A tsakar gida zainab ta sake shimfida musu wata tabarmar suka koma ciki.
Hira sosai suka dinga yi har da mama,abdur rahman na basu labarin garin ma’aiki madinatul munawwara har aka kirayi sallar magariba,tare suka fita sallar shi da malam da yaya abubakar,koda suka dawo ma bai tafi ba tare suka ci abincin dare sannan ya musu sallama.
Hannunsa dauke da abdallah ya fito daga gudan,bahijja da sumayya na bayansa wadda ta fito don ta dan taka musu,a bakin motarsa sabuwa da ya sauya qirar range rover yaja burki yana duban sumayya
“Tsarabar abdallah bata qaraso ba,ko zaki dan rakamu waccan titin dake gabanku naga akwai wami super market na dan masa siyayya kafin su iso?”. Kai ta kada tana dubansa
” haba sabida dorawa kai wahala,mun yafe duk sanda suka iso ma amsa”.kunu ya dan sha yana dubanta
“Dorawa kai wahala kuma?,niba babansa bane?,ko kina so kice ba yarona bane?” Baki ta bude tana dariya tare da dubansa tace
“Ni na isa in fadi haka,kai matsala ta da kai son girma fa”
“Ban kai naso girma ba ko sumayya?” Ya fada cikin wani irin salo da ya sauya yanayin muryarsa idanunsa cikin nata,wanda ya haifarwa da sumayyan rage farashin dariyarta,karon farko da taji duban qwayar idonsa ya mata nauyi,sai ta janye idonta tana cewa
“A’ah,ai ko da sakan daya mutum ya girmeka ya girmemaka har abada” dan shiru yayi sannan ya gyara tsaiwarsa yana miqa mata abdallah
“Karbeshi yau mun wunar muku,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu” ta amsheshi tana cewa
“Allah ya nuna mana goben” cikim zuciyarta ta dauka da wasa yake,hannun abdallahn ya bude ya sanya masa ‘yan dubu dai dai guda uku yana cewa
“Kasha sweet my son”
“Habba abdur rahman….”
Katseta yayi ta hanyar cewa
“Shshshshsh!,ai bake na bawa ba ko?,kuma wai bakijin kunyar fadar suna na haka gatsal?” Galala ta saki idanu ta bishi da kallo
“Kunyar kamar yaya?” Ta fada tana dubansa,murmushu kawai yayi ya bude gaban motarsa ya zauna sannan yace
“Sai goben ko ‘yamma ta?” Murmushi ta saka mamakin abdur rahman din na kuma kasheta
“Nice kuma yau ‘yammata abdur rahman ga yaro na a hannu?”
“Oh,kuma fadar sunan nawa dai kika yi?” Ya tambayeta yana kada kai,shuru ta masa tana zagayawa wajen bahijja ta dubeta
“Bahijja ki gaida mama kinji,naga alama wannan yayan naki bayan karatu sa ya tafi qarowa ya qaro yadda ake canjin hali” dariya bahijjan tayi tana amaa mata da zata ji,shima dariyar yayi sannan ya tada motar tasa yayin da sumayya ta shige gida.
Tunda ya shigo da motarsa layin su sumayyan ya hagi tsaiwar wata motar a qofar gidansu,har zuwa yanzu da motar tazo ta wuce ta gefan tashi yana binta da kallo tare da qoqarin tantance waye a ciki,saidai duk qwaqqwafinsa ya kasa gane waye a ciki saboda glasa din motar mai duhu ne,hakanan sai yaji wani abu mai tauri ya riqe masa wuya,rabin ‘yar walwalar da ya samu wunin yau ta kau baki daya,a sannu yaci gaba da tuqa motar tasa har ya qaraso qofar gidan ya tsaya ya fito ya samu yaro ya aikashi ciki,ba jimawa yaron ya fito dama sun riga da sun saba duk sanda aka aika akace ana gaida mama to mukhtar din ne kuma sun san me yazo yi,sai halima ko zainab ta kawo masa abdallahnsa,nan cikin mota yake zama da shi su qaraci wasan su sannan yayi horn su fito su karbeshi da abinda ya kawo masa sannan ya wuce,sau tari yakanji sha’awar ganin sumayyan saidai babu wannan damar,rabon da ya ganta ma bazai iya tantance adadin kwanakin ba,tilas yaje danne komai don ya sani a yanzu ta fita a huruminsa.
Yau din ma kamar kullum hakan ce ta kasance,abdallahn nata masa gwalanto saidai bai gane me yake cewa ba biye masa kawai yake,bai wani jima ba ya maida shi ya tafi zuciyarsa na sakutarsa kan motar da ya gani,ya mance cewa a yanzun sumayyan rabon mai rabo ce ba mallakinsa bace
**** ***** ****** ****
*BAYAN KWANA BIYU*
Tun daga ranar abdur rahman ya maida gidan gurin hirarsa,wani lokaci yazo shi kafai wami lokaci ya taho da bahijja,da yake su biyu Allah ya bawa mamansu,sukan dauki lokaci da sumayya suna hirarsu,yayin da wani lokaci idan ya furta wata maganar sai ta sanya ta a duhu,wani sa’in takan yi murmushi ta alaqanta hakan da girma da abdur rahman din ya sake yi,ya fara zama babban mutum shi yasa yanayin hirarrakinsa suke sauyawa,bata taba kawo komai cikin zuciyarta ba saboda ita din rainon mutum daya ce da mutum daya ta taba gina duniyarta wato mukhtar,ba komai take iya ganewa ba ko fahimta game da wasu baqin al’amura a gun d’a namiji ba.
Sau biyu mukhtar na katarin ganin motar na tasiwa daga qofar gidansu ta fice daga layin,saidai har yau bai samu nasarar gano waye ba,lamarin ya tsaye masa a zuciya,duk da yasan baida hurumin hakan amma zuciyarsa ta gaza daurewa,hakan ne ya sanyashi cin washin zuwa ya tadda ko waye.
Tunda ta fito daga makarantar tasu ta lura yake bin bayanta cikin mota wanda hakan ya matuqar tsorata ta musamman data lura yau unguwar tasu babu yawaitar jama’a,hakan ya sanya ta qarawa qafarta sauri.
Ganin tana neman bace masa ya sanya shi faka motar sannan ya fito ya biyo bayanta,gabanta taga an sha wanda ya hakan ya dan tsorata ta taja baya taba dubansa,matashi ne wanda a qalla zaiyi shekara arba’ain da biyu,dogo ne baqi maras jiki sosai,za’a iya karansa da chaculet colour,babu laifi yana da kyau dai dai gwargwado,kana kallonsa kasan yana cikin rufin asiri da wadata dai dai gwargwado
“Assalamu alaikum” ya fada yana murmushi wanda sallamar ta dauke kaso mafi yawa daga cikin tsoron da ya cika zuciyarta,cikin qarfin hali ta amsa masa
“Don Allah kiyi haquri,nasan ban tsaidaki a yanayin da ya dace ba,nidai suna na lukman,na gaza daurewa zuciya ta ne shi yasa ni aikata hakan,na lura kamar a darare kike da ni,idan ba zaki damu ba ki bani lambar wayarki sai muyi magana” kamar kuwa ya sani a takuren take,saboda wannan shine karo na farko da ta fara tsaiwa da wani namiji,ga masu shugewa jifa jifa suna faman binta da kallo,hakan ya sanya cikin rudewa ta karanto masa lambar halima don bata da niyyar bashi tata,yayi serving yana murmushi gami da yi mata godiya,bata ko jirayi amsa masa ba tayi gaba da sauri shima ya wuce ya tada motarsa ya fice a layin.
Tun daga nesa take hangowa kamar shine sabe sa abdallah ya zuba mata idanu,sai data qaraso gab da shi ta tabbatar shi din ne kuwa,hannunsa dauke da leda wadda ta tabbatar abdallah ya yiwa siyayya kamar yadda ya saba
“Waye wancan?” Ya tari numfashinta ya furta fuskarsa a dan daure ta hanyar riga ta yin magana,dan galala tayi tana dubansa cikin mamaki,sai kuma ta basar ta saki dariya cikin tsokana tace
“Bazawari na ne”
“Bazawarinki?” Ya tambaya cikin nanatawa har sau uku yayin da ta tsaya tana sake dubanshi
“Eh mana” ta fada kanta tsaye,shiru yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya sauya akalar abinda zai fada din da cewa
“Ok,muje qofar gida akwai maganar da nakeso muyi” ya fada cikin magana ta gaske yana yin gaba,kamar an qulle bakinta sai ta ja qafafunta ta bishi.
Qofofim gaban motar ya bude ya shiga nashi mazaunin yana dauke da abdallah wanda baiko damu da ganin maman tasa ba,ya wani lafe jikin abdur rahman din yana ta fama da biscuite,dubanta yayi ganin tana tsaye qiqam a waje
“Bismillah shigo ki zauna” kafadunta ta daga
“Haba,ai kaima kasan bai kamata ba,mu shiga cikin gida kawai ko meye ai ina ga sai yafi dadin tattaunawa ko ba cikin mota ba”
“Ai nasan da cikin gidan,amma maganar bata cikin gida bace,idan kuma kina da wani gu da zamu mu tattauna kuma to” kanta ya daure tana mamakin wacce iriyar magana ce haka da yakeso suyi da sai su kadai?
“To amma kuma malam fa,idan ya dawo ya ganni cikin motarka”
“Indai malam me baki da matsala,na gaya miki hakan da gaske” dan shiru tayi sannan ta sake bude murfin ta shiga ta zauna ba tare da ta maida murfin ta rufe ba,abdallah ne ya soma yunqurin tahowa gunta hakan ya sanya ya miqa mata shi,sai da ta zaunar sa shi sosai ya nutsu a gunta sannan ya soma magana
“Sumayya…”
Yadda yayi kiranta ya sanya ta daga kai ta dubeshi
“Kinsan cewa tun kafin a haifemu Allah ke rubuta mana dukkan wani abubda zai faru da mu har ya zuwa ranar mutuwarmu ko?”.kai ta jinjina tana bashi dukkan nutsuwarta
” a gaskiya sumayya bazan cuci kaina ko na zalunci kaina ba,sumayya…..haqiqa na ga dukkan wasu halayya na mace ta gari,naga dukkan wasu dabi’u na macen da za’a iya aure ta zama uwar ‘ya’ya,na gamsu na nutsu,nagano alkhairai a tattare da ke sumayya,da haka zuciya ta ta fara qaunarki sumayya,zuciyata ta gamsu da ke a matsayin wadda zamu rayu tare,ina sonki ina qaunarki,ina buri ki zama mata ta,ina kuma fatan zaki amince da maganganuna,kin san ko waye abdur rahman sumayya tun ba yau ba,saboda haka mene ne ra’a yinki a kaina?”
Dariya dariya ta saki duk da tarin mamakin dake cunkushe cikin zuciyarta
“Kai abdur rahman,Allah ka iya wasan kwaikwayo,kyanka dramer”
“Sumayya!” Ya kira sunanta da dan qarfi wanda shi ya sake jan hankalinta gareshi
“Dubeni da kyau!,kinga wasa a idanu na da fuska ta bare kalamaina?,wallahi billahi babu wasa cikin lamari na,da qarfina nazo gareki sumayya ko yau kika amince a shirye nake da a daura min aure da kai”.
Sosai maganar ta daki qirjinta,sai ta shiga kada kai kamar qadangaruwa,da qyar ta qwaci kalmar
” haba abdur rahman,ka rufamin asiri mana,ka manta kai waye ne?,kai dan kawun mukhtar ne fa,ko ka manta mukhtar kamar yaya yake a gare ka?,baya ga haka ma so kake duniya ta zage ni?,nifa bazawara ce har da yaro na,kai kuwa matashin saurayi ne da ko auren fari baka yi ba”murmusawa yayi yadda yaga tsantsar tashin hankaki kan fuskarta kamar wadda aka ce za’a yanka,sai maganarta ta biyu data bashi dariya,dududu ita din ma nawa take,’yammata da yawa wasu masu shekaru irin nata ma ba’a fara zancan aurensu ba,wasu kuwa sai a lokacin suka isa auren ma,shekara ashirin kacal da take da su din,idan ba ita ta fada ba babu mai yadda tayi auren fari ma bare haihuwa,kai ya kada da ya tuna ita din farin shiga ce,baki daya ta rude,dole ya bita a hankali har ta sake da shi
“Dukka wadan nan basu isa hujjoji a gareni ba sumayya,jeki gida ki nutsu kiyi shawara,na baki nan da sati guda,amma kada ki manta ni din ina sonki kuma in sha Allahu sai na aureki”. Har wani tsoro ta dinga ji haka taja qafafunta da sukayi sanyi tamkar an buge mata su ta fita daga motar ta rufe masa ita,sai ta kasa motsi har yaja motar ya soma fita a layin tana jin motar da idanu.
Horn din da aka danne shi ya sanya ta dawowa daga karanta wasiqar jakin data tsaya yi a qofar gida,abdallah na kafadarta duk ya bata mayafinta da nashi bakin da burbushin biscuite amma sam bata ma ankara ba,idanunta ta juya zuwa gabanta,mukhtar ne zaune cikin motarsa yana dubanta,fuskarsa a hautsine kamar wanda aka kikkifawa mari,a hanzarce ya fito daga motar ya zagayo zuwa inda take yana fidda wani huci
” waye waccan?”ya tambaya yana mata nuni da motar abdur rahman dake gab da qulewa zuwa kan babban titi,sai tabi inda yake nunin da kallo kamar bata san motar da yake nunawa din ba,mamakin tambayarsa da dalilin fusatarsa ya taru ya sake daskarar sa qwaqwalwarta,cikin qarfin hali tace masa
“Gurina yazo,sai me?”, mamaki ya kamashi,shi sumayyan ke gayawa haka,zuciya ta taso masa iya wuya,hannu yasa ya fincike abdallah daga hannunta har ya dan tsorata ya tabe baki zai sa kuka,sai ya rungumeshi a aqirjinsa,yayi luf kuwa abinsa don tuni ya jima da gane shi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu,cikin tsantsar bacin rai yace da ita
” sai me kuwa?,ba damuwata bace,saidai ki sani bashi da alaqa ya yaro na,kiyita fitowa gunsa amma badai da yaro na ba”sai ya juya ya bude motarsa ya shige ya tada ta ya bar layin.
Kuka ta saki ta shige cikin gida da gudu wanda ya ja hankalin mama dake bakin qofar madafi zaune tana gyara kwanukan abincin daren malam,tsaye ta miqe tana tambayarta lafiya
“Mama ya karbe abdallah ya tafi da shi”
“Waye?,waye ya tafi da shi” ta tambaya cikin rudewa
“Mukhtar mana” ajiyar zuciya ta saki hankakinta na kwanciya,tayi zaton wani ne ma daban,harara ta balla mata
“Sai aka ce miki saceshi yayi?,ko ce miki akayi bazai dawo da shi ba?”.kai ya gyada
” bazai dawo da shi ba mama”harararta ta sake yi
“Maras kunya,idan bai dawo da shi din ba sai me,ba ubanshi bane,ke yanzu akan dan farin kika tsaya kina min kuka?,matsa ki bani guri”janye jikinta tayi ta shige daki tana ci gaba da matsar qwalla,ta yadda lallai har yau akwai sauran quruciya akan sumayyan,ko tsabar tabara ce oho.
Har maman ta gama abinda take bata iya yin shiru ba,ji take kamar ta fita ta karbo yaronta,ganin bilhaqqi da gaske kukan take ya sanya maman binta daki ta kwantar mata da hankali,ita dai jin maman take kawai,gani take bazai dawo mata sa shi ba,da qyar ta fita ta dauro alwalar sallar magariba ta dawo ta tada sallar tana kasa kunnen ta inda abdallanta zai bullo,abun sai ya hadu ya dagule mata,ga zancan abdur rahman ga kewar yaronta.