KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 7 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari, karfe 10 na safe ringing in wayan ta ya tashe ta daga bacci, Ummiy ce. Ba wai Dan tana so ta ke baccin safen ba illa don ragewa kanta kewa sai da tayi wanka sannan ta Kira Ummiyn “Amarya dadin Amarcin ne ya sa a ka ki daukan wayana?” Ta fada cike da zolaya “Ummiy ya kuke?” Ta fada cike da takaici “Zahra ya miki wani Abu ne, wlh duk abinda ya miki ki rama in ba haka raina ki zai yii Allah ki ajiye wannan tsoron na ki in ba haka ba sai ya kashe ki” “lallai kin iya ba da shawara coz na ki daban ya ke da na kowa” ta fada tana dariya sanin zafin Ummiyn “Zaki Sani an sa ranar biki fa ending December”. ” Dan Allah da gaske?” Ihun murna ta fara yi sannan su kayi sallama.+
Yau ma a dinning ta iske abinci ganin bai falon ya sa ta lallaba ta zuba ta ci a nan, kwana biyu kawai dakin ta ya fara gundurar ta, wani ta ga ya fito daga kitchen din da tsintsiya a hannun shi “morning madam” ya fada yana rusuna wa, ita abin mamaki ma ya bata kar dai ace wannan ne mai aikin gida “madam oga don know how to choose very well oh, you don pretty well well” ya fada yana yashe hakora yanda yayin ne ya sa ya bata dariya. “So you laugh oh, oga don’t laugh oh you are nice, is the food nice? We cook together with MUSA but oga send him away because you are coming so now am to do all the chores, I don suffer gsky”
“Sorry” ta fada tana dariya da alamun akwai surutu ganin informations in da ya jero ma ta ba tare da ta tmby ba. “Thank you so much madam, you must be nice atleast you are here now things will get easy” ita dai kawai murmushi ta mishi sannan ta ce “You are welcome” “seriously madam you don resemble all this fan oyinbo ladies we go see on TV, is just that them are stupid to be walking half naked showing their body they are all ashawo…” Fitowan Aliyu daga daki ne ya katse mishi maganan da ya ke yi. “Morning oga” ya fada yana sada kai kasa “What are you doing here David?” “Sorry oga, I want to sweep the first parlour, am leaving ya fada jikin shi na rawa yayi saurin barin wurin ya nufi falon.
A hankali ya karaso dinning ya ja kujera sannan ya zauna ko kallon gefen da ta ke bai yi ba ” INA kwana uncle” ta fada cikin rawar murya, daga ma ta hannu yayi alamun ya ji sannan ya cigaba da cin abincin shi. Ta Riga ta gama cin abincin gashi jikin ta sai rawa ya ke hakan ya sa tayi saurin tashi domin komawa prison in ta wato dakin ta. “Dawo ki zauna” ya fada in a commanding voice. Jiki na rawa ta koma inda ta ke ta zauna, a hankali ya fara magana “ban ga amfanin zaman ki a gidan nan ba so gwara ki dinga ayyukan gidan nan domin ni ba a zaman min gida a banza, Shara, mopping, goge da sauran su na can dakunan” ya nuna dakunan da ke side inta “sannan parlour duka biyu da kuma kitchen ban bukatar ki taba min komai a nan dakunan” ya nuna side in shi “sai kuma kitchen akwai kayan abinci duk abin da bbu ki rubuta ki ba David house boy INA ne zai hada da sauran abubuwa, kuma kar ki sake ki ce zaki dinga girki da ni sanin kanki ne ba zan iya cin jagwalgwalan ki ba sannan yau ya za mo na karshe da zan kara fito wa in same ki a falo, dakin can kadai na baki daman zama kina iya komai a cikin shi ciki ko hadda cin abinci, hakan ma Dan ba yanda na iya so ki kiyaye mu rabu lfy zuwa lokacin da zan samo dalilin da zai sa A warware wannan hadin ko kadan ni ba ajin ki bane so kar ki taba sa wa ranki akwai ranar da zai zo mu yi irin zaman da ake miki nasiha akai, No way ma so ke ma in kin gaji its free you can also find your way, daga yau kar ki bari in sake ganin ki domin hakan kadai ba ta min rai ya ke kaf mata a rasa wacce za a bani sai ke, Kinsan time in ayyukan ki daga yau ko motsi na kika ji ki koma daki Allah ya gani ban bukatar ganin ki” shiru ta yi har ya gama maganganun shi sai dai ko me yace yana isa cikin jikin ta, ko kadan ba ta yi mamakin abubuwan da ya fada ba asali ma ta yi tunanin fiye da haka, sai dai ita ma ba abinda za ta yi dashi Dan ko kadan bbu burbudin son shi a zuciyar ta kai ita ko a matsayin Dan uwa ma ba ta tunanin akwai.
Tun daga ranar ta fara duk abinda ya lissafa ko a jikin ta da ke daman ba kiwuya gare ta ba hira ko daga ita sai wayan ta, Anty Amina ma ta kara dawo wa sau daya sai Umar ya kan leko ta akai akai ba ta yi tsammanin yana da kirki ba kila tausayin ta ya ke ji ko da ta fadawa su Maijidderh yanda ya ke mata su kayi ta mamaki ita dai Nanah CE wa ta yi daman mai kirkin ne.
Mopping falon ta ke ya shigo, bai yi sallama ba kuma itan ma hankalin ta gabadaya bai jikin ta ta tsunduma cikin duniyar tunani hakan ya sa bata ji motsin shi ba. Wani irin wawan rankwashi ta ji a kan ta tsabagen a zaba da firgita ya sa ta yi kanshi ta ririke shi hankadar da ita yayi ta fada kasa ta buge kai da kujera, wani kara ta saki tana haki. Sai ranar ta kara tabbatar da Uncle Aliy bai da imani kallon ta kawai yayi ya ce “Wannan shi ne punishment inki gobe ki bari mu kara haduwa” sai da ta sha kukan ta sannan ta lallaba ta tashi ranar ko abinci ba ta ci ba amma da ke ba Wanda ya damu da ita ba a ma Sani ba.
Three weeks ta yi a gidan aka koma school, Mami ta yanke shawaran kira amma ko da ta kirata har su ka gama waya ta kasa fada mata nauyin ta tmby ta me ya sa ba ta fada mishi ba ta ke ji domin kullum mamin sai ta kira ta ji ya zaman su ya ke. Ammah ta kira bayan sun gaisa ta sanar ma ta “Ammah mun yi resuming school”
“To kin fada wa Aliyu a ji yanda za a yi?”
“Aa Ammah Ku fada mai mana”
“Saboda wani dalilin ma za ki je ki fada mai kina ji na” ba yanda ba ta yi amma Ammahn ta ki haka ta hakura ta yanke shawaran tunkarar shi, a hankali ta dinga dakon fitowan shi falo kusan awa daya sannan ta fito, links ya ke daura wa a hannun shi da alamun he is in hurry amma this her only chance she won’t miss it, jiki na rawa ta karasa gaban shi wani irin kallan baki da hankali ya mata ganin ta na kara nufo shi ya sa yayi saurin dakar da ita “tsaya daga nan malama, lafiya za ki zo ki sa ni gaba”. “Mun koma school” ta amsa cikin In ina” tsakai ya buga sannan yace “hakan ne ya sa zaki karya min doka ko? Ina ruwana da karatun ki? Ni na sa ki ko ni na nasa a kawo ki garin nan” ba ta San lokacin da ta amsa mai ba “Aa amma pls ka maida ni wurin wadan da su ka kawo nin za suyi farin cikin mai da ni schl …” Saukan Marin da ta ji a fuskan ta ne ya sa ta kasa fadan abinda ta ke bakin ta, dafe wurin da ya mare ta tayi sannan ta sadda kai kasa za ta iya rantse wa shatin hannun shi ya fito akan fuskan ta wani zafaffen kwalla ta ji ya sako kan kumatun ta ba za ta iya tuna ranar da aka daga hannu a ka mare ta ba “har kin yi girman da zaki fara gaya min magana ko? To ko Deedat ba zai taba maida min magana ba balle ke kanwata ta nawa in kuma aure da kike ganin an daura ne ya sa kike ganin mun zama sa’anni to kiyi maza ki farka daga mafarkin da kike yi, this should be the last” ba ta tsaya jin karshen zancen shi ba ta ruga daki, kuka ta yi tsakanin ta Da Allah ta na mamakin wannan bakin halin Aliyu. Babban Yaya ne ya fado mata a rai tabbas uncle Aliy ba zai ki jin maganan shi ba she can’t bear loosing her studies sai dai kome zai faru ya faru.
A lokacin ta kira shi tana kuka, a rude ya ke tmbyn me ke faruwa, kasa fada mishi komai ta yi illa Aliyu ya hana ta koma wa schl lallashin ta yayi da kyar sannan ya tabbatar ma ta za su yi magana.Abinda Aliyu bai Sani ta fi shi rashin son zaman gidan da ya kira nashi Dan dai a wurin ta kufai ma ya fishi, kwana uku kenan da maganan ta da babban yaya amma shiru kake ji ba ta so kuma ta kira shi ya ga kaman tayi gajen hakuri, karatun ne kawai a ranta dan ba wai farkon komawa bane balle ace ba a komai hutun mid semester, New year da Christmas break ne so tana da tabbacin karatu ake sosai gashi 200 level ne lokacin su ke fara departmental courses insu.+
Novels in ta da su ka zame ma ta abokan hira ta zauna tana karanta wa a wattpad, English novel ne ya mata dadi sosai, ba ta Ankara ba sai ganin mutum ta yi akan ta yana huci Sam ba ta ji takun tafiyan shi ba balle kuma lokacin da ya shigo “wani sabon iskanci kika koyo ko? Ki naji ina ta kiran ki ba zaki amsa ba, well ba laifin ki bane cuta na da aka yi aka hada ni da ke ne ya jawo hakan” kan sofan ya nemi wuri ya zauna hakan ya sa ta yi saurin tashi ta zauna tana kallon kasa “Sanin kanki ne ba ki kai matsayin da zan zauna in yi maganar hankali da ke ba saboda hankalin ma ba wai kuna dashi bane, anyhow I have no choice” ya fada yana daga kafada, folding lips in shi yayi sannan ya kare ma ta kallo daga sama zuwa kasanta, tsarguwa ta yi da kanta ita ma ta fara kallon jikin na ta dogon riga baka ke jikin ta kuma ko kadan bai kama ta ba balle ace jikin ta ya fito, wani siririn tsaki ya ja sannan yace “hey calm down ba ki da abinda zan iya kallo a jikin ki INA kallon irin cuta na da aka yi” ita dai kala ba ta ce mai ba coz da zai gane ita ganin shi a gaban ta ma ba so ta ke ba talk less of maganganun da yake ma ta “Zaki koma schl kaman yanda kike bukata amma fa da sharadi” kallon ta yayi yaga expression inta ga mamakin shi attention in ta ma bai kanshi gabadaya sai dai da ka kalle ta kasan a tsorace ta ke “Kehhhhhh” wani irin tsawa ya daka mata da ya sa ta saurin dagowa tana kallon shi jikin ta ko sai bari ya ke “Ina miki magana kina wani abun? Ni tsaran ki ne?” Saurin girgiza kai tayi “Aa” ta furta muryan ta na shaking ta San karamin aikin shi ne ya ce zai taba lafiyan ta yanzu su biyu kadai a gida ba mai ceton ta “Gobe zan sa a maida ki Zaria amma fa sai kin amince you will do everything possible ki ga ba ki dawo gidan nan ba” Ganin yana kallon ta alamun yana jiran amsan ta ya sa ta tmby “How”. ” I don’t know kawai ni dai na San ban bukatar ki a rayuwa ta so find a way in ba haka to Wlh duk ranar da kika kara dawowa gidan nan ke da makaranta sai dai ki ga wasu nayi” “Na amince” ta yi saurin fadi. “Kin taimaki kanki ki hada kayan ki” mikewa yayi ya bar daki, kaman an mata albishir da aljanna haka ta dinga ji ranar kafin kace kwabo ta hada kayanta akwati biyu ciki ko ba kayan ta da aka kawo da sunan lefen ta ko daya bata taba ba.
Ta yi murnar ganin yan gidansu sosai sai dai yan uwan na ta sun koma schl dai hamza da deedat da su ka tasa ta gaba da tsokana wai ta dinga bi musu hankali da yaron su ko INA su ka ga cikin oho!. A wurin Mami ta ke jin Uncle Aliy wani course ya tafi na nine months a Florida sannan an kara mishi matsayi daga captain zuwa major, ta dai nuna ma ta ta Sani coz shi ma abinda ya nuna mata kenan apparently, Baffah ce ma ta yayi ta koma gidan Aliyun da ke nan kuda da gidan su ta zauna amma fir mami ta ki tace ba za ta zauna ita kadai ba ta zauna a gida har a ga dawo wan shi.
Aliyu namijin duniya ne na karshe har wani driver ya kawo musamman da zai dinga kai ta schl ya jira sai ta gama lectures ya maido ta duk Dan kar a zargi wani abun, duk end of month kuma sai ya aiko wa deedat makudan kudi a bata ita dai amsa kawai ta ke ta ajiye saboda dga Abbah har Baffa sun wadata ta da komai.
Duk yanda Aliyu ya so boye abun shi sai da Mami da Ammah su ka dago shi ita dai Ammah shiru ta yi kawai ta zuba wa sarautar Allah ido Mami ko sai da ta tsare Zahrau ta fada ma ta yanda su ke da Aliyu amma mai? Ita kan ta Zahrau sai ta zabi boyewan saboda su rabu lfy kar ya hana ta karatun ta.
9 months later
Zahrau karatun ta take sosai ba ta da wani damuwa ko kadan karshe ma wurin Fatima ta koma a off campus da farko kin yadda aka yi sai da ta kira Umar da ke daman ya kan kira ta akai akai ya ji yanda ta ke, shi ya tura ma ta numban Aliyun, text ta tura mishi domin ko ta kira ba ta San mai za ta ce mishi ba, reply ya mata akan ta yi duk abinda ta ga dama she is free, amma kuma wani abun mamakin da kan shi ya kira Baffah akan a barta ta je Dan Allah zai fi ma ta saukin karatu.
Shirye shiryen bikin su Maijidderh da ya rage wata da sati biyu su ka sa a gaba, a bangaren Zahrau ko har ga Allah mantawa ta ke da tana da wani aure a kanta mostly ma sai anyi maganan ta ke tunowa. A ranar da su ka gama jarabawar second semester 200 level ta koma cikin Zaria sune manya iyayen biki so komai sune a gaba.
Kaduna su ka je kammala wasu shirye shiryen su sun Kai sati biyu a can sun kai sati biyu a can sannan su ka koma Zaria.
A haka dai a kwana a tashi har bikin ya gabato gaba daya shirye shirye bangaren Amare Zahrau ne da Nanah komai a kan su ya kare har wani rama su kayi sai kace sune amaren. Zahrau har tsokanar ta ake wai kewar mijin ta ke sa ta rama ita dai sai ta yi shiru tana jinjina abin.
Bridal eve ne first event in da za ayi kuma a nan cikin gidan su, kusan a kasuwa su ka wuni sannan su ka dawo gidan sai da su kayi making sure komai is set sannan su ka tafi shiryawa.
Gidan Uncle Aliy da ke nan kusa dasu su ka nufa, Mami ta sa su komawa can tunda mutane su ka fara cika ba wai dan suna so ba.
Takalman da su ka fara hangowa a kofar falon ya sa su mamaki coz key in gidan ma a hannun su yake sun kulle, a hankali magana ke tashi a falon.
Zahrau ce ta fara Sallama gaba daya su ka dago suna kallon ta, four eyes su ka yi da shi da sauri ta dauke idanun ta “Ina wunin Ku” tare su ka fada ita da Nanah da ke rakube a banyan ta “lafiya kalau” su ka amsa banda Aliyu da ke bin Zahrau da kallon mamaki. “Matar mu ki na nan” Salim ne ke maganan, murmushi kawai ta mai. Nanah ko ba ta iya magana ba sai kokarin rakube wa bayan Zahrau ta ke. Sosai mamakin abinda Nanah ta yi Zahrau ta ke don hakan ba halin ta bane, karaf idon ta ya fada kan Umar da ke bin bayan ta da kallo, tabbas da alamun magana saboda shi kanshi Umar ba su taba haduwa bai tanka mata ba. Ganin Nanahn ba ta da niyyan tafiya ya sa Zahrau ta ja hannun ta su ka nufi ciki tana fadin “bari mu shiga”
“Toh” sai sannan Umar in ya tanka.
Ita dai Zahrau kallon tuhuma ta bi Nanah dashi har su karasa daki.Ko da su ka gama shiryawa su uncle Aliy ba sa falon da alamun masallaci su ka tafi saboda an shiga Sallah, an gama shirya ko mai so nan da nan aka fara program ba African time, its all ladies event so komai ya zo da sauki sai da aka fara kiran magariba sannan aka watse.+
Washegari ana shirin tafiya kamu ta je dauko Abu a gidan Babban yaya nan ta iske taron mazan family insu da abokanan su ba ta so wuce wa ba am she is in hurry ana jiranta Allaha ya taimake ta ta roki fati ta raka ta da ke ta zo bikin da hakan nan za ta koma, ta gefe ta lallaba ta wuce dan ba ma ta so su lura da ita sai dai me sun fito kenan za su wuce Yaya deedat ya kwala ma ta kira, ba yanda ta iya haka nan ta karasa gaisuwan da ba ta so dai sai da ta yi shi As usual Umar da Salim su ka sa ta a gaba da tsokana “INA Maman khalipha” ta tmby Salim, “tace ba ki da Kirki ai ba kya nementa”. ” Ayyah pls ka ba ta hakuri I will call her” Gogan na ta ko hankalin shi gabadaya na kan waya ta fi jin dadin hakan Dan ba ta cika so abu na shiga tsakanin su ba, sakon da Ya deedat in ya ba ta ta kai wa Ammah ta amsa su ka wuce da Fati.
*** *** ***
Sai da ta tabbatar kowacce ta samu motan da za ta wuce dinner sannan ta yi cikin gida ko ta huta “Aa Antyn mu ke ba za kije ba ne na ga ko shiryawa ba ki yi ba” Hamza ke magana “Wlh ko hamza a gajiye na ke” “Aa fada min gsky ko dai ya Aliyu ne ya hanaki” Girgiza mi shi kai tayi sannan ta yi hanyan sassan Ammah “Zahrau” ta ji an kwalla ma ta kira hamza ne dai still “Ana miki magana” ya fada sannan ya wuce, direction in da ya nuna mata ta kalla, four eyes su ka yi da Uncle Aliy ganin bai da niyyan dauke idon shi ya sa ita tayi saurin dauke na ta, alama ya mata da hannu ta karaso ita abin ma mamaki ya fara ba ta. “Me ya sa ba ki je ba? Ban son karya”. ” Ammah ce ta hanani wai sai na tmby “
“Ke kuma kin fi karfin tmby ko?”
Shiru ta yi tana kallon shi cike da mamaki “je ki shiryo in kai ki ba za su ji dadi ba in ba ki je ba” ba musu ta wuce cikin gidan ta shiryo. Ba Wanda ya ce ma wani uffan har su ka isa ya sauke ta, tana fita ya ja motan shi ya dawo gida ba komai ya sa shi yin hakan ba sai gudun Abbah ya ji lbr rashin zuwan ta ya ce shi ya hana ta a tunanin shi kenan.
Washegari aka daura aure sannan aka shirya kai amare gidan su, sun ci kuka kaman ba su ke son auren ba rungume junan su kayi suna kuka da kyar aka raba su Dan ganin lokaci na tfy, kano a kai Ummiy sharadda phase 2 Maijidderh kuma Kaduna Nasfat village saukin su ma Anty zee na kano while Kaduna kuma Anty Rukayya, ita dai Zahrau ba inda ta je a cewan ta sai bayan kwana biyu za ta je ta ga gidan na su saboda har ga Allah ba ta son wa za ta raka ba they are all equal to her. Sai kuma gidan ya zama shiru saboda kowa ya watse su Yusrah ma sun tafi school boarding hamza ma ya koma, yaya deedat Tun safe ya ke fita aiki daga ita dai sai mami da Ammah sai kuwa Adnan, Uncle Aliy ma tun bayan bikin ba ta gan shi ba kuma ba ta tmby ba “Anty Zahrau Abbah na kira” Adnan ya katse ma ta tunanin da ta ke “Yana parlor?” Gyada kan shi yayi ya wuce.
Abbah da Mami ta tarar a falon sai da ta zauna ta gaishe su cikin fara’a su ka amsa ma ta “Yaushe za Ku koma makaranta”. ” December” ta bashi amsa kanta a kasa “Nan da one month kenan” “eh” ta amsa still kanta a kasa “me ye sa ba ki bi Aliyu ba” wani irin Abu ta ji a zuciyan ta ko tunanin komawa gidan ba ta so ma, shiru ta yi Dan ba ta San me za ta ce mishi ba “ba ki ma San ya tafi ba ko?” Gyade mishi kai ta yi Dan ba ta San me za ta ce mishi ba “Good, fada min wani irin zama kuke yi dashi, kuna ma magana da shi kuwa”
Abbah mutum ne mai hikima ga iya karantar mutum abinka da tsohon lauya duk yanda ta so boye mishi sai da ya fuskance ta, yanayin fuskan ta kadai ya tabbatar mishi abinda ya ke zargi “tashi ki tafi zan neme ki”
Sati biyu kenan da maganan su da Abbah amma bai kara Neman ta da maganan ba ba kuma Wanda ya taba ma ta maganan Aliyun ita har ga ranta tafi jin dadin hakan ma. Ita da hamza ke kallo a falon mami suna musun siyasa kowa da Wanda ya ke bi wa baya, ko sallama ba su ji ba sai ganin mutum su ka yi akan su yana tmby INA mami “yanzu ta shiga” hamza ya amsa, ko gaisuwan da ya ke mishi bai bi ta kai ba ya yi hanyan daki “toh fah wa ya tabo mutumin naki ne Antinmu” hararar shi ta yi sannan ta mai da hankalin ta kan kallon da ta ke yi, ya kai 30 minutes sannan ya fito har yanzu dai ranshi a bace ya ke “Ki same ni a dakina na cikin gidan nan” ya fada ba tare da ya kalle ta ba sannan ya yi hanyar kofa itan ma kallon ta ta cigaba da yi sai da hamza ya tabo ta “ke mijinki na Neman ki ba za ki tashi ba ko? Haka aka koya miki” “Allah hamza ka sa min ido INA ruwan ka ne wai?” Dariya yayi sannan ya ce “Allah Zahrau ku shirya kanku da Ya Aliyu za Ku dace sosai” banxa ta yi dashi ta cigaba da kallon ta sai bayan kaman mintuna Ashirin sannan ta tashi ta dauki mayafin ta tafi ta daga falon tana jin hamza na tsokanar ta “Za a amsa kiran mijin kenan bayan an gama Jan aji” bazan ta yi dashi ta wuce abin ta.
Zaune ya ke ya hade girar sama da na kasa sai kofa ya ke ko da tayi sallama banza yayi da ita sai da ta zaune sannan ya bita da harara “tun yaushe na neme ki?”
“Tun dazu” ta bashi amsa kai tsaye
“Okay raini ya hanaki zuwa” shiru ta mai “ba magana na ke miki ba?” Tsawa ya mata da sai da ya sa ta yi baya dan tsoro jikinta har kyar ma yake, wani siririn tsaki ya ja sannan ya ce “ke ga shegen tsoro ga kuma rashin kunya, me da me kika je kika ce wa Abbah na miki?” Kallon mamaki ta bishi dashi sai kuma ta yi saurin sadda kai kasa “Tmby na yayi ya alakar mu da kai ni kuma na fada mai?” Ta fada a hankali though da kaji muryan ta kasan a tsorace ta ke dashi “saboda kina son alakar ya fi haka? Ko kuma ki na son hadani da mahaifina” girgiza kai ta yi cikin sauri “kace in nemon hanyan da bazan kara komawa gidan ka ba shiyasa” “karya ki ke yi to albishirinki INA mai taya ki farin cikin Abbah ya ce duk ranar da na sake ki ba zai taba yafe min ba, INA son in gama da duniya lfy so sai ki shirya damarar zama da ni da dukkan halaye na da za ki tarar gaba but FYI I will never see you as a wife so is good ki shirya rayuwa cikin kunci da wahala da kuma rashin so” sheshekar kukan ta da yaji ne ya sa shi dakatawa ba komai ya sa ta kukan ba sai jin hukuncin da Abbahn ya yanke “Dakata malama ki dena min kukan munafunci, na fi ki tsanar labarin da na ke baki, upon all matan duniya ma me zan yi da mace irinki?” Girgiza kai yayi cike da kunci sannan ya ce ” wlh an cuce ni amma Aliyu wlh ya fi karfin ajin ki, I will never love you in my life” tsakin da ta buga ne ya katse mai maganan da ya ke yi this tym around, ya tsani a mai tsaki ko da wasa wani irin mari ya kife ma ta a fuska ba shiri ta zube a kasa “Na tsaneki wlh” ya furta ya na bin ta da kallon tsanar da ya fada yana mata, a zabure ta tashi ta fita waje da gudu.
Mami ganin yanda Aliyun ya fita ya sa hankalin ta bai kwanta ba tuntuni, dakin shi ta nufa domin tana son su tattauna dashi amma sai dai me? Zahrau ta hango ta fito da gudu daga dakin tallabe da fuskan ta da sauri ta karasa gun ta tana tmbyn lfy? Ganin idon ta ya fara rufe ta yi kasa ya sa ta saurin rike ta tana girgiza ta amma ina b ta ma San ta na yi ba. Jin maganan Mami ne ya sa Aliyu fito “ruwa ruwa” mamin ke ta kira, da sauri ya dauko bottle da ke kan study table in shi ya mika mata, sai da aka yayyafa mata sannan ta saki ajiyan zuciyan mai karfi kirjin ta sai buga ya ke da karfi, “dauko key mu tafi asibiti” Mami ta fada a rude hijabin ta ma hamza ne ya dauko ma ta.Accident and Emergency aka shiga da ita, sun dauki kusan 5 hours akan ta sannan aka fita da ita zuwa wani dakin, a rude su ka bi bayan likitan zuwa dakin da aka kai ta “Alluran bacci mu ka mata please a bar ta ta huta” Dr ya fada sannan ya juya ya kalle su daya bayan daya “is she married?” Ya tmby mami ganin duk ta fi su damuwa so he just assumes she is her mother, gyada mi shi kai tayi “fine, if the spouse is around I will like to meet him and you in my office”. Aliyu da Mami su ka bishi office in, sai da su ka zauna sannan ya bisu da kallo, a hankali ya fara magana “she had an attack due to sudden frightened, I guess this is not the face time kuma hakan na barazana ga zuciyan ta, she is just young please kar a mata ruining rayuwa more especially you the husband ta kai stage in da kiris zuciyan ta ya ke jira ya buga so you have to be careful Dan Allah” Godiya su ka mai sannan su ka bar office in.+
Ko da su ka koma dakin Ammah ce kawai a wurin sai hamza, Zahrau kam ba ta farfado ba “kai ba yau za ka koma ba?” Mami ta tmby hamza “eh daman wai naga Zahraun ne”
“Kai za ka ba ta lfy” girgiza kai yayi “to maza tafi gida ka shirya ka wuce” sum sum hamza ya fita ya bar dakin sannan Mami ta kalli Ammah “Ammah da kin je gida kin hutu, tun da dai zahrau n ta farka”
“Mami sai kuma na bar ki ke kadai?”
“Aliyu zai zauna”
“Haba Mami INA namiji INA zaman Asibiti?”
“Shi ya nemi zaman ai Dan Allah kuje Ammah kya dawo ko anjima”
“To shknn” ta fada
Wani kallo Mami ta bi Aliyu dashi da sai da yaji gaba daya jikin shi na rawa “me kayi wa Zahrau Aliyu” kasa magana yayi sai in INA da ya ke ta tayi da kyar ya ce “ma Mami ba ba abinda na na mata” harara ta bishi dashi da yasa shi saurin sadda kanshi kasa “tmby ka nayi ka ban amsa ” wlh Mami magana kawai mu ka yi da ita shi ne fa tana fita naji maganan ki kina Neman ruwa”
“Maganan ma kala kala ne ai, ita ta maka laifi da za ka sauke fushin ka kan ta, shatin fuskan ta fa? Tunda na gan ta tana rike da wurin”
“Mami to ba INA mata magana bane ta min tsaki ni ban ma San na mare ta ba tsabar takaici”
“Inalilahi wa’inna illaihi raji’un Mari Aliyu, har yanzu ba za ka dena saurin hannun ka ba Ashe duka mace za ka dinga yi, yarinyar da daman ba ishashen lfy gare ta ba za ka buga”
“Ki yi hakuri Mami ba zan kara ba” ya fada kan shi a kasa.
“To in dai akan Farida ne ya sa ka dukan ta to wlh Aliyu bazan taba baka goyon bayan auren ta ba, ba da yawuna ba” wani irin faduwan gaba yaji jin abinda mamin ta ambata Duke da dai ba yau ta fara ambatan ba.
Abinda ya faru shi ne bayan auren Aliyu da Zahrau fir Farida ta ki yadda ta auri Wanda babanta ke so, juyin duniyan nan aka yi ta ki, karshe baban ya rufe ido ya aura mata shi a dole, ko sati daya ba ayi da auren ba ta daga wa mijin hankali, wulakanci kala kala karshe ya gaji ya sake ta. Tun da ta dawo gida ta fara Neman Aliyu tun yana doje ma ta har ya hakura a haka su ka cigaba da soyayyan su, wannan karon mahaifin ta da kanshi ya nemi ya turo mahaifin shi, shi ne ya zo fadawa Abbah bai San daman yana kule dashi ba kaca kaca ya mai sannan ya haramta mishi sakin Zahrau da kuma auren Faridan, wurin Mami ya je ita ma fir ta ki amincewa shi ne ya sauke haushin shi akan Zahrau baiwar Allah.
Satin Zahrau daya a asibiti ba laifi ta Dan warware, Aliyu kuwa har yanzu bai koma bakin aikin shi ba, fir mami ta hana shi a cewarta sai Zahrau ta warke sannan za ta bar shi ya tafi, ba yanda ya iya haka ya zauna ba dan yana so sai dan mami ce ba yanda za ayi ya mata musu. Zahrau tun da ta farfado ba abinda ta ki jini irin ta farka ta ji muryan Aliyu ballantana Kuma ta ganshi da idanun ta, wani irin kiyayan shi ta ke ji yana yawo a jinin jikin ta dan she even doubt ko soyayyan yan uwa tana mishi, ita ma ta tsane shi kaman yanda ya furta ma ta ido da ido ba kunya balle tsoron Allah.
Damuwar shi Farida itama ba ta da lfy, a cewarta tun daman yaudarar ta ya ke yi tunda yanzu ance ya fito ya ki, ya sha fahimtar da ita amma ta ki fahimta, zargin ta bai tabbata ba said da aka kwantar da ita a asibiti ya kasa zuwa ya dubo ta. Gaba daya ya susuce banda rama ba abinda ya ke zubawa, ga tunanin makomar aikin shi da aka hana shi komawa, banda hantara ba abinda ke hada shi da mami, Abbah ko ko kallo bai ishe shi ko gaishe shi yayi bai amsawa ga kuma farida, gabadaya yana cikin tsaka mai wuya ya rasa mafita.
Tsaki ya ke ta bugawa ya rasa mai ke mishi dadi gabadaya a duniyan, abinci da ke gaban shi ya bi da kallo amma me? Duk rashin wasansa gun ciki yau ko kara kallon abincin bai son yi, a hankali ya bi wayan shi da ke ta ringing tun dazu da kallo, mostly abokan shi na Abuja ke ta kiran shi bai San me zai ce musu ba shiyasa ya kasa dagawa.
Sallaman da yaji a kofan dakin shi ne ya katse mai tunanin da ya ke ciki said dai kafin ya amsa har mai sallaman ya shigo, Umar ne kallo ya bishi dashi kaman yanda shi ma ya ke kallon sa “ba ka da lfy ne frnd” kai ya girgiza mai “ka rame ka yi Baki, you are not picking your calls”
Ajiyar zuciya Aliyun ya sake sannan yq nuna wa Umar wuri alamun ya zauna su yi magana, “INA jinka”
A hankali ya labarta mishi abinda ke faruwa har karshe, kallon tausayi ya bi abokin na shi dashi, ko kadan Aliyu bai daukan shawara ne tun farko da hakan bai faru dashi ba “Aliyu gsky ba zan boye ma ka dole iyayen ka su yi fushi da kai ganin yanda ba ka dauki auren da su ka ma ka da mahimmanci kaga tun da Kai ba ka faran ta musu ba suma ba zasu faranta ma ka ba, the best solution kawai ka rabu da farida INA ga tun farko ba alkhairin ka bane shiyasa hakan ya faru, ka samu mami da Abbah ka ba su hakuri sannan ka rungumi auren ka hannu biyu ba ka San alkhairin da Allah ya boye a ciki ba kuma in kayi hakan dukkan matsalar ka zai kau ko ya ka gani” shiru yayi yana bin abokin nashi da kallo tabbas duk abinda ya fada gsky ne and it’s the best way out.
“Frnd Wlh ban taba kallon yarinyar nan da sunan mata ta aure ba bansan yanda za ayi na sa zuciya ta ta fara kallon ta a matsayin hakan ba sannan kuma farida za ta ga kaman yaudarar ta na ke Dan man yanzu haka zargi na ta ke. Girgiza kai Umar yayi sannan ya fara magana ” Zahrau mace ce da ko wani da Namiji ke burin ya samu fahimtar kawai za kayi Aliyu, she lacks Nothing sai dai abinda ba a rasa ba daman Dan Adam ba zai taba cika goma ba please frnd give this marriage a chance, Allah kadai ya San dalilin shi na yin hakan. Farida kuma ka barni da ita zan ma samu Salim da madam in shi akan magana su zasu iya fahimtar da ita ta yi hakuri ta koma gidan mijinta don shima yana son ta ta dai ki zaman ne, in kuka yi hakuri dukkanku sai Allah ya ba Ku abinda za kuyi alfahari dashi kilan ma jarrabawa ce yanzu dai mu fara da su mami” murmushi Aliyu yayi Wanda ya manta rabon da yayi irin ta “ko ruwa ban baka frnd” hararan shi yayi sannan ya ce mishi “yau kuma bako na zama a gidan nan” kallon shi yayi alamun au haka ne fa dariya su ka kwashe dashi dukkan su harda tafa hannu “yaushe ka zo?”
“Yanzu nan daga Abuja direct nan gidan na iso ka daga min hankali shi ne na zo inga lfy”
“Allah sarki abokina Allah ya ba ka matar da za ta kula da kai irin haka”
Hararan shi Umar yayi sannan ya ce “au tsiya za ka min to sha kurumin ka har na fada wa Baba ina neman aure yanzu ma muje in fadawa Abbah”
“Kai fa ba ka da kunya, wai kai yanzu da gaske kanwar Anty Rukiey nan za ka ke so”
“Tsaya nan kwanan za ka ji anje Neman aure ne”
“Allah sa alkhairi” ya fada yana tabe baki hararan shi Umar yayi sannan ya fita daga dakin ya bishi.Abuja, Nigeria.+
Idanuwan shi kar akan TV in da ke gaban shi, a hankali hankali yana daukan kayan marmarin da ke gaban shi yana kai wa baki. Duk Wanda ya gan shi zai yi tunanin gabadaya hankalin shi ya tafi ga tv din da ya ke kallo amma ko kadan ba hakan ba ne domin idanun shi kawai ke gun amma hankalin shi gaba daya ya tafi ga Neman mafita a kadararren auren da aka mai kaman yanda ya ke ikirari.
“Kar ka kara zuwa wuri na da sunan Neman in yafe ma har sai ranar da ka dauki auren da na maka da mahimmanci Aliyu in har na isa da kai” abinda Abbah ya ce mai kenan da su kaje wurin shi tare da Umar.
Mami ko fada ta rufe su dashi daga shi har Umar in da bai San hawa ba balle sauka, har gwara ita ma ta hakura daga baya nasiha ta musu sosai tare da sharadin zai gyara rayuwan auren shi.
A yanzu haka bai da mafitan da ya wuce ya gyara rayuwan auren na shi ba dan komai sai dan ya faranta ma iyayen shi ta hanyar cika musu burin su.
Sai dai bai san ta yanda zai fuskanci yarinayar ba bayan irin maganganun da ya sha fada ma ta ma rasa dadi duk da dai ba wai har zuciyan shi hakan ya ke ba Aa yayi hakan ne kawai dan ya ba ta ma ta rai sai dai har ga zuciyan shi bai jin yana son ta.
Bai so ta raina shi ko kadan bai son raini shi ya sa ya ke kama girman shi wurin kowa amma matsala zai iya takun shi dole ya San abin yi.
Numban ta ya bukata gun Umar don shi kadai ne zai iya amsan numban ta wurin shi ba tare da ya tuhume shi ba, Nan da nan Umar ya turo mai numban tare da farin ciki abokin shi da gaske ya ke zai canja.
“Fatima” ya tsinci kanshi da ma ta saving, sai kuma ya ji sunan ya mishi dadi kuma yayi kama da mai shi din.2
Har yayi dialling numban sai kuma yayi saurin katse wa gwara ya turo ma ta text zai fi.
“Hey, how is ur body And school? Hope you are good? Its Aliyu ur brother”
Zaria, Nigeria.
Littattafai ne dayawa a gaban ta kala kala da note book da text book duka, Assignment gare ta na pharmaceutical microbiology, washegari za su yi submitting gashi yana da yawa ga research kuma printed one ya ke so sai tayi typing tukunna bayan haka kuma a washegarin ranar suna da test in biochem duk abubuwa sun hade ma ta dan ma Allah ya taimake ta kullum cikin karatu ta ke.
Searching ta ke yi a different kind of websites da kuma text books tana Neman convenient amsan da za ta ba lecturer in, karan shigowan text ta ji a wayan ta, tsaki ta ja cike da takaici tana fadin “MTN in nan su in shi mutane su bar mutum ya ji da abu daya mana”
“Wai miye sa da mutum yaji karan text a wayan shi sai ya ce MTN Ku duba mana sai Ku yi ta musu sharri” Fatima ta fada ita ma tana karatun test in biochem in da za suyi gobe da ke akwai courses dayawa da su ke yi tare.
“Duba ki gani mana su kadai ke da tym din banza”
Jawo wayan fati tayi sannan ta duba text in “ai ko kin dauki hakkin don ko numba ne ya miki text” shiru Zahrau ta ma ta Dan ta yi tunanin tsokanan ta tayi sai da taji ta fara karanta text in sannan ta dago tana kallon ta kaman daga sama taji tana fadin “its ur brother Aliyu” mamaki ta fara yi wani yaya gare ta Aliyu kuma “Aliyu kuma brother na” ta tmby fati
Hararan ta fati tayi sannan ta ce “a gidanku ba Aliyu ne” girgiza kai tayi “okay, ki duba true caller”
“Aliyu Abubakar Tafida” ta gani a rubuce, mamaki ne ya mamaye ilahirin ruhin ta gabadaya me zai sa uncle Aliy ya turo ma ta mssg.
“Yanzu kin gane kenan” fati ta tmby ta kai da gyada ma ta sannan ta ce “ni nafi sani Uncle Aliy ko kuma Yaya Aliy”
“Ehm yanzu da ki gane ai sai ki mai reply” tsaki ta ja ta cigaba da abinda ke gaban ta Girgiza kai fati tayi tana kallon ta cike da mamakin irin yanayin auren kawar ta.
•••••
Tun Aliyu na tsammanin reply in Zahrau har ya sadakar, “ita har ta isa ya daga waya ya mata text amma ba za ta mai reply, what the hell do she think she is? Ita har ta kai matsayin nan?” A fili ya ke magana sai dai shi kadai ne a falon, tsaki ya ja yana fadin duk su Abbah su ka ja min amma ba komai zai yi komai dan ya faranta musu sai dai ba zai dau raini.
Share ta yayi bai kara bi ta kanta ba. Weekend su ka tafi Zaria shi da Umar, yayi tsamanin ganin ta a gidan amma sai ya ga sabanin hakan Yusrah ya tmby ta ce mishi ba ta zo ba.
Umar ya fadawa komai akan fa shi fa ba zai iya daukan raini ba gwara kawai a barshi “haba Aliyu daga text daya sai ka yanke hukunci, in ba ta gane Kaine ba fa, bayan haka ka ma yarinyar abubuwa dayawa kasan mata da riko so matukar ka na son ganin ka cika wa mahaifanka burin su to ko shakka bbu sai ka sauke son girman da komai ka shawo kan ta tukunna”
Wani siririn tsaki ya ja cike da takaici “kar ka manta ba Wanda ya taba ce maka ta taba son ka balle ta ma ka abinda kake so, kai ke son abu so dole ka sauke kai ka nema Aliyu”
Ajiyar numfashi yayi sannan ya ce “this is totally annoying wlh, miye abin yi yanzu?”
“Pay her a visit” harara Aliyu ya juyo yana bin shi dashi alamun ka sha wani abu ne? “De na harara na kalau na ke”
“Sai dai in tare zamu” ya fada ba don zuciyan shi na son abinda ya ke shirin yi ba “ba matsala na raka ka yawon banza ma balle inda lada zan samu”
Murmushi ya saki Wanda akan fuskan shi kadai ya tsaya sannan ya ce “When are we going?”
“Tomorrow of course sai dai in you are eager sai mu je yau”
Hararan shi ya yi sannan ya ja tsaki “na Shiga daki ni” girgiza kai yayi sannan ya bi shi.
Washegari, a samaru su kayi Sallahn magariba. Sun zabi dare ne ganin irin ranar da ake yi da rana. Umar ke driving Aliyu ko yana gefe tunanin shi kawai inma sun je me za su ce Mata, “ka ma fada ma ta kuwa”
Dan dakata da tukin Umar yayi sannan ya ce “au ba ka fada ba ma kenan ka sa mu ka taho, in ba sa nan fa?”
Kallon takaici Aliyu ya bishi dashi, tsaki ya ja don bai jin yin magana ballantana ya maida wa Aliyu amsa.
Wayan shi ya ciro yayi dialling numban ta for the first time a rayuwan shi sai dai har ya katse ba ta dauka ba. Citson yatsa yayi cike da takaici hakanan ya hakura ya kara dialling numban na ta, sai da ya kusa katsewa sannan aka dauka.
Shiru yayi haka ita ma ba ta tanka ba ta kuma kashe wayan ba “Assalamu Alaikum” Ya fada a hankali “Wa’alaikasalam” ita ma ta fada a hankali, har cikin jikin shi ya ji saukan muryan na ta ko da yanda ta yi maganan a hankali ne kila “kina gida ne?”
“Ehmm”
“Okay, ga mu nan zuwa”
“Emhmm” kawai ta ce sannan ta yi shiru ganin haka ya sa yayi ending call in.
Sai sannan Umar in ya cigaba da driving da ke da man ya taba kai su Nanah gidan.
Kallon Fati tayi sannan ta ce “Wai Uncle Aliy ke ce min gasu nan zuwa, ko dai wani Abu ya faru ne”
“Daman sai abu ya faru Miji ke zuwa gurin matarsa”
Tsaki Zahrau ta ja sannan ta ce “to ni me zai min? In ba zuwa yayi ya bata min rai ba wlh ni ban son ganin shi”
“Ai da kin fada mishi a wayan”
“Fati me ye haka ina fada miki abu kina fada min magana”
“Me kike so ince miki Zahrau? So kike in biye miki ki kashe auren”
“Muna waje” ya turo ma ta mssg
“Sun iso wai, I can’t go alone”
“Ya za ayi kenan”
“Kin zuwa zanyi mana”
Dariya fati tayi sannan ta ce “tashi mu je in raka ki”
Ajiyar zuciya ta yi sannan ta mike.
Umar na tsaye jikin mota shi ko gogan ya na zaune a ciki ya sa ko kafafun shi ta waje.
Da ke dare ne hasken da ke wurin ne ya haska fuskan Umar hakan ya sa su ka gane idan su ke.