KUNDIN KADDARATA CHAPTER 3 BY HUGUMA

KUNDIN KADDARATA CHAPTER 3 BY HUGUMA

 

 

 

Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayi jim yana jiran amsa sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar
“Da wa nake magana?”,cikin karyar da murya akace
” mukhtar baka ganeni ba,fa’iza ce fa”
“Fa’iza?,wacce fa’iza” wani murmushi akayi mai fidda da sauti cikin siga ta nufin jan hankali
“Fa’iza amaryarka mana”.

Hade rai yayi kana cikin dakiya yace”ok,ya akayi?”,sake marairaice murya tayi
“Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?”
“Yayi kyau,ina gajiya?”
“Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin sake zuwa guna bakayi,haba”
“Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?” Kai ta girgiza kamar tana gabansa,cikin ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa
“A’ah ba shi bane”
“Fadi uzirinki kai tsaye”.

Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana
“An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka bawa uwar gidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantar ciki da falo”tana direwa ya dora
“Ko?,a wanne hadisin?”.

Fara quluwa tayi amma ta dake”haka na ya dace ai”
“To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki haqqinki” ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don kada kwabarta tayi ruwa
“Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba” tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki.

Itama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare.

Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tana jiran dawowarta,ita ta gyare mata jikinta fes,zuwa la’asar ta fito shar,fatarta ta sake wani kyau da haske.

Tsokanarta sosai mukhtar ya dinga yi,yana mata waqa
“Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)” dariyar itama ta dinga yi.

Ranar juma’a aka zo aka mata lalle ja da baqi,ta aika halima da zainab suka karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya.

Wuni tayi babu laifi ta dan tara jama’a,sosai mutanen unguwar suka yi mata kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata suna jira a kawo amarya su karbeta.

Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya kada ‘yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshe jikinta sannan ta nemi baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo.

Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na darw babu ita babu alamarta,hakan ya sanya maqotam suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa ‘yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za’a bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama suka tafi,maman nana kawai ta rage.

Qarfe goma na dare maman nanan na shirin tafiya itama ganin shirun yayi yawa sai ga hayaniyarsu da ta motocinsu,hakan ya sanyata ta koma ta zauna tana tsumayin isowarsu,saidai ga mamakinta yadda akeyi a al’adance a fara kai amarya ga uwargida su ba hakan bane,dakinta suka bude kai tsaye suka shige da ita suna faman yada kirari tamkar jinin maroqa
“Shiga da bismillah uwar ‘ya’yan mukhtar”.

Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana
” maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba”dan murmushin kwantar da hankali tayi mata
“Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni’imal wakeel,ni’imal maula wa ni’iman nasir” kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya hannunta ta share tana mai bawa kanta qwarin gwiwa tare da hana kanta da kanta kuka.

Labule aka bankade aka shigo,fiddausi cs goye da ‘yarta,ta dubi sumayyan sannan tace
“Kije dakin amarya,yaya bara’atu na son ganinki”,cikin mamaki maman nana ta dubeta
” a’ah,ai ba’a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?”duban maman nanan tayi sai ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.

Ko minti daya ba’a qara ba saiga yaya bara’atun ta shigo
“Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da sumayya kawai zakiyi,don zama fa’iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don ta tafi ba,saboda haka ke sumayya ina jiranki”, wani abu yazo ya tokare maman nana a wuya,tamkar zata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun ya juye kan sumayyan wanda bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji.

Itama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya har zuwa dakin marya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.

Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata shigowa dakin,wata ‘yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube fuskarta da mayafi tace
” to sumayyatu,ga ‘yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman lafiya,muna fata zaku hada kanku ku zauna lafiya”
“Kowa ya kwana lafiya ai shi yaso ato,fa’iza dai gata nan zama daram ila yaumut takunu” yaya bara’atu ta karbe zancan daga gun tsohuwar,rai bace maman nana ta daga kai ta dubi yaya bara’atu,mamaki take bata,wai ‘yar yarinyar da duka duka take cikin shekaru na sha takwas take zagewa babba da ita tana yadawa wadan nan habaice habaicen da suka girmi kanta,babu lallai ma kan nata ya iya dauka,ina laifi ma ta bar yaranta masu shekara sha hudu sha biyar su gayawa sumayyan?,wata qila ace wadan nan sine dai dai da ita,amma ba ita ba wadda ta kusa linka shekarun sumayyar ba.

Ta tabbatar idan taci gaba da zama cikin dakin tabbas za’ayi batacciya da ita,bata so kuma wani abu na tsiya ya hadasu,tunda duk tsiya tafiya zasuyi ba zasu shekara ba,kuma gidan dan uwansu ta shigo sunci albarkacinsa,tunda mukhtar kowa ya shaidi halinsa,sai ta kama sumayyar ta miqar sannan ta ari bakinta ta ci mata albasa,don ta fuskanci ba zata iya magana ba kuka take qasa qasa kanta duqe
“Insha Allahu baba babu wata matsala,don sumayya bata da damuwa mu mun shaideta tun tana tatsitsiyarta muke tare da ita,zaman lpy an sameshi an gama da izinin Allah”
“To Allah ya yarda ‘yar nan” cewar tsohuwar.

Da sauri ta janye hannun sumayyan suka fice saboda ta soma ganin bakinsu yana motsi suna shirin fara qananun maganganu,sai data tabbatar sumayyan ta samu nutsuwa kana tayi mata sallama ta tafi,zuwa lokacin suma ‘yan kawo amaryar suna qofar gida suna shirin tafiya.

Sha daya na dare agogon falon nata ya nuna mata,gidan yayi shiru kowacce na dakinta,sauqinta daya akwai wutar nepa da ta haskake ko ina cikin gidan,ta sauke ajiyar zuciya tana ci gaba da jan hasbunallahu wa ni’imal wakil,har zuwa lokacin da taji an turo qofar gidan an shigo,sai ta miqe tsam a tsorace kasancewar basu taba barin qofar gidan nasu haka ba.

Tana ji aka rufe qofa ta biyu hakan ya alamta mata cewa mai gidan ne,ta aauke ajiyar zuciya duk da cewa tana tsayen bata zauna ba.

Da sallama ya daga labulen dakin idanunsa ya sauka a kanta,ta kowa yayi a hankali ya shigo dakin yana dubanta yadda tayi carko a tsaye,cikin sanyin murya yace
“me kikeyi a tsaye haka kamar wadda taga wani abun tsoro” ta saki ajiyar zuciya,muryarta a sanyaye tace
“Ji nayi ana taba qofa ne”,murmushi yayi yana ajjiye ledojin hannunsa
” ke kam farar kura ce sumy”sai tayi murmushin yaqe tana kawar da kai,ta qarasa inda yake tana masa sannu da zuwa ya amsa yana zama kan daya daga cikin kujerun falon
“Hada min ruwan wanka sumayya” ta danyi sororo kamar tace wani abu sai kuma ta fasa tace to.

Wanka yayi sannan ya sauya kayansa,falon ya dawo ya zauna yana maida numfashi cike da gajiya,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kowa ya rasa abinda zaya cewa dan uwansa har kusan sha daya da rabi.

Motsi suka dinga jiyowa a tsakar gida,kallo juna suke suna sauraron motsin ba tare da kowa ya cewa kowa komai ba,sumayya ce ta fara fahimtar amarya ce,sai ta dubi mukhtar
“Ya mukhtar bacci nakeji”
“Hala ma korata kike da dabara ko?”kai ta kada zuciyarta a cunkushe
” a’ah ya mukhtar ba haka bane”shiru yayi har kusan mintina goma wanda motsin da suke ji na qara qarfi kadan kadan.

Miqewa yayi ya dauki leda biyu cikin ledojin da ya shigo da su ya tura mata daya sannan yace
“Tashi muje ki rakani” daga kai tayi kawai ta dubeshi,tamkar tace ba zata ba amma sam bata iya rashin kunya da gardama ba,kuma ba zata fara a kan ya mukhtar din ba da take ganin qimarsa.

Mayafinta ta janyo ta yafa sannan ta miqe,tare suka jero har zuwa qofar dakin.

A tsaye suka sameta a bakin qofar dakin,tana ganinsu tayi hanzarin komawa kan kujerar ta zauna,saidai kallo daya zaka mata ka fuskanci ko kadan babu walwala saman fuskarta.

Mazauni kowanne ya yiwa kansa,shiru ya dan ratsa,sumayya ta gyara zama tayi qoqarin cewa
“Sannu amarya”
“Uhmmm” kawai ta fadi,shirun suka sakeyi,sai da ta mula don kanta wai ita an mata laifi kana ta gaida mukhtar din,ya amsa sannan ya fara magana,daki daki daga bisani ya gangaro ga rufewa
“Daga qarshe ban auroki don ki raina min mata ba,ban auroki saboda sumayya ta gaza ta kowanni fanni ba,ina son mata ta matata tana sona,bana son tashin hankali cikin gidana,na riga da nasan halin sumayya tun tana mitsitsiyarta,saboda haka ku hada kanku ku zauna lafiya…..haka kema sumayya duk da nasan ki tun ba yau ba baki da matsala,inaso ki dore kan halayenki kada kice zaki sauya,saboda bazan lamunci rashin gaskiya ba……akwai wani sauran mai magana?”.

Jin shiru ya sanya duka suka gane ba zata yi magana ba,sai cika da take tana batsewa,hakan ya sanya sumayya cewa
“In sha Allah ba zaka samemu da matsala ba,zamu zauna lafiya da junanmu,Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu”
“Amin amin” miqewa sumayyan tayi sai shima ya miqe
“Muje na rakaki ko” duk da suyar da ranta yakeyi amma sai da yasa ta dan murmusa,ina dakin fa’izan ina dakinta.

A tsakiyar falon suka tsaitsaya suna kallon juna,hannayenta ya kama a sanyaye yace
“Kiyi addu’a ki kulle qofar dakin,kiyi bacci sosai kada ki sa damuwa a ranki,mukhtar naki ne kinji ko” kai ta gyada
“Sai da safe” ya fada yana juyawa a sanyaye.

Duk yadda taso danne qwallar data cika mata ido abun ya faskara,duk yadda taso jurewa ta kasa,ashe kishi gaskiya ne haka yake?,ada idan ana zancan shi dariyarta take tuntsirawa abunta,sai ta cafko hannunsa ya waiwayo yana dubanta
“Ya mukhtar,ka zama mai adalci tsakaninmu,don Allah kada ka wofantar da ni” kai ya gyada ya janyota jikinsa ya rungumeta yana share mata hawaye yana fadin
“In sha Allah” sai da ya tabbata ta hau gadonta ta kwanta sannan ya fice ya rufe mata qofar.

Ta rufe idanunta a hankali tana fata bacci ya dauketa,karo na farko kuma rana ta farko a shekarun aurenta da zata fara kwana ita daya cikin dakinsu kan gadon su.

Idonta ta runtse tana jin qarar rufe maga qofar da yayi,ta gefe daya ta kwanta ta sake mirginawa daya gefan,gaba daya take jin gadon yayi mata fadi.

Ganin tana neman cinhe daren idanu biyu ya sanyata runtse idonta,ta damqe filon da take kai tana fadin
“Ya rabb,afrig li sabra” tayi ta maimaitawa babu qaqqautawa,Allah maji roqon bawansa,bata san lokacin da wani bacci ya sadado ya sace ta ba.

Qarfe shida ta farka firgigit tana ambaton sunan Allah,tayi mamakin yadda tayi bacci mai nauyi irin haka,cikin mutuwar jiki ta sauko daga kan gadon ta fito.

A hankali ta murda qofar dakin nata kana ta tura ta ta bude,tashin farko idanunta suka sauka kan qofar dakin fa’iza amarya,qofar dakin na kulle gam da alamu ba’a bude ta ba tunda aka rufe,sai taji wani qunci na ziyartar zuciyarta,ta kau da kai tana jan tsaki kana ta wuce bakin fanfo,ta taro ruwa ta shige bandaki ta kama ruwa sannan ta fito ta daura alwala.

Har qarfe takwas na safiya tana saman abun sallar,ta kalli agogo sannan ta janyo rediyonta data kunna wadda ita ta tayata zama ta kashe,ta miqe ta zare hijabin jikinta ta ajjiye ta fito zuwa tsakar gidan,ta saba tun tuni da kammala ayyukanta da wuri saboda ya mukhtar bai wuce goma a gida.

Idanunta suka sake sauka kan qofar dakin karo na biyu,sabanin dazu yanzu an sassauta rufin qofar da alama an budeta ne,sake dauke kanta tayi sannan ta shiga ayyukanta kamar yadda ta saba.

Sai da ta tsabtace ko ina har zuwa dakinta sannan ta shiga tayi wanka,tsab ta shirya cikim daya daga cikin ragowar sabbin dinkunanta,atamfa ce dinkin riga da skert da ta fidda shape din qugunta yayi das,bata sake yarda da kyawun dinkin ba sai da taga yadda yayi mata a jikinta,maman nana ce ta zabar mata shi.

Tsakar gidan ta dawo,kitchen ta shiga,sai yanzu taga jeran da aka ma fa’iza,za’a iya cewa ta fita duk wani kayan aiki na kitchen nesa ba kusa ba,bangaren ta ta nufa ta wanke tukunya ta tara ruwa ta dora ruwan tea wanda ya sha hadin kayan qamshi sannan ta koma gefe ta fara fere dankalin turawa,babu abinda mukhtar din bai siya ba na kayan abinci tun shekaran jiya.

Aikin take amma zuciyarta a cunkushe take,fuskarta kawau zaka kalla ta gaya maka hakan koda bata bude baki ta fada ba,ta gama firar ta wanke sannan ta juye shayin cikin wani sabon tea flask wanda yake seat ne da farantansa da kofuna.

Tana cikin suyar dankalin ta dinga juyo motsi a tsakar gidan,bata fasa abinda take ba kamar yadda bata damu tasan waye cikin su biyun ba,aikinta taci gaba da yi har lokacin da taji hancinta ya cika da qamshin turaren mukhtar,kamar ta waiwaya sai ta fasa,wani haushinsa ta dinga ji tana ji hakanan.

“Sannu da aiki uwar gida na” taji ya ambata yana takowa zuwa cikin kitchen din,ta dan waiwayo hannunta riqe da abun tsame dankalin yana tsaye a bayanta gab da ita,maimakon ta tarad da annuri da qyalli irin na ango sai ta tarad da sabanin hakan,fuskarsa tana nan kamar kullum
“Ina kwana” ta fada a taqaice fuskarta a daure ba tare da ta damu da yanayin fuskarsa ba,maimakon ya amsa sai taji ya sanya hannu ya karbe abun tsamewar ya matsa gefanta ya shiga kwashe dankalin wanda shi yayi saura cikin man
“Sumy,me yake faruwa?” Ya tambayeta yayin da take jingine da kantocin fa’iza hannunta harde a qirjinta
“Kamar me?” Ta tambayeshi tana debo qwan da zata soya tana zubawa cikin kwano,ya bata amsa sanda yake qwace bowl din ya fara fasa qwayayen
“Babu fara’ar nan a fuskarki yau ko kadan” shiru tayi masa bata da niyyar fankawa,ganin haka yasa shima ya ja bakinsa ya tsuke har ya kammala suyar.

Nata kayan karin ta diba ta kammale musu nasu a kitchen ta wuce dakinta,tana zaune kan kujera tana kallon mbc yayin da take zarar dankalin da dai dai da dai dai tana ci tamkar bata so mukhtar ya shigo dakin,yayi kyau cikin dinkin shadda ruwan qasa mai turuwa sai qamshi ke tashi
“A’aha,ya kike karyawa ke kadai ina namu break din”
“Yana kitchen” ta fadi tana ajjiye plate din hannunta,kai ya girgiza yana zama gefanta
“Ba haka na tsara ba,ki shirya mana a nan falon naki,gaba daya zamu karya,daga nan ki shiga ki kira fa’izan” bata ce komai ba ta miqe ta fita din ta dinga kwaso kayan tana jerawa har ta kammala.

A qofar dakin ta tsaya ta qwanqwasa mata,tunda tana ganin bai kyautu ta fada mata kai tsaye ba tunda ba falo gareta ba,sai data qwanqwasa kusan sau biyar sannan tace cikin alamun fusata
“Wai waye ne?”
“Sumayya ce”, sai data bata kusan minti biyu sannan tace
” shigo”ciki ciki kamar wadda aka cusawa tsumma a baki.

Kan gado ta tarad da ita kwance,ta samu gefan kujera tadan dosana tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta
“Sannu amarya” cikin shan qamshi da dauke kai tace
“Yauwa” ta danyi jim sannan tace
“Amm…..dama mukhtar ne yace ki fito mu karya” shiru tayi kamar bata ji ba sannan ta bude baki da qyar tace
“Bazan samu fitowa ba,kuna iya karyawa”, bata sake cewa komai ba ta miqe ta fice ta isarwa da mukhtar saqon,kai ya kada sannan yace da ita
” zauna mu karya”gefan kujera ta zauna tana kada kai
“Nikam na qoshi”
“Ban son musu kinji ko,oya sauko” ya fada yana hada tea cup biyu,bata sake cewa komai din ba ta sauko ta karbi cup din tea din daga hannunsa ta fara kurba.

Duk yadda yaso janta da hira ta kasa sakin jikinta sama sama take amsa masa shima bai tsawwala ba har suka kammala ya miqe ya ajjiye mata kudin cefane ya fita.

Tattare kwanukan tayi da nufin fita da su ta dauraye,a bakin qofa taga fa’izan a tsaye mukhtar na bakin qofar yana sanya takalminsa,fuskarta a quntace da alama wani maganar take gaya masa
“Sai na dawo” ya fada bayan ya kammala sanya takalminsa,bata ce komai ba sai komawa dakinta da tayi rai bace,sumayya ta miqe daga durquson da tayi ta bi bayansa ta bude masa qofa kamar yadda ta saba
“A dawo lafiya Allah ya kiyaye ya bada sa’a”
“Amin my sumy” ya fada cikin jim dadi.

Bakin famfon ta dawo taci gaba da wanke wankenta,tana iya jiyo qunquni daga dakin fa’izan wanda batasan dawa take ko me take cewa ba.

Tana gab da gama wanke wanken taji ta turo qofar ta fito,qerere tayi a kan sumayyan
“Ke” ta fada cikin gadara,dago kanta tayi a hankali tana dubanta,sai yanzu ne zata iya gane kamannin fa’izan,baqa ce sosai mai matsakaicin jiki,bata da qiba bata da rama,tana da dogon hanci mai tsini sai qananun idanu,aqalla ta tasamma shekara a shirin da uku zuwa da hudu zata bata shekaru biyar ko shida kenan
“Yana kitchen” ta fada tana ci gaba da wanke wankenta zuciyarta na bugawa,addu’a take cikin zuciyarta kada Allah ya sanya fa’iza na daya daga cikin masifaffun kishiyoyi,indai ko haka ne bata san ta inda zata sanya kanta ba,bata san inda ta inda zata fara tarar wannan bala’in ba,mutum ce ita tun asali da bata son tashin hankali saboda sam bata iya ba,wani tsaki ta ja sannan ta juya zuwa cikin kitchen din.

Sai gata ta fito hannunya dauke da flask din data zuba mata dankalin don kada yayi sanyi,bude flaak din yayi ta sake tsayuwa a kanta cikin hayaniya tace
“Wai ke,kina nufin wannan abun zanci da ya sassanqame yayi sanyi?” Sai ta kuma dagowa tana dubanta
“Ina zaton kamar baiyi sanyin da zaki kasa ci ba,tunda cikin flask yake ko” tayi shiru tana jira taji ko zata tanka
“Shi yasa tun dazun ya mukhtar yace ko fito mu karya din gudun kada yayi sanyin”ta fada tana dan murmushi

Zaro ido tayi cikin masifa
“Iyeee,ashe abinda ake fada gaskiya ne lallai yarinya baki san wace fa’iza ba to banyi niyyar karyawar ba alokacin,ko dole ne?,gidan miji na ne fa,saboda haka babu wanda ya isa ya takurani sai abinda naga dama shi zanyi,saboda haka ki kiyayi shiga hurumina” ta juya fuuu ta shige kitchen din.

Ita dai binta kawai tayi da ido abun na bata mamaki,me tayi mata daga yin maganar da bata kai ta kawo ba?,tana tattare kayan zata maida kitchen din sai gata ta fito hannunta dauke sa dan matsakaicin kwandon tace taliya cike da dankali daya hannun wuqa da kujera ‘yar tsuguno ta dawo bakin kitchen din ta zauna.

Bata ce mata komai ba ta rabe ta ta shiga kitchen din ta maida kayan wanke wanken muhallinsu ta jera ta sake goge gurin sannan ta fito.

Zamanta kenan taji muryar yaranta na sallama,murmushi tayi tana miqewa,ko banza ta samu anokan debe kewa,don ta lura fa’izar akwai matsala tattare da ita,haka take ko wani abun ke damunta oho Allah masani,miqewa tayi ta fito da tabarma hannunta,da yake wani lokaci idan bata so su bata mata gu a tsakar gida suke zamansu.

Tana shimfida tabarmar yaran na gaida fa’iza da dai dai da dai dai,ta amsa musu babu yabo babu fallasa,suka qaraso gun antyn tasu.

Tana tsakiyarsu tana biyewa surutunsu,fa’iza na kitchen tana fama da suyar uban dankali da qwai wanda a zahiri yafi qarfinta,so take tun daga yau ta fara nunawa sumayya ikonta cikin gidan kafin ta haifo yaran da zasu zama ajalin zamanta cikin gidan,kamar yadda yake cikin KUNDIN BURINSU ita da su yaya yahanasu.

har zuciyarta sumayya take jin dadin hirarta da yaran,duk wani bacin ranta ya gudu,ta miqe ta nufi kitchen don dauko dankalin da fa’izar taqi ci ta rarrabawa yaran don kada ayi asararsa,a nan taga uban dankalin da fa’izar ke soyawa daidai lokacin data kammala ta juye cikin babban bowl da tadauka ta fice,bata tanka ba tunda dazun ta fara mata da jan kunnem fita daga sabgarta.

‘Yar carafke yaran keyi musu ya sarqe tsakaninsu kan rinton da aisha tayi musu,sumayya nata qoqarin sulhuntawa,tsawa suka ji wadda ta sanya su yin shiru baki dayansu suka waiwaya suna kallonta
“Dalla malamai kun cikawa mutane kunne,ina buqatar nayi ramuwar bacci kun hana mutane aikin banza aikim wofi,to wallahi bazan lamunci takura cikin gida na ba ku kintsa bakinku” ta banko qofar tata ta shige ciki.

Tsuru tsuru yaran sukayi saboda basu taba ganin an musu haka cikin gidan ba,sumayya ce tayi qarfin halin yin murmushi sannan ta miqe cikin son bagarar da abinda tayi musun
“Ku zo kuyimin cefane maza” nan suka miqe da hanzarinsu kuwa ta rararba musu aiken suka fice,yayin da ita kuma ta tattare tabarmar ta sake share gun kafin su dawo,sannan ta moma kitchen ta gyara duk inda fa’iza taci ubansa har bangaren fa’izar duka.

Bayan sun dawo ta gyara kayan miyar ta bada suka kai mata markade,suna dawowa ta rarraba musu alewa ta turasu gida ganin qarfe daya na rana tayi saboda zuwa islamiyya.

Shinkafa da miya da wake tayi niyyar dafawa a abincin rana,tunda mukhtar ya aiko da nama daga kasuwa,tana tsakar gida tana yankan salad ta juyo sallama da muryoyin mutane,ta daga kanta tana amsawa,baqi ne su kusan shida
“Sannunku da zuwa” ta fada fuskarta a sake,shigewarsu sukayi yayin da uku daga ciki suka juyo suka mata kallon banza kana suka wuce,sanyi sosai jikinta yayi,wai dama haka ake?,haka ake kishin ne wai?,ita kam sam bata sani ba ji take qwaqwalwarta ta kasa jan zaren ko wanne tunani.

Tana nan tana yanka salad din ta soma jiyo tashin maganganunsu gami da shewa
“Wai dama wannan ce kishiyar taki?
Cab di wannan ai ma’aikaciya kurum kika samu
Lallai ai wannan banga abun kishi ba
Ke irinsu fa sunfi iya tsiya wallahi,kada ki soma cewa zaki sakar mata fuska balle ta rainaki,ki dasa mata tsoronki,bada umarni ne kawai tsakaninku
Wallahi ki bautar da shegiya,ki mori bati” take taji jikinta ya kama rawa gabanta ya shiga faduwa,lallai ba shakka suna iya dukanta,haka zuciyarta ta dinga raya mata,zuciyarta tsoro fal irin na yarinta,su kamsu suna sane suka dinga maganar don ta jisu,saboda su dasa tsoro cikin zuciyarta.

Kitchen din ta tattara ta koma tana ci gaba da ayyukanta,sai dai har yanzu tsoron bai saketa ba,addu’a ta dinga yi cikin zuciyarta hakan ya sanya ta dan samu nutsuwa.

Tana gab da kammala girkin fa’iza ta shigo kitchen din ita da daya daga cikin baqin nata tana fadin
“Ga bangare na nan,ki dafa duka abinda kuka ga ya muku yadda zai isheku” sumayya ta waiwayo tana dubanta
“Amma amarya har da ku nayi abincin fa zaya ishemu duka,ina ga idan aka dafa wani zaiyi yawa” juyowa itama tayi ta zabga mata wata harara sannan ta nunata da yatsa
“Ina cewa ko awa biyu ba’a yi ba da yi miki maganar ki guji shiga sabgata ba ko,ke har kin isa kina sa’ar qanwata ki dinga dafawa kina bani iya limit din da kika ga dama ina ci?,kin shirya cin na jaki kenan,don wallahi jibgarki zanyi a gidan nan banza juya kawai” sai ta dauke kanta daga garesu ta maida kan girkinta,abun mamaki sai kalmar juya yau tayi mata zafi,karo na farko kenan da ta taba jin hakan.

Tana jinta ta gama gayawa baquwar tata abinda za’ayi ta fice,bakin fanfo ta wuce ta tari ruwa ta shiga wanka don sai yanzu ta samu damar yin.

Tana kammala girkin ta zubawa mukhtar nashi,ta zuba nasu fa’izan ta aza a bangaren kantarta ta dibi wanda zata ci ta shige daki abinta,bata sake fitowa ba har suka gama tsiyar da zasuyi suka tafi wajen qarfe biyar na yamma,a sannan ta fito ta shiga kitchen don dora ruwan wanka.

Tamkar ba’a taba guara kitchen din ba haka suka lalatashi,ga uban abinci nan da suka dafa sun kasa cinyeshi cikin tukunya a bude,kwanukan duka vikin sink din fa’iza gaje gaje,hatta wanda ta ajjiye musu sun cakalkala shi sun bar cooler rabi a bude rabi a rufe.

Ranta taji ya baci karo na farko,ta tsani almubazzaranci da abinci,saboda tana da imamin abinda ka raina shi wani ke nema yasa a bakin salatinsa amma ya gagareshi,to don me kai don Allah ya baka zaka wulaqanga,bayan ya baka ne ba don kafi kowa ba.

Bata gaji ba bayan ta dora ruwan ta soma tattara kitchen din,ta gyara ko ina fes,saidai batasan ya zatayi da abincin ba tun kafin mukhtar ya gani yaji babu dadi,ita ba leqe take ba kuma yaro gidan bare ta samu almajiri ta bashi,dole ta jira dan aike yazo.

Ruwanta na zafi ta juye ta shiga wanka,can ma sai da ta tsaya ta gyara,sam bata qaunar taga guri ko yaya ya sauya yanayi.

Taji qarar babur dinsa sanda take maida kaskon turaren wuta kitchen,sanin cewar gidan a bude yake ba kamar sanda tana ita daya ba saboda haka ta toge a tsakar gidan tana jiran shigowarsa.

Cikin mintuna ya qaraso tsakar gidan,tana murmushi ta qarasa inda yake tana niyyar karbar jakarsa,sai ya bude hannayensa ya kai mata runguma sai ta goce tana murmushi tare da kallon qofar dakim fa’iza,qasa qasa da murya tace
“Bamu kadai bane fa a gidan” ta miqa hannu ta karbi kayan hannun nasa,sai ya kalleta yana turbune fuska
“Haka kawai tun yau an fara shiga haqqina,ai shikenan” yayi maganar yana wucewa dakinsa ta bishi a baya tana masa gwalo.

Har ta kammala kintsa abinda ya shigo da shi babu fa’iza babu alamarta,sai da ta gama zata fita daga dakin sukayi kacibus da fa’izan na shigowa,harara ta balla mata,gefe ta matsa ta raba ta kawai ta wuce.

Tunda ta gabatar musu da abinci tayi alwalar sallar magariba shigewarta daki,bata sake fitowa ba sai da taji mukhtar na qwala mata kira,ta miqe a hankali ta gyara daurin dankwalinta ta amsa tana fitowa.

A kitchen ta tadda shi tsaye ransa bace yana qarewa himilin abincin kallo,gefe guda kuma ga dankali da qwai da fa’izan ta soya a wulaqance cikin cooler ba’a idasa cinye shi ba,ya dago idanunsa daga kallon coolers din ya maida su ga sumayya,da hannu yayi mata nuni
“Me wannan?,meye haka sumayya?” A ladabce tace
“Nima ban sani ba ya mukhtar saidai ka tambayi amarya” baiyi musun hakan ba tunda a gefanta yaga tarin coolers din,ya daga murya ya qwala mata kira,ta shigo kitchen din sanye da hijab
“Gani” ta fada tana kallonshi.

Ya kalli kayan ya kalleta sannan yace
“Wannan na waye?”
“Na baqin da nayi ne” ya hadiye wani takaici saboda yadda tayi maganar cikin halin ko in kula da nuna rashin muhimmancin laifinta,wacce iriyar yarinya ce ita,yinin farko kenan a gidan mijinta?,yayi qoqarin danne bacin ransa yace
“Na lura kamar harda dankali ya akayi aka dafa abinci yayi yawa haka?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *