KUDIRI
CHAPTER 4
Gaban Asiya ya fadi. Wace ce kuma wannan matar? Wace ce jikanyar ta ta? Me ye gamin ta da Yusuf, ko kuma shi din da wata jikanyarta?
“Ina yini Yafendo.” Yusuf ya furta ga wannan mata cikin muryar da ke nuna ya na kokarin danne zuciyar sa.
Ta katse shi tare da daga ma sa hannu, idanunta na ci da wuta, ta ce, “Ba gaisuwar ka na ke bukata ba Dan-auta, so nake ka bani jika ta. Domin Khalid ba mutuwa yayi ba da ransa. Kuma ni ce na dace na yi renon ‘yar sa, ba kai ba. Don haka ka bani ita yanzu na yi tafiya ta, idan kana son a zauna lafiya. In kuwa ba haka ba, to lallai za ka ga abin da zai ba ka mamaki, har tashin duniya.” 2
Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un! Me Asiya ke ji kuma? Wai da ma wannan din ta zo ne a bata Amatullah? Ya salam! Amatullah? Rana tsaka? Zuciyar ta ta kara bugawa, ta kalli Yusuf. Bai kale ta ba. Idanun sa a kan wacce ya kira da Yafendo ne, fuskar sa a natse. Ko dai ba a dakin da suke ciki yak e ba, ko kuma yak ware wajen boye sirri.
Cikin natsuwa, ya ce, “Ba zan iya bayarwa ba. Ba na kuma tsoron abin da za ki yi.”
Ba ta nuna alamar amsar sa ta girgiza ta, ko ta ba ta mamaki ba. Daure fuskar ta ta kara yi, sannan ta ce, “Oh, haka ka ce ko? To duk duniya ba bu wurin da a ka taba rikon diya na dole, muddin da dangin ta na kusa.”
Ta kalli saurayin da suke tare, ta ci gaba da cewa, “Kai da na dauko ka don ka karbi ‘yarka ka tsaya ka na ji na kamar rediyo?”
Ta dan ingiza Khalid gaba zuwa wajen da Yusuf din ke tsaye, “Ga Khalid, a ba shi diyarsa, mu tafi.” Furucin umarni ne. 3
Bai ce komai ba har a lokacin. Ta sako shi gaba kamar wani yaro dan shekara goma, ko kuma wanda a ka buga a makaranta mahaifiyar sa ta je kwatar ma sa fada. Ta kalli Yusuf, Idanun Asiya su ka tsaya kan saurayin nan, Khalid. 2
Ta kura ma sa idanu, ta ji wani irin bacin rai ya shige ta, duk da rudanin da suka samu kan su ciki. Wannan shi ne ya jefa Mariya cikin ukuba, wanda ya yaudare ta, har ma yayi sanadin bata wa gidan su suna. Wannan shine azzalumi, maci amana. Shin ina ya shiga ne tun tsawon lokacin nan?
Yusuf ya kalli Asiya, karo na farko ta ga ya nuna ma ta alama a cikin kwayar idanun sa. So ya ke yi ta yarda da shi, ta nuna ma sa fahimta. Ta ji zuciyar ta ta yi zogi.
Ta san auren su ba mai dadewa ba ne, amma ta fara samun gargadar da tilas zai bukaci ta tsaya tare da shi don su fuskanta tare. Balle ma, wannan barazana ce ga Amatullah, wacce dukan su biyun suka yi alwashin tsarewa da karfin ikon da Allah Ya ba su.
Nan take ta ji bukatar ta kasance tare da Aman, don ta rungume ta a jikin ta. Kafin ta motsa, ta ji Yusuf ya ce da Yafendo, “Kamar yadda na ce ne, ba zan bayar da Amatullah ba. Ba na kuma tsoron abin da za ki yi, tun da ba zai yi tasiri a kanmu ba da ikon Allah.”
Idanun Yafendo suka canja kala, muryar ta na amon wuta, ta ce, “Ka yi furucin a hankali Dan-auta, don da sannu zan sa ka zuba su a kwano, ka cinye su daya bayan daya.”
Ya yi murmushi, “Tun da na kira Allah to na gama komai.’’
“To ka sani cewa zan dawo ko ka na so, ko ba ka so dole ka mallaka mini ita. Ka sanar da uwar taka, cewa na fi karfin ta. Ta fita daga hanya ta, ko kuwa na gama da ita. Don kuwa ba ta kare ba tsakanin mu.’’
Bai kara ce da ita komai ba, ya juya zuwa ga bakin su, “Don Allah ku koma ku zauna ma na. Ku yi hakuri…”
Yafendo ta sake katse shi, “Lallai Dan auta, an ce yaro bai san wuta ba sai ya taka. Da sannu zan gwada mu ku cewa masallacin kura ko da kudi ne, kare ba zai shiga ba!” 1
STORY CONTINUES BELOW
Ganin bai kula tan ba har a lokacin ya sa ta yi kwafa, sannan ta ce, “Mu je zuwa, mahaukaci ya hau kura.’’
Ta juya ta fita yadda ta shiga tamkar guguwa.Ta bar duk dakin da girgiza, ko ina da kura. Wacce ta fi samun illa kuwa ita Asiya Laminde Sabo Ali. Ita har bari take yi, ta shiga karkarwa. 4
Ganin haka ya sa su Amina shiga da ita daki. Ta na zaune gefen gado, sun a tofa albarkacin bakin su, amma ta kasa cewa komai. Kwakwalwar ta ta sandare, ba ta iya yin kuka domin shi ta nemi yi a lokacin ko zai taimaka ta ji sanyi.
A ce za a raba ta da Amatullah, ko a mafarki bai zo gare ta ba. A yanzu ma ta kasa gaskata kunnuwan ta, zuciyar ta ta ki amincewa.
Ta rungume Amatullah, tana mai tausayi. A zuciyar ta kawai cewa ta ke yi, yi hakuri Amatullah. Mariya ta tafi ta bar ki, mahaifin ki ba ya tare da ke . Ni ma din a na neman a raba mu. Za a kuma a raba ni da Yusuf… 2
Zuciyar ta kuna ta shiga yi mai radadi. Wayyo! Ina mafita?
* * *
Yusuf ya kai gwauro ya kai mari, ya na neman mafita. Karshe dai ya tsaya, ya ja gwauron numfashi bai taba kawowa a ran sa yau asabar, za ta kasance bakar rana ba.
Kafin zuwan Yafendo, ta kasance ranar da ta fi kowacce farinciki a rayuwar sa. Komai na tafiya dai dai kwatsam sai ga bata-gari.A yanzu ga shi ta na neman jefa rayuwar da ya fara ginawa cikin halaka.
Hadi ya fito tare da Suhaima da kishiyar ta. Su ka shige motar su bayan sun ma sa sallama, shi kuma ya tsaya wajen abokin sa, aminin sa.
“Kar ka damu komai zai yi sauki. Su Suhaima sun bata baki sosai, ga alama kuma ta dan rusuna.’’
Zuciyar sa ta sosu ainun. Hakika ya jefa mutune biyu cikin rayuwar rashin tabbas, mutane biyun da suke da muhimmanci a rayuwar sa. Sannan ga mahaifiyar sa. Shi kansa ta sa rayuwar a birkice ne a halin yanzu.
“Thanks. Nagode sosai.’’
“Haba, aboki na, ka san da akwai abin da zan yi ya wuce hakan da na yi. To amma, me zai hana ka nemi lauya? Kar mutanen nan su ba da mamaki, su yi ma na ba-zata.’’
Yusuf ya gyada kan sa, “Éh, mun yi maganar da Kabir. Ya ba ni lambar wayar wani kaninsa. Ya ce min babban barrista ne.’’
Hadi ya nuna jin dadinsa, “Good, hakan ya yi kyau. Idan da abin da za mu yi, just let us know. Za mu kasance tare da kai da Asiya a ko da yaushe.’’
“Na gode, Hadi already kun riga kun yi fiye da zaton ku. Allah Ya kara zumunci.’’
“Amin.’’ Hadi yayi murmushi, ya mika ma sa hannu suka yi musabaha. Kwatsam, sai ya ce, “Akwai shawarar karshe da nake son baka. In har, ba fata mu ke yi ba, ya kasance Amatullah ta koma hannun Yafendo, me zai hana ku shirya wa samun naku ‘ya’yan? Na tabbata muddin Asiya ta samu juna biyu, zafin rabuwa da Ama zai yi muku sauki gaba daya.’’
Yusuf ya yi iya kokarin sa na nuna maganar bata sa zuciyar sa tsalle ba. Kusan ma dariya ta so bashi. Kafin zuwan Asiya da Amatullah rayuwar sa tunanin auren ma bai dame shi ba, balle a ce samun ‘ya’ya. Amma a yanzu da rayuwar sa ta tsinto wannan farincikin mai tsada, bay a kaunar ya yi rashin sa.
“Allah Ya kawo ma su albarka.” Ya fada wa Hadi, duk da sanin cewar ba ya da wannan hurumin a wajen Asiya. Don kuwa alkwari ya yi mata, ba zai saba ba, muddin ba ita ta nemi hakan ba.
Suka yi sallama da Hadi, tare da yi ma sa godiya. Ba dole ba ne ya yi ma sa bayanin halin da ya ke ciki da matar sa. Amma dole ne ya kama shi zuwa ya same ta, ya rarrashe ta. Lokacin ya kai na neman fahimta daga gare ta. Da wannan ya nufi dakin ta.
STORY CONTINUES BELOW
Ya same ta a dunkule, ta na gefen Amatullah, wacce ke kwance a tsakiyar gadon da ke dakin. Ba barci take yi ba, amma ga alama tunani take yi, don ta kura wa bangon dakin idanu. Zuciyar sa ta sosu matuka. Bai taba ganin ta cikin wannan yanayi ba, ko bayan haihuwar Mariya da ma guduwar ta.
“Assalamu Alaikum.’’ Ya furta a hankali
“Wa alaykumus-salam.” Ta amsa sanyaye.
Wani abu ya tokare ma sa wuya. Ya daure, ya ce, “How are you feeling, ya ya ki ke ji?’’
Jin ba ta amsa ba, ya sa shi kusan ciza harshen sa. Kowa ya ganta,ya san ta na cikin tashin hankali,amma shi kuma ya na tambayar ta yadda ta ke.
Ya nisa, sannan ya ci gaba da magana, “Na san ba abu ne mai sauki ba, amma ina son ki saurare ni, don ni da ke ya dace mu yi wata muhimmiyar magana.”
A lokacin ta kalle shi, idanun ta su na bayyana fargaba da tsananin rudani. Ya ji kamar ya ja ta zuwa jikin sa, ya rika rarrashin ta, har sai wannan tsoro ya gushe. Maimakon hakan, sai ya ja kujerar gaban madubin ya zauna, suna fuskantar juna.
“A ranar da na nemi auren ki, kika kuma amince, ba mu saka komai a gab aba, face bada rayuwa mai inganci wa Amatullah. Abin da ya faru yau, ban kawo wa a raina cewa zai faru ba, a kalla ba nan kusa ba. Shi yasa tun farko ban fada miki komai game da shi ba. Amma a yanzu dole ne ki sani.’’
Ya gyara zaman sa sosai, bayan ta kara bas hi hankalin ta. Lokaci ya yi, da za ta san waye Yusuf bayan wanda ke zaune a gaban ta. “Kamar yadda ki ka sani ne, sunana Yusuf, wanda mutane da dama ke kira Dan-Auta. Lakabi ne da Ummata ta yi min ba wai don ni ne autan ba. Ina da kanne har bakwai. Cikin su, kin hadu da Sara da kuma wanda kika gani yanzu a zahiri, Khalid.
Ni likita ne cikakke, kuma kwararre a fannin fida, wato surgeon. Ina daya daga cikin kwararrun (consultants) da ba sa da yawa a fadin jihar nan. Baiwa ce da kuma hazaka tukuru suka sa a karancin shekaruna na haihuwa na kai wannan matsayi.
Mahaifana dukkan su ‘yan garin Jakusko ne. Ita Umma bafulatana ce, shi kuma mahaifina babarbare ne. Haduwar su hadin iyayen su ne,wanda ya samo asalin tun alkawarin da suka yi wa junan su cewa za su hada auren ‘ya’yan su, don inganta zumuncin su ne.
A lokacin alkawarin Baba ya yi auren san a fari ma, Umma kuwa ba ta wuce shekaru goma ba. Da ta kai shekaru goma sha biyar, mahaifin Baba ya hada auren, duk da cewar mahaifin Umma Allah Ya ma sa rasuwa.
Babana ya auri umma ne lokacin yana da mata biyu. Dan sa guda daya tilo don kuwa suna haihuwa amma ‘ya’yan suna rasuwa. Bayan zuwan umma, ta haifi babbar diyar ta maimuna, wacce ta rasu ta na da shekara goma sha daya. Sai bayan rasuwar ta tukunna Allah Ya sa ta haife ni, sai kanina Suraj da kuma kanwata Halima.
A shekarun baya Halima ta yi aure a Ikko, Allah Ya mata rasuwa wajen haihuwa. Diyar da ta Haifa ba ta fito da rai ba ita ma. Suraj ya na koyarwa ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Kaduna. Amma tun da suka tura shi karo ilimi don digir din san a biyu zuwa kasar Malaysia, bai dawo ba. Shekara biyar ke nan.
Na kasan ce da, wanda ya fi kusanci da mahaifina. Don haka ne ma sauran ‘yan uwana da uwayen su suke kishin hakan. Don kuwa Allah Ya nufe shi da samun dimbin arziki, su kuma idanun su kan dukiyar sa ce. Dukiyar da ta raba tsakanin mu.
A shekarun baya ne, kafin rasuwar sa, a lokacin ya na tashen dukiya sosai, ya yi wata wasiyya; cewar duk dan sa namiji da ya haifa ma sa jikan farko, to zai mallaka wa wannan jika wani makeken gidan sa da ke Maitama a Abuja, da filin daya ke da shi a gewayen GRA na garin nan. Wannan ya bari cewa ko da ransa, ko babu, tilas a cika masa wannan wasiyya. 5
A lokacin ina makaranta don haka, sai su Yafendo suka dukufa, wajen tilasta wa yaya na Muttaka kan ya yi aure, don ya mallaki wannan gida. Ya yi aure da wata shida, shi da matar sa su ka yi hatsarin mota, su ka rasu nan take. A lokacin matar ta na da juna biyu wata biyar.’’
STORY CONTINUES BELOW
Ya dan yi shiru don jimamin faruwar hakan. A kullum ya tuna da Muttaka, sai ya ji zuciyar sa ta na kuna matuka, Don kuwa sun shaku da junan su sosai. 3
A cikin yayyen sa ma shi kadai ne suke shiri. Lokacin auren say a halarta cikin farin ciki. Rasuwar say a kawo ma sa gibin farko na rashin wanda yake so a rayuwa. Bayan nan sai Halima, sannan mahaifin su. Abida kuma ta biyo baya, ta kuma kasance ma fi zafi da radadin jurewa.
Ya ci gaba da cewa, bayan wannan ne, Usman kanin Muttaka ya yi aure. Amma sai ya kasance mai yawan aure ne ya na sakewa. Yafendo ce ta saka shi hakan, don da zarar matar da ya aura ta haura watanni shida ba ta samu juna biyu ba sais u tilasta shi ya sake ta ya auri wata. A hakan, cikin ikon Allah ba bu wacce ta haihu a gidan.
Wadda ta kai shekara guda a gidan karya ta yi mu su, cewar ta samu rabo. Bayan sun gama kasha mata kudi da yin bauta, suka gano gaskiyar. Ita ma suka kore ta, kora irin ta wulakanci. Ita kuwa, ta bar musu babban tabo, don kuwa a yanzu haka, ya na da cutar kanjamau, wanda ya samu ta dalilin ta. Ya na can, ba bu mata ko daya.”
Ya nisa, ta lura ya na neman daurewa kana bin da yak e fada ne. a tunanin ta, duk abin da zai fada ya na da matukar wahala gare shi. “Na hadu ne da Abida a gidan su, wata rana da na raka Hadi dauko matar sa, lokacin da ta je yini.
Abida ta kasance mace kyakkyawa, mai natsuwa da kamun kai. Tsabar hankalin ta da iya kalaman ta suka san a fada kaunar ta a wannan rana.”
Muryar sa ta nuna tsananin kaunar sag a Abidar sa, wacce ta kasance ginshikin rayuwar sa a lokacin. Idan suka hadu yak an yini cikin farinciki, sannan su kan kwana hirar soyayya ba tare da sun kosa ba. A lokacin ba ya da burin da ya wuce mallakar ta.
Ya gyara zaman karo na biyu, ya nisa sosai sannan ya ci gaba, “Lokacin da aure na ya tashi da Abida, su Yafendo su ka nu na adawar su sosai. Har ma abin ya kai su ga zuwa gidan su Abidar, su ka bata ni da Ummah don kar a bani ita. Kasancewar kyakkyawar alaka ta da Hadi, wanda ke auren yayar ta Suhaima, a ka mallaka min ita. A wannan rana na kasance cikin farinciki marar misaltuwa. Na shiga kirga ranar da auren mu zai kasance, don zumudin fara rayuwa da wacce nake matukar kauna.”
A hankali ya mike ya tsaya a gefen ta, ya na kallon ta. Gani yak e yi kamar a mafarki ne, kasancewar sa tare da mata har ma da ‘ya. Ko da kuwa na wucin-gadin ne. cikin saukaken murya mai kamar rada-rada, ya karasa, “Sai dai Allah bai nufa zamu zauna ba. Ranar auren mu, Allah Ya yi ma ta rasuwa.’’
Ya sake yin shiru, ya na kokarin seta kwakwalwar sa. Abin mamaki, bai ji cikowar kwalla a idanun sa kamar kullum ba. Bai taba zaton zai yi maganar Abida, bai kare da hawaye idanun sa ba. Ko ma wani ciwo mai zogi cikin zuciyar sa. Abida bangaren rayuwar sa ce mai muhimmanci.
Ya kura idanu wa Asiya, wacce ke kallon sa ita ma, ba ta ko kiftawa. Zuciyar sa ta yi yamutsi. Ba ya iya karanta fuskar ta, don kuwa fayau ce. Ya yi gyarar muryar sa, sannan ya ci gaba da cewa,
“Tun daga lokacin, ban sake tunanin aure ba. Ko ma yunkurin sake yi. Umma ta fahimce ni, don haka ta bar tilasta min kan maganar. Haka ma Baba, har zuwa lokacin rasuwar sa. Tun bayan nan ne Umma ta fara nu na sha’awar ta kan na yi wani auren. Duk da hakan, ba matsawa ta yi ba, sai a ‘yan watannin da suka gabata.’’
Ya kawar da kan sa, a kalli wurin da Amatullah ke kwance a gefen Asiya. “A lokacin da Mariya ta nu na Khalid a matsayin wanda ya yi ma ta juna biyu, sai da tunani guda ya fado min, cewa dukiyar nan ya hanga, don ya mallaka. Bayan na tunkare shi game da amfani da suna na ya na lalata, sai na fahimci cewa bai san da maganar ba gaba daya. Shi dai kawai ya yi ne don ya bata min sunan, ya rugurguza rayuwar da na gina wa kaina da Umma. Na kuma fahimci cewar su Yafendo bas u san da zancen ba. Don haka na yi shiru na kyale.
“Duk da haka, hankali na bai kwanta ba, sai na fara tunanin yadda zan bullo wa al’amarin. Na san tilasta wa Khalid ya aure ta shine abin da ya dace. Amma ya riga ya nun aba zai yi hakan ba. Sai kuwa sauki ya zo, dalilin auren mariya. Nan na ji hankali na ya kwanta, na samu sukuni…na kankanin lokaci.
“Haduwar da mu ka sake yi a asibiti da kuma jin cewar mijin Mariya ya sake ta, su ka sake dawowa da matsala ta. Na san tilas ne na dauki mataki mai dorewa. To daga nan ne kuma fa matsala kan matsala, har zuwa lokacin da na san ba mafita sai ko na rike Amatullah da kai na. Hakan ya sa na furta mi ki niyya ta, kuma har mu ka kawo yanzu.
“Wata kila za ki yi tunanin manufata game da rikon Amatullah, ko don mallakar dukiyar da mahaifi na ya bari ne. Ko kadan ba hakan ba ne. Ba da wannan niyyar na rike Amatullah ba. Na yi imanin Khalid ba zai rike ta ba, tun da tun farko, ya ki amincewa da ita.
“Khalid ya na fama da rashin lafiyar sickle cell anaemia, cutar sikila. Ganin Ama ta fito da rashin lafiya, ya sa na ke neman kulawa da ita. Don idan ta gaje shi, dole na yi hakan na musamman.”
Ya sake jan numfashi. Ya na bukatar ta yarda da shi, ta amince da manufar sa yadda ya fada ma ta. Don kuwa bait aba yi mata karya ba, ba kuma zai fara ba.
“Zancen dukiya kuwa, ba wai babu ba ne. Mahaifin mu ya yi jingina ce da ita, ya karbi basussuka da dama don neman tsayar da kasuwancin sa da ya ruguje kusan zai rasu. A yanzu haka, kokarin na ke na karasa biyan bashin, don na karbe su. ‘Yan uwana ba su san da wannan ba. A ganin su, ya salwantar da dukiyar sa ce don ya gina min asibitin Sauki sannan ya mallaka min. ni kuma ba na son na fada wa duniya cewar, mahaifina ya tallafa min kam wajen ginin, amma dukiyar Umma ce da ta sayar da gonakin da ta gada wajen mahaifin ta da sauran kadarorin ta, hade da kudaden abokai na guda biyu, Hadi da Sadi. Tayar da maganar dukiyar a ko yaushe, dole ya tona asirin hakan, ni kuwa tserar da martaba da kimar mahaifin mu na ke muradin yi, duniya da lahira, don haka na yi alwashin biyan basussukan da ke kan sa, ko da zan tashi ba bu komai gare ni.’’
Ya dan yi shiru na wani lokaci. Ita ya ke kallo, ko zai hangi rashin yarda a idon ta? Bai gani ba. Hakan na nufin ta yarda da shi ke nan, ta kuma fahimce shi? Ya kamata ta fahimce shi, ko da duk duniya za su gaza yin hakan. Yardar ta aba ce mai matukar muhimmanci gare shi. A yanzu ya ke fahimtar hakan.
Tambaya ta yi ma sa, wacce a lokacin bai shirya ma ta ba. “Idan Amatullah ta kasance ta koma hannun su ya ya matsayin auren mu?”Yusuf yayi kasake tambayar ta na shigar sa a hankali. Hakika, ta fi shi shiga tashin hankalin rabuwa da Ama. Don haka ne ma tun dazu take zaune cikin fargabar rabuwar su. Ba wai don tana tsoron fuskantar duniya ba ne, sai don rabuwar za ta zame mata tashin hankali. +
Sai ga shi ya zo ma ta da zancen tsohuwar soyayyar sa, wacce ya nuna alamar ta na da matukar mahimmanci a rayuwar sa har a lokacin. Watakila shi ya sa shi ya furta auren su na wucin gadi, tare da bata damar rabuwa a lokacin da take so. Yanzu ne damar ta, na ganin ko zai cika alkawarin sa ko zai saba?
Amatullah ta yi motsi a lokacin, gaba daya suka mayar da hankalin su zuwa gare ta. Motsin mika kawai ta yi, ta koma ta ci gaba da barcin ta. Kowannen su da abin da ke ran sa. Allah sarki! Ga ta dai ba diyar su ba ce, amma ta hada su zaman aure kuma a dalilin rashin ta, auren su zai iya fuskar ta barazana, wadda a yanzu ba ta shirya wa ba.
Bayan kamar zamani mai tsawo, ya ce da ita, “Ina ganin ya dace mu yi abu daya bayan daya. Farko, mu gama da matsalar da ta same mu a yanzu, kafin mu yi tunanin wata.”
Daga nan, ya tsaya jikin Amatullah tare da shafa ma ta kumatun ta, sannan ya sake kallon Asiya, “Idan kina bukatar wani abu a ko yaushe sai ki sanar da ni. Sai da safe.” Daga nan ya yi ficewar sa.
Ta zuba wa bayan sa idanu. Ba ta san ta rike numfashin ta ba, sai da ya rufe kofar bayan ya fice daga dakin na ta. Ta nisa. Ya ce idan ta na bukatar wani abu ta sanar da shi. Ga amsar da tafi bukata, amma ya zille ya ki badawa.
Ita ma kan ta, idan ba karya za ta yi wa kan ta ba, zuciyar ta ba son jin amsar take ba. Amma dole ta yi wannan tambayar. Ta san dole ne rabuwar su ta yi kusa, idan har a ka raba su da wadda ta yi dalilin auren na su. Tabbas, Yusuf ba zai bukaci komai daga gare ta ba.
Yusuf ya bata zabi, cewa idan ta na so, ta yanke alakar su. Don haka, da zarar ta furta hakan, to fa ba makawa, a tsammanin ta, zai cika alkawarin da ya dauka.
Ta sake nisawa, tare da kallon Amatullah. Kan ta a daure ya ke. Ta na fatan da a ce ita ce wannan jaririyar, wacce ke kwance abin ta, ba ta san me duniya ke ciki ba.
A lokuta irin wannan, ta kan mike ne ta yi sallolin dare, ta fada wa Allah damuwar ta, ta kuma yi fatan samun alheri bisa jagorancin Sa. A wannan dare ma ba ta yi barci ba. Ta yi kusan kwana ta na raya daren da nafilfili da karatun Al-kur’ani. Lokaci-lokaci Amatullah kan katse mata idan ta farka. Bayan ta ba ta madara ko kuma ta rarrashe ta, sai ta koma abin ta. Ita kuma ta koma abin da ta ke yi, har a ka kira sallar asuba.
Bayan ta idar da sallah ne ta yi zikirin ta, idon ta na kan Amatullah. Son ta kara bulbula ya ke cikin zuciyar ta, abin har ba ta tsoro ya ke yi. Ga rabuwa ta zo, ga shi kuma sai son ta ke karuwa. Wata kila hakan alheri ne?
Ta nisa. Ta bar komai a hannun Allah, don Shi ne Buwayi, Gagara misali. Shi Ya nufe ta da shiga rayuwar Ama, don haka idan rawar da za ta taka cikin rayuwar ta ta ta zo karshe, babu yadda ta iya. Da wannan ta mike zuwa kicin, don hada wa Amatullah madarar ta. Wanda ta hada sun kare, kuma za ta iya bukatar sha da zarar ta tashi. Hakan ma zai bata damar rage tunani da radadi daga cikin zuciyar ta.
Motsin da ta ji a kicin ya sa ta kalli agogon falon, karfe shida saura kwata. Duk da cewa Larai ta kan tashi da wuri, ba ta shiga madafi kamar yanzu. Ita kan ta dai ba karyawa da wuri ta ke ba.
Wasu lokutan ma ta kan ci abincin safe a matsayin na rana ne. Shi kuma Dokta Yusuf bai cika zama da safe ba, yawanci a asibiti ya ke. Umma kuma ba ta nan. Don haka Larai ta kan yi kaye-kayen ta ne na wasu bangaren gidan, sai kamar hantsi ta fita su gaisa.
STORY CONTINUES BELOW
Gaban ta gadi, kan ta tsaye ta shiga kicin din, ta iske Yusuf ya na zaune bisa daya daga cikin dogayen kujerun da suke kicin din, gaban sa da babban kofi, ya na turiri. Mamaki da fargaba suka kamata. Ta gagara daga kafafun ta. Tsabar kaduwa, gorunan bulumbotin da ke hannun ta guda biyu suka fadi kasa. 6
Yusuf ya mike don ya kai ma ta agaji. Hantar ta ta shiga kadawa. Me ya ke yi a nan? Ta lura shayi ne ko gahawa ya ke sha… amma me ya sa a kicin?
Ta kwabi kan ta. Gidan sa ne, duk wurin da ya ga dama zai zauna, ya sha shayin sa ko gahawar sa. Kawai dai, don bai taba yi bane tun zuwan ta gidan ya sa ta shiga wannan yanayi, har ma take ganin cewa sabon abu ne.
“Ina kwana?” Shi ya fara gaishe ta, ya na kallon ta. Kafin ta ce za ta amsa tuni ya debe gorunar bulumbotin din da su ka fadi daga hannayen ta, ya kai wajen wanke-wanke.
Da kyar ta amsa, “Lafiya”.Ta ci gaba da cewa, “Bari na koma na baka waje… kar na dame ka.”
“Oh no, ki zo ki yi abin da ki ke son yi.” Bai juya ya kalle ta ba, ya ja abin da suke wanke gorunan bulumbotil din da abin tsaftace shi ya shiga wankewa cikin natsuwa da kwarewa. Zuciyar ta ta kara matsewa. A yanzu ta kara tabbatar wa, Yusuf zai iya rayuwar ba tare da ita ba. Idan gadarar ta iya reno ne, ta ga alama ba za ta gwada ma sa komai ba.
Ta yi kokarin seta tunanin ta. Ko da ba za ta gwada ma sa komai ba, tilas ta gudanar da aikin da ya dauke ta a kan sa…oh, ya aure ta don yin sa, ta gyara. Idan ya ga damar taimaka mata, wannan shi ya yi niyya, amma ba gazawar ta ce dalilin hakan ba.
Don haka ta nufi rishon gas ta kunna, sannan ta dora tukunyar ruwa don hada abincin Ama, shi kuma ya na amsa wayar sa, wanda yawanci daga asibiti ne. bayan ya gama, ya ajiye gorunan cikin abin tsaftace su, ya koma ya ci gaba da kurbar gahawar sa.
Asiya dai ta saba hada abincin Amatullah, amma a yau, a takure ta ke. A tunannin ta, gwara ta koma daki, tun da Aman ba ta farka ba. Sannan za ta ba shi damar shan gahawar sa a tsanake.
Kar dai ya dauka da wata manufa, sai ta ce da shi, “Bari dai na duba naga ko Amatullah ta farka.”
Ko da ta yunkurin komawa dakin ta, ta ji ya ce,“Dole ai ki koma. Ba kin ga mai kaho a goshinsa ba?” Fuskar sa fayau ya na kallon ta. 1
Farko ta fara ne da tsimewa, sai fuskar ta ta yamutse da murmushi. Furucin sa ya sanya ta kallon kan sa, ganin kaho a goshin sa zai masa kyau… in har zai samu. Murmushin ya taimaka mata wajen sakewa a cikin zuciyar ta.
“Hmm, na san kina tunanin ganin kahon ne a goshi na, ko?”
Ta yi sauri ta girgiza kan ta, a kokarin ta na kade tasirin da muryar sa ke yi cikin zuciyar ta a lokacin. Ta amsa, “A’a.”
Ya ce, “Fadi gaskiya dai. Goshi na ki ke kallo.” Muryar sa a sake take, bai nu na alamar ran sa ko ya baci ba.
Nan ta kara girgiza kan ta, sannan ta dan sunkuyar da kan ta cikin jin kunya. Hakan bai taba faruwa ba. Ko don labarin da ya fada mata ne game da shi daren jiya? Shi ne dalilin sakewar sa? Cewa ya kara sa su kusanta cikin fahimta?
“Ina son fada mi ki wa ta magana. Amma kar ki min gurguwar fahimta, don Allah.” Ya furta tare da nuna mata alamar ta zauna kan daya daga cikin kujerun da su ka rage kusa da shi.
Ta kalle shi, a yayin da zuciyar ta ke tsalle a kirjin ta. A halin da a ke ciki ko kallon ta ya yi zuciyar ta sai ta yi hakan. Balle kuma a ce zai yi ma ta magana. Me zai ce kuma?
Ta dai yi yadda ya bukata, amma zuciyar ta sai bugu take cikin sauri. Ta lura idanun sa sun gwada alamar rashin barci. Bai yi barci ba? Mamaki ya kara kama ta. Me ya sa?
STORY CONTINUES BELOW
Kamshin gahawa hade da na turaren sa suka gauraye tare da cakudewa, suka cika mata kai. Shigar sa ta kwat mai jan shat da nektayel din sa sun burge matuka. Ya yi kama da wanda za a dauke shi a rataye cikin abin hoto a yi ta kallon sa kullum. 3
“Akwai bukatar ni da ke mu kara fahimtar juna, idan har muna son samun nasara kan wannan kura da ta taso mana.”
Me ya ke cewa ne? Cewa ya son su yi nasara kan su Yafendo?
Ya ci gaba da cewa, “Duk zamantakewar miji da mata, ya dace akwai abota ciki, kamar yadda tun farko ki ka nuna kafin auren mu. Don haka, idan ba zaki damu ba, ina son ki zama kawata, ni kuma abokinki. Me kika ce?” 4
A lokacin ruwan da ta saka a kan wuta ya nuna alamar tafasa. Ta na son tashi ta duba, amma ta kasa. Tsoro take ji, kar garin hakan ya sa ta farka daga wannan barcin da ta ke yi. Barcin da a cikin sa Yusuf ya nemi su yi abota da ita.
Me za ta ce? A ganinta, a yanzun ma ita da shi akwai ‘yar fahimta a tsakanin su. Shin gani ya ke bata wadatar ba? Ta ce, “Ni da kai mun wuce duk wani tubali, mun zarce zuwa ga gini. Auren da mu ka yi, ya take duk wata abotar da zamu yi.”
Ya dan yi murmushi, “Ba a makara da yin abu a rayuwa. A yanayin da mu ka yi auren mu, ba zai hana mu yin abota ba, musamman tun da za ta taimaka wa zamantakewar mu. So….. friends?” 5
Ta tsaya kallon sa. Ya kamata ta bar kokwanto a kan duk wani abin da ya fito da shi. Idan har zai iya kaskantar da kan sa don su yi abota, me zai hana ita ma ta mika ma sa na ta? Ta amince, “Shi ke nan.”
“Shi ke nan, me?”
“Shi ke nan, za mu yi abota. Idan har hakan zai taimaka ma na wajen samun nasara a kan wadan can.”
“To ai ba haka a ke yi ba.” Ya mika mata hannun sa, “Ki miko hannun ki mu daura a kan abotar nan, tare da alwashin kasancewa kusa da juna a duk yanayi; dadi ko rashin sa, cuta ko lafiya, ko da mun kasance ma’auratan juna ko mun rabu.”
Ta mika masa hannu suka daura. Na sa da dan sanyi kamar nata, amma ya na aika ma ta zogi a duk jikin ta. Karo na farko ke nan take hada hannu da shi. Kai da kowane da namiji ma ba shi ba. 5
Ba ta son kalmar rabuwa, amma a wannan hali, za ta karbi abin da lokaci ya bata ne, ko da kadan ne. Zai iya yiwuwa ya kasance abu ma fi wahala wajen rikewa a rayuwar ta.
Amma ita ba mai saurin barin abu bane. Ta na da naci kana bin da take ji a zuciyar ta daidai ne. Don haka ta ce da shi,“Na yi alkawari.”
Ya ce, “Good, ya yi kyau. So yanzu bari abokin ki ya fara mi ki da albishirin samun damar karo ilimin da ki ka yi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ta fannin gyara takardar ki, wato Remedial studies. Na kai musu takardar ki ta kamala sakandare, sun kuma ce ya yi kyau, amma kasancewa baki rubuta jarrabawar shiga jami’a ba, ba za ki samu shiga aji daya kai tsaye ba. Anjima zan aiko mi ki da takardar shaidar hakan. A yanzun na ga ya dace ki fara da yin wannan karatun, in ya so sai ki yi rajistan JAMB ki rubuta daga baya. Don haka, sai in ce Allah Ya ba da sa’a.”
Ta bude baki za ta yi magana, amma muryar ta ta makale. Watakila rudanin farin ciki da ta shiga ne. hade da mamaki. Idanun ta suka ciko da kwalla, karshe muryar ta ta fito bayan ta kyafta idanun ta sau biyu,
“Ban san abin da zan ce maka ba.”
“Then, kar ki ce komai. Alkawari na yi. Ki yi min fatan Allah ya nufe ni da cika wa.”
Zuciyar ta ta shiga zogi don jin irin sautin muryar sa, wanda ya kasance kasa-kasa. Idanun sa kunshe suke da abubuwa, wadan da ba ta fahimce su ba, amma sun sanyaya mata jiki. Ta saki murmushi, “Na gode. Allah Ya maka sakayya da mafificin alherinSa.”
STORY CONTINUES BELOW
Ya mata murmushi, “Ba bu wanda ya ki kari. Amma da sai in ce, Ya riga Ya bani. Bayan wannan ba na bukatar komai.”Muryar sa kasa-kasa, mai birkita mai sauraro. 1
Ta ji yawu ya sake wucewa ta makogwaron ta. A kalla, muryar tasa ta birkita mata kwanya. So take ta dauke shayin nasa, ko gahawa ne? Ta kwankwade lokaci guda ko zata ji sanyi. Kunya ta hana ta daga fuskar ta ta ci gaba da kallon sa. 2
“You know, kasar nan za ta karu matuka da ilimin da za ki bida, na tabbatar da hakan.”
Kwatsam ta ji ya canja akalar hirar ta su. Ta daga kai ta kalle shi. Ya na kurbar gahawar sa a hankali, bai bar kallon na ta ba. Sai dai fuskar sa fayau ce, ba ta iya karanta komai. Ba ta san dalili ba, amma sai ta ji bata so hakan ba. Amma dai hakan ya fi.
Ta ce,”Hmmm, har ka sa na ji kunya. Kai da a ke samun karuwa daga gare ka dalilin kannin ka, har za ka hada da ni?”
Ya fadada murmushin sa, “Kin san ilimin mace ya na da alaka da ilimin alummma gaba daya. Kowa da kowa zai amfana da ilimin ta kana daga iyayen ta,’ya’yan ta zuwa ga mijin ta…” 1
Ya fadi kalmar mijinta cikin wani salon muryar, wanda ya sa ta shiga wani sabon radadi. Ga shi ya kura mata idanu, ba ya ko kiftawa. Ba ta taba shiga irin wannan yanayi ba, ba ta kuma san dalilin ba. Ko kila don ya furta kalmar ta na shawagi a sararin samaniya ne, ko kuma don ya saukar da kan sa daidai ita, su suka sa zuciyar ta shiga yanayin da bai kamace ta ba.
“Haka ne.” Ta fadada murmushin ta ita ma, “Ilimin mace ya na da muhmmanci sosai, musamman idan ta samu boko da islamiyya. Samun hakan kan sa ta samu kyakyawar alaka da mutane.”
Wani dan gulliti ya nemi tokare wuyan ta. Rayuwar su ta gida ta gifce mata a idanun ta, yadda Dada ta sha wahala wajen hidimar neman ilimin su.
Ko ba komai, don su tsaya da kafafuwan su, kar su yi rayuwa irin wadda ta ke cikin ta. Cikin su shida, babu wacce ta wuce sakandare. Ita da Maree ne ma suka kai sakandaren. Sauran kam ko firamaren ba su karasa ba.
Maree. Allah kadai Ya san wurin da ta shiga. Ta yi gaba ta bar baya da kura. Ko da ta na nan din ma babu abin da za ta iya yi game da ceto Amatullah. ta sha fada a zuciyar ta, cewa da Maree ba ta san hanyar zuwa Jos ba, da wannan abu bai faru ba. Sai dai kaddara a har kullum, ta kan riga fata.
Ta kalle shi, a lokacin da ya ke cewa, “Shi ya sa na ke da burin Amatullah ta samu ilimi mai zurfi, wanda zai amfane mu da addinin mu gaba daya.”
Ta dan yi murmushi mai garwaye da kunci. Za ta so a ce ta ga girman Amatullah, amma wannan mafarki ne da ita kanta bata cancanci yin sa ba. Ba ta da ‘yancin yin sa, balle ta zuba dinbin fata cikin zuciyarta. Dole ta fuskanci dacin gaskiya komai daren dadewa. Yusuf ya fi karfin ta, duk da cewa mijin ta ne.
Ta mike zuwa ga tukunyar da ke ta tafasa a kan wuta. Zama haka su rika hira ba zai taimaka ba. Zai iya sa su yi shakuwar da rabuwar su za ta ba ta wahala. Balle ma ba ta cikin ransa, jiya ya tabbatar mata da hakan.
“Na san za ka iya yin hakan. Zan yi ma fatan Allah Ya taimake ka.
A lokacin da ya mike shi ma, ya shiga taya ta hada abincin jaririyar su. “Allah Ya tamake mu dai. Ko kin taba jin hannu daya ya dauki jinka?’’
Ya kasance dab da ita, sannan ya kara jefa zuciyar ta cikin wani irin shauki. Ba ta san yadda za ta kwatanta ba. Ya sauke muryar sa sa sosai, ya ci gaba, “A duk lokacin da mutum ya samu haihuwa, burin sa, ya ga girman dan sa, ya kuma inganta da kyautata wa rayuwar sa har zuwa lokacin da zai amfani kan sa da al’umma baki daya. Shi ba kya son ganin hakan game da Amatullah?”
Ta kalleshi da kyar, domin kuwa duk kwanyar ta ta rude, rabin maganar sa ba ta fahimta. Kamshin sa mai dadi ya kara juya ma ta kwakwalwa.
“Zan so hakan. Amma ba lallai ba ne na kasance har zuwa lokacin.”
Ta lura da wani kyalli a cikin idanun sa, tare da wani murmushi, wanda ba dalili suka rika buga ma ta zuciya. Ya ce, “Haka ne. wa ya san lokacin da mutuwa za ta riski mutum?”
Ta nisa. Mutuwa ya ambata, amma ba na aure ba. Ita ma zuciyar ta ta bata kaunar Kalmar mutuwar auren, amma tambayar da yayi mata na gaba ta kada ta ainun.
“Ina ki ke ganin auren mu, nan da shekaru arba’in ko hamsin… ko fiye?” 10
Wai me ne? Hamsin ko fiye? Ta ina wannan tambayar ta fado? Me ya kawo wannan tunani a cikin auren wucin-gadi kuma? Ta nisa, sannan ta amsa, “Ba na da wannan hurumi kan abin da bai zo ba. Kamar yadda ka ce ne, babu wanda ya san gobe.”
Wani daci ya nemi mamaye bakinta. Ya ma zai yi wasa da hankalin ta. Ya fi kowa sanin yanayin auren su, sannan daga baya ya nemi dandana mata zuma a baki? Me yake nufi da hakan? Ba ma za ta fara dogon nazari a kai ba. Laifin ta ne, da ta biye ma sa, ta zauna hira na fahimta da shi.
A lokacin Larai ta shiga kicin din kan ta tsaye. Ganin su duka ya sa ta sauri ta koma, ta na ba su hakuri. A lokacin ne Asiya su ka gama hada abincin Ama, ta zuba cikin gorunan ta, sannan ta jera su cikin firij, don in ta tashi nema, sai ta duma ma ta. Duk abin da take yi, bai sake cewa komai ba. Ita ma ba ta san abin da za ta ce da shi ba. A ganin ta, babu sauran magana da za su yi.
Can ta daure ta kalle shi, “Akwai abin da ka ke bukata ne, na ma ka?”
Ya girgiza kan sa, “No, zan je asibiti yanzu.” Ya yi yunkurin ficewa daga kicin din, ya dora da, “Kar na makara, ina da ayyuka yau din nan.”
Ta hadiye yawu a hankali, ta tambaya, “Abincin rana za ka turo a dauka ma ka ke nan?”
Ya girgiza kan sa, “No, zan samu abin da zan ci a can. Idan ma har zan bukaci abinci zuwa dare, zan nemi Larai ta yi min.” 6
Daga nan ya yi ficewar sa, ko wane takun kafar sa ya na murkushe zuciyar ta. Ba ta san tunanin da ya dace ta yi ba, a lokacin da ta wuce kan ta tsaye zuwa dakin ta. Zuciyar ta radadi take yi, saboda tsabar bugu.
Ta riga ta fada yanayin da ta ke guje wa tuntuni. Rayuwar ta ba za ta taba kasancewa daidai ba. Don a yanzu fiye da ko yaushe, ta fahimci cewa ta fada son Yusuf, ta shiga kaunar sa…..ba tare da sanin lokacin ba. 8
Ta dafe kirjin ta, a yayin da ta lumshe idanun ta, kwalla suka zubo ta cikin su. A hankali ta bude su. Ta shiga yanayin da ba za ta taba bayyana sirrin da ke zuciyar ta ba.
Don kuwa Yusuf na Abida ce, ba bu wurin da zai saka ta, ko da ta nemi gurbi cikin zuciyar sa. Hakika ba za ta iya gasar neman gurbin zuciya da matacciya ba….Yusuf ya nufi bangaren da ofishin sa ya ke, mutane ne ke jere a kujeru su na zaune. Kowanne na jiran ya gan shi. Nas nas su ka gaishe shi, ya gyada mu su kai kawai a matsayin amsa, sannan ya shige ciki. Ko ina a tsaftace ne, kamar yadda ya ke so, an kuma jera ma sa fayel fayel na marasa lafiyar da zai gani a ranar. Kafin nan, zai fara nazari kan tiyatar da zai yi da azahar. +
Ya zauna a hankali bayan ya duba kalandar kwanan wata kamar yadda ya saba, ya kalli dimbin fayel na marasa lafiya, ya nisa. Akwai aiki sosai a yau. Ya dauko fayel din farko ya bude, amma bai ga komai ba, idannun sa sun rufe.
‘Wa ya san gobe’ fa ta ce ma sa. Manufar ta daya ne, auren ta da shi bai dame ta ba. Nan ya ga wautar sa na ganin cewa kila akwai damar da Asiya ke da shi na maye gurbin Abida. Kwana ya yi bai runtsa ba a kan hakan. Sai ga shi ya ma ta shigar sauri, ya razana ta. A takaice dai, dole ya canja salon sa.
Hadi ya shiga ofis din ba tare da sallama ba. Ko da Yusuf ya dago ya lura da yanayin sa, ya ga tashin hankali da bacin rai ke bayyane cikin idanun sa da ma fukar sa. 3
“Lafiya Hadi? What is it?” Ya tamabaya cikin kulawa da damuwa. Ya tsayar da ta sa damuwar don fuskantar ta aminin sa. Yanayin Hadi kan canja ne idan wani majiyyacin da yake kulawa da shi ya mutu; ko kuma bai karya da safe ba.
Don kuwa yunwa ta kan daga masa hankali. Amma Yusuf bai taba ganin sa cikin wannan yanayi ba. Ya sha bamban da sauran, shi ya sa ya ba shi hankalin sa gaba daya. 2
Amsar da ta fito daga bakin Hadi ta girgiza Yusuf daga silin gashin kan sa zuwa yatsun kafar sa. “Na saki Kausar yau da safen nan.’’ 6
Tun da Yusuf ya zaro idanu, sai kyafta su kawai ya ke yi. Hadi ya zauna kan kujerar da ke fuskantar sa. Mamaki ne ya cinye harshen sa.
“Garin ya ya hakan ya faru, Hadi?” Karshe muryar Yusuf ta dawo. “Babu fada ko sabani, sai kawai rabuwa?”
Dole ya girgiza, domin kuwa jiya suna tare da iyalan juna har yamma. Har shi Hadin ya ba shi kwarin gwiwar fuskantar matsalar da ta kunno ma sa a jiyan. Sai ga wannan kuma ya bijiro?
Hadi ya amsa, “Hakika ba mu yi fada ita ba. Ko jiyan bayan mun koma gida mu na tare cikin fara’a. rabuwar mu ta fahimta ce, ba gaba ko fada ba. Ka san yadda mahaifin ta yake, ka kuma sha shiga tsakanin maganar mu.
To a jiyan kamar kullum, ya ziyarce mu, ya kuma jefa min bukatar sa na neman sakin diyar sa. Ni kuma a gaskiya na ji na kosa, na tsani jin kallaman sa a kullum idan ya tsaya a gaba na; wai tun da babu kira, me zai ci gawayi?”
Yusuf ya ji wani daci wa a wuyan sa. A kullum furucin Baban Kausar ga Hadi ke nan. Sai ka ce mutum shi zai ba wa kan sa haihuwa ba Allah ba. Ba abin boye ba ne, cewa Kausar ce ta so abin ta, amma mahaifin ta bai taba kaunar Hadin ba. Balle kuma da a ka samu wannan jarrabawa shike nan ya gaza hakuri. 2
A daren jiya, ni da ita mun dauki tsawon lokaci mu na tattaunawa irin ta fahimta da natsuwa. Ta gwada min cewa burin ta ne a duniya; karin karatu da kuma haihuwa.
Ta san zan iya daukar nauyin karatun nata, amma ta na son ta je wani wajen, ko Allah zai sa ta samu haihuwa. Saboda haka da safe nan, cikin tashin hankali da ban taba samun kaina ciki ba, na rubuta ma ta takardar saki daya, na kuma kai ta gidan su da kaina.
“I really don’t know, Yusuf, ban san abin da zan yi ba. Ni likita ne, kuma na bi hanyoyi da dama wajen gwaje-gwaje ni da matana duka, komai ya nuna cewa muna da lafiyar samun haihuwa, Allah ne bai bayar ba.”
Muryar sa cike da takaici da kunci. A bayyane ne, wannan rabuwar ta girgiza shi fiye da yadda ya ke nunawa. Hadi mutum ne mai saukin kai tare da daaukar rayuwa cikin sauki. Ba karamin abu ba ne ya ke jijjiga shi.
STORY CONTINUES BELOW
Yusuf ya mike zuwa kujerar zaman da ke gefen Hadi ya zauna. Ya tausaya ma sa matuka, amma baa bin da ya kamata ya nuna ma sa bane. Tun da abin da ya faru ya faru, sai dai a samo mafita. “I am sorry, a gaskiya jin wannan bai min dadi ba.”
“Ko ni ma ban so ba Yusuf. Na kwana ina tambayar kai na, shin dole ne zaman aure sai da haihuwa ne? Ma’aurata ba za su zauna cikin aminci da kaunar juna ba har sai sun haihu? Yusuf, yara bonus, kyauta ce wadda ko da su ko babu, bai kamata ya shafi alakar miji da matar sa ba. Musamman idan Allah bai ba su ba ne kawai, ba wai don sun yi wani laifi ba.” 1
Kan Hadi a sunkuye ne, amma muryar sa ke kara nuna halin da yake ciki, wanda ke kara murza zuciyar abokin sa. Ya dan dafa hannun sa, “Its alright Hadi. Ba karshen duniya ba ne. kuma ka san z aka iya mayar da ita, ko?”
Hadi ya girgiza kan sa, “Ta tafi ke nan Yusuf, har abada ta kubuce min.” Ya dago suka hada ido, “Ashe haka sakin mace yake Yusuf?”
Hadi dole ya girgiza,don kuwa rashin haihuwar sa na damun sa balle a ce kuma dalilin hakan ne ya kawo rabuwar sa da matar sa. Yusuf ya nisa shi bai saki tasa matar ba, amma ya fi Hadi shiga tashin hankali.
A lokacin Sadi ya shiga, ya gan su cirko-cirko. Ya tambayi dalili. Bayan Yusuf ya fada masa, sai ya dafe kafadar Hadi ya ce, “Ka yi daidai bro, don kuwa idan mace ta nu na ba ta son zama da kai to ka sallame ta, don kwaciyar hankalin ku gaba daya. Ko ba haka ba ne Dan auta?” 2
Yusuf ya lashe lebban sa, bakin sa ya bushe gaba daya a lokaci guda. Hakika, yadda Sadi ya furta hakan ya dace. Sai dai ba abu ne mai sauki ba.
“No Sadisu, ba dalili ba ne don matar auren ka ta ce ba ta son zama da kai, zai sa ka sake ta. Kamata ya yi ka ja hankalin ta, ka wa’azantar da ita tare da nuna illar sakin. Na san saki hala ne, amma ya na jerin halal din da Allah Ba ya so.”
Sadi ya ce, “Shi ya sa Ya halarta din, domin wasu lokutan, ya kan zama dole ne, gudun kar a takura wa wani ko a zalunce shi. So, ta je gaba kawai, kila rabon ta ya na can ne.”
Hadi ya nisa. Shi kadai ya san abin da yake ciki. Yusuf ya ce, “It’s not too late, ba mu makara ba. Za mu iya mayar da ita, mu ba ta hakuri.’’
Sadi ya dan dofane a jikin tebur din ofis din, “Dan auta, sarari kan ka, ka ji yadda ka fi zakewa, alhali ka san gaskiyar komai. Na san za ku ga kamar ban damu da halin da Hadi yake ciki bane nake fadin hakan. Amma na ga kamar ba zai yiwu a hana wa Kausar wannan damar ba, don son zuciya. Mu yi fatan Allah Ya sa hakan shi ya fi alheri.’’
Hadi ya kalle su duka, sannan y ace, “Na riga na yi mata alkawarin ba zan yi kokarin mayar da ita ba. Balle ma na samu suna shirin kai ta Legas, wurin da za ta zauna da wata kanwar ta da a ka yi tiyatar haiuwa a can.’’
Sadi ya ce, “Ni fa na ce its alright, hakan daidai ne. Kai dai ka yi hakuri, ka ci gaba da addu’a. Sannan ka yi kokarin dawowa da rayuwar ka kamar na da. Ai da ba ta nan ka rayu, ko?”
“Zan yi kokarin amma ba daya ba ne da rayuwata a da, kafin na aure ta. Ba zan taba dawowa kamar da ba.’’
“Kar ka raina addu’a abokina. Ka mika komai ga Allah, za ka samu mafita.”
Ya kalli Yusuf, “Dan auta, ina gaya dai mu ba shi day off don ya je ya seta kan sa. Aikin tiyartar sa a daga zuwa gobe ko jibi. Da ma shi na zo tuna ma sa, na samu wannan damuwar.’’
“Kar ku daga. Zan iya yi.”
Duka suka kalle shi cikin tababa. Sadi ya tambaye shi, “Ka tabbata? Wata kila baka kasance cikin yanayin da zai baka natsuwar hakan ba.”
Ya gyada kansa, sannan ya mike tsaye, “Ni likita ne, kwararre. Matsala marasa lafiya su ne a gabana, kafin na saka nawa. So, mu je, zan iya.’’
STORY CONTINUES BELOW
Da wannan Hadin da Sadi suka fice, suka bar Yusuf. Tsawon wannan rana ya yi ta ne cikin tunani. Gaba daya jikin sa ya yi sanyi dalilin wannan sakin, don kuwa a iya sanin sa, Hadi na zaune ne da matansa lafiya, kuma babu wanda ya taba jin kansu. Amma a ce hakan ya faru? Gajan hakuri ne ko ma rashin sa? Tun da a kan haihuwa ne, bai kamata a ce su dan kara jira ko za su samu nan gab aba? Me ya sa Kausar ba ta zama kamar Suhaima ba wacce ke tare da Hadi tuntuni?
Shin matar sa za ta iya guje ma sa nan da wasu shekaru kan dalilin rashin haihuwa? Shi ba ma matsalar rashin haihuwar ba ce. Matsalar babu abin da ya taba hada su ne da ita, balle ma a san wata matsalar.
Ya nisa. Canjin shawara ya zama tilas. Dole ya yi kokarin jan hankalin Asiya ta zauna da shi, ba don komai ba, sai don ta raya aure, da farin ciki mahaifiyar sa, wacce ta dora fata a kan auren sa.
Abu mafi muhimanci kuwa, don ya na son matar sa, ba ya jin zai iya rabuwa da ita. Ya na son Asiya…so na hakika.
10
* * *
Falo ne da ba ya da girma sosai, don haka duk tagogin hudun da ke cikin sa a bude ne, an daga labulayen su, sannan kofar an wangale ta don sukunin wadan da ke zaune cikin sa, kasancewar yanayin zafin da a ke ciki.
Asiya ta daga kai ta kalli Yusuf karo na uku, amma ba ya ko dagowa ya kalle ta. Kan sa a sunkuye balle ta gane halin da ya ke ciki. Tun fitar su daga gida haka ya ke. Ita kan ta ba ta iya fassara yadda ta ke ji ba. Komai na rayuwar ta ya raja’a bisa hukuncin da za a yanke a yau din nan. Yanzun nan. Cikin falon nan.
Ta mayar da hankalin ta kan matar da a ke kira Yafendo. A yau surarta ta fito sosai a bayyane. Mace ce mai hasken fata amma ba can ba. Ta na da kaurin jiki, da tsawon fuska. Idanun ta madaidaita ne, amma ta na da karan hanci a tsaye. Ta na da kyau ba don a ce shekaru sun fara cimmata ba, don kuwa ta girmi Umma nesa ba kusa ba.
Asiya ta sake kallon Umma wacce ke zaune a gefan ta.Babu abin da take yi face lazimi da carbin ta a hankali.Fuskar ta a natse take, amma kuma fayau ce ba alamar komai.
“Ina son ku saurare ni da kyau, ku ji jawabin da zan yi, dukan ku.’’
Duka suka mayar da hankulan su kan wanda ya yi furucin nan, wanda su ke kira Baba Mai keke. Kanin mahaifin su Yusuf ne, shakikin sa. Sauran jama’ar da ke falon su ne Alhaji Dalhatu, aminin Baban Yusuf kuma babban alkali a kotun shari’ar musulunci da ke garin Bauchi, sai kuma wasu kannen mahaifin na su, Alhaji Musa, da Gwaggo Baana.
Akwai ma’aikacin kotu guda wanda ke rubuta bayanan da a ke yi don bugawa a raba wa kowa bayan an tashi, kamar yadda alkalin ya umurta. Sai kuma shi kan sa Khalid da wasu kannen sa, da daya matar baban su da kuma yayan ta hudu, cikin su har da Sara.
Baba Mai keke ya ci gaba da cewa, “Wato mun nemi a zo nan ne domin a sasanta magana cikin natsuwa da fahimtar juna. In dai a kan wannan maganar ce zancen kotu ma bai taso ba. Don kuwa da Alhaji Rabe na da rai, ba zai so hakan ba. Don haka zan ba da fili ma kowanne cikin ku ya zayyana korafin sa, in ya so Alhaji Dalhatu ya warware mana zare da abawa.’’
Bayan kowa ya fadi irin na sa, Alhaji Dalhatu yayi grarar murya, “Ahh, mu na neman tsari daga shaidan, mu na kuma mika jagorancin mu ga Allah madaukakin Sarki, Buwayi gagara misali.
“Ba tare da na bata lokacin kowa ba, zan je kai tsaye zuwa ga matsalar mu,wacce ta tara mu a yau. Matsala ce game da wasiyar da margayi Alhaji Haruna ya bari na cewa akwai gida a Abuja da kuma filin da ke GRA a nan Bauchi, wanda za a ba da jikan farko na tsatson sa. Ah, hakika,wannan fili da gida suna nan kamar yadda Dan auta ya shaida min tare da binciken da ni kaina na gudanar a kan su.
Wato ina son jan hankalin mu ne zuwa ga manufar wasiyya, da kuma yadda a ke yin ta a addinin musulunci. Wasiyya ta kunshi umarni ne kan dukiyar wani ko wata ya bar wa wani na sa, wala alla ko don ya kyautata wa wancan din, ko kuma don tausaya ma sa, musamman idan wanda a ka yi wa kyautar ba ya da gadon wanda ya yi ta, gudun kar ya fada wani mawuyacin hali idan ya mutu.
STORY CONTINUES BELOW
“Ahhh, a kan bi umarnin wasiyya ne muddin dukiyar da aka yi wasiyyar da it aba ta haura kashi daya cikin ukun dukiyar da mamaci ya bari ba. Idan ta haura, to za a watsar da maganar wasiyyar gaba daya, gudun kar magada su takura.
A kan wannan maganar da mu ke yi, ina son na kara jan hankulan mu kan bayanan da Dan auta da Lauyan sa suka tattara ma na.
“Ahh, tun da mun fahimci mene ne wasiyya, za mu dawo ga bayanin mu na farko. Ala hakika, an samu jikan farko a gidan nan, wanda ta tsatson Khalid ta fito, da halartacce ga Alhaji Haruna. An samu cika sharadi na farko. Amma akwai matsaloli guda biyu, wand azan zayyana su a yanzun nan ba tare da bata lokaci ba.
Farko dai, an ja hankalin kotu zuwa ga cewa Alhaji Haruna ya jinginar da dukiyar da yayi wasiyyar da ita, da ma wasu kadarorin sa, ya karbi basussukan da bai biya ba har ya koma ga Ubangiji. Abin da ya fi dacewa kafin a raba gado ko aiwatar da wasiyya, shi ne a biya basussukan da ke kan mamaci. Domin babban nauyi ne a kan sa, wanda ba zai bari ya kwanta cikin kabari a sukuni ba.
“Wajibi ne sai an sauke nauyin bas hi, kafin a kai ga rabo. Ina mai sanar da ku cewar Yusuf Dan auta ya tabbatar min da ya biya fiye da kasha casa’in na bashin da ya dauka, har ma ya karbi wasu daga cikin takardun.
A halin yanzu, kotu za ta yi amfani da bayanan kan takardu don yi wa wadannan kadarori kudi, sannan a ga ta yadda wasiyyar nan za ta shigo.”
Alkali ya fidda takardu, sannan ya sa a ka raba kwafe kwafe wa duk wanda ke zauren, har Asiya ma, wadda ba ta san abin da za ta yi da it aba. Ya ci gaba da cewa, “Bayan an karbi gidan Maitama da ke Abuja da kuma filayen da ke nan Bauchi, wadan da biyu suke GRA, dayan kuma a Zango; an hada jimmillan kudaden su gaba daya zuwa miliyan dari daya da ashirin da takwas, wanda ya kasance dukiyar magada. Akwai kuma gidajen da ke Jabi, Mabushi da Kubwa, wadanda jimmillan kudaden su suka kai miliyan dari hudu da sha biyar. Su ba a karbe su ba ne, shi yasa ban saka lissafi da su ba.
“Zan je ga karshen abin da ya tara mu. Alal hakika, wasiyya zata tabbata, don kudin gida da filin cikin ta bai haura kashi dayan ba. Duk da ba a biya bashi ba, zan sanar da mallakar ta don kawai a warware wannan takaddama da a ke cikin ta.
“Kasancewar diyar Khalid ce, ta cancanci mallakar miliyan dari da ashirin da hudu, kudin gida miliyan dari da ashirin, da na fili miliyan hudu, wanda shi Khalid zai mallake su a madadin ta.’’
Yafendo ta shiga washe baki, ta na hamdala, wai ‘yan bakin ciki sai su mutu, kuma dole a mallaka mata jikanyar ta.
“Sai dai akwai wani hanzari ba gudu.” Alkali ya ci gaba da bayani. Yanzu mun zo ga matsala ta biyu, wadda muhimmiya ce. Dukkan mu nan musulmai ne kuma kowa ya san abu halartacce, da wanda ya kasance na haram.
Wannan diya ta Khalid ce, amma hanyar da a ka yi a ka same ta bai halarta ba a musulinci. Don haka, ba za ta iya gadon Khalid, balle kakan ta. Don haka wannan dukiya za ta ci gaba da zama har zuwa lokacin da Allah Ya cika wa Alhaji burin wasiyar sa. Allah Shi ne Masani.” 2
Nan Yafendo ta zabura, “Ban gane ba. So ku ke ku ce ba za a ba da wannan kudi ba? To ina ruwan ku da hanyar da a ka same ta? Ku dai ba kun samu an ciki wannan sharadin wasiyyar ba? Ko ce mu ku a kayi ‘yar wani mu ka dauko mu ka mayar ta mu, kamar yadda wasu ke kokarin yi? To mu ba hankaka bane, mai da dan wani na ka.” 3
Yusuf ya kalli Yafendo kadan sannan ya girgiza kan sa a hankali. An samu fiye da mintoti arba’in ana jayayya da ita kan wannan mallaka, duk Malaman nan sun tsaya kan bakar su, ta hana wanna dukiya wa Khalid. Har ma Alkali ya ja ayoyin Al-Qur’an mai girma da Hadisan Manzo. Amma duk a banza.
Baba Mai keke ya ce, “Idan so ki ke a mallaka mi ki jikanyar ki, to sai a ba ki ita, amma ba za ki samu sisi ba. Ba nan ba duk wurin da ki ka je ba za ki samu nasara ba. Sai ko in ki na so, ba ki makara ba. Ki na iya yi wa dan ki aure ya haihu, sai ku mallaka. Nan ma sai kun riga kowa tukunna.”
STORY CONTINUES BELOW
Cikin bakin ciki ta tambaye su, “Wai shin, ce mu ku a ka yi Khalid bai auri yarinyar nan ba a lokacin shigar wannan cikin?”
Asiya ta kalle ta cikin tsoro da mamaki. Yau kan dukiya a na neman a mayar da haram ya koma halal. Ko sunan Mariya ma ba ta sani ba balle na Amatullah. Amma ta na yage wuya kan sai ta mallaki dukiya domin su.
A lokacin ne Yusuf ya yi magana, “A lokacin da labarin wannan cikin ya same mu an riga an saka kwanan auren Mariya, wato mahaifiyar Amatullah da wani.
Har ma na nemi ta hakura ta janye da yin auren har sai mun warware matsalar da ta samu, amma mahaifiyar su ta ki amincewa. Don haka, bayan ta haihu ne iyayen tsohon mijin ta su ka sa ya sake ta, a bisa zargin ta aure shi ne alhalin ta na dauke juna biyu na wani daban.”
Yafendo ta dage, “To da a lokacin ka sanar damu, ai da an gwada ma ka yadda ainihin komai ya ke a fili. Amma sai ka yi shiru don munafurci.” Ta murguda mu su baki cikin tsiwa. 2
Yusuf ya mayar da martani, “Ban munafurci kowa ba. Don kuwa a lokacin na tunkari Khalid kan maganar, amma ya gwada ba bu ruwan sa da maganar. Ni kuma ban rike Ama don son zuciya ba. Na yi ne don rufa asirin gidan mu.”
“Wani asiri za ka rufa? Ai tun da Alhaji ya auro uwar ka ba bu wani rufin asirin da ya rage a gidan nan.”
Alhaji Dalhatu ya yi sauri ya ce, “A’a, ba abin da ya kawo mu ba ke nan Hajiya Ramatu. Mun zo ne game da gado da wasiyya, wanda mu ka ce ba bu shi a tsakanin yarinya da kakan ta, har abada.”
Ta katse shi, “Ai wannan ba gado ba ne wasiyya ce, wacce ko waye ya cancanta. Tilas a ba mu tun da hakkin jaririyar Khalid ce. In ya so ya yi yadda ya ga dama. Na tabbata da Alhaji cewa ya yi a kai a marayu a basu ba sai an tsaya binciken asalin su, za a ba su.”
Baba Mai keke ya ce, “Mu bamu shakkar kasancewar ta diyar Khalid a gidan nan. Haifar ta da a ka yi babu aure, ita ce matsala. Dukkan mu mun san cewa Alhaji Rabe ba zai taba karbar diyar da a ka Haifa ba a kan sunnah ba. Ke da kika daura wa dan ki aure alhali mu na raye ba mu sani ba, ki na iya daukaka kara a ko ina. Ki yi abin da ki ke ganin zai ficce ki.”
Ta rusa guda tare da tafa hannaye, sannan ta tabe baki, ta ce, “Jika dai ta gidan nan ce duk yadda ku ka juya. Ina ruwan ku da auren sat un da ba ku kuka ma sa ba? Dole ku ba mu dukiyar nan, tun da shi Alhajin bai rubuta hanyar da ta wajaba ba ta wajen hanyar samu jika. Ko kuwa ya yi?”
Alhaii Musa ya tsoma bakin sa karo na farko tun zaman sa cikin zauren, ya ce, “Ba ma son shashanci, wai rook a gidan kurma, kin ji ko? Kar ki mayar da mu mahaukata mana, kuma mutanen banza. Ke me yasa baki zauna gaban iyayen ki ba ki ka haifi ‘ya’yan naki a yawon baraki? Sai yanzu don abin duniya za ki jefa yaro cikin halaka? Ki na neman halatta abin da Allah Ya nemi a kyamace shi? 2
“Zancen wasiyya kuma, mun yarda Yaya bai fayyace ba ko samun jika da aure ko babu amma kowa ya yi tunani da kwanyar sa ya san daidai. Ko akwai mai son jika ta hanyar haram ne? To mu ba za mu bi son zuciyar ki ba. Ke har wani abin alfahari ne ki na buga kirji dan ki ya aika ta zina? Ko tunanin halin da uwar jikanyar taki ta shiga ba ba kya yi? Ke dai kawai a ba ki dukiya.?”
Cikin halin ko-in-kula, ta amsa, “To ni kuma me zan iya game da wannan? Ni na kore ta, ko kuma laifi nane don ta shiga duniya?”
“Laifin dan ki ne, da ya jefa ta cikin halin da ta shiga har ya sa ta gudu.”
“Ah…to, abin da ya faru ya wuce ai dan ba nawa bane ni kadai, don ya aikata laifi sai a like min shi a jiki na?” 1
Duka suka kura mata idanu, su na girgiza kan su cikin takaici da mamaki. Baba Mai keke ne ya iya cewa, “Mun san ba dan ki ba ne ke kadai, don haka mu ka taru a nan don neman gyara abin da rashin tarbiyyar sa ya bata. Ga alama ke ba ki damu a gyara ba. Ke kawai rungumar abin ki ka yi, ki na neman mu ma mu yi hakan.”
Ta ce, “To me ye aibin hakan? Canja abin da ya faru za ku yi? Ko kuma kun manta cewa yarda kaddara mai kyau ko marar kyau cikar imani ne? To ni ban manta ba.” 6
Alhaji Dalhatu ya ce, “A tunani na, duk cikin mun nan, ba bu wanda ki ka fi shi sannin Qur’an ko Hadisi…” 2
Ta katse shi da cewa, “Ba zan ce zan yi gasar hada sani da ku ba. Kawai ku ba mu hakkin mu, kowa ya huta.”
“Gwara da ki ka furta hakan, cewa mu ba jahilai ba ne. Zaman mu a nan don Allah ne, mun kuma san hakokin Sa a kawunan mu. Sannan mijin ki marigayi ma ya na da hakki a kan mu don ganin mu cire son zuciya mun mu yi adalci wa kan mu gudun kamun Allah. In ban da na zo gida ne da kai na, da sai na sa an wa Khalid bulala dari a gaban jama’a, domin aikata zina da ya yi.”
Yafendo ta mika hannun sa cikin sauri, ta ce, “A yi ma sa…wallahi a yi ma sa, amma a ba shi dukiyar ‘yar sa bayan an masa.” 9
Farkon zaman su a zauren har kawo wannan lokaci, Asiya mamaki hade da haushin Yafendo ta ke ji. Amma a yanzu tausayi ta fara bata. Son abin duniya ya rufe mata idanu, ko shiriyar dan ta ma bai dame ta ba.
Asiya ta kalli Khalid fiye da kirgawar ta. Ashe ba laifin sa ba ne don ya yi hakan wa Mariya. Ko ma wasu ‘yan mata kamar ta. Wata kila gare shi, daidai ya ke yi. Mahaifiyar sa ba ta so a dauki matakin gyara, sai ko neman kara zurma shi cikin halaka. A da ke nan ya yi hakan, balle ya samu dukiya ai sai godiya.
Alhaji Dalhatu ya ce, “To tun da kin amince hukunci Allah mu ka bi a nan, za ki fahimci dalilin da ya hana na mallaka masa wannan dukiya. Saboda haka, ya je ya ci gaba da istigfari, ya nema tuba a wajen Ubangijin sa. Ina kuma mai jan kunnen sa na game da sake aikata irin wannan laifi nan gaba a rayuwar sa.
Sannan ita wannan jaririyar da a ke maganar ta, a mallaka wa kakarta Hajiya Ramatu wato Yafendo. Dukiya kuma a ci gaba da adanar ta, har zuwa lokacin da Allah ya nufi cikar wasiyyar Alhaji Haruna Rabeh. Allah Ya jikan sa, Ya kara ma sa rahama. Da wannan na ke nufin rufe wannan taro” 2
Kowa ya amince da hakan, amma ban da Yafendo da ‘ya’yan ta, wandan da su ka yi alwashin kai wa gaba, don karbar hakkin su. Taro kuma ya waste, kowa ya kama gaban sa.Yusuf ya kalli Larai wacce fuskar ta ke nuna zakuwar ta na son ta je ta huta. Idan an duba ta na da gaskiyar ta. Ta ce da shi, “Ina ga ta kwanta ne fa. Don na dade ina bugawa amma ba ta amsa ba.” +
Yusuf ya gyada kan sa, ba don ya amince da hasashen Larai ba ne, sai don ya kyale ta ta je ta huta ita din. “Shi ke nan, je ki yi aikin. Zan dauka daga nan.”
Ta yi ma sa godiya sannan ta koma bangaren da a ka ware mata daki cikin sa, ta lume shiru. Ya kura wa kofar dakin Asiya idanu wanda ke rufe gam. Kwanaki biyu ke nan da dawowa daga taron su. Shi da ita ba su zauna na minti biyar tare ba. Hasali ma tun daren jiya, rabon sa da ganin ta.
Ya mike tsaye ya shige dakin sa. Ya san abin da ya dace ya yi. Dole a yau ya gana da ita, don kuwa ya san ba kwanciya barci ta yi ba. Wane irin barci ne za ta fara da karfe takwas na dare?
2
Ya shiga dakin sa ya nufi kofofi biyun da ke hannun riga da juna. Guda daya na shiga bandakin sa ne, guda kuwa, kai tsaye zai shiga bangaren saka kaya na dakin Asiya, wato closet. Bai taba amfani da kofar ba, don kuwa damar yin hakan ba ta samu gare shi ba. Ya tuno da irin jayayyar da ya yi da Sadi a lokacin da ya bayar da shawarar fasa kofa a wajen.
A cewar Sadi, kyaunta shi da matar sa su rika shiga da fita ba tare da sun fito falo ba. Wai hakan ‘Romantic’ ne. Yusuf bai ga romantic a nan ba. Ya dai amince ne a wancan lokaci don Sadi ya kyale shi. Har a yanzun ma bai gani ba. Tukunna. 8
A kasa ya iske Asiya, bayan ya shiga dakin ta. Ya yi mata sallama. Ta dago fuskar ta wanda ke manne da gwiwar ta, idanun cike da tsoro da fargaba, da mamaki. Ta na kallon sa tamkar kunnuwar sa sun yi girma fiye da tsawon sa, ya tsiro da kaho da fuka fukai.
Cikin tsananin kaduwa, ta tambaye shi, “Ta ina ka shigo?!”
Ya dan yi murmushi sannan ya zauna a gaban ta, a kasan, ya amsa, “Ta kofa.”
“Ta ya ya a ka yi hakan bayan na kulle kofar?” Ta kura wa kofar dakin idanu, sannan shi.
Ganin fargaban ta ya sa shi neman hanyar da zai kawo ma ta sassauci, ya ce, “Idan Allah Ya sa a ka rufe ma ka kofa, sai Ya bude maka wata kofar daban.”
Ta sake kallon kofar dakin ta, har lokacin makullin sa ya na sakale da shi. Ya gyara muryar sa ya ce, “Kwantar da hankalin ki, akwai kofar da ta hada daki na da naki ta closet. Ta nan na shigo, don kuwa na turo Larai ta kira ki har sau hudu, amma kin ki amsawa balle ki fito. Shin a ganin ki, hakan ne zai kawo mana masalaha ko me?”
A wannan lokaci ne ya ga rudani da kaduwa sun gushe daga idanun ta, kunci da bacin rai suka mai da gurbin su. Ta kife fuskar ta sannan ta nisa, “Ban amsa ba ne…” ta dago ta kalle shi, “…don ban san abin da zance ba. Kwakwalwa ta a birkice take, zuciya ta a cikin rudani. Ban san ta yadda zan fara ba.”
Ya kara tausaya mata ganin irin kuncin dake cikin su da rauni. Kiris ya rage ya ja ta zuwa jikin sa har sai wannan kunci ya gushe. Amma yin hakan ba zai taimake su a ba a lokacin. Ya ce, “Shi ne ki ka boye kan ki? A ganin ki yin hakan ya fi?”
“Addu’a na ke yi domin neman Jagoraci da Yardar Allah na. Duk abin da Ya zaba min zan karba da hanu bi-biyu.”
Ya sauke muryar sa sosai, “Amatullah ba mutuwa ta yi ba.”
Ta kawar da kan ta daga fuskar sa, ta ce, “Na sani. Amma gobe za ta tafi wajen kakar ta.”
Ya hadiye yawu amma makogwaron sa a bushe ya ke. Tun da Mariya ta haifi Amatullah bai taba rabuwa da ita ba, ko da na awa guda ne. Nan ma sai ko in aiki ne ya nisantar da shi daga gare ta.
Ya tuna ranar da ya mata huduba, da irin sadaukarwar da ya yi domin ta. Amma a ce wai za a raba shi da ita? Ya san dai tilas Asiya ta ji zafin rabuwar su, amma bai kamata ta ga kamar rabuwar ba zata dame shi ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ya nisa, tare da mikewa tsaye, ya ce da ita, “Idan a tunanin ki, barin Amatullah gidan nan ke kadai ya shafa ban da ni da Umma, to ban san abin da zan ce da ke ba.
Don haka, ki ci gaba da tunanin ki, ki kuma aiwatar da duk abin da zuciyar ki ta raya mi ki. Na yarda da kaddara, na yarda Allah Shi ke hana ka, Ya kuma baka duk lokacin da Ya so. Na yarda da jarabawar da ya sauko min, ina kuma rokon Sa da Ya nufe ni da ci.”
Da wannan ya koma wurin da ya fito. Babu amfanin zuwan sa dakin ta, koma ya nemi maslaha. Asiya har yanzu ba ta amince da matsayin sa na mijin ta ba. Shi kuma ba zai tilasta ma ta ba.
Da gaske ya ke, ta aiwatar da tunanin zuciyar ta in hakan zai kawo ma ta sukuni. Ya amince da kaddara, ya yarda da hukuncin Allah a kan sa. Don kuwa ya san Allah ba ya dora wa bawa abin da ya fi karfin sa.
A lokacin ya shirya wa zuciyar sa juriya mai tsanani, juriyar rashin Amatullah. Da kuma juriya ma fi girman da zai taba fuskanta a rayuwar sa; rashin matar sa, abar kaunar sa, ko ta san da hakan, ko ba ta sani ba… 2
* * *
Asiya ta na ganin ya bar dakin, amma kamar wacce a ka manne da gam. Bakin ta a bude ne ta na yunkurin kiran sunan sa, amma muryar ta a makale ta ke. A hankali ta ji saukar hawayen bisa kuncin ta.
Ta ina za ta jefa kan ta? Da gaske ta ke yi, ba ta san madafa ba. Shin ya ya za ta yi? Zuciyar ta sai bugu ta ke da karfi. Yanzu me ye abin yi? Don kuwa ya zama tilas ta ba shi hakuri. Ta san ya yi sadaukarwa kan don rike Amatullah, an fi karfin sa ne kawai.
Ta ja gwauron numfashi ta fidda iska ta bakin ta sosai. Zama haka ba zai taimaka ma ta ba, balle nutsar da kan ta cikin kogin tunani. Hankalin ta ya kai ga kofar da ta hada dakunan su, kofar da ya shiga wajen ta ta ita, wadda za ta kai ta zuwa nasa dakin.
Ba tare da bata lokaci ba, ta shiga bandakin ta ta wanke fuskar ta fes, sannan ta je bakin wannan kofar ta tsaya tana kallon ta, na lokaci mai tsawo.
Tun zuwan ta dakin ranar da a ka kai ta, Muhibbat ta damu da son sanin ko kofar ta mece ce. A lokacin a kulle ta ke, don haka suka watsar da binciken su. Tsawon zaman ta ta cike hankalin ta kan Amatullah. Ba ta taba kawo war anta kofa ce da za ta kai ta ko in aba. Ba ta damu da sanin abin da ke daya bangaren bangon ba.
Ta shiga mahawara a zuciyar ta. Shin ya dace ta shiga yanzu ne, ko kuwa bari za ta yi sai da safe ta yi ma sa magana? Wa ya ga gobe? Ta kwabi kan ta.
Idan har ta bari sai gobe ba lallai ba ne ta hadu da shi da safe. Sannan idan an karbi Amatullah maganar ba zata yi tasiri ko amfani ba. Hausawa sun ce da zafi a ke dukan karfe. Don haka komai ta fanjama, fanjam!
Ta kai hannun ta ta buga kofar. Da farko a hankali, daga baya da dan karfi har sau uku, tana yin hattara kar ta ja hankalin sauran mutanen gidan zuwa ga abin da suke ciki . Shiru ba amsa.
Gaban ta sai dungure ya ke yi. Ko dai ya yi fushi ne? Ta sake kwankwasawa. Nan ma shiru. Ta ja numfashi, wata zuciyar na raya mata kanta koma dakinta kawai. Wata kila ma ya sake kulle kofar. Ko ma ya kwanta barci. Don haka bata lokacin ta kawai take yi.
Za dai ta shiga, wata zuciyar ta fada ma ta. A halin yanzu da Ama za ta bar su, ya zama dole ta san matsayin ta. Daya daga cikin dalilan da su ka sa ta rike kauce wa hanyar sa ke nan a kwanaki biyun da suka gabata. A yanzu ya zama dole su yi magana a kai.
Ta sa hannu ta murda, kofar a bude ta ke. Ta sa kai tare da sallama a hankali, gaban ta na ba da dudum! Dudum!! Dakin babu haske sosai, sai na fitilar gefen gado. Hakan ya ba da haske mai saka mutum ya ji sukuni cikin zuciya.
Sanyin iyakwandishan hade da kamshi su ka fara mata lale. Kafin idanun ta su ka sauka kan abubuwan da ke ciki. Makeke ne, ya fi na ta girma. Ya na kunshe da gado irin na ta na kasar waje, wato Royal bed, amma na sa baki ne.
STORY CONTINUES BELOW
Wadurof din gadon ya na bangare daban, hade da madubi. A wani gefe guda tebur ne da kujera, an zuba takardu a kan sa. Akwai laptop komfuta ta na ajiye a gefen takardun.
Akwai talabijin babba na bango a like, ya na kunne da tashar labarai ta turawa. Sai gefe guda da ke dauke da takalman sa gari guda, duk kuma ma su tsada. Manyan tagogi ke fuskantar juna sun sha labule ma su kyau da tsari.
Bayan ta gama kallo ne ta nisa. Zuciyar ta ta ci gaba da gudu da sauri. Ba ta taba shiga dakin sa ba, a tsawon watanni hudu da sati daya da su ka wuce, sai a yau. Dakin ya na nuni da yanayin sa da halayyar sa ta natsuwa da kima, da dabi’ar sa ta son tsafta.
Ta yanke shawarar komawa dakin ta, tun da ba ta gan shi ba ciki. Wata kila fita ya yi ta daya kofar. Shi yasa bai amsa sallamar ta ta ba. Har za ta juya ta ji motsin bude kofa. Ta yi tsmmanin shi ne, ya na yunkurin shiga dakin ta hanyar falo.
Shi din ne amma ba ta kofar falo ba ne, ta wata kofar ce daban, wacce tsabar kyaunta, ba ta yi zaton kofa ba ce tun farko. Idanun ta da nasa suka hade. Nan take gabanta yayi dam! Numfashin ta ya nemi yankewa cikin huhun ta, a yayin da rudani ya sauka mata.
Yusuf ya na tsaye ne kusa da kofar, daga shi sai dogon wando. Ya nufo wajen da ta ke, alamar mamaki a idanun sa. Ita kuwa ta zama wata kankara a girke waje guda. Sai da ya tsaya gaban ta, tukunna ta lura mamakin ya kau, ya mayar da fuskar sa fayau.
A wannan lokaci Asiya ba ta san ko numfashi ta ke yi, ko ma iska ta na fita da shiga kirjin ta ba. Da kyar ta yi kokarin tsayar da idanun ta kan fuskar sa, ba kirjin sa ba, wurin da ke bayyana faffadan kafadar sa da ma cikar halittar sa. Ta dade da sanin ya na da wadan nan, amma ba ta taba ganin sa ba bu riga ba. Ba ta ma taba ganin wani namiji a hakan ba. 2
Sun samu wasu dakika ba bu wanda ya yi magana. Karshe shi ya ce, “Bata ki ka yi ne? Dakin ki na ta arewa ne.”
Numfashin sa yayi dab da fuskar ta, sannan ya sakar ma ta murmushi. Ta kara fadawa cikin rudani. Ta daure, ta ce, “Da ma… wajen ka na zo… kuma na yi sallama ne ban ji kowa ba…sai…na…sai…na shiga… ban san… zan koma kawai sai wani lokaci.”
Yusuf ya fadada murmushin sa. Hakan ya kara masa kyau. Wayyo Allah! Zuciyar ta ta shiga harbawa kamar za ta faso kirjin ta. Har gani ta ke yi idan ya lura da kyau, zai iya ganin ta ta kayan da ke jikin ta. Nan take ta dan kame jikin ta da hannayen ta. Doguwar rig ace a ta saka, amma sai ta na jin kamar ba ta saka komai ba.
Ya ce, “Relax, wasa nake mi ki. Shigo ciki mana sosai ki zauna.”
Ya na gama furta hakan ya juya ya nufi wadurof din sa, ya bude ya fidda riga, ya shiga sakawa. Ya sake kallon ta, a lokacin ya na saka botul din shat din sa, ya ce, “Bismillah, ga bakin gado nan, ki zauna ma na. Kar ki damu, ba na cizo. ”
Kan ta ya koma kasa, ba ta zaunan ba. Ba ta ma motsi. Shi kuwa yi ya ke kamar sun saba da yin hakan ne a kullum. Ya matsa kusa da ita, ya mamaita, “Na ce ki zauna a bakin gado don na tabbata ko ma me ya kawo ki, ba zai kyau ki fade shi a tsaye ba.”
Ta hadiye yawu da kyar, sannan don kar ta nuna ma sa ya na shafar ta sosai, sai ta nufi gefen gadon, ta dan dofane a zaune. Ji ta ke yi kamar ta zauna ne cikin kankara. Jikin ta bari shiga yi, a hankali.
Yusuf ya ja kujerar da ke girke gaban teburin rubutun sa, zuwa bakin gadon sa ya zauna. Ya kale ta sosai, fuskar sa da dan murmushi, ya tambaye ta, “Kin tabbata kin zauna?” Ta kalle shi sannan ta gyada ma sa kan ta. Ya ci gaba da cewa, “Kar fa ki fadi kasa.” 2
Kusan murya a shake, ta ce, “Na zauna, ba bu damuwa.”
Ya daga kafadar sa ya sauke, ya ce, “To, in kin ce haka. Ina Amatullah? har yanzu ta na wajen Umman ne?”
STORY CONTINUES BELOW
Nan take zuciyar ta ta koma wannan layin tunanin. Amatullah. Abin da dama ya kai ta gaban sa ke nan. Kuma abin da ta ke bukata ke nan don ta rage zogin da zuciyar ta ke yi a halin da a ke ciki.
“Eh. Umma ta bukaci ta kwana a wajen ta.” Ta kusan ciza harshen ta. Me ya sa ta fadi hakan? Ai sai ya dauka ko ta shiga dakin na sa da wa ta manufa ce cikin zuciyar ta.
Ta dan gyara zaman ta kadan ta shiga murza yatsun hannayen ta da na kafa. Hakan yak an faru ne idan ta shiga cikin taraddadi. Ta daure, ta ce “Da ma a kan ta na zo, don na baka hakuri.”
Ta sunkuyar da kan ta kasa, ta ci gaba da cewa, “Don Allah ka yi hakuri. Sam ban yi tunanin da ya kamace ni ba. Na fi kowa sanin irin sadaukarwar da ka yi, da irin kulawar da ka ke yi wa Amatullah, wan da ba kowa ne zai iya yin hakan ba. Sai ga shi na dauki son kai na saka a farko, ba tare da yin la’akari da yadda kai ko Umma za ku ji ba.”
Idanun ta suka dan ciko da kwalla. A gaskiya tunanin kan ta kawai ta yi ta yi. Yadda bayan an raba ta da Ama rayuwar ta a gidan Yusuf za ta kasance. Shin zai nemi su rabu ne, ko kuma zai ci gaba da rike ta? Idan ya rike ta, alhali akwai wacce ya ke kauna, ta kuma mallake zuciyar sa, me za ta zama? Fifa ‘ya-koma-baya?
Yusuf ya dan nisa, ya ce, “Ban taba kawo zargin ki na son kan ki na saka a zuciya ta ba. Ina ganin ni na fi kowa son kai cikin wannan al’amari, idan a ka yi la’akari da hanyar auren mu. Ni na tsara, na yanke komai don cikon buri na, ba tare da na damu da na ki burin ba.”
Ta yi saurin katse shi, “Ka yi la’akari mana, har ma fa gurbin karatun gaba da sakandare ka nema min. Hakika ka cika alkawarin ka.”
Ya nisa, sannan y ace, “A gaskiya, na yi amfani ne da hakan don na jawo hankalin ki, ki amince. A bisa gaskiya, ba kowa ba ce zon samu ta amince ta zamo uwar jaririya a dare daya ba. Ko da na samu ma da zarar ta shigo gidan, za ta watsar da ita, ta shiga bin son zuciyar ta. Amma sam ba ki gaza ba don wajen kulawa da Ama. Ko Mariya ce ma ba za ta yi abin da ya wuce yadda ki ke yi ba.”
Duk da cewa bata sake sosai ba, kan ta kamar ya fashe don dadi. Tun da bai ga gazawar ta ba to hakan ya wadace ta. Shi yasa ta ke jin takaicin rabuwar ta da Ama. Don kuwa ta san da Mariya ce ba za ta taba yarda ta rabu da ita ba…
A mafarkin ta ba! In ce Mariyar ce ta tsallake Amatullah, ta shiga uwa duniya? Me zai sa ta ganin cewa za ta kaunace tamkar ita ta haife ta, alhalin uwar ta ta watsar da ita ta yi? Me yasa ta ke ganin kulle kan ta zai canja komai?
Ta dan yi murmushin da bai wuce hakoran ta ba, ta ce, “Hmm, na so ne na rike ta, na nuna mata nau’in son da ya kamata, sabanin wanda mahaifiyar ta ta nuna ma ta.”
Sai da ta ji cikin bakin ta ya cike da yawu mai daci. Babu yadda za ta yi ta haihu, sannan ta jefar da yarinya ta shiga duniya. Shin Mariya ta na tunanin Ama kuwa a duk yadda take a halin yanzu? Ta na nadamar abin da ta yi kuwa? Hakan zai sa ta juyo ta dawo, ko kuwa za ta ci gaba da son zuciyar ta ne?
Yusuf ya ce, “Ko wane Dan Adam da irin halittar da Allah Ya yi ma sa da kuma baiwa. Haka zalika, Allah kan turo ma kowa jarabawar da Ya ga dama. Mu cikin ta mu ke, ke, ni, Mariya…. don haka kar ki zargi Mariya ko kadan don ta nuna rauni fiye da jarumta. Kar ki kasance mai hukunta wani kan halayyar sa. Ki bari, Allah ne mai kowa mai komai. Shi Ya san daidai.”
Ta kalle shi ta na cike da mamaki, “Shin ba ka ji haushin abin da Maree ta yi? Ba ka fushi da abin da ta yi wa Amatullah?”
Ya amsa, “Ban so abin da ta yi ba. Amma ban rike ta a zuciya ta ba. Na san duk wurin da ta ke, zuciyar ta na tunanin Amatullah. Don kuwa abu ne mawuyaci mace ta haifi da sannan ta shiga duniya. Wata rana za ta waiwayo nan don Amatullah. Shi ya sa na ke son ta samu kulawa sosai kafin Allah ya kai mu lokacin.”
In har ta na raye a lokacin, Asiya ta fadi a zuciyar ta. Ko ma Amatullah din ba ta mutu ba. Ga shi gobe za a raba su na har abada. Ta ji zuciyar ta ya kara yin daci.
Ta nisa. Murya kasa-kasa, ta tambayi kan ta, fiye da shi, “Ya ya rayuwar Amatullah za ta kasance idan har ta girma ta san yadda ta zo duniya?” ba ta san su Yafendo kamar yadda ya san sub a. amma a bias alama, ba za su yi sanyi wajen jifar Amatullah da muggan kalamai ba bayan ta koma wurin su. Ji t ke yi har ta mutu ba za a daina kiran ta shegiya ba a gidan.
Shi ma ya nisa, sannan ya dan duka, fuskar sa ta yi kusa da ita, ya ce, “Bai dace mu yi wannan tunani ba, don abin da Allah Ya ba mu ikon yin sa, shi mu ka yi a yanzu. Ni da ke ba za mu hana ta bakin ciki ba idan Allah Ya sa ta girma. Sai dai zamu iya sassauta ma ta shi, ta hanyar ba ta so da kauna, mu kuma kula da ita na musamman.”
Ta ce, “Haka ne. Domin kaddara ta riga fata.”
“Exactly. Hakan yak e.”
Nan kuma ta sake jin takurar idanun sa a kan ta. Zuciyar ta da hanjin ta sun cakude su na yamutsi, kwakwalwar ta ta sake fadawa rudani. Idanun sa kyam a kan ta, baya ko kiftawa. Kyawawan idanun sa.
Ita ma ta kalle su, ta rika jin wani haske na fita daga gare su, ya na tabo can cikin ruhin ta. Numfashin ta ya yanke, ya na fita da kyar. Gwara ta fita, tun bata narke ba. 5
“Dare ya yi… zan je na kwanta.” Ta mike tsaye.
Idanun sa cike da tambaya, “Karfe tara da rabin?”
“Eh, zan kwanta ne, domin zan tashi da wuri gobe idan Allah Ya kai ran mu. Sannan ba mamaki cikin dare a kira ka a asibiti.”
5
Daga nan ta yi masa sallama ta koma zuwa dakin ta. Nan ta shiga jin kadaici tamkar ita kadai ce cikin gidan. Ba Amatullah… sannan babu Yusuf. Ya ya za ta yi? Ba kuma wai tambayar yadda za ta yin a daren ranar ba ne. na tsawon rayuwar ta ta ke nufi.
Ko dai sallar nafila za ta fara tun daga yanzu? Ko kuma karatun Qur’ani? Karshe ta kwanta kan gadon ta, karo na farko ta yi ta mirginawa, ta na tunanin Yusuf da irin kyaun surar sa, da ma murmushin sa… mai tsananin tsima ta Dokta Yusuf Haruna ya shiga gidansa cikin sauri, zuciyar sa da idanun sa sun kagu da son ganin matar sa. Da ma Amatullah, diyar da kotun da ta mallaka ma sa; ko kuma ta mallaka wa Asiya. 5
Yusuf bai zauna ba kwana daya rak, bayan hukuncin da Malam Dalhatu ya yanke a zauren su, har sai da ya ja hankalin iyayen sa a kan raba ta da Amatullah. Ya yi nuni da yadda addini musulunci ya tsara a kan cewar idan babu mahaifiyar jaririya, to za a samu ma fi kusa da ita, wato ko mahaifiyar uwar ta, wato kakar wajen uwa, ko kanwa ko yayar ta ta jini. Idan an duba babu, to shine sai a koma kan kakar wajen uba.
Yafendo ta ja da hakan, ta na nuna cewa ai tun da shayar da ita nono a ke yi ba, to ita ma za ta iya ba ta. Sai da kotu ta binciki yadda za su rike ta, ma’ana wajen suturar ta, wajen kwana da kuma sayen irin abincin da ya kamata su rika ba ta idan sun karbe ta.
Da farko dai Khalid ba ya da sana’a ko aikin yi. Don haka ba zai iya kulawa da jaririya ba. A karshe dai bias dole, a ka bar wa Asiya rikon diyar ta. A yanzu komai yayi dai dai a tsakanin su. A kalla, kusan komai……
Ko da shigar sa, kai tsaye ya wuce dankin ta, wajen da ya same ta zaune bakin gadon ta.
Shigar ta ta doguwar rigar atamfa (fitted gown) ta karbe ta. Kan ta babu dankwali, sumar kan ta a daure ya ke, baki wuluk sai sheki ya ke yi. Fatar jikin ta ta kara haske, sannan fararen idanun ta sun inganta kyaun ta. Ba kwalliyar tashin hankali ta ke yi ba, amma wadda ta ke yi, ba karamin fidda kyaunta ya ke yi ba.
Ta mike tsaye, a kunyace ta ce,“Sannu da dawowa.”
Sai da ya hadiye yawu da kyar, jin muryar ta sassanya da kuma ganin surar ta mai shagaltar da shi. Ya matsa kusa da ita, ya lura ta shiga rudani, kamar ranar da ta fara shiga dakin sa. Sai da ya tsaya a gaban ta ya tuno da yadda numfashin ta ya rika hawa da sauka a kirjin ta a rannan, da yadda kamshin ta ke ratsawa cikin kwanyar sa. Ta sauke idanun ta cikin jin kunya. Hakan ba karamin tsima shi ya ke yi ba. 2
“Yau sati guda ke nan rabon da na tsaya mu gaisa da ke sosai. Ko ma dai na san halin da ki ke ciki.”
Ta dan dago kadan ta kalle shi, sannan ta saki murmushi, hakoran ta su na burge shi, ta ce, “Yanayin aikin ka ne ya sa hakan. Kuma har ga Allah b aka bar mu cikin kunci ko matsala ba. Haka ma Amatullah.” Ta dan kara sunkuyar da kan ta, ta dora da, “Kuma ta yi kewar ka.” 3
Muryar ta da kadan ta fi rada. Ya tabbata ba ta san yadda hakan ke s aka shi ji ba. Ya saki ‘yar murmushi shi ma, wanda ya tabbatar zai iya aika ma ta kadan daga cikin halin da zuciyar sa ke ciki, “You have no idea, ba ki san yadda na yi kewa ba…” Ya dan kara matsawa dab da ita, sannan ya sauke muryar sa sosai, “Kewar dukan ku biyu.
Ya lura ta kara sunkuyar da kan ta. Shauki ya kara kama shi. Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na dawo yau da wuri, na samu off na sauran yau gaba daya.”
A lokacin karfe uku ne, da ya kalli agogon san a hannu. “So, dama ina ta son kewaya cikin gari, and I was wondering, ko zan samu ‘yar rakiya?”
Ta dan kalle shi kadan, “Kewaya? Yanzu? Na ga yanzu ka dawo.” Ta tambaya. 1
Ya yi murmushi, “Na sani. “Na yi la’akari ne da cewar tun da ki ka shigo nan gidan ban taba kai ki ko ina ba. Ki shirya kawai bayan sallar la’asar sai mu je.”
Ita ma ta yi murmushi, “Bari na shirya Amatullah, in ya so sai mu same ka a falo.” Muryar ta da zumudi.
“Actually, wannan fitar ba tare da Amatullah za mu yi ba. Daga ni ne kawai sai ke. More like, kamar fita date ne, tsakanin abokai biyu. Hakan zai kara ba mu damar fahimtar juna a matsayin haka.” 1
STORY CONTINUES BELOW
Nan ya sake ganin rudani a idanun ta. Me ta ke fada cikin zuciyar ta? Ya san dai ya na bukatar dama da lokaci tare da matar sa. Kuma gwara ya fara tun bai makara ba.
Ganin dai ba ta ce komai ba, sai ya dauki Amatullah, ya ce,“To bari na kai Ama wajen Umma. Sai na gaishe ta, kafin nan kin shirya.” Ya fita zuwa sabon bangaren Ummah, wanda tun kafin auren sa ta tare zuwa wajen. Ba zai saurari wani abu daga wajen ta ba.
Ya dade su na maganar magungunan Ummah na hawan jini, ta na masa mitar ba ta jin dadi maganin. Shi kuma ya yi alkawarin canja ma ta da wassu. A hakan Asiya ta same su.
Ummah ta nemi ta zauna, sannan ta kalle su tare, ta ce, “Da ma na dade ina son yi mu ku magana dangane da halin da a ke ciki. Ba na son ku daga hankulan ku. Na san Hajiya Ramatu za ta sake bullo da wani abin da zai fi wanda ta yi a yanzu. Ko a ce ma ba ta fito da shi ba, Mariya za ta iya bayyana a ko yaushe. Don haka, na ke son ku mayar da hankali wajen samun na ku na kan ku. Na san Allah ne Ya ke bayar wa, don haka ne ma na dukufa wajen rokon Sa, da Ya ba ku. Da zarar kun fara samun ‘yan dugui-dugui za ku ji saukin komai. Fata na dai Allah Ya kawo masu albarka. Ko ni ma zan samu wadan da zan rika rankwashin su.” 1
A wannan lokaci bai damu da sharadin da Asiya ta gindaya a tsakanin su ba. Shi dai ya san har ga Allah zuciyar sa ta sosu, ya ji son ‘ya’ya ya mamaye shi. Ko don ma ya cika wa Ummah burin ta. Ya fahimci cewa Asiya ta gagara daga kan ta. Ya san kunya ce ke damun ta.. ko kuma haushi? Za ta so haihuwa da shi kuwa?
Su ka dan yi dariya, Yusuf bai san abin da ta ke tunani ba. Ya ce Amin, ita ma ta furta amin din da kyar. Daga nan suka bar ma ta Amatullah suka fita.
Karo na farko suka shiga mota tare tun bayan auren su. Ko zuwa kai Amatullah riga-kafin da ta ke yi asibiti tare da Bature direba su ke zuwa. A yanzu zaman ta ya tunasar da ita ranar komawar su Dagauda tare, da irin gwagwarmayar da suka sha tare.
Babban kantin Jifatu Super Stores suka je, wurin da ya dage kan saya ma ta kayayyaki da dama, duk da dagewar da ta yin a cewar ba ta bukatar komai don na lefen ta ma ba ta taba wasu ba. Sun saya wa Amatullah riguna iri iri da turarrukan yara kanana, sabon gadon kwanciyar ta da sauran tarkacen da suka kunshi motar yara, keke, lilo da kayan wasa daban daban.
Daga nan ya kai ta Skycrown Bakery, don zaben abin da take so na dangin fulawa dai iskirin. Ta na zaba ta saka kan faranti, ta kai kan cookies masu shigen biskit, ta dauke su cikin ledar su ta kalla da kyau, sannan ta mayar ta ajiye. 6
“Ki dauka ma na. ki dauki duk abin da ki ke so.”
Ta girgiza kanta, “Wannan abin bay a da dadi.”
“To ai baki gwada cin sa ba, balle ki gane. Ta na iya yiwuwa ki so shi.”
“Na taba gwada cin sa sau daya, tun ina gida. Sai na rika jin sa kamar kitse ne nake taunawa.”
Cikin mamaki ya ce, “A can gida, Dagauda?”
“Eh. A duk lokacin da Rabi’u ya je waje na, sai ya cika min ledodi da ire-iren wadan nan. Ko ya kai mun, yara na ke tarawa na raba mu su.”
A lokacin ya ji tamkar kibiya ta soki zuciyar sa ya tambaye ta, “Rabi’u?”
Ta gyada ma sa kai, “Eh, Rabi’u Gwammaja. Wai idan na kushe abin ‘yan birni a lokacin sai ya rika cewa ni ‘yar baba ce.”
Tooo! Wato ashe akwai wanda ta rike tunanin sa a zuciyar ta? Rabi’u. To ko shi ne dalilin da ya hana ta sakewa da shi ko ma ta kaunace shi? Ko waye shi?
“I see.” Amma bai gani ba. 4
Ta ci gaba da zaben sauran har suka kai ga mota. Ya kasa hakuri, sai da ya tambaye ta, “Me ya sa baki taba ambaton sunan sa ba?”
STORY CONTINUES BELOW
Ta kalle shi da kyau, fuskarta na nuna alamar tambaya, “Wa? Rabi’u? Zancen ne bai taba fadowa ba. Kuma ban yi tunanin akwai damuwa ba idan na yi yanzun.”
Damuwa? Kwarai kuwa akwai damuwa. Sunan damuwar shi ne Rabi’u. Ya san dai kafin ya aure ta, ba ta ambaci cewa ba a kai gaisuwar aure gidan su game da ita ba. Amma bai ta ba tunanin wani zai zauna cikin zuciyar ta har zuwa lokacin ba. Tilas ya nemi sanin ba jiran ta Rabi’un ya zauna yi ba, don in haka ne, to zai dade ya na jira.
“Kawai. Ban taba sanin akwai wani kamar hakan ba ne a rayuwar ki?”
Ta saki murmushi mai taushin gaske, ta ce, “Akwai mana, amma a da. Tun gabanin auren mu ban ji duriyar sa ba, har ranar yau din nan.”
Wani irin sanyi a tabo zuciyar sa. Ashe dai Rabi’un ya zama tarihi ne gare ta. Baya da abin da zai ba shi tsoro ashe.
Bayan sun kamalla da nan ne su ka nufi Haisan, wani kawataccen wurin sayar da abinci ne da kayan nama, wanda matasa da sauran jama’a ke hallara. A lokacin yamma ta yi lis, don haka, ciki da waje cike ya ke da jama’a. 4
Ya nemi ta zauna daya daga cikin kujerun da suke shirye, shi kuma ya je yi mu su odar abin da za su ci. A cewar sa, zai mu su takeaway don ba sai ta yi abinci ba.
Bayan ya ba da odar sa, sai ya koma ya zauna a gefen ta, cike da nishadi da jin dadi. Wasu ‘yan tsiraru suka gan shi, suka je suka gaisa. Ya na amsawa a takaice, don kuwa wannan fitar musamman don Asiya ya yi ta. Zai kuma ba ta dukkan lokacin sa.
Odar su ta shinkafa da naman kaji. A wani bangaren ta hangi mutane na layin sayen abu. Ta tsaya kallon su, ta nu na alamar jin mamaki, “Ni wai me wadan can ke layin saye ne kamar gugguru?”
Ya yi murmushi, “Ko ki na sha’awa ne?”
Ta dan kalle shi, “Cimar yaran? Mu a kauyen mu yara ke ci. Manya ba sa kulawa.”
Ya dan yi dariya, ganin yadda ta saki jikin ta da shi. Wata kila don fita wajen da su ka yi ne, ko kuma yanayin wurin mai kyau da tsari a gewaye da furanni. Ko ma me ye, ya na son ganin wannan Asiyar, idan da hali, kullum na tsawon abada.
“To ai nan ba kauyen ku ba ne. Nan manya da yara duka su na ci. Bari dai na saya mi ki guda, ki ci ki ji irin na mu.”
Ya saya ma ta guda daya, ta dandana, sannan ta ce, “Lallai gugguru ya samu mukami. Har fa da madara.” Ta fada ne a hankali, amma ya na iya jin ta. 5
Ya ce, “Da ga yanzu dai kin dawo yarinya.”
Ta dan yi dariya, zuciyar sa ta zogi ainun. Ya kura ma ta idanu. Bai taba ganin dariyar ta ba. Ba irin wannan mai armashin ba, mai cike da farin ciki zalla. Ta yi kyau. Ta yi masifar kyau. Hakoran ta suka kara bayyana, idanun ta su ka yi kyalli.
Ya kasa daure zuciyar sa, “You are very beautiful. Dariyar ki tana da kyau.” Dukanin ta ma ta yi kyau. Abaya ta saka a kan riga da siket din atamfa da ta canja kafin fitar su. Tun fitar su ya gagara dauke idanun sa daga kan ta sai ya zama dole.
Ta dan kalle shi kadan. Kunya ce ya hango cikin idanun ta? Ta ce da shi “Bai kai naka ba.”
Ya dan yi dariyar, “Allah? Ai da na san haka, da kullum zan rika yi.”
Ta ja takeaway na abincin da suka saya, kamar ta yi wata Katanga tsakanin su, ta sunkuyar da kan ta a kai. “To, daga yanzu na kayyade maka; biyu da safe, biyu da rana, biyu da yamma.”
Ya fashe da dariya, sosai. Ta fara komawa yanayin ta na jin nauyin sa. Ba ya son hakan. Ya ce, “Ba kya da dama. Yaushe ki ka zama likita?”
Ta amsa, “Makwabcin mai kanwa ai ba ya rasa burbushi.” 2
STORY CONTINUES BELOW
“Iye?! Ashe dai ke din bahaushiya ce.”
Ta kara sunkuyar da kan ta, ta hada har da rufe fuskar ta da hannu, “A’a, ni guddiri ce. Rigima na yi.”
A lokacin wata mata da mijin ta su ka zo teburin da ke gefen su ta yamma, tare da ‘ya’yan su uku. Babbar mace ce, ta sha adon kaya da kuma na gashin kai. Fara ce sol, kamar baban ta, kuma ba za ta wuce shekara hudu ba.
Sai ‘yan biyu, mace da namiji. Sun fi kowannen su ba da sha’awa. Mijin ya gaida Yusuf, sannan ya shiga fama da su kan su zauna, zai je ya odar mu su abin da su ke so. Ganin irin karfin su da gagarar su, su ka sa Yusuf murmushi, tare da jin sha’awar su.
Ba shi kadai ba ne ya kamu, don sai ya ji Asiya ta ce, “Dubi babbar yarinyar can, yadda ta yi kyau. Har ta bani sha’awa, kamar na dauke ta na gudu.”
Idanun ta da muryar ta suna nuna. Sha’awa biyu suka damki zuciyar sa, ta son ya haifi yara, sannan kuma matar sa.
Ya ce, “Ni, actually, ‘yan biyun sun fi ban i sha’awa. Kyaun ta a ce Ama ta samu kanne irin su.”
Ta kalle shi, fuskar ta dauke da mamaki, “Ka na nufin za a samu wadda za ta haifi ‘yan biyu ta jefar?” 2
Kan sa ya daure, “ban ga ne ba.”
“To ina ne zaka samo ‘yan biyu wa Amatullah?”
Abin ya ba shi dariya. Da gaske ta ke yi kan furucin ta. Ya ce, “Ina a ke samun ‘ya’ya?”
Ta dan tsaya nazari, ta amsa, “Asibiti ma na, ko gidan marayu.”
Yayi murmushi mai fadi, ya ce, “Akwai hanya ta uku, wadda ba ki fade ta ba. Hanyar da babu yan sanda, ko kotu, ko takardar gwamnati. Hanya ce da ta kunshi mutum biyu…”
A lokacin ya kai hannun sa ya ja nata, ya rungume su a tafin hannun sa. Ya ji fargaba tare da ita, don sai da ta dan yi bari kadan. Idanun ta su ka bayyana mamaki kadan. Shi kuwa, ya sauke muryar sa sosai, ya ci gaba dacewa, “Ni da ke… sai Mahaliccin mu.” 14
A hankali ya ga rudani mai tsanani ya sauka a fuskarta. Daga bisani kuma kunya. Hannun ta ya sandare a lokaci guda kuma ya sake tamkar an cire mata jijiyoyin ta.
Bai san tunanin ta ba a lokacin. Amma ya san har ga Allah, ya fadi abin da ke zuciyar sa. Abin da ya rage, ya furta mata kalmar so da kauna. Wanda ba da dadewa ba zai yi wannan furucin. 1
* * *
A hanyar su ta komawa gida sun bi ta ne kusan a kuramce. Duk da Yusuf ya yi bakin kokarin sa na jawo hankalin ta zuwa ga wani abin daban, zuciyar ta ta ki barin bugu cikin sauri. Hantar ta ta ki barin yamutsi, kwakwalwar ta har yanzu a birkice ta ke.
“Ni da ke, sai Mahaliccinmu…”
Abin da ya furta ke nan. Ba ta son wannan tunani amma zuciyar ta maimaita mata ta ke yi, kwakwalwar ta na kara nu na ma ta yanayin zaman su na dazu, da yadda ya rike tafin hannayen ta, da irin kallon da ya yi ma ta, da irin muryar da ya yi mata magana da ita….
Ta karkade wannan tunani. A lokacin da ya yi maganar sha’awar ‘yan biyu, ba ta kawo komai a ran ta ba, sai ko watakila ya na nema ne ya sake kawo wasu yaran gare ta. Ashe manufar sa daban. Ko kadan ba ta taba kawo wa a ranta Yusuf zai yi tunanin haka ba. Ba wai haram ba ne.
Amma anya… da ita ya ke son haihuwa? Me ya sa ya ke son haka? Ko don furucin Umma ne kafin su fito, wanda ya yi tasiri a tunanin sa? Ko kawai ta kasance matar sa? Ko matsi ne wajen abokan hulda?
Tun kafin Ummah ta yi mu su magana dazu, ta sha nuna mata alamar son ganin jikokin ta. Ta kuma san hakan shi ma za ta nuna ma sa. Yin hakan ba laifi ba ne. Amma sharadin da su ka yi ne karfen kafa. Wannan karfen ya hada da rashin kaunar ta tun farko. Ita ma ba son shi take ba da farko, daga baya ne ta ji son sa ya shigeta a hankali. Duk da hakan, ba za ta sake ta yi abin da zai kawo ma ta nadama ba daga baya.
Ya tsaya a bakin shagon sayar da magani na AMB stores da ke titin Wambai, ya fita. Bayan lokaci kadan ya dawo dauke da magunguna a cikin‘yar ledar da ke hannun sa.
“Ummah ce ke mitar magungunan ta dazu. Shi ne na sayo ma ta wasu daban.”
Ya na magana amma bai tayar da motar ba. A lokacin an shiga kiraye-kirayen sallar magrib. Ya ta matsa dab da ita sosai, sannan a hankali cikin saukakken murya, ya ce da ita, “Asiya, idan mun koma gida akwai maganar da za mu yi, anjima.”
Wannan bugun zuciyar ya dawo, ya na neman ya dagargaza ma ta kirjin ta. Fuskar sa dab da nata, numfashin su suka hade. Idanun sa kuwa a kan ta, kirrr.
“Maganar me?” Ta daure, ta tambaya.
“Maganar da mu ka bar ta yanzun nan, a Haisan.”
Yanzu kam kirjinta ya wargaje, domin wani irin zogi ta ke ji a duk jikin ta. Wani radadi mai dadin gaske ya rungume zuciyar ta, ya mamaye ta. Ta na son tambayar sa dalili, amma ta fi son ya janye daga kusa da ita. Ko don kwakwalwar ta za ta iya tunani, har ma ta iya furta kalma ta bakin ta. Ta sunkuyar da kai kasa cikin tsananin kunya da ma rudani, ta ce, “To. Allah Ya kai mu.”
Ya dan yi jinkiri ya na kallon fuskar ta. “Amin”. Ya furta daga karshe. A lokacin ya tayar da motar, sannan su ka bar wajen.
Zuciyar Asiya babu abin da ta ke yi sai tunanin maganar su ta dazu, da kuma wacce za su yi in an jima. Me zai ce mata? Ita ma me za ta ce da shi?
Ya ya rayuwar su za ta kasance bayan yau din? Me zai faru a yau din? Ta tuna da alkawarin sa, ta kuma tabbatar zai cika shi. Shin ita din, zata bada kai bori ya hau kuwa?
Ta sake karkade wannan tunani amma ba ta yi nasara ba. Komai ya na faruwa ne cikin sauri, ta yadda kwanyar ta ba za ta iya nazarin komai a lokaci guda ba. Za ta yi sallar magrib, bayan nan ta samu zarafin tunani, kafin tattaunawar sun. Za ta ba shi kunne, ta ji abin da zai fada mata.
Kusan tare suka kai gidan da motar dokta hadi. Sun shiga harabar, suka tsaya lokaci guda.