Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane daban daban cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da shuni ne da kuma masu rufin asiri ko wadanda suke ma’aikatan gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna kamar su anty dije.
Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan ta masa godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma hamshaqin gida dake kallon nasu.
Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila ita ce babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta amina minal,a qalla laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara ganin shigowar sumayya falon,ihu ta sanya wanda ya janyo hankalin ‘yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran suka baibayeta wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma tambayarsu anty dijen don bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa sumayyan tana cewa
“Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki baku iso ba har ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na kirata” ta fada tana yafa dan yalolon mayafinta tayi waje da sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet ta shiga tayi alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa
“Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau motar haya inji hajiya bilki” murmushi sumayya tayi tana duban anty dije wadda ta sake gogewa bisa dukkan alamu zaman garin ya karbeta matuqa,ta kuma zama ‘yar gayu ita da yaranta baki daya
“Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan har mun dau hanya wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo dinki”
“Eh inaga man ne dinkunan su’ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin mu zauna hirar yashe gamo” ta fada tana sanya su laila dauke akwatunta zuwa wani daki da aka tanada saboda baqi irinta.
Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe gamo,kusan haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din yaran ma tazo guduwa sukayi suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa sukayi tare da sumayyan zasu kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi zance,sosai suka sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai anty dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da fadi cikin sigar tsokana
“Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara zuwa mata” itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita ta barta,to nan din ma lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin bacci sannan yace
“Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji”ajiyar zuciya ta saki sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji ya abdallah yake,amma ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta barwa gobe,duk sai taji tana kewar yaron nata.
Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi sosai,kullum yaran na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama jarabawa hutu kawai suke jira,wani lokaci da yammaci anty dije kan debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta kaisu park su dan sha iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai ko yaya ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi dadi.
Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta yiwa sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf.
Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya sumayyan na tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty dije ta fito ta dubesu
“zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi da ni za’a yi sunan nan ba”sumayya ta daga kai ta dubi anty dije
” au haihuwa akayi halan?”
“Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki taba karar ki shiga ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki daga kano fa,surukar gidan ce ta haihu” murmushi sumayya tayi
“To ai ban sansu bane anty”
“Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar mutunci da karrama mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi amma basu raina na qasansu,mai gidan bakiga yadda ya dauki abban khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu tamkar jikokinsa” jinjina kai sumayya keyi sannan tace
“Allah ya saka musu da alkhairi,kice ina musu barka”
“Zasuji tunda ba zaki din ba” inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta bita da dariya.
Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke da baqar leda,ta cillar kan cinyar sumayya
“Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo miki kiyi fitar biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe tare kuka shiga shagon da mansur din”. Baki ta saki sanda ta fiddo leshin taga daya daga cikin wadanda suka siya dinne
“Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?”. Dariya anty dijen tayi
“Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku shirya ku wuce wankin kan nan kada dare yayi muku hanya”ta furta tana miqewa ta nufi kitchen.
* *
Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu wani event da sumayyan ta tsara yi,yaya abubakar ne kawai zaiyi walima bayan an gama daura aure.
Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar abdallah ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu
“wai nikam ina abdallah ne?” Maimakon maman ta amsa mata sai tace da ita
“Kije malam nason magana da ke” hakanan taji jikinta bai bata ba,ta miqe ta zura hijabinta ta fice.
A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta abuja ta karbeta,sai ya bata kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta kuma ya darsu a zuciyar malam din
“Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin raba da da uwa sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki mukhtar yazo ya karbi yaronsa….” A firgice ta dago ta dubeshi muryarta na rawa idanunta na fidda ruwan hawaye
“Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken…….”kaaa qarasawa tayi tayi qas da kanta
” kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace baiso yaron yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya rabaku bane na har abada saboda yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa bane,abinda na lura shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har kika tafi da shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za’a dinga kai miki shi”malam ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga lallashinta yana bata kalamai har ta samu ta danji sauqin zugin zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar yaron har yau bai sauya ba.
Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar tayi,ba shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko mutuwa tana shakkar idon uwa,yaya wadanda suka rabu da ‘ya’yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da sauqi ita tunda yana nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da zazzabin da ciwon kai mai tsanani har ranar da aka daura auren,haka nan aka tattarata aka kaita dakinta tana mai ci gaba da kuka mai qunshe da abubuwa iri daban daban
**** 9:30 pm *****
Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin qaramar hukumar kano municipal,yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada kasuwanci gadan gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin tal ta haifa,hakan ya sanya ta dauki so da qauna da kulawa ta dora masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk lokacin da yayi aure ta fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata bari a mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda yayi mata da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya rabu da mata kusan hudu kenan duk da cewa yana dacen matan aure masu matuqar haquri da biyayya saidai ita sam bata gani,haquri da biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna gunsa,amma ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta bada adinka musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk cikin matan da yake aurowa mutum daya ce ta haihu da shi don na wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a gidansu ta haife sai da ta yaye hajiyan tasa aka karbota,’ya mace ta haifa wadda ake kira da nuwaira.
Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada lukman da KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta haifa masa yara uku dukka mata zaitun marwa da radiya,da fari kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki jiki da ita,sannan daga bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka sanya su qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a bayan idonta su yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba wanda ya isa yayi,mutane da yawa sunyi murna sunyi shewa da wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.
Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a yanzu da yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren sumayya,sanda yake gaya mata zai qara aure a tsorace yake,ita kanta tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira wayar malaminta ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai nemeta,ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai an yishi saboda yarinyar nada addu’a hakazalika ‘yar gidan malamai ce,wannan kalma ta sake tunzura karima ta sanya aka sake sabunta aiki mai kyau akan hajiya da lukman don kada sumayyan ta samu kafar rusa mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin ranta,haqura tayi saidai duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi su,komai sai data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga dama,sauqin daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda ya damu dabtsada ko yawan abinda aka zuba cikin lefen.
Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da ita yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa mamaki sannan aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya makeke sai dakunan bacci na kowacce mace da bandaki a cikinsa,sai dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin babban falon,cikin falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon tun kan a kawo sumayyan har kowa ya watse
“To sumayya wannan itace uwar gida na uwar ‘ya’ya na,idan kika bita kamar kin bini ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kuma ki raina min ita,hatta hajiya farincikinta shine farincikin karima da fatan kin gane” kanta ta cira a hankali tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta ta furta
“Ikon Allah,yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?”.
Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina
” idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar”
“To….to to” ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce dakinta,da sauri ya dubi sumayya
“Amarya ta muje na rakaki daki kinji” ya fada cikin kwantar da murya,ba musu ta miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka lukman din yake?me yake shirin faruwa ne?.
Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi
“Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki nan idan kina jin yunwa kici kafin na dawo” ya fada yana juyawa ya fice da sauri,binsa tayi dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take dan gani a da suna ficewa fit daga ranta,hawaye suka soma fita daga kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar makamanciyar wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma nata salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar da hawaye.
Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama sama,ta bude idanunta tana dubansa,murmushi yake yana kallonta shima tare da duba bakin qofar dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin ya murza key,kamar wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana
“Tashi maza ki dauro alwala,ina fatan dai kinci abincin ko?…..kinyi sallar isha’i?…..dauro alwala sumayya babu lokaci….”ya fadi yana satar kallon qofar dakin
Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure kamar yaya take tambayar kanta
” don Allah tashi mana sumayya kada ta…..”bai qarasa fada ba aka fara dukan qofar kamar za’a ballata
“Innalillahi wa inna aihi raji’un” ya fada yana dafe kansa.
“Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana” inji mai buga qofar,jiki ba qwari ya nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana raba idanuwa,kubra ce sai data qarewa dakin kallo ta fuskanci babu abinda ya faru sannan ta kalleshi
“Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana a dakin baka yi butulu kawai,maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce muje nace ka tsaya ka kafeni da idanuwa” sai ya waiwaya yana duban sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya fice yana waiwaye.
Kan sumayya ta dawo da kallonta”da sauran quruciyarki amma kin zabi nakasta rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to kinyi babban kuskure don yadda kika zo haka zaki koma,don babu wasu ‘ya’ya da za’a haifa a gidan nan sai nawa yaran,itama wadda aka haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na rugata zuwa da bata isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo”
“Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da QADDARA mai kyau ko akasinta,hikinar ubangiji kuma yawa gareta,hakanan sanin gaibu sai Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar ya dawo tsakiyar kan wanda yayi jifan”
“Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba”
“Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso nayi kwanan kabari baki daya” sumayya ta fada hankalinta kwance,don ya zuwa yanzu tana jin ta gama daukar haquri da rainin wayon kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga cutar da ita,tabbaa dafi da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar jikinta ba,don kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take ganin wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta jima rabon da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata daga inda sumayya ta fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai ta sake shiri a kanta,qwafa taja sannan ta juya tana fadin
“Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba”bata yi nauyin bakin maida mata amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba
“hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo”. Bayan fitarta muqulli sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura alwala,sam bata ji wata damuwa na barinta da angonta yayi ita daya a dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata sake a cikinsu sannan ta sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya daren sosai da su kafin bacci ya rinjayi idanuwanta.