KUNDIN KADDARATA CHAPTER 54 BY HUGUMA

Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa’annan ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan hadin humrarta tana fadin
“Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya quren”
“Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki” dariya sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare
“Ai ba’a shiga fadan uwa da d’a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty dije kemin har naxo na daina” murmushi mama tayi
“Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke” kai take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata.

Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata
“Yaya ana kiranki” kanta ta daga ta dubeta
“Waye?”
“Baquwar lambace” ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa
“Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah” gabanta ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin qarfin hali tace
“Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba” dariya ya dan saki sannan yace
“Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa mijinki a karo na biyu” jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida mafitan
“Halima lukman ne wai” ta fadi muryarta na rawa
“Mene?,me ya gaya miki?”
“Ba komai”
“Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba”
“Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina”
“Dole aka ce haka ce zata tabbata?” Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta niqa mata wayar tace ta tafi da ita.

Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta tsareta da shi
“Ya aka yi?”
“Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne” tsaki ta ja tana ci gaba da ayyukanta,ta gama lura da take takensa
“Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa”
“To” haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin.

Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy
“Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu” shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.

Idanu ta dinga zubawa tana addu’a kada yazo,addu’arta kuwa taci don baizo ba din har suka kwanta,saidai washegari da yammaci ta gama wanka kenan tana shafa mai taji muryarsa a tsakar gida,yau duka a kasalance ta wuni cikin mutuwar jiki,saboda yadda lukman ya matsanta mata da kira da turo saqonnin ban haquri yafiya da kuma yunqurin dawowa gareta,baki daya ya birkita mata kwanya,baisan yadda ta tsani batun aure ba yanzun,sam ya fice mata a kai,ta yaya zatayi marmarin abunda tasha wuya cikinsa,baki daya tarihin rayuwarta wahalar aure ce wadda ta cimmata ta jigata ta cikin qananun shekaru.

Ta kammala sanya kayanta tana shirin tada sallah wadda zata yita ne a makare don lokacin ya fita zainab ta shigo wadda ta gama shiryawa zasu yinin biki ita da mama
“Ya sumayya kizo inji yaya abdur rahman”
“Ina zuwa” tace tana yunqurin tada sallah
“To mu mun tafi inji mama,tace ki kula da yadfa halima zata sa sanwa kada tayi yawa tunda yau banda malam” kai ta gyada mata don ta riga ta tayar din.

Falo zuwa tsakar gida ta duba duka baya nan,hakan ya sanya ta leqa soronsu a bakin sitting room ta hangi takalmansa,sai ta sanya silifas ta fita zuwa can,da sallama ta shiga ya daga kamsa daga wayar da yake daddannawa ya dubeta,gefe can ta samu ta gaidashi ya amsa idanuwansa na kanta,kallon ya fara mata yawa saboda haka ta kau da kai tana shirin magana sai kuma ya rigata
“Nima sai an ja min aji sannan za’a fito?” Idanu ta watsa masa wadanda suka sanyashi lumshe nashi idon,sau tayi murmushi ba tare da ta dubeshi ba tace
“Wanne irin jan aji kamar saurayin da yazo zance gurin budurwarsa”
“Ai hakanne,saurayin ne yazi zance gun budurwarsa ko kin manta?” Sai ta sake dubansa,Maganar ta taba ta duk da ta tsammaci haka,shima ita yake kallo,cikin son maida maganar wasa tace
“Ah ko?,to ai kayi kuskure,ka manta ni din ba budurwa bace,saboda haka saidai bazawari yazo guna ba saurayi ba,saurayi sai budurwa ai”
“A haka na gani nake kuma matuqar so” shi kuma ya fada ba tare da alamun wasa ba,ganin yanason maida zancen gaske sabanin yadda take son maidawa saita waske da cewa
“Yau kuma tsurfa ce ta tashi daga toge a sitting room maimakon ka shiga ciki yadda ka saba?”
“Neman aure nazo,kinga bai kamata naci gaba da shiga cikin falom surukai ina zama ba” sai ta danyi dariya duk ason bagarar da zancan
“Ah wai…auren halima ko?”ya fuskanci da gangan take watsi da manufofin da yake son yadawa,hakan ya sanya ya kira sunanta wanda ya tilasta mata dubansa
“kinsan ko a da idan na fadi magana irin wannan da gaske nake ko?,to har yau din ma hakan take,da gaske sumayya na dawo neman aurenki ke karo na biyu babu wasa,kuma ina fata wannan karon ni zan jefa qwallon”shuru tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,mukhtar dinta ta tuna,ta daga kai tana kallon abdur rahman idanuwanta fal qwalla
“yanzu kaima sai ka yarda naci amanar ya mukhtar?” Cikin rashin fahimta ya tsuke gira
“Cin amana kamar yaya,da aurensa ne a kanki?,ina cewa koda yana raye halas ne na aureki bare ya rasu?”
Kalmar ta mata ba dadi sai ta miqe
“A gunka mukhtar ya rasu amma ni a cikin zuciyata rayayye ne tamkar yadda kake a raye” sai ta juya ta fice kuka na qwace mata,sam bayi tunanin wannan maganar ta isa bata rai ba,amma da ya tuna cewa har yau tana cikin zafin mutuwar uban danta sai ya mata uziri,hakan ya sanya daga sitting room din ya wuce ba tare da ya dawo ciki ba,har dare ranta na a jagule,tana zaman zamanta yana neman jagula mata lissafi,tana ganin kiransa ta share shima da yaga bata daga ba sai ya tura mata tex ya qyaleta.

*******    *******   ********

Batasan cewa ana shirin jagula mata lissafi ba sai washegari da azahar data tsinkayi sallamar su nuwaira a tsakar gidansu,baki daya yaran ne cikin kyakkyawar kaka data bayyana mata har yau basu sauya kan turbar data dorasu ba,zuciyarta ta dinga bugawa tsoro ya cikata,duk da a bangare guda tayi farinciki da ziyarar tasu.

Sosai taji dadin zuwan yaran,basma ta dubeta
“Anty abbanmu ne ya kawo mu,yace wai kema zaki dawo gidanmu ko?” Yarinyar ta tambayeta,murmushi tayi tana shafa kanta
“Basma,har yau surutu na nan kenan” ta fada da sigar son bagarar da maganar,tare suka wuni da ita,suna zagaye da ita suna bata labarun gidansu da yadda lamura suka sauya,inda sukayi dai dai ta yaba musu,inda suka kuskure ta gyara musu ta nuna musu yadda akeyi.

Da yamma bayan sun gama sallar la’asar sun sake cin abinci nuwaira ta dubi sumayya
“Anty,don Allah ki daure ki dawo gidanmu,abba yace mu roqeki,muna sonki wallahi anty,baki ga yadda hajiya ma ke son ki dawo ba,naji tana cewa ne ba zata sanya baki ba tun yanzun,kada nauyinta ya sanya kiyi abinda bakiyi niyya ba ta shiga haqqinki,don Allah anty ki dawo” ta fada tana karkatar da kai,sai islam ma ta matso
“Eh wallahi anty tunda kika tafi baki daya gidan babu dadi,ko abba ma barin garin yayi,baifi wata daya da dawowa na,da ya dawo kuma kullum masifa suke da mama,gidan ba dadi muna gun hajiya ko yaushe,ki dawo anty don Allah kinji” kasa magana tayi baki daya,wato lukman kwaso mata yaransa yayi kenan su masa campaign ko su daure ta da jijiyar jikinta?
“Anty baki ce komai ba” cewar nuwaira wadda ta qagu taji sumayyan ta amsa,murmushi ta sanya ta kama hannayensu ta hade waje guda
“Kunsan komai nufin Allah ne,kuma ko wanne bawa da irin tasa qaddarar,to ku yita addu’a idan akwai alkhairi zan dawo in sha Allah kunji?”
“To anty” suka fada jikinsu a sanyaye,duka sai suka bata tausayi,babu shakka yaran abun tausayi ne,su masu uwa ma kenan bare mara uwa a gidan,ko da yake dace da uwa ta qwarai shine jigon farinciki da jin dadin rayuwar ‘ya’ya duniya da lahira.

Qarfe biyar saura yaro yayi sallama gidan yace su nuwaira su fito,tuni basma ta sheqa da gudu ta gano abban nasu sannan ta dawo
“Abba ne,yace ku fito”,kyautar humra da kwalakca ta yiwa kowannansu,sannan ta zuba wata da yawa ta hada da turaren wuta tace su kaiwa hajiya.

A bakin qofar soro ta ja tunga tana musu sallama,nuwaira ta dubeta tana narai narai da idanuwa
“anty iya nan ko qofar gida ma ba zaki rakamu ba?”dariya tayi,ta fuskanci wayo wai yarinyar keson yi mata
“shikenan muje”ta fada don faranta musu,yana tsaye bakin mota ya bubbude qofofin,da dai dai yaran suka dinga shiga tana musu sallama sannan ta rufe musu qofar motar,tana dagowa suka hada idanu
“Ku gaida gida ku gaidamin hajiya” ta fada tana juyawa da niyyar shigewa ciki,da sauri ya tari gabanta
“Haba mana sumayya,ko gaisuwa ai kya tsaya kuyi ko?” Ta tabbata idon yaran yana kanta hakan ya sanyata tsayawa tana dubansa
“Don girman Allah sumayya kimin alfarma ki koma gida na,kimin alfarma ko don rayuwar yara na”
“Ni kuma tawa rayuwar fa?” Ta masa tambaya kai tsaye
“Sumayya gida na ya sauya a yanzu,da qafafuna nake tsaye,hijabin dake lullube da idanuwa Allah ya yamin shi,ki taimaka ki koma gidana ki sa cikasa mana sauran haske da farincikin da muke da buqata,kowa a gida na na buqatarki sumayya,don Allah kada ki gujemu”. Kai ta kada
” lukman,bani da buqatar nayi aure har na koma ga mahalicci na,domin ina fata naje na hadu da mijina uban ‘ya’yana,ina mai baka shawara tun wuri kayi haquri da ni”ta qarashe zancan zuciyarta na raurawa ta kewayeshi ta wuce ciki,jiki babu qwari a sanyaye shima ya koma cikin motar ya tada ita ya bar layin.

Tana shiga zainab na miqa mata waya,bata san ko waye ba haka bata tambaya ba,tama yi tsammanin anty dije ce don tace anjima zata kira ta,wayar ta maqala a kunne,muryar abdur rahman ta mamayi dodon kunnen nata
“Ba mukhtar kadai ba,ashe har lukman ma na raye a zuciyarki?” Tambayar da ya fara jefo mata kenan wadda ta sanyata saurin janye wayar daga dodon kunnenta,yaushe abdur rahman ya ganta da lukman?,tambayar data yiwa kanta kenan,kawai sai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,saman katifarta ta fada tana kife kanta a saman filo,baki daya cikin kwanaki hudu zuwa biyar kacal suna son lalata zaman lafiyar zuciyarta ruhinta da ma gangar jikinta?,wa yace musu tana da buqatar aure a yanzu?,wa yace musu tana buqatar wani daga cikinsu?,akan me zasu yi mata kutse cikin rayuwar data lallabata ta fara samun nutsuwa da dangana?su suke suce ta mance da mukhtar ta fara sabuwar rayuwa da su?,ta mance da mutumin da shi ya fara gina tunani da zuciyarta?.

Qarar wayarta karo na biyu ya sake katse mata tunanin da ya karade ilahirin qwaqwalwarra,kamar ba zata daga ba sai taga lambar anty dije ke yawo bisa fuskar wayar,qara fashewa tayi da kuka da taga sunanta,zuciyarta ta sake karyewa,tasan a irin wannan yanayin babu wanda take budewa damuwarta irin anty dijen,taso ace a yanzu tana kusa da ita,sai ta daga kiran da sauri,saidai maimakon sallama da anty dijen ta tsammata sai taji sautin kukan sumayya ya karade kunnuwanta.