Asiya ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita. Ba ta iya jin kowane hakurin da su Umma ke ba ta. Su kan su hankulan su a tashe ya ke. Yusuf dai ya bar ta dakin ta ne don ba zai iya jure ganin hawayen na ta ba. Don kuwa hankalinsa kara tashi ya ke yi, kwakwalwar sa ta gagara yin tunani. +
Lokacin da Asiya ta fara gaya ma sa cewa Mariya ce ta shiga gidan ta fitar da Nurain, ya sandare, mamaki ya toshe kwakwalwar sa a yayin da kalaman Asiya ke nutsewa cikin ta.
Mariya? Ta dauki dan sa? A fadin duniya idan akwai wadda ya tsani jin sunan ta, ya kuma tsani ganin ta, to bai wuce Mariyar ba. Ko da kuwa ‘yar uwar matar ta sa ce. Ta ja ma sa matsalolin da har ya mutu ba zai manta ba. ba sai ta kara da wannan ba.
A lokacin ya bi sawun ta da kafa, Bature ya same sh Gudu ya diba ya na ci da zuci tare da kwafa. Idan har Allah Ya sa ya same ta da dan sa, Allah Ya gani, zai mance da dangantakar ta da matar sa, kuma uwar ‘ya’yan sa.
Zai mance da cewa ita uwa ce ga Amatullah. Don ta wuce gona da iri a wannan karon. Ta wuce kan su iyaye ta zarce kan dan su. Ba zai juri hakan ba.
Ya karade gewayen su kaf, tun ya na yi da kafa har Bature same shi da mota. Ba su ga Mariya ba. Shi kuwa bai zame ko ina ba sai gidan su Yafendo.
Kan sa tsaye ya shige gidan, zuciyar sa na tafarfasa don takaici. Ya san duk yadda a ka yi, su na da masaniya ko nasaba game da abin da Mariya ta yi a wannan dare.
Ya san cewar tun haihuwar Asiya, Yafendo ba ta taka kafar ta zuwa yin barka gidan sa ba, sannan ba ta je sunan ba. Ta fi kowa adawa da wannan haihuwa don ta tsani Umma, ta kuma ji haushin cewar ta tsatson ta a ka fara samun jikokin gidan, wandanda shari’a ta amince da su.
Ko da ganin sa cikin gidan su, fuskar ta ba ta nuna alamar jin mamaki ba. Sai ma kallon sa ta yi cikin gatse, sannan ta ce, “Yau kuma Dan auta an yi batar hanya ne a ka zo nan?”
“Ina da na Yafendo?” bai bata lokaci ba. kowane dakika daya ya na kara nisantar da Nurain gare su.
Ta saki dariya busasshiya, ta ce, “Yau na ga ikon Allah, wai na kwance ya fadi! Ina ruwan maza da wankan jego? Ina ruwan kwado da rigar ruwa? Me ya hada ni da gidan ka ballantana danka? Kai kuma waye, wai kiyashi a jirgi! An gaya maka ni hankaka ce kamar ka, wanda ke mayar da dan wani na sa?”
Kokari yake ya danne zuciyar sa, amma ba don haka ba da ya aikata abin da zai yi nadamar sa daga baya. Ya ce da ita, “Duk in da mai aro ya je, da sanin mai riga. Mariya ba zata taba aikata abin da tayi min ba tare da hadin kan ku ba. Na san kun san wurin da ta ke. Ki fada min na karbo da na, mu wuce wurin. In kuwa ba haka ba, za ku yaba wa aya zaki, gaba dayan ku.”
Yafendo ta kalle shi sama zuwa kasa a lokacin da ta mike tsaye, ta ce, “Iye, sannu Dan auta. Wato uwar taka ce ta turo ka ta ce ka zo nan ka ci min mutunci ko? To wallahi ka bar ganin girman kuka, bagaruwa ce babba. Kuma ka da ingarma ya raina gudun kura. Kudin ka da matsayi ba za su yi tasiri a kan mu ba. Je ka yi duk abin da zaka iya yi, yadda ka gan mu, haka zaka bar mu. Sai dai kaska ta mutu da haushin kifi a ruwa!” 2
Yusuf ya ce, “Ni dan zamani ne Yafendo. Kuma idan zamani ya riski manshanu ko an soya shi baya kamshi. Zan fice zuwa gida, na ba da nan da awa daya, ya kasance na samu da na a kwance a gida.” Da wannan ya juya zai yi yunkurin ficewa daga gidan.
Bai san dalili ba, amma ya tsinkayi sautin gaskiya a cikin kalaman ta. Duk da haka, ya ce, “Idan shege ya bata, shege a ke sawa ya nemo shi. Kin fi kowa sanin wurin da za a samu Mariya, don haka ki yi gaggawar aika sakona gare ta.” Ya sake kallon agogon sa na hannu, ya dora da “Awa daya tak!”
STORY CONTINUES BELOW
Awa biyu ke nan da suka gabata, amma shiru kamar an shuka dusa. Ya shiga safa da marwa, zuciyar sa na radadi. Wannan jira ya fi komai tsananin ciwo a rayuwa. Jiran tsammani, ko na gawon shanu.
“Dan auta, mu na bukatar sanar da jami’an tsaro a halin da a ke ciki.” Hadi ne ya ba da shawarar.
Yusuf ya kalle shi sanna ya yi godiya wa Allah da Ya ba shi abokai nagari. Ya san ya yanke amarcin sa ne da Muhibbat ya zo gare su don suna bukatar hakan. Haka shi ma Sadi da Kabir, kowannen su ya hallara. Ya lura Suhaima ma ta samu zuwa.
Ya nisa. “Na dauka za mu yi ‘yar gida ce mu warware. Amma a yanzu ba su ba ni zabi ba.”
Kafin ya rufe bakin sa, tuni Sadi ya fidda wayar sa. Bayan wasu ‘yan maganganu da yayi, sai ya kalle duka, ya ce, “Abokina ASP Hashiru Musa na kira a waya. Na yi ma sa bayani a takaice yadda a ka yi. Ya na bukatar bayanan wadan da su ke nan abin ya faru.” 2
Yusuf ya kalli dakin Asiya. Karo na fiye da kirgen sa, ya gagara samun kwarin gwiwar hada idanu da ita. Ya gaza wajen ba ta tsaro ita da Nurain.
Ya gaza a idanun duniya. A ce za a shiga har cikin gidan su sannan a dauke dan sa a karkashin idanun sa……
To wannan wane irin uba za a dauke shi? Har yaushe zai kara samun aminci da yardarm matar sa? A kullum cikin tunanin sa, yard ace komai, ita ce ginshikin zamantakewar aure. Sai ga shi nan ya gaza dasa yarda cikin zuciyar matar sa, da ma Ummar sa.
“A shirye nake na je.”
Dukan su suka tsinkayi muryar Asiya, wacce ga mamakin su, ta na natse, fuskarta na nuna juriya. Ya yi sauri ya je kusa da matar sa, ya lura da cewa kwayar idanun ta suna nuna akasin hakan. Wani irin mashi ya soki zuciyar sa. Ya san karfin hali take nunawa, wanda ba sai ta yi hakan ba.
A safiyar wannan rana dukkan iyalin gidan sa sun kasance cikin farin ciki da annashuwa. Tashi guda komai ya juya, ya dawo tamkar gidan mutuwa. Idan a ka duba sosai ta wani bangaren, mutuwar ce.
Ya kara jin wani daci ya ciko zuciyar sa, a yayin da ya kara jin tsanar Mariya a zuciyar sa. Ba zai kyale ta ba. Sai yayi ma ta irin na sa hukuncin kafin hukuma ta yi ma ta wanda ya dace da ita. 4
“Aslam ya na bukatar ki a nan my dear. Ki bari kawai na je ni kadai.”
Ta kalle shi cikin sauri, idanun ta na nuna tsananin tashin hankali, amma muryar ta na kokarin dannewa, “Nurain kuma ba ya bukata ta?”
Ya yi shiru bai amsa ba, don ya san ta na da gaskiyar ta. Shi kan sa ya kusa zaucewa kan son ganin dan sa balle a ce mahaifiyar da ta yi wahalar daukar cikin sun a watanni tara, ta sha wahalar nakudar su.
Sannan kuma ko dumin numfashin su ba ta gama ji ba a ce an raba ta da daya daga ciki.
Bai san yadda ta ke nuna karfin halin ta ba, amma ya san zuciyar sa tamkar tukubar tsire take don zafi.
“Duba, ba sai kun zo ba. zan ma sa magana ya zo nan da kan sa don ma ya ga yadda komai ya gudana. Ban yi tsammanin amarya ta na da zarafin iya zuwa ba. Kuma yes, Aslam ya na bukatar ta.” Sadi ya yi tsokacin hakan, sannan ya sake buga waya.
Yusuf ya koma cikin dakin sa. Ba don komai ba sai don kara kashe lokaci. Don kuwa a tunanin sa, zai ji motsin su Yafendo ko na Mariya sun dawo ma sa da dan sa. Zuciyar sa ta rika bugun kato a yayin da yake cura burodi.
A nan Asiya ta same shi. Ya gagara kallon idanun ta, “Na rasa abin da zan ce mi ki, don Allah ne kadai ya san yadda kike ji a zuciyar ki.”
“Kai ba ka jin komai ne?” Ya kalle ta sosai, muryar ta da rauni, idanun ta cike da kwalla.
STORY CONTINUES BELOW
Ta ci gaba da cewa, “Zuciyata hakika a rugurguje take a dalilin yaudara da zaluncin ‘yar uwata, wanda ya wuce kaina, ya koma ga dan da Allah Ya bani. Na riga na tabbatar da cewa komai na yi ma ta na alheri ba za ta taba gani ba, balle a ce ta nuna tausayin ta gare ni. Don haka ne ya san a dogara da Allah da kuma karfin halin mijina wanda nake ganin zai fara raunata a cikin wannan hali.”
Kwallar da ya ke neman tare wa suka ciko idanun sa, ya ja hannayen ta duka biyu ya rike, baya iya cewa komai sai jan numfashi da fitar wa. Kalaman ta sun kara nutsar da shi tare da kara masa karfin gwiwa.
“Babu abin da zai samu dan mu, ka ji ko? Na yarda da kaddara, na kuma san ba bu wanda ke wuce na sa. Ka tuna, Allah Ya mana baiwar da ba kowa yake yi ma sa ba, to fa dole ne ya jarabce mu. Na sani, abu marar kyau ba zai taba yin tasiri kan abu mai kyau ba. Don haka in shaa Allah, nasara tana tare da mu.”
Tausayin ta ya kama shi, ya dan rungume ta na takaitaccen lokaci. Ya na bukatar karfin halin ta, kamar yadda shi ma yake bukatar na ta.
Dole ne ya tabbatar mata kudirin san a wannan lokaci, kudirin da ya dauka wanda yayi alwashin cikawa ko da zai rasa ran sa ne ta wannan hanyar.
Ya ja daga jikin na ta, “Zan dawo mi ki da Nurain, bi’izinin lallahi Ta’ala. Zan dawo mi ki da shi cikin koshin lafiya nan ba da jimawa ba.”
Shi kan sa ya na furta kalaman ne wa kan sa, fiye da wa ita. Ya na son ya kara yarda da kan sa, fiye da ita ta yarda da shi.
Wayar sa ta dauki kara, ya kalli wurin da take. Asiya ta kale shi cikin sauri. Kwayoyin idanun ta suna nuna abin da yake tunani ne shi ma. Ya kalli fuskar wayar cikin hankoro, zuciyar sa ta kara tsere. Bakuwar lamba ce. Watakila wayar Mariya ce, ko ma Yafendo.
“Hello?” Ya amsa wayar, zuciyar sa kamar ta fito ta bakin sa.
Ya ji muryar wani namiji ta kwararo ta daya bangaren, “Hello, Assalamu alaikum. Wannan Dokta Yusuf ne?”
“Eh, ni ne.” Wani bangaren jikn sa yayi sanyi. Ya so a ce Mariya ce, ko Allah Ya sa tausayi ya ratsa zuciyar ta ta yanke shawarar mayar musu da Nurain.
Amma a yanzu kila ma wani marar lafiya ne mai neman maslaha kan cutar da ke damun wata ko wani nasa. Ba don jiran kiran da yake tsammani daga wajen Mariya ko abokan huldar ta ba, da ya dade da kashe wayar sa gudun kar a dame shi.
“Au, shi ke nan, faduwa ta zo daidai da zama. Da ma tun dazu nake son na bide ka. Na san a yanzu ka natsu waje daya, rashin dan ka ya ratsa ko ina a jikin ka.”
Gaban sa yayi ras! Yayi sauri ya kawar da kan sa, sannan ya ba da bayan sag a Asiya, wacce ga alama hankalin ta ya tsaya jikin wayar da ya fara yi idanun ta cike da fata. Ta ba da hankalin ta sosai. “Ban gane ba. Kai waye?”
Mai muryar ya tintsire da dariya. “Ni waye? Ni waye fa ka tambaya? Ni kuwa waye zan kasance, in ban da wanda danka ke hannun sa?”
Rudani ya bayyana a fuskokin su, a yayin da Yusuf ya tsuke fuskar sa, “Don Allah Malam, kar ka kawo wasa da hankali wa mutane.”
“Wasa da hankali?” A lokacin Yusuf ya danna kan nade murya ta wayar, wato recording. Ya kuma danna babbar murya wato speaker don Asiya ta ji komai tare da yi mata alamar tayi shiru da yatsar sa bisa lebban sa.
“Sunan sa Nurain ko? Yaro mai sanye da farar riga ta biri da wando na barci. Yaro ne kyakyawa, a yadda nake ganin sa.” Muryar daya bangaren a natse take, ta yadda mutum zai rantse mutumin arziki ne.
Asiya ta gwalo idanu, sannan ta kai hannun ta dora bisa bakin ta don idanun ta sun nuna kaduwa. Yusuf ya sake yi mata alamar yin shiru, ya ce da shi, “Yaya za a yi na gane cewa Nurain din da ka ke magana na san shi?”
“Eh to, ka na da gaskiya. Amma na tabbata ka san Mariya Sabo Ali.”
Wani kara Asiya ta saka, ta na kokarin toshe bakin ta don bin umarnin Yusuf. Amma idanun ta sun fara zubar da hawayen da tun dazu suka kasa tsayuwa, suke ta zuba kamar ruwan saman marka. Ya san tunanin ta.
Nan ya hadiye yawu da kyar, wata tsana ta mamaye zuciyar sa. Ya tambaya, “Kai wane ne?” Bai taba jin irin muryar sa ba.
Ya dan yi dariya, “Wannan ma duk bai taso ba. Tone-tone kara bata lokaci ne. Ni mutum ne mai adalci doctor. Kuma Mariya ta zo nan kotu na, dole na karba ma ta hakkin ta.”
Ya na son yayi ihu, amma ya daure, ya tambaya, “Me kake nema a wajena? Wane hakki Mariya ta ke magana?” Har a lokacin jin sa yake yi kamar a cikin fim. Ko kuma cikin mafarki mai firgitarwa, marar dadin nan.
“Wannan tambayar ce ta dace ka yi min ita. Kuma ba tare da bata lokaci ba zan amsa ma ka ita.”
Nan ya ji kukan yaro a ta bayan fage, kamar wanda a ka muntsina. Ko da a ce ba dan sa ba ne , ya ji zuciyar sa ta sosu. Ya lumshe idanun sa, tsananin zogi na takaici ya kara ratsa jikin sa gaba daya.
Ya damki wayar da ke hannun sa kamar ya fasa ta. Ji ya yi kamar ya saka hannun ya ja ko ma waye da ke daya bangaren, ya rika jibgar sa kamar Allah ne Ya aiko shi.
Da gudu ya ji Asiya ta kwace kan wayar, ta na cewa, “Don Allah ku dawo min da Nurain. Duk abin da kuke so za a ba ku.” Muryar ta cike da ban tausayi da tsima jiki.
“Ina son hakan, Hajiya. Amma ya danganci yadda mijin ki ya so ya mi ki adalci. Na san ma su kudi irin ku sun fi son ‘ya’yan su a kan dukiya. Na kuma san ba za ku bani kunya ba.”
Yusuf ya so ya dan ja mutumin da Magana ko Allah zai say a ji wata kara, wanda zai taimaka ma sa wajen fahimtar wurin da dan sa yake. Amma jin kukan dan sa game da na matar sa suka sa shi tsayar da komai.
“Nawa kuke so?” Muryar sa ta fito a bushe.
Ya kara dariya, “Hakan a ke son ji. Naira miliyan talatin ne kacal.”
Ya lumshe idanun sa karo na biyu sannan ya bude, “Ba na da wannan kudi.”
Sautin dariyar da ya ji a daya bangaren ya kara ma sa fadin kullitin da ke makale cikin wuyan sa. Ya na kuma sane da idanun da Asiya ta zuba ma sa, wadan da yake son su yarda da shi.
“Me ka ce?” Muryar ta zo cikin sanyi. “Dokta, ban taba aure ba balle na haihu har a ce na san zafin da. Amma kai ka sani, don haka yanzu zan bar ka da wannan.”
“Na san komai likita, ba tahiri na nema wajen ka ba. zan b aka damar ceto danka ta hanyar bin umurni na. kar ka manta, kai ke da abin da babban hasara idan ka yi taurin kai. Sannan ba sai na gaya maka cewar ban da ‘yan sanda cikin wannan al’amarin ba.”
Daga nan wayar ta katse, kamar yadda ta shigo, kwatsam.Daki ne cike da duhu kamar yadda yake a waje. Ba a iya ganin ko da tafin hannu ne. asiya ta dafe kirjin ta cikin tsananin tsoro da fargaba, ta shiga addu’ar Allah Ya raba mu da duhun kabari. +
Kuka take ji mai shiga jiki, amma ba ta iya ganin komai. A yayin da kukan ya tsananta, zuciyar ta ta shiga tsere, ta na matsawa cikin duhun. Ta fahimci kukan dan ta ne Nurain, wanda ke yin sa cikin tsananin bukatar dauki.
Ta fara gudu, ta mance da dukkan wani duhu ko tsoro, zuciyar ta na tsalle. Nurain! Nurain ya na bukatar ta, za ta je gare shi cikin gaggawa. Da wannan zummar ta nufi wurin da ta hangi wani haske kadan, wurin da ta lura da wata mace tsaye a wajen, ta na rike da jariri.
Ko da ta matsa kusa, ta ga Maree ce, ta na kuma rike da Nurain. Amma maimakon ta mika ma ta, sai ta yi miskilin murmushi sannan ta daga shi sama.
Asiya ta shiga rokon ta da ta ba ta dan ta, amma idanun ta a soye, suna cike da muradin son su kuntata ma ta. Ta na ji ta na gani, Mariya ta jefar da Nurain ta taga..…
Nurain! Asiya ta farka daga gyangyadin da ya sace ta, cikin zufa da haki. Karo na uku ke nan a wannan dare irin wannan mummunar mafarkin ke faruwa da ita.
Yusuf ya dafa ta daga kan sallayar da yake zaune, idanun sa cike da tausayi irin na ta. Tsawon dare biyu ke nan suna cikin fargaba da zullumin rashin dan su. Babu abin da suke yi sai salloli da adu’o’i.
Umma ta sa an bayar da sanarwa masallatai don a taimaka mu su da addu’ar Allah Ya bayyana Nurain, sannan ya tona asirin wadan da suka sace shi.
Cikin kwanaki biyun nan ba ta cikin hayyacin ta. Numfashi kawai take iya yi, amma ba ta san yadda a ka yi ta ke yi din ba. Ta zama kamar fatalwa.
Ba ta sanin lokaci sai idan Dada ta sanar da ita lokacin sallah ya yi tukunna take tashi. Abinci kuwa ya kaurace wa makoshin ta, sai fa a dole take shan ruwan dumi don kar ta cutar da Aslam.
Kukan Aslam ya na kara tayar ma ta da hankali, musamman idan za ta shayar da shi. Karshe ma madara ya koma sha dindindin, a maimakon farkon rayuwar sa da yake hadawa da ruwan nono.
Yusuf ya ci gaba da kallon ta, yana du’a’i. Ba sa iya ce wa junan su komai don sun kai ga ganin kalamai bas a isar su wajen kwantar da zukatan su. Sun dagara ne kan idanun su wajen isar da kowane sako.
Asiya ta mike ta koma bandaki don sabonta alwalar ta. A kowane dakika kukan Nurain take iya ji, ta na tunanin abin da a ka shayar da shi, in har an shayar da shi din. Hakika, Maree ta kai kololowa kan zalunci.
Tsawon kwanaki biyun nan sun yi waya daban daban da Yusuf, kan maganar kudaden da suka bukata. Yusuf miliyan goma ya iya hada wa don karancin kwanakin da su ka ba shi ya hada mu su ya ba su.
Suna hakan kuma ‘yan sanda suke binciken su game da wannan al’amari, a yayin da fitilar su ta haska Larai da maigadin gidan. ASP Hashiru, cikin kwarewar aiki da sanin halayyar dan Adam, ya sanar da su cewa akasarin sata irin wannan, a kan yi nasara ne idan akwai hannun na gida a ciki.
Wai hausawa sun ce da dan gari a ke cin gari. Bugu da kari kuma ita ce mutum ta karshe da ta gan shi, kuma ma itace ta mika shi wa Mariyar.
Larai ta ci kuka kamar ran ta zai fita, har ta ba wa Asiya tausayi. A ranar da a ka fita da ita da sunan kai ta cibiyar bincike na ‘yansandan ciki, wato CID, Yusuf kau da kan sa yayi, ya sunkuyar ba tare da ya kalle ta ko ya kula kukan da take yi ba.
“Yallabai, ka yi min rai. Na dade da ku ina aiki, a nan na ke ci da sha tare da rufa wa kaina asiri. Na rufa asirin gidan nan, kar ku tozarta ni. Wallahi yallabai ban san komai ba.” ta juya ga Umma, “Hajiya Umma, kar ki bari su tafi da ni don a wulakanta ni.”
STORY CONTINUES BELOW
Da gudu Asiya ta je ta rike ta, ta na zubar da hawaye. Ganin hakan ya sa ita ma Laran ta durkusa a gaban ta, tana kuka mai ratsa zuciya. Ta yaya Yusuf zai iya kawar da idanun sa, ya bari a tafi da Larai?
“Ku bar tafiya da ita, ina bukatar ta a nan tare da ni.” Asiya ta furta cikin hawaye. Ita kan ta mamakin cewar har a lokacin ruwan na iya fita daga idanun ta a matsayin hawaye.
A lokacin Yusuf ya kalle ta, “Zai fi kyau idan ki ka bari ‘yan sanda su yi aikin su. Laifi ne ki zama katangar da zata hana su yin hakan.”
Mamaki ya kara kamata, “Larai ce fa. Ta yaya za a yi Larai ta yi lahani wa Nurain?”
“A halin yanzu ba zan yarda da kowa ba a tare da mu.” Ya furta cikin murya busasshiya.
Kalaman sa suka sosa ma ta zuciya. Ta ce, “Ke nan, ni ma ba ka yarda da ni ba?”
Ya yi sauri ya kalle ta, idanun san a nuna jin zafin kalaman ta, “Kin san ba hakan nake nufi ba. Larai ce ta karshe wajen ganin Nurain. Lokacin da Mariya ta zo ba ta neme ki ba, kuma sannan a cewar ta, aiken ta ta yi zuwa kicin. Mu dauka hakan gaskiya ne. Amma ta yaya a ka yi Mariya da mutanen ta su ke sanin duk abin da a ke ciki game da kudaden da muka tanadar da ma duk maganganun mu? Yaya a ka yi suka san cewa mun sanar da ‘yan sanda? Ranar da na shigo da miliyan bakwai gidan nan yaya a kayi suka sani har suka min waya a kai?
“Shirin da a ka yi na farko, kan a kai kudin kauyen Bojinji kusa da makarantar firamaren su, ASP tare da yaran sa sun shirya mutanen su a boye cikin fararen kaya don kwantar bauna wa wanda zai dauki kudin. Sai gas hi sun min waya, sun ce sun fasa zuwa wajen, sun canja shirin su.”
Ya mike tsaye, ya ja hannun ta daga Larai, “Dole ne akwai hannun na cikin gida a wannan al’amari.”
A yanzu da take tunanin furucin sa, komai ya fada gaskiya ne. kamar su Maree na da kunnuwa a cikin gidan. Ta nag a kamar sun saka kyamera ne cikin gidan suna iya kallon su. Sai ta ke ganin, anya, ba ya shakkarta ita ma? Watakila zai iya dauka da hannun ta wajen taimaka wa Maree don ta samu cikar burin ta na dukiya.
Ta yi sauri ta kakkabe wannan tunanin daga zuciyar ta. Yusuf ba zai taba yarda za ta saka dan su cikin hatsari ba. Sun yarda da junan su, kuma komai bambancin ra’ayin su, babu abin da zai jijjiga hakan.
Ta koma daki ta shiga nafila. Tun da safiyar wannan rana ya so ya mata allurer barci amma ta ki yarda fir. Barcin ma tsoro yake ba ta, don mafarkan da take yi ma su firgitar wa ne matuka. Ta fi son ta zauna ido biyu, ko da a galabaice ne.
Asubar fari wayar Yusuf ta yi kara. Gaba daya hankalin su ya koma kan ta. Fargaba su ke yi, suna tunanin ko da me wayar ta shigo? Ko da ya duba fuskar, ya kalle ta, “ASP Hashiru ne.” Sannan ya amsa.
“Abubuwa dama suka saka na yi waya.” Ya furta, bayan Yusuf ya saka babbar muryar wayar. “Farko dai, kamar yadda ka sani, wadan da suke maka waya kan kudin da zaka bayar don a mayar maka da dan ka sun yi amfani da lambobi daban daban na layin waya.
Hakan ya tilasta mana zuwa kamfanonin wayar sadarwa ta MTN da Etisalat, don bin diddigin wadan da suka yi rajista da wannan layin wayar, wanda hakan ya kai mu ga wani mai sayar da lemo da ke bakin hanyar zuwa babban shagon Jifatu. Mun kama shi, amma kuma babu wani abin da muka samu, don binciken mu ya nuna cewar an sace ma sa waya wajen awa daya tak, kafin a yi amfani da layin. A dole mu ka sake shi.
“To wannan ne ya tilasta mana aikawa babban ofishin su da ke Abuja, muka samo bayanai a kan duk lambobin da suka shiga suka fita a wayar ka. Nan dai muka yi nasarar samun layuka biyu na wasu, kuma tuni mun cafke su a sirrance, suna ofis din mu ma a yanzu.”
Yusuf ya gyada kan sa, “Hakan yayi kyau.”
“Mun samu cewar suna da nasaba da satar yaron, kuma a na nema karin bayani daga gare su. A halin yanzu dai zan karasa maka sauran bayanin bayan ka zo nan asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.”
STORY CONTINUES BELOW
Ya kalli Asiya, ita ma ta kalle shi. Zuciyar ta bar bugawa, don ta fara fitar da yin fata a cikin zuciyar ta. Ta ji ASP ya ce, “Mu na bukatar ka zuwa wajen ne, don duba ko Nurain ne a ka samu, ko ba shi ba.”
Ba su tsaya sauraron sauran bayanin ba. a kalla Asiya ba ta tsaya ba. mikewa ta yi, ta nemi ya kai ta asibitin don gane wa idanun ta.
Tare suka fita su uku; ita, shi, da Umma. Sun bar Dada da Muhibbat a gidan suna tsumayen komawar su. Da suka je fita ne za su asibitin suka hadu da su Hadi suna shiga harabar gidan. Nan ya ajiye amaryar sa, shi kuma ya bi bayan su.
Cikin mintuna goma sha biyu suka shiga harabar asibitin daga Inkil. Yusuf ya falfala gudu kamar jirgin Arik cikin hankoro da zumudi. Rabon Asiya da asibitin tun bayan haihuwar Amatullah da Maree ta yi.
Ta fannin jarirai, wato nusery suka samu ASP Hashirun da kan sa ya na jiran su. Asiya ba ta tsaya jira ba, zuciyar ta na tseren kilomita goma a dakika daya, tsabar gudu. Lokacin da ta shiga dan lungun da zai kai ta zuwa dakin, ta ji ta na tsalle a kirjin ta.
Ta dan rage sauri kadan, ta na tunanin, in ba Nurain din bane fa? Yaya za ta yi? Ina za ta jefa kan ta? Idan shi din ne kuma, a wane hali za ta gan shi? Me a ka yi ma san a tsawon kwanaki biyu?
Yusuf ya dafe kafadar ta na hannun dama, ta dan waiga ta kalle shi, idanu cike da kwalla. Na sa idanun sun ba ta kwarin gwiwar ta shiga, ya na tare da ita. Da wannan ta nisa, sannan ta shiga.
Dakin karami ne, ya na dauke da gadaje biyu na yara da kuma kwalbar ajiye su, wato incubator. Ba karon farko ba ke nan ta shiga dakin. Lokacin jinyar Amatullah ta shiga sau biyu don kai ta gashi cikin kwalba.
Likita daya, nas daya da kuma wata macen dan sanda ta tarar a ciki, sun saka wani jariri a gaban su. Ta nufe su, tana jin karar bugun zuciyar ta cikin kunnuwan ta. Ta fara jin suna rawa, amma ta daure ta karasa. A kwance cikin bargon yara na asibiti, ta yi arba da Nurain, wanda ke kwance idanun sa a rufe.
Tun kafin ta saka hannu ta dauke shi ta fara zubar da hawaye. A yanzun ma ba ta yi zaton tana da sauran hawaye a jikin ta ba. ta dauke shi ta rungume shi, ta yi biris da maganar da likita yake ma ta.
“Hajiya, ki dan yi hakuri, mu na yi ma sa gwaji ne don tabbatar da lafiyar sa…”
Kuka ta ke yi, wannan karon na farin ciki ne, sabanin na kwanaki biyu, dare uku da suka wuce. Gani take yi tamkar a mafarki ne, cewa Nurain ya na hannun ta. Ta shiga sumbatar sa a fuska, kan sa, gaba daya jikin sa. Dumin sa da kamshin sa suka ratsa jikin ta, suka sanar da ita cewar ba mafarki ba ne.
Likitan nan zai yi magana karo na biyu, Yusuf ya dafa kafadar sa kadan, ta idanu ya nemi fahimtar ya yi shiru. Ya yi shirun, sannan Yusuf din ya bambare Nurain da kyar daga hannun ta. Gani take yi kamar zai sake firewa ko ya bace, idan yayi hakan kuma ba za ta kara ganin sa ba har ta bar duniya.
“Bincike ya nuna, cewa wadan da suka hada kai da Mariya Sabo Ali wajen sacewa da kuma rike dan ku sangartattun yara ne, wadan da ba su wuce shekaru sha shida zuwa sha tara ba.” ASP Hashiru ya shiga yin bayani wa Yusuf da su Hadi a ofishin ‘yan sanda da ke titin ‘Yandoka.
“Mun yi zaton ko suna tare ne da gungun manyan barayin yara da fasa-kwaurin miyagun kwayoyi. Amma dai mu na kan bincike a kan su.”
“Amma shi wannan wanda na yi magana da shi bai yi kama da yaro ba, ina nufin, ba ya da muryar yara.” Yusuf ya furta cikin darewar kai.
STORY CONTINUES BELOW
“Tabbas, ba yaro bane. Ina mai lemon nan da mu ka fara kamawa tun da farko? To abokin sa ne. Shi ya karbi aron wayar ya buga maka da layin sa. Karya mai sayar da lemo ya mana, na cewar an sace wayar sa ne.
Shi ma mun dawo da shi hannunmu, mun kulle domin karyar da ya mana. Abokin na sa ya shaida mana cewar ya ba shi naira dubu biyu ne a kan ya bayar da layin sa yayi waya da ita. Bai san wayar me ye bane ya bayar don ya ga kudi.
A dabarar abokin na sa, kafin a gano lambar wayar, tuni sun karbi kudin su sun yi nisa daga wuraren nan. Idan ma za a yi kame, to mai sayar da lemon za a kama, ba shi ba.”
“Lallai sun yi dabara.” In ji Hadi. “Mamaki na ke ji a ce ma su karancin shekaru ne suka aikata wannan.”
ASP ya ce, “Well, ka san tarbiyya ce yawanci ba sa da ita tun daga gida. Wasu kuma suna da ita amma kawai son zuciya da kuma yin arziki ko ta halin kaka ne ke sa su shiga wannan harkar. Actually, wadannan karo na farko ke nan suka fara wannan harka, amma fa a ganina ne.”
“Ta ina Mariya ta san su?” Yusuf yayi tambayar da ta dade ta na juyawa cikin kan sa.
“A cewar shugaban su, mai suna Aliyu, Mariya Sabo Ali ta same su ne da tayin kaso mai tsoka na daga kudin da za ta samu daga gare ku.
Da farko dai ta ja hankalin su ne, kana bin da za ta samu na miliyoyin nerori, sannan ta yi mu su alkawarin kasshi talatin, ita kuma ta rike sauran. Gaskiya yawancin sub a su san abin da suke yi ba. ita ce dai master-mind, wato jigon su a kan komai.”
“Bayan mun gaza samun nasarar cafke su a Bojinji, sai muka san akwai aikin na cikin gida a al’amarin. Shi ya sa muka kama Larai da Maigadin ku. Da farko dai mun fi shakkar Larai bisa dalilan da ku ka sani. Zargin mu ya zama gaskiya, bayan ta bar wasa da hankulanmu, ta amince da laifin da ta aikata.”
Yusuf ya zaro idanu, “Ya salam!”
ASP ya gyada kan sa, “Tabbas, ita ce ta kai jaririn bakin kofar fita gidan, sannan ta ja hankalin maigadin har ta mika shi wa daya daga cikin samarin nan, wanda ya je da Keke Napep ba tare da ya lura ba. sannan ta yi sauri ta koma. Mariya ba ta je gidan k aba a zahiri, saboda kar a gan ta har ma a alkinta ta da wannan satar. 7
“Amma a kusan asubahin yau muka samu kira daga wasu bayin Allah, wadan da suka ce suna zama a gidan haya a unguwar Tirwun da ke nan garin Bauchi. A cewar su, sun ga gilmawar jariri a gidan su tare da wasu matasan da ke zaune a gidan su.
Sun kuma tabbata mana cewar gwauraye ne. hakan ya sa suka neme mu a waya don ba su yarda da su ba. Wadan nan yara su ma ajiya a ka ba su na Nurain, tare da madarar sa da ruwan sha. Su ma an musu alkawarin dubu goma goma idan suka rike shi da kyau.”
Yusuf ya lumshe idanun sa, ya na neman kwantar da takaicin da ya mamaye zuciyar sa. Wannan abu ya ma sa waya. Tsawon kwanaki biyu baya runtsawa, hankalin sa a tashe kan halin da Nurain ke ciki, wanda ya san dole abin da ya auku zai iya shafar shi ta kwanyar sa ko da a ce jariri ne. allah kadai Ya san irin yadda suka rika dura masa madara, da yadda suka rike shi.
Kafin isar su asibiti, sun samu an wanke shi fes, an canja ma sa kaya jikin sa, wanda ya tabbata sun yi tsami. Shi da kan say a duba shi da kyau, ya tabbatar da lafiyar sa bayan ya karbe shi daga hannun Asiya da kyar. Dukan su sun sha wahala; shi, Asiya da Nurain. Dukanin su sun dandana zaluncin Mariya.
“ASP, Mariya fa? An same ta kuwa?”
ASP ya nisa, “Sauran kiris ta guje wa jami’an tsaronmu. Amma mun same ta a garin Babaldu, kan hanyar ta ta zuwa wurin da ita kadai ta sani, sai kuma Allah. Ta na tare da jaririya, sai mu ka karbe ta, ta na hannun mu wajen dakin renon yara na ‘yan sanda a yanzu haka.”
Amatullah! Allah Ya sa ita din ce. Bayan sun bukaci su ga babyn da a ka karba ahannun Mariya, ASP ya hada su da wata kurtuwar ‘yan sanda, wadda ta kais u wurin da Amatullah ke zaune cikin wani daki mai girma, cike da kayan wasa da yara tsiraru.
Sai da yayi kwalla don yadda ya gan ta. Ta rame, ta lalace, sannan ga rashin koshin lafiya. Ya je gare ta, ya dauke ta a hankali ya na kiran sunan ta.
Ba ta da nauyi kamar wata gashin kaza. Ba ta ki shi ba, amma ta so ta manta da shi. Idanu kawai ta zuba ma sa, wadan da suka fito koro-koro kamar wacce take gudu ne aka manna mata su. 3
Ba zai sake kuskuren barin ta a hannun kowa ba, ko da kuwa wacce za ta sake karbar ta mahaifiyar ta ce. Alkawari yayi wa kan sa, cewar zai rike ta tsakanin sa da Allah, ya kuma yi kwadayin fidda ita daga matsalar rayuwa. Bai san yadda a ka yi ya biye wa son zuciyar Mariya har ya jefa Ama cikin hatsari ba.
Mariya ba ta damu da kowa ba sai kan ta. Ba ta san son kowa ba, don haka ba ta cancanci son da kaunar kowa ba. Ya kalli ASP, cikin muryar da shakewa, ya tambaya, “ASP, zan iya tafiya da ita gida? Ta na bukatar agaji.”
ASP yayi murmushi, “Me zai hana? Da ma kai muke jira ka zo ka yanke shawarar abin da za ka yi game da ita. Mahaifiyar yarinyar….”
“Yadda duk ka ce. Za ka saka hannu a kan takardun da za su baka damar tafiya da ita daga hannun mu, you know, doka ce ta bukaci hakan ba wani abu ba. Da fatan ba za ka damu ba.”
“Ko kadan. Na fahimce ka.”
Bayan sa hannu kan kiyaye sharrudan dokokin shari’ah, a ka ba wa Yusuf Amatullah ya kai ta asibiti don ta samu kulawar sa a matsayin likita. Daga baya ne zai mayar da ita gida wajen da tun farko bai kama ta a ce ta bar shi ba.
Assalamu Alaikum, my wonderful people. I apologise for the late update. I know you all have been waiting patiently for it.
And now I hate to announce here that our story is gradually coming to an end. We only have one update to go! 5
Sad, right? I feel sad too. But you know me. I will return sooner than you think, with a new story. Until then, keep voting, commenting and sharing. Love you loads.Mun janye kara a kan duk wani laifin da Larai ta aikata mana, ASP.” +
Asiya ce ta furta hakan a lokacin da suka je ofishin cibiyar bincike na ‘Yan sanda. Tun farko sai da ta shiga wajen Larai, kafin ta shiga ofishin na sa tare da Umma.
Warin da ya buso hancin ta ya rike ma ta wuya kamar za ta yi amai. Sai da ta rike numfashin ta iya zama a wurin da suke. Sautin tari ta rika ji na mutanen da ke tsare, wadan da suka zuba idanu wa ma su shiga da fita cikin kalar nadama.
Larai ta kalli Asiya, idanun ta a kumbure su ke, suna cike faal da nadama. Ba ta san dalilin da ya sa ta aikata wannan zambar cikin amincin ba.
“Wallahi Anty, son zuciya ce ta saka ni wannan hali. Ban taba rasa ci ko sha ba a gidan likita. Hajiya Umma ta yi min riko tamkar ‘yar uwar ta. Ke ma kuma kin dora daga nan, kin min riko tsakani da Allah. Amma na ci amanar zamantakewa. A ranar da Mariya ta same ni da maganar kun tafi Dagauda biki. Ban karbi maganar ba sam, amma daga baya ganin yawan kudaden da ta yi min tayin su, sai na amince.”
Kan ta a sunkuye ne, ba ta iya kallon idanun Asiya. Ta ci gaba da cewa, “Na shiga ruda kaina, cewar zafin nema ba ya kawo samu. Na dubi yawan shekarun da na dade ina bautar aiki wa mutane ka’in da na’in, amma babu wani abin da na tara shi ne na ga dama ta samu, ta yadda zan samu ‘yancin kaina, na samu na sayi gida da jarin juyawa.”
Wani daci ya cike makogwaron ta, “Shi ne ki ka jefa Nurain cikin hatsari, don cimma burin ki.” Ba tambaya ta yi ba, bayani take mata, don tsabar fadin kullitin da ya toshe ma ta wuya saboda takaici.
“Wallahi Tallahi, ce min su ka yi ba za su cutar da shi ba. Kuma mun yi a kan komai ba zai wuce awa shida zuwa bakwai ba za a mayar da shi wajen ki. Ban yi zaton zai zarce har haka ba. Ki yi hakuri Anty.”
Asiya ta shiga tunanin idan ta yi magana a lokacin to ba za ta kame kan ta ba. Tabbas, za ta iya aikata abin da za ta iya nadamar sa daga baya. Ba sa da ‘yancin cutar da dan ta bisa kudirin su na neman dukiya! Ba sa da wannan damar cutar da su duka kamar yadda suka yi.
“Da gaske ne Larai, zafin nema ba ya kawo samu. Abin da ki ka min Allah ne kadai zai hukunta ki, don kuwa ko da a ce cutar da ke mu ke yi, ba za ki aikata ba balle kuma ba ma hakan. Hakkin Nurain ba zai taba barin ki ba tsawon rayuwar ki. Ki je da halin ki!”
Daga nan ne ta bar ta cikin kuka mai shiga jiki, ta na Anty ki yi hakuri. Na shiga uku! Wallahi sharrin shaidan ne.”
Na ta idanun sun ciko da hawayen, amma na takaici. Lallai sharrin shaidan da na son zuciya sun yi tasiri a kan duk wadan da za su iya cutar da jinjiri dan kwanaki bakwai don cimma burin su. Da ma ita suka dauka ba shi ba. Don idan ta tuna raba shi da ita da suka yi na tsawon kwanaki sai ta ji wani tirniki cikin makogwaron ta.
“I am afraid, satar kananan yara babban laifi ne wa kasa.” ASP ya fidda ita daga nisan zangon tunanin da ta yi. “It’s a capital offence, wanda dokar kasa ta yi babbar tanadin horo wa wanda aka kama da aikatawa. Ko da a ce ke kin yafe, tilas za a hora ta don zama aya wa masu hali irin na ta. Ko kuma ma su shirin yin sa.” Ya karasa zayyanawa.
“Babu yadda za a yi ne?” Umma ta yi tambayar.
ASP ya girgiza kan sa, “Babu. Don kuwa ita ce da hannun ta ta mika yaron wa sauran abokan laifin ta, kuma ta fadi hakan ne da bakin ta. Dole ne a hukunta ta. Sai dai za a iya nema ma ta sassauci kan yawan zaman kason da za ta yi.”
STORY CONTINUES BELOW
Ta rika tunanin dalilin da ya sa take neman afuwa wa Larai, da ma na matsa wa Yusuf kan su je su gan ta a can. Abu daya ne, tausayawa da kuma kyautata wa dan Adam. Duk mutum ajizi ne, ba bu wanda ya fi karfin laifi.
Idan kuma ya yafe kuskure ko laifin dan uwan sa don Allah, to zai kasance cikin sukuni da sanyin zuciya. Hakika, Allah zai Yafe wa mutum laifuffukan da ya aikata gare Shi.
Larai ta na bukatar second chance, wato wata dama, don ta gyara halayen ta duk da cewa ba mayar da ita aiki za ta sake yi ba.
Hausawa sun ce tsalle daya shi ke sa mutum shiga rijiya. Hakika, Larai ta daka tsallen da yayi sanadin shigar ta gidan kaso. Allah Ya kyauta, Yak are mu daga sharrin zuciya.
Mahaifin su yayi gyaran murya, a kokarin san a jan hankalin kowa zuwa gare shi. Ya yi hakan sau uku ke nan, ba tare da ya furta komai ba. ‘Yan uwan san a jini, Malam Isa da Malam Sani suna gefen sa. Kowa ya yi zugum, ya na jiran makasudin kiran wannan taro.
“Kamar yadda kowa ya sani ne.” A karshe Malam Sabo ya fara magana. “Ni mutum ne da ya yi sakaci wajen rikon iyalin sa, tare da sake komai wa mata ta. Na dauka matsalar ta ce, ba ta shafe ni ba. cewa nake, tarbiyyar ‘ya’ya mata sai uwar su. A yau na ke mai dimbin nadama, domin na yi matukar hasarar lada mai girma na tarbiyyar ‘ya mace ta zama tagari, sannan kuma ina fuskantar hukuncin Allah a kaina, bisa rikon sakainar kasha wa amanar da ya damka min.
“Wata kila da ko sau daya na dafa wa matata, da abubuwa ba su kai ga yadda su ke a yanzu ba.”
Asiya ta na sauraron sa tare da ganin nadama tsantsa cikin idanun sa. Ta dauke idanun ta. Abu ne mai kyau da yake neman gyara, amma dai kamar ya makara da hakan, don an ce icce tun ya na danye a ke tankwara shi. Idan ya bushe shi ke nan.
Ta kalli wurin da Maree ke zaune cikin isa da nuna halin ko-in-kula. Idanun ta ba sa dauke da nadama. A kangare suke, ta na kallon kowa biyu taro uku sisi.
Hakan ya kara sukar zuciyar Asiya. Ta san zai yi wuya Maree ta canja. Amma nunawa cikin rashin kunya ya kara wutar da ke ruruwa cikin zuciyar ta tun bayan dawowar ta gare su.
Ta yaya za a ce uwa daya uba daya take da Maree? A ce ita ce ta sha nono ta bar mata? Wace irin kiyayya ce haka take yi, irin wanda ya fita a musulunci, ya fita a layin halin zamantakewar dan Adam?
A makon da ya gabata ne hukuma suka sake ta a kan baili har zuwa lokacin da za su kare binciken da suke yi. A cewar su, babu shaidar da ta nuna alakar Mariya da abubuwan da suka faru. Na farko dai Mariya ba ta je gidan Asiya ba kwata-kwata.
Sannan ba ita ce ta dauki Nurain daga gidan ba, kuma ba da ita a ka yi waya ba, babu ma shaidar ita ta saka yaran da a ka samu da laifi dumu-dumu.
Abu kamar wasa, ta fidda hannayen ta tsaf daga dukkan wani laifi, ta fito cikin shawagi. Ko a jikin ta, wai an mari kumama. Hakan kara kona wa Asiya rai ya ke yi. Shi ya sa a wannan rana mahaifin su ya kira su dukkan su ya nemi gyara da sulhu a tsakani.
“Ya kamata ku yafe wa junan ku, Yalwaji da Laminde. Bai kyautu a ce kuna gaba da junan ku ba. Abin da ya wuce ya wuce.”
Maree ta juya idanun ta, ta ce, “Ni dai ban yafe sharrin da a ka kulla min ba. Babu abin da na yi a ka ce na yi. Don haka tilas a bani hakuri.”
Wasu hawaye ma su zafi suka ciko wa Asiya idanu, amma ta yi kokarin mayar da su. Babu amfanin zubar da su a kan Maree. Ba za ta bari bakin cikin ta ya kashe ta ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Ke Yalwaji!” Baban su ya tsawata mata, wadda ma kamar ba ta san yana yi ba. “Ba ki ji abin da nace ba ne? Sulhu na ke neman ku yi a tsakanin ku don komai ya wuce…”
Ta mayar da martani, “To sai na amince da sharrin da a ka kulla min? Ba a fi ni tsumma ba amma a na neman a barbada min kwarkwata? Kuma sai kowa yayi shiru ya kyale don an ga kudi.”
“Ke Yalwaji, ki ji tsoron Allah.” Malam Sani ya furta. “Ba bu wanda zai miki sharri, don da ganin kura an san za ta ci akuya. Mu dai ba baki bane wajen sanin halayen ki. Don haka idan za ki yi mana shiru to.”
“In ban yi shirun ba fa? Ni da gidan mahaifina amma a hana ni magana? Zai yiwu a mare ni sannan a ce za a hana ni kuka?”
Ba tare da cewa komai ba, Asiya ta mike ta nufi wurin da Mariya ke tsaye kerere kamar ta hadiye tabarya, ta sa hannu ta ja ta zuwa dakin mahaifiyar su. Sauran jama’ar dakin sai kallon su kawai suke yi, babu wanda Allah Ya ba shi ikon ko da motsa bakin sa ne.
Bayan Asiya ta sa sakatar kofar dakin, sai ta takarkare karfin ta, ta kai ma ta mari tau! Irin wanda zai sa mutum ya fadi har kasa, bakin ta yayi jini. Idanun ta suna ci da wuta, ta yi wa Maree kallon da zai iya narka kashin jikin ta ya zama hoda. 5
“Kut! Ki ka mare ni Laminde?” Mariya ta jijjiga matuka, amma takaici ya cike idanun ta. 3
Mariya ta mike, cikin yunkurin mayar da martani wa Asiya. Nan ne ba ta samu dama ba, don kuwa Asiya ta kara zuba mata wasu ma su ji da lafiya babu adadi. Yi take yi tana ci da zuci ba kakkautawa, har sai da Mariya ta shiga kwala ihu. 6
A lokacin ne ta zare mata ido, “Yi min shiru!” Ta nuna ta da yatsar hannun ta na gaba, sannan ta manne kan labbanta. 2
A lokacin sauran jama’ar gidan sun je jikin kofar dakin Dada, suna rokon da su bude kofar, ya isa haka.
Nan ne Maree ta samu bakin magana, “Tabdi! Ai kuwa allura ta tono garma. Wallahi sai kin san ni kika mara, don kowa ya ci tuwo da ni, miya ya sha.”
Ta na magana cikin muryar da take tunanin zai iya tsorata Asiya. Ga hawaye nan cike tab a idanun ta.
Tau! Asiya ta sake kai ma ta mari mai sa mutum ya ga walkiya. Nan take sai ga habon jini daga hanci. Idanun Mariya suka gwalo waje don tsananin kaduwa da tsorata, hawayen da ke ciki su ka kwaranyo. Ta kura wa Asiya idanu cike da fargaba.
“Me kike tsammani Maree? Cewa zan ji tsoron ki ne? Ai kin gama kure abubuwan da za ki yi min, wadan da za su daga min hankali.” 4
Mariya ta nufi kofar dakin da gudu, tana neman budewa, amma Asiya ta ja ta ta zubar a kasa. “Farko, kin ba da jikin ki, kika zubar da mutuncin gidan nan. Mun yi bakin kokarin mu, amma karshe guduwa kika yi kika bar mana diyar ki.” Tau! Ta sha wani marin. 4
“Sannan kika dawo kika wargaza mana rayuwar da muka gina ba tare da jin tausayi ba, ki ka kuma nemi hada ni husuma da Yusuf don ki raba mu.” Tau!
“Hakan bai ishe ki ba, sai da ki ka sa a ka dauki Nurain, ki ka raba ni da shi na tsawon kwanaki, ki ka jefa rayuwar sa cikin hatsari da tamu cikin garari.” Tau!!! 9
“Ban san abin da zan kira ki ba….me son zuciya ce ko marar zuciyar? Ba ki san ma meye so a rayuwar ki ba, balle a ce kina yi wa zuciyar ki. Ke har wacece da za a miki sharri? Me ki ke da shi da za a yi riba don an mi ki hakan? Zuciya ko kyawawan dabi’u?”
“Kin fito neman arziki, amma babu wanda ya kai ki talauci Maree. Duba da kyau, ki yi lissafin abubuwan da Allah Ya baki a rayuwa, kika fatali da su. Allah Ya ba ki mahaifa biyu, amma baki san darajar su ba; Ya baki ‘yan uwa amma ba ki san muhimmancin su ba; sannan Ya baki diya, Amatullah, amma ba ki san kimar ta ba. Shin me zaki nema a duniya ki samu, alhali duk abubuwan da suka dace ki daukaka kin zubar?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ki nemi gafarar Allah Maree, tun lokacin yin hakan bai kure miki ba. Da farko na yi tunanin yafe miki, tun ba tare da kin nemi gafarar ba. Na kuma so mu yi sulhu don mahaifan mu su samu sukuni. Amma a halin yanzu, Allah Ya gani, ba zan taba yafe mik i kan abin da ki ka yi wa Amatullah da Nurain ba, ko da a ce zan yafe mi ki kan abubuwan da ki ka yi min tsawon rayuwa ta.”
Sai da lura da sanyin jikin da Mariya ta yi ne, sannan ta sake kai mata mari uku kyawawa, “Wannan kuma na yi ne don da a ce tun bayan dawowar ki daga dandi a ka mi ki su, da wata kila ba ki aikata abin da ki ke cewa sharri a ka mi ki ba.” 4
Ta juya ga mahaifan ta, ta bude dakin suka shiga. Ganin Mariya a zube a kasa, hannu kan kumatun ta da ya fara kumbura, babu wanda ya kara cewa uffan, har Asiya ta fice ta bar su cikin dakin. 2
Watanni shida ke nan da suka gabata. Duk da cewar ta na zuwa Dagauda, kuma ba ta bar alherin da take yi wa iyayen ta ba, Allah bai sa ta sake haduwa da Maree ba. Ba ta kuma tambayi wurin da take ba, don karshen ta bacin rai ne zai biyo baya.
A wajen Muhibbat take jin abin da ya samu Maree, lokacin da ta je duba ta don rashin lafiyar da take yawan yi. A bayyane yake, cewa juna biyu ne gare ta. 8
Hadi kamar ya haura sama ya fisgo mata duniyar wata ya ba ta don dadi. Zumudi da karkarwa kam sai kace tsohon da ya auri budurwa. Ita ma Asiya ta yi matukar farinciki a kan hakan. 2
“Oh, Allah Sarki! Dokta Hadi ya rika sintirin dan malele. Ashe dai rabon malelen ne ke kan hanya.”
Muhibbat ta harare ta, “Ni fa yayar ki ce…tam.”
Dariya Asiya ta yi, ta ce, “Ai an bani damar wasa da yaya ta.”
Sai da ta furta hakan ta ji wani daci ya ciko bakin ta. Muhibbat ta lura da hakan. Ta ce, “Me yasa kike yi wa kan ki haka?”
Asiya ta yi kamar bata fahimce ta ba, “Kin san dole na taya ki farin cikin samun wannan karuwa. Kowa fa ya dauka Hadi ne ba ya iya haihuwa. Ashe da bakin cikin Suhaima ya kashe shi ba don Allah Ya sa kin kasance da shi ba.”
Muhibbat ta yi murmushi, “Gaskiya ne Minde. Hadi mutum ne mai kirki da kula da auren sa. A dan zama ta da shi, na kara fahimtar kauna da kuma yarda da wani mahaluki bayan iyaye na.”
Idanun ta suka ciko da alamar kauna, ta kai hannun ta tana shafa kan cikin ta, “Allah Ya mana kyauta ma fi girma da zai yi wa dan Adam, Ya kuma kara nuna mana shaidar kaunar mu ta gaskiya ne.”
Asiya ta dan yi dariyar zolaya, “Hinyau! Hinyau! Muhi an koro soyayya. Allah Ya karo wasu bayan wannan, ‘yan uku sau uku.”
Muhibbat ta kara dalla ma ta harara, “Na fada miki, ni fa yayar ki ce.”
Asiya ta juya idanun ta, “Matar babban aboki kuma ba. wai ina labarin Suhaima ne?”
“Zan iya baki labarin ta. Amma yaushe ne za ki tambaye ni labarin Maree?”
Nan take ta hada ran ta. Muhibbat ta dan yi dariya, “Ban san ki da hakan ba Minde. Wannan yanayi ba irin naki bane; bacin rai, fushi da ‘yar uwa…”
Ta kalli Muhibbat, “Ke kike fadin hakan?”
“Well, gaskiya ne ai. Ban ga amfanin fushin ki da Maree ba, don kuwa a komai kin fi ta. Kin fi ta kyau, hankali, tunani; sannan Allah Ya baki miji mai son ki da kauna, ya kuma baki ‘ya’ya, ga karatu kina yi a jami’a….me zai sa ki kula damuwa da ita?”
Asiya ta nisa, sannan ta furta a hankali, “Saboda abin da ciwo, a ce Maree ta yi min abin da ta yi min.”
Asiya ta kalli Muhibbat sosai, “Ko dai Maree ce ta zaga ta aike ki wajena?”
Muhibbat tayi dariya, “Mareen? Lallai ma. Ai kin fi kowa sanin ba nata style din ba ke nan. Dada na tarar rannan take koka min hali da kika shiga, take cewa ba halin ki ba ne. Ta fi son Laminden ta ta da, wacce ke da zuciya mai tsafta, mai son ‘yan uwan ta komai halayen su. Ta na ganin rikon da kike yi zai iya jefa ki cikin halin da zai cike miki zuciya da daci. Ta rasa Maree kan hanya mara kyau, ba ta son ta rasa Laminden ta.”
Hawayen da suka dade ta na mayar da su suka zubo daga hawayen ta. Dada ta so yi ma ta magana sau da dama, amma kuma sai ta fasa.
Hakika, an dade ana ruwa, kasa ta na shanyewa. Amma da gaske ne, Maree ba ta kai ta jefa ta cikin fushi ko tashin hankalin iyayen su ba. idan ta biye mata, za ta mayar da ita kamar ta, marar tunani da son kan ta.
“Ban san dalili ba, amma da na yi tunanin ta, sai na kara jin bacin rai Muhi.”
“Duk shaidan ne ke kara ruda ku. Amma ki daure zuciyar ki, ki mayar da komai ba komai ba. Rayuwar ki ba za ta tsaya don kin yi hakan ba. Ba bu abin da zai rage kan rahamar da Allah Ya miki.”
Ta kara nazari. Ba wani abu mai wahala a ke neman ta yi ba. Kawai ta furta ko da wa kan ta ne a cikin zuciyar ta cewa ta yafe wa Mariya, in ya so ta fawwala wa Allah komai. Hakan ba zai rage ta da komai. Ta yafe wa Larai ma balle ‘yar uwar ta ta jini?
Ta kalli Muhibbat, ta ce, “Ba za ta taba canjawa ba ne Muhi.”
“Ai ba hurumin ki ba ne ki canja ta, wannan sai wanda Ya hallice ta. Ke dai kar ki bari ta canja ki, shine kawai mu ke fata.”
Ta nisa, “Haka ne. Halin mutum sai Allah. Allah ya yafe mana gaba daya.”
“Amin.”
“Ba ki gan ta ba ne kwanaki da tayi ciwo kamar za ta mutu. Har su Dada ma sun fara fidda rai da ita.” Muhibbat ta furta, muryar ta a sanyaye. “Na je Dagauda a lokacin da naje duba lafiyar jikin Alfa.”
Kwanaki ita Asiya ta so ta ji labarin hakan. Amma da yake fushi ya rufe idanun ta, sai bata bi kai ba. ta san dai ta tura wa Dada kudi mai yawa, a can kololuwar zuciyar ta, tana fatan zai taimaka wajen jinyar Mareen, duk da ta ki yarda da hakan a cikin ta.
Ba su ce mata Maree tana kwance ba, ita ma bata tambaya ba. ba ta kuma ji son sulhu da ‘yar uwar tata ba, ko da a ce ma kar ya kasance bata tashi daga ciwon ba.
“Amma fa ta na warkewa ta sake komawa duniya, har yau babu duriyar ta.” 8
Asiya ta nisa tare da girgiza kan ta a hankali. “Kura bata taba barin cin nama, haka komai a kayi da jaki, sai ya ci kara.”
Muhibbat ma ta nisa, “Allah dai Ya kyauta, Ya shirye ta da mu baki daya.”
“Amin.” Kawai ta furta.
Yanzu ta kara fahimtar yadda Dada ke ji game da komai. Hakika, Maree ta yi nisa, ba ta jin kira. Dada ta rasa ta, dole ta ji tsoron kar ita ma ta zama mai bakar zuciya irin ta.
Nan take ta yi kudirin bayan yafiyar da za tayi wa Maree, za ta yi bakin kokarin ta na zama diyar kirki, wacce ke burin rabuwa da mahaifan ta lafiya.“Ka na ganin na canja?”
Yusuf ya dago kan sa daga komfutar da yake latsawa, ya kalle ta. A hankali. Ta na sanye cikin riga da siket na shadda mai kyaun adon dinky launin ruwan hoda. Ta sha kwalliya a fuskar ta, wadda ba ta cika yawa ba, amma ta fitar da kyaun na ta. 2
Ya bar abin da yake yi sannan ya ba ta hankalin sa, “You look the same to me, ba ki canja ba gaskiya. Idan a ka dauke katon hancin ki, da bula-bulan kumatun ki da kuma taibar da kika saka…”
Ta zaro idanu, “Taiba? Yanzu ashe na yi kiba?”
Ya saki murmushi. Zolayar ta yake yi, amma a kullum yayi hakan sai ta ba shi dariya. A lokacin dariya ta so ta kubce ma sa, ganin yadda ta rika kallon kan ta.
“Ta ina nayi taibar?”
Ya mike tsaye, “Bari na nuna miki.” Ya kuwa cafko ta, yana tsakurin ta yana ma ta jakulkuli, “A nan, da nan da ma nan…” A hakan har suka fada kan gado.
A cikin dariya, ta ce, “Tsokana ta kake yi, ko?”
Ya saka kan sa tsakanin wuyan ta da kafada ya shaki kamshin humranta. Har cikin kan sa ya ji ya na tsuma don dadi.
Ya ce, “Mhmm.”
“Me ya sa?” Ta tambaya cikin shagawaba.
“Saboda hakan ya kan bani damar yin abin da na ke miki yanzu.” Ya sake shakar kamshin ta, sha’awar ta ta wanzu cikin kan sa.
“Ba zan kara yi ma ka magana ba.”
Ya saki dariya mai sanyi, ya na hura mata iska jikin fatar ta, “Ko da na ce babu abin da ya canja a tare da ke?”
Ta juya su na fuskantar juna, “Da gaske?”
Ya lakaci hancin ta, ganin yadda ta nuna zumudi, “Da gaske. You are as beautiful, kyaunki bai ragu ba, kamar ranar da na fara ganin ki.”
“You mean, ranar da na fara jijjiga ma ka duniya?” Ta na ‘yar dariya.
Ya sake lakatar hancin ta, sannan ya ja ta zuwa jikin sa, shi ma dariyar yake yi. Zuciyar sa bulbular dadi take yi, ya rika jin farinciki na wanzuwa cikin ta.
A kullum suka tuna da ranar haduwar su dariya kawai suke yi, kowannen su da irin tunanin sa. Shi a kullum jinjina ma ta yake yi da irin kundunbalar da ta yi, duk da cewar ya na kallon hakan a matsayin wauta.
Can ya ja ta kadan, ya kalle ta, “Dakata! Ko dai so kike yi ki ce min ki na da juna biyu?”
Ta wulkita idanun ta, “What? Me wai?”
Ya dan bata fuskar sa, ya ji ta fashe da dariya, “A’a. Ba hakan nake nufi ba. So na ke yi na ji ko na canja ne a halaye na da mu’amala ta da mutane, musamman da kai.”
“Me zai sa ki wannan tambayar?”
Ta dan sunkuyar da fuskar ta, “Haka kawai.”
Ya nisa, “Ki na son na fada mi ki gaskiya?” Ta gyada ma sa kan ta a hankali. “A gaskiya, rayuwar ki ta canja, idan kin yi la’akari da yadda kika fara har zuwa yanzu. Daga sarauniyar yakin da ta zo karbar ‘yancin ‘yar uwar ta, zuwa ga uwa, mata da kuma mahaifiya. Duk duniya idan an zagaya samun irin ki ba su fi a kirga ba. Kin fara ne da neman hakkin ‘yar uwar ki, zuwa ga sadaukar da rayuwar ki don ba wa diyar ta rayuwa mai inganci. Idan ki ka auna rayuwarki daga dakin mahaifiyar ki zuwa nan, ta canja, kuma yanayin canjin mai inganci ne.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ka na ganin a dan tsakani ban zama mai riko, mai son kan ta, mai gaba da ‘yar uwar ta ba?”
Ya fadada murmushin sa. Allah Sarki matar sa. “Ki na da riko my dear, amma na amana. Ba kya da son kanki, kalmar gaba kuwa bakuwa ce gare ki, ko da kuwa yanayin hakan ya bayyana gare ki.” 2
Ta dan dago ta kalle shi, ba mamaki don ta tabbatar wa kan ta cewa ya furta hakan ne har zuciyar sa. “This…” ya shiga shafa gefen fuskar ta hankali, “Wannan dabi’a ta ki, ta rashin son kan ki ta sa na fada kaunar ki. You are one in a million.”
Jin kan sa yake cikin tsananin kaunar ta. Da gaske ne bai san lokacin da son ta ya shige shi ba. Amma ya san halayen ta suna nasaba da hakan. Kai tsaye ya fada kaunar tata, babu ko gargada.
Ta yi ma sa kallon da ya tafi da rabin imanin sa, “Two million fa?”
Ya daga girar sa, sannan ya kara jan ta jikin sa, “Bari na baki wannan amsar.”
Ya lura ta hadiye yawu ta makogwaron ta, hakan ya kara tsima shi. Ya sumbace ta kadan, yana jin zuciyar sa ta na bugawa cikin kaunar ta, abubuwa da dama suna wanzuwa a cikin kan sa.
Ya dan daga kai ya kalle ta, “Har yanzu akwai wata shakka a tare da ke?”
Ta sake wulkita idanun ta tare da lashe lebban ta, “Ammm, ina ga dai sai ka sake yi min bayani.”
Fuskar ta dauke da miskilin murmushi, hakan ya kara jefa shi cikin kogin son ta ya na ninkaya. Wannan karon shi ya hadiye yawu da sauri.
“Ba zai dauki lokaci ba daga bangare na. Amma sai dai ke ce nake ga ba za ki iya dauka ba.”
“Is that a challenge, kalubale ne Dokta Yusuf?” Ta daga girar ta cikin murmushin da kara wanzar da kaunar ta cikin birnin zuciyar sa. Sannan ta zagaye kafadun sa da hannayen ta duka biyu, “Ka fa san ina son kalubale.”
Ya kara manna kan sa tsakanin wuyan ta da kafadu, “You are on babe, yau zan gwada mi ki waye boss?”
Ta na dariya suka ji motsin shigar yara cikin hayaniya. Nan take ta ture shi ta mike tare da gyaran zanin ta. Kafin su isa wurin da suke, ya rike tsintsiyar hannun ta na dama cikin kalar tausayi.
Bai so yaran su dawo daga gidan Hadi ba a lokacin. Yanayin aikin sa ba ya bashi zarafin ganin su a yaushe. Don haka ba ya wasa da lokacin su idan ya samu. Musamman da ‘ya’yan sa.
Ta dan yi dariya mai sautin da ke sanyaya masa jiki, sannan ta matso dab da kunnuwan sa a hankali ta fesa cikin kwarkwasa, “Yau an kashe boss.”
Ya lumshe idanun sa a lokacin da tasirin sautin muryar ta ke ratsa jikin sa. Kafin ya farga har yaran sun shiga dakin da suke a guje. Amatullah ce gaba, ta na sanye cikin doguwar riga mai launin shudi da ruwan hoda. Adon jikin sa kamar leshi amma babu yawa sosai.
Biye da ita kuwa Nurain ne da Aslam, wadan da ke sanye cikin riga maidogon hannu, daya ja, dayan rawaya, sannan wandon su na jins ne.
Dukanin su da takalma a kafar su, in ban da Nurain, wanda ya riko fanka-fankar takalmar mahaifin sa, shi a dole sai an saka ma sa su.
Ganin Yusuf cikin dakin suka sheka da gudu cikin farin ciki don murna, “Paapa!”
Yusuf ya shirya hannayen sa don daga su sama daya bayan daya. A duk haduwar su sai an musu hakan. Wani lokacin ma har tacici da mai da yaji yake wa kowannen su. Ya zauna da kowannen su kusan a cinyar sa yana haki.
“Ya Allah! Me kike ba wa yaran nan ne suke kara nauyi haka?”
“Soyayya…..mai tarin yawa.” Ta amsa, ta na ‘yar dariya.
STORY CONTINUES BELOW
Ya dan kalle ta, “I see. Ya kamata a rika rarraba soyayyar nan don kowa ya samu.”
Ya lura gaba daya kunya ta kama ta. Ta kawar da kan ta kawai ta na murmushi.
“Paapa, Afleen tana ta kuka za ta bi mu, amma Momi Muhibba ta hana ta.” BBC Amatullah ta yi masa bayani cikin turbine fuska. Ita tsabar wayo ma harshen ta sosai yake fita,in ban da furta Kalmar ‘r’ da ke mata wahala. Kamar ba ‘yar shekara uku da rabi ba. Su kuma su Nurain, shekaran su biyu.
Ganin hakan Aslam ya ba da himmar kokari shi ma, ya jijjiga Asiya, “Maama, maama, Afleen biji…bijji..biiji mmm..mmm. kuka.” Ya na bayani har yana kwatance da yatsar sa tare da shan mur.
Dariya ta rika yi, don shi kadai ne bai iya ‘yar maganar su ta yara ba. amma Nurain kam yana tabawa. Amma fa shi din sai a hankali, don bai fiye maganar ba saboda miskili ne shi.
Ya dan kalli mahaifin sa, sannan ya koma kan harkar sa. A ko yaushe Asiya ta gan shi sai ta tuna daukar sa da a ka yi, ta rika tunanin yaya rayuwar ta za ta kasance a ce babu shi a ciki? Shi da dan uwan sa kammanin su daya, amma kuma halayen su kamar rana ne da dare.
“Paapa, a shayo mana baby irin Afleen a ashibiti mu ma.” Amatullah ta sanar da bukatar su.
Asiya, wacce ta gwalo idanu, shi kuma ya kalle ta ya yi dariya, “To ai ba ni ke sayo wa ba. Sai ko Maama.”
Suka juya gare ta, cikin roko da magiya, Ama ta ce, “Maama, a shayo min baby Afleen, in ta washa da ita, ban da su Aslam. Saboda shuna hana ni washa da motar shu.”
Yusuf ya kyalkyale da dariya, “To fa, Maama, kin ji.”
Ta harare shi, hakan ya ma sa dadi. Ko shi kan say a san dai tana karatu ne kam, amma yana matukar son ta sake haifa ma sa baby, musamman mace.
“To Ama, Allah Ya kawo.” Ta fada kawai.
Amatullah ta dage, “Maama, mu je to yanju mu shaya, amma ba irin shu Ashlam ba. Afleen ne nake sho.”
Tabdi! Yaro wai man kaza. Ita kawai a je a lokacin a sayo mata kanwa. Ya ga Asiya ta mike, ta ce, “Oya, surutun ya isa haka. Ku je Gwamma ta ba ku madara ku sha. Wa zai ci macaroni?”
“Ni!” Dukan su suka amsa, ban da Nurain. Suka fice a guje, suka bar shi da kwama takalma, ya na tafiya da kyar.
Yusuf ya kwalla kiran Gwamma ta dauke shi a lokacin da ya fice ya na bin ‘yan uwan sa zuwa kicin.
“Ina ga ya dace a duba bukatar yaran nan.” Yusuf ya ce da ita, bayan sun watse.
Ta dan kalle shi, “A sayo musu Afleen din a asibiti?”
Ya ja ta ya na dariya, “A dai sama musu irin Afreen din.” Ya sake manna kan sa a wuyan ta.
“Saboda lokacin da nayi hoton cikin a satin da ya gabata, wanda Dokta Hadi yayi ya tabbatar min cewa namiji ne.”
Ya kura mata idanu ya ga ko akwai alamar wasa. Ya san zai yi wuya tayi wasa da sunan Hadi. Amma so yake ya kara jin cewa kunnuwan sa ba zagi suka ma sa ba.
Ta sake dora hannayen ta kan kafadun sa, “Yes, za ka sake gyara hannayen ka wajen daga wani babyn sama daga nan da watanni hudu. Umma kuma zata sake yin wani maigidan, tun da ta ce su Aslam sun tsufa.”
Ta kwanta a jikin sa ta na murmushi, “Ni ma hakan nake ji, mijina, abokin rayuwa ta, uban ‘ya’yana. Kai ne rayuwata, wanda ke kawo haske ga zuciya ta a yayin duhu. Ba na jin zan iya rayuwa babu kai a duniya.”
Ya dade da sanin hakan, cewa shi da iyta sun zama daya. Ta kawo ma sa farinciki a rayuwar sa, sannan ta yi sanadin sulhun sa da Khalid, bayan ta yin a ta sulhun da Mariya. Duk da cewar ba shiri sosai da Yafendo ba, an samu saukin abubuwa sosai a tskanin su. Kamar yadda ita din ma a ka samu dan karamar fahimta tsakanin ta da Mariyar.
A satin da ya gabata ne ya ji ta na cewar za ta bikin Mariya da wani ma’aikacin asibitin tarayya, wato FMC da ke garin Azare mai suna Malam Shehu.
Kallo daya mutum zai ma sa ya san danye-canye ne, gara bai nun aba. Amma tun da ita ta kai shi da kan ta, ta kuma amince da zaman istibra’I kafin a yi auren, shi ke nan. A lallaba ne kawai, auren zamani.
Fatan alheri zai bi ta da shi, tare da cikakken fatan ba zata kara bi ta kan iyalin sa ba. Ko da yake, ya tabbata bayan horon da Asabe ta ba shi labarin Asiya ta ma ta, bai yi tsammanin za ta yi kuskuren karawa ba.
Har yau Asiya ba ta fada ma sa ba, shi ma shiru yayi kamar bai ji ba. shi yasa yake kara son matar sa, don kuwa ba a taba ta ta kyale, sai ko idan akwai dalili mai karfi.
Tusshh! Kara fasa gilas ya watsu cikin gidan. Salatin Gwamma wacce ke taimaka wa Asiya da rainon yara ne ya saka murmushi a fuskokin su.
“An kuma.” Ta furta cikin dariya. “I wonder, waye kuma yanzu ya fasa kofin. Don zan iya canka, tsakanin Nurain, wanda ke dagewa da son shan abu a kofin manya, ko kuma Amatullah, mai daukar discipline na yaya baba da muhimmanci.”
Ta yi yunkurin fita ne ya rike hannun ta, “Bar su da Gwamman, za ta kula da komai.”
Ya na jan ta a hankali zuwa gare shi, ta ce, “Ni din kuma me zan zauna yi a nan?”
Cikin rada-rada, ya amsa, “Za ki kula da ni ma na. don ni ma ina bukatar wannan siyayyar da a ke cikawa wa yara. Zan so ki ci gaba da kula da ni har gaban abada!”
“My darling, wannan karon akwai wucin gadi cikin yarjejeniyar?” ta tambaye shi da lankwasasshiyar murya.
Ya dan yi dariya, “Kwarai, wucin gadin tsawon rayuwar mu ta duniya, kafin mu zarce don ci gaba a aljanna.”
“In dai hakan ne, ka samu yadda kake so.”
Wata dariya ya sake, mai ratsa zuciya yare da watsa sanyi a dukkan illahirin mai sauraro. Dadi ne cike fal da zukatan su, domin rayuwar da suka amince wa junan su tare ta zarce har zuwa aljanna. Fata daya suke, Allah Ya sa su cika da Imani. 3
Da wannan ya tura kofar dakin su, ni kuma na tattara komatsai na. Sai jango, sai doji, sai jiim, Allah Ya tabbatar mana da mafi kyaun alherinSa!