KUDIRI
CHAPTER 7
Wannan bai yi ba.” +
Muhibbat ta nisa sosai, “Me ye aibun sa Minde?” Ta tambaya, hannun ta rike da riga dikin atamfa. Ta sha kwalliya kuma ta yi zanzan, dinkin zamani daga likitan kaya, Jibayor da ke kasuwar central da ke Bauchi. Sanin kwarewar say a sa amare da ma wadan da ba amaren ba ke kai ma sa kayan su ya fere mu su dinkuna na gani a fada.
Asiya ta gyara zaman ta, ta na nazarin rigar, “Ba bu. Sai dai kyaun atamfa, in za a kai ki gidan ki ne. Don haka ki daura wancan leshi mai launin shunayya (purple). Zai fi fitar da ke.”
A ranar an saka walimar auren Dokta Hadi da Muhibbat. Auren kan sa sai washe gari za a daura.
Muhibbat ta daga leshin da Asiya ke magana a kai ta duba. Dinki ne fitted, kuma ta gwada ya karbe ta ainun, ta ce, “Kin fa san walima kawai zan yi, ba wani luncheon ba.”
“Ai a na sakawa. After dress kawai za ki dora a kai, ko ki yafa babban laffaya. Abu mai sauki!”
Muhibbat ta zauna a bakin gado, ta na fuskantar Asiya. Ta kai hannun ta ta dora a kan ta, ta na shafawa, “Wayyo Allah! Wannan abu duk ya ishe ni. Rabo na da barci na fi sati, ba na yin sa sosai. Ba na can, ba na nan, kamar zan balle biyu.” Muryar ta cike da gajiya da takaici.
Asiya ta yi dariya tare da tausaya ma ta, don ta san yadda ta ke ji. Shirin aure abu ne gagarumi. Duk da cewar ba ta ji hakan a na ta ba, ta yi na Mariya ta dandana, don kusan komai na shirin tare su ka yi shi.
“Wannan duk mai sauki ne.” In ji Asiya.
Muhibbat ta harare ta, “Ba ki ji abin da na ce ba ne?”
Asiya ta fadada murmushin ta, “Za fa ki auri mutumin da ki ke so ne. Shi ma kuma ya na son ki. Me ya fi hakan dadi?”
Muhibbat ta nisa, ta saki murmushi, “Kin san Allah Minde, ko tunanin sa ma ba na yi a halin yanzu. Don abubuwa sun min yawa. Ni ce karbar dinki, ni ce shirya walima, ni ce yin lalle, ni ce mai taron jama’a. Shi kuwa ya na can, hankalin sa a kwance.”
Asiya ta kyalkyale da dariya, “Amarya ke nan. Ai kowa ke ya ke sha’awar gani. Wa zai damu da sha’anin ango? Balle na tabbata, aikin da ya ke yi a yanzu ya na yi ne don ya samu damar cin amarci da kyau.”
“Dalla ja daga nan!”Muhibbat ta daga hannun ta, ta sauke kamar mai kade sauro, “Sai ka ce wannan ne auren sa na farko?”
“Hhmm, amma ke auren ki ne farko, ko da ba ke ce matar sa ta fari ko ma ke ce kadai ba. Dole ya yi yadda zai yi don ya tabbatar kin samu natsuwa da kwanciyar hankali. Balle ma in dai namiji ne ko kara mata sau dari zai na aure sai ya yi karkarwa nan da rawan jiki.”
Muhibbat ta kalle ta, fuska cike da zolaya, “Iye! Su Laminde manya. An yi kwas.Yanzu na zama dalibar ki ko?”
Asiya ta yi ‘yar dariya, “Ke dai bar wannan. In dai zaman gidan Dokta Hadi ne nice gaba zan dawo dalibar ki.”
Ta yi yunkurin tashi. Muhibbat ta dakatar da ita, “Me ki ke shirin yi?”
“Tashi zan yi mu gama zaben kayan, in ya so sai na duba wajen zaman walimar da a ka shirya a waje.”
“Don Allah rufa min asiri. Da wannan tukeken cikin naki ki je wani abu ya same ki mijin ki yakama ni. Da ma da ya ya ya bar ki zuwa bikin nan?”
Asiya ta ce, “Ai shi ya ce na rika motsa jiki na, ina dan juya wa.”
“Hakan da kyau. Amma ki motsa a gidan sa, ba a nan ba. Ke kin ga mutum kamar zai hadiye ki? Tabdi! Wace ni?”
Asiya ta yi dariya. Sanin kan ta ne irin kulawar da Yusuf ke gwada ma ta tare da kauna, mata da yawa sai dai su yi mafarkin sa. Ba ya bari ta rika aiki sosai.
STORY CONTINUES BELOW
Idan kuma ya fita, to bayan kowane awa biyu zuwa uku zai neme ta a waya don jin lafiyar ta a yinin ranar. Har ma ta saba.In ba ta ji shi ba duk sai ta damu.
Kamar yadda yau tun wayewar gari ba ta ji shi ba.Ta nemi wayar sa amma ba ta shiga. Jikin ta ya bata babu kafiya.Amma ta san mijin ta, ta kuma yarda da shi. Ba ya rufe ma ta komai.
“Wace ce Asiya?”
Wata ‘yar uwar su ce Muhibba wacce ta zo biki Dagauda daga Kano ta shigo ta tambaya.
Gaban Asiya ya fadi. Duk garin Dagauda da ma wadan da su ka san ta, da Laminde su ka santa. Ba bu mai kiranta Asiya.
“Ga ta nan Gudidi.” Muhibbat ta amsa. “Me ya faru?”
Gudidi ta kalli Asiya cikin fara’a, “Oh, ashe ke ce? To wai ki je gida yanzu, Dada ta na neman ki.”
Hankalin Asiya ya koma gidan su. Me ya faru kuma? Ta na jin Muhibbat na tambayar ‘yar uwar ta ta ko waje ya kawo aiken? Amma ba ta tsaya sauraron amsar ba. Ta dauki gyalen ta ta yafa, ta kama hanyar fita.
A tsakar gida ta tarar da mahaifiyar Muhibbat, ta sanar da ita za ta je gida amsa kiran Dada, amma za ta koma nan ba da dadewa ba.
Da kyar ta kutsa cikin jama’ar da ke gidan, wadan da ke hayaniyar hidimar biki. Muhibbat na da dimbin ‘yan uwa maza da mata kuma duk sun hallara. Ita dama mai son zumunci ce, ta kuma gata a wannan lokacin. Ko ina sai surutu ka ke ji. Gidan ba masaka tsinke.
Asiya ta na tafiya, ta na tunanin abin da zai sa Dada neman ta a lokacin, alhali ba ta dade da barin na su gidan ba. Sun ma yi da Dada cewar za ta kasance a gidan da zarar ta kammala da ayyukan gaban ta.
A can gidan su Asiya a ka yi hidimar abincin walimar yammacin ranar. Sai da Asiya ta tabbatar ba bu matsalar komai kafin ta bar gidan a dazu.To me ya faru? Zuciyar ta na bugu da sauri, ta nufi kofar gida.
Yusuf ta hango, ya na zaune kan motar sa. Fuskar sa ta na kallon wurin da za ta fito daga gidan su Muhibbat. Su ka hada idanu, ya sakar ma ta murmushi. Ta kara rude wa don mamaki da jin dadi. Shi fa ta yini nema ta way aba ta same shi ba.
Ta tambaye shi cikin kaduwa, “Dokta me ya faru?”
Ya bude ma ta kofar motar, ya sha murr, “Shiga mu je zan yi mi ki bayani a hanya.”
Ta shige cikin motar cikin damuwa da tashin hankali. Ji ta ke yi kamar ta zama tsuntsuwa zuwa wajen Dadar. Ga Yusuf kuma ya iso, fuskar sa a daure. Ya Allah! Me ya faru ne? ta na fatan dai ba gagarumar matsala ba ce.
Ta zauna cikin zumudi da hankoro, ta na jiran ya fara yi ma ta bayani bayan ya ja motar sun fara tafiya. Bai ce komai ba, hakurin ta na neman gazawa. Musamman ma da ta ga sun wuce kofar gidan na su.
“Ka wuce gida. Dada ce ke son gani na fa.”
Bai kalle ta ba, “Relax, Dada ba ta aika ki je ba.”
Kan ta ya daure, “Ba ta aika ba? Ban gane ba.”
Sai da ya kai wurin da ya yi niyya tukunna ya kalle ta. Masaukin baki ne wato Guest House, wanda wani ma’aikacin gwamnati da ke karamar Hukumar Misau ya gina a garin na su. 6
Nan a ka mayar masaukin baki, kuma nan Dokta ya kama don sauka. Su ka shiga cikin babban falon, mai dauke da rabin setin kujeru ma su kyau. Sannan akwai daki da bandakin sa a gefe.
“Ni na aika ki fito. Na yi amfani da sunan Dada ne don na mi ki ba-zata. So, surprise!”
Lallai ya ma ta ba-zatan. Amma ta tambaya, “Ka ga yadda ka tsinka min zuciya kuwa? Kuma yau tun safe na ke neman wayar ka, amma shiru b aka daga ba?” ta dan tsuke fuska.
STORY CONTINUES BELOW
Yayi murmushi, “Wanne ki ke so? Ganina a zahiri ko sauraron murya ta?”
A lokacin ya sukurkutar da muryar sa ce, mai watsa ma ta dadi a illahirin jikin ta.Ta ci gaba da kallon sa ita ma ta na murmushi. Sai a lokacin ta bar zuciyar ta yi ninkaya cikin kogin farin cikin ganin sa.
Ya sha farar jamfa sol, ga kamshin sa da ya yi mazauni cikin kwakwalwar ta. Yadda ya karkata hular sa a kan say a nuna cewa ya na cikin matukar nishadi. Ita ma ta ji farin cikin ya karu ma ta.
“Na dauka gobe ne z aka zo.”
Ya girgiza kan sa, “Ba zan iya ba. I can’t stay away from you for long. Na yi kewar ki already, shi ya san a gaza hakuri, na zo yau.” 3
Ta gagara cewa komai, sai dadin da ke bulbula daga zuciyar ta, ya na barazanar hallaka wa. 2
Da kyar ta iya magana, ta na yi ta na sunkuyar da kai cikin jin kunya. “Kwana biyar fa kawai na yi.”
“Kwanaki biyar…Asiya kamar abada na ji. Idan na shiga gida ba na jin motsin ki, ban a ganin kyakkyawar fuskar ki. Sannan kuma Umma ta gudo jiya ta bar ni. Gaba daya kadaici ya addabe ni jiya, na ga zan zauce idan ban yi ido hudu da ke bay au din nan. ”
Har a lokacin kunya ta hana ta kallon fuskar sa sosai. Ta ce, “Ni da zan koma Bauchi a gobe?”
“Na sani. Ba zan iya jira har jibin ba ne. Don haka tun safe fita na zuwa aiki na yi shirin zuwa nan.”
“Ya yi ma ka kyau. Shi ne ka razana ni da gangan. Da na suma fa?” Ta daure fuskar ta, ta samu waje ta zauna a falon ta zauna.
Shi ma ya zauna kusa da ita, ya na kokarin yin magana. Ba ta bas hi dam aba, ta mike tsaye tare matsawa nesa da shi. A hankali ya lalabo, ya saka hannun sa daga ta bayan ta ya rungume ta. Nan take jikin ta ya mutu, ta ji kafafuwan ta kamar su narke.
Ya kai bakin sa dab kunnen ta, ya kara saukar da muryar sa zuwa rada-rada, “Fushi kika yi? Ki yi min afuwa. Me zan yi don ki ji sanyi a zuciyar ki ki yi min afuwa? Wallahi na gagara jira har jibi ne, don ina kewar ki sosai.” Ya juya da ita ya shiga sumbatar ta, fuskar ta, wuyan ta, ya na ci gaba da cewa, “I have missed you so much, na yi kewar ki fiye da zaton ki. Ki yafe min, please. Zuciya ta ba za ta iya jure fushin ki ba.”
Ta shiga jin kanta na shawagi. Cikin wannan kan nata, a wani bangare akwai kwakwalwar ta. Amma ba ta iya amfani a lokacin. Rudani da radadin zogin son miijin ta sun toshe ta. A dole ta yi saranda, ta mika ma sa kan ta.
* * *
Yusuf ya jiwo muryar Asiya na waya da Muhibbat. Magana dai kawai su ke yi, irin ta sha’anin su mata.Ya fito daga wanka y na daure da tawul a daidai lokacin da ta ajiye wayar a kan madubi, wurin da ta ke kokarin kintsawa don komawa gidan su anjima.
Ya lura da kallon sa da ta yi ta madubi sannan kuma waigawar da ta yi ta sake kallon na sa. Ya san irin wannan kallon daga wajen ta. Ya kuma san abin da kallon ke haddasa ma sa a kwakwalwar sa, idan ta yi ma sa.Ya matsa zuwa gare ta, ita kuma ta mike ta na saka dan-kunnen ta.
“Muhibbat ta yi waya? Me ya faru?” Ta yi ma sa kallon da ya sa duk jinin jikin sa dumi, ya shiga jin tamkar ya ja ta zuwa jikin sa ya rungume ta. Daren jiya sun nu na wa junan su zallar so da kauna. Amma a halin yanzu jin sa ya ke tamkar ranar ya fara ganin ta. Zuciyar sa sai kara natsuwa ta ke yi da son ta.
“Mita ta yi. Wai ka hana ni zuwa walima da wuri jiya, sannan kuma da dare ka dauke ni zuwa nan.”
Yayi musmushi, “Kin san dai ba zan bari ki shiga cikin jama’a cikin halin da ki ke ba. Duk hayaniya da cikowa…gaskiya sai dai ta yi hakuri.”
Ita ma ta yi murmushi, “Ta na da zabi ne? Kuma kafin na manta, Hadi ya neme ka a waya. Haka dai ya fada min da ya min waya kafin Muhi. Ya na son jin yadda a ke ciki kan shirin da ku ka yi.”
Ya kalli wayar sa, amma bai dauka ba, “Ok. Zan nemi shi…”
Ta dan dubi lokaci a kan wayar ta. Karfe bakwai saura kwata. Ta ce, “Zan koma wajen su Dada, na san yanzu an yi nisa da abincin ma su zuwa daurin aure. Dole na kasance a wajen.”
Yusuf ya nisa. Bai son ta tafi, amma ya zama dole ne ya hakura.Ya dan ja ta zuwa jikin sa kadan, “Ina son ki san cewa dole ne ya sa za ki bar ni a yanzu. Zan yi kewarki.I will miss you.”
Ta dan sumbaci kumatun sa, “Ni ma haka.”Ta dan ja daga jikin sa ta nufi kofa, “Sai ka zo ke nan.”
Ya dan rike hannun ta bai sake da wuri ba. Ta juya suna kallon juna, ya ce, “Ki kirani nan da minti ashirin.”
“Me ya sa?”
“Kawai, don na ji muryar ki hankali na ya kwanta.”
Ta dan kalle shi, tare da nazari, amma ta amince, “An gama. Zan kira. Bari na tafi tun Muhbbat ta garzayo nan da kanta ba.”
Ya kyale ta ta fita zuwa motar sa,wurin da Habu zai kai ta har gidan su.Ya na jin dadin aiki da Habu, wani matashin da kan yi ma sa hidima a duk lokacin da ya je Dagauda. Kama daga share ma sa mota da goge ta, zuwa daukan kaya ya kai cikin gidan su Dada.
Ya kammala Difuloma a Jami’ar Bayero da ke Kano, amma ba bu aikin yi. Hankalin sa ne ya ja shi zuwa ga Yusuf, wanda a halin da a ke ciki, ya samar ma sa gurbin karatun digiri a fannin Hausa education a nan Jami’ar Bayeron. Da kan sa ya kawo ma sa takardar daukar.
Yusuf ya nemi Hadi a waya ya kuma tabbatar ma sa sun kamo hanyar zuwa Dagaudan tun da sassafe don daurin auren. Shi kuma ya shiga shiri bayan ya ajiye wayar don tarbar su. Da ma dimbin bakin da za su zo domin sa.
A zuciyar sa, ya yi wa Hadi murnar wannan aure. Don kuwa ya na cikin matsala mai girma. Ba wai na rashin haihuwar kadai ba. Har ma da rashin samun biyan bukatar aure daga wajen Suhaima. Ba ta amince ma sa wajen hada kwanciya.
Tun ya na shiru ya na shanye wa, har abu ya gagare shi. Ya shiga dauke-dauken matan banza a waje don su biya ma sa. Ko da Yusuf ya gano ba karamin batawa su ka yi da shi ba. Sai da Sadi da Kabir su ka dage wajen sasanta su tukunna. A iya tunanin sa, wannan ne kadai fada babba da su ka taba yi da juna tun farkon abotar su.
Hadi mutum ne mai hankali.Ya na da barkwanci, ga kuma kyautata wa. Amma ya dora matsalar rashin haihuwar sa a ransa. A gidan su sun kai tara; mazan su da matan su. Kowa ya na haihuwa amma ban da shi. Iyayen sa su ka hada auren sa da Kausar, amma daga baya ga yadda auren ya kasance.
Yusuf ya saka kaya a jikin sa,bay a son ya zurfafa tunanin sa cikin rayuwar auren Hadi. Malun-malun ya saka na shadda mai launin ruwan goro. Sai sheki ta ke, ta na dauke ido.
Ya na makala botul din riga, ya na mai fatan Allah Ya sa wannan aure na abokin na sa ya dore. Ba wai ya tsani Suhaima ba ne. Sai dai ya na son ganin abokin sa ya samu kwanciyar hankali da natsuwa. Kuma ga alama, wannan aure zai kawo ma sa biyan bukata.
Ya koma falon ya na daura agogo hannun sa, zuciyar sa na tunanin Asiya. Ta kai minti talatin da tafiya amma ba ta kira shi ba. Ba wai ya na tsammanin matsala ba ne.
Amma dai zuciyar sa za ta fi samun natsuwa idan ta kira shi din. Sauraron muryar ta ya fi dukkan sauti jin dadi da debe kewa. Kamar halin da ya ke ciki ke nan yanzu, na kewar ta.
Ya tarar da kayan karin kummallo, wanda ya san Asiyar sa ce za ta aika ma sa da su.Wainar gero ce da miyar ta tare da ferfesun naman rago da kuma dafaffiyar taliya mai danyen kifi ciki kaca-kaca. Ruwan zafi na cike da filas a gefen da kayan shayi su ke.
Yusuf ya yi murmushi. Zai so a ce tare su ka zauna ci kamar yadda suka saba. Amma tilas ya yi ta yi a kwanaki biyar din da ba sa tare. Ya zauna a kan kujerar falon, kamshin abincin ya cike ma sa kai da ma ko ina. Asiyar sa ta san cikin sa.Ta san abin da zuciyar sa ke so.
Habu ya yi sallama, “Yallabai, ka yi bakuwa…”
Yusuf ya kalli Habu, kwakwalwar sa ta shiga nazari ko wace ce. Amma kafin ya gane komai. Iyaka abin da ya sawwaka gare su ke nan, kafin wacce ta zo neman sa ta shiga falon da ya ke. Sai da ya kusa shakewa da wainar da ya ke kokarin hadiye wa lokacin da ta tsaya a gaban sa ta yi ma sa sallama. Nan take ya farfado daga kaduwar sa. Ta ya ya a ka yi ta san ya na wajen? Ya daure fuskar sa, ba bu alamar annuri ko kadan, ya ce, “Idan Asiya ki ka zo nema, ta na can gidan ku.” +
Mariya ta yi murmushi, “Na san da haka, don na ga shigar ta gidan. Wajen ka na zo musamman.”
Ba tare da bata lokaci ba ta zauna. Ganin hakan ya sa Habu ya ficewa don ya ba su wuri.
“Ban tuna lokacin da na ba ki damar zama ba.”
Idan ta ji tsoro ko shakka to ba ta nuna ba. Ba ta kuma yi yunkurin mikewa ba. Ga alama da abin da ta zo da shi, wanda bai kasance alheri ba.
Ya na ganin hannun su Yafendo cikin wannan ziyara na ta dumu-dumu. Lallai akwai matsala. Babba ma kuwa.
“Me ya kawo ki?” Muryar sa sanyi kalau mai kaushi. Ko za ta fahimci sakon sa, na ta fita ta ba shi wuri. Bai san dalili ba, komai na Mariya ba ya tattare da alheri. Bayan haihuwar Amatullah da ta yi, zai iya cewa rayuwar hasara ta ke ciki.
“Zuwa kawai na yi don na nuna ma ka godiya ta, bisa rikon amana da ka yi wa diya ta Mansura. Hakika hakan ya tabo zuciya ta matuka.”
Bai kula ba, jin cewar ta canja wa Amatullah suna zuwa ga Mansura. Ba ya son ya nuna ma ta har yanzu ya damu da rashin ta, ya na kuma bukatar ta zauna a matsayin ‘yar sa. Ko ma yadda kowa a gidan sa ya shiga wani hali don rashin ta.
Mariya ta fadada murmushin ta, “Na gode ma ka kwarai da gaske. Allah Ya ma ka sakayya ma fi girma.
Wani takaici mai hade da kulliti suka tokare ma sa wuya. In ban da wannan lokacin, bai taba zama kusa da Mariya sosai ba. Ranar farkon ganin ta kafin auren ta da ma bayan haihuwar ta duk a takaice ne babu natsuwa.
“A tunanin ki don ke na yi? Ai ke da Khalid ba ku kai na yi abu don ku ba. Na rike Amatullah ne don Allah, don kuma dukkanin ku, a matsayin iyayen ta kun gaza.
Idan kuma godiya ki ke son yi, to wa Asiya ya dace ki yi godiya. Ita ce ta cancanci yabo, domin ta sadaukar da rayuwar ta wajen ganin tabon da Amatullah ta zo da shi duniya bai shafe ta ba. Sannan ba ta guje ma ta ba, alhali uwar da ta haife ta ta yi hakan.”
Tun bayan haduwar su ta farko ya saka ta a jerin wadan da ke da son zuciyar su. Ta tabbatar ma sa da hakan bisa amincewar auren mijin ta na farko da ta yi, ta kuma kara tabbatar ma sa a lokacin da suka neme ta ba su gan ta ba.
Sannan ta dawo daga baya, ba tare da godiya ko nadama ba ta bukaci diyar ta. An ba ta, me ya kawo ta wurin sa kuma?
Ga alama maganar sa ta soki Mariya. Ta turbune fuska, “Eh to, ai don kudi ta yi hakan. Ka na tsammani ba don kudin da ka ke da su ba za ta amince ne?”
Ta soke shi a zuciya da furucin ta, amma bai yadda ta gane a fuskar sa ba. Mariya ce. Komai ta yi ba zai ba shi mamaki ba.
Ya ce, “Ban tuna lokacin da na yi tayin kudi wa Asiya don ta aureni ko ta kula da Amatullah ba. Hasali ma ba ta juya wa diyar ki baya ba. Ta gwammace ta fuskanci fushin mahaifin ku don Amatullah ta samu haske a rayuwar ta. Amma don rashin adalci irin na ki, za ki zo nan wajen ki zarge ta kan abin da ya kamata a ce kin ji kunyar fadar sa. 1
Idan kuma na yi la’akari da yadda ki ka dauki rayuwar ki, kunyar ce aba ma fi tsada gare ki. Ina son ki san har a nade kasa, ungulu ba za ta rama gayyar zabuwa ba. Abin da Asiya ta yi mi ki, ba za ki taba rama ma ta ba.”
Mariya ta tashi ta nufe shi, ta na ya yake hakoran ta, “Mu bar zancen kanwata.” Ta zauna a kan kujerar da ke gefen sa. Bai motsa ba. Ta ci gaba da cewa, “Na zo ne mu yi magana ta fahimta tsakanin mu.”
Ba ya son yadda sautin muryar ta ke fita. “Tsakanina da ke babu wata magana. Idan akwai abin da ki ke son tattaunawa a kai, ki fada wa Asiya, in ya so sai ta fada min.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta dan yi faar da idanu. A nan ta yi masa dibi da Asiya. Uwa daya uba daya su ke, amma komai na su daban ne. Kammanin su kusan daya ne, amma dabi’un su da halaye sun saba da juna. Asiya haske ce, ita kuma Mariya, bakin duhu.
Ta lankwasa muryar ta cikin ‘yar dariya, “Kar dai ka ce min tsoron ta ka ke ji? Kar ka damu, abin da zai faru a nan ba za a taba sani ba. Don ni ba zan fada wa kowa ba, hatta ita Asiyar ta ka.”Ta kashe ma sa idanu daya. 12
Yusuf ya fuskance ta sosai, zuciyar sa ta na kuna kamar ya rufe ta da duka ya rika ji. Ya shiga karanta Inna lillahi wa inna ilayhir-raji’n!
Mariya ba ta fi karfin sa ba. Sai dai bai san sharrin da za ta iya yi ma sa ba, wanda zai iya keta ma sa rigar mutuncin sa, tun da ita babu ita gare ta.
“Kar ki dauka ni mutum ne wanda zan aikata abin da zai hana ni fuskantar mata ta. Idan ki na tunanin zan ba ki kudi ne kamar yadda Khalid ya mi ki alkawarin karya; ko ma Yafendo ce ta turo ki, ba za ki samu ba.
“Ba kya da abin da za ki iya yi min Mariya. Don da Allah na dogara. Khalid ya yi kokarin tozarta suna na, Yafendo ta yi nata duk ba su yi nasara ba.”
Daga nan ya mike tsaye, ya dauki hular sa, ya dora bi sa kan say a fice ya ba ta wuri. Auren abokin sa ne a gaban sa.
Hakika wannan ziyara ta Mariya ta yi ma sa ba-zata. Bayan jijjiga shi da ta yi, dole ya ma ta iyaka da zuwa wurin da ya ke ko da nan gaba ne a rayuwa.
Ya san akwai alaka mai karfi tsakanin ta da matar sa,wadda ba zai iya yankewa ba. Don haka ne ma ya saurare ta.
Amma ya fi karfin a yi wasa da hankalin sa. Sun dauka idan su ka raba su da Amatullah za su haukace ne, su rika bin su suna rokon su mayar mu sui ta.
Sun kuma dauka da zarar sun karbe ta, kudi zai samu gare su. Nan ma sun ga wayam. Shi ne yanzu suka fito da wannan sabon salon.
Ya dan tsaya waige-waige, ko wata kila zai hangi Khalid. Ya na kyautata zaton tare su ke da Mariyar.
Ya duba agogon hannun sa, lokaci kara tafiya ya ke yi. Kuma kamar yadda ya sa a gaban sa, auren aminin sa ne, shakikin sa. Don haka ya ja motar sa zuwa cikin gari.
* * *
Asiya ta kira wayar Yusuf, amma ba ya dauka. Karo na hudu ke nan, ta fara jin tashin hankali, don hakan bai taba faruwa ba.
Idan har ta kira ba zai iya amsawa ba, to ya kan yi mata sakon waya, ya sanar da ita cewar zai kira, ko ma yana wani aiki ko taro ne.
Wannan daban ne, domin shi ne ya bukaci ta kira shi, sannan kuma ba ya dauka. Ta nisa. Ta san laifin ta ne, don ya bukaci ta kira shi ne baya minti ashirin, sai da a ka yi minti talatin da biyar sannan ta tuna.
Babu mamaki yayi ta jira har ran say a baci ne. shi yasa yake hora ta hakan. Don haka sai ta yanke shawarar yi ma sa sako, ta na mai ba shi hakuri da ma dai wasu kalaman da ta san za su faranta ma sa. Ta yi imanin da zarar ya gan su zai kira ta a lokacin.
Ta dan yi murmushi, ta na tunanin yadda tasirin kalaman za su kasance a zuciyar sa bayan ya karanta. Ba ta bata lokaci ba ta tura.
A ka tabbatar ma ta sakon ya shiga,sannan ta ajiye wayar ta na jiran amsar sa. Ta na kallon agogon kan wayar, karfe tara da kwata ya nuna mata. Da sauran lokacin da za a ce ba zai iya karanta wa ba.
“Duba ki gani ta nan Minde.” Muryar amarya Muhibbat ta kutsa cikin tunanin ta.
Shaf, ta manta ma suna tare ne a dakin. Ko da yake, Muhibbat din ta kebe ne cikin uwar daki, ta na gwada wasu dinkunan da zata yi amfani da su a walimar cin abincin da abokan ango su ka shirya a ranar da dare, amma a Bauchi ne.
STORY CONTINUES BELOW
Daga can kuma, ango ya yi tafiyar sa da amaryar sa. Ko dayake, sai bayan iyaye sun kai ta dakin ta tukunna a je liyafar.
Muhibbat ta na sanye cikin yadin material fari sol da ratsin ruwan hoda mai shar-shar, amma wanda a ka shafe ta cikin sa tsaf, a ka kuma fidda dinkin riga da siket mai tsarin gaske. Ya karbe ta, amma Asiya ta girgiza kan ta.
“Ya nuna asirin jikin ki da yawa. Ki gwada dayan, mai fari da bakin.”
Muhibbat ta wulkita idanun ta, “Na rantse, babu abin da ya kai zama amarya wahala.”
Asiya ta kyalkyale da dariya, “Sannu amarya. Aikin me kika yi tun safe?”
Muhibbat ta harare ta a lokacin da ta fidda daya kayan, “Aikin zuwa ma a ganni har fuska ta ta fara canja kala.”
Suka kyalkyale da dariya, “Ai kuwa dole a so ganin ki. Kin san an ce mutane uku ne suka fi farin jini a fadin duniyar nan: barawo, sabon jaririn da a ka haifa, sannan kuma sai amarya. Adana fuskar ki da kyau, don idan angonki ya gan ki sai ya suma.”
Muhibbat ta girgiza kan ta cikin murmushi, “Ke ko?” Ta mike tsaye, “Ba na da lokacin ki. Zan gwada wannan rigar mai launin ja din nan. Kin san My dear ya na son jan kala.”
Asiya ta gwalo idanu, “Iye?! My dear? Heeee! Har an canja ma sa suna daga Hadi zuwa My dear?”
Muhibbat ta ci gaba da gwada rigar da ta dauka, “Ban hana ki kiran na ki mijin da wani suna ba ai, ‘yar rainin hankali kawai.”
Ta tsaya a gaban Asiya, “To ya ya kika ga wannan?” Rigar da ta saka doguwa ce, ja mai ratsin ruwan gwal. Ta yi ma ta kyau sosai.
“Ina zan sani? Tun da kin san kalar da ‘My dear’ ya ke so shi ne ki ka wahalar da ni?”
Asiya ba ta bar dariya ba, ta na daga ma ta gira cikin zolaya.
Muhibbat ta girgiza kan ta, “Kin san kar a ce na yi azarbabi ne ai, irin ni miji dadi din nan.”
“Sai na kai ki kara, in ce ki na ta wahalar da ni har na tsawon awa biyu.”
“Kin san an bani damar hakan….tun da amarya ce ni.”
“Kin kusa zama ungwozoma kuwa idan ba ki bar bani wahala ba.”
Gaba daya Muhibbat ta rude, “Don Allah ki rufa min asiri, ki ba wa Dan-Baba hakuri. Na tuba, ya bari sai na mayar da ke wurin da na dauko ki sannan ya fito.”
Asiya ta kara gyara zaman ta, a yayin da ta ji abin da ke cikin ta ya dan motsa. ta kalli cikin na ta, “Lallai Muhi. Wa ya ce da ke namiji ne? Har da wani ba shi suna Dan-Baba.”
“Na san za ki saka ran cewa mace za ki haifa tun duk cikin yayyen ki Asabe ce kadai ta haifi namiji tilo. Amma ke kam in Allah Ya yarda, namiji za ki haifo mana.”
Asiya ta yi murmushi ba wai don ta fi son namiji a kan mace ba ne. Sai dai don ta san yadda rashin haihuwar namiji a gidan su ya mayar da mahaifiyar su baiwa. Ga yayyen ta mata ma har an fara cewa sun yi gadon Dada. Kamar hakan wani laifi ne da ba zai yafu ba.
“Kowanne Allah Ya bani ina so. Ni dai ina rokon Allah Ya sa mai lafiya ne, ya kuma zama mai jinkan iyaye.”
Muhibbat ta yi murmushi, “Amin Minde. Allah Ya raba lafiya, amma ba a nan ba don Allah.”
Asiya ta yi dariya, “Za ki ga laifin sa ne don ya na son fitowa ya ga anty amaryar sa?”
“Wuuu! To ya jira Baban sa, ko uncle ango tukunna. Wa yaga wujiga-wujiga! ”
Suka dan yi dariya. Asiya ta shafa kan cikin ta. A ranar da ta fara jin motsin dan ta wani irin yanayi ta tsinci kan ta ciki, wanda ba za ta iya kwatantawa ba.
STORY CONTINUES BELOW
Da farko zuciyar ta fayau, ta gagara tunanin komai. Daga baya da yayi sau biyu, uku, hudu, sai ta fara jin wani irin shauki ta musamman.
Loto-loto tunanin haihuwa yak an zo gare ta. Shin abin da za ta haifa zai zama mizanin kaunar mijin ta gare ta?
Wata zuciya ta sha gwada ma ta ba zai damu da jinsin abin da ta haifa ba, ganin yadda ya rike Amatullah. Amma dai abin yak an gifta a zuciyar ta.
“Za ki iya bani hankalin ki a nan, ki bar ogan ki?”
Asiya ta kalli Muhibbat cikin kunya. Rigar ta yi ma ta kyau matuka. Sai dai a gaskiya rabin hankalin ta bay a wajen ta. Tun bayan tura sakon da ta yi, minti goma ya yi, amma ba ta ji amsa ba.
Ta duba wayar har ta gaji.
“Ina tsammanin fushi ya yi da ni Muhi.” Ko da ta furta hakan, muryar ta ma tsoro ta ba ta. A ce Yusuf ya yi fushi da ita, ina za ta saka kan ta?
Muhibbat ta dan yi dariya, “Fushi dai? Don kawai ba ki kira shi da wuri ba sai ya yi fushi? A’a, ina ga dai kila ya tsaya tarbar baki ne.”
Ba mamaki Muhibbat gaskiya ta fada. Amma ba za ta iya jure zama ba tare da sanin halin da ya ke ciki ba. Shin ya ma ci abinin da ta aika ma sa kuwa?
Ta na bukatar natsuwa, don haka dole ta sake daukar wayar, ta sake kiran lambar. Wannan karon, ta yi sa’ar an dauka.
“Hello?”
Muryar mace ce ta kwararo ta cikin kunnuwan ta daga daya bangaren. Asiya ta ji kan ta ya daure. Ta kalli fuskar wayar ta sosai ta tabbatar dai lambar mijin ta ta buga, sannan ta sake mayar wa kunnen ta.
“Assalamu alaikum.”
“Wa alaikumus salam.”
Babu shakka muryar mace ce ta daya bangaren. Zuciyar Asiya ta shiga harbawa. Wata kila sha’anin layin hanyar ne, don ta sha jin a na cewa su kan yi hakan wasu lokuta. Za ta sake bugawa don ta ji.
Bayan ta katse ta sake bugawa, muryar macen ce ta sake amsawa. Muryar ma Asiya ta so ta gane mai ita, amma ta ture a bayan ran ta. Me zai kawo mai nuryar nan Dagauda?
“Halo Minde, mijin naki baya kusa ne. Ya shiga bandaki ya na wanka.”
Mamaki da fargaba suka kamata. Ta mike tsaye a yayin da numfashi yake neman yankewa cikin huhunta.
Tambayoyi fiye da dubu suka shiga kan ta a lokacin; me Maree ta ke yi da wayar mijin ta? Me take yi a masaukin sa?
“Maree? Me kike yi da wayar Dokta? Tambayar da ta iya furtawa ke nan, ta na jin karar bugun zuciyar ta.
Mariya ta yi jinkirin amsawa. Asiya kuwa ta ji tamkar shekara dubu ta yi ta na jira. Karshe ta amsa, “Bai fada mi ki ba ne? Ko da yake, ba zai fada ba, don bay a son wata kila hankalin ki ya tashi.” 2
“Bai fada min me ba?”
“Cewa shi ya ce na zo, a kan kin fita. Tun dazu mu ke tare da shi ai. Yanzu ne dai ya shiga bandaki ya bar ni a kan gado don yayi wanka. Kin san bakin su za su fara zuwa a wane lokaci.” 4
“Karya ki ke yi Maree!”
“Ai sai ki yi. Ban ce lallai ki yarda da ni ba. Ni dai na fada mi ki abin da yake faruwa ne, tun da naga kamar kin matsa da yin wayar.”
Jiri ya so ya dauke ta, Muhibbat ta yi sauri ta tallafe ta. Kafafuwan ta ba za su iya daukar ta ba sam. Ta ji kan ta na sarawa, zuciyar ta na zogi.
Bayan Muhibbat ta tallafa ma ta ta zauna, sai ta karbi wayar daga hannun ta, sannan ta saka a babbar murya, wato speaker.
“Maree, me kike ye?” Muryar Muhibbat na nuna tsananin bacin ran ta.
“Haba Muhi? Dokta Yusuf ne fa ya kirani don tattauanwa kan wata muhimmiyar magana. Na zo kuma sai a ga laifina? Idan ma ba ku yarda ba sai ku jira bayan ya fito daga wanka, ku tambaye shi.” 6
Daga nan ta katse wayar. Muhibbat ta ja tsaki, sannan ta sake buga lambar, amma ta ji a kasha gaba daya. “Zancen banza! Wannan duk shirin ta ne na ganin ta dasa mi ki fitina a cikin gidan ki. Wa ya san ma ko sace wayar ta yi?”
Zuciyar Asiya ta bijiro da tunani kala kala. Ta na iya yiwuwa Yusuf bai san da zuwan Maree ba. Amma yaya a kayi ta shiga har masaukin sa? Yaya a ka yi ta san ba ta nan din?
Muhibbat ta jijjiga ta, ta na neman jan hankalin ta, “A’a, a’a! Kalle ni nan Minde. Kar ki bari sharrin zuciya ta debe ki, ta kai ki garin da ba dawowa. Sharri Maree ta yi. Kin fi kowa sanin halin ta.”
Ta dauko ruwan gora na Faro ta mika ma ta, “Ki sha wannan, ki dawo hayyacin ki.”
Asiya ta karbi goran ta jika makogwaron ta. Hakika, ta fi kowa sanin cewa Maree ta fi kowa son kan ta. Sannan kuma idan ba ta samu abu ba kuma ba wanda zai samu. Ta san kuma za ta iya yin kulle-kulle da makirci don ta wargaza farin cikin wadan da suka samu.
“Allah Ya hada ni da Maree! Wallahi sai ta yaba wa aya zaki. Ba don hidimar nan ba da yanzun nan zan je na same ta a duk wurin da ta ke, na yi mata wankin babban bargo.”
Asiya ta ji sarawan kan na ta ya dawo. A ina Mariyar ta ke? Ta san Yusuf ya san muhimmancin wayar sag are shi, musamman a kan aikin sa da ma girman da ya samu watannin baya.
To yaya a ka yi wayar ta shiga hannun ta, alhali ita da ta ke matsayin matar sa ba ta dauka?
Sannan shi ya nemi ta yi ma sa wayar, a cewar sa, don ya ji muryar ta. Shin hakan ne ko kuwa……Misalin karfe daya na rana motoci suka yin jerin gwano tun daga Dagauda har zuwa garin Bauchi. Amarya Muhibbat ta na zaune cikin motar alfarma, Prado, wanda mijin ta ya tanadar ma ta don kai ta dakin ta. +
Cikin motar iyayen ta, kannen mahaifin ta su biyu da kuma ‘yan uwan mahaifiyar ta su biyu su ma. Babu wata kawa a cikin su ko daya, domin an tanadar mu su wasu motocin na musamman, ta yadda abokai su ka hada karfin su ya kasance kusan kowacce motar da za ta koma Bauchi, bai wuce kawar amarya daya ne cikin ta da aboki day aba.
Yusuf ya ki amincewa matar sa ta shiga ko ina da ya wuce ta sa motar. Ba ya kaunar ta takura, ko ma wani ya kalla ma sa matar sa. Yayi biris da tsiyar da abokai ke ma sa, cewa ya fiye kishi da yawa. In dai a kan Asiya ce, to lallai zai iya yin fiye da hakan.
Ganin tafiyar ta ya yi a lokacin ya na kofar gidan su, kamar ya tintsire da dariya. Cikin ta bai girma sosai ba, hasali ma ya ma ta kyau ne. sai dai yunkurin tafiyar da take yi da kyar ya saka shi son ya dara. Ya san bai wuce gajiyar da ta yi fama da it aba.
Shi ya bude ma ta kofar da sauri na motar ta shiga ta zauna da kyau, ya yi biris da zolayar Sadi, da yake cewa a bar amarci wa Hadi, tun da shi ne sabon ango. Bai damu ba, don bay a kaunar matar sa ta sha wahala.
“Idan mun koma gida zan mayar da ke gida, ba sai kin je Dinner ba. Idan ya kama ma, sai na zauna na mi ki tausa.”
Ya kashe ma ta ido daya, sannan ya ja motar suna tafiya a jeren. Ita ma ta yi ma sa murmushi mai taushi. Amma ya hangi wani abu cikin idanun ta.
Tun shigar ta motar ba ta ce da shi uffan ba. akwai abin da ke damun ta. Ba dai gajiyar b ace, duk da sanin cewar gajiyar ma za ta iya saka mata kasala. Ya tabbata za ta fada ma sa komai, don ya yi imanin matar sa ba za ta boye ma sa komai ba.
Sun yi nisa kan hanya, amma ba ta yi yunkurin cewa komai ba. Ga shi kowacce dakika da ta wuce ya na jin yadda take shaker numfashin ta da yadda take fitar wa. Tabbas, akwai matsala….
“Sarma-sarma duduf!!” Ya furta ya na kallon ta. 2
Ita ma ta kalle shi,da farko ta nuna alamar daurewar kai, “Me ke nan?”
“A’a, ba haka ba ne.”
Ta nisa, sannan ta ce, “Wane ne yake mini Sarma-sarma duduf?”
Ya dan yi dariya, “Ko ke fa?”
“A’a, ba haka ba ne.”
“Okay. Masoyin ki ne, wanda ke kaunar ki, yak e kuma damuwa da damuwar ki, ya ke mi ki Sarma-sarma duduf.”
Ta dan yi murmushi sannan ta kawar da kan ta. Me ke ran ta? Ya na son ya sani. Tuntunin ma ya na son ya tambaya, amma bay a son ya takura ma ta, har sai ta yi hakan don kan ta. Ko ma meye, ya san dai bay a da nasaba da shi, sai ko sha’anin hidimar su ta mata.
“Na kira wayar ka kamar yadda ka bukaci hakan, amma ba ka dauka ba.”
Fuskar sa na kallon titi ya sake murmushi. Zancen ke nan, kan waya? Mata bas u da dama. Ya ce da ita, “Bayan har na bar masauki ban ji kiran ki ba? kin fi kowa sanin yadda nake son jin muryar ki a ko yaushe.”
“Na kira ka ma na. Ka duba ka gani.”
Ya dan kalle ta. Akwai wani abin da ke cikin muryar ta, wand aba zai iya fassara shi ba. Ya ce, “What’s the big deal? Tun da kin ce kin kira, na yarda.”
Ya ci gaba da kallon titi. Bai ga abin jan maganar ba a nan. Ya yarda da ita, dari bisa dari. Kawai dai ta na neman daga wa kan ta hankali ne.
Ta dan yi shiru na wani lokaci, kafin ya ji ta ce, “Na kira wayar ka, amma Maree ce ta amsa. Ta ce min ka na wanka ne a lokacin.”
STORY CONTINUES BELOW
Tukin da yake yi bai hana kan sa sarawa ba nan take ya ji kamar a mafarki? Wayar sa a wajen Mariya? Tabbas ya lura wayar sa mai layin Airtel ba ta jikin sa, amma a tunanin say a bar ta ne cikin motar sa. Zafin kai kuma ya hana ya bi ta kan wayoyin ba ma.
Ya kai hannun sa ya laluma aljihun rigar sa, ya dan taba na wandon sa, sannan ya kalli wurin da ya saba ajiye wayoyin sa a duk lokacin da ya shiga motar sa. Kamar tsafi, babu wannan waya.
Idanun Asiya a kan sa su ke kirrr, fuskar ta fayau. Ya yi dariyar takaici a takaice, sannan ya ce, “Unbelievable! Abu sai k ace mafarki? Dazu da safe bayan tafiyar ki sai ga Mariya. Na yi mamakin ganin ta matuka.”
“Me ta je nema a wajenka?”Tambaya ce halaliya, wadda ta dace ta yi ma sa ita. Amma yanayin muryart ta na nuna bacin rai da kuma….zargi?
“I don’t know, ban sani ba nima. Na yi zaton ko ta fada mi ki. Don na fada mata cewar idan akwai abin da ta ke so, to ta neme ki ta fada miki kai tsaye. Ke za ki gaya in idan kin gay a dace. Nan na bar ta a falo, na tafi abin da ya fi muhimmanci gare ni.”
Iyaka gaskiyar lamarin ke nan. Yayi tunanin fayyace ma ta komai, amma kuma sai ya ma sa kamar mai neman kare kan sa ne bisa zargi. Bai so hakan ba, amma ya na da muhummanci Asiya ta fahimce shi.
Ta kawar da fuskarta sannan ta kura wa motocin da ke gaban su idanu. Ba don a jerin gwano suke ba, da zai tsayar da motar sa ce don su yi magana a natse. Ya fi son ya san abin da ta ke tunani a kan komai. Hakan ba zai samu ba, don bay a son jan hankalin jama’a zuwa gare su.
“Tell me, fada min abin da ke ran ki.”
So ya ke yi ya sani, don shirun ta na bayyana abubuwa da dama, wanda ta kasa furta su. Ya ji baya son hakan. Har ga Allah, ya sha alfahari da irin yarda da amincin da ke tsakanin su. A halin yanzu kuma, kamar zargin sa take yi, abin da hankalin sa ba zai dauka ba ke nan.
“Babu komai a raina.” Ta amsa ba tare da ta kalle shi ba.
A lokacin ya ji fusata, amma ya yi kokarin dannewa, “Kar ki gaya min wannan. Don nib a yaro ba ne. a tunanin ki, zan fado kasa kamar haka, ba nauyi ne?”
A nan ta kalle shi, fuskar ta cike da nadama. Watakila ko jin yadda ta yi muryar sa ta fito ne a bushe, kakkausa. Ta ce, “Ba hakan na ke nufi ba.
Kawai yadda Mariyar ce ta amsa wayar ya saka ni kaduwa. Sannan ta ce min kai ne ka aika ta je don za ku tattauna kan wani abu.” Ta dan sauke muryar ta don wata kila kar ya fahimci tsatsar da ta dauka, ta dora da, “Kuma ce min ta yi a lokacin wanka ka ke yi.”
Akwai wasu lokuta da dama da idan mutum ya tsinci kan sa cikin mummunar mafarki zai so ya farka. A lokacin Yusuf ya yi fatan farkawa daga irin wannan mafarkin. Karo na farko ke nan ya samu kan sa cikin wannan yanayin. Ko ranar da ta fara fuskantar sa a gidan sa kan zargin yi wa Mariya ciki bai ji kamar yadda ya ke ji a yanzu ba.
“I can’t believe this!” Ya furta, ya na mai jin zuciyar sa ta kama da wuta, “A gaban kin a fito daga wanka! Me zai sa ki yarda na sake shiga wata wankar?” 2
Bai ba ta damar cewa komai ba, ya ci gaba da cewa, “Kin taba yi min irin wannan a kan Mariya. A wancan lokacin na kyale ne don na san cikin rudani ne da rashin sani. Amma a halin yanzu, na dauka kin fi kowa fahimtar halayena, ma su kyau da munana. Shi ne ki ke neman yin zargina a kan cin amanar auren ki, da kuma ‘yar uwar ki?” 1
Ya dan kalle ta. Ba ta kalle shi ba, sannan ba ta ce uffan ba. hakan ya kara ma sa takaici masaki masaki. Ya cura hannun say a buga jikin sitiyarin, ya na iya jin turirin bacin ran san a tasowa fuskar sa.
“Ashe karya ne….duk kaunar da ki ke shelar cewa ki na min karya ce.” 4
Ya yarda da ita, ya na kuma mutuwar kaunar ta. Amma ashe za ta iya yi ma sa wannan mummunar zato da zargi ko da na dakika daya a cikin zuciyar ta?
STORY CONTINUES BELOW
Ita ce mace ta farko da ya fara sani a matsayin ‘ya mace. Ya kuma same ta cikakkiya, kamilalliya. Hakan ya ma sa dadi matuka, har ma ya rika zuba ma ta albarka ba kakkautawa.
Ta kasance abar alfaharin sa, abar yardar sa. Yanzu ne yak e la’akari da cewar idan wadan da ka yarda da su suka juya wa wannan yardarm baya, tabbas akwai babban takaici a ciki. 3
Ya lura ba ta sake cewa komai ba. hakan ya kara kular da shi. Bai san abin da ya fi ba shi haushi ba. zargin da ta yi masa, ko kuwa kyaliyar da ta ke yi ma sa a lokacin?
Ya ci gaba da tukin motar sa ba tare da sake cewa uffan ba. Ba bu amfani. Zuciyar sa sai tafarfasa ta ke yi, wajibi ne ya kame harshen sa. Ko ba komai, biki ne a gaban sa. Dole ya tsaya ya kamala, in ya so daga bisani ya san abin da zai yi. Wanda ya dace.
* * *
Asiya ta yi shiru ba don rashin abin fad aba ne, sai don guje wa babban husuma tsakanin ta da Yusuf. Kwata kwata ba hakan ta so fito ma sa da maganar ba. ganin yadda ya damu da cewa akwai abin da ke damun ta ne ya sa ta yanke shawarar yi ma sa tambayar.
Har ga Allah, tambaya ce kawai ta so yi ma sa don son ta tabbatar da cewa Maree ta kai ma sa ziyara ce don kan ta, amma ba don shi ya kira ta ba kamar yadda ta yi hasashe ba. Amma sai tambayar ta fito a hagunce, jin yadda furucin sa ke fita.
Don haka ta yanke shawarar yin shiru har zuwa lokacin da a ka waste a bikin Hadi lafiya, sannan kuma Yusuf din ya dan huce. A kalla hakan ta ke fata.
Ta tuna da muryar Maree a lokacin da ta amsa wayar Yusuf da irin kalaman ta. Nan take wani bacin rai ya murza zuciyar ta. A gaskiya ba ta yi zaton ran Yusuf din zai baci har haka ba don tambayar da ta yi ma sa.
Ya kamata a ce ya fahimci cewa tana neman gamsar da zuciyar ta ce bisa kalama Maree.
A lokacin da ta sake kallon sa, sun iso tashar Awalah. Fuskar sa kamar hadarin gabas, idanun sa a tsuke. Nan take zuciyar ta ta sosu, ta murda sosai a yayin da abin da ke cikin ta ya motsa. Bacin ran say a haddasa ma ta jin haushin kan tana yarda damaganar Maree.
Gaskiyar Muhi ce. Da tun farko ta zubar da maganar da hakan ma bai faru ba. Sai dai duk wannan tunanin fargar jaji ce, duk daga baya ne, wai auren sadaka da bazawara.
Awowin gaba ta yi su ne cikin hidimomin bakin sun a biki. Sun kai Muhibbat da farko hard akin auren ta, wurin da suka tarar uwargida Suhaima ta shirya wata kwarya-kwaryar walima don tarbar amaryar ta.
Daga nan kuma da dare ya yi, kowa ya kure adaka a ka halarci liyafar cin abinci na dare a babban dakin taro na New York Hall da ke hanyar Maiduguri. 2
Taron ya samu halarta abokan aikin sun a asibiti da ma na arziki hade da ‘yan uwa. Hadi da farko ya so ya ki amincewa, amma abokai ne su ka matsa don ya zama kafar haduwa da ‘yan uwan da aka dade ba a hadu ba.
Asiya ta ji dadin kasancewa cikin mutane. Don ta dan cire komai cikin ran ta, ta tsaya wa Muhibbat sosai wajen komai, duk da cewar ta na tsaya kan kafafuwan ta ne da kyar.
Ta kasance tare da Muhibbat har wajen sha dayan dare, bayan an waste daga liyafar, an kuma mayar da ita dakin na ta. A gajiye ta ke, ta kasance cikin kewar jin kalaman Yusuf, wanda ke nu na ma ta yadda ba ya son ta rika wahalar da kan ta. A lokacin liyafar, ko yi ta wajen da ta ke yi bai yi ba. ta ji zafin hakan, amma ta yanke shawarar yi ma sa uzuri.
Lokacin da Yusuf ya dauke ta, bai ba ta fuskar da za ta shawo kan sa ba. ta so ta far aba shi hakuri, amma ya ja da baya. A motar bai ce da ita uffan ba. Haka ma da ya tsayar da motar ya fidda jakar sa, bai bari ta karbe shi da su ba. 3
Kai tsaye ya wuce dakin sa. Ita ma ta shige na ta, ta zaga don rage marar ta, sannan ta gagara watsa ruwa a jiki. So kawai take yi su yi magana da Yusuf. Ko a kalla ta ba shi hakuri kar ya kwana da fushin ta a zuciyar sa. Ciki ne da ita, komai na iya faruwa. Kar ta mutu da wannan nauyin a kan ta.
STORY CONTINUES BELOW
Ta same shi cikin dakin say a na kokarin bude jakar say a fitar da kayan da yayi balaguro da su. Komai dare idan ya dawo daga tafiya bay a bari su kwana cikin jaka.
Ta je da sauri ta na yunkurin karba. Ko ba komai, aikin ta ne. Ita ce ke ma sa tun bayan sun dawo zaman aure na kwarai.
Sun dan yi jayyaya kafin ya bar mata. Duk da hakan, bai ce ma ta komai ba. Ta zuge zip din jakar, shi kuma ya juya ma ta baya. Ta daure, ta sauke muryar ta cikin ‘yar made, ta ce, “Haba Yallabai, ya kamata ka sauko daga fushin nan nake. Don bai karbe k aba kwata-kwata.” 5
“Ba fushi na yi ba. na gaji ne, ina son na kwanta.” Muryar sa a bushe ta ke, babu armashi.
Wani kulliti ya tokare ma ta wuya. Ta ji kamar ta fashe da kuka. Haba, me ya yi zafi har idanu ke cin wuta gira na hayaki? Shi ke nan kar ta yi kuskure? Ta gagara hakura ta bar shi ya huce.
“Ka yi hakuri don Allah ka saurare ni. Wallahi ba hakan na so ba. ban a son bacin ran ka, ka san hakan.”
Ya daga hannun sa kamar me tsayar da mota, “Please, don Allah ki bar ni, hutu na ke so.”
Wannan karon kwallar ce ta zo ma ta, amma ba ta zubo ba. yanzu Yusuf ne ke ma ta haka? Ashe zai iya juya ma ta baya da wuri kana bin da bai taka kara ya karya ba? a tunanin ta, bayan sun dawo za su zauna ne su warware matsalolin su. Sai ga shi ya na ta shan kamshi. Hakan ke kara sa ta tunanin cewa lallai akwai abin da yak e boyewa na rashin gaskiya.
Kwanciyar sa ya yi tare da juya bayan sa sosai. Ta nisa, sannan ta kalli jakar da ke gaban ta. Ta dan share kwallar da suka zubo a hankali ba tare da nuna alamar komai ba. ba za ta ci gaba da matsawa ba.
Allah Ya gani, ta yi irin na ta kokarin. Dole ne ta samu abin da zai dauke ma ta hankali, don ta san daren wannan rana, babu ita ba bu barci.
Ta fara fitar da kayan cikin a hankali. Ta yi nisa wajen cirewa ne hannun ta ya kai kan wani abin da ya firgita ta. Ta saki salati tare da jin wani tsini ya soki zuciyar ta.
Ya juya ya kalle ta, jin yadda muryar ta ta fito, sannan ya kalli abin da ke hannun ta. Ya tambaye ta, “Me ye wannan? Ya ya aka yi suka shiga kaya na?” 2
Tambayoyin da ya yi mata sun nuna cewar bay a da masaniya game da kasancewar su cikin jakar sa. Ko kuma ya raina ma ta hankali ba. ta sake duba jakar, tabbas ta sa ce.
A hankali ta ajiye kayan, sannan ta nufi dakin ta ta kofar da ta hada dakin sa da na ta, ba tare da tace uffan ba. Ba ta da abin da za ta ce da shi. Shi ma ba ya da sauran abin da zai furta.
Wata kila shike nan, rabuwar su ta zo. Domin ba ta san abin da za ta yi cikin wannan sabon yanayin da ta samu kan ta ciki ba. ba ta son fada wa zuciyar ta, cewa Yusuf zai iya cin amanar auren su, ba ta son neman karin bayani daga gare shi, gudun kar abubuwa su sake girmama.
Ta nufi gadon ta ta tsuguna a jikin sa ta sake tabkin hawayen da ta dade ta na rike su, ta bari suna zuba ba tare da tare su ba.
Hawayen ta sun a kunar zuciyar ta da kundukukin ta. Ta rasa wurin da zata jefa kan ta don ta ji sanyi.
Ba ta san tsawon lokacin da ta dauka ta na wannan hali ba. wan ciwon ciki ne ya muntsine ta, ta samu kan ta tana numfashi da kyar.
Bayan wani lokaci ya tsaya. Bayan wani lokacin kuma ta sake jin ciwon. Sai da ya lafa sannan ta shiga bandaki. A nan ta zo tsarki sai ta lura da jinni a kamfen ta. Ta kara razana.
Ta yi yunkurin komawa dakin amai ya zo ma ta. Ta yi ta haraswa kamar hanjin cikin ta za su fita. Ciwon ya sake dawowa, wanda ya fi na farkon. Bayan ya lafa, sai ta koma dakin, ta na nazarin abin yi.
Ta yi tunanin komawa dakin mijin ta, wata kila ko zai kai ta asibiti. Wa ta zuciyar kuma ta tsayar da ita.
Don me za ta neme shi? Mutumin da ya nuna bai damu da ita ba? ai sai ya ga kamar matsuwa ta yi da yin sulhu da shi. To ya sha kurumin sa, domin a halin da a ke ciki, shi ne mutum na karshe da ta ke son gani.
Bayan kamar awa biyu, ta ga bukatar ta watsar da fushin ta don neman taimakon sa. A kalla, za ta samu sauki, in ya so daga baya su dawo kan matsalar su.
Kai tsaye ta koma dakin kusan a dudduke, don yadda ciwo mai tsanani ya cafki marar ta. A yanzu yi yake yi da a kai-a kai. Sai dai ba ta same shi cikin dakin ba. ta daure ta duba bandakin sa, nan ma wayam.
Ina ya shiga cikin daren nan? Ba ta ji lokacin fitar sa ba kuwa. 4
Da ma wayar ta a dakin ta bar ta, don haka ta nufi wurin da ta bar ta a gefen jakar sa, kan gado. Nan ta ga kayan nan yadda ta bar su, haka ta dawo ta samu. Wani tsini ya soki zuciyar ta, ta ji marar tata ta sake murdawa har ma da jin wani gumi ya keto mata. Sai ka ce babu sanyin iyakwandishan cikin dakin.
Wayar Muhibbat ta kira , bayan ta koma dakin ta, duk da cewar ta san yin hakan bai dace ba. a halin yanzu ba ta iya tunani da kyau. Ta na bukatar taimako ne.
Bugu biyu Muhibbat ta dauka, “Hello Minde? Lafiya kuwa?” Muryar ta da nauyin barci.
Nadama ta kama Asiya, a yayin da agogon bangon dakin ta ke nuna karfe uku da kwata na dare. Ta lumshe idanun ta a lokacin da wani ciwon ya sake damkar ta, “Hadi ya na kusa ne Muhi?”
“Me ya faru?” Muryar Muhibbat na nuna ta ware daga barcin ta garau.
“Ina bukatar taimakon sa ne. mara ta ke ciwo mai tsanani Muhi….”
Wani sabon ciwon ya sake murdawa, ta yi shiru ta na mirgina kan ta a hankali tare da salati cikin zuciyar ta. Tun da ta zo duniya, ba ta taba jin ciwo mai tsanani irin wannan ba.
“Ina Dokta Yusuf? Ba ya kusa da ke ne?”
Tambaya ce mai sauki, amma mai wuyar amsawa.”Ke dai ki yi wa Hadin magana.” Wani ciwon ya sake murdawa, ta dora da, “Zan mutu Muhi, wallahi zan mutu…” 2
Hankalin Muhibbat ya kara tashi, “Kar ki damu Minde, ga mu nan zuwa. Ki yi ta addu’a kin ji?”
Asiya ta jefar da wayar da ke hannun na ta don azabar da ta ke ciki. Numfashi da kyar, ta damki hannun gadon ta tana ta salati. 2
Idan haihuwa ce to Allah Ya kawo ma ta da sauki. Fatan ta dai taimako ya zo gare ta, cikin gaggawa.