KUDIRI
CHAPTER 1
Akwatina shida ne ke jere gaban wasu mata, suna kallon abubuwan da ke cikin su daya bayan daya. Kowacce cikin su tana tofa albarkacin bakin ta, nay abo ko kuma gates da habaici. 6
Wata mace fara, mai daure da bakar atamfa ta na zaune a gefen su kan karamar kujerar zama. Ba ta ce wa kowa komai ba, don ita kadai ta san halin da ta shiga a lokacin.
“Tubarkallah!” daya da ga cikin matan da a ke kira da Tambai ta furta a yayin da ta dago wata atamfa wadda da ganinta sabuwar yayi ce.
“Lallai yaro ya yi kokari sosai. Yalwaji ta yi sa’a.”
“Lallai kuwa.” Wata ma mai suna Larai ta amince. “Allah Ya sa gidan zaman ta ne. su ma ‘yan uwan ta na baya, Allah Ya ba su kamar na ta.”
Duka suka ce, “Amin.”
Bayan sun gama kallon kayan auren, sai Tambai ta kalli wacce ke zaune a gefen nan, ta ce, “Wai ni yaya batun Laminde ne kam, Dada? Har yanzu ban ji an ce komai ba. Ko auren ne ba ta samu ba tukunna?” 1
Dada, wadda asalin sunan ta Amina ce, ta samo lakanin ta ne dalilin yadda kannen ta ke kiranta da shi. Ita ce babba cikin ‘Ya ‘ya ashirin da Allah Ya bai wa mahaifanta, sannan “yar usulin garin Bauchi ce. Lakanin Dadan ya bi ta zuwa dangin mijin ta har ma da ‘ya’yan da ta haifa a cikin ta. 2
“Na ta lokacin bai yi ba. In maganar ta taso ma ai ku ne ma su fada a ji.”
Tambai ta ce, “Yo kun ji min Dada fa. Ke da kike uwar yara, meye nawa in ba bada shawara ba? Kuma ba lallai ne a dauka ba ma.”
“A matsayin ki na kanwar mahaifin yaran, ba su da uwar da ta wuce ki.”
“Hmm, a bar kaza dai cikin gashin ta. Sau nawa aka yi, sai an ci an cinye tukunna na ke samun sudi?”
Dada ta mike, “Wannan kuma ke ya shafa. Bari na ga ko abincin ya nuna, in ya so na sa a zubo muku.”
Har ta bar dakin, cikin matan nan babu wacce ta tsoma baki cikin maganar su. Kowa ya sani, tsakanin Dada da Tambai, ba kasafai a ke shiri ba. Su na dai kula juna ne don ya zama dole.
Dada dai ta san kara zaman ta a dakin zai kai su ga gutsiri-tsome, wanda kuma bas hi ne ke gabanta ba. Abin da ke gaban ta ya fi karfin ta, ko duk wani tunanin ta. Tun daren jiya ko runtsawa ta gagara yi, ta rasa wurin da za ta jefa kan ta. 1
Ta iske biyu daga cikin ‘ya’yan ta mata uku da suka rage ma ta a gida a cikin ‘ya’ya shida da Allah Ya ba su ita da mijin ta Malam Sabo. Da ganin ta suka zauna da kyau cikin natsuwa.
Ko kallon su ba ta iya yi, ta ce, “Sai ku fito ku duba abinci, don iyayen ku su na jin yunwa.”
Muryar ta fayau, babu farinciki a cikin ta ko nishadi, ko ma alamar ba su umurni, tamkar yadda idanun ta su ke. Daga nan ta koma wajen sauran matan ta zauna. Wa su ma a lokacin su ke zuwa ganin kayan, don haka ta yi kokarin dauke hankalinta ta mayar zuwa gare su.
Ba ta da ikon yin abin da ya fi hakan.
* * *
Tun da asubar farko Asiya ta hura wuta a madafi, sannan ta dora ruwan dama koko. Bayan ta idar da sallar asuba ne ta dama kokon, sannan ta share tsakar gidan su tsaf.
A wannan rana ta na da abubuwa da dama a cikin kan ta, da ma cikin zuciyar ta. A wannan rana ta yanke aiwatar da hukuncin da ta yanke a zuciyar ta, cewar tilas sai ta fuskanci azzalumi, mayaudari kuma macuci.
A wannan rana ta yi alwashin kudirin kawo karshen komai, ko za ta iya warware tarkon da mahaifiyar su ta fada ciki.
Ta na aikin, ta na tunanin zaluncin maza. A sanin ta, mahaifin su bai san ya kula da su ba, don kawai su ‘ya’ya mata mahaifiyar su ta haife su. Bai san cin su ba, balle a ce magani ko sutura. Komai ya rataya a wuyan mahaifiyar su ne. 1
STORY CONTINUES BELOW
Ga shi yanzu ‘yar uwar ta Mariya ta ballo mu su wa ta ja’iba, wai cuta bayan rai. Su kan su ba su san yadda za su fita daga cikin ta ba, sai yadda Allah Ya hukunta. Amma a wannan rana kam,
Asiya ta yi niyyar ganin karshen komai. A wannan rana.
Bayan ta kammala dumamen safe, ta hada da kokon ta kai wa mahaifin su, wanda ke shirin fita bakin shagon san a sayar da kayan koli da ke bakin kasuwar garin su. Ba don Dada ta ba da umurnin hakan ba kila da ba za su ba shi ko gutsirin gaya ba.
Ta gaishe shi ya amsa cikin fara’a. Wata kila hakan ya na nasaba ne da cewar daya daga cikin ‘ya’yan sa za ta kauce a gaban sa, sannan kuma an ma sa kyautar kudi na naira dubu dari da hamsin a jiyan daga wajen wanda zai auri Mariya.
Sannan ya ma sa alkawarin canja ma sa ginin laka zuwa ga na bulok bayan ya bayar da diyar sa ga aure. Ya nemi Asiya ta tura masa Dada idan ta koma dakin su. Bayan ta ida sakon mahaifin nasu sai ta koma zuwa ga ‘yar uwar ta.
Mariya Sabo Ali ta na zaune bakin katifa tuntun din da ke dakin, ba ta iya yin komai. Daga kuka sai kwanciya. Ba ta iya ci, sha ko ma yin wanka, sai Asiya ta dage mata da gaske tukunna. A ganin Mariya, ta riga ta yi sallama da rayuwa, dalilin dorawa kan ta matsala babba.
Asiya ta kalle ta cikin ban tausayi. Kayan da yake jikin ta kwanakin sa hudu ke nan ba ta cire sub a tun da ta saka. Ba wai sun a da wadatar suturar ba ne, amma yanayin Mariya, ya ci a ce ta canja.
‘Yar gaye ce kamar ba komai. Komai tsufa ko kodewar suturarta za ta saka abin ta kamar diyar mai kudi. Har hakan na sa Dada yawan yi ma ta fada, cewa ba ta son tattalin suturar da suke samu da kyar.
Ko kadan Mariya ba ta taba kallon kan ta a matsayin diyar talaka ba. Ko ma a ce wadda za ta kasance matar talakan. Don haka ko ‘yar makarantar bokon nan da Dada ta yi fafutukar tura su tare da taimakon yayyen su mata da ke dakunan mazajen su, Mariya ba ta taba yarda ta nuna cewa daga kauye ta ke ba, balle gidan talaka. Ta kan nuna gidan su akwai kudi, akwai isa da bajinta.
Kawayen ta da yawa sun yarda da hakan. Sai ko na kusa da su ne suka san ba hakan abin ya ke ba. Ko a lokacin da Dada ke ziyartar su a makarantar WTC da ke garin Azare, Mariya kan ce wa kawayenta mai mu su wanke-wanke ce a gidan su. Asiya kuwa, shiru ta ke yi, ba ta iya cewa komai. 4
Wajen hutu kuwa, Mariya ta zabi zuwa garin Jos ne, wajen kanin mahaifin su, wanda suke kira da Baban Jos. A can masifar da suke ciki ta same su.
Sallamar da suka ji ne ta sa Mariya daga kan ta, ta kalli wajen da Asiya ke kallon ta. Ba ta san ma kila ta yi nisa cikin tunanin ta ba. Asiya ta leka, sannan ta ce, “Muhibbat ce.”
Tun sallamar ta suka gane mai muryar. Muhibbat ta gayar da Dada a tsakar gida sannan ta karasa wajen su. Sama-sama suka gaisa, sannan ta kalle su daidai, “Sai kawai na ji waya. Kun tabbata abin da ku ke son yi ke nan? Anya, ba kwa jin tsoro?”
Tsoro, kalma ce da a halin da suka tsinci kan su, ba ta da ma’ana ko tasiri. Asiya ta ce da ita, “Ni kadai ce mai zuwa.”
Muhibbat ta nisa, “Kun fada wa Dada kuwa?”
Asiya ta girgiza kan ta, “Ba lallai ba ne. mu dai idan kin zo ma na da su, to.”
Muhibbat ta dan yi jinkiri, sannan ta fidda kudi daga gefen marar ta cikin kullin bakin leda, “Kirga ki gani, near dubu biyar ne cif.”
Asiya ta karba ta na kirgawa, a yayin da Muhibbat ta ci gaba da cewar, “Ina ce dai ba za ki wuce kwana daya ba? Ni fa tsoro na ke ji.”
Asiya ta kalli Mariya, wadda idanunta suka yi hulu hulu tsabar kumburi, sun rine sun yi jajur tsabar kuka, wani kulliti ya makale ma ta a wuya na takaici. Nan ta kara jin karfin gwiwar kudirinta.
“Ba komai Muhi, Allah Yan a tare da mai gaskiya. Yanzu dai bari na shirya in ya so ki koma gida sai na biyo wajenki don ki min rakiya zuwa tashar mota.”
“Ni ma zan yi rakiyar.” Mariya ta furta cikin shakekken murya, ta fara yunkurin tashi ta na goge fuska tare da jan hanci.
Asiya ta girgiza kan ta, “Ki zauna Maree, ki yi hakuri kar ki kara dagula al’amura. In shaa Allah zan je na dawo kafin Dada ta fahimci abin da a ke ciki.”
Bayan Muhibbat ta fice ne Asiya ta shiga yin shirin ta. Ta riga ta shirya karyar da za ta yi wa Dada, na cewar za ta je Azare ne don ta karbo takardar shaidar kamala sakandaren ta, wato certificate.
Ba ta yi tsammani Dadar za ta amince ba tare da bincike ba. Wata kila abin da ke gabanta ne ya fi karfin ta. Ta tsani karya wa iyayenta, to amma wannan kam tilas ce. Ta na fatan Allah zai Yafe ma ta.
Karfe tara da rabi na safe ta shirya cikin wata farar shaddar ta wadda aka yi adon wuyan da zare mai launin gwal. Yayar ta Asabe ce ta yi mata dinkin a bariya lokacin sallar azumi. A lokacin ba ta saka shi ba don ya yi mata yawa sosai. A yanzun ma sai da ta sa a ka rage shi, don tayi burin saka wa ne a bikim Mariya ita ma ta gwangwaje. Sai dai kash!
Ta fito bayan ta yi wa Dada sallama, ta nufi gidan su Muhibbat. Duk wanda ya gan ta cikin farar shaddar ta da hijabi fari sol zai ga ta haska. Sai dai amma zuciyar ta tamkar gawayi ne wajen baki.
Ta na tafe garin ko haske bay a mata. A duk lokacin da ta hadu da wani namiji ta na wucewa sai ta tuna Mariya da ma mahaifiyar su.
Tabbas, maza sun cika azzalumai. Ba ta san dalilin zaluncin sub a, amma an dade a na ruwa kasa tana shanyewa. A wannan rana ta yi kudirin fuskantar azzalumi daya domin ta kawo karshen matsalar su. A yau za ta nema mu su adalci, ko a na ha-maza ha –mata! 1
* * *
Karfe biyar na yammacin wannan rana Asiya ta sauka a tashar mota da ke kasuwar Muda lawal da ke garin Bauchi. Ta sha wahalar gaske, ganin irin yawan tsayawar da motar da ta shiga ta yi a hanya.
Ga yunwar da ke kwakular ta, ga kuma bacin ran da ta fito da shi daga gida.
Ba ta taba zuwa cikin garin ba. Iyakar ta, wucewa zuwa Jos. Nan ma sau biyu ta je, lokacin da aka yi bikin ‘yar baffan na su da kuma lokacin da ta raka Dada zuwa gaisuwar ta’aziyyar rasuwar matar sa. Don haka, ganin kasuwar a cike ya sa ta dan razana, amma ba ta janye daga kudirin ta ba.
Ta samu mai keke Napep, ta tambaye shi ko ya san asibitin Sauki. Cikin sa’a ya shaida ma ta cewar ya sani. Ta shiga ya ja, yana tafe a hankali.
Ta rika jin tamkar a dofane take. Kamar ta zama tsuntsu ta je ta yi abin da ya kai ta. Wannan wahalar da ta sha ma kadai ya ishe ta. Ga garin ya fara dishi-dishi na duhu. Tun a kan hanya ta bar duba agogon wayar Nokiar da Mariya ta ba ta a lokacin zuwan ta. Ta san lokaci ya kure, amma babu yadda ta iya.
Lokacin da ya sauke ta a kofar asibitin, sai da ta hadiye yawu da kyar. Asibitin babba ne, ginin bene. Ya na tsaye tamkar dutsen garin su. Sai gani ta yi kamar zai kifo a kan ta. Ta roki mai keke Napep da ya tsaya ya jira ta, ya kuwa amince.
Ta na tafe, zuciyar ta na bugun goma-goma. Idan dai wannan shi ne asibitin, to yaya girman mai shi ya kasance? Ta na taka sumuntin interlocking din kamar wadda ke taka zuciyar ta tsabar fargaba. Amma ba ta fasa ba
Ta lura da harabar asibitin, a gewaye ta ke cikin furanni launi kala kala. Ga kamshin da suke bayar wa. A kalla, ta dan ji sassauci kadan.
Jikin benen kamar da dutse a ka yi shi, ta taba gani a garin Jos, dan baffan ta yake mata bayanin cewa wannan din ‘wall tiles’ a ke kira. A lokacin ta yi tunanin bayan tiles din kasa har ma da na bango?
Mutane suna ta shiga ta fita kamar babban asibitin garin su, wato Dagauda. Lokacin da ta kai bakin kofar shiga, sai d ta yi jinkiri,zuciyar ta ta na yamutsi don taraddadi. Shin yaya abubuwa za su kasance idan ta fuskanci wanda ta fito nema? Me zai ce idan ya ji abin da ya kai ta?
Ta yi kyakkyawar nisawa, sannan ta hura iska ta bakin ta. Komai ta fanjama fanjam!
Da wannan ta tura daya daga cikin manyan gilas na kofar shiga, wadda ta kai ta zuwa ga wata farfajiya babba mai dauke da kujerun zama ma su tarin yawa masu fuskantar gabashin dakin. Cikin da sanyi amma ba sosai ba. +
Wata kila don tiles din da ke baibaye da kasan ne ko kuma iyakwandishan din da ke kunne. Kamshin Dettol ya riski hancin ta.
Akwai wani kabet babba, wanda da gani takardun fayel fayel ne dankare cikin sa, sannan ta lura da wata ma’aikaciyar da ke zaune a bayan wani makeken ginin da aka baibaye saman sa da duwatsu masu sheik na marbles launin ruwan kasa. Ta nufi wajen ta, ta lura da silin din da ke wajen na zamani ne wato POP.
Ta dan tsaya muhawarar yin sallama wa nas din nan, wadda da ganin kalar ta ba bahaushiya ba ce. Karshe dai ta yi ma ta sallamar. Ganin ba ta dago kan ta ta kalle ta ba, ya sa ta ci gaba da cewa, “Ina son ganin Dokta Yusuf ne.”
“Ki na da appointment ne?” Nas din ta tambaye ta cikin murya kasa-kasar da sai da ta dan duka sannan ta ke iya jin ta.
Ta amsa, “A’a. Daga Dagauda na zo ganin sa.”
Nas din, wadda sunan da ke sakale a gaban aljihun ta ya nuna Bridget, ta ce, “Kawo takardar da a ka turo ki da ita daga can asibitin garin naku.”
Asiya ta ji zuciyar ta ta zo bakin ta. Ba ta yi tsammanin samun matsala ba. Don haka dai ta amsa da cewa, “Ba daga wani asibiti na zo ba. Zuwa na yi don na gan shi.”
Bridget dai ba ta daga kai ta kalli Asiya ba har a lokacin, rubutun ta kawai ta ke yi, “To za ki bude fayel a nan. Za ki biya kudin a wancan dakin da ke kallon nan.”
Da yatsar ta ta nuna wa Asiya wata taga, wato window wadda wani namiji ke zaune kan tebur a ta cikin sa. Ta lura an rubuta ‘Cashier’ a saman sa. Ta tsaya yin muhawara cikin zuciyar ta. Shin ta sayi katin da zai ba ta damar ganin sa ne ko kuwa? Ita dai lafiyar ta kalau, magana ce kawai ta je ma sa da ita mai karfi. Ba ta kuma da lokaci a tare da ita. Sayen katin ba zai bata ma ta lokaci ba?
Ta yanke shawarar fadin gaskiya wa Bridget, “Ni ba na da wata cuta. Ina son ganin sa ne kawai.”
A lokacin ne Bridget ta dago ta kalle ta, “Sorry, marasa lafiya ne kadai ke iya ganin sa a nan. Ko ki bude fayel, ko ki neme shi ta wani waje.” Muryar ta dauke da umurni, fuskar ta a daure.
Asiya ta shiga roko, “Don Allah na roke ki. Wallahi wata muhimmiyar magana na zo da ita. Ba zan dade a ciki ba, na yi miki alkawari.”
Bridget ta sake kallon ta, wannan karon sama zuwa kasa, sannan ta koma fuskar ta. Ta lura da yadda ta tsuke fuskar ta, “Duba malama, nan tun safe mutane ne ke zaune sun a jiran ganin sa. Ta yaya zan bar ki ki gan shi haka kawai? Balle ma ba ya nan asibitin. Ya fita.”
Ta na gama furta hakan ta dan ja tsaki sannan ta ci gaba da rubutun ta, ko kallo ma Asiya ba ta ishe ta ba. Da farko dai kamar ba zata yarda da maganar ba, amma Asiya ta san ba ta da wata madafa illa ta yi hakan.
Ta shiga tunanin yadda za ta yi. Ga alama hanyar da ta biyo ba za ta bille ma ta ba. Sai fa idan za ta koma gida can garin su, ya kasance ta yi zuwan banza kawai.
Gida. Dakata. Idan an hana ta ganin sa a nan asibitin ai ba za a hana ta ganin sa a gidan sa ba. Nan take ta ji wani abu ya tokare ta mai kama da tsoro, amma ta matse. Ba tare da wani tunani ba ta sake neman taimakon Bridget, kan ta yi ma ta kwatancen gidan na sa.
Wannan karo kam hararar ta tayi, ta sake yi mata kallon biyu-taro uku sisi. Kai tsaye ta ba ta amsa, “Ban san gidan ba, amma na san a Kandahar ya ke.”
Muryar Bridget na nuna kyama, idanun ta dauke da kallon raini. Amma Asiya ba ta ji haushin ta ba. Ba za ta ga laifin na ta ba, don wata kila an sha zuwa neman na sa kamar yadda ta ke yi. Ta dai yi godiya sannan ta yi ficewar ta.
STORY CONTINUES BELOW
Ba ta san abin da ta ke yi ba, ta na tafe tana furta wa kan ta. Me ta ke tunani, cewa komai zai zo ma ta kamar yadda ta tsara? Me ta tsara ne? Yadda ta tsara ba yadda yake afkuwa ba ne. Anya? Tafiyar nan akwai alheri kuwa a cikin ta?
Ta iske mai keke Napep yadda ta bar shi, ya na jiran ta. Dadi ya kama ta. A kalla, shi bai jefar da ita ba. Ta fada ma saa unguwar da zai kai ta, shi kuwa ya ja, su ka fara tafiya. Ba ta iya cewa komai don rashin sanin tabbas. Ta dai yi karo da birki kala biyu, farko motar da ta shiga, na biyu kuma wannan Bridget din, amma bas u za su hana ta cimma burin ta ban a wannan rana.
Rurin hadari ya ja hankalin ta zuwa ga lekawa waje lokacin da suke kan hanya. Ta lura d yadda gari ya dau duhu, ya fara baki kirin. Ga walkiyar da ta ke walwalawa. Zuciyar ta ta kara tsinkewa. Tabdi! A na wata ga wata, wai a na dara ga dare ya yi. 4
Ta shiga tunanin Mariya, da irin halin da take ciki. Nan take ta ji kwarin gwiwar ta ta dawo. Idan har ta karaya, yaya za ta yi ita kuma? Ita fa ta yi ma ta alkawarin kawo karshen komai, kuma sai ta saduda tun ba a je ko ina ba?
Ta ai shiga damuwar irin abin da Dada za ta yi ma ta bayan an waste daga ganin kayan auren na ta. Fatan ta dai ta kai ga kudirin ta tun abu bai baci ba. Ta san Mariya ta na da laifi kana bin da ya same ta. Amma idan a ka duba ta bangaren Imani, sai a ce kaddara ce, wadda ta riga fata. Babu kuma wanda ya fi karfin ta, ko ma ya guje ma ta.
Suna tafe zuciyar ta cike da tunani, ta jiyo muryar mai tuka keken nan ya na ma ta magana, amma ba ta ji abin da ya ce ba. “Me ka ce?” Ta tambaya ta na mai mamakin yadda har hankalin ta yayi nisa ba tare da jin abin da ya ce ba.
“Na ce, ta ina ne zan kai ki a Kandahar din, don mun iso.”
Asiya ta kalli wajen da suke. Don tsabar tunani ma ba ta sa kan ta kallon cikin garin ba balle ta ga girman sa ko ma tsari da kyau. Kawai zuciyar ta cike ta ke da taraddadi. Ga shi ta na kallon gidaje a gaban ta bila-adadin, kamar wadan da a ka yi barin su. Ta ina za ta fara tambayar?
“Ka san gidan Dokta Yusuf Haruna?” ta yanke shawarar tambayar sa da farko. Ba mamaki ya san gidan, tun da direban kasuwa ne shi.
“Yusuf Dan-auta?” Ya tambaya cikin sani.
Asiya ta girgiza kan ta, “A’a, Dokta Yusuf Haruna dai.”
Mai keke ya dan yi murmushi, sannan ya ce, “Ai shi din ne Yusuf dan -autan. Ina ce wanda mu ka fito asibitin sa yanzun nan, asibitin Sauki?”
Ta gyada kan ta, “Eh, shi.”
Direba ya fadada murmushin sa, ya ce, “Ai ya tashi daga nan unguwar, ya koma can gaba da Inkil.” 5
Idan akwai tashin hankali a rayuwa to Asiya sai a lokacin ta ji shi. “Ina ne kuma gaba da Inkil?” Ji ta ke kamar taja direban ta shake shi. Meye na murmushi kuma, kamar wanda ya ma ta albishirin ta ci nera miliyan dari a wata gasar da ba ta san da ita ba?
“Kar ki damu, zan kai ki ainihin gidan na sa idan kina so.” Sannan ya ci gaba da tuka keken sa, a yayin da suka kara mikewa hanyar da ba ta san kan ta ba. Ga rurin hadarin da ke nuna ruwan sama zai iya zubowa a kowane lokaci. Karan rurin ya yi kama da wadda ke zuciyar ta.
Ta dai dan ji sanyi kadan, na cewa za a kai ta ta fuskance shi a wannan lokaci. Ko da ma zai kasance a tasha za ta kwana, tun da yanzu babu makawar faruwar hakan, a kalla za ta samu sukunin cewa hakar ta ta cimma ruwa.
“Ai na san likitan sosai wallahi. Mutumin kirki, mutumin arziki.” Mai keken nan ya ci gaba da fada ba a tambaye shi ba. “Ga shi da tausayin talakawa ko na kasa da shi.”
Ba wannan ta ke son ji ba, amma ba za ta hana shi maganar sa ba. Ya na da ‘yancin fadar ra’ayin sa, musamman ma da wata kila bai san shi kamar yadda ita din ta san shi ba. Mariya ta san shi dai, ta gyara tunanin ta. Ina ruwan ta da ko shi likitan talakawa ne ko na larabawa? Ina ruwan hanci da zakin miya kuma? 4
STORY CONTINUES BELOW
Sannu a hankali sai ga su a kofar wani gida, wanda ba don a ce a cikin wannan yanayi ta je ba, da tabbas ta tsaya ta yabawa gidan don tsarin sa.
Amma a wannan lokaci ta kara masa hauka a kan zalunci, a matsayin halayen Dokta. In ba mahaukaci ba, wa zai nemi jejin Allah sannan ya kera kankararren katafaren gidan da ke gaban ta? Kofar gate din sa abin kallo ne. 1
Ko da ta kwankwasa a ka bude kofar, ta ga kamar wata duniya a ka bude ma ta. Gidan bene ne mai hawa uku, sannan an rufe shi irin kwano na zamani.
Furanni kala kala sun kawata gidan hade bishiyoyi na ba da inuwa da iska. Harabar mai fadi ce, za ta rabin unguwar su a Dagauda. Ita ma an baibaye ta da interlocking masu launin ja da ainihin wanda ta san shi, wato kalar sumuntin. 2
Bayan ta yi wa maigadin abin da ke tafe da ita, sai ya nemi ta jira, bari ya sanar a ciki. Ta tsaya kallon jerin motoci ukun da suke ajiye gefe guda cikin wurin da a ka tsara musu na musamman. Hmmm, lallai ma. Wai likitan talakawa. A wacce duniyar ke nan?
Wato shi nan ya zo ya na more rayuwar sa, su kuma ya tsayar mu su da ta su ko? In ban da hatsabibi, har zai iya runtsawa bayan ya yaye wa wasu barcin su? Hmmm, to dai yau ga ta nan, har sai taga abin da ya ture wa buzu nadi.
Maigadi ya koma wajen da take, tsoho ne ba yaro ba. Amma sai da taga saurin sa. Ya ce da ita, “Baya gida, amma mahaifiyar sa ta na ciki. Ta ce ki shiga.”
Sai da ta fara taka wa a fadin harabar tukunna ta kara jin yamutsi a cikin ta. Ko don rurin hadarin da ke kara haduwa ne? ko kuma don walkiya, oho. Ta san dai ta ji sanyi, wanda ba ya da nasaba da wanda iskar da ke hurawa ta ke bayarwa. 4
Ba ta yi zaton akwai wata mahaifiya ba a gidan. Kai ba ta ma yi zaton akwai wata mace ba. A tunanin ta, shi kadai za ta samu, su yi ta ta kare.
Amma a yanzu me zata ce wa mahaifiyar ta sa? Shin ko ma bayan mahaifiyar ta sa akwai matar da ya ke aure? Yaya za su dauke ta? Za su yarda da abin da ta je da shi kuwa?
Ta na tafe tana sake-sake har ta kusa kai wa kusa da kofar shiga gidan. A nan ne fa ta ji haushin karnuka wadan da suka sa zuciyar ta yin tsalle ta fice daga cikin kirjin ta. A firgice ta kalli wurin da sautin haushin ya fito, hantar ta tana kadawa, kafafuwan ta suka kafe tsabar tsorata. Ta lura cikin wani keji su ke, amma suna tsalle ne kamar za su balle su cimma ta.
Ta dafe kirjin ta tare da salati sannan ta hada da hamdala. Karnukan suka kara matsa kai mi wajen haushin, ta dan tsaya tunanin shiga gidan ne ko ta koma kawai, kai a waye, wai bazawara da jaka. 3
Don a tunanin ta, idan Dokta Yusuf din nan ya kore ta daga gidan tare da sakammata wadannan karnuka ma su kama da maraken shanu kam ai sai da kasusuwan ta, idan Dadarta ta na da rabon samu ke nan. Don har kasusuwan na ta za su rabarbasa.
Ganin ta da sauri, maigadin gidan ya dan taka mata, ya na ce ma ta ba za su yi ma ta komai ba, don a daure suke. Hmmm, jin sa kawai ta ke yi. Don ko da shi din ma a gefen ta sai da suka sake daka tsalle, su ka haukace don haushi. Asiya ta ji kamar ta sake fitsari a jikin ta.
Amma ganin maigadin ya kara mata karfin hali har ta shige zuwa kofar cikin sauri. Whew! Ta sha da kyar wannan karon. Farko karnuka, yanzu kuma mahaifiya. Hmmm, abin gaba gaba ya ke yi. 2
Hannun ta dafe a kan kirjin ta, ta shiga falon gidan. Falo ne da ya dace da aljannar duniya. Tiles na falon marbles ne, sai sheki su ke yi da walkiya. Ga wani irin kamshin turaren wutar da ke tashi ya na ratsa hancin ta, kamshi mai sa sukuni da dadi. Hakan ya fara sa ta dan fara jin sanyi a ran ta. 2
Ta yi sallama wa wata mata, wadda ta amsa ma ta cikin sassanyar murya tare da yi ma ta iso. Masha Allah, komai na falon ya kayatar, don ba ta taba ganin kayan alatu irin su ba. Amma ba ta tsaya kalle kalle ba, don ba abin da ya kai ta ba ke nan. Sai dai da za ta so Alhaji Inuwa mai dukiyar garin su ya ziyarci wannan falo don ya bar yi musu rigima. 6
STORY CONTINUES BELOW
Matar da ke zaune cikin makeken falon ta nemi ta karasa kusa da ita, sannan ta yi mata nuni da ta zauna kan daya daga cikin kujerun falon. Asiya ta zauna a kasa, sannan ta kalli matar nan da kyau.
Sanyin kasa ya ratsa ta, hade da iyakwandishan din da ke kunne game da sassanyar muryar matar nan. Ga kamshin da take yi ma daban ne da wanda falon ya ke yi. Haka kawai sai Asiya ta ji tsarguwa. Ina za a hada tsamin jikin ta, wadda ta yini a rana da kuma kamshin alfarma irin wannan?
Tabbas ma su zama cikin wannan gida na alfarma za su iya mancewa da Ubangijin su, su shagalta da duniya. Wato gidan azzalumi ke nan, macuci? 2
Kamar me neman musun hakan, matar nan ta gyara zamanta, Asiya ta lura da carbin da take ja. Duk da dai ba ta taba ganin likitan nan ba, wadda ke zaune a gaban ta tayi yarinya a ce ta haifi da kamar sa.
Ba za ta wuce shekaru hamsin ba, ko da daya ko biyu ba. Wankan tarwada ce mai faffadar fuska, wadda ba ta yi wa kwalliya barkatai ba.
Duk da hakan sai da ta haska. Hancin ta har baki, ga jin dadi da annushuwa sun nuna sosai a jikin. Ga ta da siffar kamala da natsuwa. Anya, ba batar hanya ta yi ba kuwa?
Bayan ta sa an kai ma ta lemo da ruwa ma su sanyi, sannan suka gaisa. Ba ta yi kasa a gwiwa ba, ta tambayi Asiya sunan ta da kuma abin da ke tafe da ita.
“Sunana Asiya, daga garin Dagauda na ke.” Asiya ta amsa, kan ta a sunkuye.
“Ni kuma sunana Umma, ni ce mahaifiyar Dokta. Lafiya dai Asiya, na ji kin zo neman sa har gida?”
Asiya ta daure ba ta dago ta sake kallon matar nan ba. Anya, mahaifiyar sa ce kuwa? Duk da dai ba ta ga wata a gidan ba bayan wadda ta yi mata hidimar kayan sha dazun nan. Amma dai ba za a rasa ba.
“Na fito asibitin sa ne a ka ce baya can. Shi yasa na biyo gida don na gan shi. Ina son ganin sa ne da gaggawa, don Allah.”
Fatan ta idan ta furta hakan wata kila ta yi sa’ar Umman nan ta neme shi cikin gaggawar da ta ke bukata. Akwai sauran lokaci, idan har ta na son komawa garin su. Ta san Sani Kwatambe, direban garin su zai iya jiran komawar ta tasha, musamman ma da ya kasance Muhibbat ta ba shi amanar ta ne.
A lokacin ne yayyafin ruwa ya sauko, kamar wanda ke nuna ma ta cewar komai ba a hannun ta yake ba. Umma ta ce da ita, “To ga shi nan din ma ba ya nan.”
Asiya ta lura dai Umma ta ba ta filin fadin abin da take tafe ne da shi. Ta shiga muhawara. Komai zafin da ta debo ba za ta iya saukewa a kan mahaifiyar azzalumi ba. Wata zuciyar ta na raya mata cewar ta fada kawai, ai dan kuka shi ke ja wa uwar sa jifa.
Sai dai ba zata iya ba. Sunkuyar da kan ta kawai ta yi, ta na tunanin idan ta yi shiru to komai zai iya rushewa. Komai, hatta rayuwar Mariya. Ta daure dai ta ce, “Na zo ne nag an shi dangane da ‘yar uwata Mariya.” A kalla hakan gaskiya ne.
“Ta na ina ne ‘yar uwar taki? Gida ne ko asibiti?” muryar Umma da sanyi har a lokacin. Ta jinjina ma ta, domin da za ta ji abin da ke tafe da ita, wata kila da duk sanyin dakin da suke ciki sai ta yi zufa!
“Ni ma ban san halin da take ciki ba a yanzu.” Da gaske ne, ba ta san abin da ya faru a bayan ta ba. Takaici ya kara rike mata wuya.
Ba ta ko wane hali Maree ta ke a lokacin ba. Ita ma kan ta ba ta san wane hali za ta shiga ba. Rashin ganin likitan nan ya dagula ma ta lissafi. Ga dare yayi, ga hadiri. Ga bawan Allahn da ta ajiye a waje mai Keke Napep din da yake jiran ta.
“Don Allah Umma, ki taimaka don yau din nan na samu ganin sa in da hali.”
Umma ta nisa, fuskarta cike da tausayi, “Ga shi yau din nan suka shiga taro da kusoshin ma’aikatar kiwon lafiya. Amma na san ba mamaki sun fito.” Ta na fadin hakan ta fidda wayar salular ta, ta shafa kan sa a hankali. 2
Bayan ta yi magana a cikin ta, sai ta kalli Asiya, wacce ta dunkule waje guda kamar maggi, ta ce, “Na same shi. Ya na nan zuwa yanzu in shaa Allah.”
Bai kamata ba, amma sai ta ji karin bugun zuciyar ta a cikin kirjin ta.
Nesa ta zo kusa ke nan. Alla alla ta ke yi ya zo ta gan shi, komai ya wuce ma ta a wuya. Wani Karin kulliti ya rike ma ta wuyan, fargaba ta kara kamata.
“Daga ina ma ki ka ce kin taho?”
“Dagauda.”
Umma ta kara nuna ma ta tausayi, ta ce, “Allah Sarki. Kin sha hanya, duk da ban taba zuwa wajen ba. Na tabbata kin a bukatar wajen da za ki yi sallah, sannan ki samu abinci ki ci.”
A tunanin Asiya, ba ta taba shan bakar wahala irin ta ranar ba, wahalar zahiri da na badini. Amma ba za ta bari hankalin ta ya kauce kan niyyarta ba. Ta fara son ta ki tayin da Umma ta yi ma ta, amma ba ta saurare ta ba.
Umma ta kira mai aikin ta mai suna Larai, kan ta kai ta dakin baki ta yi alwala ta yi sallah, sannan a kai ma ta abinci kafin likita ya iso.
Wani abu game da muryar Umma da yanayin fuskar ta suka sa ta ji sanyin jiki. Ta daure ta sanar da ita cewar akwai wanda ta je da shi, ya na kuma jiran ta a waje.
“Kar ki damu.” In ji Umma. “Zan sa a kai ma sa ruwa da abincin shi ma, in ya so sai ya zauna wajen Iro mai gadi ya ci gaba da jiran naki. Balle ma an fara yayyafi, ba zai kyautu ku fita cikin wannan ruwa ba.”
Asiya ta yi godiya sannan ta bi bayan Larai, idanun ta suna shagala da ganin abin duniya, duk da dai zuciyar ta a bace ta ke.
Ko cikin mafarki ba taba tunanin samun kanta cikin irin wannan gida ba. Sai ga ta cikin sa ta na takawa. Ko ina sai sheki da kamshi ya ke yi.
Dakin da a ka kai ta, wanda a hakan ma wai na baki ne, kyaunsa baya misaltuwa.
Ga girma, zai kusa filin tsakar gidan su. Ta tambayi qibla sannan ta shiga bandakin da Larai ta nuna ma ta.
Nan ta tsaya ganin yadda za a yi a ce bako ya zo wannan duniya sannan ya yarda ya koma wurin da ya fito. Koda yake, ba kowane irin bako ne ke ziyartar irin wannan wuri ba. Ba irin ta ba, na-wuro.
Kasancewar tayi sallar kasaru na azahar da la’asar tun suna kan hanya magriba kawai ta yi. Kafin ta idar Larai ta dire ma ta babban kwanon abinci mai kyaun gaske. Don gulma, cikin ta ya shiga ruri kamar hadirin da ke waje.
Ruwa kuwa ya sauko ba kama hannun yaro. Cikin gidan kuwa ko ina haske kamar rana. Su a garin su idan a na ruwa haka dauke wutar lantarki a ke yi.
Ko bude kwanon ba ta yi ba, ta koma falon. Ba ta samu kowa ba. Ga alama Umman ma sallah ta je yi.
Bayan dan lokaci kankani, Umma ta fito falon, wayar ta dore a kunnenta ta na magana. Ko da ta gama, sai ta zauna tare da kallon ta, “Ina fata dai kin ci abinci. Likitan ya tsaya ne yin sallar maghrib a masallaci, amma yanzu haka ya kusa zuwa.”
Rufe bakin ta ke da wuya suka ji karar ham na mota. Gaban Asiya ya kara faduwa ras!
Zuciyarta tayi wayam na dakika biyu kafin ta shiga bugawa cikin sauri. Jin tsayuwar motar ta kara mata gudun famfalaki.
Da safiyar wannan rana ta tashi ne da kudirin ganin wannan likitan da kuma niyyar kalubalantar sa.
A yanzu kuma da ya iso gare ta ta shiga jin fargaba. Lokacin da ya bude kofar, ta ji zuciyar ta ta buga, ta tsaya.
Assalamu Alaikum.”
Sassanyar murya game da mutumin da ya shiga falon suka zuciyr ta sandarewa. Dogon mutum ne, ya na da haske amma ba can ba. Ya na sanye cikin kwat baki da farar shat a ciki. Kamshin turaren sa ya naushi hancin ta, a yayin da hadiye yawun da ke bakin ta, wanda ba ta san da shi ba. 2
Yanzu ne ta ke ganin dalilin da ya sa Mariya fada wa kogin son sa, har ma da na yarda da shi kamar yadda ta yi.
Ya dace da mafarkin ‘yan mata. Ko da ya saki murmushi, za ta iya rantsewa zai iya narka dutse ya zama gari. Duk da cewa ma ba wa ita yayi ba. 5
Bayan ya gai da Ummar sa, sai ta gabatar ma sa dalilin kiran da ta yi ma sa. Ya mayar da hankalin sa kan Asiya. Ba tare da bata lokaci ba, ya tambaye ta dalilin neman ganin sa.
Makogwaron ta ya bushe, sannan ta gyada kanta, ta kuma girgiza a lokaci guda. Ba ta san dalilin rudewar da tayi ba. Watakila ko don Umma ta na zaune ne a wajen. Ko kuma don wannan ne karo na farko da take fuskantar sa.
Ya zauna kan kujerar da ke fuskantar ta, kamar yadda Ummarsa tayi zato ne, shi ma hakan yayi, “Ke ce marar lafiyar ko wani?”
Muryar sa cikin natsuwa, wanda wata kila likitoci ke amfani da su wajen jan hankalin marasa lafiya. Ko kuma wanda mayaudari ke amfani da ita wajen jan hankalin ‘yan mata masu rauni, irin su Mariya.
Nan take ta ji bacin ran da yake ran ta ya taso. Mariya! Mariya!! Ta amsa da, “Na bar wacce ke da matsalar a can gida. Na zo ganin ka ne dangane da matsalar ta.”
Kallo ya ma ta, irin na marasa tunani, kauyawan nan. Ya ce, “I am sorry, ki gafarce ni, ba zan iya yi mi ki komai a kai ba muddin babu marar lafiyar. Baya ga haka, ni ba wata mu’ujiza ce gare ni da zan warkar da marar lafiya ba tare da ganin ta ba. Don haka idan kin shirya sai ki kai ta can asibiti ku same ni. Don ban cika son a na zuwa gida a kawo hidimar asibiti ba. Yau don albarkacin Umma ne ya sa na saurare ki.”
Iye! Ga mutum da gadara da ji ji da kan tsiya. Ya kuwa san da wacce ya ke magana? Har ya mike zai bar wajen, irin ya gama yanke hukunci din nan, ta tsayar da shi, “Na zo ne don na yi ma ka bayanin halin da Mariya ta shiga ciki.” 2
Ya kalle ta, “Mariya?”
Haushin sa ya kara kama ta. Ya ma ta tambaya kamar bai san Mariya ba? Dan rainin hankali kai. Ta yanke shawarar yi ma sa bayani dalla-dalla. Tun da abin da ya ke so ke nan.
“Eh, Mariya. Wacce ka jefa cikin halin da ke neman jefa gidan mu cikin jafa’i.”
Idanun ta suka ciko da kwalla, zuciyar ta ta fara ci da wuta don jin zafin halin da suka tsinci kan su. Shi waye ne da zai jefa su cikin ukuba da tashin hankali, alhali shi kuma ya zauna cikin sukuni? Wannan ai zalunci ne da son kai.
“Wace ce Mariya?” Ya kara tambayar, muryar sa ta na nuna rashin fahimtar sa karara. 3
Cikin gifcewar dakika daya, Asiya za ta iya yardar cewa wannan likitan bai san Mariya ba da gaske. Amma kuma hakan salon ‘yan yaudara ya ke. Kamar sari-kutuf ne, su sare mutum su noke. Balle ma ya na gaban mahaifiyar sa ne, tilas zai yi taka-tsan-tsan. 2
“Mariya Sabo Ali. Har ka mance da ita? Ko da yake ba abin mamaki ba ne. Mutum irin ka zai dauke ta tamkar tsummar goge takalmi, ka yaudare ta ka jefar. Amma na sha alwashin cewa ba zan kyale ka ka huta ko ka kasance cikin sukuni ba har sai na samar ma ta adalci daga gare ka.”
Har wani haki take yi, tsabar takaici ya rufe mata ido. Ba ta ko iya ganin girman mahaifiyar sa balle ta yi ma sa sassauci. Musamman ta fito domin sa, ta kuma samu damar fuskantar sa tare da fada ma sa abin da yayi mu su. Ba ta san abin da zai iya yi ma ta ba, tun da mai dukiya ne. Ba ta damu ba kuma.
Nan ta ga ya tsuke fuska, kyaun fuskar sa bai gushe ba. Ya kalle ta da kyau, “Who are you? Ke wace ce? Daga ina ki ka zo haka har za ki nemi yi min isgili a cikin gidana?”
STORY CONTINUES BELOW
Ta dan razana, amma ba ta yarda ya gane ba. Amsar tambayar sa ta yi yunkurin bayar wa, “Daga Dagauda. Amma a garin Jos Maree ta ce min kun hadu har kuka shaku. A nan ta yarda da kai, har hakan ya kai ta ga amincewa ta baka kan ta. Ga shi hakan ya sa ta na da juna biyu!”
Ga shi nan, ta fada. Me zai yi mata? Ko zai kashe ta ne sai ta fadi gaskiya. Ta fada, sai dai fa kuma a yi duk wadda za a yi, wai bera ya zub da garin kyanwa.
2
Dokta ya gwalo idanun sa, a lokacin da Umma ta saki salati cikin tsananin kaduwa da girgiza. Tun farko ta so ficewa ne, amma a tunanin ta, bakuwar su za ta bukace ta a kusa da ita. Don ta san dan ta baya yarda ya ga marasa lafiya a gida. Ko da ganin ta, ta yi zaton babban al’amari ne ya kawo ta. Ashe ba ta bata ba.
“Baiwar Allah, kin tabbata babu wani motsi a cikin kan ki? Kin san da wanda kike magana kuwa?” Ya tambaye ta cikin rashin gaskata kunnuwan sa.
Ikon Allah, wai na kwance ya fadi. “Da dokta Yusuf nake Magana, shugaban Sauki Clinic, saurayin yaya ta Mariya wanda ya yaudare ta da kalmar soyayya, sannan ya yi mata ciki.” 2
Ta ci gaba da cewa, “Bayan ka gama biyan bukatar ka, sai ka yanke duk wata hulda da ita, kullum lambar wayar ka a kashe. Har ta hakura wa ran ta sai ga wannan al’amari ya bullo. Ga shi yanzu an kai kayan auren ta har ma an saka ranar auren. Komai ya na shirin kacame mana. Shi yasa na fito neman ka.”
A zahiri ko kuma a na ta tunanin, Dokta ya kara tsuke fuskar sa, idanun sa na ci da wuta. Ba ta damu ba. Ta san kan hanyar gaskiya ta ke, kuma ta tabbata komai dadewa za ta yi halin ta.
“Umma ta koya min tarbar baki, ko da kuwa sun kasance mahaukata ne. Ba don hakan ba da na gwada miki irin tawa haukar. You are very stupid, da za ki zo har gidana, gaban mahaifiyata sannan ki min wannan mummunar zargin!” 2
Kalaman sa sun sosa ma ta zuciya matuka. Ta yaya ma zai zage ta? Wannan shi ne ga mari ga kuma tsinka jaka. Ta kuma kallon wajen da Umma ke zaune ta na kallon su, kamar wadda ta saba jin dan ta ya na yin cikin da ba aure wa ‘yanmata a kullum.
“Me zai hana?” Asiya ta mayar ma sa da martini. “Ai ba abin mamaki ba ne don ka yi hakan. Gwara ka gwada karfin ka a kan halitta mai rauni, zai tabbatar wa duniya mazakutar ka.”
Muryar sa ta fito a tsanake. Da jin hakan, kokarin danne zuciyar sa ya ke yi, “Kafin na yi wani abin da zan yi nadamar sa, ina son yanzun nan ki fice min daga gida. Idan na kara ganin ki nan da kilomita goma, sai na dauki mataki a kan ki!”
A lokacin ne Umma ta daga hannun ta, ta tsinto muryar ta, ta ce, “A’a, dan-auta, ba za a yi hakan ba.”
Ya kalli mahaifiyar sa, “Yanzu Umma kin yarda cewa zan iya aikata abin da take zargi na da shi?” Muryar sa cike da mamaki da kuma daci.
Hakan ya sa Asiya ta dan ji sanyi a ran ta. A kalla, Umma ta fi shi hankali. Sannan a can kokon ran ta, ta san ta sha ke nan, ba zai sakar mata karnukan sa a kan ta ba. Don ba ta yarda cewa ba zai iya yin hakan ba, a yadda ya bata ran sa. 2
Umma ta girgiza kan ta, “Ko kadan ban kawo hakan a raina ba ma.” Ta kalli Asiya, ta ci gaba da cewa, “Dan-auta ba zai iya aikata abin da ki ke zargin sa da shi ba.”
Bayan ta nemi ya koma ya zauna, ta ci gaba da bayanin ta, “Ba bu wacce ta taba zuwa neman sa har gida, shi yasa da na gan ki da yanayin ki, sai na matsa ya zo don ya gan ki.” Ta nisa, “Amma hakika, kin zo da babban al’amari.”
Ta tambayi Asiya wadan da suka san da wannan magana, ita kuma shaida mata cewar daga ita, Mariya, Muhibbat kawar Mariyar, sai mahaifiyar su. A yanzu ke nan, tun kafin abin ya bazu a duniya kamar gobarar daji.
Umma ta kara nisawa, ta kara tambayar Asiya, “Ita Mariyar ce ta ce dan-auta ne ya jefa ta cikin halin da take ciki?”
“Eh, ita ce.”
STORY CONTINUES BELOW
Ai kuwa Dokta ya mike cikin harzuka, ya daka mata tsawa, “Ke mahaukaciyar ina ce? Ni fa ina kyautata zaton cewar ke tafintar barayi ce, ko kuma na ‘yan damfara.” Ya kalli Umma, “Yanzu kin ga dalilin da ya sa ba na yarda mutane su zo nan su neme ni?”
Umma ba ta kula shi ba, ta ci gaba da tambayar Asiya, “Ta na iya yiwuwa wanda kuka sani ba wannan Yusuf din bane, wani ne?”
Asiya ta girgiza kan ta, sannan ta amsa, “Shi Mariya ta ambata. Kuma ta bani shaidun da zan nuna idan har yayi musun sanin ta. Ga abin da ta ban, ta ce shi ya bata a lokacin da suke soyayya.” Ta mika wa Umma.
Dokta ya karbi abin bayan Umma ta karba ta duba. Zoben azurfa ne mai sheki da walwalwal. Ba irin wanda a ke samu a ko ina bane, irin wanda mutum zai sa a ma sa ne. A lokacin ne ta lura ya kalli Umma cikin rudani, sannan ya kara bata ran sa, Wannan zoben tabbas na sa ne. Ta yaya ma za a yi ya je hannun wadan da bai taba ganin su ba? Ya lura ita ma tambayar da ke idanun ta ke nan.
Umma ta ci gaba da tambayar ta, “Bayan wannan fa? Akwai wani abin da zai nuna shaidar soyayyar Mariya da dan-auta?”
Asiya ta kalle su duka. Me suke nema kuma? Ta amsa, “Akwai lambar wayar da ta kan kira shi a da, kafin ya bar shiga.”
“Mu ga lambar.”
Ta fidda Nokiar da Mariya ta bata don idan ta isa Bauchin ta buga waya wa Muhibbat su ji yadda ta isa. Tsabar tashin hankali ma ba ta kira sub a tun bayan wanda ta yi kan hanya kafin su iso.
Nan ma ya duba lambar, sannayan ta nuna sakonnin text wato na wayar da ya yi ta aika mata, har ma da wasikun da ya rika aika wa.
Ta kura ma sa idanu ta ga yadda zai fara musun cewar ba sunan sa ba ne a kasan su, ko ci gaba da musun cewa bai san wata Mariya ba.
“Wannan ba rubuta na bane.” Ta ji ya furta, fuskar sa a turbine. “Kuma ni ba na ma rubutun wasika irin wadan nan. Ba na ma da lokacin.”
To ko wani ya ke saka way a ma sa, ko kuma ya na da baiwar rubutu iri iri, wanda yak an yi amfani da ita a duk lokacin da ya ga dama. To ko ma dai mene ne, yanzu ya rage nasa ne.
Agogon bangon falon ya buga karfe bakwai. Yayyafin da a ke ya dan tsagaita. Umma ta nemi dukan su su je su yi sallar isha’i. Ta shaida wa Asiya cewar za ta sallami mai Keke napep, in ya so za ta sa a mayar da ita gida.
A lokacin ne Asiya ta fada ma ta cewar ba ta da wanda ta sani a Bauchin. Umma ta nisa, ta ce ba matsala, za a shirya ma ta wajen kwana a dakin bakin gidan. Da wannan ta kira mai Keke zuwa dab kofa, ta bas hi hakuri tare da kudi mai kauri sannan ta sallame shi.
Ya yi godiya, ya yi mu su bankwana.
Ba a sake tayar da maganar ba har bayan sallah. Asiya ba ta Umma ba balle Dokta. An bar ta da abinci a gaban ta, tuwon shinkafa miyar kubaiwa busasshiya. Ga kamshi, ga kuma kifi da nama zako-zako a ciki.
Ta ci dai kawai dan kadan don taran rai, amma ba don dadi ba. Duk da ma dai gaskiya ya yi dadin. Abin da ke gaban ta ya wuce gaban wasa. 2
Can ta na kishingide har barci ya sace ta da kyar. Don da ta runtsa sai ta farka, ta na ganin kamar Dokta zai iya shiga kan ta, ya nemi fan sa.
Ko ma ya fidda ita waje sannan ya sakammata karnukan nan na sa. A duk lokacin da ta ji gurnanin su, sai hantar cikin ta ta kada.
Ta kalli sama tare da nisawa. Allah Ya gani, Ya san halin da suke ciki. Shi kadai ne zai bullo ma ta da mafita. Allah dai Ya fitar mu su da ita cikin gaggawa!
* * *
A duk ranakun duniyar nan, Dokta Yusuf Haruna bai taba samun kan sa cikin bacin rai mai tsanani da tashin hankali irin na wannan rana ba. Ko mutuwar mahaifin sa ba ta daga ma sa hankali kamar yadda wannan yarinyar ta yi ba. 3
STORY CONTINUES BELOW
A rayuwar sa, shi ba mai yawan yawo ba ne. Yawanci daga asibiti sai gidan sa. Hatta abokan sa na wajen aiki, kuma aminan sa sun yi mitar rashin ziyartar su da ba ya yi har sun kyale shi. Don haka, abu ne mai wahalar gaske, a ce ya lalata rayuwar wata.
Wacece ma wai? Mariya…. Tun da yake bai taba sanin wata mai wannan sunan ba, bai taba ganin wadda ta zo gidan nasa a yau ba.
Ta yaya ma za a kalle shi, tsabar rainin hankali a ce ya aikata mummunar abu kamar hakan?
Allah Ya sani, shi ba mazinaci ba ne. bai taba aikata zina ba. Hana-rantsuwa, ya taba sumbantar wata yarinya a lokacin su na karatu tare. 8
Mabruqa sunan ta. Tun bayan wannan rana mai ya tuba tare da neman gafarar Allah. Bai kara ba har sai da ya yi auren fari. To don me za a yi masa wannan zargi? Kai anya, yarinyar nan ba ‘yar damfara ba ce, irin ma su neman su dora ma sa laifin da bai aikata ba? Yo, ko ma dai ita din ce mai cikin ta wani fake da wata wai Mariya?
A ganin sa kudi ta je nema. Kuma ya yi alwashin ba zai ba ta ko taro ba balle sisi. Ta ma yi sa’a Umman sa tana nan, da ta raina kan ta! Don kuwa da zai tabbatar mata cewar bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane. Shi ba kanwar lasa bane.
“Dan-auta.”
Muryar Umma ta kutsa cikin tunanin sa. Ya mike tsaye a lokacin da ta karasa cikin dakin sa, fuskar ta babu alamar bacin rai. Amma idanun ta kirr a kan sa.
Ya tsani hakan, ba ya kauna ko kadan. Ya na matukar son ta fahimce shi, don haka ya ce, “Don Allah, Umma ki bani damar na kori wannan yarinyar daga gidan nan. Karya take yi, sharri ta kulla min. Ki bar ni na hada ta ‘yan sanda har sai ta nuna sauran abokan huldar ta an yi maganin su.”
Umma ba ta yi murmushi ba, kawai cewa ta yi, “Kar wannan ya daga maka hankali.” Muryar ta a natse.
“Dole hankalina ya tashi Umma.”
“So nake ka bani hankalin ka. Na yarda da kai, dari bias dari. Amma a duk lokacin da ka ga abu ya faru, wanda ya wuce tunanin ka, to tabbas akwai dalili. Ruwa ai baya tsami banza. Don haka, ni da kai zamu hadu mu warware wannan kullin zaren tun kafin maganar ta fi karfin mu.”
Wai me? Ba dai yarda ta yi da wannan yarinyar ba. Ya san Umma ta yarda da shi. Amma yarda da maganar wannan yarinyar zai kara sa shi cikin tababa? Me zai sa ba zata kore ta ba?
Ya san dalili, a kalla a tunanin sa. “Umma me ya sa za ki ba da damar a ci gaba da raina mana hankali ne? Ina tabbatar miki da cewa wannan bada dama ne wa wasu su zo su mana hakan, idan har mun bata muhimmanci.”
“Ka yi min shiru! Ba a raina maje wuya, sai ‘yar wuka. Duk wanda ya raina gajere to bai taka kunama bane. Ka san gidan ku, ka san ko kai waye. Ai bin diddigin maganar ce zai kara bamu haske a kan komai. Shi ciki da gaskiya wuka bata huda shi.” 1
Hakika, Yusuf ya san ko shi waye, daga kuma wurin da ya fito. Da ne ga hamshakin mai dukiya, Alhaji Haruna Rabeh. Mahaifin sa dan kasuwa ne wanda kafin ya rasu, yake harkokin sa a can Ikko.
Babban mai raba kayan kamfanoni ne irin su PZ da Unilever. Da an yi fitar a kamfani, wajen sa a ke sara.
Karayar arziki ce ta sa ya dawo da harkokin sa nan arewa, musamman tsakanin Kano, Bauchi da Filato. A cikin ‘ya’yan da Allah Ya ba shi, babu wanda ya tallafa ma sa a kasuwancin sa.
Dukkanin su ‘yan a ci ne kawai, ba a son wahala ba. Babu wanda ya kula da karatun sa ma balle kasuwancin.
Matan Alhaji Haruna uku ne a lokacin. Umma ce karamar su, kuma Yusuf ya kasance dan ta biyu bayan babban yar sa Rukayya. Sauran kuma Saratu da Abdul-Basit, wanda ya kasance dan autan su.
Lakanin dan-auta, Umma ce ta saka ma sa ba don shine autan ba, sai don ya kasance mai biyayya da bin umurnin na gaba da shi. Don haka take ma sa taken dan autan ‘ya’ya.
A jami’ar Maiduguri ya yi digirin san a zama likita, wato MBBS, sannan ya kara wasu kwasa-kwasen a kasashen waje da ma Zariya, ta yadda ya zama consultant a karancin shekarun san a haihuwa. Hakan ya sa mahaifin sa gina ma sa babban asibiti, wanda daga baya shi da abokan huldar sa suka fadada har ya tsaya a hakan.
Wannan gina asibiti ya haddasa gaba mai tsauri a tsakanin sa da ‘yan uba, wadan da suke ganin an fifita shi a kan su. Tun bayan mutuwar Alhaji Haruna suke neman lallai sai an sayar da asibiitin, an raba gado. Har kotuna an je, amma Yusuf ya na rike da asibitin, tun da ban a sa bane shi kadai.
Kishiyoyin Umma suka saka ta a gaban su da gaba mai zafi. Bab abin da suke hari illa neman ganin bayan su. Wannan ne ma dalilin da ya sa Yusuf sayen wannan gida da yake ciki, sannan ya karasa gina shi, ya gyara Ummarsa ta koma abin ta.
Abin da ‘yan uwan sa bas u sani ba, shine, mahaifin su ya dauki basussukan banki da dama don bunkasa kasuwamcin sa. Ya kuma mutu ba tare da ya biya ba. Shine Yusuf din yake biya a hankali, cikin rufin asiri. Ko da sun sanin ma babu wanda zai damu ya biya ma sa.
“Ka shirya gobe in Allah Ya kai mu, za mu je garin su, domin mu warware komai, gaskiya kuma ta yi halin ta.” Ta umurce shi sannan ta ficewar ta.
A tunanin sa, Umma ba za ta so maganar nan ta shiga kunnuwan kishiyoyin ta, ko ma ‘ya’yan su bay a sa ta ba ta muhimmanci. Za ta yi sauri ta yi wa tufkar hanci, kuma ko da shi ko babu, zata aiwatar da abin da tayi niyya.
Ya nisa, baya kaunar abin da zai bata wa mahaifiyar sa rai sannan ba ya son wasa da aikin sa. Ya na da aikin tiyata biyu da zai yi su aa goben, wanda haka ma bai yi aiki sosai ba a yau, don ya ji shi garau.
Ba yadda iya. Dole ya bi ta su je ko don ta samu kwanciyar hankalin ta. In ta nasa ne, ya san bai yi komai ba, wanda bai ci buzu ba ai ba zai yi aman gashi ba.
Daga yau, yayi alwashin kara tsaro wa gidan sa, ko da wasu mahaukatan za su yi batan kai su sake zuwa da abu kamar hakan.
Bayan ya buga waya wa abokan sa ya shaida musu ba zai samu zuwa aiki washegari ba don haka suka shaida masa cewar zasu rike masa bakin na sa aikin. Ya gode da basu nanata ma sa tambayoyi a kan dalilin tafiyar da ta taso masa babu shiri ba.
Ya yi kudiri a ransa, cewa sai ya daure wannan yarinyar da iyayenta har igiya ta yi saura, ta yadda gaba ko mai sunan sa suka ji, sai sun kadu daga kan su har kafafuwan su.
Bai kwana a gida ba. A asibiti ya kwana, don ya na bukatar abin da zai dauke hankalin sa a kan tashin hankalin da ya same shi. Sai kusan asuba ya koma gidan. Ko da gari ya fara wayewa, ya ja gwauron numfashi. Allah Yayi dare, gari ya waye. Wannan rana ta kasance mai cike da abubuwa da dama. Bai san abubuwan da zai fuskanta ba, amma ya san kamar yadda Ummar sa ta ce ne, ciki a gaskiya, wuka bata huda shi. Kaza mai ‘ya’ya ita ke tsoron shaho, sannan idan mutum yana tsoron kira, to yayi laifi ne.
Ba ya tsoron komai, kawai lokaci yake jira. Allah Ya kai kowa lokacin, shi ne babban fatan sa.Tun da karfe shida Asiya ta gama shirin ta, ta zauna cikin dakin da ta kwana jiya. Ita da ma tun can ba mai barcin safe ba ce, sannan ta saba da kaye-kaye. +
Sai dai a wannan lokacin ta zauna ne jiran aiwatar da hukuncin da Umma ta yanke game da maganar da ta zo mu su da ita.
A yanzu da ta fuskanci Dokta, tambayoyi ne cike da tunanin ta fiye da amsoshi. Shin zai yarda da laifin da ya aikata, ko zai ci gaba da musantawa?
Me zai faru daga yanzu: tsakanin Dokta da Maree; tsakanin ita kan ta Asiyar da Dada; tsakanin mahaifin su da su; tsakanin Mudassir da Maree; tsakanin gidan su da mutanen garin su?
Ba zata iya cewa akwai nasara tattare da tafiyar nan da ta yi ba. Amma ko da hakan ma, shi ma Dokta Yusuf zai yin a sa irin hasarar, ba su kadai ba.
A kalla hakan ta so ya faru tun farko. Ta yi hakan ne don koya ma sa darasi, ya san nan gaba cewar su ba kanwar lasa ne bane, ba zai mayar da Maree gangar da zai ci moriyarta ya jefar da kwauren ba. Kuma ko da nan gaba ne, ba zai kara yin hakan wa wasu abin da ya aikata wa Maree ba.
Ta nisa. A can cikin zuciyar ta, za ta so a samu maslaha game da wannan matsalar. Za ta so a ce likitan nan ya amince da wannan ciki a matsayin tsautsayi, ya tausaya mu su gaba daya, ya auri Maree da zarar ta haife abin da ke ciki. In ya so sai a tsara cewa ta koma Jos da zama har zuwa lokacin da za ta haihun, shi kuma Mudassir a ba shi hakuri, a mayar da kayan sa.
Mafarki ne da ta san zai yi wuyar faruwa. Amma ai ba a hana ganin sa ai ko? Sai dai ganin mafarki alhali ba barci a ke ba bata lokaci ne, kamar yadda ta ke ganin wannan kudirin na ta. Amma it aba mai saurin karaya ba ce. Za ta tsaya ta ga abin da zai faru.
Tare da sallama mahaifiyar Dokta ta shiga dakin da take, ta na daure da atamfa mai launin ruwan toka da ratsin ja. Da shigar ta kamshin ta ya mamaye dakin.
Ta kalli Asiya, fuska a yatsine, ta tambaye ta, “Me ya sa ba ki kwanta kan gadon ba? Ai kuwa ba ki huce gajiyar jiyan ba.”
Asiya ta durkusa cikin ladabi ta gaishe ta, sannan ta amsa, “Nan din ma ya wadatar.”
Hakika, kasan kilishin da ked akin akwai taushin gaske. Da ma ita tun can kan tabarma ta saba kwana, don haka gado ya sha zaman sa. Ya ma fi karfin ta. Ita dai alla-alla take yi ta ji abin da Umma ke tafe da shi.
“Na ga kamar kin shirya, ko?”
Asiya ta gyada kan ta, “Eh, na shirya Hajiya.”
Umma ta yi murmushi, “Umma za ki kirani. Larai za ta kawo miki kalaci. Ni kuma zan je na yi shiri, don zamu je tare da ke har can garin naku, domin mu taru mu samo maslahaa baki daya. Ko yaya kika ce?”
Zuciyar Asiya sai bugawa take yi da sauri. Za a so hakan, amma ba za ta so ba. Saboda zuwa hakan da Umma kwatsam zai iya haddasa babban damuwa tsakanin ta da Dada. Amma idan ta ki kuma za a ga rashin gaskiyar ta. Don haka ta amince. Komai zai faru kam sai dai ya faru, don ta riga ta shiga har wuya, babu halin fita ko ja da baya.
Larai ta kai mata lafiyayyen sinasir da miyar naman rago zako-zako, hade da ruwan shayi. Shayin kawai ta kurba, don du’a’i sun cika mata cikin ta dam. Roko ta ke yi, tare da cikakken fatan komai zai zo cikin sauki.
Karfe bakwai da kwata Umma ta sa Larai ta kira ta, kan ta fito su tafi. Ta fito ta iske ta canja kayan jikin ta zuwa ga wani leshi mai kyaun gaske launin ja da zaren gwal. Ga daham nan a wuyan ta wandaa ke zikirin nera.
Ta rufe jikin ta da gyale babba amma na yayi. Hannun ta da munduwa guda biyu manya. Ta tabbata su ma gwal din ne. shi yasa shekarun ta bas a nuna wa. Ga dai Asiya ce yarinya, amma sai ta ga kanta kamar ta saka ganye ne a jikin ta ba sutura ba. 3
Da suka fita waje, daya daga cikin jerin motocin da ta gani a jere jiya ne ta gani dab da bakin kofar fita daga gidan. Motar a kunne take, ga alama direban ya shirya ne ya na jiran su.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da suka kai dab da shiga kafin ta lura da wanda ke zaune kan kujeran direban. Dokta Yusuf ya sha jamfa shudi, kan sa da hula ta zanna tangaran, sai sheki ta ke yi. Ita ma ta san hular ce albarkacin wanda zai auri Maree. Su ya ke yawan sakawa idan ya je zance.
Maree. Asiya ta sake nisawa. A wannan rana dai komai zai zo karshe cikin ikon Allah. Abin da ke duhu zai fito haske. Wata kila hakan zai kawo haske gare su baki daya.
A gaban motar Umma ta umurce ta da shiga, saboda nuna mu su hanyar. “Ba na son mutane da yawa su san abin da ake ciki. Ina fata kin fahimta.”
Asiya kuwa ita ta fahimta, saboda ko mahaifin su ba su gaya wa ba.
A lokacin ta gaishe shi ya amsa cikin makogwaron sa. Ba ta yi zaton Dokta Yusuf zai amince da zuwa Daugauda da kan sa ba. Gaskiya ta yi mamakin hakan. Yin hakan zai fallashe shi, amma duk da hakan zai je? Karfin hali ne ko kamun Allah? Za dai su gani.
Suna tafe fuskar sa a murtuke kamar hadirin jiya da yamman nan. A yau da safe kuwa wuri da danshi, rana kuw ta leko a bayan gajimare manya manya. Iskar damina ta na busawa a ta tagar motar, wadda ya sauke kadan.
* * *
Sun isa garin Dagauda cikin awa uku da rabi. Asiya ba ta taba shiga mota mai gudu irin ta Dokta ba. Sai kace jirgin sama?
Dokta kuwa tun shigar sa bai furta komai ba, kallon gaban sa kawai ya ke yi. Sai lokacin da ya tambaye ta hanyar da zai dauka zuwa Dagaudan, sannan da wanda zai dauka zuwa gidan su. 1
Garin kamar kullum yak e, manoma suna gonakin su, matasa suna gewaye da teburin Isa mai shayi da indomie, tsofi kuma na zaune a filin kasuwa a karkashin bishiyar cediya. Wasu su na kofofin gidajen sua gindin maina. Wasu har sun fara aikin gyara ginin su da ya zube, kasancewar ruwan saman ya fara ja da bay a ta wajen su.
Mota irin ta Dokta Yusuf ba kasaifai take zuwa garin na su ba. don haka duk wuraren da suka bi sai an bi su da ido yuuu. Wasu wuraren ma har sai da wasu suka tashi suna dunkule hannayen su suna furta, “Kiyaye ka!” Kamar yadda suka saba yi a garin wa ‘yan siyasa idan lokacin zabe ya kusa, sun je neman kuri’u.
Yara kuwa suka rika bin su da gudu, suna murna da dariya tare da shafa jikin motar.
Asiya ta tabbata a lokacin sunan ta zai bazu a daba-dabar garin na su nan, Wadan da ba su sa da san ta ba ma za su sani saboda ganin ta da a kayi a gaban bakuwar mota. Ita dai zuciyar ta di-dif take yi, ta fara jin taraddadi.
Babu kowa a kofar gidan su, hatta yaran da suka saba zama a kan yashin da makwabcin su ya tara suyi wasa. Yaran da suka bi bayan su ne suka tsaya kallonta, wasu kuma suna yi mata oyoyo.
Umma ta fita daga motar, shi ma dan nata ya fito. Irin kaallon da ya yi wa kofar gidan ya bayyana kyamar sa.
Me zai hana shi kyama? Tun da ba kamar gidan sa ba ne. Ta yi iso wa Umma, suka shiga tare. Shi kuma ya tsaya daga wajen, kan san a kallon wani waje.
Yaran sun waste, an bar wasu masu kallon kwakwaf. Wasu manyan ma suka isa gare shi suna mika gaisuwan su. Ba mamaki ma su kwaram ne.
A tsakar gidan su suka tarar da Maree ta na shara. Ai kuwa sun a sallama da ta ga su ne, ta jefar da tsintsiya tare da daka tsalle ta rungume ta. Dada ta fito cikin sauri a razane, jin ihun da tayi.
“Me ya haka? Sai ka ce ba jiya ba ne kuka rabu? Na ma yi zaton wani maciji kika gani da wannan ihun na ki.” In ji Dada.
A lokacin su ka dan fara dariyar kwatancen Dada, kafin hankalin ta ya kai ga kan bakuwar su. “Bakuwa mu ka yi ne? Barka dazuwa.”
“Umma ta yi murmushi, ta amsa, “Yauwa, barka kadai.”
Ganin yanayin ta da shigar ta suka sa Dada nan take ta sa Maree dauko wundin ta a daga dakin Baban su, ta shimfida mata cikin dakin ta sannan ta yi ma ta iso. 3
STORY CONTINUES BELOW
Asiya ta durkusa ta gaida Dada, ita kuma ta tambaye ta makaranta. “Muhibbat ta shigo jiya ta ke ce min kun yi waya, cewar kwana ta kama ki ko? To ya ya Malam Sunusin? Kin bar su lafiya?”
Asiya ta hadiye yawu. Ta fahimci kare ta da Muhibbat ta yi. Amma dai kam yanzu komai zai bayyana. Ta gabatar da bakuwar su wa Dada, sannan ta fita ba su wuri, ta na jin Dadar ta umurci Maree ta kai musu abin sha.
Bayan sun kebe cikin dakin su, cikin zumudi Maree ta tambaye ta, “Ya ya, kin same shin?”
Fuskar ta na nuna hankoron ta da zumudi, Asiya ta kalle ta sosai. Ko idon ta ne? don sai ta ga kamar ta kara zubewa. Ta ji zuciyar ta ta kara sosuwa. In Allah ya yarda za ta samu waraka daga yanzu, na har abada.
Ta amsa, “Na same shi.”
“To me ya ce? Me ya sa ya daina daukar waya ta? Ya amince zai aure ni? Wace ce wadda ku ka zo tare? Ko ba tare ba ne ku ke?”
Saura kadan ta yi dariya, duk da bugun da zuciyar ta ke karawa duk kowacce dakika. Ta ce, “Za ki samu amsoshin ki idan har kika bar ni na amsa su.”
Suka dan yi murmushi, Maree ta ce, “Ki yi hakuri. Wallahi tun jiya mu ke ta sa ido ni da Muhi. Ko da ba mu gan ki ba sai mu ka yi karya wa Dada, cewar kin kwana ne a gidan malam Sunusi Lalaye.”
Hmmm. To da aiki. Don kuwa al’amari ya girma, ya wuce kananan karairayin su. Ta ce da Maree, “Farko dai ya ce bai san ki ba…”
“Me ne?” Ta katse ta tare da gwalo idanun ta da dafe kirjin ta.
“Shhhh, yi a hankali. A yanzun mun zo ne da mahaifiyar sa, da ma shi kan sa.”
Maree ta kara dafa kirjin ta, “Da gaske?”
Asiya ta gyada kan ta, “Da gaske. Yan a ma kofar gida. Kin ga a yau komai zai warware, a san me a ke ciki, ko?”
Har a lokacin bata cire hannun ta daga kirjin na ta ba. Asiya ta fahimci hakan. Ko ita ma kirjin ta barazanar fashewa yak e ya fiddo da zuciyar ta balle a ce Maree.
Dada ta kwala mu su kira dukan su. Su na isa suka same ta fuskar ta daure, babu alamar haske ko kadan. A lokacin kam, ta tabbata zuciyar ta ta faso kirjin na ta.
“Ba haka mu ka yi da ke ba.” Dada ta furta cikin murya mai kaushi.
Kan Asiya a sunkuye yake, abin da ya rage cikin zuciyar ta ta na cike da nadama. “Ki yi hakuri Dada. Na san zzai yi wuya ki bar ni na je idan har kin san wurin da zan je din.”
“Ba laifin ki ba ne, laifina ne da na nuna muku yarda, har ya sa ku ka yi amfani da raunina ku ka min karya?”
Umma ta tsoma bakin ta, “Yanzu dai ki yi hakuri don Allah. Kuskure dai an riga an yi shi. Tun da mun zo, sai su je su samu Dan-autan a waje, su gama komai. A shirye nake da na tilasta masa auren mariya, idan har shi ya aikata laifin nan a gare ku.”
Dada ta kalle ta, “Idan kuma ya ki amincewa fa?”
“Wannan ne dalilin da ya sa na zo tare da shi. Ai ba shi ya yi kan sa, ba kuma shi ya haifi kan sa ba. Dole zai bi umurni na.”
Dada ta nisa, “Zai fi kyau idan ya shigo cikin nan, don a yi komai cikin sirri. Kin san nan din karamin gari ne.”
Nan take Umma ta fidda wayar ta ta latsa kira, “Ka shigo ciki.”
Ta kashe wayar sannan ta kalli Asiya, “Ki je ki nuna masa hanya.”
Ta fita zuciyar ta da nauyi. Ta san Dada dai ta yi shiru ne don Umma, amma ba wai don ta hakuran ba ne. Tabbas sai ta fuskanci hukuncin ta bayan sun watse. Lokacin da ta isa kofar gidan ta gan shi tsaye, ya na fuskantar kofar tare da wayar sa a hannun sa.
Ta nisa. Lokacin gaskiya ya yi, lokacin bayyanar haske ya yi. Za ta ga idan zai ce bai san Maree ba idan ya fuskance ta.
“Bismillah.” Kawai ta ce ma sa.
Ta yi gaba ya na biye da ita, shi ma bai ce uffan ba. Ya na tafiya kamar wanda zai shiga kurkuku. Ko da ta kai ga kofar dakin, ta yi ma sa izinin shiga.
Umma ta matsa ma sa don ya samu wajen zama a cikin tsukukun dakin su da babu girm. Gadon Dada ne daya wanda a ka shimfida wa tsohon zanin gado kodadde, sai teburin da ta jera masu murtalan ta farare a kai, da kuma wasu shirgin a ta kasan tebur din. Dakin talaka ne, amma a tsaftace ya ke.
Bayan ya samu wuri ya zauna, sai Asiya ta shiga, ta na jin yana gaisawa da Dada. Ta lura har a lokacin idaon Maree bai bar kallon kofar ba. Ta bi idanun ta, sannan ta kalle ta, “Maree, ya ya ne?”
Maree ta kalle ta cikin tambaya, “Kin ce kun zo da Yusuf.”
Asiya ta kalle ta cikin mamaki, “Eh mana. Ba gas hi nan ba?”
Maree ta kalli Dokta tare da daure fuska, ta ce, “Wannan?” sannan ta girgiza kan ta, “Wannan ba shi ba ne Dokta Yusuf dina.”Asiya ta kalle ta a firgice, “Me ki ke ce? Ba Dokta Yusuf ba ne a gaban ki?” Me ta ke shirin ji?
Mariya ta sake kallon sa, “Ko shakka ba na yi Laminde. Wannan ba s hi ne Dokta Yusuf ba.”
Ya salam! Asiya ta ji kamar numfashin ta zai dauke. Me ya samu Maree kuma? Ko ganin sa ne a gaban ta ya sa ta rude?
“Kin ce Dokta Yusuf Haruna…”
“Eh, Yusuf Haruna, shugaban asibitin Sauki da ke garin Bauchi ba.”
Cikin takaici fiye da rudani, Asiya ta kara nuna ma ta shi, “To ai shi ne wannan.”
Mariya cikin natsuwa ta ce, “Na fa san abin da na ke yi Laminde. Wannan ba shi ba ne.”
A lokacin da Asiya ta sake kallon Dokta, ta lura da cewa ya lumshe idanu tare da jan gwauron numfashin sa, sannan ya bude su ya zuba ma ta su. Ba shi kadai ba ma, hatta Umma.
“Yusuf din da na sani ya yi makaranta ne a jami’ar Maiduguri. Ya na da abokai biyu, Hadi da Sadi. Hadi matan sa biyu, amma Allah bai ba shi haihuwa ba. Shi kuma Sadi kwanan nan ya yi aure. Dukan su su na aiki tare ne a asibitin sauki tare da Dokta Kabir.
Ainihin gidan su Dokta ya na Kandahar ne, babban gida da koren fenti, gidan marigayi Alhaji Rabeh.”
Wannan karon Umma ce ta yi magana, domin Asiya ba ta da karfin yin hakan. Ba ta yarda da kan ta ba. Ga shi ta dan kalli wurin Dada, ta ga irin hararar da ta galla mata.
Jin ta ta yi kamar a tsakiyar tukubar tsire take. Sai gumi da ke keto ma ta. Yawu kuwa ya kafe a cikin bakin na ta, ta lashe labban ta, ta na jin karin sautin bugun zuciyar ta cikin kunnuwan ta. Da ta na da iko, da ta yi fukafukai ta fire ta saman dakin.
“Mariya, idan ta kwatancen ki ne, to wannan shi ne da ke gaban ki.”
Mariya ta rika kallon kowannen su kamar marasa kunnuwa, “Ni fa wannan ban san shi ba, ban ma taba ganin sa ba.” 2
Asiya ta na jin idanun sa a kan ta. Ba ta yarda da motsi ba ma, kar a tsire ta da ran ta. Ta makara wajen yin nadama. Duk bakar wahalar da ta sha, da bala’in da ta fuskanta tare da hatsari sun tashi a banza.
Har fa karnuka sun kusa far ma ta amma wai a ce komai ya tashi a tutan maho? 2
“Sai dai akwai kammani kadan tsakanin wannan da Dokta Yusuf.”
A lokacin ba Asiya kadai ba, dukan su da ke dakin suka zubo ma ta idanu. Zuciyar ta fat fat ta ke yi. Anya, ba za ta hadu da hawan jinni ba kuwa da bugun zuciya?
“Kama kuma?” Umma ta tambaya.
“Eh. Akwai dan dibi kadan. Za a iya cewa ma kanin sa ne.”
A lokacin Asiya ta dan samu kwarin gwiwar kallon Dokta, ta lura ya tsayar da hankalin sa ne kan Maree. Ta rika yin addu’a a cikin zuciyar ta, na cewar kar ya ce zai watsar da kashin su ya yi ficewar sa. Ba mamaki zai dauke su makaryata, wadan da ba su san abin da su ke yi ba. Ta san ba don Umma ba, kila da ya kira mu su ‘yan sanda sun tafi da su.
“Bai kai ka tsawo ba, amma ya fi ka hasken fata. Idanun sa manya ne, ya na da murya mai nauyi sosai.”
Dokta ya bude bakin sa yayi magana karo na farko, tun bayan sallamar da ya yi, “Ki na da hoton sa ne?”
STORY CONTINUES BELOW
Maree ta girgiza kan ta, “A’a, yawancin hotunan da muka dauka suna wayar sa ne. Ya ce zai tura min da zarar ya saya min waya irin ta sa.” 2
“Idan na nuna miki wani hoton, za ki gane shi?”
Ta gyada kan ta, “Me zai hana?”
Dokta ya fitar da wayar sa daga aljihu, ya shafa kan ta ta yi ‘yar kara, sai ta dau haske. Ya shiga shafe shafe, har ya kai ga wurin da ya ke son ya tsaya. Asiya kuwa gani take ya dauki tsawon shekara guda kafin ya kai nan, tsabar kosawar da ta yi.
“Ya na cikin nan?”
Ya nu na ma ta wani hoton da ke da mutane hudu suna zaune a jere cikin wani dakin taro, kowannen su cikin jamfa, suna fuskantar wanda ke daukan su hoton. Hoto kuwa yayi tar tar kamar za su fito suyi magana.
Ta girgiza kan ta, “Ba ya cikin nan.”
Asiya ta ji wani yawu makwat ya wuce ta wuyan ta. Ita dai sai yadda Allah Ya yi da ita kawai. Rashin fadawa Dada ne ya kawo hakan.
Da ma tun a hanyar zuwa ta ga yadda ta rika samun cikas jikin ta ya raya ma ta, cewar wannan tafiya babu alheri a cikin ta. Amma taurin kai ya kara mata kaimi. Yanzu ga shi, ta janyo mu su matsala fiye da wadda su ke cikin ta tun farko. 2
Lallai allura ta tono garma. Kaza ta tona wukar yanka kan ta. Dole mutane su yi tonon dalilin zuwan wannan mota kofar gidan su a wannan rana. Kuma za a tono asirin da suka rufe a da. Me Baban su zai ce ke nan a yanzu?
Dokta Yusuf ya ci gaba da taba wayar sa , hotuna sun a wucewa waaal waal. Ya tsaya kan hoton wani saurayi, fari sol da shi. Asiya ba ta ga kammanin sa da doktan ba. Kamar tana jin tunanin zuciyar ta, Maree ta girgiza kan ta, “Ba shi ba ne.”
Bayan kamar hotuna shida, Maree ta yi sauri ta tsayar da shi, “Wannan ne.”
Asiya ta ji zuciyar ta ta doka tsalle ta shiga bakin ta. Ta shiga rokon Allah Ya fidda ta kunya, kawai sai ta ji Maree ta kara da cewa,”Ina tsammani.”
Shi ma kan sa ya kulle, “Ki na tsammani?”
Maree ta yi saurin amsawa, ba mamaki kar a dauke ta mahaukaciya, “Eh. Saboda Yusuf ya na da gashin baki da dan saje da hana-karya. Bayan nan, babu abin da ya bamban ta shi da wanda ke wannan hoton.”
Asiya ba ta san numfashin ta na rike ba har sai da ta ga Yusuf ya kalli Umman sa, cikin murya kasa-kasaa, ya ce, “Khalid ne.”
Gaba daya Umma da Maree suka ambata, “Khalid?”
Maree ce ta kara da wata tambayar, “Waye Khalid kuma?”
Umma kuma salati ta ci gaba da yi, tana jinjina al’amarin; Yusuf ya sadda kan sa yana girgizawa a hankali, a yayin da Asiya numfashi kawai ta ke sakewa.
Ba ta san Khalid ba, ba ta san yadda a ka yi aka fara da Yusuf a ka kare da Khalid ba. Abin da ta sani kawai, shi ne tafiyar ta ba ta zama a banza ba. A kalla dai hakan ta ke gani.
“Waye Khalid kuma?” Maree ta kara tambaya.
“Kanina ne, wanda mu ke uba daya da shi. Tabbas, Khalid ya na da yayan mahaifiyar sa a Jos, ya na kuma yawan zuwa. A nan ne ina ga ku ka hadu?”
“Eh, a Jos mu ka hadu. Amma me ya sa zai min karyar suna? Shi din ma likita ne?”
Maree ta fi kowa rudewa a cikin wannan yanayi. Ita kam Asiya ta gagara ko motsi.
“A’a, ba likita ba ne.”
Dada ta yi Magana a karo na farko tun bayan shigar Yusuf, “Ni fa har yanzu ban fahimci komai ba. A min karin bayani don na gane.”
Yusuf ya nisa, “Ni ma kai na ban fahimtar nake nema. Ina neman amsoshi ga tambayoyi da dama.”
Hakika, babu mai amsa ko daya a tare da su. Iyaka dai sai an nemo Khalid din nan a same su. Karon da bata san da ba ta san adadin sa ba, Asiya ta yi nadamar tono wannan garmar. Da ta sani……
STORY CONTINUES BELOW
* * *
Yadda jirgin sama ke tashi sama haka Dokta Yusuf ya kwashi motar sa. A lokacin tafiya Dagauda ya tsula gudu don warware matsalar da ta fuskance shi.
A yanzu yana gudu ne don neman Karin amsar kullin tambayar da ya bayyana gare su.
Kwakwalwar sa gudu ta ke yi, ta na juya waannan yanayi a cikin ta. A tunanin sa, bait aba shiga tashin hankali irin na jiya ba. Ashe nafila ce.
Duk da cewar bas hi ne ke da alhakin aikata abin da ya samu mariya ba, jin cewar kanin sa ne ya yi hakan, kuma da sunan say a jefa shi cikin karin rudani.
Hakika ya waanke kan sa. Da ma bai yi tababa ko shakkar cewa sharri a ka mas aba. Amma gas hi ya kasance cewar jinin sa ne ya aikata hakan.
A kalla hakan yak e tsammani. Don ta nuna hoton khalid zai iya kasancewa bas hi din bane. Ya nag a bakin su daya ne kawai, duk gidan. Sun makala ma sa da farko, da suka ga an tsile su, sai suka canja sheka, suka nu na Khalid. Ba mamaki, za su iya wasa da hankalin kowa don wata biyan bukatar su.
Amma a can kololuwar zuciyar sa, Yusuf ya san Khalid zai iya aikata abin da a ke zargin sa da shi. Yadda Mariyar nan ta kwatanta shi, ta bayyana siffar say a nuna tabbas ta yi ma sa farin sani.
Sai da ya kara yi ma ta tambayoyi game da Khalid din, ta kuma bayar da amsar daidai. Sannan ba kowa bane ya san Khalid ya ajiye saaje da hana-karya a shekara da ta wuce. Wadannan ne suka tilasta ma sa yarda da maganar ta.
Umma ta nisa a gefen sa cikin motar. Ya san ita ma nazarin take yi, “Na dade da sanin cewa Khalid da ‘yan uwan sa suna maka wutar ciki. Amma wannan? Me za su ribata idan sun bata ma ka suna?”
Bai amsa ba, don bai san abin da zai ce ba. Ta ci gaba da cewa, “Tilas mu kara taka-tsan tsan. Mu kara bincike don tabbatar da hakan ba zai kara kunno kai ba. a yanzu dai wannan za mu fuskanta.”
Ya nisa sosai. Tilas ya fuskanci Khalid don jin amsoshin tambabyoyin da suka addabe shi. A matsayin san a dan uwan sa, bai taba ragar sa da komai ba. komai ya tambaya ko da cikin iko da gadara ne baya damuwa, sai ya biya masa bukatun sa. Shi ne zai ma sa sakayya da hakan?
Ya kara kwasar motar da gudu, zuciyar sa tana ruruwa kamar rushen wuta.
* * *
Biki ne a ka yi shi gawurtacce, kuma kasaitacce, kasancewar garin Dagauda ba a taba yin kamar sa ba. babu abin da aka nema a ka rasa, daga bangaren makulashe zuwa ga kyaututtukan da aka raba wa baki manya da yara.
Kowacce budurwa a fadin garin dagauda ta shaida cewa Mariya Sabo Ali ta yi dacen auren Mudassir. Kowacce fatan gam na katar take yi da irin mai tarin dukiya kamar sa.
Ko daga sanya suture Maree ta burge kowa, don kuwa ba karya, shiga ce ta ma su alfarma. Ba a taba tunanin za a samu wadda za ta yi shiga irin na ta ba fadin garin ma gaba daya.
Asiya ta yi tagumi ta na kallon ma su shiga da fita a gidan su suna shagali. Zuciyar ta tamkar za ta kone kurmus. Kafin zuwan wannan rana, ta roki Dada, kan cewar a fasa wannan auren, don aure da juna biyu haramun ne. amma Dada ta galla ma ta harara, sanan ta zazzage mata masifa na neman tona wa ‘yar uwar ta asiri.
Ta san zai yi wuya Dadar ta mance zuwan ta Bauchi da ta yi, kan hakan sai da suka fi kwana uku ko gaisuwar ta bata amsawa. Sai da ta kira yayyen su suka saka baki sannan. A hakan ma ba wai ta yi hakuri can can bane. Don haka, Asiya ba ta wani ja maganar da nisa ba.
Ba abin duniya ne ya rufe idanun Dada ba, face kasancewar ta uwar da ke son rufa wa diyar ta asiri, da ma su Asiyar gaba daya. Idan aka san komai wa zai auri Maree? Wa zai kula auren su Asiya daga baya?
Abin zai shafe su gaba daya, daga su har jikokin su nan gaba idan sun ma yi auren ke nan. Don haka dada taga a rufe maganar kawai, ya fi.
Dokta Yusuf ya koma dagaudan kwanaki hudu bayan zuwan san a farko. Shi kadai ya je, babu khalid. Amma ya je ne don neman wata maslaha game da juna biyun da ke jikin Maree.
Dada ba ta saurare shi ba, domin ta riga ta yanke hukunci a kan hakan. “Ba zamu yaudari kan mu. Matsayinmu bai kai mu kalli wurin da kuke ba. ina tsuntsun da ke sama, ina kifin da ke ruwa da har a ce su kulla alaka? Wanda Yalwaji za ta aura ma ita ta kawo shi, ya kuma ce ya ji ya gani, shi yasa na ba da amincewa ta. A yanzu ka tafi abin ka, Allah ya hada kowa da rabon sa.”
Muhibbat ta iske ta cikin wannan yanayi, ta zauna a gefen ta, ta dan zungure, “Ke kuma tunanin me kike yi ne kuma? Yau fa ranar auren ‘yar uwar ki ce. Ya kamata a ce kina cikin nishadi da farin ciki. Ba doka uwar tagumi ba kamar wadda kudin ta suka bata.”
Asiya ba ta yi murmushi ba, duk da ganin yada Muhibbat ke son ta sa ta sakewa. Ta ce, “Hankalina ya kasa kwanciya ne Muhi, na rasa abin daa ke mun dadi. Ta yaya za a yi wannan auren a hakan?”
Muhibbat ta dan yi dariya, “Oh, ke wannan abu ne har yanzu yak e damun ki?”
Asiya ta kale ta cikin mamaki. Ta ci gaba da cewa, “Laminde ke nan. Ai fadar da ta fi karfin ka ai sai ka mai da ta wasa. Ke dai ki saki jikin ki, don tagumin da kike yi ba zai yi maganin komai ba, sao ko ma ya saka miki hawan diwa ma ba hawan jinni ba.”
Wannan karon ta dan yi murmurshi. Muhibbat ke nan. Daga ta ce hawan diwa sai ta ce hawan ruwa. Ta girgiza kan ta. Muhibbat ta kasance kawar Maree ce tun suna firamare. Tare suka tashi suna amintar juna.
Kasancewar tazarar Mareen da na asiya ba mai yawa bane, sai ta zama kawar t ita ma. Amma dai saukin kan Muhibbat din ne da kuma gamon jinin su suka kara karfafa hakan.
“Ko ke fa? me zai dame ki, ki sha shagalin ki kawai ki more. Allah Ya nuna mana naki mu ragashe.”
Asiya ta fadada murmushin ta. Aure ne bait aba giftawa cikin tunanin ta ba. ba wai bata so bane. Kawai dai ta bar shi a matsayin ya zo duk lokacin da allah ya yi niyya. Ba ta taba matsa wa kan ta a kai ba. ita ko saurayin ma ba ta da shi. Har Maree kan nuna cewar rashin farin jinin ta ne ya hana mata yin saurayi. 2
“Ba mu sha naki ba, sai a juyo na wa?”
Muhibbat ta ce, “Kin ji ki. Abin ai na Allah ne, wai matar takaba ta yi ciki.” 4
Suka yi dariya dukan su. Har Asiya ta fara jin dama-dama, sai ga kira, “Laminde, Dada ta na kiran ki. Ta ce ki je yanzun nan.”
Ta nisa, sannan ta mike ta nufi wajen da Dada da wasu manyan mata da tsofi suke.
Ta san dai ba fasa komai za a yi ba, tun da an riga an daura auren. Kafin ta kai, ta ji Muhibbat a gefen ta. Murmushi kawai ta yi, a lokacin da ta shiga daki, ta ce, “Dada, ga ni.”