajan dan Adam ba.

  Zuwan Baffah da Babban Yaya Kaduna kiri kiri Dad ya nuna ma su ba zai bada diyar shi ba in har basu daga auren ba, abinda ke basu bai wuce ganin Dad din ba talaka bane balle a daga mishi kafa, yau aka ce za a aurar da diyar shi zai iya mata komai a ranar kuma bana kushewa. Take taken shi suka gano inda ya dosa. Ba karamin fusata su kayi ba sai dai inda abin ya zo da sauki daga Baffahn har Babban Yaya duk masu hakuri aka tara.

  Abin duniya suk sun taru sun ma Abbah zafi ta ya zai fara kallon duk dimbin mutanen da ya gayyata ace an fasa aure, shi za a kunyata a idon duniya kan abun duniyan da za a barta. Kafa ya karkadawa ya na Neman mafita sai dai ya rasa ta ina zai fara ma.

  Lura da tashin hankalin da Baffah ya lura dan’uwan shi ya Shiga ba karamin damunshi yayi ba. Damuwar shi tashi ce shakka bbu. Murmushi yayi ganin Alamun mafitan da ya samo musu zata iya fisshe su.

“Abbah ga shawara sai dai kafin mu yanketa zan so a kira Aliyun mu tambaye shi ko akwai wacce ya samo a bisa sharrudan da ka sa mai”

“Baffah kenan ka fada min shawaran, ina zai samo mata cikin yan kwanakin nan na sa masa sharuddan ne saboda lokacin ina tunanin akwai hope in gyaruwan Al’amarin”

“To shknn, me zai hana kawai mu hada su da Fatima tunda a yanzu haka ita kadai ce muke da ikon aurarwa”

Murmushin da bai San lokacin da ya fito ba Abbah yayi, ji yayi sakayau damuwar shi ta kau “Alhamdulilah Gsky kayi tunani mai kyau, Allah ya sa alkhairi zamu kulla”

Ghen Ghen yau ake yinta.

••••••••••

   Mami shiru tayi tana sauraren Abbah inda yake labarta mata hukunci da suka yanke shida dan’uwan na shi. Sai da ya kai aya sannan ta dube shi “haba Abbah Aliyu fa da yan matan gidan nan ko kadan ba jituwa su ke ba Dan in za a daka ta tasu cewa suke ya tsane su, anya ba ka ganin da matsala a hada su da Zahrau, bama shi yace yana so ba.”

  Murmushi mai sauti Abbahn yayi sannan ya ce “Mami kenan ina tsangwa man da ya musu kan karatu ne kafin yaran naki su yi hankalin Kansu, ina da yakinin Aliyu zai kulan min da Fatima in Sha Allah, ke dai kawai kuyi addu’an hakan alkhairi ne”

“Shikenan Abbah tun da kace haka Alkhairi ai kullum shi muke nema” Ba wai dan ranta ya so ta fadi hakan sanin cewa ba abinda zai sa Abbah ya canja ra’ayin shi.

  A bangaren Ammah ko da aka fada mata fatan alkhairi ta wa abun domin ita dai bata da haufi akan Aliyu mutum ne nagarttace gashi kuma tuwo na maina za ayi.

  Babban Yaya ma yayi Na’am da abin Wanda haka yake wurin Anty Zainab da Anty Rukayya ma. A cewar su Aliyu zai kula musu da Zahrau ko shakka babu. Ni dai nace anya kuwa?

••••••••••••••

   Zaune ta ke tana karanta English Novel a wattpad, kwannan duk shi ke debe mata kewa sai ko karatun da ta kanyi a gidan cause tunda aka koma school day take yi bata yadda ta koma school din ba ta kafe akan sai January bayan mid semester.

  Shahida tayi Sallama sannan ta sanar mata da Abbah na nemanta a Babban falo. Haka kurum taji gabanta ya fadi “lafiya Abbah ke nema na” ta tambayi kanta, tunawa da tayi ba kyau bad thought ya sa tayi saurin kauda duk wani tunani da ke ranta ta dauki gyalenta ta yafa sannan ta bi hanya Babban falon domin amsa kiran iyayenta.

  Gab da zata karasa falon ta hango Aliyu da Abokin sa Umar sun fito daga falon. Rashin a hade yake kaman wani mayunwacin zaki, haka ba wani Sabon abu bane a wurin ta, Sunkuyar da kanta tayi sai da ta zo gab dasu sannan ta dube su ta kasan ido. A hankali ta furta “INA wuninki”

“Lafiya kalau Malama Zahra” Umar ya amsa, Aliyu kam harara ya bita dashi. Ita kam ko a jikin ta wai an tsikari kakkausa. Gab da za ta Shiga falon ta ji Umar na ce mishi “Bawan Allah ba fa ita ta maka laifin ba da kake nema ka huce akanta”

  Sallama tayi suka amsa Mata, kaman yanda ta zata su biyu ne a falon. Zama tayi ta gaida Abbah sannan ta juya ta gaida Baffah.

“Fatima ya makaranta?” Baffah ya tambayeta

“Lafiya kalau” ta amsa

“Ma Sha Allah, Allah ya bada sa’a”

Kanta a kasa ta amsa da Ameen “ki bamu aron hankalinki nan Abbah yi mata bayani”

Gyaran Murya Abbahn yayi sannan ya dube ta “Fatima natsu ki saurare ni, mun yanke hukunci akan ki Wanda mu ke fatan zaki mana biyayya”

A hankali ta furta “In Sha Allah Abbah”

“Mun hada ki Aure da Yayanki Aliyu nan da sati biyu…” Dif taji gabanta ya fara dukan Uku uku , A firgice ta dago tana kallon Abbahn, gani ta ke kaman kunenta ba su ji da kyau, ko dai mafarki take aure ita? Uncle Aliy? How can that even be possible kuma ma wai in 2 weeks time. Maganganu taji Abbah da Baffan nayi Wanda yayi kama da nasiha sai dai ita ko fuskanta ba tayi. “Ta shi kije shikenan”

Da sauri ta tashi ta nufi side in Mami dan ita zata tabbatar mata da abinda kunnenta yaji.

  A falo ta iske Mamin na kallo, jikinta ta fada sannan ta saki wani irin razannen kuka da ya rikita ita kanta Mamin. Dago tayi tana lallashin ta cause ta gane Zahrau n taji maganan auren nata ne “Mami Dan Allah kice min su Abbah wasa suke” Maganar ne ya katse saboda sheshekar kukan da take yi.

Deedat da Hamza ne suka shigo falon suka iske su a haka.

Taruwa sukayi su kayi suna bata baki game da yi mata nasiha abinda basu gane ba binsu kawai take da kallo ba wai tana fahimttan abinda su ke fada ba Tana Neman yiwuwar abin ne dai dai ko ta INA bata gani ba. Shi kanshi Hamza sai da ya jinjina abin cause kusan a gaban shi komai ke faruwa.

A ranar da labarin ya iske Maijidda lokacin ta shirya ita da Nanah suka wa Zaria tsunke saukin abin ma an kusa mid semester break. Ummiy ma Dan dare yayi ne ta Bari washegari tayi asubanci saboda ba zasu iya barin Zahrau ita kadai cikin situation in ba a cewar su they will did everything possible su ga auren bai yiwu ba.1

Yau ake yinta…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *