KUDIRI
CHAPTER 3
“Aure ya kunshi abubuwa guda uku; abota, aminci/yarda, sannan so da kauna. Su ne ginshikin aure, ma su saka shi yayi inganci da karko, wadanda babu ko daya a tsakaninmu. Anya, b aka ganin kuskuren aure idan babu su?”
A lokacin tana fuskantar tagar dakin, wajen da hasken alfijir ya fara bayyana. A ka fara kiraye kirayen assalatu. Ya matsa kusa da ita, y ace, “Kuskuren da zamu yin a jefar da yarinyar nan zai fi na auren mu. Kamar yadda na ce ne, auren wucin-gadi ne. Ba zan matsa miki wajen zama da ni ba. A duk lokacin da ki ka yanke shawarar rabuwar mu, ina baki tabbacin sawwake miki, ki yi tafiyar ki.”
Wucin-gadi. Ko da dai ba ta damuwa da Kalmar aure, amma ta tabbata wannan kalma ba ta cikin lissafi. A tunanin ta, aure idan aka yi shi, to na har mutu-ka-raba ne. Karewa ma, ba ta taba tunanin wani zai nemi auren ta a dakin asibiti wajen karfe hudu na asubahi ba. Abin kamar a mafarki. 2
Ta dan kale shi, “Ka fada min abin da Umma ta ce game da wanna shirin.”
Bai kalleta ba, “Ban fada mat aba tukunna. A tunani na, bayan mun daidaita sai na fada mata.”
Duk da cewa Umma ta matsa ma sa kan yayi aure, yanke wannan shawarar da yayi ba tare da neman shawarar ta ba gaganci ne. amma shi a gaban sa jaririyar nan ce.
Ya ji ta ce, “A duk aikin da ake so yayi kyau ya na da muhimmancin a samu hannun manya. Duk da na san mahaifana ba lallai sub a da goyon baya gare ni ba, zan so a ce Ummarka ta san shawarar da ka yanke.”
Dokta ya ce, “Fair enough. Yanzu zan je na yi sallah. Kafin azahar zan dawo nan, a lokacin zan so jin amsar ta ki.”
Da wannan ya dan tsaya a gefen jaririyar, wacce ke barcinta a tsanake, sabanin asubahin jiya. Ya sa hannun sa duka biyu ya dauke ta, ba tare da karin magana ba, ya kai kunnuwan ta dab bakin sa……
* * *
Asiya ta tsaya kallon Dokta Yusuf, wanda ga alama, huduba yak e yi wa Baby A. hakan ya matukar sosa mata zuciya. Idan a da ta na shakkar son da yake yi wa yarinyar, a yanzu ta cire. 8
Ya ajiye ta a kan gadon ta sannan ya ci gaba da kallon ta, “Na rada mata suna Amatullah. Ina mai mata addu’ar Allah Ya raya ta cikin addinin musulunci, Ya kuma daukaka ta duniya da lahira.” 2
Kwalla suka ciko idanun Asiya, ta ce, “Amin.”
Har ya bude kofar zai fita, ya tsaya ya sake kallon Asiya, “Kar ki matsa wa kan ki. Idan har zuwa lokacin da na dawo amsar ki a’a ne, ina baki tabbacin komai zai zauna tsakaninmu a matsayin sirri. Zan ba da mota a mayar da ke har gida cikin aminci. Ina son ki sa abin cikin addu’a. allah Ya mana jagora.”
Daga nan ya fice, ya bar ta da neman wuri ta zauna don kar kafafuwanta su jefar da ita. Sai a lokacin komai ya zo mata gaba daya.
Da farko ta dauka ko zagin kunne ne, ko ma zolaya da rainin hankali. Daga baya ta ke tabbatar da cewa kudiri ne, wanda ko da ita ko babu, yayi niyyar cimmawa.
Ta kowane bangare Yusuf ya na ba ta mamaki, da ma fargaba ko tsoro. Kalaman sa sun jijjiga ta, sannan suka yi majajjawa da ita zuwa wata duniya daban- wurin da komai ke faruwa cikin mafarki. Ba ta san ko hakan abu ne mai kyau ba. 1
Kai tsaye ta samu kwarin gwiwar shiga bandaki ta yiwo alwala sannan ta dawo dakin ta bada farali. Ta na zikiri baby A…. Amatullah, ta motsa daga kwance.
Ta mike cikin sauri ta daga ta tun kafin ta bude bakin ta ta rera mu su wakar da babu kida. Ta bata ruwan dumi kadan ta sha. A zuciyar ta, ta so ta bata ruwan zam-zam ne. amma babu abin da ke tafiya daidai game da rayuwar Amatullah.
Amatullah, baiwar Allah. Sunan ya dace da ita matuka. Ta rungume ta, zuciyar ta na nazari. Kamshin Dokta Yusuf da ke jikin shawul din daukar ta ya kara shige mata kwanya. Ta kara tuna da kudirin san a rike Amatullah ko da ita ko babu.
STORY CONTINUES BELOW
Ta kuma tabbata idan ba ta amince ba akwai dubban matan da zasu daka tsalle su karbi tayin sa da hannu bi-biyu ba tare da wani dogon tunani ba. Don kuwa ba kullum ne a ke samun damar rayuwa irin wannan ba; rayuwar sukuni da jin dadi, rayuwar cikar mafarki.
Hakika Yusuf ya tabo wurin da yake mata kaikayi. Idan ta aure shi za ta samu damar da ke nema a can cikin zuciyar ta, damar ci gaba da karatun ta. Ta tabbata ba zai saba alkawari ba idan ya dauka saboda kamalar sa da natsuwa. Amma me yake hana ta amincewa ne da auren na sa?
Ta sake nisawa. Idan Maree ta dawo fa, yaya matsayin wannan tsarin na su? Da a ce Mareen bata gudu ba, da ita zai aura ko kuwa? 2
Ta san dai gaibu, kuma ba ta da hurumin tunani a kai. Amma duk da hakan ta kasa karkato zuciyar ta daga kai. Ta san idan Maree ta dawo komai zai lalace.
Ta mayar da Amatullah a hankali tamkar kwai zuwa makwancin ta. Ta san za ta iya rasa komai idan Maree ta dawo, a duk lokacin da ta dawo, idan har ta dawo din ke nan.
Ta sake wata nisawar. Ra’ayin Umma ta ke son ji, ko za ta amince da dan ta ya aure ta…a matsayin mata, ko kuma mai reno? Ta lumshe idanun ta. Ya Allah! Ta na neman jagora a kan wannan kudiri na su, domin kudirin say a zama na ta, na ta ma yanzu ya zama na sa. Amatullah…..
3
* * *
Atishawar da a ka yi ne ya fargar da Asiya. Ta kalli gefen ta, Gwaggo Tambaya ce ke jaye-jayen hanci. Ita ma kanta murar ta fara kama ta. Balle ma yanzu hunturu ne a ke yi sosai, ga kura da hazo.
Ta mayar da hankalin ta gefe tagar motar da take cikin ta. Gilas din ya na baibaye da bakin yadi, don haka bata iya ganin waje sosai sai ta manne da goshin ta. Idanun ta na kallon duwatsu, bishiyoyin da ma gonakin da ke kan hanya. 2
Hankalin ta baya kan su balle ta yabe su. A ranar sati guda ke nan da ta koma Dagauda bayan maganar ta da Dokta Yusuf. Ta tuna kowacce kalma, kowane lafazi.
A ranar ne kuma a ka daura auren su. Sai da ta ji yaar a jikin ta. Kowacce amarya ta na zumudin ranar bikin ta, ta na dokin shiga sabuwar rayuwar ta. 6
A duniyar nan, ba ta hadu da wadda ta yi aure irin na ta ba. A ce mutum ko kwakkwarar Kalmar arziki ba ta taba hada shi da wanda zai aura ba?
Babban gudumawar da ta samu it ace daga Umma. Umma ta nuna goyon bayanta kwarai matuka, ta kuma bude hannayen ta hannu bi-biyu, a zahiri, ta karbe ta. Ba kamar mahaifin ta ba, wanda ya nuna kyaliyar sa ga shirin karara. 3
Ko dayake, har zuwa lokacin da Dokta ya sa aka rufe ma sad akin na sa da rufin kwano sannan aka yi fenti wa sauran gidan bayan an musu filasta da suminti fes. A cewar sa, saboda karbar bakin su. 2
A zuciyar ta, Asiya ta san yayi hakan ne don ceto mahaifan nata daga karin shiga abin kunya ne ya sa. don kuwa duk gari ya dauki maganganun su. Ko ina shi ake nunawa. A je har rumfar sa a kasuwa ana masa habaici da gatse.
Dada kuwa ba mai fita ba ce tun can. Don hakan na ta ya zo da sauki. Amma fa an samu ma su shiga har gida, wai sun je yi mata jajen abin da ya faru.
Wannan yanayi ya na daya daga cikin dalilan da suka sa Asiya amincewa da auren bokan turai. To a yanzu kuma, sai me? Ta zama matar sa, yaya ke nan? Ta dan nisa, tana yawan yin hakan a cikin kwanakin nan. Ta san don yawan tunani ne ke kawo mata hakan. Komai nata na faruwa ne kamar yadda ake bude shafin littafi, da sauri sauri.
Me za ta tarar a gidan Dokta Yusuf? Sabon yanayi, fargaba da zumudi suka cika zuciyar ta. Dokta bako ne gare ta, domin ba ta san halayen sa ba balle a ce hakan ya kawo mata natsuwa da sukuni.karewar komai ba, ba ta tabbatar wa kan ta ko ta yarda da jinsin maza ba ma. Ita dai kawai idan ta tuno da Amatullah to sai ta ji karfin gwiwa.
STORY CONTINUES BELOW
Ta tuna da maganar da suka yi a wancan rana, kafin ta yarda ta amince da auren sa. “Ina da wani sharadi, idan ka yarda, to sai mu yi aure.”
Ya dan saki murmushi, ta kawar da kan ta dole, sannan y ace da ita, “Ina sauraron ki.”
Haka karar bugun zuciyar ta take? Ta so ta dan dafe kirjin na ta, don a tunanin ta ya na iya jin karar sautin. Ta daure ta ce, “Hakika b aka boye min manufarka na yin wannan aure ba, hakan ya san a ke kara yi maka godiya wajen sadaukarwar da ka yi wa Amatullah. Ba kowa bane zai yi hakan, musamman a wannan zamani. Shi yasa nake kara yi maka godiyar bani daman a zama uwa ga Amatullah, ka yarda cewar zan iya.
“Sai dai abu daya nake son ka fahimta. Zan iya zama uwa ga Amatullah, surika ga Umma, amma b azan iya zama cikakkiyar mata gare ka ba.”
Ya kalle ta sosai, “Ba kya da hannaye biyu ne? ko kafarki daya kike shirin cirewa?”
Ta kalle shi sosai, ba wai bai fahimta be ne, kawai ya mayar da abin barkwanci ne. wanda ba hakan take so ba. Ta fi so ya dauki komai da muhimmanci.
Tilas ne ta yi hakan, ta gina katangar karfe a tsakanin su, domin ta kare zuciyar ta daga afkawa cikin kogin kaunar sa. ya yarda da ita, ya amince mata wajen kulawa da Amatullah. Duk wani abin da zai ratsa zuciyar ta zai iya sawa ta mance da ita. Hakan kuma saba alkawari ne.
Ta amsa da cewa, “Ina tabbatar maka da babu ko daya daga ciki.”
“Hakan ni ma na yi tsammani.”
Ta lashe labbanta, wadanda ba ta san sun bushe ba sai a lokacin, ta ce, “Don Allah, bana son ka min gurguwar fahimta. Auren ka zai bani damar cikar mafarkina tare da samun rayuwa mai ma’ana. Don haka zan yi komai don ganin ban gaza ba, don tabbatar maka baka yi nadamar zabena ba….”
“Idan na fahimce ki, ba za ki iya hada shimfida da nib a.” 2
Sai da taji zuciyar ta tayi yamutsi a lokacin da ta ji ya furta abin da take son fadi, kai tsaye ba tare da wani shamaki ba. Kunya ce ta fi damunta, don yin irin wannan hirar da namiji, kuma wanda zata aura, amma bata san shi ba… 4
“Ina son ki san cewa daga lokacin da na biya sadaki aka daura mana aure, to mun zama ma’auratan juna, ma su hakkoki. Aure ya wuce tsarina da tsarin ki. Allah (SWT) ne Ya tsara. Ba na jin akwai dalilin da zai sa ki kaurace wa shimfida ta, alhali ba na da niyyar tauye mi ki hakkin ki ko daya.”
Ta ji yawu ya wuce ma ta ta wuya da sauri, “Ba hakkin ka nake son tauyewa ba. Kawai na fi son mu fahimci juna,idan har zamantakewar mu tayi karko…idan komai ya daidaita….”
Wai shin me take fada ne? ba ta yi zaton za ta samu gargada ba cikin wannan tsarin nata. Ta ma yi tsammani daga bangaren sa wannan sharadi zai fito, amma sai ya bata mamaki da bai ma zana shi cikin tsarin zamantakewar da za su yi ba.
“Aure za mu yi, Dokta. Auren wucin-gadi. Ba na jin ya dace mu tsarar zamantakewar mu a kan tsari mai dorewa ko na dindindin.”
“Fair enough, hakan ba laifi. Na amince da sharadin ki. Babu hada shimfida, kowa da dakin sa.” ya kalli agogon sa kamar mai gudun kar ya makara, “Anything else? Akwai wani abu bayan wannan?” 5
Ta girgiza kanta, idanun ta a kasa. A kalla an samu wata fahimta a tsakanin su. Suka shiga gargadar da ta dan jijjigata tare da taimakawa wajen farfado da ita daga dogon tunanin ta. Har ma sun isa cikin garin Bauchi, don ta gane babban rawul(roundabout) din da ke kasuwar central. Daga nan suka dauki hanyar zuwa gidan Dokta. 5
Ta tuna da yadda hanyar take, tun ranar da ta fara zuwa garin da kudirin neman sa. a yanzun ma ba ta mance ba, kawai dai wannan karon, a matsayin matar sa ta sunnah za a kai ta. Matar wucin-gadi, ta tunasar wa kan ta.
STORY CONTINUES BELOW
A gidan sun samu tarba daga ‘yan uwan Dokta. Motoci uku ne a ka tura mu su. Biyu kanana, guda kuma bus komfuta. An kais u masaukin su, wani bangare ne na gidan Dokta, wanda ke gefe da gidan nasa ta baya.
Bayan sun idar da sallolin zuhr da asr, a ka jera mu su manyan kwanukan abinci na zamani cike da abinci iri da kala. An zuba musu jus-jus din nan kamar motar daukarsu ce tayi barin su a wajen. 3
Sun ci, sun sha, sun kuma gyatse. Har ma akwai wadanda suka kunsa nama a ciki ledodi, wai za su yi tsaraba da su. Duk da hakan, wanda suka ragen ya na nan.
Bayan sallar isha’i suka nemi a kai su wajen Umma don za su kai mata amarya.
Ba tare da bata lokaci ba, a ka nuna musu hanya. Gwaggo Tambaya ce jagora, “To, Hajiya. Ga Laminde nan mun kawo miki a matsayin diyarki, ba matar danki ba. Don Allah, kar ki kawar da kanki a kan laifuffukan da za ta rika aikatawa cikin kuskure ko ma ganganci. Ki rika yi mata fada yadda ya kamata, domin mun riga da mun zama daya. Ki kuma kara hakuri, don zama da yaro dole sai da hakuri.”
Kan Asiya a sauke yake, a lullube. Amma tana iya jin fara’ar da ke muryar Umma, tana cewa, “Ni zan muku godiya, da kuka bani diyar ku kyauta. In shaa Allahu, b azan bambanta ta da Dan auta ba. A wurina duk daya suke. Don haka zan rike ta ta yadda har za ta mance da soyayyar da kuka nuna mata can baya.”
Suka yi dariya gaba dayan su. Gwaggo ta ce, “Ai hakan a ke so Hajiya. Hakan mu ke so mu ma.”
“In Allah Ya yarda, hakan zai faru. Domin na fi kowa farin cikin wannan auren. Ba zan iya kwatanta muku misali ba. Ina mai fatan Allah Ya taya mu rikon amanar da kuka danka mana, Allah ya danka mana. Allah Ya mana jogora, duniya da lahira.”
“Amin!” sauran jama’a suka furta.
Umma ta sa a ka mika musu akwatuna biyu manya, cike tab. Ta nuna babban cikin, ta ce, “Ga kayan godiyar uwa, wanda a ka ce kuna yin sa a ta can garinku. Karamin kuma na sayen bakin uwa ne. Don haka muna kara yi muku maraba.” Daga nan suka yi godiya, sannan suka nemi a nuna musu dakin amarya.
Kamshi yana baibaye da gidan, kamar yadda Asiya ta ji tun zuwan ta na farko. Sai ma abin da ya karu, ba raguwa. Ana tafe ana rusa guda, wasu har da wake-wake iri iri. Ita dai tana jin ta ne tana taka kafafuwan ta daya gaba, daya baya.
Ko da suka shiga dakin, ba ta daga lullubin fuskar tata ba. Tana iya jin yadda sauran matan ke yabon tsarin dakin. Amma hakan bai sa ta bude fuskar ba.
“Minde, bude idanun ki ki ga dakin ki.”
Muryar Muhibbat ta ji, wadda ta zauna dab da wurin da take, a kan wani bencin da ke jikin gadon dakin. Ba ta bude ba. Muhibbat ta ci gaba da cewa, “Ke sun watse dai. Sun koma masauki. Don haka ki bude idanun ki, ki kalli gatan da mijin ki yayi miki.”
Miji. Wannan kalma tana kara razana ta. Shi mijinta ne, ita kuma matar sa ta sunnah. Ta sha tambayar kanta tun bayan daurin auren su; shin abin da tayi daidai ne? daidai ne, wani bangaren zuciyar ta ya raya mata.
Komai daidai ne, komai yadda Allah ne Ya kaddara. Kuma komai Allah Ya yi, daidai ne.
Ta bude fuskar ta hankali, a tunanin ta, Muhibbat zolayar ta take yi. Ta yi tsammanin bude ido taga kowa ya na kallon ta. Amma kuwa da gaske ne, duk sun watse.
Ta tambayi Muhibbat, “Ina suka je kuma?” Ta fi jin mamakin yadda har suka watsen amma bata gane ba sai da a ka fada mata.
“Ina na san musu. Sunje kara cika tankunan su ne, tun da cikin su ya sauka a yanzu. Sai dai Allah ya kiyaye zawayi kawai a daren yau. Hahaha.” 4
Asiya tayi murmushi, “Kai Muhi. Wacce irin fata ce haka?”
“Hmmm wai tambayat ma kike ne? don dai baki ga irin yadda suka rika handama abincin bane kawai. Ci suke da shi aradu, kamar lalle. Ni dai b azan kwana can ba, amma ina tausayin ma su kwana.
Bandaki daya ne kuwa, za sha layi. Kuma zan yi in ce musu duk wadda ta fita waje don yin zawayi to ta kuka da kan ta. Domin kuwa za a sake manyan karnukan da suka fi dan maraki girma suyi watanda sa kafar mata.”
Sai da ta ji dariya ta kubto mata, “Kai Muhi.” Ita ma kanta sai da tunanin karnukan suka zo mata. Ba ta ji kukan su ba, har ta dauka ko bas a nan ne. Amma a yanzu da Muhibbat ke Magana, sai ta fara jin haushin su.
“Kin san dai ba za sake karnuka ba tun da sun tara baki.”
Muhibbat ta yi miskilin murmushi, “Ke kin san hakan, ni ma na sani. Amma sub a su san hakan ba.”
“Babu kyau fa Muhi.”
Muhibbat ta murguda bakin ta, “Kun ji min Laminden nan fa. Sai mutum ya shirya ‘yar abin sa ki zo kina wani ‘Babu kyau fa Muhi’. An ce mi ki maganin su ke nan. Kin manta yadda suka yi ne a bikin Maree lokacin da muke Azare?”
Nan take ta ji zuciyar ta ta matse kamar kayan da za a shanya. A yau ne ranar farinciki gare ta, ko ma wani abu mai kama da hakan. Amma babu ‘yar uwar ta a tare da ita. Shin ina ta shiga ne? wane hali take ciki? A kullum tambayoyin da ta sha yi wa kan ta ke nan.
Muhibbat ta bata ranta, ta ce, “Wai ke hakan za ki ci gaba da bata ranki, a duk lokacin da a ka ambaci Maree? Kar fa ki manta, zabin ta ne, guduwa ta bar ku. Sannan ba ke kadai b ace ke bukatar wannan auren da kika yi yayi kyau. Dada ma ta dora fatan ta a kan ki.” 9
Asiya ta kale ta, “Dadar? Da gaske Muhi?”
Muhibbat ta gyada kan ta, “Da gaske na ke Minde, kin san mun tattauna yadda za a yi da Amatullah tun bayan da Baba ya je har Bauchi ya mayar da ita gida. Ta gagara samun natsuwa kan barin ta da suka yi. A lokacin da kuka zo mata da zancen auren ku, baki ga yadda ta yi murna ba. Kawai ba za ta nuna miki ba ne.”
Ta ji wasu kwalla na farin ciki sun ciko mata. Ta san dai Dada ba ta furta mata komai game da auren ta ba. Amma jin kalaman Muhibbat sun sa ta ji sanyi cikin zuciyar ta. Ta goge hawayen da ya kubuce ya sauka kan kumatun ta.
“Ahh, kar ki bata min jin dadina da kuka, kina ji na? Wato nib a ‘yar uwar ki ba ce, sai Mariya kawai?”
Asiya ta ji zuciyar ta ta sosu. Za ta yi magana, Muhibbat ta katse ta, “Don Allah bar ni na kare wad akin nan kallo. Kar ki kara bata min rai.”
Asiya ta nisa, fuskar ta da murmushi. Muhibbat za ta iya bata rai. Amma tana da saurin sauka. Balle ma a lokacin ba fushi ta yi. Kawai so take ta ja akalar hirar su zuwa wani abin daban.
Ita ma ta bi sawun Muhibbat, na kallon dakin da aka tanadar mata. Gado daya ne tilo cikin dakin wanda ya ji shimfida da zanin gado kalan ja da fari, hade da makeken madubin sa da wadurof. Dukan su launin ruwan kofi(coffee). Akwai abin ajiye takalma a gefen sa mai girman gaske. Akwai kuma iyakwandishan babba irin split din nan. 2
Akwai kuma manyan tagogi wadan da aka rufe su da labulaye manya kuma dogaye masu kyaun gaske. Sannan ta lura da kofofi biyu; daya na shiga cikin dakin da fita, sannan dayan kuma tana tsammanin bandaki ne. don haka taga tsarin yake a lokacin zuwan ta na farko.
Ko da ta bude kofar bandakin, ta gan shi da girma da ma fadin gaske, fiye da wanda yak e dakin baki a kasa. A lokacin ta lura da wata kofar da ke bangare guda ta karshen bandakin. Ko ina zai bulla? Oho.
“Minde, zo ki ga.” Ta jiyo muryar Muhibbat. Ta rufe kofar ta je wajen da take tsaye hankalin ta na kallon wani wuri. Ko da ta iske ta, ita ma ta ga abin da take gani. Dan karamin daki ne da take ga an yi shi ne don zuba akwatina, wato boxes room.
Akwatuna ne a jere guda goma, wato set mai biyar biyar kala biyu. Ta zaro ido, zuciyar ta na tsere. Me ke nan wannan? Ta tambayi Muhibbat a bayyane, “Akwatinan waye?”
“Nawa ne.” muhibbat ta amsa, fuska a daure. Hakan ya sa Asiya ta kalle ta, ta na murmushi. 3
“Dakin na waye?” Muhibbat ta tambaya. “To kamar yadda dakin ya kasance naki, haka ma kayan. Ina tsammanin kayan aurenki ne. don haka ki bar tambaya marar ma’ana. Da n ice ke, da mayar da hankalina zan yi wajen kyankyashe ‘ya’yan da za su cika makeken gidan nan. Ba tambayoyi ba.”
“Haba Muhi, sai k ace wata kaza?”
“Tab. To meye? Allah Ya miki gyadar dogo, sama ‘ya’ya, kasa ma ‘ya’ya. Ni fa ‘yar fada miki gaskiya ne. Haaa! Allah Ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba zai yi birgima. Allah Ya bani mijin aure ki gani.” 2
Cikin murmushi, ta ce, “Allah Ya baki.”
Ita kanta Asiya ba ta yi tunanin samun miji kamar Dokta Yusuf ba, amma gas hi Allah Ya ba ta. Ko da ma a ce na wucin gadi ne ba dindindin ba. A kalla, Allah Ya mallaka mata farincikin zama mata da uwa a lokaci guda.Assalamu alaikum.” 2
Wata mace kyakkyawa da ita, fara sol mai kyaun sura da sutura ta shiga dakin. Ta matsa dab da su cikin fara’a. ga ta da kyaun diri, tana ta kamshin dadi. Hakan ya sa Asiya jin kaskanci da karanta. 2
“Amarsu ta ango, mai dadin tuwo. Lallai na taki sa’ar kasancewar wadda ta fara ganin fuskar ki.”
Asiya tayi murmushi. Irin shigar da wacce ke gaban ta , idan an gan su za a yi zaton it ace amaryar. Irin su ne suka dace da auren maza irin su Dokta. Ba irin ta ba. Komai nata ya na nuni ga ajin ta da kwarjini ba tare da nuna rawan kan ta ba. 2
“Sunana Sara. Ina fata nan gaba ni da ke zamu saba sosai. A halin yanzu, so nake na ji ko da wani abin da kike bukata?”
Asiya ta amsa, “Babu komai.” Alhali so take yi ta tambaye ta Amatullah. Bakin ta ne ya mata nauyi.
Bai kyautu ta rika nuna wa mutane dalilin amincewa da wannan auren ba. Kawai dai ita ke bukatar tuna wa kanta hakan, musamman idan ta ji rudani ya sauka mata. Ganin Sara ne ya kara ankarar da ita cewa ruwa ba sa’ar Kwando ba ne, linzami kuma ya fi karfin bakin kaza.
“Kin tabbata?” hakorin Makkan ya bayyana cikin jerin fararen hakoranta farare fat, masu kyaun tsari.
Asiya ta gyada kan ta, “Na tabbata.”
Sara ta ce ta na zuwa, sannan ta fita daga dakin. Ta ji Muhibbat ta riga ta furta abin da ke zuciyar ta, “To ita kuma wannan wace ce?”
Ita ma bata da amsa. Tunanin ta, idan har Dokta ya na ganin ire-iren su Sara, to lallai ba zai ma kalle ta a matsayin komai ba. Ta san ya zabe ta ne don ita ce kanwar Maree, uwa daya uba daya. Ba don hakan ba, ko kallo ba za ta ishe shi ba. 2
Sara ta dawo, ta na tura wani abin ajiye kooler na abinci wanda ta jera wa kuloli manya guda uku, filet filet da kaofuna. Sannan a gefen su kuma da ruwan sha masu kala da bakin ruwa.
Ta ce da Asiya, “Amarsu ta Ango, ga wannan na kawo miki. Na san ba ki wani ci abinci ba dazu. Kar Yayana ya zo ya ce na bar ki da yunwa.”
“Yayan ki?” Muhibbat tambaya.
Sara ta yi murmushi mai fadi, “Ni kanwar ango ce, wacce ya dora wa nauyin kula da ke a wannan lokaci. Ba zan so yaga gazawa ta ba.” 4
Sanyi ta ji ya sauka Asiya, ba ta san dalili ba. Wato dai ashe kanwar sa ce. To amma bata fayyace yadda suke ba. Uwar su daya uba daya, ko ‘yar kawu da dan gwaggo ne? Shin duk zuri’ar su kamar Sara su ke? Yusuf kyakkyawa ne, haka nan ma Khalid.
6
Wai ma shin ina Khalid ya ke ne? Bai kamata bane a ce ya bayyana kan sa ko don saboda Amatullah? Me yasa bai taba zuwa ziyartar su a asibiti ko sau daya ba? Hakan ya nu na ba ya son Amatullah ke nan, ko kuma bai san dai ta ba. Hakika tun farkon faruwar al’amarin nan Allah bai sa ta yi ido biyu sa shi ba. Ko me ye dalili? 2
Bayan Sara ta tafi, Muhibbat ta bude kwano daya, kamshin fefesun kaji ya buso hancin ta. Ta shaka sosai, sannan ta ce, “Oh, garin dadi ya na nesa, ungulu ta leka shadda.” 6
Ta dauki filet daya, ta fara zuba wa. Ba ta damu da duba sauran abin da ke wadancan kwanukan ba. Asiya ta ce, “Muhi, me ki ke shirin yi? Duk abincin da ki ka ci har ki na da wajen zuba wannan?”
Muhibbat ta finciki cinya, ta ce, “Yarinya, zubi in dai ba na adashen kudi ba ne babu matsala. Balle ma, me ye na ci? Kawai shinkafa ce dafa-duka, sai salak, soyayyen nama da ferfesun kifi. Ban sha ferfesun kaji ba ai.” 10
Asiya ta rike baki, sannan ta ce, “Tab! Yau a bandaki za ki yi shimfidi ki kwanta. Wannan irin hadin duk a cikin ki ke kadai?” 3
Muhibbat ta tsotsi kashin cinyar da ta dauka, “Kin san ba zan bari a riga ni ba da labari ba. Don haka komai sai na ci a yau din nan.”
STORY CONTINUES BELOW
Asiya ta yi dariya, “Komai dai?”
“Eh. Ai ciki roba ne. zai dauki komai in gaya mi ki ba tare da ya fashe ba. Ko ferfesun giwa a ka kawo yanzu zan karba in ci. Kin san na fi kauri ta nan.”
Asiya ta yi dariya ta na girgiza kan ta, “Ban yi tsammanin za a samu ferfesun giwa nan kusa ba.”
“Ai wai misali ne.”
Asiya ta koma baking ado ta zauna a kai. Katifar mai taushi da dan tauri, tana kallon dakin. Muhibbat ta zauna a gefen ta, ta na jan hancin yajin ferfesun da take sha.
“Ke fa na lura, kin gagara sakewa Minde. Don Allah, ki saki zuciyar ki, aure fa ki ka yi. Aure ya na da aibu ne?”
Asiya ta nisa, “Ba ya da aibu, na san haka. Amma aurena bai yi kama da irin yadda nake jin labarin na wasu ba. Za ki ‘yanmata sun aba da labarin yadda suka hadu da samari, yadda suka fada soyayya, ire-iren gwagwarmayar da suka kwasa. Ni kuwa aure na yi don renon ‘ya.”
Wani daci ya cike mata baki, a yayin da take neman mayar da kwallar da ya ciko mata idanu. Tun suna yara har suka girma, Mariya ta na matukar son juya ta son ran ta. Ko makarantar da suka yi, shekarar da suka kamala firamre Maree ba ta ci zuwa sakandare ba, ita kuma Asiya ta ci zuwa makarantar mata na Bauchi, wato GGC.
Don tsabar tada-zaune tsaye, ganin ba za ta samu zuwa ba, a dole Dada ta tilasta wa Asiya ta hakura da zuwa sai zagowar shekara idan Mareen ta sake rubutawa ta ci. A cewar Dada, zuwan da za ta yi ita kadai ba zai yi kyau ba. Tun da komai tare a ke mu su da ‘yar uwar ta ta. 2
Wata shekarar kuwa da ta zago, Allah Ya yi, Asiya ta sake jarrabawa, ta ci zuwa Makarantar Gwamnatin Tarayya da ke garin Azare. Nan ma dai don Mariya ta ci Makarantar horar da Malamai na mata, wato Women Teachers College da ke Azare, sai a ka tura su duka can.
Akwai misalai iri daban daban da Mariya ke tsallake Asiya, amma Dada bata cewa komai. Misali, yadda Mariya ke zuwa hutu garin Jos ita kadai; ko yadda idan an yi dinkin kala daya na sallah, Mariya ba ta hakura ta bar mata. Idan kuma har a ka yi guda biyun, bayan Maree ta zaba, sai ta sake komawa ta same ta da lallamin cewar ta bar mata natan, don ya fi mata kyau. 2
Komai Asiya ta na jurewa ne gudun kar Dada ta dauka it ace ke jawo fitina. Hakika komai ta yi, Dada sai ta ga girman sa. idan kuwa Maree ce, sai ta ce dama haka halin ta yake, ya zama dole a lallaba ta. Babu wanda ya taba ba wa Asiya abin da ran ta ke so, sai ko idan Maree ce ta ke son a bata. Ta sha nuna son abu daga baya idan Maree ta ce ita ma tana so, sai a karbe a ce ita ta yi hakuri. 5
“Ungo wannan.” Muhibbat ta mika mata ribena mai sanyi tare da filet cikin sakwara miyar ganye da rabin kaza a gefe. 3
Ta ci gaba da cewa, “Karbi abin da zai taimake ki, kin ji ko? Don ba wa ni za ki yi gulma da makokon nan ba.” Ta murguda bakin ta.
Asiya ta na son ta ki, amma Muhubbat ba ta bata damar hakan ba, “Ina fa ganin ki, yadda kika wani numfasa bayan Saran nan ta bayyana miki cewar ita kanwar Dokta ce. Yanzu kina wani cewa wai auren reno.. mene mene. Karba ki ci dalla, ‘yar rainin hankali kawai.” 1
Asiya ba ta san lokacin da dariya ta kubuce mata ba. Ta yi kokarin lullube kunyar da ta kama ta a lokacin. Ta ce da Muhibbat, “Kef a baki da kirki wani lokaci.” Sam,ba ta lura cewar Muhibbat ta lura da ita ba.
“Ke din kirkin ne da ke? Ki dai zauna garin kallon ruwa kwado ya yi mi ki kafa. Ko so ki ke a kira shi ya zo ya baki bakin ki da hannun sa?” 4
Ta gwalo idanun ta, don kuwa ta san Muhibbat za ta aikata hakan idan ta kuskura ta bata dama. “Ki yi hakuri. Zan ci amma bari na yi sallah tukunna.”
“Ko ke fa? aure ya kamata a shiga cikin san a farin ciki ba zullumi ba. Wa ya san gobe? Ki na ganin da baki burge shi ta wani waje, zai kwatanta auran ki ne? Na san dai auren na ki ya zo cikin gaggawa ne, amma idan ki ka mayar da hankali, za ki yi nasarar shiga zuciyar sa ki rike. Namiji ne fa shi.
STORY CONTINUES BELOW
Duk namijin da ya auri mata kuwa, biyyayar aure ke sa hankalin say a koma gare ta. Idan ki ka kula da cin sa da shan sa, dama gidansa da Umman sa, to kin gama da shi. An ce miki amatullah ce kadai ke bukatar renon? Har shi ma yana bukata in gaya miki.”
Asiya ta dan zauna nazari, “Ban yi tsammani Dokta cinya ta za ta iya daukan sa ba balle na ba shi abinci cikin baki kamar jinjiri.” 3
Muhibbat ta galla mata harara, ita kuma ta mike zuwa bandaki don ta yi alwala. Fitowar ta, ta ga Sara, wannan karon tare da wata. Suna rike da wani ambulam da karamin akwati.
“Yaya Yusuf ya bayar da kudin barin dandali.” Ta mika mata ambulam din. Ta ba su akwati, “Kayan sayen baki namu na kanne da yayyen sa. akwai kuma na aure, wanda ke dakin akwatuna. Kuna iya duba su a lokacin da kuka samu dama.”
Muhibbat ta karba ta bude ambulam taga damin kudi ‘yan dubu guda biyu. Ta fitar da kadan daga ciki, ta ce, “Madallah, ga tukwici. Kar ku ce ba za ku karba ba. Domin yaba kyauta, tukwici.”
Sara ta karba tare da yin godiya, sannan ta yi mu su sai da safe, suka fice tare mataimakiyar ta. Muhibbat sai da ta mike don tabbatar da cewar sun tafi, sannan ta dawo ta zauna, “Laminde, duk wannan kudi wa barin dandali kadai? Oya, cire min kaso na, don nice uwar saka gada a dandali.” 1
Suka fashe da dariya, sannan suka bude kayan akwatin suna kallo,har ma da na lefen na ta. Sai gari yaw aye za su nu na wa sauran da iyayen su. Kaya ne da Muhibbat ke tabbatar mata, da cewa sun nu na yadda bokan turai ya ke mutunta matar sa, ya ke darraja ta. 4
* * *
Dokta Yusuf ya fito daga daki na karshe daga zagayen dakunan majinyata da ya yi, sannan ya shige ofis din sa. Ya san so yake lokaci ya tafi da sauri, amma a halin da ake ciki, tafiyar hawainiya yake yi. Don kuwa ya kamala dukkan abin da ya kamata ya yi amma lokaci ya na tsaye.
A wannan rana shi ango ne, wanda aka kai wa matar sa har gida. Sai dai baya jin zumudi irin na angwaye. A kalla ba kamar dai lokacin sa da Abida ba.
Ya nisa sosai. Ba zai taba sanin yadda auren Abida yake ba, tun da bai dandana ya ji ba, tun da dai mutuwa tayi da auren sa, amma bata taka kafar ta zuwa gidan sa ba. Allah bai nufi hakan ba. wanda Ya nufa din kuma kamar a tatsuniya.
Wasu lokuta sai ya rika ganin kamar ba shi ba ne yayi aure, har ma yake rike da jaririya. Hakika, Amatullah it ace abar kulawarsa a halin da a ke ciki. Ya tuno da hasken fatarta, da girman kwayar idanun ta. Yarinyar a kullum kara kyau take yi.
A dazu da yaje duba lafiyar ta a dakin da ya kebe mata na asibiti, ya tabbatar da samun lafiyar ta, a kalla ta fita daga hatsari. Saura kawai ya mayar da ita gida, ta koma karkashin kulawar yaganar ta. Ya san Asiya za ta iya, don kuwa alkawari ta dauka masa. Shi ma kuma zai cika bakin na sa da ya dauka.
Da wannan ya tattara daga asibiti ya nufi sabon masaukin sa a otel na Executive Nest. Tun da daren bay a gudu, bari ya je kawai ya kasha daren a can. Ba mamaki a neme shi a asibitin cikin dare. Ya saba da hakan.
A cikin harabar ya hangi abokan sa guda biyu, suna jingine jikin motar Sadi. Matsala. Babbar matsala. Da ganin sa suka nufo shi, “Ango! Ango!!” dukan su suka furta lokaci guda.
Sun sha shadda dinkin jamfa, ta Sadi ruwan kasa, Hadi kuwa algashi. Sai kamshi suke yi da huluna a kan su, damanga. Suka tsaya suka kalli ango uban gayyar, kwat ne a jikin sa. Na tun safe ma.
Sadi ya kalle shi, “Me ye hakan? Wannan ai sai a dauka kai ba ango ba ne, sai ko angogu. Tun safe da bakaken kaya kamar mai tsaron shugaban kasa?” 4
Suka fashe da dariya. Shi ma ya yi murmushi. Tun jiya suke fama da shi, kan lallai ya dauki hutun kwanaki uku a kalla kafin ya kama aiki, amma ya yi biris. Idan bai je aikin ba, me zai yi? Tunani zai kusa halaka shi. Idan ya tona can zuciyar sa ma, har da zullimi.
STORY CONTINUES BELOW
Yusuf ya ce, “Kai ma ka san ba zan iya barin aikina ba.”
Hadi ya ce, “To ce maka a ka yi karewa zai yi? Ai gobe ma rana ce. Yanzu dai ka zo ka shirya don mu raka ka dakin amaryar ka.”
“Don me?”
Tambayar ta riga ta fice kafin ya fahimci yayi ta. Kusan kamar ya tauna harshen sa ko za su koma. Su kuwa suka fashe da dariya har da tafawa, “Ina ruwan sabon shiga, ungozomar wasai.” In ji Sadi. 1
“Mayar da wukar, ba sai ka cinye mu da kishi ba. Don dai kar mu je wajen amaryar taka ce ko, ina ce?” In ji Hadi.
Ya yi ‘yar dariya, “To in ban da abin ku, gidan cike ya ke da mutane. Sai kuma na shiga a yau?”
“Mun san da haka.” Hadi ya furta. “Amma yau ne kawai muke da lokaci, don tafiyar da zamu yi gobe Abuja. Idan mun raka ka, sai ka dawo kayi kwanciyar ka abin ka.”
“Ni ma goben zan je Abujan. Ka ga sai mu dage komai sai bayan mun dawo, tunda rana daya ne gaba daya.”
Hadi ya girgiza kan sa cikin rashin amincewa, “Kai wane irin ango ne? Maimakon ka yi zaman ka wajen amaryarka ku shagalin ku sai ka tafi ka bar ta?”
“Ko kuma ya tafi tare da ita ba.” Sadi ya furta tare da miskilin murmushi, ya na daga masa gira.
Yusuf ya kusa tuntsirewa da dariya. Da sun san sharadin matar sa da ba haka ba. Ya dai ce, “Zaman ta a nan zai fi, don Amatullah.” 3
“Kawai don tafiyar kwanaki uku? Ko a yanzun suna tare ne? Ai kawai sai ka bar ta a asibiti don a ci gaba da kulawa da ita, kai kuma ka je ka more amarcin ka.”
Hakan bai taba zuwa ma sa a tunanin sa ba. A matsayin matar sa ya san ta na da hakkoki da dama a kan sa. Zai yi kokarin sauke su. Ita ce ta gindaya sharruda a tsakanin su ba shi ba. Don haka ba zai tilasta ma ta komai ba, har sai ta amince da shi don kan ta.
“Ba zai yiwa ba.” Ya furta
“Me ya sa kai na ga alamar sanyi a tare da kai. So ka ke a baka shawarar yadda a ke yi da amarya?” Inji Hadi
Yusuf ya girgiza kan sa ba sanyi ba ne “Sirri ne tsakanin miji da mata.”
Suka bushe da dariya. Hadi ya ce, “Yaro ba ka san komai ba. Ka bar mata yadda su ke dan kuwa sai su ba ka mamaki.”
“Allah ko?”
“Allah kuwa shawara ce na ke baka, a matsayina na yaya babba a cikin aure.”
Yusuf ya yi murmushi, ya san Hadi da son nu na cewa matan sa biyu ne.
Sadi ya ce, “Kai aikin ka ke nan. Da zarar an yi magana ka ce kai ne yaya babba. Ai duk daya ne, da mai mata daya da mai biyu, duk kanwar ja ce.”
“Duk biyu dai. Da zarar matar ka tayi tafiya shi ke nan ka zama gwauro. Sai ka koma cin indomie da shan ruwan shayi.” Hadi ya mayar da martini cikin zolaya. “Mai mata daya karen motar gwauro.”
“To ai ni ban shirya raba fad aba ne. karatun likitan ya isheni, ba sai na hada da na lauya ba.” 2
“Rabiyar fada ai ban a rago bane, sai jarumi.”
Yusuf ya san Sadi zai mayar da martini, amma shi a yanzu ba wannan ba ne a gaban sa. don haka ya yi sauri ya tari numfashin su duka, “Look, na san kauna ce ta kawo ku nan, amma zan so gobe da safe mu je tare da ku. Tun da ba da sassafe zan yi ta ba. Kun ga zamu samu an watse gaba daya.”
Bayan karamar jayayya duka suka amince da wannan tsarin. Yusuf ba zai so nuna kyaliya ga matar sa ba, amaryar sa. yin hakan zai jawo ma sa fushin Ummar sa, wadda ke ganin du’a’in ta sun samu karbuwa. Don haka zai yi abubuwan da zasu faranta ma ta rai. Da wannan ya fidda wayar sa sannan ya buga wa kanwar sa Saratu.
Ya ya kika ganni?”
Asiya ta daga kan juz’i Amman da take karantawa ta kalli Muhibbat daga sama zuwa kasa, sannan kasan zuwa sama. Ta cancada kwalliya, ta saka leshi mai launin tsanwa mai ratsin ruwan gwal. Kamar kullum, dinkin ya karbeta zanzan don Allah Ya yi mata baiwar kyaun sura da diri. Kitson da tayi sun kwanta daidai kafadunta, gami da daurin dankwalin ‘maintain’ a kan su.
“Kin yi kyau, sai ka ce wata amarya.” Asiya ta furta cikin murmushi. Da gaske ne ta yi kyau. Don ta na da aji, duk da a kauye suke. Idan Muhi ta yi kwalliya ta yi dauri, ba kowane namiji ba ne ya kan tunkare ta. Sai irin wanda ya yarda da kan sa sosai.
Muhibbat ta bata fuskarta, “Ke kuma dube ki, kamar ba amarya ba.” 2
Asiya ta kalli kan ta. Duk da cewa ba ta yi kwalliyar amaren bana ba, ba za a ce ta yi rashin kyau ba. Atamfa ta saka mai dinkin loose-fitted, launin shudi a gauraye da ruwan kasa da ja. Sabon dinki ne da Umma ta aika mata a cikin wannan satin, don kasancewar ta amarya. A cewar ta, ta san lokacin yin shirye-shirye ya kure musu baki daya, don haka ta aika mata dinkuna uku kala kala. 4
“Ai baki isa ba. Ko da cewa daga kauye mu ke, ba za mu nuna karanta ba.” Muhibbat ta fice ta bar Asiya ta na murmushi.
Muhibbat kawar Maree ce, kuma a kalla ta ba wa Asiya shekara biyu a haife. Amma jinin kawancen su ya fi karfi saboda yadda Muhibbat ta fi Maree jan ta a jiki. Sau da dama, kowa kan dauka Asiya ce kawar Muhibbat, ba Maree ba. 2
Jim kadan Muhibbat ta koma dakin, tana rike da yadin material mai launin ja da ruwan gwal, sai sheki yake. Ga shi da sulbi kamar siliki. Dinkin riga da siket ne mai shef na yayi.
“Ga wannan. Tashi ki saka yanzu. Na fi son idan mijin ki ya shigo ya ga kin gwangwaje ma sa.”
Kalmar ‘miji’ ta kara sa zuciyar ta tsalle, kamar yadda ta yi a dazu bayan sun karya da soyayyen dankali da miyar hanta da koda hade ruwan shayi mai kauri.
A wancan lokacin Sara ce ta sanar mu su cewa Yusuf ya na tafe da abokan sa. Gwaggo Tambai an mayar da su Dagauda. Ta roki Muhibbat ta zauna ne don ta samu kwarin gwiwar fuskantar sa.
“Atamfar ta fi kyau Muhi.”
“Kin fara ko? Tashi ki je, don kin san ba kyale ki zan yi ba har sai kin canja.”
A dolen ta ta shiga bandaki ta canja, don ta san Muhibbat za ta tara mata jama’a idan ta cije. Ko da ta koma, ta samu tana jiranta da kayan kwalliya. Rabon ta da shafa hoda a fuskar ta har ta manta. Watakila tun zuwan ta Bauchi na farko.
Tun can da ma Maree ce mai damuwa da kwalliya. Idan ta sayi kayan kwalliyar sai ta boye ta hana ta. Wasu lokuta Asiya ta kan sayi nata, amma ko Maree ta shafe su kare da wuri, ko ma ta je ta zuba cikin salga a boye. Idan fa har Muhibbat ta dage kan sai ta yi kwalliya, Maree kan kushe ta, ta nun aba ta yi kyau ko fasali ba sam. 6
“Kin hadu fa Minde. Yanzu kika fara kama da amarya.” Muhibbat ta furta. “Zo nan ki zauna don sai na sumar da angon ki yau idan ya kalle ki.” 2
Abin ya so ya bata dariya, amma sai ta ga ba amfanin sace gwiwa wa wanda ke mafarki irin na Muhibbat. Don haka ta zauna ta ba da fuskar ta.
Wani abin ma ba ta san sunan sa ba, amma an mulka ma ta. Ta na gamawa ta ce da Asiya, “Yauwa, nan ya kammala, yanzu tashi za ki yi don na ga yadda za ki yi tafiya idan ya shigo?”
Asiya ta tura bakin ta tare da harara, “Ni yarinya ce a ka gaya miki?”
“Ke din ce ai. Na ga sai na dage a kan ki.”
Tun daren jiya ta ishe ta da ta yi wannan ta yi wancan. Kunnuwan ta sun gaji da ji. “Muhi, wani abin sirri ne, sai tsakanina da shi zan yi shi.” 4
STORY CONTINUES BELOW
Ta furta hakan ne don ta katse Muhibbat, sannan ta yi hakan ne don ta san za ta rusa shewa. Ba ta bata kunya ba, ta kuwa rangada guda, ta na cewa,”Lallai darasi ya zauna. Ko yau na koma na san za ki iya zaman dakin aure.”
Cikin dariya, Asiya ta ce, “Haka ne, Dada.”
“Oho dai. Kya ji shi, cutar ajali a yatsa. Gulma ta yi miki yawa Minde.” 2
Asiya ta wulkita idanun ta, a lokacin ne kuma suka tsinkayi sallamar Yusuf da abokan sa. Nan take zuciyar ta ta buga, ta shiga yamutsi. Bayan sun kimtsa sun yi lullubi kuwa sai suka yi mu su izinin shiga. Asiya ta rufe fuskar ta ne da gyale mai ruwan baki da shekin gwal.
Su uku suka shiga, kowannen su cikin malun-malun na shadda, kamshi kuwa ya baje ko ina. Iya abin da Asiya ta iya gani ke nan ta kasa-kasa. Daga nan ta sunkuyar da kan ta, kafafuwan ta na kan gado a nade.
“Ga amarya, ga ta hannun damar amarya.” In ji daya daga cikin su.
Muhibbat ta tsime, ta dake, ta ce, “Ga ango, ga na hannyen damar ango.”
Suka yi dariya, “Hannayen sa biyu ne a dama? A dai tsaya a dayan dai.”
Ta ce, “To ai ku biyu na gani, shi ya sa.”
“Kin yi gaskiya. Ni sunana Muhammad Sadisu. Shi kuma dayan, sunan sa Muhammad Hadi. Na tabbata kun shaida angon namu, wanda tun jiya yake ta sheki da kyalkyali na musamman saboda amarya ta shafa masa. Na kuma tabbata ya na dokin ganin amaryar sa, don haka ba za mu bata lokaci ba. A yanzu zan ba wa babban yaya Dokta Hadi damar fadar albarkacin bakin sa.”
Dokta Hadi ya ce, “A gurguje zan yi mana fatan alheri ne gaba daya- da ku ma’auratan, da mu ma, ma su kaunar ku. Aure nufi ne na Allah, ta kowane hali sai an yi shi. Idan Allah Ya kaddara aure tsakanin mutane biyu, to gari baya nisa, lokaci kuma bay a tsawo. Don haka muke fatan wannan aure ya jure dukkan hassada, munafurci da cusa ra’ayin zargi. Allah Ya albarkace shi da ‘ya’ya nagari, domin manzonmu ya umurce mu da mu yi aure don mu hayayyafa, don mu zama abin alfaharin sa ranar lahira.”
Dokta Sadi ya dora da cewa, “Ni kuma zan bukaci ku rike junan ku bisa amana, yarda da kauna. Ku tabbata duk abin da zai zame mu ku matsala ku tabbata kun zauna kun warware shi tare. Aure baya son buya a duhu. Hakan zai sa ku kara fahimtar juna. Da wannan ni ma zan yi muku fatan alheri a rayuwar duniya da na lahira.”
Zuciyar Asiya ta ci gaba da bugawa. Jawaban su kamar shirin gidan rediyo take jin su. Ita da ‘mijinta’ sun gama shirin sun a yadda tsarin zamantakewar su zai kasance. Ba lallai ne duniya ta sani ba.
“To ke kawar amarya ba ki ce komai ba. Ko ba kya farinciki ne?” In ji Sadi.
Muhibba ta dan yi murmushi, sannan ta kalli Asiya a takaice. A madadin shakiyancin da ta saba, sai ta sake shan muur, ta ce, “To ni me zan ce? Kun fadi komai ai. Sai dai na dora a kan naku, na jaddada cewa ku kara hakuri da juriya da junan ku. Sannan ku rike sirrin juna ku kuma yi kokarin fada wa junan ku abin da ku ke ciki. Sadarwa shi ne ginshikin aure.
“Ke Minde, ki kasance mai tattalin mijin ki, amanar sa da dukiyar sa. Ya riga ya danka mi ki komai, sai ki rike tsakani da Allah. Tilas ki zama mai kishin sa tare da kyautata ma sa. Ki dage kuma wajen kyautata wa mahaifiyar sa, domin kamar yadda aljannar ki ke karkashin kafar sa, shi kuma ta sa ta na kafar mahaifiyar sa. Tilas ki taimake shi wajen yi mata biyayya har lokacin da Allah Ya kaddari zaman ku tare. Allah Ya sa yadda muka hadu a wannan hidimar, ku kara tara mu nan da shekara daya.” 5
STORY CONTINUES BELOW
Bayan sun dan dara sun kuma ce Amin, sai Dokta Hadi ya kalli Muhibbat,
“Shi ne ki ka ce ba kya da abin cewa, bayan kin fi mu yin sharhi mai muhimmanci?”
Dokta Sadi ya ce, “Ai ni ma shin a gani. Mun ci sa’ar samun babbar malama ce ashe ta hannun damar amaryar.”
“Kayya, ni din fa daliba ce. Ga malama nan kusa da ni?”
“Amaryar?” Hadi ya tambaya cikin mamaki.
“Kwarai kuwa, ko shakka babu.”
Sadi ya ce, “Ki ce abokin mu ya taki sa’a, kamar yadda ke ma mijin naki yayi sa’a.”
Muhibbat ta wulkita idanu, “Eh to, zai takan dai. Ni din dai da saura kadan.”
Hadi ya ce, “To, Allah Ya tabbatar da alherinSa.”
Duka suka furta, “Amin.”
Sadi ya ce, “To ke amarya ba ki ce komai ba. Ko sai an sayi bakin naki ne tukunna? Dan Amin din nan ba za ki ce ba?”
Asiya ba ta dago ba balle ta ce uffan ko ma taga yanayin su. Dukan su biyu ta hadu da su a asibiti a lokacin zirga-zirgan Amatullah.
Amatullah. Shin ina ta ke ne? Me ya sa har yanzu ba a kawo mata ita ba? Ta na bukatar ganin ta, ko za ta samu natsuwa. Abubuwa sun fara cakume kan ta. 5
“To tun da haka ne abin, bari mu saya, don zamu so a ce Amin idan mun sake addu’a. Kin san fayau kamar jaririya ki ke.”
Jaririya. Amatullah. Ina ta ke ne? Ta ji sun ajiye mata abu a gefen ta. Kudi ne dami biyu. Ko ba ta san nawa ba ne, ta ji Muhibbat na cewa, “Lallai fa, da gaske ku ke yi. To za ta yi muku amin, idan Ango ya bude baki yayi magana.”
Sai a lokacin ne Asiya ta dan daga kanta ta kalle su ta cikin gyalen. Yusuf ya na zaune a tsakiyar su cikin farar malun-malun, su kuma sauran na su ruwan kasa ne daya, dayan kuma shudi.
A takaice ta kalle shi, amma yayi kyau matuka. Ita kuma yake kallo, kafin ya kalli abokansa, “Mun ji abubuwan da kuka ce, in Allah Ya yarda za mu dauka. Mun gode, Allah Ya saka mu ku da alherinSa.”
“Amin.” Suka furta. Hadi ya dora da, “Amarya, baki ce Amin ba.”
Murya kasa-kasa, Asiya tace, “Amin.”
Yusuf ya kalli abokan sa, “Mu tafi ko?”
“Au kora da hali a ke mana? To, mun gane abin. Da ma sirri ne.”
Da wannan suka fice cikin barkwanci da tsokana, bayan Dokta Sadi ya ajiye wani damin kudi na ‘yan dari biyu, “Wannan na sallamar kawar amarya ce.” 2
Ta yi godiya,bayan sun fita, Muhibbat ta ce da Asiya “Yarinya, karenki ya kama zaki. Ki kama shi da ga-gam, Allah Ya kasha Ya baki.” 1
Asiya ta nisa. Ta rasa me za ta dauka. Cewar sayen bakin ta akayi, ko kudin bautar da za ta shiga yi ne nan ba da jimawa ba. Ta ce da Muhibbat, “Ki dauki kudin nan ki kai wa Dada Muhi, babu abin da zan yi da su.”
Da gaske ne babu amfanin da za su yi mata. Mahaifiyar ta ta fi bukatar su. Muhibbat ta ce, “Ga shawara zan baki, idan yayi to, in kuma bai miki ba ki watsar. Na san kina son kyautata wa Dada. Amma ki ajiye guda daya a wajen ki, gudun kar a kwace ma ta…kin gane ai ko?”
Asiya ta gyada kan ta alamar ta fahimta. “Ki kai mata kawai ba damuwa. Ki ba ta daya, Baba kuma daya. Na san idan na aika dayan ma zai lallabe ta ne ya karbe da wayo.”
Wa take yaudara ne? Ta san cewa duka zai kwace har da na Dadar. Ita din neman kan su take yi, kamar dai cin hanci ne, musammam bangaren mahaifin ta. Ta tabbata idan ya ga kudin zai sa ya fara samun natsuwa da auren da ta yi, duk da cewa ba a son ran sa a ka daura mata aure da Dokta Yusuf ba.
STORY CONTINUES BELOW
Fatan ta dai, Yusuf kar ya zama Mudassir na biyu, hakan ma ta san fatan iyayen ta.
* * *
Tsayuwar motar da Sara ta saba shiga da fita da ita gidan su ne ya sa Asiya barin dakin ta ta sauko kasa zuwa falo. Sanye take cikin doguwar rigar abaya, bayan ta saka riga da siket na turawa ta ciki. Ba kwalliya sosai a fuskar ta, daga hoda, gazal da man baki.
Ta rungumo Amatullah, wadda ta sha kwalliya cikin riga fara da fulawa launin ruwan hoda. Kan ta an sakala ma ta ribom din kayan, kafafuwan ta da takalman irin mai hade da safa. Sai kamshi ta ke yi, ta kuma sha kyau.
Bayan kwanaki biyu da auren su a ka mayar mata da Amatullah, da akwatuna biyu, daya babba dayan karami, cike tab da kayan sakawar ta. Sara ce ta kai ta wajen ta bisa umarnin likitan. Tun daga wannan lokaci ba ta yarda ta bar idanun ta. Ta yi kewar ta matuka, har ta na ganin kamar za ta bace mata idan ta kawar da kanta daga fuskar ta.
“Na zo mi ki ne da telolinmu don ki zabi dinkunan da za su miki. Mun zo da albom din na su, in ya so ki duba.” Sara ta furta, bayan ta sa an kai mu su ruwan sha da jus.
Tun bayan auren ta Sara ke nuna mata kauna, har sun fara sabawa. Sauran dangin likita kam, babu wanda ya leko, ko ya damu da ziyartar Ama. Ba ta taba ganin kowa ba in ban da ita din. Har ta shiga zargin, anya, ya na da su din ma kuwa?
Asiya ta shiga duba babban albom din na su, wanda ke kunshe da hotunan dinkuna iri da kala bayan ta dan jinkiri. A ranar satin ta uku ke nan a gidan Dokta Yusuf a matsayin matar sa. ya kamata ta mayar da hankalin ta wajen rayuwar auren ta.
Hakan ya kusa ba ta dariya. Ba bu komai a cikin sa illa kula da Amatullah da kuma Umma. Rabon da ta ga Dokta tun ranar sayen baki. A wancan ranar ya tafi Abuja ne na tsawon uku sannan ya dawo. Ta kan ga gilmawar sa, ko motsin sa. Hakan ya fara so ya dame ta.
Bai rage ta da komai ba, ta bangaren alkawarukan da ya dauka mata. Komai take so, wanda ta furta da wanda ta yi shiru duk ya na bata. Hakan ya saka ta jin tsarguwar anya, ta na kyautawa kuwa? Duk da cewar ta san it ace ta yi zabin hakan gare su, ai bai dace a ce ko gaisawa ba sa yi ba.
Duk wayewar gari Larai za ta kai Amatullah dakin Umma, shi kuma a can zai je ya tarar da ita, ya dauke ta ya duba ta. A hakan ma kwana uku ke nan bai gan ta din ba, domin Umma ta yi tafiya umrah, kan cewa za ta je godiya wa Allah, wanda Ya nuna mata auren dan ta, ta kuma roka mu su zaman lafiya.
Ta yi zaben ta na dunkunan shaddodi, atamfofi da materials, Sara ta taya ta zaben wadan da za a dinka da dama, wajen akwati guda tab. Sannan suka yi tafiyar su. Kudin dinki za a yi jimillan sa wa likita ya biya ko da nawa ne.
Nan ma ta kara jin tsarguwa. Duk da cewar auren su a suna yake, bai hana shi kasancewa aure ba. Abin nufi a nan shine, aure, aure ne, na wucin-gadi ko dindindin. Kuma duk abin da ta yin a lada ko zunubi a na rubuta mata. To me zai hana ta nemi ladan muddin tana nan? Balle ma, hada shimfida ca kawai ta ki yarda, amma komai za ta iya yi bayan nan. 4
Sun dan yi hira da Sara kafin ta koma na ta gidan abin ta. Ita ma a bara ta yi aure, amma Allah bai ba ta haihuwa ba tukunna. Daga nan ta kwantar da Amatullah, ta nufi kicin din gidan wajen Larai saboda gaskiya kadaici ya fara damunta cikin wannan makeken gida.
Ta kai kwanaki uku a haka, kullum sai ta yini wajen ta. Ta lura da yadda take sarrafa gidan, da irin abincin da take dafawa, da kuma lokutan da Dokta ke dawowa da ma abubuwan da yak an bukata bayan dawowar ta sa.
A rana ta hudun ne ta yanke shawarar shiga kicin ta dafa ma sa abincin da yake so. Don yin hakan, ta nemi taimakon Sara, wacce ta shaida ma ta cewar yayan ta yana matukar son dambun zogale. Zai iya cin sa kullum ba tare da ya hau kan sa ba.
STORY CONTINUES BELOW
“A kan ma sa na couscous ne, amma fa idan ya samu na shinkafa, ba dama ne Anty.”
Asiya ta murmushi. Duk da dai ba dadi kamar hakan suke samu a gida ba, ta taba hada dambun mai shinkafa a gidan su Muhibbat, da kuma gidan Sirajo mai wanki, da matar sa Kubura ta haihu.
“Kyaunta idan ki ka shirya, ki hada wa Yaya da ruwan matsattsen lemon zaki a gefe mai sanyi da fefen kaza.”
Asiya ta nisa. Ta fara jin fargaba. Anya, za ta iya kuwa? A hankali dai Sara ta rika mata bayanin yadda za ta hada, da tsara har ta yi. Duk da haka dai, sai gani take ba zai so ba watakila ba zai ji yadda ya saba jin sa ba.
“Kar ki damu.” Sara ta furta a karshen wayar ta su. “Yaya ba zai san lokacin da zai sude kwano ba. Kin san ba kullum yake samun cin abin da ya ke so ba. Daga shinkafa sai taliyar Larai.”
Asiya ta dan yi dariya. Gaskiya ne, kullum a tukunyar Larai babu komai sai shinkafa ko taliya dafaffiya da miya. Sai watarana idan ta canja su ga doya ko soyayyen dankali. Ita ma kan ta abin ya fara fita kan ta. 3
“Bayan wannan kuma zan gwada miki yadda a ke hada burabusko. Shine abin da Yaya ke so na biyu.”
“Burabusko?” Ta tambaya cikin mamaki. Ta saba yin buskin gero musamman, da miyar yakuwa. Amma ba ta yi tsammanin Dokta ya ma san shi balle a ce yana so.
“Kwarai kuwa. Ai kin san mahaifinmu asalin sa babarbare ne. Kakan sa ne ya zo ya zauna a Bauchi har ya haifi mahaifin sa, shi kuma ya haifi Baban namu. Don haka baa bar gargajiya ba har yau a gidan.”
Asiya ta ji ta na matukar son ta je gidan ta ga sauran ‘yan uwan sa. Amma ba ta yi maganar ba don ita ma Sara bata taba kamanta yi mat aba. Da farko, abin bai dame ta ba, amma yanzu sai ta fara son hakan. Ko ba komai, ‘yan uwan Amatullah ne, ya dace su karbe ta a cikin su kamar yadda kowacce diya ta cancanta. Sai dai ba huruminta bane. Dokta da Umma ne za su yanke hukuncin hakan.
“Hmm bari dai na gama da wannan kafin na dauki darasin gaban. Allah ma Ya sa na yi adalci wa wannan din.” Ta furta tare da zullumi.
“Kar ki ji komai Antina, na san yau Yaya zai ci beta. Ni kuma gobe ina nan tafe na karbi tukwicina.”
Asiya ta yi dariya, “Allah Ya kai mu. Kin ga idan rankwashina yayi, ke ma ki zo ki karbi naki.”
Sara ta fashe da dariya, “In dai rankwashin a cikin soyayya ne, ba matsala.”
Daga nan suka yi sallama da juna. A ka bar Asiya cikin kadaicinta na farko. Amatullah ta yi barci, ita kuma babu abin yi. Don haka ta bude Jakarta ta fidda ledar da ta zuba takardun ta na islamiyya, ta fitar da su tana bitar su daya bayan daya. A gaskiya, kadaici bai yi ba a rayuwa. Amma ba za ta yi korafi ba, don kuwa ita ta zabi hakan.
* * *
Dokta Yusuf ya dawo gidan sa a gajiye. Kamar kullum, ya kan cika wa kan sa ayyuka ne don ya nutse cikin hakan. A ranar ya fi kullum aiki don haka gajiyar ta ninka. Ya shaida cewa ba zai iya fita call ba, sai ko a nemi Dokta Rufa’i idan a na bukatar likita. Idan na gaggawa ne kuma a nemi Sadi.
Kamar yadda ya saba bayan ya koma gidan sa, ya fesa wanka da ruwan zafi na shawa. Bayan ya canja kaya zuwa soci da wando, sai ya zauna kan teburin cin abincin sa. Tun bai gama zama ba kamshin abincin ya rika tsokanar hancin sa har ya fara sa yawu ya tsinke ma sa.
Ai kuwa ya na budewa ya shaki kamshin abin da yake matukar so, idanuwan sa suka yi lale da abin da ya bashi sha’awa, kwakwalwar sa ta amince, harshen sa ya karba. Ba tare da bata lokaci ba, ya zuba a filet ya kai loma daya cikin bakin sa. Sai da ya lumshe idanu don dadi. Ba zai iya kwatanta yadda ya ji ba, ya kuma san wacce ta yi ma sa wannan hidima, don haka ya fidda wayarsa, ya latsa lambarta.
Bayan ta amsa ne ya ce, “Yau kuma kin tuna da dan uwanki ne haka, kika burge ni haka da dambu?” Ya sake kai cokali guda cikin bakin sa.
Sara ta dan yi dariya, “Ya yi ma ka dadi ne Yaya?”
“Ke ma kin san yadda nake so ai. Kuma komai ya ji daidai, dandanon yadda na ke so.”
Ta ce, “To ya kamata ka fada wa Antina Asiya ne, don ita ta yi maka, ba ni ba.”
Ya ajiye cokalin sa, ya tsayar da hankalin sa, “Really?”
“Kwarai kuwa Yaya. Ita ta y ma komai. Yaya ka ji jus din lemon?”
Ya kurba a lokacin, “Good. Yayi dadi shi ma.”
Sara ta yi dariya, “To a ci a hankali dai Yaya, ban da hadama don girkin Anti amarya ce.”
Ya girgiza kansa, tare da ajiye wayar. Anti amarya. A hakika, bai saka wa kan sa cewar ya na da amarya ba. Ya san dai Amatullah ta na samun kulawa ta musamman, sannan ya na bakin kokarin san a rike su gaba daya. Bayan nan, sai aikin sa kawai kamar kullum. Babu abin da ya canja a rayuwar sa.
Cikinsa ya fara rurin tunasar da shi yunwar da ya ke ji. Ya shiga cin dambun sa a natse, ya na nazarin dalilin wannan karimci na matar sa. Matar sa! Sai ka ce a mafarki, wai ashe ya na da mata. 2
Sai da ya ci iya isar sa, sannan ya mike zuwa ga dakin ta. Ya san dai wajen zai same ta kai tsaye tun da ko yaushe a nan take makale da Amatullah. Zai iya rantsewa guje ma sa take yi. Shi yasa shi din ma ya kauce a hanyar ta ta.
Bayan ya buga kofar, sai yayi sallama. Abin ya zama bambarakwai. Shi da gidan sa, dakin matar sa, amma sai ya jira izinin shiga. Bayan tsayuwar sa kadan, ya tabbatar wa kan sa cewar ba ta ji sallamar ba ne.
Ya shiga shawarar yin wata sallamar ce kawai ko ya hakura sai sun sake haduwa nan gaba, ya ga ta bude kofar.
Mamaki ya bayyana a fuskar ta, kallon sa ta ke yi kamar ya dirko ne daga sama. A hankali ya lura ta dan sunkuyar da kan ta cikin ladabi, ta gaishe shi, “Ina yini?”
Wannan ba shi ne karo na farkon ganin ta ba. Amma wannan ne karon farko da ya tsaya dab da ita ba cikin tashin hankali ko damuwa ba. Hakan ya ba shi damar nazarin fuskar ta.
Fuskar ta madaidaiciya ce, mai dauke da hanci siriri madaidaici shi ma, da idanu farare fat. Labbanta ma su kyaun tsari. A hankali ya lashe na sa labban ba tare da sanin dalili ba. Ya dai san wani abu ya dan tsima shi. 5
“Lafiya. Ya ya Amatullah?” ya shiga zargin kan sa na kaiwa tsawon kwanaki uku ba tare da saka ta a ido ba. Ko don ya amince da wacce ke renon ta ne? Ko kuma yana taya ta guje ma sa ne?
Nan take wannan fargabar ta sake bayyana a fuskar ta, “Amatullah? Ta nan nan lafiya.
Babu shakka wani abu ya hango cikin kwayar idanun ta…kyawawan idanun ta, shin ta dauka ko yana zargin ba ta kulawa da Ama ne? Ya ce, “Good, ya yi kyau. Da ma ban zauna ba ne a ‘yan kwanakin nan don jin lafiyar ta. Ko da yake, na san idan da wani abin ma za ki sanar da ni.”
Abu ne mai muhimmanci, ya nuna ma ta ya yarda da ita da kuma rikon da ta ke wa Ama. Tun da ita din ma ta na da alaka ta jinni da mahaifiyar ta.
Ya kuwa lura cewar idanun ta sun yi sassauci,amma wannan damuwar, damuwar cewar watakila bat aba wa jariryar kulawa yana nan cikin idanun ta. Ba ta ce komai ba, kallon sa ta ci gaba da yi.
Bai san dalili da ya sa idanun na sa suka gagara barin nata ba. Ta na tsaye cikin rauni. Ya tabbata akwai abin da ke kwayar idanun ta, wanda ke tsima shi.
“Amm, na ga abinci. Ya yi dadi sosai.”
Ta dan yi murmushi mai cike da taraddadi. Bai taba ganin murmushin ta ba. Hakoranta farare fat suka bayyana. “Na yi ta jin tsoron ko ba zai yi dadi ba. Ban taba yin irin sa ba ne ya sa. Shi ne na nemi taimakon Sara ta koya min.”
Ya saki murmushi shi ma. Sai da ya san akwai hannun Sara a ciki tun farko dama. Ya ce, “Ya yi dadi sosai, har ma ya fi wanda Saran ta saba yi min. hakika, ke gwana ce.”
Ta sunkuyar da kan ta cikin jin kunya, ta ce, “A’a, ni ‘yar koyo ce.”
“Ai kin fi malamar ta ki iyawa.”
Ta sake kallon sa, sannan ta sunkuyar da kan nata. Wannan abin da ke kwayar idanun nan na ta ya kara tsima shi. Tun kafin ya aikata abin da za su yi nadamar sa nan gaba, sai ya yanke shawarar barin wajen. Har ya juya, sai ya tsaya ya kalle ta sosai.
“Asiya, nan gaba idan kin yi abincin, zan so ki rika kai min tebur da kan ki, ba sai Larai ta yi ba.” 8
Da wannan ya jiya yayi tafiyar sa.Asiya ta zuba wa bayan sa idanu har ya bace. Ta rufe kofar dakin ta sannan ta jingina da jiki, ta dafe kirjin nata da hannun ta. A lokacin zuciyar ta ta kumbura cikin kirjinta ta yi mata nauyi, sannan ta shiga bugu da sauri. ‘Asiya’ fa ya ce….karo na farko ke nan da ya kira sunan ta.
Tun bayan auren su, bai taba yi ma ta magana tsawo ba kamar na wannan lokacin. Har ma ya kira sunan ta. Ba wai hakan ne ya mata dadi ba, yadda ya ambata ne ya ruda ta. Sannan kuma ya bukaci nan gaba ta kai ma sa abinci da kan ta. Nan gaba….ta shiga jin dadi saboda ya yabi girkin ta, sannan ya bukaci ta ci gaba da yi, kamar dai matar sa. 3
Nan ne kuma ta dakatar da zuciyar ta, ta lalumo zahiri kan ta ya bar shawagi cikin sararin samaniya. Ita matar sa ce, amma ta wucin-gadi. Ya aure ta ne don ta kula ma sa da Amatullah.
Me ya same ta ne? Dan abin da ya faru ne zai sa ta shiga wannan hali? Girki ta yi ma sa, irin wanda ran sa ke so. Idan bai nuna farin cikin sa ba, me zai yi?
Ai ba wani abu ba ne, kawai ya yi kokarin nuna jin dadin sa ne game da wahalar da ta dauka na yi ma sa abincin. Kamar yadda take zaton shi ma yake nuna mata jin dadi game da kula ma sa da Amatullah da take yi.
Ta yi sauri ta matse zuciyar ta, lokacin da ta tuna da yadda ya kalle ta kafin ya bar kofar dakin na ta.
Ta sake matse idanun ta a kokarin ta na cire yadda shigar sa ta yi ma sa kyau matuka. Yadda rigar sa ta bayyana faffadar kafadun sa da cikar hallitar sa, da yadda gashin bakin sa da ya fito ya bayyana tsarin fuskar sa, zuwa ga yadda gashin kan say a ke taje fes….. 13
Kai! Ta bude idanun ta cikin sauri. Da gaske ne, ta na bukatar a duba kanta. Ta yaya ma a ka soma hakan? A ce wai duk ta lura da wannan a dan tsayuwar da yayi ba da dadewar nan ba? 2
A’a ba zai yiwu ba, tilas ta canja akala. Yadda shi bai saka rauni a zuciyar sa ba, ita ma ya dace ta fitar da wannan shirmen daga kan ta. Idan bah aka ba, to za ta iya fadawa wata masifar ta daban. Babbar masifa!
Da wannan kudiri ta jera tsawon ta na ma sa girke-girke kala kala. Tun ta na neman taimakon Sara har ta gwanance a kai. Sara ta mallaka mata littafan kirke-kirke irin na gida da na waje, har da My Kitchen Essentials na Azizah Idris Gombe. Tun daga lokacin ta ji Azizah ta fara burge ta don tsantsenin ta da basira. 30
A kullum Dokta zai ci abincin ta. Ko da rana ko dare, a duk lokacin da ya samu damar hakan. Sai dai bayan gaisuwa ba ya tambayar ta komai bayan lafiyar Amatullah.
“Gobe idan Allah Ya kai mu za ki kai Amatullah asibiti don allurar riga-kafin sati shida.”
Asiya ta daga kai daga zuba ma sa ruwan sanyin da take yi cikin kofi bayan ta jera masa abincin sa. burabusko ne da miyar danyen kifi.
A kwana a tashi ba wuya. Wai har sun yi arba’in. Ikon Allah!
“Allah Ya kai mu.” Kawai ta ce da shi.
Har ta juya za ta tafi ta ji furta, “Zauna mana.”
Ta kalle shi sosai, “Na’am?”
Ya dan kalle ta, “Please, ki zauna, akwai wata muhimmiyar maganar da na ke son mu yi.”
Ta zauna a hankali tare da hadiye yawu da kyar. Zuciyar ta bugu take yi ta na tsalle. So ta ke ya yi yagama fadin abin da yayi niyya tun kafin ta suma. Duk da cewar tana kokarin kauce ma sa, ta kan sa ran ganin sa kullum tare da ba shi abinci. Ta tsinci kan ta a cikin jiran lokacin da za ta ga ya saka lomar farko cikin bakin sa, da yadda zai nuna godiyar sa ko da ta kwayar idanu ne.
“Abokanai na kuma aminai na, Hadi da Sadi, sannan kuma abokin aikina Dokta Kabir suna son su gabatar da matan su don ku gana sosai. Kamar dai ziyarar suna su ke nufi. Sannan hakan zai sa Sadi ya kyale ni na huta.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta dan yi murmushi, alhali ji take yi zuciyar ta na kara yamutsi. Magana yak e ma ta kamar ita ainihin matar sa ce. Ta ce da shi, “Ka na ganin hakan babu matsala? Ina nufin, auren mu ba mai dorewa ba ne, gabatar da ni ba zai kawo matsala ba?”
Idan har ya ji ta, to bai kula ba, “Kin san cewa a da sun tsara kan mu hadu a Vanilla ne, sai nace a’a, Amatullah bai dace ta fara yin yawo ba, musamman bayan ciwon ta. Shine su ka bani damar na zabi wurin da naga ya dace. A halin yanzu, na bar miki zabin.”
Kallon ta yake yi kirr, idanun sa suna shigarta suna narka ta kamar kitse cikin wuta, a lokaci guda kuma sun a tsorata ta. Ba ta san yadda za ta fara haduwa da matan abokan sa ba, balle ta san yadda zata tarbe su. 6
“Ba dai tsoro kike ji ba.” Fuskar sa da alamar ‘yar murmushi. Hakan ya sa zuciyarta zogi mai dadi. 2
Ta cije cikin karfin hali, “Tsoron me zan ji…”
Ya katse ta da cewa, “Good. Don kuwa idan har zaki iya barin garinku, ki zo nan Bauchi ki fuskance ni, to ina ga babu abin da zai baki tsoro.” 2
Ta kalle shi sosai. Da gaske ya ke yi. Sai dai ba ta san ko yabon ta yake yi ba, ko kalubalantar ta. “Ko kadan ba na tsoro. Yaushe ne zasu zo?”
Ya saki murmushi sosai, sannan ya koma ga cin abincin sa, “So kike su zo nan?”
Ta gyada kanta a kokarin ta na matse zuciyar ta, ba wai don ba da amsa ga tambayar sa ba. “Zan so mu hadu a wajen da Amatullah za ta fi sakewa sosai. A hakan ma za ta samu damar yin abota da ‘ya’yan su.”
Ya sake kallon ta, “Kwarai, haka ne. Ki na ganin ranar asabar zata yi?”
Asabar. Nan da kwanaki hudu ke nan. Lokacin da take bukata ke nan don ta shirya tarbar su. Don haka ta ce, “Allah Ya kai mu.”
“Amin. Amma fa za su zo bataliya guda; gari ne har da kasuwa.”
Ita ma ta saki murmushi, “Har na ji kosawar zuwan asabar din. Allah Ya kawo su lafiya.”
Bai amsa ba a lokacin, don kuwa ya bar cin abincin say a kura mata idanu. Me ye wai? Ta fadi wani abin da ba daidai bane? Ya kawar da kan sa, ya kara barin ta cikin zullumin amsar tambayar ta duk da cewar ba ta furta ba.
Larai ta leko dauke da Amatullah, wacce ke rusa kuka, “Hajiya maman Ama, ga ta nan ta tashi tana kuka.”
Wuuf ta mike cikin sauri sannan ta karbe ta, ta shiga rarrashin ta a hankali, tana mata kalamai ma su nuna kulawa da neman natsuwa. Nan take Ama ta yi shiru kamar wacce ke iya fahimtar su. Ya ji da a ce shine mana a hannun nata, ta na masa abin da take yi wa Ama. Ta rika yi ma sa rada cikin kunnuwan sa, tana saukar ma sa kalamai ma su narka zuciya. 12
Ya Salam!!! Ta ina wannan tunanin ya fado kuma? Me zata dauke shi idan ta san tunani yake a kanta, tunanin yadda miji ke yi game da matar sa? Wai me yasa ya kasance mai yawan tunanin Asiya alhali akwai Abida a cikin zuciyar sa? Ya danganta hakan ne bisa dalilin cewar Abida ta dade da barin sa. Ita kuma Asiya take tare da shi, take kula da abincin sa da Amatullah. 2
Makaryaci! Ya ji wani bangaren zuciyar sa ya zarge shi. Idan hakan ne, me yasa Larai ba ta dauki wannan muhimmancin ba a zuciyar sa tuntuni? Me yasa tun a da babu wacce ta taba kaiwa wannan matsayin? 7
A lokacin ta dago kan ta daga jikin Amatullah ta kalle shi, idanun su suka kulle da na juna. Nan take ya ji abin da bait aba tunanin zai ji ba. Akwai dai wani abu, wanda ba ya kaunar tonawa.
Ba tare da wata-wata ba, ya mike tsaye, “Tun da mun gama tsayar da magana, bari na koma ofis don na sanar mu su.”
Bai jira amsar ta ba, ya suri makullin motar sa kawai ya fice abin sa. Ya yi hakan ne don ya na bukatar shan iska, ya kuma kakkabe duk wani abin da ya jibanci Asiya a lokacin.
STORY CONTINUES BELOW
Dole ya seta kan sa da ma tunanin sa, ko don a samu zaman lafiya. Shi ya dauki alkawari gare ta, na cewa babu abin da zai shiga tsakanin su. Don haka ba zai ma fara daukar hanyar da za ta dauke shi ga hakan ba a karshe.
Asiya ta gagara ce masa komai, sai kawai bin sa ta yi da idanu har ya fice. A ranar bai ci rabin abincin kamar yadda ya saba ba, ya bar ta da tunanin ko laifi ta yi ne?
Lallai, yanzu ta kara tabbatar da cewar akwai abin da ta furta ma sa, wanda bai dace ba kuma bai ji dadin sa ba. yinin ranar ta rika wasa kwakwalwar ta don fahimtar ko mene ne? sannan kuma ta yaya za ta fara ba shi hakuri game da hakan?
* * *
Asiya ta kalli kan ta fiye da kirgawar ta a madubin da ke dakin ta. Awa uku ke nan da ta kamala girke-girken bakin ta, sannan ta bade kamshin oudh a ko ina. Awa guda da ta fito daga wanka, amma ta gagara zaben kayan da zata saka.
Da farko dai atamfa ta daura na superwax mai launin kore da ruwan kasa da ratsin ja. Ta cire don dinkin ya fidda surar ta sosai. Ta koma kan shadda mai ruwan zuma, dikin doguwar riga, ya sha aikin zare daga wuyan har kasa.
Nan ma ta cire gudun kar a ga zumudin ta, kar a ga kwalliyar tayi yawa wa ziyarar abokan Yusuf kawai da iyalin su. Ta koma kan leshi mai kyaun ado na swiss, launin kore da ruwan gwal. Tsarin dinkin ya fidda kyaun dirin ta da na fuskar ta.
Ta fidda iska ta bakin ta. A lokacin da take gidan su da bata da yawan kaya irin wadanan, ba ta samun matsala wajen zaben kayan saka wa. Amma yanzu ta gagara tsayar da hankalin ta kan abu daya. Ko dai ta kira Muhibbat ne?
Ta nisa. Ba sai ta yi hakan ba. za ta zabi kayan ta da kan ta, wand aba zai fidda surar ta ba, kuma sannan zai burge sosai. Don haa dai ta kare da zaben shaddar, amma launin shunayya (purple) amma wanda bai shiga sosai ba.
Aikin na sa ba mai yawa ba ne, sannan dinkin riga da zani ne. sumar kan ta kuwa ta daure shi ne da ribom, amma duk da hakan sai ta ya nuna alamar cikar sa. Ga shi baki yana silbi. Sara ce ta kai ta wajen gyaran gashi a jiya da kyar, saboda gudun rabuwa da Amatullah. A can an gyara mata faratun ta na hannu da kafafu, amma ba ta yarda an mata lalle ba. kar Amatullah ta tashi ita kuma ta yi nisa. 2
Ta daura dankwalin shaddar sau biyu kafin na ukun ya zauna da kyau. Ta rufe gashin kanta sosai, ta yadda babu wanda zai gani a waje. Ta sake kallon kan ta a madubi, sannan Amatullah.
“Yaya kika ganni, Ama??”
Ta koma jikin gadon Amatullahin da ke girke cikin dakinta, tana kallon rufaffun idanun na ta cikin barcin da take yi tun bayan da tayi mata wanka. Ta san ba iya jin ta take yi ba, amma dai hakan zai taimaka wajen rage taraddain da ta ke ciki.
Amatullah ta sha kwalliya cikin dofuwar riga ‘yar kanti fari sol mai jikin kamar leshi. Kafar ta takalman yara da safa farare sol masu adon duwatsu. Kan ta da ribom din da ya zo da kayan, ta Makala mata kan gashin kan da bai wuce ta damke shi da hannun ta day aba. Kamshin ta kuwa ba mai tashi bane, ba kuma wanda zai iya saka mata mura ba.
Ta yi murmushi a lokacin da ta ga girar da ta dan zana mata a goshin ta kadan. Hakan ya kara fidda tsari da kyaun fuskar ta sosai. “Kin hadu sosai my dear.”
Amatullah ta dan yi motsi har ma ta dan yi dariyar kuda. Ta ji zuciyar ta ta matse, irin kamar yadda mahaifiya ke ji na cewa diyar ta na girma. Kamar ta kwala kira wa Yusuf kan ya zo ya gani; akwai lokuta da dama da ta kan so ta kira shi don ya ga yadda Amatullah ke kara wayo. Amma sai ta daure zuciyar ta. Ita kadai ta kan ci ta cinye kawai.
“Babanki idan ya ganki zai ji dadi sosai. Kin san fa beauty queen yak e kiran ki.”
Asiya ta nisa. A tun wancan ranar da suka yi maganar tarbar baki, bai sake yarda sun hadu ba. ko ta ajiye ma sa abincin, to har ya shiga ya ci ba ta sani.
Abincin rana ya kan aiki Bature direba ne ya kai ma sa asibiti. Na dare kuma sai bayan ta kwanta yak e shiga. Ta san yanayin aikin sa ne, babu yadda baya kamawa. Ba kuma zata zarge shi kan komai ba, don bai rage ta ko Amatullah da komai ba. hakan ya bata tabbacin cewa ko bayan rabuwar su, zai ci gaba da kula da ita.
Ta ji wani irin suka marar misaltuwa cikin kahon zuciyar ta. Me yasa ne Dokta Yusuf ya kasance kyakkyawa kuma mai kyaun halaye da dabi’u? da a ce akasin hakan yake, da za ta fi samun saukin mu’amala da shi har zuwa ranar tafiyar ta.
Amma a halin yanzu, rabuwar su zata bata wahala, har tsoron zuwan ranar ta ke ji. Sai dai wa za ta yaudara? Wannan rana tilas za ta zo komai dadewa.
Da wannan ta fita zuwa falo, bayan ta saka Ama cikin dan karamin gadon da ake daukar ta a ciki. Za ta ajiye ta ne a gefe don bakin na su su samu ganin ta da kyau. Ta yi kicibis da Likita bokan turai a daidai lokacin da shi ma ya ke shiga falon.
Ba wai sun kara ba ne, amma tasirin girgizan kasa ne ya kusa tumbuke ta daga wajen da ta ke tsaye ta na kallon sa. Ta sha ganin sa cikin kananan kaya, amma a duk lokacin da ta gan shi cikin jamfa, ma sha Allah, Tabarakallah! Ba kullum a ke karo da kyaun halitta irin sa ba.
Ya nufo wurin da take, shi ma ita yake kallo ko kawar da ido baya yi. Dole zuciyar ta ta kusa toshe mata numfashi, ta koma yin sa da kyar. Ga wasu darurrukan tsuntsayen da suka bazama a cikinta suna shawagi. 1
Ya tsaya a gabanta, ta sunkuyar da kai don kunyar da ta ratsa zuciyar ta. Ta shiga rudani, gas hi ya kura mata idanu ba tare da y ace komai ba. dole ta fincike kan ta daga wannan yanayi, tun ba ta makara ba.
“Amatullah ta zo nuna maka kwalliyar ta ne.” muryar ta tana rawa, zuciyar ta ta na narkewa.
“Oh haka ne?” Ta ji ya furta a hankali.
Ta dan daga kanta ta kalle shi. Ba Amatullah yak e kallo ba, har a lokacin bai bar kallon nata ba. sai dai a lokacin da wani yanayi daban. Ya ce, “Jira ni, minti daya.” 1
Ya shige dakin sa, wanda ya kasance kusa da na ta. Tsawon zaman su a kusa da juna, sun zauna ne kamar makwabta, ba ma’aurata ba. bai jima bay a dawo da wani ma’aji mai sheki launin jay a mika mata.
“Bude.” Ya umurce ta.
Ko da ta bude, ta yi idanu hudu da Sarkar da ba ta taba ganin mai kyau da sheki irin sa ba. ta kale shi, fuskar sa cike da murmushi. Ta tambaye shi, “Wannan fa?”
“Na saye ta lokacin da na je Abuja ne kwanaki. Ban baki ba ne gudun kar ki dauka da wata manufa. Ki dauka tsarabar ki ce,”
Ta rufe tare da mika ma sa, “A gaskiya ba zan iya karba ba. Wandan da ka saka su a lefe ma ban gama bude su ba.”
“Na sani. Amma ba na kyauta na karba daga baya. Balle ma ba ke kika roke ni ba, ra’ayin kaina ne ya san a saya miki. Idan baki saka ba, sai ko na saka a wuyana. Kin ga kuwa hakan ba zai yi kyau ba ai ko?
Ta dan so ta yi murmushi. Ya ci gaba da cewa, “Wai tsaya, min ti daya. Ba dai kina tunanin yadda Sarkar za ta yi min a wuya bane dai ko?”
Ta dan yi dariyar kunya tana girgiza kan ta. Idan an ce mata Dokta ya na da sake fuska da barkwanci a watannin baya za ta yi musu. Sai gas hi nan, yana bata mamaki a kullum. Zama da shi ya sa ta rika jin kamar a kullum take haduwa da shi a karo na farko.
“Na san ma zai yi maka kyau idan ka saka din.” Ta yanke shawarar zolayar sa.
“Kin ga kuwa sai na fito kamar Yusufanatu.” 4
Ta dan yi dariya, “A’a, b azan so ka zama haka ba. zan saka kawai.”
Ba tare da ta yi aune ba, ta ji ya karba daga hannun ta ya zaga ta bayan ta ya sakala mata. Numfashin sa ya rika busawa a hankali a ta wuyan ta, sannan duk da cewar hannun sa bait aba jikin ta sosai ba, urin da ya shafa suka rika kamar an kona da rushen wuta.
“Beautiful.” Ya furta, bayan ya juya fuskar ta gare shi. Ya sa hannu ya tallabo fuskar ta a hankali zuwa sama, ta yadda yake kallon idanun nata. Ya Allah! Ta tabbata numfashin ta ya dauke, ba zai kara dawowa ba. 2
“Very beautiful.” Ya sake furtawa.
A hankali ya matsa da fuskar sa dab da nata, tana iya jin dumin numfashin sa a fuskar ta. Ba ta san duniyar da ta shiga ba. amma ta ji ham din mota tana shiga gidan na su. 11
“Ina ganin bakin namu sun iso.”Ya furta hakan, amma bai motsa ba, bai kuma bar kallon ta. Tsawon say a kara bayyana a yadda yake tsaye a gaban ta. Rudani da kasala su ka yi barazanar jefar da ita, a yayin da wata kunya ta nemi nutsar da ita cikin kasa. Karar bugun zuciyar ta kuwa, ta yi yakinin yana iya jin sa…du-dum! Du-dum!! Du-dum!!! 6
Haushin karnukan gidan da hayaniyar mutane ta ke ji a kofar shiga, amma ta gagara motsawa. Amatullah na gefen ta amma ta gagara kallon ta.
Karshe dai shi ne ya sakar mata murmushin da ya jefa mata karin rudani cikin kwakwalwa sannan ya juya ya nufi kofar fita waje. Ta kura wa bayan sa idanu ya na tafe cikin kasaita don ya tarbi bakin su, tamkar ba wani abin da ya kusan faruwa a tsakanin su a yanzun nan.
A tsawon rayuwar ta, ba ta taba tsayawa kusa da namiji ba kamar hakan. To amma idan ta duba, ba ta taba yin aure ba sai yanzu. Kuma wannan din mijin ta ne, halal, na sunnah.
Ta yi sauri ta danne duk wasu abubuwa da suka taso cikin zuciyar ta. Baki ne a gidan na su, baki na musamman. Duk yadda ta daure da ma yadda Dokta ya nuna mata karfin halin ta, sai da ta ji shakkar haduwar su.
Ba ta san yadda za su dauke ta ba, ko kuma yadda suke dukan su. A jiya ne da suke wajen gyaran gashi Sara ke mata bayanin su.
“Sunan matar Dokta Sadi Amina, ‘yar cikin garin Bauchi ce, unguwar Makera. Ta na da son kwalliya a fuskar ta caba-caba, ta yadda duk ranar da ba ta yi ba, za ki ga ta canja, har ma ki yi zaton ba ta da lafiya ne. mayyar son taliya ce…” Saran ta kara sauke murya tare da kare bakinta da hannun ta na dama, “…don bata iya dafa komai ba sai ita.”
Asiya ta dan yi dariya, “Kai Sara.”
“Ina gaya miki. Da safe da rana da dare duk taliya. Aminar taliya a ke ce mata, shi kuma mijin nata kamar noodles. Hahaha.” 7
Dole Asiya ta dara, “’Ya’yan su kuma fa?”
Sara ta gyara hannun ta don mai zana mata lallen hannun ta ji dadin cancara wa. Ba ta fara sol, lallen ya ba da kala. Ta amsa, “Babu ko daya. Sau biyu ta na haihuwa amma bas a fitowa da rai. Sun ce dai wai jinin ta ne ya fi karfin na yaron ne ko ya na hawa na yaron ne? Wai dai abin a tsatson wato genetical.”
Asiya ta tausaya mata kwarai da gaske. Sannan ta sa ran haduwa da ita, don ta na ganin alakar su za ta yi kyau.
“Sai kuma Fatima, matar Dokta Kabir.” Sara ta ci gaba da sharhin ta, sai ka ce wata mai aikin gidan rediyo. “’Yar Kaduna ce. Mace ce mai son nuna aji da isa don kawai ita ‘yar birni ce. Dole ai, don ta na ganin ya tsallake kogi goma sha biyar kafin ya kai gare ta, irin ita ta fi kowa a nan Arewan nan.”
Asiya ta girgiza kan ta, “Ba ki da dama.”
“Ina gaya mi ki, yadda take ji da mijin nan na ta. Sun haifi da daya ne, ya na kuma wajen mahaifiyar Doktan.”
“Masha Allah. Abu yayi kyau.”
“Hmm, sai fa a hankali. Ai da suka kai shin ba wai yaye aka ma sa ba. Sai don dai kawai it aba mai yawan son fitina b ace da hayaniya. Renon yaro kuma akwai wahala shi ya sa suka kai wa kakar sa ta rike mu su.”
“To?”
“Ah, ki na mamaki ne? To ko da za ta haihu ma tiyata aka mata, wai idan ta yarda ta haihu da kanta to za ta lalata ni’imar ta.”
Asiya ba ta taba jin hakan ba, abin kuma y aba ta mamaki. A zaton ta, haihuwa baiwar Allah ce da kowace mace ke burin sam, sannan zafin nakudar ma kan ta ibada ne, don duk wadda ta mutu ta wannan hanyar ta yi shahada. To ita me ta sani, tun da ‘yar kauye ce ita.
“Sai nag aba, matan dokta Hadi guda biyu, Suhaima uwargida, Kausar amarya. Suhaima irin matan nan ne da suka kasance sari-ka-noke, wato Musa a baki, Firauna a zuci. Kausar kuwa ‘yar ba ruwan ta ce. Mijin su kuwa, shine babban aminin naki mijin, sannan kuma mayen tuwo miyar kuka ne.
STORY CONTINUES BELOW
Ya kan ci miyar kuka da dare, a duma ma sa da safe ya ci, idan kuma miyar ta rage da rana zai ci. Miyar kuka ko da shinkafa kika ba shi zai ci balle da kowane irin tuwo. A gidan sa sau biyar ake kada kuka a sati. Ina gaya miki, idan matan sa suka sha yaji ko, to kada miyar kuka ce ta kore su.” 13
A lokacin ta ci dariya har ta gode Allah. Don kuwa ba ta taba jin mutum irin sa ba. A ce miyar kuka ba ta ginsar sa? Sai dai ta rike batun matan na sa a ran ta. Hakika za ta iya mu’amala da kowaccen su, gwargwadon yadda ta dauke ta ita ma.
Bakin sun shiga makeken falon mai cike da kamshin oudh da na abinci kala kala. Sun sha adakar su, suka kama wurare a falon suka zauna. Asiya ta gaisa da su daya bayan daya, bayan Yusuf ya gabatar da su gare ta, sannan ta shiga yi mu su hidima da abubuwan da ta yi mu su tanadin sa.
Ta na kicin wajen hade-haden ta, ta na jin muryar Yusuf ya na zuba hira har ma da barkwanci. A cikin sintirin na ta ne ta ji ya cafke hannun ta, kowanne ne daga ciki ba zata iya sani ba, tsabar kaduwar da ta yi.
Ya sake mata murmushin sa mai karfin tiransifoma goma, y ace, “Ki zauna ma na my dear. Sun zo ne mu gana da su, a kalla ki zauna a dan yi hira kafin anjima ki ci gaba.” 4
Ta tabbata ta fi kankara daskarewa, sannan ta fi wuta ci bal-bal. ba ta iya jin komai, kallon lebban sa kawai take yi suna juyawa. Ta tuno da tsayuwar su kafin isowar bakin su. Shin a ce bas u zo ba, zai sumbace ta ne? yaya sumbar yake? Yaya ake ji idan anyi ta?
Har zuwa lokacin dai ba ta zauna ba. Da gaske ne, karfin wutar da ta fi ta lantarkin NEPA ta ratsa jikin ta. Idan bah aka ba, me zai sa ta ci gaba da tsayuwa, sai ka ce daya ga wata? 1
Ko da ta lura kallon ta kowa yak e, sai wata kunya ta ratsa ta. Yusuf ya na iya kokarin san a nu na wa duniya auren su daidai yake da na saura, musamman a gaban abokan sa. Shi ke nan, ita kuma uwar zumudi, sai ta ara ta yafa? Yaya zai dauke ta idan ya ji irin tunanin da take yi a lokacin?
“Zan je ne na dauko Amatullah.”
Amina ce ta ce, “Ga ta nan a hannuna tun dazu.”
Ta ji wani abu kamar yawu ya wuce ta makogwaron ta, ta yi sauri ta ce, “Zan je ne na dauko ma ta madarar ta.”
Fatima ta ce, “Ai kuwa barci ta ke yi. Da kin kyale ta kawai sai jimawa.”
Ta yi sauri ta zare hannun ta daga na Yusuf, sannan ta zauna kan kujerar mai zama daya. Ta yi hakan ne gudun kar ta zauna a gefen sa tilas. Don ta lura kowacce mata ta zauna ne kusa da mijin ta a falon.
Yusuf ya zauna kan hannun kujerar da ta zauna. Amma dai bai sake kama hannun na ta ba. Sai dai ya yi kusa da ita…kusancin yayi yawa har ma karar bugun zuciyar ta kadai take iya ji cikin kunnuwan ta, ba sautin muryoyin kowa ba. Jiri ne yake neman ya debe ta, a yayin da numfashin da ya dauke gare ta ya dawo nan take.
1
Ta yaya ya ke iya zama a hakan ba tare da abin ya shafe shi ba? Me yasa ita kadai c eke wannan hali, shi kuwa ko a jikin sa? Ba mamaki don ya saba mu’amala da mutane a asibiti da ma waje; maza da mata.
Amina ce ta kalle ta, sannan ta ce, “Asiya, ya kamata idan mun zauna ki mana gudumawar sirrin girke-girken naki mai dadin da kika mana, wandan da suka sa mazajenmu santi.”
Suhaima ta yi dariya, “Gaskiya ne, yau Allah dai ya kiyaye mance hula a gidan nan.”
Dokta Sadi ya ce, “Mijin ki ne zai mance hular sa, don shi ne kadai mai jamfa.”
Hadi ya mayar da martini, “Ai idan hula ce mai sauki ce. Kai naga alamar ba ka ma da niyyar komawa gidan ka yau. Filet na uku ke nan ka ke zuwa karaye.”
Sadi ya dago da cinyar kaza cikin bakin sa, ya fige ta, sannan y ace, “Sauki na nema wa mata ta. Ka gay au ba sai ta dora mana taliya ba idan mun koma.” 4
STORY CONTINUES BELOW
Dokta Kabir ya ce, “Na ku wasa ne. ni fa takeaway za a mana, don gobe shi zamu ci abin mu.”
Haka dai suka rika barkwanci a tsakani. Daga baya kuma a ka sako bayanin asibiti da was u harkoki. Wannan y aba da dama wa matan sub a su wuri, don a cewar su, hirar ta su ta koma ta magani da wukar fida.
“Asiya, bari ki saba da jin wannan hirar. Ina gaya miki, wukar yanka albasa ma sai ta shiga baki haushi idan kika gan ta.” In ji Amina, bayan sun koma dakin na ta, suka zauna hirar su ta mata.
“Za ki ji yadda ake yanka mutum kamar wasu mahauta.” Kausar ta tofa na ta albarkacin bakin.
Ita kuwa Suhaima, hankalin ta na kan Amatullahi ne, ta kura mata idanu, ta ce, “Wallahi yarinyar nan abar tausayi, a lokacin da na samu labarin abin da mahaifiyar ta ta yi. Na ji kamar na yi tsuntsuwa na dauke ta na boye.”
“Haka ne.” in ji Fatima, wacce ke kishingide a kan gadon Asiya, tana ta danne dannen wayar ta. “Ni ma na dade ina tunanin yadda za a yi wai uwa ta gama shan wahala a kan haihuwa sannan ta jefar.”
“Ki dade kin a tunanin ki har ki gama ba zaki gane ba, tun da ba haihuwar da kan ki kika yi ba.”
Fatima ta harari Amina, “Duk daya ne. na san dai kasancewar ki wacce kika sha zafin nakuda ba zai sa ki zama uwa tagari fiye da nib a. allah kadai Yasan dalilin da “ya’yan ki bas a zama. Watakila da ba ki kai ni wajen kula da da ba.”
“Haka ne. shi yasa naga kin kai wa mahaifiyar mijin ki dan ki don kin gaza rikewa.”
Asiya ta yi kasake, ta na jin cec-kuce a tsakanin mata abokai biyu, ba tare da sanin abin da zata fada ba. Ya kamata ta ji haushi, don a fakaice an zagi Maree, an zage ta ne. amma bata da bakin kare ta, don abin da ta aikata bai dace ga hankali ya dauka ba. Duk da haka, idan suka ci gaba to ta na ganin za ta tanka mu su. Ko da bata kare Maree ba, za ta iya nuna mus u kowacce ta fuskanci damuwar ta , ta kyale na wasu.
Ta gode Allah da Sara ta yi mata bayanin su kafin su hadu a ranar. A kalla, ta san irin wadan da za ta hadu su yi mu’amala da su. Kasancewar su matan abokai, dole ne su yi hulda. Sai dai yadda suka dauke ta, gwargwadon yadda za ta yi hulda da su ke nan.
Cikin sa’a, Amatullah ta tashi cikin kuka. Nan take ta karbe ta daga hannun Suhaima. Ta shiga yi mata abin da take tunanin za ta fi bukata. Ta fara da canja pampers, sannan dauko gorar madarar ta don ta ba ta ta sha.
“Rayuwar duniya sai a hankali. Komai ya na da dalili.” Suka kalli juna, da Suhaima, sannan ta ci gaba da cewa, “Ba mu taba tsammani Yusuf zai yarda ya yi aure ba, musamman bayan abin da ya samu Abida.”
“Abida?” Kan Asiya na juyi ta tambaya.
“Bai taba baki labarin Abida ba?” Fuskar Suhaima na nuna mamaki.
Asiya ta girgiza kanta. Ta shiga jin haushin kan ta fiye da nasa, “A’a.”
“Abida, kanwa ta ce, uwar mu daya, uban mu daya. Ita Yusuf ya so tamkar ran sa. Ranar auren su Allah Ya yi ma ta rasuwa. Shekaru hudu da suka wuce ke nan. Tun bayan nan, an buga an buga da shi ya yi aure, amma ya ki. Ni kai na abin ba ya min dadi, in na gan shi hakan. Don haka, ranar da ya sanar da mu niyyar auren ki da ya yi, ba karamar murna nayi ba.” 2
Amina ta yi sauri ta ce, “Ni fa a tunanina, idan namiji bai fada min abu ba, to bai shafe nib a ne. ko ya shafe ni ma sai ya ga dacewar na sanin. So, idan bai fada min abu ba, to bai dauke shi da muhimmancin sai na sanin ba ne.”
Ta kai hannunta, ta dafa na Asiya, “Ke dai kin samu Yusuf, kar ki bari ya kubuce mi ki.”
“Ta dai mallaki dakin sa… saura ta mallaki zuciyar sa.” Suhaima, wacce ba ta ji dadin kalaman Amina ba ta mayar da martani.
STORY CONTINUES BELOW
Ba ta san dalili ba, amma sai ta karanta manufa a cikin kalaman Suhaima, kamar gatse ko habaici. Da farko dai ba ta tambaye ta labari ba, amma ta shiga ba ta. Sannan a fakaice ta nuna ma ta cewar ba za ta taba mallakar zuciyar Yusuf ba.
Hmmm. Ta yi sa’a, cewar ita ba wannan ta saka a gaba ba, amma ba za ta kyale ta ba. Don dai garaje ba fad aba ne, kalmar baki kowa ya iya. Ta so ta ce mu sub a kama zuciya ta shiga gidan yi ba. Amma yin hakan zai nuna cewa maganar ta ta shafe ta.
Amina ba ta kyale ba, ta ce, “Tun da har wacce ta mutu ta yi nasarar rike zuciyar rayayye, me zai hana mai rai shiga?”
Suhaima ta yi murmushi, “Hmm, aure kaddara ce daga Ubangiji. Kin ga duk son da yayi wa Abida kuwa? Allah ne bai nufa zai zauna da ita ba. Tsabar kewar ta nag a dakin da ya yi niyyar saka ta ma har yanzu bai saka kowa ciki ba. Na san babu mai iya maye gurbin ta a zuciyar sa.”
Amina ta mike, ta ce da Asiya, “Mu je ki nuna min kicin din ki, ina son na sha ruwa.”
“Ba ga ruwa ba a nan?” Fatima ta nuna jerin gorunan da ked akin.
“Zafi suka yi. Na fi son me sanyi.”
Bayan ta ja ta zuwa kicin ne, ta ke ba ta hakuri. “Kar ki damu da maganganun ta. Wai a hakan ta na taya kanwar ta kishi ne. ta dauka Dokta ba zai taba yin aure ba, tana ganin mijinta aure ya kara alhali ta na raye. Ina ruwan namiji kuma?”
Ta kurbi ruwa, ta ci gaba da cewa, “Hakika na san mutuwar ta ta shafe shi matuka. Kowa ma ya sani. Amma a yau, na ga alamar da ta gamsar da ni cewa Yusuf din da muka sani a da, ya dawo.” Ta kale ta da kyau, ta ba da muhimmanci ga kalaman ta na karshe, “Saboda zuciyar sa ta samu natsuwa da sukuni tun bayan mutuwar Abida. Yadda ya ke kallon Abida a da, haka ya ke kallon ki a yanzu.”
Ta hadiye yawu da kyar. Bata san abin da za ta yi tunanin sa ba. Ba ta ma san abin da ya dace ta ce ba. Ba ta son a hada ta da wata-musamman a ce wacce ta dade da mutuwa. Watakila furuci Amina ke yi, game da abin da ba ta san shi ba. Ta san Yusuf ba ya mata wani kallo na musamman. Ba ta ma san yadda a ke kallo na musamman din ba.
Kwan kwan kwan!! A ka kwankwasa kofar kicin a hankali. Yusuf ya bayyana tare da sallama. Fuskar sa da annuri, wanda ke inganta kyaun sa da ma kwarjinin sa. Ya tambaya, “Ya ya dai? Is everything alright?”
Amina ta yi murmushi, “Komai zanzan. Mun sauko shan ruwa ne, yanzu za mu koma falo.”
Maimakon ya juya ya fita, sai ya ci gaba da tsayawa. Asiya ta kalleshi… ita yak e kallo. Ita kuwa Amina, ta fita, ta na cewa, “Kar kim mance da abin da na fada yanzun nan.”
Ya karasa kusa da ita. Ta so ta dan yi baya, don kuwa idan ya yi hakan ba ta iya tunani mai kyau. Zuciyar ta ta rugurguje, sannan ta sake hadewa, ta shiga zogi. Ya kamata ta tashi. Ya kamata ta bar wurin. Amma wata kasala ta sauko mata, a yayin da ita ma ta gagara dauke idanunta daga nasa. Numfashi da kyar ta ke yinsa. Ta ji kirjin ta kamar zai fashe.
A lokacin Asiya ta yi nasarar fisge idanunta daga na sa, ta na neman mafita. Tabbas, idan ta ci gaba da hakan zai dauke ta marar kamun kai, ko tsayawa ga Kalmar ta. Ba zai kyautu a ce mai dokar hana barci ya bige da gyangyadi ba. Ita ta gindaya sharadi a tsakanin su, it ace ya dace ta bi, sau da kafafu.
“Bari ni ma naje na hada madarar Amatullah.”
Ya tsayar da ita, “Ki bar shi kawaidi y ace, “, idan ta tashi Larai ta dauke ta. Ki zo mu je bakin mu suna jiran mu.”
A dole ta bi shi suka koma falo. Sun tarar dukan su suna nan a hallare, kamar wadan da ke shirin tafiya. Yusuf ya kira Larai ta karbi Ama. A lokacin Sadi ya ce, “Yauwa, amarya, ga wannan”.
Ta lura da akwati a gefen su. Ya ci gaba da cewa bari mu hada da gaisuwar sunan ta. Allah ya raya mana ita, ya kuma bata koshin lafiya.”
“Amin.” In ji Hadi. “Allah kuma ya nuna mana kannen ta.”
Su ka yi dariya, amma ita ya ke ta yi. Da akwai hali, da ta ta ga kasar da kanta, ta kutsa ciki, ba sai ta jira ta tsagen ba. Kowa na cewa, “Amin. Amin.”
A wani lokaci ne wannan abu ya faru! Ba zato ba tsamamni, suka ji muryar wata mace, ta na hayaniya da mai gadin gidan daga ta bakin kofa. Watakila sa-in-sa su ke yi, don ya hana ta shiga ne da farko.
“Me ke faruwa?” Kabir ya tambaya, ya na kallon Yusuf.
“Ban sani ba. Let me find out, bari na bincika.” Ya mike zai nufi kofar.
Daidai lokacin kuma matar ta yi nasarar shigowa falon. Kowa ya zuba mata idanu. Asiya bata taba ganinta ba. Amma yadda ta ke huci, ta ke cika da batsewa, ke nuna ta san abin da ta ke yi.
Biye da ita, wani saurayi ne kyakyawa, fari, kamar matar. Kallo daya in ka yi masa, ka ga mai kwarjini da kyaun halitta. A nata tunanin, kamar ta taba ganin sa.
“Na zo ne, a ba ni jikanya ta!” Kawai ta furta kai tsaye.
Well, well. There’s certainly love in the air. But there’s trouble also…..