Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta
“Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?” Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace
“Alheri”
“Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?”wani irin kallo ta masa
“Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani banbanci” ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance
“Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?” Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
“Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!” Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
“Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?….”
“Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi bayan wannan” a kaikaice takw dubansa sannan tace
“Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya” tana gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.
Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.
***** ***** *****
Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan ana tare cikin jama’a zasu yi magana da shi kamar kowa.
Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.
Abinda bata sani ba malam din na sane da komai,bata san da hakan ba sai ranar da aka kai kudin auren abubakar da saka rana wanda baki daya aka tsaida watanni biyu,washegarin ranar malam din yayi kiranta falonsa,bayan ya kammala duka abubuwan da yake ya dubeta
“Am sumayya,nasan cewa kinsan tsarina da al’ada ta gidan nan,sannan alhamdulillah kin san mutuncin mace dakin mijinta,baki da inda yafi nan daraja,dukkan wani abu da ya faru a baya mu ajjiyeshi gefe haka Allah ya tsarama rayuwarki,cikin KUNDIN QADDARARKI yake,babu wanda ya isa ya goge miki ko ya kautar miki da shi”
“Haka ne malam” ta fada kanta na duqe zuciyarta ba bugawa kamar zata bullo,addu’a take kada Allah yasa malam ya bullo mata da zancan da bata da buqatar jinsa a yanzu
“Sumayya,yaron nan abdur rahman yazo guna ya gabatar min da kansa a matsayin manenin aurenki,to amma kasancewarki bazawara a yanzu addini ya baki damar zabawa kanki mijin aure ya sanya nace sai na tambayeki naji mene ne ra’ayinki,kada ki zalunci kanki a yanzu kina da dama,sannan zaman aure zama ne bana yau ko gobe kawai ba,zama ne na har abada”. Wani tashin hankali ne ya rikito mata,abubuwan da suka dinga faruwa da ita zamanin tana auren mukhtar tsaf suka dinga dawo mata,a hankali ta bude bakinta muryarta na rawa
“Kayi haquri malam,abdur rahman dan uwa ne ga mukhtar dan wan babansa ne nasan kasan haka malam” murmushi ya saki
“Sumayya,sumayya kenan,wannan duka ba abun damuwa bane tunda dai aure ya halasta a tsakaninku ba haramun bane” tashin hankali ta fada cikin zuciyarta,’yan uwan mukhtar fa sune dai ‘yan uwan abdur rahman,ba’a canzawa tuwo suna
“Malam,ina tsoron sake kasancewa da ahalin su mukhtar….” Sai tayi shiru ta kasa qarasawa,shima shirun yayi yana nazarin maganarta,tabbas sumayya yarinya ce mai matuqar zurfin ciki,a iya zamanta na aure bazai iya fadar ranar data kawo matsalarta ba,saidai idan an fahimta a maganta mata.
“Ke kike da zabi a hannunki ai,ba zan miki auren dole ba”
“Malam,ina so abdur rahman ya janye daga qudurinsa,bana son sake shiga ahalinsu” ta fada zuciyarta na raurawa muryarta na rawa
“Shikenan zancansa ya wuce,sai ki fidda miji ina son hada aurenki da na yayanki abubakar idan ta kama har da su halima baki daya”
“Amma malam ba…….”
“Sumayya,bana son qorafi ko wata magana,kinsan ba zaiyiwu kici gaba da zama a gida ba,shekara nawa,shekara daya ana gab da cika ta biyu” shuru tayi don tafi kowa sanin waye malam,amma ina mafita meye mafitarta?,
“Sumayyan luqman fa?” Taji ya jefo mata tambayar wadda ta sanya dago kanta ta dubeshi,murmushi ya kuma yi yana dubanta
“Mamaki kike yadda na sanshi?,ya fara zuwa gunki ba da izini ba ya karya doka ta,hakan ya sanya nayi bincike a kansa,na samu gamsassun bayanai a kansa,mutumin kirki ne bakin gwargwado” sai ya dan ja fasali yana dubanta kafin yaci gaba da cewa.