KOMIN HASKEN FARIN WATA CHAPTER 9 BY ayshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yayi kwana biyu sannan ya warware gabadaya ya koma bakin aikin shi, still ba wani abinda ke shiga tsakanin su sosai yawancin ma gaisuwa ne sai ko in shi ya ja ta da lbr.+
A haka azumi ya riske su, zuwa yanzu Aliyu ya sadakar dacewa Hakkin yaran nan ne ke bibiyar shi, haka kurum ya dauki kin duniya ya sauke a Kansu, hantara da kyar hade da duka ba Wanda ba su sha a wurin shi ba, hakan yasa su ke mugun tsoron shi har ya kai dacewa ba sa yarda su zauna inuwa daya dashi.
Da farko ya San kiriniya da rashin jinsu ya Fara kawo rashin jituwar su daga baya kuma shi kanshi ba zai ce ga dalili ba illa ya San cewa gudun shi da suke ma ya taimaka sannan ko kadan bai son raini kuma ya ga alamun hakan a tattare da su.
Ajiyar zuciya ya saki yana tunanin hanya da zai bi ya goge laifin shi a wurin su duka, ni dai nace Allah ya ba da sa’a.
Yan barrack insu sun zo shan ruwa gidan nashi sosai farkon azumi, haka Zahrau ke dawo wa daga asibiti a gajiye ta hau aiki gashi shi sai da Yamma ya ke samu ya dawo gida so ba karamin wahala ta sha ba.
Ranar da aka kai azumi na Tara ya same ta a dakin ta bayan sun dawo asham, a mota kullum yake daukan ta su tafi though banda gaisuwa ba abinda ke shiga tsakanin su.
“Zan yi tafiya Fatima kuma zan kai Sati daya ko fi ma, in bar ki a nan ne”
Ya fada yana kallon kasa ita ma kasan ta ke kallo kaman masu kunyan juna ko ince surukai.
“Ka kai ni Zaria” ta bashi amsa
“Zaria Kuma? IT in naki fa?” Dan jum yayi Yana tunani “ki shirya zan Kai ki gidan Salim”
Fuskan ta yake kallo yaga reaction Inta sai dai ya kasa karantan komai.
“Ko bakiso?”
Girgiza kai tayi kafin ta amsa “ba matsala” amma zuciyan ta tunani ta ke kaji min bawan Allah bayan ka gama yanke shawara kuma.
Flight insu karfe sha dayan safe ne so tun karfe Tara su ka kama hanyar gidan Salim in. Su uku za suyi tafiyan so already Umar yana can.
•••
Taji dadin zaman ta da Maman Khalipha kasancewar ita mutum ce mai son mutane game da Jan su a jiki, ga Khalipha yaron yana birgeta sosai ya kan tuna mata khaliphan Anty Rukayya.
Kasantuwar maman Khalipha na da mai aiki nan da nan su ke gama aikin su.
Kullum za ta je Asibiti ta dawo ba abinda ta sa a ranta bare ya dame ta sanin irin matsalan da ta ke dashi. Tunda ya tafi ko sau daya bai kirata ba itan ma ko a jikinta dan ko ba ta daura a ka ba, har ba ta so ya dawo ma Dan ta fi jin dadin zaman ta a gidan.
•••
A gajiye driver ya sauke ta a gida, gabadaya yau a asibitin ta wuni ga ayyuka dayawa da tayi hakan ya sa tafiyan da tayi ma zuwa cikin gidan na karfin hali ne.
A parlour ta iske mai aikin Maman Khalipha ta fito da fruit a hannun ta tana kokarin sawa a fridge “yau kam nayi lattin dawo wa ba dai har kun gama aikin ba” ta fada bayan ta gaishe ta.
“Ai ko dai kadan ya rage”
Murmushi tayi ta nufi kitchen in tana kiran Maman Khalipha, sai dai maimakon ita wata kyakyawar mace ta gani tana kokarin hada soup. “Sannu da aiki” tayi saurin fada ganin sun hada ido da ita
“Yauwa Sannu” ta amsa tana smiling.
Hakanan Zahrau ke ganin kaman ta Santa amma she can’t really remember how.
Ganin komai ya kammala ya sa ta wuce dakin da take zaune domin ta watsa ruwa.
“Besty Ina Kika samo kyakyawa” fareeda ke tmbyn
“Kyakyawa Kuma? Ina Kika ganta?”
“Bata dade da shigowa ba ai da lab coat a hannun ta”
“Oh Zahra ta dawo kenan, IT ta ke zuwa”
“Ban San ta ba”
“Haba Matan Aliy ce fa”
“Oh really she looks familiar”
“Maybe kin Santa wurin tsohuwar Zuma”
“Kai Besty ai ya Zama history”
“Au you finally let it be kenan”
“Is not like I have a choice” ta cikin rawar kaman za ta yi kuka. Lura da hakan ya sa Maman khaliphan saurin canza hiran nasu gabadaya duk da dai jikin ta ya riga ya yi sanyi.
Ruwan zafi ta watsa saboda ta samu jikin ta ya warware don kam ta gaji sosai, nan da nan ta shirya ta iske su already a falo suna jiran a kira sallah don they are already done.
“Sannun ku da aiki” ta fada bayan ta zauna
“Sannu Zahrau yau dai an Sha aiki”
“Hmm ai ba a cewa komai, Su khalee boy yau azumin ake yi ne”
Daga kan Shi yayi hade da rike cikin Shi Yana bata fuska kaman da gaske azumin ya ke. Dukkan su sai da su ka dan dara.
“Ehmm Zahra Captain ya ce numbanki is not going through, in ce miki sun dawo but za su Sha ruwa a gidan Brigadier so ki shirya in yazo za ku wuce”
Shiru tayi jikin ta duk yayi sanyi coz har ga Allah ba ta son tafiya Kuma ba ta San wainan da zasu toya da Aliyu ba, ya kikirata ba tayi picking ba.
Dan Bata fuska tayi kafin tace “Kai Shi ko daga dawo wa? Gsky ni Maman khalipha ban son tfy gidanki da Dadi”
Murmushi ta yi “Ina ruwan Zahrau nima ban son ki tafi ammaba zan iya wa mijinki fashin ki ba kwanan da yayi Shi kadai ma ai ya Isa ko?” Ta fada tana daga mata gira
Sunkuyar da Kai tayi cike da kunya still dai ba ta son tafiyan
“Mommy wai Anty tfy za tayi” Khalipha yayi saurin mikewa
“Eh my boy Uncle Aliy zai zo ya dauke ta”
“Zance mishi ya barta Muna son ta ai yana da kirki zai bar Mana ita, Zaki zauna ko Anty”
Daga mishi Kai tayi tana murmushi, yayi saurin zuwa ya haye cinyanta kaman yanzu aka ce za ta tafin.
Ita dai Farida kala ba ta ce musu illa ma danna wayanta da take ta faman yi.
A haka a ka Kira Sallah, su kayi Sallah kafin su ka yi buda baki su kayi haramar tafiya Asham.
Fareeda da Zahrau kadai su ka je saboda Maman khaliphan ta ce zata zauna kar su Salim su dawo basa nan.
Driver ya sauke su a mosque in duk da dai ba nisa da gidan, sai da aka idar gabadaya su ka dawo Amma ba wani magana sosai ya shiga tsakanin su ba.
•••
Karfe Tara dai dai ya musua gidan Salim, burin Aliyu kawai ya ga Zahrau sosai yayi kewan ta, ko da ya ki kirat ba ta dauka ba hakura yayi ya kyaleta but ko da yaushe tana cikin ranshi, da azaman neman soyayyarta ko ta halin Kaka ya dawo.
Ko da su ka Isa falo su ka iske Matan Salim kawai ji yayi kaman ya tambayeta Ina ta ke, dube duben hanyan bedrooms ya dingayi har sai da ta dago Shi ta sanar mishi sun tafi masallaci, nan fa su ka hau mishi tsiya Shi dai yake kawai yake nan ta ke sanar mishi tare ma da Fareeda su ka tafi, he just blushed yana tuno old memories, Allah sarki he will never forget about her sbd da irin tsaftataciyar son da su ka wa junan su but Allah bai yi ba.
A haka Mijin Faridan ya iso daukan ta but still ba su dawo ba. Aliyu na ganin Shi ya gane shi, Shima Yana ganin Aliyun ya shaida shi, a tare Suka sakan wa junan su murmushi sannan su kayi shaking hands.
Tun daga haraban gidan su ke Jin voices na tashi hakan ya tabbatar musu dawowan su Aliyun.
A tare su ka shiga Falon “To Frnd finally duba kofa ya kare” dare su kayi dukkan su, Aliyu na hararan Umar din da yayi maganan.
“Kaga laifin sa? Kwana nawa bai ga abun sa, ko da ya ke bari sai kayi Aure za ka gane what I mean” Salim ne yayi maganan Yana kashewa Umar ido
“Dadin ta ma na kusa, sai Kuma in ga Wanda za a wa gori again” dariya su kayi.
Sai a sannan su ka samu su ka gaishe su game da musu ya hanya. Zahrau daki ta nufa while Umar da Salim sai Jan Farida su ke tana maidawa wani Sa’in ta yi dariya kawai. Farida ce ta kalli mijin ta “sorry dear na barka kana ta jira ko” smiling yayi sannan ya ce “Ina Kika bar wayanki? Ammah na ta fada”
“Oh Yana jaka bara in dauko mu tafi ko?” Ta fadi hade da nufan dakin.
Ko da ta dawo already mijin na ta ya musu sallama ya fita waje, ita ma Sallaman ta musu, Amina na ce mata to “besty thanks, sai na zo kafin ku bar Abuja” A hankali ta Isa wurin kujeran da Aliyu ke zaune Wanda ya ke daga Shi sai kofa, he is totally busy with his phone, Kallon shi tayi sannan ta dan buga kujeran ya dago su kayi four eyes, Saurin dauke idon shi yayi “are we fighting?” Ta fada in a very low voice. Girgiza ma ta Kai yayi “sorry, I don’t know anything deserve to say” shrugging shoulders inta tayi “You are right” shiru ta danyi sannan tace “she is pretty” nodding head in shi yayi in approval sannan ya ce “thanks”
“All the best” ta fada tana heading out
“Besty haramun” Amina ta fada while Umar cewa yayi “Daki da waje dai ba nisa” giggling ta yi tana musu waving hand Shi ko Umar Mai da hankalin shi yayi kan waya kafin can ya dago ya kalli Amina. “Mommyn boy please Kira min ita mu tafi its getting late”
Ko da ta shiga daki sakan baki tayi domin ganin Zahrau ta yi bacci hadda ko kayan bacci a jikin ta, tada ta tayi.
“Kai Dan Allah please ki ce Mai ya banni Mana gobe sai in koma”
“Ehm ehm Zahrau ayi haka? Nikam ba ruwana ki dai tashi kwana nawa ko kewan mijinki ai Kya yi” tabe baki tayi tace “Allah am sleepy ya barni kawai gobe sai in koma”
“Shknn fito ki fada mishi da kanki, maybe ya yadda Amma ni ai har daki ya biyo ya zo ya fiddo ki”
Ba yanda ta iya hakanan ta tashi ta daura dogon hijab har kasa kan night gown in da ke jikin ta sannan ta fita, Maman khalipha na ganin ta fita ta yi saurin hada mata kayan ta hatta brush inta da ke toilet sai da ta fiddo ta sa mata a trolley sannan ta jawo shi Falon.
Ko da ta fito shi da Salim kadai ta tadda coz Umar na sauri ya tafi, Gabadaya attention in shi na waya so ta ma rasa ta yanda za ta mishi magana sai da Salim ya tabo shi. Kallon ta yayi sannan ya ce “ba dai har kin fara bacci ba?”
“Ehh nace da da ma ka banni a nan kawai tunda dare yayi gobe na dawo” habawa me Salim zai yi in ba dariya ba hadda rike ciki. Kallon takaici ya bishi dashi hade da Jan tsaki sannan ya juya wurin ta wani irin harara ya bita dashi ba shiri tayi saurin koma wa daki ta dauko kayanta luckily ta hadu da Maman khaliphan ta jawo kayan.
Kallon Salim da har yanzu bai dena dariyan ba yayi sannan yace “Kai fa ba fa na son iskan ci Allah”
“Yi hakuri ba ni na kar zoman ba” ya fada still Yana dariyan.
Maman khaliphan ta ja mata trolley in har motan Aliyn Yana ji Salim na fadin “madam sai Kuma a maida min mata Mai Jan trolley” banza yayi dashi.
Hugging inta Amina tayi tana fadin “nagode Zahrau sai na zo ziyara na musamman, toh Captain mun gode fa da Zumun ci”
“Nine da godiya Mommyn boy zan zo ma ai specifically “
Cewa tayi “haba Captain bakomai ai”
Ita dai Zahrau shiru tayi coz har ga Allah ba ta son tafiyan da kyar ta iya masu wavinKala bai ce mata ba har su ka isa gidan ita din ma shiru ta yi har su ka Isa, a tare su ka karasa cikin gidan sai dai kowa hanyar dakin shi ya nufa, ita dai burin ta bai wuce ta ganta kan gado ba saboda gajiyan da tayi ranar gabadaya.+
Ruwa ya watsa sannan ya canja kayan jikin shi zuwa light jallabiya, Falo ya fita ya kunna TV, Wayar sa ya ciro yayi dialling numban ta.
Har za ta kwanta ta ga Kiran nashi kaman ba za ta yi picking ba Kuma sai ta daukan.
“Ki fito falo” kawai ya ce mata ya katse wayan.
Dogon hijab inta da ta cire ta dauka ta Mai da sannan ta fita Falon.
A hankali ya dago ya kalle ta bayan ta zauna ji ya ke kaman ya tashi ya rungumo ta tsabagen soyayyarta da ya ke ji Yana yawo a jinin jikin shi gabadaya.
“Pls Ina son Shayi” ya fada yana Kallon ta ta kasan ido
Ba ta ce komai ba ta nufi kitchen in ta dafa Mai shayin da ya ji kayan kamshi, kan stool ta aje Mai cup, flask da spoon.
“Thank you” ya fada yana kare mata Kallo
Ganin ta tafi daki ya sa yayi saurin kiranta “dawo Ina son magana da ke”
Ba musu ta dawo ta zauna, kusa da shi ya nuna ma ta ta matso ta zauna.
“Fatima” ya Kira sunan ta, Dan dagowa ta yi ta kalle shi sannan ta sadda kanta kasa.
“Me yasa na Kira ki ba kiyi picking ba” shiru tayi ba ta ce komai ba don ko ba ta da abin cewa.
“Naga Alaman you don’t even Miss me ko kadan ko?”
“Dago kanki muyi magana Mana” ya fadi a hankali, dago kanta tayi Amman ba ta facing in shi.
“Ba ki son Zama da ni ko?” Girgiza mishi Kai kawai tayi
“Dan Allah ki dinga bani amsa, kinsan i hate all this ban son ki yi provoking Ina inzo inyi abinda Zan zo Ina da na sani, help me pls”
Tasowa yayi ya karasa inda ta ke, a kasa take zaune Daman, gab da ita ya je ya zauna, da sauri ta ja baya, Girgiza ma ta Kai yayi ya kara matsawa kusa da ita dab da dab ta yanda su kan iya jiyo numfashin junansu, Tsabagen tsoro ji ta ke kaman kirjin ta zai fito Shima ya fahimcin hakan sai dai Shima nashi kirjin bugawa ya ke sosai kaman zai fito fili.
Hannun ta ya riko duka biyu ya zuba ma ta fararen idanuwan shi cikin na ta, saurin sadda Kai ta yi kasa ya sa hannu a fuskan ta ya dago ta ta yanda su ka fuskanci juna, “Fatima” ya Kira slowly da wani rin murya da shi kanshi bai San yana da ita ba.
“Am sorry please kinji” ya fada cikin rawan murya, gyade kanta tayi da sauri saboda ita har ga Allah a takure ta ke ta kosa ya sake ta.
“Na San ba kijin dadin Zama dani kawai ba ki da choice ne Amma ni Ina son kasancewa tare da ke, Dan Allah ki bamu Daman mu fahimci juna ko ma samu Daman albarkan wannan aure na mu da ya fita daban da na mutane” a hankali ya ke maganan ga wani irin rawa da muryan nashi ya ke daga ita har shi gabadaya jikin su rawa ya ke sai dai kowa da nashi dalilin rawan jikin, ita dai zallan tsoro ne da ya mata katutu daman Zahrau da tsoro balle ga dodon a gaban ta gabadaya, shi ko wani irin shauki ne yasa haka, zuciyar Shi sai harbawa ya ke, hannun ta da ya rike ba karamin affecting in shi yayi ba Yana Jin kaunar ta a kowani sashi na jikin shi, ji ya ke kaman ya jawo ta ya rungumeta kam kam inda dama ma ya maida ta jikin shi gabadaya. There is not doubt ya sa sakan yan abubuwan da ya dinga ma ta a baya ne ke bin shi, he don’t even know how to confront her and confess his deep and endless feelings for her, Amma dai ya daukarwa kanshi alkawarin koya mata son shi.1
A hankali ta yi kokarin zare hannun ta daga nashi Amma ba ta yi succeeding ba “Uncleeee” ta fada tana Kallon cikin idanun shi, ganin irin Kallon da ya ke mata ne ya sa ta dauke idon na ta saboda there is no way za ta yi believing abinda ta ke gani cikin idon shi, ajiyar zuciya Mai karfi ta sa ke sannan ta ce “Am sorry but you are selfish” a razane ya dago Yana Kallon ta, gyade mishi Kai ta yi “Na San kana komai ne saboda gudun fushin Ammi da Abbah akan ka Amma ba matsala Kila kaddara ta ce hakan” ta fada kafin ta saki wani irin kuka Mai sosa rai.
He is speechless, ya ma rasa abinda zai yi ga kukan ta da ya ke Jin har cikin zuciya, Handkerchief in shi ya dauko ya Mika mata bayan ta yi calming kan ta ta rage kukan, he feels so guilty Dan tunda har ta iya bude baki tayi magana abin ba karamin cin ta yake ba Sarai ya San halinta, she hardly talks ma sai Kuma da alamun za ta yi riko”
Ba musu ta amsa ta share hawayen ta “Bakomai as Always za ka samu abinda kake so” ta fada tana kokarin tashi.
Riko hannun ta yi ya maida ta zaune “No let’s talk please, spill it out Dan Allah ba Dan ni ba”
Ba musu ta cigaba da magana “Tun tasowa ta you are always harsh on us, ka nuna Mana kyama da hantara kaman ba jinin ka ba unfortunately aka aura ma ka ni, Knowing well tsoro da fargaba ma kadai sun ishe ni Amma ba ka banni da wannan kawai ba, Ka tsangwame ni ka yi hitting Ina several times, zagi da cin mutunci ba wanda ba Ka min ba Uncleeee bayan kasan ko kadan ba laifina a ciki, har asibiti ka sa na kwanta” ta fada tana lumshe idanu cike da nuna jin zafin abin. “After all this, ban San me Mami da Abbah su ka ce Maka ba but nasan su Suka say ka same ni har ka bani hakuri, hakuri da ba Ka damu nayi ko banyi, it was not even genuine Kai Dai kawai burin ka in hakura in biyoka mu zauna ba tare da kayi la’akari da halin da Zan shiga ba balle Kuma ra’ayi na akan hakan Kai Dai kawai kayi fulfilling na ka burin, haka zamana gidan nan duk abinda kake so shi kake so ya faru sai dai da kaman wuya faruwar hakan abu Daya na sani Zan jure Zama har karshen rayuwata Amma Kuma ba Zan iya kara binka a duk yanda kake so ba, ni ma mutum ce kaman kowa, I have my worth, feelings and dreams”
Kara lumshe ido tayi tana expecting ta ji ya kwashe ta da Mari kaman yanda ya Saba.
Kallon ta ya ke har ta gama bai taba ganin ta yi dogon magana ba sai yau, a jiyan zuciya yayi a hankali ya jawo ta jikin shi ya sa hanky Yana goge ma ta hawayen da ke fitowa daga cikin idanun shi, mutsutsu ta dinga yi tana son kwace wa daga rikon da ya mata “Duk abinda Kika fada haka ne ba kuskure ko kadan a cikin Shi Amma ki sani dukkan Dan Adam ajizi ne, Dan haka gani a gabanki Ina Mai rokon yafiya a gare ki Fatima Dan Allah ki yafe min am so sorry”
Kallon yanayin fuskan shi tayi da idanuwan shi, Saurin Girgiza Kai tayi a zuciyan ta tana fadin “no hakan ba zai taba yiwu ba” Nadaman da take gani cikin idanun shi is fake ba abinda ke cikin zuciyan shi da ya wuce zalunci da mugunta, he have his reason for doing this. Ko kadan bata karyata zuciyan ta ba.
Kafin ya ankara har ta ruga ta bar wurin, Wani irin sarawa yaji kanshi nayi da sauri ya rike Yana fadin “Ya Allah! Help me” a daddafe ya karasa dakin shi, Ranar daga ita har shi ba wanda yayi sahur.
Washegari, ya Kama Friday. Bai da aiki sai Monday saboda course in da su ka je. Sai dai zaku su hadu da Umar akwai tattaunawan da zasu karasa akan shirye shiryen bikin shi Umar in.
A falo ya iske ta tana zaune, shaf ya manta da zata asibiti a rana da alamun Kuma da Shirin ta ta fito “Ina kwana” ta gaishe tana facing kasa.
“An tashi lfy?” Ya fada yana mata murmushi sai abin ma ya so ya Bata tsoro la’akari da yanda su ka rabu jiya.
“Meyesa baki kirani ba? So kike kiyi latti?” Girgiza mishi Kai tayi, he hates body language in da ta ke mishi but bai da wani choice a yanda ya ke ji ranshi ma gabadaya zai iya sadaukar ma ta.
“Mu je in sauke ki, ya fada yana sa links”
Sai da ya fita gidan sannan ya kalle ta hakan yayi dai dai da juyowan ta, Four eyes, Murmushi ya sakan ma ta hade da kashe ma ta ido Daya.
“Fatima na nemi yafiyan ki ba kice komai ba”. Shiru tayi ba tace komai ba
“Baki yafe min ba ko? Shknn fada min me Zan miki ki hakura ko ma mene zanyi saboda ban son inta Zama da hakkin ki a kaina” a hankali ya ke maganan hankalin shi na kan driving in da yake.
“Ni ba komai Kuma bani kadai ma kayiwa abubuwan ba ai” Kaman daga sama ya ji siririyar muryar ta.
Juyo yayi ya kalle ta in shock “da su wa? Su Ummiy”
Daga mishi Kai tayi
“In su ka yafe min kema Zaki yafe min” kan ta kara daga mishi
Daganan Bai kara cewa komai ba har yayi dropping inta ya wuce gidan Umar.
Ba komai ya sa ta yin hakan ba sai tunanin da tayi in dai da gaske Nadaman yayi ai su Maijidda sun yi deserving ya basu hakuri coz dukkan su ya takura wa rayuwar su, a ganin ta ba zai iya ba Amma za dai ta gani.
Bin shi da Kallo Umar yayi har sai da ya Kai aya “Ai ga irinta nan Aliyu da nake ce ma ka ka daina takurawa rayuwansu gani kake kaman bayan su nake bi yanzu wa gari ya waya? Call them kannen ka ne duka biyun uwa Daya uba Daya ko ba komai ka goge tabon da kake dashi a wurin su, taimaka ma tayi”
“Ko numban su Banda shi Fa”
“Kira Mami ko Ammah” ya bashi amsa.
“Yes Ammah is the best solution” ya fada a fili, nan da nan ya Kira ta bayan sun gaisa yayi requesting numban su, har tsiya ta mishi kafin ta tura Mai.
Maijidda ya fara Kira sanin cewa ta fi saukin Kai. Yana magana ta gane muryar shi “Uncleeee Ina wuni” ta fada a daddafe there is not doubt har yanzu tsoron shi bai barta ba
Amsa gaisuwan na ta yayi hade da tmbyn Mai gidan nata “Ya akayi Kika gane ni ko Daman kina da numbata”
“Aa fa muryar ka na gane”
“To Shknn just call to say Hi tunda ku ba kwa neman na at all ko har yanzu Muna fadan ne” Girgiza kan tayi kaman Yana gaban ta “Aa ban San za ka so na Kira ka bane”
“Saboda har yanzu Kuna rike da ni right? Anyway, we are siblings Kuma Yan uwa ba sa fada so am sorry” ita dai gani ta ke kaman a mafarki, she still couldn’t believe it.
“Lah ba komai Uncleee and we are also sorry”
“So are we good?”
“Yes we are”
“Ko kefe, I will be expecting your call” ya fada kafin su yi sallama.
Ummiy ya kira, the same process da yayi na Maijidda ya mata sai dai ita ta kasa shiru sai da ta ce.
“Kai Uncleee ni dai am so suprise gsky, In my entire life ban taba tunanin za ka Kira ni ba”
“Why? Ke Kika dauki abin da zafi ai, hope my apology is accepted”
“Sure, Ina Zahrau?”
“She is fine”
“Alhmdlh now I feel comfortable she is in safe hand”
Dariya yayi Yana fadin “Ummiy kenan ba ki da dama”
Ko da su ka Kira Zahrau su ka fada ma ta she is so shocked Amma sai ta ji zuciyan ta na fada mata he is definitely up to something ba a banza yayi ba…Dawowan su kenan daga tahhajud, a Ranar aka fara so ba karamin gajiya su kayi ba, daurewa tayi ta je kitchen tayi warming abinci da ta dafa duk da ma a warmers su ke, ta ajiye akan dinning “Na gama” ta fada mishi “okay let’s go” ya amsa Yana Kallon reaction in fuskan ta coz ba ta taba cin abinci in Yana kan dinning in ba “muje Mana time na tafiya”1
Har za ta musu sai Kuma ta fasa ta bishi kujera ya jawo mata kusa dashi alamun ta zo ta zauna.1
Zaman ta yi sannan tayi serving in shi Dan ta San abin da zai ce next kenan. Ta jawo plate za ta zuba nata yayi saurin rike hannun nata, Wani irin shock ne ya ziyarce su duka biyun da sauri ya dauke hannun shi “mu ci wannan” ya fada ya tsare ta da Kallo kaman zai cinye ta. 1
Kasa sakin jiki tayi taci abincin saboda Kallon da ya tsare ta dashi shi ko gogan sai aika abin shi ya ke har da Kari duka duka Bai fi spoon bakwai tayi ba. Ta Sha jin cewa Yana da cin abinci Amma yau da ta gani da gaske tayi matukar mamaki sai da ya koshi sannan ya Sha ruwan shayin dake gaban shi hadda fruits.1
“Fatima ba fa kici abincin nan ba” ya fada yana Kallon ta cike da so1
“Am okay” ta amsa
Bata rai yayi ya fito mata a Uncle Aliyun shi da suke matukar tsoro, harara ya kara bin ta dashi “kici ko in miki dure” ya fada ba alamun wasa a fuskan shi.2
Sanin zai iya aikatawa ya sa ta fara cin abinci kaman maganin ta ke ci dariya ma ta bashi “dadin abin ma ke Kika dafa in ma Bai miki Dadi ba” ya fada yana tabe baki, itan ma dariyan ya so ya bata Amma sai ta shanye. Har fruits in sai da ya sa ta Sha har ta ji ta koshi cikin ta ya cika ba sauran space Amma Bai kyaleta ba, ganin za ta Mai kuka ya sa ya kyaleta ko a tunanin shi cin su daya ne oho?1
“Ya alkawarin mu?”
“Ai ai na yafe”
Wani irin annashuwa ne ya ziyarci hade da wani ajiyan zuciya “Alhmdlh, Shine ba ki fada min ba”
Ita dai shiru tayi tana Kallon kasa gabadaya ta gaji da zaman, Kiran Sallahn da aka saki ne ya sa ta yi hamdalah a zuci unknown to her ya fito fili, Bai ce mata komai ya tashi ya nufi masallaci. Rokon shi daya Allah ya sa ta so shi ko da rabin son da ya ke mata ne.
Weekend ne ba aiki, ko kadan ya gaza rintsawa bayan Asuban hakan ya sa ya dauki Qur’ani ya cigaba da muraja’an da yake yi, sai da yayi Izifi goma sannan ya ajiye addu’a sosai yayi mafiyawanci na samu Zaman lafiya da soyayya tsakanin shi da Matan shi ne, Wurin Umar ya wuce bayan ya gama ranar tare su ka Sha ruwa, Zahrau dai ta Sha aiki baiwar Allah. Gogon sai sannu da aiki ya ke mata ita dai karfin halin sakin fuska ta dinga yi ganin Umar Yana tafiya ta koma yanda ta ke da coz she can’t keep pretending.
Tun da ya gane Yana takura ma ta Yana takura ma ta ya daina shige ma ta sosai gudun raini ya shiga tsakanin su illa iya ka suna gaisuwa Kuma at times Yana kokarin Jan ta da hira tana nuna bata so.
Five days to Sallah ya same ta a kitchen tana kokarin hada musu abin Shan ruwa, Salin alin ya fara Taya ta ba Wanda ya tanka ma wani “ki shirya zamu tafi Zaria gobe” kaman daga Sama ta ji ya fada Yana yanka fruits, Saurin Kallon shi ta yi ya daga mata kai, kasa boye murnar da ke ranta tayi, Murmushi ta saki nan da nan.
“Kin fi son can ko?” Ganin Bata amsa shi ba ya cigaba da magana “shknn ki shirya kayan ki gabadaya tunda can in kike so sai ince wa Abbah da Mami kince ba za ki iya Zama Dani ba ga amanan su na maido”
Da mamaki ta dago tana Kallon shi Amma ko kadan ba alamun wasa a fuskan shi “ni na fadi haka?”
“Baki fada ba amma actions inki sun nuna Kuma ance labarin zuciya a tambayi fuska, Tunda ni kin nuna baki Sona sai in sawwake miki ki auri Wanda kike so”
Sakin baki tayi tana Kallon shi, tabe bakin shi yayi sannan ya fita kitchen in, ko da su kazo Shan ruwa kala Bai ce mata ba har su ka je Asham su ka dawo sai bayan Sallan Asuba ne yace mata “ki shirya da wuri 2 Zan bar garin nan” Yana magana Yana tafiya dakin shi hakan ya sa ta shiga ta fara tattara kayan nata.
Yana idar da Sallan Asuba ya Isa gidan straight dakin ta ya nufa ya iske ta gama shiryawa “ki fito mu wuce”
Akwatina biyu ya ga ta fiddo karamin trolley da na tsakiyan shi sai hand bag inta “Sauran kayan naki fa?”
Ita dai har ga Allah canjawan Uncle na bata mamaki yau Yana fara’a gobe kuma kaga ya hade Rai kaman bai taba dariya.
“Na barka Maka?”
“For what reason?”
“Ka ba wa Matan da zaka aura”
Hararan ta yayi sama da kasa sannan yace “tafi karfin tsumokaran ki ai”
Ba ta ce komai ba ta fidda babban akwatin, sannan ta dawo ta ja karamin ko Kallon ta Bai kara yi ba ballantana ya taya ta.
Bayan motan ta bude zata shiga, wani wawan kallo ya bita dashi ba shiri ta bude gaba ta shiga sannan ya ja motan ya bar gidan Mai gadi na mishi Allah ya kiyaye hanya ya daga mishi hannu.
“Haka za ki zarian ba abinda Zaki Kai musu?”
“Ina dashi” ta amsa
Sahad store ya nufa ya bukaci ta fita ba musu ta biyo shi, atamfofi, takalma da turarurruka su ka debo sannan su ka dau hanya.
Sai da Suka fara tsayawa gidan Anty Rukayya, Ana ta shirye shiryen bikin Nanah, Baban ta da kanshi ya Bai wa babban Yaya waliycin ta a cewar shi shi ya girmar da ita tun tana karama rabi da kwatan rayuwar a gidan ne.
Sai 6:00 pm su ka Isa Zaria, direct side in Mami ta wuce sosai tayi murna da ganin Zahraun nan fa hira ta kicime tsakanin ta da Hamza da Deedat, Su Yusra ma sunyi hutu.
Ko da dare yayi ta fara kokarin kwanciya Koran ta Mami ta yi ta wuce wurin mijin ta, ba wai Dan ta so ba ta tafi, Yana dakin shi na cikin gidan Bai wuce gidan shi ba.
Sallama tayi ya amsa “lafiya” ya bukata
“Mami ta ce inzo”. Kallon yanayin fuskan ta yayi yanda tayi kicin kicin kaman za tayi kuka, dariya ma ta bashi Amma Kuma sai ya fuske “to shigo ki zauna” karasawa tayi kujeran.
A hankali ya taso ya zauna kan kujeran dab da ita, ganin tana kokarin matsawa ya sa yayi saurin juyo da fuskan ta “Kina so in sawwake miki da gaske” girgiza Kai tayi sannan ta lumshe idanuwan ta ko kadan ba ta son hada ido dashi.
“Me yasa to?”
“Su Abbah ba zasu ji dadi ba” ta bashi amsa Kai tsaye
“So you choose to scarifice your happiness for them” gyade mishi Kai tayi.
“Amma Kuma you are not making them happy ai”
Kallon shi ta ke alamun tana neman Karin bayani
“Eh mana haka ake zaman aure? Ba su Abbah ba har Allah kina sabawa ma, I thought kinyi karatun islamiyya”
Shiru tayi saboda ta fahimci inda ya dosa, wayan shi ya dauka Yana dannawa sannan ya fara magana kaman ba da ita yake ba. “Nima ba Zan iya rabuwa dake ba Fatima sai dai ni ba Saboda su Abbah bane” Dan Jim yayi kafin ya cigaba da magana “kin San dalili?”
“Aa” ta fada a hankali
Murmushi yayi sannan ya juyo Yana Kallon kyakyawan fuskanta yanda ta ke sauke numfashi cikin kwanciyar hankali, da alamun yanzu ta rage mugun tsoron da ta ke mai. Yana Jin ta har cikin ran shi, yanayin da ya ke ji akanta Mai wuyan fasaltawa , Yana son ta sosai a yanda ya ke Jin kirjin shi na bugawa gani ya ke da ya rasa ta zai rasa rayuwar sa gabadaya ma.
Dago idon ta tayi don taga me ya hana shi cigaba da maganan da ya ke, karaf su kayi ido hudu, maimakon ta dauke kaman yanda ta Saba sai ta tsaya itama tana Kallon idanun nashi.
Saurin rintse idon ta tayi tana girgiza tana fadin No No No a fili, ba yau ta fara soyayya ba Saboda haka ita ba bakuwa bace a faggen sai dai tana son karya ta abinda ta gani a idon nashi, He can’t love her, abinda ta dinga ayyanawa a ranta kenan bayan hakan ma she is not ready for another love, Wanda ta yi a baya are okay for her, ba ta iya shiga wani risk in Kuma Daman yanzu ma ya lafiyan Kura…
Kallon ta ya ke cike da fargaba ba shiru ya kamo hannayen ta ya tsaida natsuwan ta wuri Daya hakan ya sa tayi saurin bude idon ta tana Kallon sakonnin da ya ke son isar mata sai dai tana son karyata hakan “Fatima na gaji, wlh na gaji da Kallon kiyayyan da kike min a cikin idanun ki baroro, Daman haka kiyayyan Wanda kake so ke da zafi?” Kallon shi tayi cike da mamakin kalmar So in da ya ambata, Gyade mata Kai yayi “Yes, Nima ban San ya akayi ba Kuma bansan yanda aka yi hakan ya faru ba, Ina sonki sosai Fatima so bana wasa, ki taimakeni ko ba za ki so ni ba ki goge kiyayyan da kike min Wlh Yana wargaza min duk wani walwalata, Help me pls” In baza tayi karya ba Amma kwalla ta ke gani ya fito daga idon shi, a hankali ya ke magana with a sorry voice.
“Uncleeee so fa? So kace “
“Na sani Fatima, Ina sonki kima daina doubting abinda kike gani a idanuna don Son ki ya riga da ya gama wa zuciya ta illa I can’t hide it anymore” Girgiza Kai ya ke Yana magana.
Zuwa yanzu kam ta gama tabbatar da gaskiyan da abinda Aliyu ke fada domin a zahira ta gani.
“Ban San yanda Zan yi ba, zaman lfy nake nema dake Amma ke kin kasa gane hakan, Kin San Ina da Saurin fushi Amma hakan Bai sa kin kwaucewa abubuwan da zai kawo fushin nawa ba, ba ma ki gudun a samu matsala Kuma kinsan ciwon da kike dashi. A kanki na koyi dauke Kai in an min abu, hakan ya sa na kam fita harkan ki na kwanaki ko Zaki canza, ke Zaki bada labarin ban son raini Amma ba ma ki gane fushi nayi balle ki gyara saboda bana gabanki, ba ki damu Dani nasan ni Mai laifi ne a wurinki Amma na baki hakuri kince min kin hakura Amma action in ki Bai tabbatar da hakan ba, Hakan ya tabbatar min Sona ne baki you, Kina da riko hakan ya sa Kika sa goge tabon da kike kallona dashi, Shin wai me Zan miki domin goge kiyayyan da kike min.”
Yanayin shi ya fara Bata tsoro, magana kawai ya ke sai kace Mai sambatu, Ta San so ta san illan shi hakan ya sa taji wani irin tausayin shi ya kamata domin ita kam ba ta taba Jin son shi ba ko kadan illa kawai ta San she is always uncomfortable in har Yana wuri.
Share zufan da ke keto mata tayi, ba ta Jin za ta iya kara son wani a zuciyan ta, Har ga Allah ta na Jin har zuciyan ta yafe mishi komai, Kuma za ta yi kokarin mantawa da abubuwan da su ka shude Amma ba ta Jin za ta iya alakar soyayya da shi dai dai Dana second Daya.
Ba ta Ankara ba ta ji hawaye Mai zafi na fita daga cikin idanun ta sai ji tayi yasa hanky Yana share ma ta hawayen, Idanuwan shi yayi ya jawur sai dai ba alamun kwalla a idon Shi da ka ganshi kasan ba karamin ciwo ya ke ji ba.
Murmushi ya sakan mata Wanda da ka gani ka San na karfin hali ne “No, ki daina kuka kinji”
Yanda ya ke maganan ma gabadaya Kara rikita ma ta lissafi ya ke, abinda bai gane ba a zaton shi kukan takuran da ya mata be Bai San shi ke sa ta kuka ban. A hankali ta fara yaddawa zuciyan ta hakurin zaman lafiyan da ya bukata ko da babu so za ta yi zaman ibada.
“Kana Sona?” Ta tmby kaman wani karamin yaro ya gyade ma ta Kai. “Then prove it” ta fada tana lumshe ido.
Murmushi yayi sannan yace “nagode” a kasan makoshi, itama murmushin ta Mai.
Ba ta ankara ba taji ya jawo ta jikin shi ya rungumeta kaman ta kwace sai ta kyale shi Kuma. A faffadan kirjin shi ya sa ta da farko jikin ta rawa ya fara saboda rashin sabo Amma da tayi luf a kirjin shi nashi da ya mata kaman bargo sai taji yanayin ya mata Dadi tana sauraran saukan numfashin shi a hankali a hankali ga kamshin turaren shi da ya mamaye jikin shi.
Shi ko gogan ji yake kaman ya Mai da ta cikin jikin shi gabadaya ga wani shauki da yake Jin Yana diban shi Kara rungumeta yayi Yana shakan kamshin turaren da ta bide jikan ta dashi.
Allah ya San Yana son Zahrau, fiye da zaton duk wani Dan Adam.
Sun fi minti goma a hakan kowannen su na sauke numfashi, a hankali ya cire ta daga jikin shi ya hade goshin su Yana Kallon cikin idanun ta Yana aika mata sakonnin daga nashi idon, kaman Mai jin bacci haka idon na shi su kayi gani tayi ba za ta iya jure eye contact in ma ta yi saurin lumshe idanuwan ta.+
Idanuwan na ta ya bi da kallo ya ga sun mishi wani irin kyau na daban hannu ya sa Yana shafa idanuwan kafin yayi faking in su da lips, tsigan jikin ta taji Yana tashi Kara lumshe idon ta yi da kyau gabadaya jikin ta sai rawa ya ke.
A hankali lustfully eyes in shi su ka sauka kan lips wani irin abu ya fara ji Yana fisgan shi Amma Kuma Yana gudun ta yi mishi mummuna zato, ya fiso ya bi komai a hankali, Yanda zai ma ta proving son da ya ke mata kaman yanda ta bukata.
“Za ki kwanta a nan ko mu tafi can gidan” ya fada Yana referring da gidan shi na Zarian.
“Can gidan” ta bashi amsa sannan ta bude idon ta
“Tashi mu je toh” Ita ji tayi ma tana kunyan shi hakan yasa ta sadda Kai kasa tana wasa da hannu black abayan da ke jikin ta.
“Ko in dauke ki ne?” Daga giran shi yayi sannan ya kashe mata ido Daya.
Smiling kawai tayi sannan ta Mike a ranta tana fadin “Namiji bashi da kunya”
“Kaya na na dakin Mami”
“Mu je mu dauko?”. Saurin girgiza Kai tayi tana zare idanu, ya gane kunyan mamin ta ganshi da ita ta ke ji.
“Shknn Zan sa Shahida da Yusrah su dauko ko Kuma Hamza”
Gyade Mai Kai tayi sannan ta bishi, Yana gaba tana baya ganin ba ta sauri ya sa ya rike hannun ta su ka nufi gidan nashi tanan cikin gida su ka wuce da ya ke akwai hanya.
A hanya su ka hadu da Deedat zai tafi dakin shi tun zuwan su sai yanzu su ka hadu.
“Ah ah ah Malaman makaranta” Aliyu ya fada cike da tsokana
“Ina wuni Yaya” ya fada yana sadda Kai kasa.
“Lfy kalau, ya students”
Amsawa yayi sai sannan Zahrau ta gaishe a kunyace ci ke da jin kunyan yanda ya gansu da Uncle in.
“Baby sis yau Kuma kunyata ake ji ne?”
Saurin sa Daya hannun ta tayi ta rufe idanun ta, hararan shi Aliyu yayi “Mata ta kake tsokana? Toh maza find your way”
“Kai Yaya Nima dai nayi zuciya auren nan Zan yi”
“Da ka kyauta Mana sosai”
Sallama su kayi ya wuce su ma su ka tafi.
a Falon gidan su ka yada zango, tana zama wayarta ya fara ruri. Sumayya ke kiranta, kunyan daukan wayan ta ji saboda ta Dade ba ta nemi sumayyan ba sai dai ita ta neme ta. “Pick the call Mana” ya fada Yana kare Mata kallo, Daurewa tayi tayi picking “Sumyyyy” ta fada a hankali.
“Zahraaah ba ki da kirki Allah”
“Sorry Sumayya nasan nayi laifi Amma Ina neman gafara”
“Au sorry fa na manta Matan aure na Kira at this time of the night”
Murmushi kawai tayi sannan tace “Allah ya shirye ki”
“Hmm Anyway, na Kira in fada miki ansa ranar biki na ne”
“Serious? Yaushe? Wa ye angon?”
“Dagaske na ke, December ending, da Al-ameen”
“Allah sarki toh Allah ya nuna Mana Amaryar Al-ameen Allah yayi” dariya Sumayyan tayi sannan tayi ending call in.
Juyo ta yi taga Yana Kallon ta, Abin ma mamaki ya ke Bata, kadan daga cikin ikon Allah kenan. Ta ayyana a ranta.
Tana fara Jin bacci ta fuske ta Mai sai da safe, kala bai ce Mata ba illa dai sanyin da jikin shi yayi, shi kanshi bai da niyyan wani Abu ya shiga tsakanin su yanzu sai ya koya Mata yanda za ta so Shi.
Ba laifi ta kan Dan sake kadan su yi hira Amma ba Dan ranta na son hakan ba, shi ma ya fahimci hakan shiyasa lokuta da dama ya ke kyaleta sbd Bai son takura ma ta duk da hakan ba karamin ciwo ya ke Mai ba, da Yana da dama da ya cire zuciyan shi ko ya huta da kaunar da ke addaban shi.
Ranar jajibari da safe ya kawo ma ta dinkunna da yasa aka Mata har kala biyar, tayi mamaki ganin tana da sabbin kayan da aka sa Mata a lefe wadanda ba tayi using ba, ta dai yi godiya kawai ta amsa.
Haka ma washegari Sallah, aiki ta yi sosai na kala kalan abinci da abin Sha su Yusrah su ka Taya ta da ke su Ammi na da masu aiki ga Kuma Ya’ya’n yan’uwa dasu ke gidan yanzu.
Aiko abokan shi na cikin Zaria sun zo sosai hadda wasu daga kaduna. Sai Ranar yawon Sallah su ka je Kallon Hawa tare da su Hamza da yaya Deedat gabadaya, ita dai Sallahn ba wai ya Mata Dadi bane saboda ba su Ummiy sai ta ji wani iri, ya zagaya da ita gidan Yan’uwa da abokanan shi karshe su ka je Family house insu da ke Unguwan alkali aiko sunyi farin cikin ganin su sosai.
Zuwa yanzu Zahrau ta gama amincewa Uncle Aleey na son ta da gaske ganin yanda ya ke kokarin kyautata ma ta ita in ma tana kokarin yin hakan sai dai har yanzu ba ta gama sakin jiki dashi ba ga zancen son shi da ba ta ji har yanzu, ta lura gudun raini ya sa ya ke share ta sometimes, ita kanta tana so ta canja but she just can’t.
Some days bayan Sallah su ka tafi kaduna tare da Ummiy da ta zo Zaria, da ke an fara shirye shiryen bikin Nanah, Gidan Anty Rukayya ya sauke su direct sannan ya wuce ba tare da wani maganan kirki ya shiga tsakanin su ba, ta lura kwana biyu fushi ya ke da ita but she choose to ignore it.
A can su ka iske maijiddah cikin ta ya fito sosai, nan fa Ummiy ta sa ta a gaba tana tsokana duk da ita ma tana kunshe da na ta karamin cikin.
Biki yayi mutane Kuma yayi armashi, Bridal eve su ka fara yi ranar Wednesday a gidan Anty Rukayya sai washegari aka yi kamu a guest house in Baban Nanah, Komai su ke bukata Ya Aliyu ke Kiran Zahrau ko su Ummiy su sanar dashi.
Ranar Juma’a bayan an sauko daga masallaci aka daura auren a nan kinkinau, Babban Yaya ne waliyyin Amaryar.
Da yamma motocin daukan Amaryar su ka isa gidansu da ke Unguwan rimi, bayan la’asar aka Kai ta can domin yin sallama da iyayen ta.
Yan matan amaryan da yayyin ta so su kayi su Bata musu lokaci a cewan su haka ake yi a al’adance. In akwai abinda Aliyu ya tsana ya biyo bayan African time, ga Yamma na Kara yi ga Kuma Shirin event da za su yi. Wayan shi ya ciro ya Kira numban Anty Rukayya ya na Mata complain.
Su na zaune su na hira abin su fuskan Amarya a rufe an ga ma Mata nasiha sai gani su kayi Anty Rukayya ta shigo dakin ta dago ta sun dauka wani magana za suyi sai su kaji tana fadin “In ba za kuje yanzu ba kuyi zaman ku mu kam munyi gaba” habawa da gudu kowa ya taso su kayi waje.
Daman a motan Aliyun za a Kai Amarya direct can Anty Rukayya ta nufa tare da wasu Aunties inta.
Gidan iyayen shi aka kaita da ke a Abuja za ta zauna.
Dinner za ayi a crystal garden by 9 pm za a fara, Gudun ba ta tym ya sa Amarya da kawayen ta su ka shirya da wuri, Aiko 8:30 dai dai Abokan angon su ka iso sunji dadin rashin African time in da aka yi.
“Alhmdlh yau ba za mu Sha mita ba gun oga” Salim ya fada cike da tsokana Yana kallon Aliyu.
Murmushi yayi “Ba kaman bikin wasu ba bah”
Dariya Salim in yayi ya na fadin “Zan Rama”
Bayan motan Salim aka budewa Amaryan ta shiga ita da angon ta, kawayen ko Motoci su ka nema su na shiga.
“Ke zo muje mu shiga motan mijin ki” Ummiy ta ja Zahrau su uku su ka nufi motan.
Murmushi ya sakan musu sannan ya bude seat in Mai zaman banza “Bismillah madam” ya fada Yana Kallon Zahrau.
Ita abin ma mamaki ya Bata ganin ta manta when last ya sakan Mata fuska sosai haka.
Mai da idon shi yayi kan maijiddah “ke Kuma a hakan zaki fita da dare” saurin sunkuyar da kan ta tayi “Mata dai akwai bidi’a Zan nemi mijin naki ai, ku shiga mu tafi”
A whatsApp group in su Ummiy ta tura message Uncleeee will never change.
Maijiddah: Allah ma ya taimake mu Manyan veils mu ka sa.
Ummiy: Wai Gsky Zahrau kina kokari, ko da yake na ga wani Kallon so yake bin ki da shi mu ma ya raina wa wayau.
Zahrau: me ya Miki? Daga fadin gsky? Tausayin ku ma yaji shi.
Maijiddah: Eyyeh!! Love tin tin su Zahrau an kamu
Ummiy: I can see, na yi shiru tunda depending mijinki kike Antynmu.
Parking yayi wurin da Motocin da suka iso su kayi sannan su ka fita, 11:45 pm su ka bar wurin dinner in ba wai Dan an tashi Aa Aliyu ne ya sa ka su a gaba hakanan su ka hakura su ka biyo shi.
Washegari, aka shirya Kai Amarya gidan ta da ke Abuja, bayan azahar aka tashi Nan da nan ko su ka isa, Gida yayi gida Ma Sha Allah komai ya ji, Amarya dai ta Sha kuka rabuwa da gida.
A nan su ka kwana gabadayan su hadda Zahrau ga mamakin ta Aliyu bai ma ta magana ba, Sai Washegari bayan sun tafi ita ma ta shirya komawa gidan ta.
“Wai ke ma tafiya Zaki yi?” Nanah ta tambaya kaman za ta yi kuka ganin Zahraun na hada akwati.
Dariya ma ta Bata “Nanah Aisha kenan, Nima gida na Zan koma”
“Kai Dai ba ki da kirki Allah Ina ba nisa ki bari sai anjima Mana”
Girgiza Kai tayi “Akwai abinda Zan yi gobe Zan je asibiti” ta fada tana danna wayanta da alamun Kira ta ke.
Sallama aka yi daga dayan bangaren ta amsa.
“Fatima…” Ya fada alamaun Yana sauraron ta
“Nace Daman Ina son tafiya gida ne”. Jim yayi kafin yace “okay, I will be on my way”
Cikin minti Ashirin ya iso gidan ya Kira ya shaida Mata.
“To Amarya ni Zan wuce” hararanta Nanah tayi “Umma ta gaida Ashha tun da baki da kirki”
“Sorry, kawata Gobe in na dawo asibiti Zan zo in Sha Allah, Daman Maman khalipha tace Zan kawo ta kinsan ita ma suna da biki a kano ne so ba ta sa mu zuwa naku ba sai yau ta dawo ita”
Tabe baki Nanah tayi “Na tmby ki ne”
“Allah ya huci zuciyan Amaryar Umar faroukh ni dai na tafi”
Murmushi Nanahn tayi “Shknn Zahrau”
Ko kafin ta karasa ya bude Mata motan, sallama ta mishi kafin ta gaishe shi, Yana murmushi ya amsa Mata “Har an gaji da gidan Amaryan ne?”
“No akwai abinda Zan yi a gida ne”
“Okay, Allah sarki baiwar Allah kin barta da kewa ita kadai”
Tabe baki tayi “Sabawa za tayi kaman yanda na Saba”
Some weeks later
Zuwa yanzu Zahrau ta gama amincewa da son da Uncleeee ke mata ta gani a idon shi, a aike ce sannan Kuma ta ji da kunnen ta sai dai me? Tausayin Shi ma ta koma tana ji Still ta kasa sakin jikin ta gabadaya dashi though dai akwai improvement sosai.
Sai dai me? Kwatsam kwana biyu ta fuskanci canjin yanayi daga wurin shi, Fuskan shi kullum a sake ya ke Amma kwana biyu gabadaya ya koma ta Uncleeee in da ta sani da Wanda take tsoro kaman Azra’ilu, ya daina Jan ta da hira ya Kuma daina shi shige Mata magana ma sai ya Kama ya ke hadasu.
Haka kurum ta ke Jin hakan bai Mata Dadi ba ko ba komai ta farawa Sabawa dashi sosai, to ko dai wani Abu ke damun shi?Hakan ta kasance Yau ma da ya dauko ta daga asibiti ma abinda ya ce Mata illa ya jira ta shiga motan sannan ya tada.+
Gani tayi she can’t take it anymore Kuma ta gaji, ya riga ya Saba Mata da fara’ar shi tun ba ta so har ta Saba “Uncleeee” ta Kira shi a hankali.
Juyowa yayi ya Dan kalleta sannan ya kauda Kai “lfy” ya fada kaman ta takura Mai
“Ehmm nace Daman baka da lfy ne?”
“Na Miki Kama da mara lfy?” Ya amsa ta a kule.
Shiru tayi tana mamaki Amma Kuma still taji ba za ta iya shirun ba. “Na ganka wani irin ne two days ko na maka wani Abu ne”
Girgiza kan shi kawai idon shi na kan tukin da yake “Toh ko dai wani Abu ke damun ka?”
“Yaushe na fara fada miki damuwata da Zaki tmby”.
Jita yi jikin ta yayi sanyi jin Amsan da ya Bata ba ta Kara cewa komai ba har su ka Isa gida.
A daddafe ta yi Sallan la’asar sannan ta nufi kitchen domin daura abincin dare, kafin Magrib ta gama komai ta sa a warmers gidan gabadaya ya dau kamshi, Kan Dinning ta shirya abincin sannan ta je tayi Sallah.
Zaune ta ke a falo tana Kallon wani Indian series a Bollywood kasancewar gobe Saturday ba za ta fita ya sa ta zaman Kallon immediately tana gama Isha.
Da sallama ya shigo Falon ta amsa Mai sannan ya Kara so “Sannu da dawo wa” ta fada
“Yauwa” kawai yace sannan ya nufi hanyan dakin shi.
“Akwai Abinci fa” ta fada tana Kallon shi tana son karantar yanayin shi ko za ta gane me ke damun shi.
“Na koshi” kawai ya fadi ya karasa daki.
Habawa, ji tayi kaman ta rusa ihu, ba ta yi tunanin abin har ya Kai Nan ba, Daman ita ma ba ta ci abincin ba ji tayi ma ba ta da appetite gabadaya Kallon ya fita ranta ta kasa fahimtar komai.
Abinci ta dauka Dan Kar ayi asara ta Kai wa masu gadi, Aiko Ranar kwana tayi tana tunanin abin, da ma ga ta da sa abu a rai.
A makare ta tashi washegari saboda baccin ta kalilan ne a Daren, Bayan ta yi wanka ne ta fita falo ta iske shi yana Kallon news, Zama tayi ta gaishe shi ya amsa kaman an mishi Dole.
Kallon flask in tea in da ke gaban shi tayi sannan tace “Uncleeee me Zan dafa ma ka?”
“Am okay” ya fada sounding not interested.
Shiru tayi ganin ko inda ta ke bai kalla ba ya sa Simi Simi ta tashi ta bar Falon.
Ranar kwata kwata Bai Mata Dadi ba sai taji dama ba weekend bane, Gashi Nanah ta koma kaduna Coz a can ta ke IT Maman khalipha ma Kaduna ta je Weekend in Nan. Fatima kawar ta ce ma ta Dan rage ma ta kewa saboda chatting in da su ke tayi a WhatsApp tana bata lbrn Sabon saurayin da tayi har ya zo neman izini a gun babanta. recently, su kayi fada da long time BF inta, she is so hurt but now sosai Zahrau taji Dadi ganin she get over him now, Dan ba karamin So ta ke mishi ba.
Kaman hadin baki suna gama magana da Fatima ta kashe Data inta Sumayya ta Kira ta.
“Hello”
“Are you at home” A Summyn ta bukata.
“Sure”
“Turo min Address in gidanki Ina Abuja”
Ba ta yi 30 minutes da and tura Mata message in ba ta kirata tana kofan gidan, Veil in black abayanta ta yafa kawai ta nufi waje tana ba maigadi ordern ya bude gate in.
Rungume juna su ka yi da Sumayya suna murmushi “Sweetheart ga Zahrau” ta fada ma Wanda ya kawo ta
Murmushi ya ma ta sannan su ka gaisa ya tafi akan anjima zai dawo ya dauke ta.
Daki ta sauke ta kafin suyi Sallah tare su kayi girki ana ta nishadi ana tuno old memories Nan fa su ka gangaro Kan Abdulrahmah Nan fa duk jikin su yayi sanyi, Addu’a su ka Mai sosai.
Su na falo kallo ya shigo gidan “Sannu da dawo wa” Zahrau ta Mai Sumayya ta gaishe shi tana ta hararan Zahrau. Faran faran ya amsa musu sannan yayi Daki Bata so tace Mai akwai abinci ya disgata ya sa tayi shiru.
Galala sumyy ta yi tana Kallon ta kafin ta Mike ta ja hannun ta la’akari da yanayin da ta shi ga tun shigowar mijin nata. “Zo kiji” ta fada tana janta.
Daki su ka shiga bayan sun zauna “Zahra don’t tell me har yanzu kina da problems da Ya Aliyu, Kar ki sa inji kunya”
Kiris ya rage Zahrau ta fashe da kuka Amma Kuma sai ta daure ta fara magana muryan ta na rawa “Aa sumyy wlh recently ne, ban San me na Mai ba”
“Eh too gsky da laifin ki Zahra, ba ki tmby koma ki yi dabarar da Zaki gano ni za ki sa ni kunya wlh, okay littafan hausan da kike karanta wa ma duk a banza su ka tafi kenan?” Ta karashe zancen ta na girgiza Kai.
“Ba haka bane, abin ya fi karfi nane, na ma sa magana share ni yake wlh”
“Tab lallai Zahrau da gyara wlh Kuma laifin ki ne, shi fa namiji yanda ka bi dashi ya ke tafiyar da Kai, Na farko ma haka ake tarban namiji?”
Sumayyan ta Dade tana Mata nasihohi kala kala da tunasar da ita dabarun mu na Mata, sosai ta ji ta gamsu Kuma ta amince da cewa hakan laifin ta ne, ko kadan ba ta damu dashi ba, ko ba ta son shi ai akwai hakkin aure, Tuba ta dinga yi wurin Allah sannan ta kudiri aniyan gyara rayuwan auren ta, Ba shakka yanzu ko ba ta son mijinta to tabbas akwai tausayi da shakuwa a tsakanin su ko don kyautata Matan da yake yi.
Tana idar da Sallan isha’i taji jikin ta na ma ta wani iri, Nan da nan ta shiga wanka ta fito, ta fi mintuna goma gaban mirror tana shafa cream, spray da humra sannan ta fara gyara fuskan ta. Wani rigo da wandon kayan bacci ta dauko cikin akwatin lefen ta ba taba using ba sai yau ta ji tana ra’ayi, Oud kala kala ta feshe kayan dashi sannan ta saka, ba shara shara bane sai dai suna da laushi sosai yanda za suyi dadin bacci, Gashin ta ta koma ta gyara sannan ta yi parking a tsakiya ta sa hulan bacci Wanda tare ya ke da kayan.
Jin motsin shi ya sa ta yi saurin daukan Abayan da ta ajiye akan gado Dan dai ba za ta iya fita haka ba. Fuskan ta faran faran ta gaishe shi hade da mishi sannu da zuwa kicin kicin ya amsa Amma Kuma sai ta daure ta ki yin fushi, Ganin ya zauna Yana kallo ya sa ta nufi kitchen, Shayi ta hada mishi Wanda ya ji kayan kamshi saboda ta San shi ya fiso a yanayin Nan.
Har Falon ta karasa ta ajiye gaban shi “Uncle ga Shayi” ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.
Kallon ya bita dashi ya ga ta mishi want irin kyau, ji yayi kaman ya jawo ta ya rungumeta, ganin fara’ar fuskan ta ya sa Bai gwalase ta ba Saboda ya San yanzu za tayi fushi Shi ko ta mishi kyau a haka, Yana son murmushin ta sosai “Ina azumi” ya fada Yana kokarin canja channel.
Dariyan da ya ji tana yi yasa ya juyo yana Kallon ta, galala yayi Yana Kallon natan, ba karamin kyau ta mishi ba sai a ranar ya lura ta na da dimple kanana. “Azumi at this time Uncle” ta fada tana lumshe idanu duk a cikin dariyan.
Shi gabadaya ma sai yanzu yayi realizing abinda ya fada ne ya sa ta dariya, shi kanshi bai San me ya Zo mishi ba ya ambato azumin. “Uncle” ta fada hade da riko hannun shi, wani Yar ji ya saukan mishi har tsakiyan kanshi a dalilin saukan lallausan hannun ta cikin nashi. “Ni ban San me na maka ba kake fushi Dani, Amma Dan Allah ka yi hakuri” shi dai Kallon ta ya ke kaman zai hadiye ta, sai da ta sake girgiza shi tana fadin “kaji, please, Dan Allah, am sorry, ba Zan sake ba” cikin shagwababban muryan ta da ya kanji ta na ma Amma da Mami ta ke magana, abin ya ma ta kyau sosai.
“Ba za ka hakura? Dan Allah fa nace” wannan karon jiki a sanyaye ta ke magana. Wani irin shauki ya ke ji Yana taso mishi tun daga tafin kafan shi har tsakiyan Kan shi, saurin lumshe ido yayi “me Kika min Fateeeeema?” Shi kadai ke kiranta da Fatima shi yasa duk sanda ya Kira sai ta ji wani iri, ga wuni irin salo da ya ke yi in zai fadi sunan.
“Ni dai ba sai na fada ba, Kawai dai Dan Allah ka yafe min, ban son kana fushi Dani”
“Meyesa?”
“Ban ji dadi Kuma Ina feeling lonely sannan Kuma Allah ya na tare da masu hakuri, remember mu ma fa mun yafe ma”
“Sun dai yafe Amma ke kam ba ki yafe min ba Fateeeeema, ban son me kike so in Miki ba”
“Wlh na yafe, kayi hakuri”
“Well, actions in ki ba su nuna hakan ba, why kike da riko bayan kinsan ba kyau”
“Shiyasa fa na ke ta ba Ka hakuri” ta fada kaman za tayi kuka hade da turo baki. Hakan da tayi ya sa tayi Kama da karaman yarinya sosai, to Daman shekarun ta nawa?
“Shekarun ki nawa” ya jefo Mata tambayan.
“20 ” ta amsa.
“Ashe har yanzu ke baby ce” ya fada Yana washe hakora
Murmushi ta yi sannan ta ce “toh ka yafe?”
“Sai kin min alkawarin za ki saki jiki Dani”
Da sauri ta ce “nayi ba gashi ma na fara ba”
Smiling yayi “sure, Bani shayin in Sha”
Da sauri ta zuba mishi a mug sannan ta Mika Mai, kin amsa yayi sannan ya nuna Mata bakin shi alamun ta bashi a bakin.
Zaro idanu tayi “Unclee kunya na ke ji” ta karasa hade da rufe idanuwan ta da hannu Daya.
Shrugging shoulders in shi yayi alamun matsalan ta “Tafi na yafe in ba za ki ban ba”
Da sauri ta bashi hakuri sannan ta matsa kusa dashi “To ai da zafi”
“Sai hura da bakin ki tukunna”
Zaro ido tayi “Is not right fa a hura abu da baki, Microorganisms su na shiga, Kuma they may be pathogenic suna leading to endocarditis”
Kallon bakin ta ya ke har ta ida zancen “Toh microbiologist ni dai a bani Shayi”
Wani mug ta dauko ta Dan fifita shayin sannan ta deba da spoon ta Kai bakin shi ba kunya ya bude baki Yana Sha har Sai da ya kare.
“Thank you” ya fada Yana murmushi
“Always welcome” ta amsa sannan ta Kai flask in kitchen.
“Wai ke ba Kya Jin zafi ne”
“Me ya faru?”
“Ki cire bakin abin Nan ki Sha iska ko in taso in cire Miki shi” ya fada ya tsare ta da idanu.
“No am okay, akwai sanyi ma still”
“So miye amfanin kayan?”
“Sleeping purpose” murmushi yayi sannan ya taso ya iso dab da ita sosai har suna iya jiyo numfashin juna, “Na fada Miki ban son musu ko?” Kallon ta ya ke sosai cikin idanu Yana hura Mata iska a kunnen ta ya ke magana.
A hankali ya sa hannu Yana cire ma ta Abayan, Rawan da jikin ta ke yi ya sa ta kasa Mai musu. “Seriously, Fatima am tired I needs a perfect marriage life kaman kowa, Its high time ma ace na fara ajiye yara, ban San time in da Zan mutu ba, ko so kike mu rasa masu Mana Addu’a?” Ita dai ba ta amsa shi ba illa ma kokarin gano manufar zancen shi da ta ke har ya gama zare Abayan jikinta ya rage daga ita sai nightie in “Wannan Kaya masu nauyin ma Kika sa wa after dress?” Ya fada Yana shafa gemun shi, ita dai jikin ta gabadaya rawa ya ke ga wani irin kallo da ya ke bin ta dashi duk a tsora ce ta ke ba ta Ankara ba sai ji tayi ya jawo ta ya manna ta da jikin shi sosai har wani sakin ajiyan zuciya ya ke Yana shafa Gashin ta, gam gam ya matse ta a kirjin shi ta yanda ba za ta iya kwakwaron motsi ba balle tace za ta gudu. “Fateeeeema wlh Ina sonki” a hankali ya ke rada ma ta a kunnen ta hakan ya karasa ta rawan jikin, ga wani feeling da ta ke ji Yana mamaye jikin ta “Pls help a soulllll kinjiiiii” Yana maganan ya na Jan karshe harafin su, sun Dade a hakan kafin ya sake ta slowly, tana Jin haka ta tashi da Saurin ta zata bar Falon, A hargitse ya fisgota, Kallo Daya ya Mata ta natsu sai dai rawan jikin da ta ke yi har yanzu “Not again please, wlh na gaji” In a pity voice yayi maganan idanuwan shi sunyi jawur. “I don’t even understand you again, one minute kin sauko another kin koma gidan jiya” Mikewa yayi bata Ankara ba taji ya cincibeta in a bridal style ya nufi hanyar dakin shi da ita bayan ya kashe wutan Falon, Fisge Fisge ta fara yi Dan har ga Allah ba ta shirya abinda ya ke Shirin yi ba, Kallo Daya ya Mata ta shiga taitayin ta, Zata yi magana ya girgiza ma ta kai, ba shiri tayi shiru sbd gabadaya ya koma Mata Uncleeee Aliyn da ta sani tana karama Wanda ta ke matukar tsoro…
Kakakarakaka.
Who is happy? Ni dai am not, Ina ji kaman Ya Aliyu is still acting selfish, ya kuka gani?
Me ke damun Zahrau ne? Zata saduda?