KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 6 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Weekend ne na karshen month kuma karshen shekara, kaman yanda su saba duk karshen shekara su ke meeting a family house insu na Unguwar Alkali cikin garin Zaria. Yan uwansu kala kala na cikin Nigeria da wadanda su ke zama abroad ma gaba daya suna haduwa a cikin wannan rana.+
Tun ranar Alhamis su ka tafi Zaria har Anty zee da ke kano ma a ranar ta iso uncle Aliy ne kadai bai zo a cewar sa aiki ne ba zai bar shi amma duk da hakan sai da Abbah ya ce mishi lallai lallai dole ne ya baro Abuja ko Saturday ne tunda ranar Sunday za a gabatar da taron. Hakan ba karamin dadi yayi ma mutanen shi a cewar su saci Karen su bbu babbaka.
Taro yayi taro in kaga mutane sai ka dauka gaba daya jama’an Zaria ne su ka taru a wurin. A nan ake sanin yan uwa yawancin musamman matayen da aka auro kafin lokacin taron nasu da sai mai tsawon rai ne zai gani. Bayan nasihohi da fadakarwa da aka yi da kuma tarihi kala kala tare da ma wadanda su ka rasu addu’a kusan na awawowi dayawa sannan aka yi addu’a. Lokaci ne na ganawa da ciye ciyen da ba irin abinci da za ka nema ka rasa a wurin.
“Kai amma wancan Brother inku ya hadu just my dream guy” Wata cousin insu Khadija ta fada tana pointing direction in da Aliyu ya ke, da yake mutane dayawa ya sa ba Wanda zai iya cewa shi ta ke nunawa. Kallon ta suka yi a tare dukkansu ukun sannan su ka juya kai “sai dai it seems like kaman bai magana gashi ni kuma am the noisy type ya za ayi kenan”
“To fah miss dream guy har kin fara hango Ku tare” Wata cousin in ta su ta fada cikin tsokana.
“In dai Yaya Aliyu ne kya yi ki gaji don ko kallo ba ki ishe shi ba I doubt in yana da budurwa, miskilancin shi yayi yawa” Nafisa ta yi magana da ke ita suna zumunci Sosai da gidan su Zahrau.
“Ehm ehm wlh An gaya miki miskilancin namiji na hana shi love ne? Bar su kawai inda kika bar su”
Ummiy da Maijidderh a tare su ka tashi “I don’t belong here kunji bari in shiga ciki” Ummiy ta fada tana tafiya bin bayan ta Maijidderh ta yi
“Are you jealous Dan ana son yayanku” Khadeeja ta fada tana musu dariya.
Zahrau kam hankalin ta na ce wurin su Rukayya suna lbrn Novels daman inda tafi karfi kenan.
Ko da za su tafi da yamma hamza ne ya zo ya Kira ta su ka wuce.
*** *** ***
Manya makaranta, Senior of the seniors and the juniors kuma masu makarantar da kanta wato Yan SS3. Zaune su ke a hostel yayin da su ka tattara yan makarantar gaba daya su ka kora prep in ka cire kalilan da ke class domin ra’ayin Kansu sai kuma yan SS2 da su ka zame musu karfen kafa domin ba daman Koran su saboda Immediate bullying in da ba ayi a girl section.
Wanka ta fito daure da zani da dankwalin shi iri daya bayan ta gama shiryawa ne ta daukko dimbin notes in da ke gaban ta ko ta ragewa kanta aiki, hakanan ta ji ba ta son zuwa class din ai ko ta samu yan uwa zama hira dayawa duk dai SS3 ke fada musu karya, inda Allah ya taimake su ba malamin da ya zo kora ranar ba ko karamin sa’an hakan su ka ci ba. “Zahrau na Abdulrahman, Abdulrahman na Zahrau” Asma’u ta fada cike da tsokana. Ko kadan ba ta iya holding blush inta matukar an ambato sunan shi, tafiya ta ke taji ance Abdulrahman sai ta waiga ta ga waye ne ballan tana ta San da Abdoulh in nata ake. Har cikin zuciyan ta ta ke ji dadin sunan ko kadan farin cikin da ke kwance a fuskanta bai boye ba duk yanda ya so boyewan “oh ni Zahra wai wani irin So kike wa bawan Allahn nan, ko dai za a daura ne ranar da aka yi grad kawai ki tare” Asiya ta fada “Wlh ni ban ki hakan ba, just wait to fall in love you will know how it feels” ta fada tana lumshe ido. “Ehm ehm anya Zahra, fada min me ya ke fada miki? Wasu kalamai ne su ka ruda ki haka” wata ta kara tmby. Ita dai shiru ta yi tana jin su. Sunga laifin ta? Abdulrahman is the perfect definition in Husband material da duk wace mace za ta so, Tattali, kulawa, kyauta da kuma nunawa mace so ba Wanda bai iya ba kalan su ne in suka so yaudara za suyi saurin yin nasara.
Wayan da su kayi jiya dare ne ta tuno. “Mera princess” ya fada bayan sun gaisa. “Naam jaanam” ta amsa su a dole indiyawa. “Ina So in ganki Soon”, ” ba kun kusa graduation ba ina last year ka ke”
“Ehm Amma kinsan Allah ji na ke kaman in jawo lokaci Wlh yayi min nisa”
“No jaanam kar ka damu Zahrau will always be waiting for you, ko yaushe ka dawo ma am already yours”
“Shknn princess Allah da na dawo zan turo gidanku yanda da na samu aiki sai ayi ko? Ko ya kika gani”
Wani farin ciki ne taji ya mamaye zuciyan ta jin abinda ya ambata.
“Amma su Ummiy da Maijidderh ba Wanda ya shirya and tare mu ka taso”
“No princess don’t start it Allah I can’t risk loosing you gwara tun ina da chance”
“Are you doubting me?”
“No just ban taking chances ne, ki kwanta pls kar kije kina bacci a Class”
“Ehmm Gud nyt”
“Thank you, luv yhu”
“Bye” ta fada yayi saurin katse ta “tsaya ma naki wayon baki taba cewa kina so na ba”
“Kai Jaanam wannan ma ai sharri ne”
“Let’s just balance the equation”
“Zahrauuuuuu INA son ki” ya fada hade da Jan sunan ta, INA aljanna a sa Zahra, ji take ta fi kowa Sa’a a duniya. “Kinji” ya kara fada a hankali da voice inshi da ke mugun affecting inta. “Naji”
“To baki ce komai, I love you”
“I love you too” ta fada hade da saurin katse wayan saboda da kunya. A daya bangaren Abdulrahman smiling yayi yana kallon wayan cike da farin ciki, kunyar ta na matukar burge shi. Fake yayi wa screen in wayan sannan ya rungume a kirjin shi. Faroukh da ke gefen shi ne ya kwashe da dariya “man bi a hankali electronic ke hannun ka ba Zahrau ba Mr lover boy” shi dai lumshe idon shi yayi yanda ta furta I love you too na kara sauka cikin kunnen shi.
Hutun nan ba su je Kaduna ba saboda Mami da Ammah sun yi kememe akan duk Hutu can su ke zuwa su ka hana su zuwa ba Wai dan sun so ba suka hakura Sai Nanah ce da su khalipha su ka zo Zaria hutun.
Maijidderh ko Ibrahim ne a ranta shi yasa duk tafi su haushin rashin zuwa Kadunan, ga abinda ya ce zai fada mata na taimakon da zata mishi kullum yana yawo a ranta, kasa jurewa tayi ta kira khalipha a sirrance tana tmbyn shi. Abinda ya sanar mata ya matukar kidimata. Yana nan amma yace yana son komawa garinsu nan da wata Uku, me ye sa zai bar aikin da ita a ganin ta da wuya ya samu aikin da za a biya shi irin shi ba saboda ba makaranta yayi ba, to wai ma meye sa ta damu da lamarin shi ne? Ta tambayi kan ta, taimako mana wani zuciyan ya bata amsa.
Sai ana sati daya su koma school ne Mami ta ce suje su musu kwana biyu, ba karamin farin ciki su ka yi ba ko Dan yanda su kayi missing Antyn nasu, sun saba da ita sosai Dan ko wani abu ya taso to da ita ake shawara.
Ita kanta tayi murnar ganin su dan tayi kewan su, bayan sun Dan huta ne ko abinci ba su ci ba Maijidderh ta faki idon su ta fita dan ba ta so su mata tsiya. Wurin mai gadi ta je ta tmby shi Ibrahim din “ya dan fita wlh amma INA ga ba nisa yayi ba, kina son wani abu ne” maigadin ya bukata. Girgiza kai tayi tace “Aa kawai INA son ma sa magana ne” tana cikin magana sai gashi yayi sallama ya shigo gidan “kinga gashi nan ma” Maigadin ya fada.
Kallon ta yayi sannan ya Dan saki murmushi “Hauwa ashe zaku zo naga har Hutu ya kare na dauko sai wani hutun ai”. Shi ma yana kewan ta kenan? Wani sashe na zuciyan ta ya fada tayi saurin kauda zancen ” Eh wlh ba mu samu zuwa bane, mun same Ku lfy?”
“Lfy Kalau, da ko ba za ki same ni ba”
“Khalipha ya ce min kace za ka bar aiki Why”
“Family na suna bukata na kinga ko dole in koma”
“Hakane amma kana da wani aiki a can ne?”
“Kala kala ma a can kauye ai ba a rasa abin yi”
“Hakane Allah ya taimaka”
Shiru su kayi yana kallon ta ita ma kallon na shi ta ke sai dai a sace, lura yayi da magana a bakin ta “fada mana” ya ce mata. Murmushi tayi tana mamakin yanda a kayi ya gano ta “daman so nake inji taimakon da kace kana so in maka ko ka fasa”
“Aa INA bukata ai, Yaushe zaku tafi”
“Jibi”. ” Zan neme ki gobe” ya fada hade da shiga dakin da yake mallakin shi a yanzu.
Cikin gida ta koma ta iske duk sun shirya cin abinci ita ake jira “Halan wurin mutuminki kika je koh” Anty Rukayya ta tmby bayan ta zauna.
“Naje mun gaisa ne” ta fada cike da kunya.
“Ni dai Maijidderh na sa ma wannan zumuncin alamar tambaya” Nanah ta fada cikin tsokana.
“Hauwa’un kauye ba” Ummiy ta fada
“Aa ba a mutunci balle Ibrahim ma bai da matsala gashi bai da hayaniya banji dadin barin aikin da zai yi ba” Anty Rukayya ta fada
“Daman Anty ai ba sa zama kila aure za su mishi tunda kika ga haka” Zahrau ta fada.
Wani harara Maijidderh ta bi ta dashi “wai Zahra kinga hararan da kika sha kuwa” Nanah ta fada
“Baki ga na kama baki na ba, Afuwan Maijidderh na tuba”
Dariya su ka kwashe da shi dukkansu ita dai Anty Rukayya girgiza kai tayi tace “Allah ya shiryeku”
Da yammaci Kowa na harkan gaban shi, kokarin daura girkin dare su ke a kitchen sai musun abinda za a dafa su ke wannan ta ce tuwo wata tace pasta kowa dai da ra’ayin shi. Khalipha na ya leko kitchen ya gan su “to kai kuma me ya kawo ka nan sarkin iyayi” Nanah ke magana tana hararan shi wai Dan yaji tsoro.
Cewa yayi “Sorry Anty Nanah ba gunki nazo ba” Da ke yaro ne mai wayau straight gun Maijidderh yaje ya jawo hannun ta yana fadin “Favorite Anty zo kije”
Ummiy ce ta harare shi “ji yaro da gulma za ka yi bayani” ita dai Zahrau faman gyara kayan miya take daman ba wai ta cika magana bane.
Har gaban Ibrahim ya ja hannun ta ya kai ta “Uncle IB gata toh”
“Thank you khalee boy ga chocolate ko”
“Thank you Uncle” rugawa yayi cikin gida yana murnar chocolate in da aka bashi.
Kallon sha’awa Ibrahim ya bi shi dashi har ya shiga parlour. “Haka kake son yara” Maijidderh ke tmby.
“Hauwa kenan ban ki inyi aure yau ba in zan samu cute babes”
“Yara ai akwai shiga rai amma lokaci ne”
“Haka ne gobe za Ku tafin”
“Ehmm za mu koma schl akwai shirye shiryen da zamu yi”
“Allah taimaka”
“Ameen”
“Maganan mu Allah ya sa zaki iya cika Alkawari”
“In sha Allah”
“Yauwa toh, Hauwa’u”
“Na’am” ta fada tana Dan Satan kallon shi.
“Zan so ki bani aron hankali da natsuwar ki kuma zan so ki ma abinda nazo da shi fahimta mai kyau.”
Shiru tayi tana mamakin abinda ya ke nufi da har ya ke wadannan maganganun “Hauwa Allah ne ya kadarta min ba ni na daura wa kaina, ban kuma San ya zaki dauki zance na Amma still zan fada miki Ina sonki” saurin dagowa tayi tana kallon shi “Nayi karfin hali ko? Pls am sorry it just happen” Daman Ibrahim zai iya speaking fluent English haka? Kai anya bai da wani boyayyen sirri?
“Nagode” ta tsinci kanta da fada “Amma ni ban San me zance maka yanzu haka ba kawai dai nasan ina son taimakon ka”
“Na Sani, taimakon da kika min ne ya fara Jan ra’ayina gare ki at your young age kin burge ni, amma bara in tmby ki, ace ina da rufin asirin da zan iya ciyar da ke in kuma kula da ke zaki iya zama dani?”
“Me zai hana?” Ta fada kanta a kasa
“Zan tafi in nemo sana’ar da zan iya rike ki Hauwa za ki iya aure na”
Kai ta gyade mi shi hade da rufa fuska alamun kunya. “Alhamdulilah I S A bazan baki kunya ba, ki ban numban da zan same ki, zan neme ki in na gama settling”
Numban ta rubuta mishi sannan su kayi sallama, ba ta ce tana son shi ba Amman ya ga alaman hakan a tattare da ita, sai godiyan Allah ya gama mission a dai dai.
*** *** ***
April 2015
A ranar su ka gama jarabawar su ta WAEC bayan extension da yan makaranta su ka bar su suna yi, a washegari su ke sa ran tafiya gida Hutu duk da dai PC sai kokarin ja musu rai yake yi.
Da Yamma ya mu su announcing tafiya gidan tuni su ka hau ihun murna, ga Zahrau murnar ta biyu saboda Satin Abdulrahman biyu kenan a cikin Nigeria duk sun kosa su hadu, bayan magriba ta kira shi ta sanar mi shi dawo wan ta Zaria a washegari, yayi murna kwarai coz ya kosa ya sa ta a idanun, princess inshi ta canja? Though koya ta ke itan dai kawai ya ke so,” jibi ni kuma in sha Allahu zan shigo Zaria” ya fada mata abinda ya sa ma ba zai zo a washegarin ba saboda ya bar ta ta huta.
A gajiye ta isa Zaria ta iske su Ummiy da Maijidderh har sun dawo nan fa su hau murnar ganin juna, Yan Uku kenan.
Da yammacin ranar su kayi Waya da jaanam din ta ya kara tabbatar mata da zuwan na shi a washegari. Da dokin murna ta yi hanyar dakin Deedat “Zahrau yan SS3 wannan farin ciki fa?”
“Ya Deedat Abdulrahman zai zo gobe” sai da ta fada tayi realizing me ta aika ta, Deedat bai San tsakanin su ba “Ya fada min, me ya faru?” Bbu tace sannan ta yi saurin barin dakin “okay in tayi tsami naji” ya fada da karfi ta yanda zai iya jin ta.
Da dare Abdulrahman ya kara kiran ta hakanan ta ji gaban ta ya fadi ba Dan komai ba sai Dan ganin sau daya su ke waya dashi a rana, saboda fahimtar da ya mata bata cika son magana bane? Ko Dan shi ma ba mai son maganan bane?.
Sun ko dade suna wayan, yana kara tabbatar da irin son da ya ke mata ita ma sai ta tsinci kanta da bayyana mishi sirrin zuciyan ta, duk ko kunyan ta yau ta kauda shi ko me ye sa hakan? Yanayin ne kawai ya zo mata a haka ta rasa dalili.
Haka da asuba shi ya tashe ta Sallah sannan karfe Taran safe su ka kara waya yace mata by 11 ya ke son barin KD. 11 din ya kira ta akan Baban shi ya sa shi wani aiki zai yi kokarin gama zuwa 2 ya taso bayan da ba ta yi ba akan ya bari sai gobe ya ki dalilin shi kuwa gani ya ke in bai sa ta a ido ba a ranar komai zai iya faruwa.
Kitchen su ka shiga ita da Yan uwanta su ka hada mai abinci na gani na fada duk Wanda ya tmby su sai su ce baki za su yi. Hamza daya dawo daga Unimaid yana 100 level kadai su ka fada ma gskyn abinda ke faruwa ai ko sun sha tsiya.
2:00 pm in ko ya taso da za su zo da Faroukh amma ya bar shi ya kara sa musu aikin, gudu ya ke sosai a hanya burin shi ya isa da wuri ya samu ishashen lokacin zama da Zahrau saboda bayan isha’i zai dawo KD.
Cikin mintuna kalilan ya isa jaji, wani irin kulle wa ya ji cikin shi nayi sauran kadan kan motan ya kubce mishi yayi saurin lallabawa ya koma gefe, kusan shekara kenan ya na fama da ciwon cikin nan duk ya taso ba karamin wahala ya ke. Gadan gadan ciwon ya taso mai rike wurin yayi yana mai kiran sunan Allah.
Jin shiru ya sa Zahrau ta kira numban shi kusan sau biyar amma bai daga ba, hankalin ta ne ya tashi da sauri ta lalubo numban Faroukh ta kira.
Bayan sun gaisa ne ta ke fada mishi ta kira Abdoulh bai dauka ba ce mata yayi bara shi ma ya neme shi yaji.
Kusan 2 hours ba kiran Abdoulh kuma ba na Faroukh gaban ta sai dukan Uku Uku ya ke.
A bangaren Abdulrahman kuwa ya kai kololuwa wurin galabaita tun yana iya magana har ya kasa. Ganin mota ya Dade a wurin ya sa mutane su ka yanke shawaran su duba su ga lfy. Suna bude motan su ka ganshi ya saki wani numfashi mai karfi sannan ya fado kasa, caa su kayi akan shi wani daga ciki ya taba shi ya ji ba ya numfashi, wayan shi su ka dauka su ka kira numban Faroukh da ya mai missed call last domin sanar da shi halin da ake ciki.
Mintuna Ashirin su kai Faroukh da Wani yayan su jaji a rude su ka sa shi a mota akan za su wuce dashi asibiti, dayawa daga cikin mutanen kyale su su kayi kawai amma sun San rai ya riga yayi halin sa.
Wannan karan Sumayya ta ke ta dialling don har ta gaji da kiran Abdulrahman da Faroukh dukkansu ba sa picking sai dai Sumayyan ba ta dauka ba, kara kiran dai tayi ganin shi ne dai mafita.
Sheshekar kukan Sumayya ne ya katse ma ta maganar da ke bakin ta. “Me ya faru” kawai ta tmby Dan ko jikin ta ya riga da ya ba ta abinda ke faruwa “Wai Ya Abdoulh ya rasu” wani irin karkarwa jikin ta ya fara yi, wayan da ke hannun ta sa kan shi ta yi a kasa kafin ita ma ta bi shi.
Sai Washegari a ka samu ta far fado already lokacin an Riga an kai Abdoulh gidan shi na gaskiya, gidan da ko ranar zuwan nashi ya ke jira Kulli nafsin za’ikatul maut, Abdoulh kam sai godiya domin yayi cikan shahada. gaba daya dakin ta bi da kallo ta tunanin me ya kawo ta asibiti, Deedat da ke gefen ta ta bi da kallo sannan abinda ya faru ya dawo ma ta “da gaske wai Abdulrahman ya rasu” ta tmby shi, gyada ma ta kai yayi kawai saboda bai ga amfanin boye ma ta abinda ta riga ta Sani ba. Gani ta ke karya kowa ke mata duka duka yaushe ya kira ta ma ace ya mutu kai ba zai yiwu ba, cikin yan awanni kalilan ace mata ya mutu ba ciwo ba komai ba kuma accident yayi ba.
Wani irin gigitancen kuka ta fara tana girgiza kan ta “wlh karya ne Dan Allah Ku ce min mafarki na ke” Mami ce ta kama ta tana rarrashin ta ga me da mata nasiha, abinda mamin ba ta Sani ba ko kadan ba ta jin ta karshe ma kara sumewan ta yi.
Da kyar likitoci su ka samu daidaituwan numfashin ta saboda shock in da ta shiga, sati biyu tana kwance a Asibiti ba ehmm ba Aa ganin ta fara warware wa Ya sa aka sallame ta ga me da daurata akan magunguna, ita dai bin su kawai ta ke Dan ji ta ke komai na duniya ya tsaya mata cak. Schl ma sai ana gobe za su fara jarabawa ta koma, sai dai komawan na ta Ma kaman taso mata da ciwon mutuwar shi yayi domin hatta kwanar ta duk sunan shi ne a jiki, yan mate insu sun tausaya ma ta sosai sanin irin soyayyan da ke tsakanin su. Jinya yau gobe sauki a haka su ka gama jarabawar da yawancin yi mata ake, haka su ka yi Grad ita dai gata nan a duniyan ne kawai ba Dan ta na fahimtan komai na ciki ba. Duk ta rame ta yi wani iri ko da su ka koma asibiti likitoci sun tabbatar da zuciyan ta na gab da buguwa saboda halin damuwan da ta kasa fita a ciki.
Sai dai Iyayen ta su ka zauna da ita musamman su ka mata nasiha mai ratsa jiki Deedat ma ya mata sannan ta fara kokarin dawo wa yanda take game da bata rabin ranar ta tana ma Abdulrahman addu’a Dan gani ta ke har karshen rayuwan ta ba za ta iya cire shi a ran ta ba.
Kallon Lafiyan ki kalau Ummiy ke bin Maijidderh da shi bayan ta gama labarta ma ta abinda ke tsakanin su da Ibrahim, sau dayawa ta sha tunanin canja numban amma in ta tuna Ibrahim din ya amsa numban ta sannan za iya kiran ta at anytime sai ta fasa hakan, tun tana sa rai har ta gaji.+
Kwatsam kiran Ibrahim ya shigo wayan Maijidderh ya na mai sanar ma ta ya gama komai na shi soon zai zo wurin ta. “Ke yanzu rayuwan da zaki zaba ma kanki kenan Maijidderh akan So?” Kallo Zahrau ta bi ta tashi tabbas Ummiy ba ta San so ba ne shiyasa ta ke fadin haka amma ita ji ta ke za ta yi abinda ya fi haka ma in dai kan soyayya ne, a kullum rashin da ta yi dawo ma ta yake sabo fil a zuciya in ta ji ana maganar Soyayya, ko kadan ba ta ga laifin Maijidderh saboda da sanar da su irin son da taji tana ma Ibrahim din, shin ma ina ruwan so da matsayi?
Anisa kanwar Khalipha ce ta tashi yau ba lafiya zazzabi ya rufe ta kirif, NNPC industrial clinic su ka nufa da Anty Rukayya sai Ummiy da Nanah su ka bar Zahrau da Maijidderh a gida da ke da rana su kaje duk likitocin Sun fita break sai doctor daya consultant ne ya zo musamman daga Aminu kano teaching hospital kuma ma sai anyi booking ake ganin shi, jikin Anisa ko yayi tsanani sai rawan dari ta ke gashi daman tana da Pneumonia sai wani nishi ta ke sama sama, Shi ko doctor din ya Dade a ciki suna magana da wani probably ba abinda ma ya shafi ciwo bane ga patients dayawa sai complain su ke tashi Ummiy ta yi ta cincibi Anisa ta yi office in doctor direct ta bude “Sorry Madam da kin Dan jira ni for some minutes zan fara kiran suna”
“Sorry doctor Alfarma nima nake nema my patients is suffering she is a young girl” ta bashi amsa kai tsaye, kallo ya bita dashi jin yanda ta ke magana kai tsaye cikin tsiwa
“Okay come in ” ya fada.
Sai da ya gama duba Anisa Sannan ya dago ya kalle ta to yan Neman Alfarma hope nima in na nema za a min? Murmushi ta mai duk tsiwan na ta sai taji ya tafi yau. Doctor Kabir Saraki, Can I have your number?
Wannan ne mafarin Alakar Ummiy da Doctor Kabir, sai ko abin nasu yazo daya domin BUK ta cika a Jamb form inta. Nanah da Maijidderh KASU sai Zahrau ABU Zaria.
“Ke ashe Ibrahim inki SSS ne” Abinda ya sauka kunnen Maijidderh kenan Anty Rukayya ke maganan, dukkan su su ka juyo suna kallon ta cike da mamaki, “Baban Khalipha ke fada min Kusan Alhaji Nakowan layin can?”
“Custom in nan Anty?” Nanah ta tmby
“Shi fa shi aka turo yin bincike akan kasuwancin shi”
“Tab to ke Anty ya aka yi kika Sani?”
“Jiya ya je office in baban khalipha ya mishi godiya, ya ce kun daidai ta haka ne?”
Hankalin ta a tashe tace “Anty ni wlh ban Sani ba sai yanzu”
“To Maijidderh ai daman is part of their job so no way zai gaya miki”.
Wuni su kayi suna mamakin lamarin kaman shirin film su ke ganin abin. Kiran shi Maijidderh ta yi tana mai complain in me yasa ya mata haka? Hakuri ya bata akan yanayin aikin nashi ne he have no choice.
Admission in su ya fito kowaccen su ta samu abinda tayi applying, sai shirin fara registration.
*2 months later*
Sun yi nisa a karatu war haka sai kokarin copping da yanayin University din, Tare su ke zaune daki daya da Fateemerh ita ma ABU in ta ke sai dai ita Biochemistry ta ke karanta wa Zahrau kuma Microbiology.
Sanye ta ke da dogon hijab inta har kasa mai hannu mai hannu, kanta a kasa ta karasa Electrical Engineering Department in da Yaya Deedat ke lecturing. Dai dai za ta shiga office in ta ci karo da maza biyu sun fito daga office in, ganin yanda su ke kallon ta ya sa tayi saurin shiga office in. ” Ya dai” Musa ya tmby Sulaiman ganin har ta rufe kofa amma bai daina kallon wurin ba. “Am in love” ya fada a hankali gami da dafe jikin bango sannan ya lumshe ido. “Hey Guy stop acting wannan ba kalan yaudarar ka ba ce , Kanwar Deedat ce fa” Wani irin ajiyar zuciya Sulaiman ya saki “Alhamdulilah abin ma zai zo da sauki kenan”
“Au har iskancin naka ya kai nan Sulaiman Kanwar Abokin ka fa ai inda kara Karen gidan siriki ma uba ne”
“Musa kenan kaman yanda ba ta ma ka kama da kalar yaudaran ba nima ba yaudarar ta zan yi ba, kyakyawan Niyya na ke dashi this time”
“Yau ka fara fada Sman? Kar ka manta …”
Dakatar da shi Sulaiman yayi “Dan Allah ya isa haka ba lallai ka yarda ba daman”
Sarai Sulaiman ya San Musan ba zai taba yadda da shi ba, kafan abokan shi na Zaria shi kadai ya San waye shi gabaki daya saboda duk kanwan ja ce, halin su daya sai dai shi MUSA a bayyane ya ke abin shi.
Deedat Sulaiman ya samu da maganar Zahrau, Kallo ya bi shi da shi daga sama har kasa yana son gano gaskiyan lamarin abinda ya fada din, ya San halin da Zahrau ta shiga ranar da aka wayi gari ba Abdulrahman ba zai so hakan ya kara faruwa ba domin ba karamin jinya su ka sha ba “Ka tabbatar da abinda kake fada? But why her?” Ya fada yana mishi kallon tuhuma. “Its just happen daga lokacin da na sa ta a idanu so pls save a friend” Dalilin da zai sa ya hana Sulaiman Hulda da Zahrau ya ke Nema sai dai ko ta ina ya bullo sai ya ga Sulaiman bai da makushi a wurin Dan a ganin shi Sulaiman ya fi shi riko da addini, duk a cikin abokanan su ba Wanda ya kai shi kokarin azumin Nafila da Salloli . lokacin su na karatu a ABU shi ke matsa mishi sai ya tashi Sallahn dare ga haddar Alkur’ani da kuma kiyaye dokokin sunnar manzo S A W. Har halaye Sulaiman halaye ne da za ayi koyi da su Unknown to him Sulaiman irin mutanen ne da ake kira Sumamman kasau macijin boye domin bai abin shi inda ya San ana ganin shi da mutunci Samun aikin shi a Abuja ya kara fidda true color in shi shi kanshi MUSA sai a nan ya gane waye Sulaiman din. Shaye Shaye, Neman mata, gidan rawa sai da yayi kaurin suna a wuraren nan hakan har ya kai shi ga shiga hanyar Smuggling, Mata kala kala ba wacce Sulaiman bai yaudara ba daga na kirki zuwa yan iskan amma fa duk abin nan the moment da aka ce ya bar Abuja zai juye kaman ba shi ba.
Gun Abbah da Baffah ya fara zuwa kafin ya gabatar da kanshi wurin ta, Daman tun asali sun San shi da Deedat kuma sun Amince da tarbiyyar shi hakan ya sa suka amshe shi hannu bi biyu amma kafin nan sai da su ka sa aka musu bincike akan shi.
A ranar da Abbah ya sanar da Zahrau anzo Neman izinin auren ta a wurin shi wuni ta yi tana kuka domin sai ranar ta kara tabbatar wa ta rasa Abdulrahman rashi na har abada. Da farko kasa sakin miki ta yi gabadaya amma ganin yanda ya ke nan da Family inta ya sa ta Dan sake mai. Hakurin shi game da addinin shi ya fara Jan ra’ayin ta akan shi. A hankali sabo ya fara shiga tsakanin su ta wannan daman yayi nasarar fara sa ma ta son shi ko da ziyaran da ya ke kawo mata inko yana Abuja har video call ya ke kiran ta tun bata sakin jikin ta har ta saba. Wa’azi sosai ya ke mata sannan shi mutum ne kwarai da ya iya tafiyar da mace ta yanda ba za ta kara kallon wani Namijin ba. Gashi da fara’a, raha da kuma saurin sabo ta haka ya siye yan gidan nasu gabadaya, lokacin da wani aiki ya kai shi kano sai da ya biya gidan Anty zee ba adadi Anty Rukayya kuwa ya sha kai mata ziyara, komai na Zahrau mai mahimmanci ne a wurin sa yanda ta fi duk matan da ya yi alaka da su mahimmancin.
*** *** ***
Bakin cikin MUSA a kullum bai wuce yanda Sulaiman ke sa mun cigaba a rayuwa ba musamman da ya ga yanda a ka amshi shi hannu bi biyu a gidan su Zahrau ya San cewa da sun San waye Sulaiman da ba su yi gigin bashi yar su ba.
Deedat ya je ya samu a office ya sanar mishi duk abinda ake ciki sai dai ko kallon arziki Deedat in bai mishi ba ya mishi tattas sannan ya kore shi daga office in. Daman tun can kyamatar shi ya ke shi kanshi Musan ya San da hakan “Good banga laifin ka ba amma you are surely gonna regret this” tsaki yayi ya cigaba da aikin da ke gaban shi hakan ya matukar kara kular da Musa fita yayi yana kwafa.Kaman yanda ta saba tafiya weekend cikin Zaria duk Friday wannan satin ba ta samu dama ba saboda test in da ta ke dashi ranar Monday gashi sai 6 na yamma su ka samu fitowa Physics practical ranar Friday din don haka a gajiye likis ta nufi North gate domin karasa wa gidan su da ke off campus su ke zama ita da Fatima ba su samu hostel ba.+
Napep ta hau ganin in tace za ta karasa a kafa ba karamin wahala za tayi ba, A shago ta tsaya ta saya ma Fatima sakon da ta ba ta, Tabbas Uncle Aliy ta gani a gaban ta bin shi ta yi da kallo shi ma itan ya ke kallo amma me? Ta bude baki za ta gaishe shi taga ya dauke kai ya karasa motan sa ya tafi, girgiza kai ta yi cike da takaici, shin wannan wani irin mutum ne da zai dauki tsanan duniya ya daura musu alhalin jinin su daya, abin har ya Kai nan kenan. A ganin su Mami da Ammah rashin jituwa ne kawai tsakanin su basu cika zama ba in yana gidan shiyasa ba su fuskanci ainihin abinda ya ke faruwa ba.
A ranar Sulaiman ya shigo Zaria jin ba ta zo gida ba yasa shi zuwa nan Samarun ganin ta.
Though a gajiye ta ke lallabawa ta yi ta fita saboda in ba ranar ba Saturday da Sunday she got a lot to cover. Yana Zaune cikin motan shi ya hango ta tafi to, dube dube ta fara yi dan ba ta ganshi ba ganin haka ya sa ya fito cikin motan, tsaf ta hango shi amma ta ki karasa wa don a ganin ta shi ya kama ta ya karaso din fahimtan da ya mata ne yasa ya karasawa “muje ko”
“Aa mu zaune a nan mana” ta nuna bencin da ke can gefen su “kaman motan zai fi nake ga”
Girgiza kan ta tayi “okay mu je din” ya fada sanin ba za ta shiga ba tunda ta ki tun farko.
“Ya hanya Gentle? Gsky kana kokarin zuwa garin nan ko gajiya ba kayi?”
“Haba Smart how do you expect me ba zan zo ba after all na ajiye ki” murmushi ta yi “To thank you amma pls a rage kar Stress ya ta damun ka”
“To ai baki Sani bah ganin ki ya na sa duk Stress in tafiya, Wai Smart yaushe zan tura gida ne am eager to have you forever” kallon ta ya ke cike da shauki ta yanda za ta iya ganin zallan soyayyan ta a cikin idanun shi ba alaman karya bare yaudara.
“Ko 100 level ai a bari in gama ko”
“Smart kenan just promise me you will be with me a cikin ko Wani hali”
“In Sha Allah Gentle”
Wayan shi ake ta kira amma yana rejecting ganin an ki daina wayan ne ya sa ya hakura ya dauka “am doing something important please zan kira ki later” ko me aka fada mishi sai ji tayi yana fadin “Allah zan kira ki trust me, OK bye” Kallon tuhuma Zahrau ta bi shi dashi sannan ta sunkuyar da kan ta kasa, Allah yayi ta da mugun kishi Mara misaltuwa hatta kawar ta tana kishin ta gan ta da sabban frnds balle kuma saurayi “Abin har ya kai da ayi a gaba na kenan” ta fada a hankali da kaji yanayin maganar ta kasan abun ya bata mata rai. “Oh no Zahrau na isa she is just a coworker akwai aikin da muke tattaunawa ne”
“Aikin ne har da dare?” Ta girgiza kai “bazan iya gasan ba sai in bar ma ta kai” da kaji muryan ta kasan kiris ya rage ta fashe da kuka
“Haba Zahrau ke Kinsan ba zan miki haka ba ko baki yarda dani bane?”
“Me yasa tun farko kaki daukan wayan?”
“Saboda gujewa irin haka”
“Gentle kenan” kawai ta fada sannan ta yi shiru.
Hakuri ya dinga ba ta yana tabbatar ma ta zargin da ta ke mishi ba haka bane
“Allah za ki sa inyi dana sanin zuwa kuma zan ga kaman next time ma in nazo similar thing zai iya faruwa”
Kallo ta bishi dashi “Saboda kasan zai iya faruwan ko”
“Ki fahimceni mana, shin Kinsan illan zargi kuwa? Bai kamata mu daura alakar mu da zargi ba Smart saboda zai zamo ba yadda tsakanin mu gaba daya kuma kinga ba amfani kenan, in har ko muna son cin ma nasara aure dole mu ture wannan mudinga wa junan mu kyakyawan zato” tuni ya cika ta da kalamai da wa’azi har ta yadda ba abinda ke tsakanin su da wacce ta kira shi ganin dare na yi ya sa ta kira Fatima su ka gaisa sannan su kayi Sallama ya tafi.
Bayan ya bar wurin ne ya kira Samira ya mata ta tas hakan yayi sanadiyar rabuwan su. Ba karamin kuluwa tayi ba ganin ba abinda ta mishi so ba ta San dalilin da zai sa ya mata haka ba. Shi ya fara sanin ta a matsayin Ya mace gabadaya ta gama saudakar mishi da kan ta da soyayyan ta gabadaya ta ya ma za ta iya kyale shi bayan shi ya bude mata idanu though bai San ta zarce idan ya ke zato ba. Kawarta leelah ta samu cike da tashin hankali nan su ka fara kula kulan yanda za su rama abinda ya ma Samiran sai dai a binciken da su kayi ne su ka gano yaudaran matan ya zama kaman sana’ar shi ne nan su ka dauki aniyar ganin karshen shi. Trap su ka mishi ya fada da leelah sai dai ita tun farko ya San idon ta a bude ya ke, Sun kai 3 months kafin su ka gama shirya planning insu sai kuma komai ke tafiyan musu yanda su kayi planning.
A ranar da aka kama shi kafin ya fita ya kira Zahrau ta Skype as usual daman system in ta na gaban ta shi ta ke jira, she is kinda obsessed with him apparently. Dariya ta fashe ta fashe dashi tana ganin face in shi akan screen in laptop in ta, he doesn’t have idea me ta ke ma dariya amma ganin yanda ta ke dariya bbu kakautawa ya ji ya burge shi, komai na Zahrau burge shi ya ke, wani murmushi ya saki saboda wani farin cikin da ya ziyarci zuciyan shi bai ta ba ganin ta tana irin dariyan ba so it memorable to him. “Haba Gentle wannan yashe hakoran fa kaga kanka kuwa?” Ta fada tana sasauta dariyan na ta. Shafa kan shi yayi sannan ya gane abinda ta ke nufi, Askin da yayi ta ke wa dariya Wanda saboda birthday in besty leelah yayi ace warta they have to look beautiful saboda su ne guest of honour “Trying to act social? To bai ma ka kyau ba ma gwara ka je kayi askin gabadaya” He feel sad the moment da tayi maganan cause da ta San dalilin da ya sa yayi askin da ba zata fada ba. Anya ya na wa Zahrau adalci kuwa? Girgiza kan shi yayi “I will change soon coz of her” ba zai iya mata karya ba so sai ya ma ta murmushi kawai sannan ya canja topic in. “Smart pls pray for me kinji?” “But why?” Ta tmby ganin face in shi he looks serious.
“Zan fada miki wani time for now kawai ki tayi ni da addu’a, its late ki kwanta ko” ya fada yana daga mata gira hade da kallon shi mai rikitarwa.
“Shknn Allah ya kawo mana sauki, Gud nyt”
“Nyt smart promise to be with me whatever the situation pls”
Faduwar gaba ta ji jin abinda ya fito daga bakin masoyin nata.
“You are my always and forever In sha Allah”
“Thank you smart, I love you, sweet dreams”
Back to the story…Har tsakan dare ta kai tana tunanin mamakon rayuwan ta, ganin har Uku ya yi ya sa ta gabatar da nafilah tana rokon Allah ya zaba ma ta abinda ya fi zama alkhairi a rayuwan ta, ba ta San sanda bacci barawo ya sace ta ba a nan kan Sallayar sai da aka kira asuba ta tashi shi ma Dan ta saba tashin ne. Tana idar da Sallah ta koma bacci da ke a gajiye ta ke ba ta samu daman tashi ba sai karfe 11.+
Ba ta yi tsammanin tym ya ja haka ba, a daddafe ta karasa bayi ta yi brush, cikin ta ne ya fara wani kuka ko shakka bbu yunwa ke damun ta tunda dai yunwa ba kanwar baban ta bane rabonta da abinci tun jiya wurin karfe biyu shi ma Anty Rukayya ce ta tasa ta sai taci da haka za ta kwana da yunwa Dan Sam Sam abinci bai mata dadi tun da aka sanar da ita auren ta, yunwan kara shigan ta ya ke sai dai ba za ta iya fita ba balle kuma batun zuwa kitchen in yana falon fa Allah ya gani tana tsoron haduwan ta dashi saboda ba ta San wani irin karba ya ma ta ba.
Umar ne yayi sallama a kofar falon , Aliyu na zaune yana kallo ba komai ya kawo shi gidan ba sai sanin abinda abokin shi zai iya aikata wa kuma ga dukan alamu zargin shi ya tabbata “frnd an tashi lfy?” Ya fada yana cicije wa “da ba lfy ai ba za ka ganni ba INA zahrau”
“Wannan wani irin tmby ne tana inda aka ajiye ta ma na”
Tsakin takaici Umar ya yi hade da girgiza kai “Allah ya shirye ka” ya fada yana dialling numba a wayan shi yayi ignoring “Ameen” in da Aliyu ya fada.
Nanah ya kira ta turo mi shi numban Zahrau sannan yayi dialling numban ta. Tana zaune kan gado tana juye juye Dan kirjin ta har ya fara ma ta zafi abinka da daman tun can tana Ulcer, New number ta gani hakan ya sa ta share ba ta dauka ba amma ganin ana ta kira ya sa ta picking. “Hello” ta fada cikin muryar ta da ta fara dishewa “Umar ne ki fito parlour pls” ya fada sannan yayi ending call din. Hijabin ta har kasa ta dauko ta sa sannan ta lallaba falon. “Bismillah zauna mana” Umar ya fada yana nuna ma ta wuri. Gaishe shi ta yi ya amsa sannan ya tmby ta gajiyan biki “Ya kuma kwanan bakun ta”
“Lfy kalau” ta amsa kanta a kasa tana wasa da yatsun hannun ta. “Ma sha Allah kaman yanzu kika tashi, kin karya kuwa?” Girgiza mi shi kai tayi “frnd ba Amina ta aiko muku da abinci ba”. ” yana dinning ” ya fada hankalin shi kan kallon da yasa a gaba. “Ai da kin fito kin duba Zahrau ba dadi zama da yunwa sai ya miki illa, Dan Allah sai kinyi hakuri fa kin San ba wai zama kika zo for a mean time ba don mu fata mu ke ace kun fahimci junan ku domin duk abinda aka ce miki iyaye ne su ka hada to tabbas ana hangen alkhairi a cikin sa, In sha Allah wata rana dukkan Ku za Ku zo kuyi alfahari da hakan Dan wani hanin ga Allah baiwa ne wlh kar ki manta har tmbyn ki an je a gida amma da ya ke Allah bai yi ba sai abin ya juye a haka kinga KO kullum Abu mafi alkhairi mu ke Neman wurin Allah domin shi ya fi mu sanin dai dai sannan ya zaba mana abinda ke alkhairin gare mu gabadaya, auren Ku da Aliyu wlh hadin Allah ne Zahrau coz dukkan Ku da wadanda Ku ke tsammanin za Ku yi rayuwa da su sai aka samu akasin haka, pls and pls ki sauke komai ki rungume auren nan da hannu biyu ibada ne a wurin ki kuma shi zai kai ki aljanna, so i will like it in kika yi accepting destiny in ki kika karbi Aliyu a matsayin mijin ki na aure ko da ko shi bai yi Na’am da hakan ba you are a Lady you know your ways”. Mtseww, wani wawan tsaki Aliyu ya ja sannan ya bi both Umar da Zahrau da harara “for God sake ya za ayi ya zauna ya na fada ma wannan yarinyar irin talks in nan she is not wise enough for that ai duka duka yaushe ta gama secondary school, karatun ma he doubt in akwai abin arziki a kwakwal war bare ta yi wayewar da zai iya zama da ita a matsayin matar shi” Kashe TV yayi sannan ya wuce hanyar dakin sa ya gaji da jin abin takaicin haka nan. Murmushi Umar ya mata “sorry please go and get yourself some food na cika ki da surutu.” Ya fada yana nuna mata dinning din. “Ehmm Nagode” ta amsa dinning din ta nufa saboda yunwan ya shige ta sosai shi ko Umar dakin Aliyun ya nufa ya iske shi ya kwanta yana kallon silin “frnd me ye haka, tsakin na menene kuma fisabillilahi ya za ayi ka bar yarinyar mutane da yunwa ta hakan za ka sauke hakkin da ke kanka da ban zo ba fa? Kuma kai kafi kowa sanin darajan Abinci Dan ko ba ka wasa dashi”
“Umar ya za ayi ka tadda wannan yarinyar ka na mata irin maganganun nan ba ta yi deserving ba Wlh” kallon mamaki Umar ya bishi dashi “au shi nasihan ne sai Wanda aka zaba”. ” I mean ka San dai ita ba tsari na ba ce kuma ba ta kai ajin mata da zan iya Hulda da su ba so banga dalilin da zai sa ka zauna kana hada ta dani ba har da CE mata ta San ways ta fa ja hankali na kenan kake nufi gsky ka cuce ni wlh me zan yi da wannan abin” tafi Umar ya mai “bravo, ka fi San wayyayu Wanda da ake damawa da su a duniya Wanda idon su a bude su ka San me ake ciki a duniya” “No atleast mace wayyaya wacce za ta iya tafiyar da Alamuranka na jama’anka da kuma yayanka wacce ba za ka ji kunyar nuna wa ba somebody educated, mai tarbiyya, amma wannan ka na ganin tana da courage in da za ta iya fuskantar mutane na in ma tana dashi me zata ce musu, she is not serious in her studies fa kawai zuwa schl din ta ke kaga ko wurin speaking a samu matsala kullum tana kunshe cikin dogayen hijabai banda shiririta ba abinda aka iya, kai ni physical appearance in ta ma is not good for my liking”
“Naga alama, amma tarbiyyan da kayi mentioning bai sa ka jin wani iri ba, gida daya kuka taso mutane daya su ka muku tarbiyyah kaga ko in har kana da shi to tabbas ba ka da shakku akan ta, karatu kuma ai kai ka mata jarrabawar shiga University ko? Batun wani kyau kuma da kake ambata Wlh karya kake kace ba ta da kyau ko da ko za a tara maka kyawawa in fact abinda ke boye shi ne mai kyau ba Wanda ke bude a duniya ba, atleast give her a chance wacce ka ke ma wa dai an riga an aurar da ita so gara ka wa kanka fada” tsaki ya ja sannan ya bar gidan gabadaya.
Bayan la’asar Amina matan Salim ta zo wurin ta, har dakin ta shigo ta same ta, taji dadin ganin domin ko kadan ba ta kaunar halin kadaicin da ta ke ciki, yaron da ke hannun ta ta amsa daman tana son yara barin ma maza “Ya sunan shi?” “Khalipha” “Kai amma dai ya fi kama da Yaya Salim” dariya Aminan ta ma ta domin ko ba gun ta ta fara jin comments in ba. Ganin she is trying to be free with her ya sa ta saki jikin ta sosai da ita, kafin ta tafi sai da ta mata nasiha sosai akan Aliyu domin ta San komai la’akari da faridan kawar ta ce. Ba ta so su ka tafi ba Dan dai ba yanda ta iya ne barin ma khaliphan ya shiga ranta sosai.