KWARYA TABI KWARYA CHAPTER A

 KWARYA TABI KWARYA CHAPTER A

KWARYA TABI KWARYA! 1⃣

Na UMMI A’ISHA

JAN KUNNE duk wanda ya canja wannan

labari ko yayi editing dinsa, ko kuma ya cire

sunan marubuciyar ko ya canja sunan taurarin

ciki Allah ya isa ban yafeba!.

CANAL AWWAB MANSUR ADAM shine sunan

dake manne agaban rigar dake jikin kyakkyawan

sojan wanda ke fitowa daga cikin babban bankin

Nigeria wato CBN acikin garin abuja dogone

kyakkyawa wankan tarwada yanada matsakaicin

jiki, sanye yake cikin uniform din sojoji wanda

suka dace dashi yana rike da waya kirar

BlackBerry bold 2 baka hannunsa daure da

agogon azurfa na Rolex, yar karamar bindiga ce

rataye agefen aljihun wandonsa kansa babu hula

shekarunsa bazasu gaza 29 zuwa 30 ba, kai

tsaye inda yayi packing din motarsa ya hara,

motar tasa yar yayi ce kirar zamani wanda sai

wane da wane ne ke iya hawanta, BMW New

modern itace motar da ya bude yashiga blue

colour, fita yayi daga cikin harabar bankin ya

nufi unguwar wuse kansa tsaye ya tasamma

wani babban gida mai yalwar shuke shuke

kamar akasar India kasancewar unguwar

unguwace ta manyan mutane kuma unguwace

tamasu kudi, yawancin ministers da mukarraban

gwamnatin tarayya ne acikin unguwar, hon yayi

mai gadi ya bude masa yashiga ya Adana

motarsa yafito yana rike da wayarsa ya shiga

cikin gidan tunda ma’aikatan gidan suka

hangoshi suka fara russunawa suna diban

gaisuwa shi kuwa canal sai shan kamshi yake

dahaka yakarasa wani wawakeken falo ginin

zamani wanda ya kayatu da kayan alatu, yar

karamar bindigar dake jikin wandonsa yazaro.

[10/8, 16:52] Admin Aysha:

KWARYA TABI KWARYA2⃣

Na UMMI A’ISHA

Bindigarsa ya zaro daga gefen aljihunsa ya

ajiye akan dan karamin stool din dake ajiye

acikin falon, benen dazai kaishi falon hajiyarsa

yabi har zuwa cikin kawataccen falon nata tana

zaune cikin shiga ta alfarma da Kamala ta

zubawa makekiyar tv din dake manne ajikin

bangon falon ido, wata drama take kallo a

channel din CTV, ahankali yashiga cikin falon

bakinsa dauke da sallama cikin fara’a ta dago

ta dubeshi tana faman murmushi, Awwab barka

da zuwa, yawwa umma sannu da hutawa kusa

da ita yaje ya zauna yafara gaida ta cikeda

sakin fuska ta amsa masa gaisuwar da yake

mata, cikin muryar shagwaba yace umma dan

Allah ki samo min yarinya wadda zata rinka

gyara min bedroom dina domin kullum idan nazo

acikin datti nake ganinsa nikuma banida time

din da zan zauna na gyarashi, murmushi tayi to

awwab akwai wata yarinya da zata zo ta zauna

awurina inyaso ko ita sai ta rinka gyara maka

dakin, yawwa thank you umma, bari naje nayi

wanka saboda ina son na dan kwanta na huta,

gobe da sassafe zan koma ibadan jirgin 6 nake

son bi, kallonsa tayi soja kenan Allah ya kaika

lfy ya tsareka maza aje a huta kafin abbanka

yadawo daga office, yayi min waya cewa 3 zai

dawo gida kaga yanzu kuma 2:20 tayi, to umma

sai nafito, saukowa kasa yayi ya dauki

bindigarsa ya nufi side dinsa wanda yake da dan

tazara kafin kaje, yana shiga dakinsa ya tube

kakinsa ya shiga toilet yayi wanka yafito sallah

yayi sannan ya kwanta akan luntsumemen

gadonsa wanda yasha shinfidu da kaya masu

laushin gaske, bai jima da kwanciya ba bacci ya

daukeshi, acikin baccin nasa yafara mafarki da

wata kyakkyawar budurwa tabiyoshi da wuka

tana cewa sai ta rama abinda yayi mata, gudu

yake itama binsa take daf dazata kamashi ya

farka a firgice, firgigit yatashi.

KWARYA TABI KWARYA3⃣

Na UMMI A’ISHA

Yana tashi yafara kiran sunayen Allah tareda

yin addu’a Allahuma inni a’uzubika min sharri fi

manami an yadurruni fi dini wa dunniyaya,

tunani yafara yi wannan mafarkin shine na 3 da

yayi wannan budurwar tana bibiyarsa da wuka,

to wacece? Tambayar da yayiwa kansa kenan

amma sai dai bashida amsar wannan tambayar,

tashi yayi ya shiga toilet yayi brush yafito, side

din mahaifinsa yanufa ya tarar dashi akishingide

acikin tamfatsetsen falonsa wanda ya tasaru

mutuka gabansa yaje ya durkusa ya

gaidashi,cikin jin dadi mahaifinsa yadafa kansa

yace son kazo lfy? Lfy lau abba nasameku lfy?

Lfy son ya aiki? Alhamdulillah abba, amma dai

zakayi 1 week ko? Girgiza kai yayi no abbba

gobe zan koma dan akwai wani training da

zamuyi har na tsawon 2 weeks kuma daga gobe

zamu fara shiyasa zan koma goben, murmushin

mahaifin nasa yayi dakyau Soja Allah ya tsare

amin Abba, hira suka zauna yi shida mahaifinsa

sai daf da magriba yafito daga falon mahaifinsa

ya dauki wata sabuwar motarshi Prado one door

mai bakin glass yafita daga gidan, wani babban

hotel mai tashe yanufa yana zuwa ya faka

motarsa yashiga cikin club, yanmata da

samarine kawai awurin yaran masu kudi sai

sheke ayarsu sukeyi kowacce ka kalla acikin

maye take, kansa tsaye ya nufi inda ake zuba

giya yaje ya karbo kwalba daya wata kujera ya

nufa yaje ya zauna, yana kurbar giya yana

kallon yanmatan dake chashewa kamar akasar

turai, ji yayi an dafashi ahankali ya waiwaya,

wata kyakkyawar budurwa baka ya gani ta tsuke

cikin riga da wando acikin maye tafara yi masa

magana, kazo…. Muje ka… Kaini… gida luu yaji

tafado kansa cikin sauri ya tureta yatashi yafito

daga cikin club din,cikin motarsa yashiga ya

zauna yanata kallon mutanen daketa kaiwa da

komowa acikin harabar hotel din anan ya raba

dare sai wurin 12 sannan yanufo gidansu.

KWARYA TABI KWARYA4⃣

Na UMMI A’ISHA

Acikin maye sama sama yake driving din har

ya iso unguwarsu yashiga gidansu cikin maye

yafito daga cikin motarsa yana tafiya yana hada

hanya har ya isa dakinsa, mahaifinsa yana tsaye

yana kallonsa ta saman benen dakinsa sai

dayaga yashiga dakinsa sannan yasaki labulen

dakin yana ajiyar zuciya shi dai yarasa a ina

awwab ya dauko wannan dabi’a ta shan giya da

neman mata alhalin da bahaka yakeba, amma

tun lokacin da yazama soja yatare a bariki

shikenan yadauki dabi’u munana bayan shikuma

yasan yabashi dukkan tarbiya wacce uba

yakamata yabawa dansa, runtse ido yayi tareda

yi masa addu’ar shiriya. Awwab yana shiga daki

yafada kan gadonsa yakwanta nan wani irin

nannuyan bacci yayi awun gaba dashi sai karfe

5 na asubha yasamu ya iya farkawa, cikin rashin

kwarin jiki yashiga toilet ya watsa ruwa yafito

yatafi masallaci, bayan sun fito daga masallaci

ne mahaifinsa yakirashi suka shiga falonsa cikin

damuwa uban ya furta son meyasa kake haka?

Yaushe zaka canja saga mutumin banza zuwa

na kirki? Son sam baka iyo halina ba kuma baka

iyo halin mahaifiyar kaba, tunda kazama soja

kazama dan iska, cikin sauri yadago ya kalli

mahaifin nasa, yes kazama dan iska awwab

baka tsoron haduwarka da Allah ko kadan domin

zuciyarka tagama bushewa, sunkuyar da kansa

yayi yayi shiru batare da yace komai ba sai da

akayi yan mintuna sannan yace kayi hakuri abba

insha Allahu zan daina, cikin alamun damuwa

uban yace to my son Allah yanufeka da dainawa

amin abba, yanzu zanje nashirya natafi Ibadan

domin jirgin 6 nake son bi, to son Allah yakaika

lfy sai munyi magana amin abba nagode.

KWARYA TABI KWARYA5⃣

Na UMMI A’ISHA

Jikinsa a sabule yafito yashiga side dinsa yayi

wanka yashirya yasaka kakinsa wanda sukayi

mutukar yimasa kyau yadauki yar karamar

bindigarsa ya soketa a muhallinta kamar kullum,

dakin ummansa yaje yasameta zaune akan

sallaya tana jan carbi zama yayi ya gaisheta

sannan yayi mata sallama yafito kai tsaye

airport driver ya kaishi yashiga jirgin kabo air

line ko minti 10 ba ayiba jirginsu yatashi zuwa

Ibadan tafiyar data daukesu 15 minutes, yana

sauka wasu sojoji guda 4 suka zo suka sara

masa tareda kamewa kai kawai yadaga musu

yashiga cikin motar da aka gindaya agabansa,

gidan baya yashiga sauran sojojin sukuma suka

shiga tasu suka nufi barikin sojoji, suna zuwa

aka bude musu gate suka shiga kofar wani gida

sukaje suka tsaya anan dagudu sukazo suka

bude masa kofar motar yafito batare da yayi

musu magana ba cikin gidan ya shiga har wani

dan madaidaicin falo inda wani babban mutum

yake zaune hannunsa rikeda jarida yana

karantawa, sallama yayi tareda sarawa mutumin

yace Weldon sir! Dagowa mutumin yayi welcome

canal awwab, atsaye ya zauna batare da ya

zauna ba, sir nakaraso, ayimin afuwa banzo da

wuriba, no problem canal, zo ka karbi wannan

taswirar kagani, wani map ya mika masa

kaduba kagani wannan dan kauyen natsakiya

ana fama da tarzomar yan tada kayar baya so

yanzu yanzun nan ina so kaje kahorar da sojoji

guda 40 katurasu suje su kwantar da tarzomar

tunda ina ganin 40 ai zasu isa saboda kauyen

bashida wani girma, yes sir yafada tareda fita

daga cikin falon kai tsaye wajen dandazon sojoji

yanufa inda ya cika umarnin da aka bashi daga

nan yatafi wani babban fili wanda iya masu irin

uniform dinsa ne kawai awajen sai wani guda

daya nasa daban da alama yafisu mukami, nan

suka fara wani training irin nasu na sojoji sai

yamma likis suka tashi, gidansa yanufa wanda

yake cikin barikin sojojin yana shiga kiran basma

yashigo cikin wayarsa basma itace budurwar sa

wacce zai aura yanzu haka tana can a babban

birnin london a Oxford university tana karantar

mass com, cike da kasala da aji ya dauka hello

basma daga daya bangaren ta amsa hy Darling

yakake am fine basma yanzu haka daga wani

training nake duk nagaji shigowana gida kenan,

sonake nayi wanka nahuta, ayya to shikenan

bari nabarka sai kajini bye, kashe wayar yayi

tareda ajiyeta agefe yashiga wanka bayan yafito

ne wani kiran yashigo wayarsa yadauka hello

canal yakub ya akayi? Canal awwab ga

yanmmata fa ansamo shine nace ko zakazo

kaduba? No yau wlh babu abinda zan iya kawai

kubarsu ni kasan bana son yan hannu nafi son

virgin, ok to ba damuwa, wayar tasa yakashe

domin baya son adameshi, salla yayi yaje

falonsa ya bude fridge din dake ajiye giyace kala

kala aciki ba don kar ummi A’isha tayi karya ba

to danace muku babu lemo ko daya duk giyane

aciki,kwalbar guilder ya dauko da cup yazo

yasamu kujera ya zauna yafara tsiyaya yana

sha.

[1/12, 8:20 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA6⃣

Na UMMI A’ISHA

Sai da ya shanye kwalbar giya 2 sannan

yatashi yana hada hanya yana tangadi yashige

dakinsa yana zuwa ya fada akan gado nan bacci

yayi gaba dashi bashi ya tashi ba sai karfe 3

nadare. Asubha tanayi yayi salla kasancewar

barikice babu masallaci ko church aciki, yana

idarwa ya fita motsa jiki bai dawo ba sai 7 koda

yadawo wanka kawai yayi ya sanya uniform

dinsa wanda yadace dashi yafita zuwa office,

office din nasa ya tsaru sosai komai najin dadi

an tanadar masa sai 5 yabaro office yadawo

gida, nan ya zauna yakira basma suka fara hirar

soyayya sai da aka kira sallar magriba sannan

sukayi sallama. Salla yayi yayi wanka ya saka

dark blue din t shirt wadda aka rubuta i can i

will ajiki yasa blue din jeans yadauki bindigarsa

yasoke ajikin wandonsa yafito yadauki motarsa

sai wani club wanda ya kasance matattarace ta

yan iska. Yana zuwa yayi parking din motarsa

yafito ya nufi inda ya hango abokansa zazzaune

kowannensu da kwalbar giya a hannunsa wasu

kuma taba sigari suke busawa gefe daya kuma

yan matan bariki ne kowacce taci ado tayi

kwalliya cikin kaya matsattsu. Karasawa yayi ya

basu hannu suka gaggaisa sannan yakoma gefe

ya zauna yayi order giya kwalba 2 masu tsada,

ana kawo masa yafara tuttulawa cikinsa sai da

ya shanye tas sannan ya ajiye kwalbar namfa

tafara aikinta jin jikinsa yayi ya mutu murus

dakyar ya tashi yashiga motarsa yarufe amma

bai baro wurinba sai karfe 3 nadare yana tafe

yana hada hanya abinka da mai kaki babu

jami’in tsaron da ya iya tareshi dahaka ya

karaso cikin barikin yabude gidansa ya shiga,

yana zuwa ya zube acikin kujera sai barci.

KWARYA TABI KWARYA7⃣

Na UMMI A’ISHA

Barci yake kamar wanda ya mutu sai da

asuba tayi sannan ya iya tashi yagabatar da

dukkan abubuwan da ya saba gabatarwa abisa

al’adarsa sannan yafita office. Kwanansa 6

agarin ibadan ya shirya tafiya zuwa garin abuja,

jirgin karfe 7 na dare yabi 7:30 ya isa gida yana

zuwa side dinsa ya wuce yana shiga dakinsa ya

ganshi tsaftsaf an gyarashi yadda ya kamata

komai an ajiyeshi a muhallinsa ga wani kamshin

dadi da dakin yake yi, bathroom yashiga nanma

kalkal an wankeshi tas, wanka yayi yafito yayi

salla ya saka wata riga karama dark brown

yasaka wando baki iya gwiwa ya nufi dakin

ummansa yana shiga yasameta kishingide

akasan carpet tana kallon wata drama atashar

CTV kusa da ita yaje ya zauna tareda gaisheta

ta amsa cikin kulawa kallonta yayi umma naga

an gyaramin dakina ko har kin samo min mai

gyaran ne? Murmushi tayi awwab kenan dama

ai nace maka kanwarka zatazo ko? To itace

tagyara maka, ras yaji gabansa yafadi, mikewa

yayi umma bari naje wajen abba dan bai ma san

nazo ba, fitowa yayi daga dakin umman adai dai

kofar fita yahadu da ita farace doguwa yar

siririya kamar baturiya amma tafi kamada yan

kasar indiya kallon ta tayi gabansa yaji yayi

mummunar faduwa take yaji ya tsaneta tsana

marar misaltuwa, ina wuni tafada cikin zazzakar

muryarta, bai amsa ba yawuceta yashige side

din abbanshi yana shiga yasameshi zaune yana

signing ajikin wasu takardu idonsa sanye cikin

medical glass, gabansa yaje ya zauna abba

barka da dare, cikin fara’a ya amsa masa

gaisuwar tareda rufe takardun dake gabansa ya

cire gilashin fuskarsa, yajuyo ga dan nasa

awwab agaskiya nagaji da ganinka haka yanzu

kayi girman da yakamata ace ka ajiye iyali,

yakamata ace yanzu kanada mata, ni yanzu

banida wani buri illa inga ka ajiye iyali dan

hakane ma yasa na zaba maka matar aure

NIHAL arazane ya kalli abbansa haba abba

wacece kuma nihal? Kanwarkace awwab tagama

karatun secondary sch dinta kuma

mahaddaciyar alqur’ani ce, cikin faduwar gaba

yace kayi hakuri abba bazan iya aurenta ba

akwai yarinyar dazan aura next week zata dawo

Nigeria tagama karatunta kuma tana dawowa

maganar aurenmu za ayi, kuma abba auren

yanzu ai ba haka ake yinsa ba kamar ni ace na

auri yar secondary? Gaskiya nafi karfin haka

danni wlh abba matar da zan aura mai cikakken

ilmi ce wadda takeda degree, dan yanzu a harkar

aure ma ana duba bright future, amma me

secondary me tasani na rayuwa? Auren yanzu

abba aurene nazamani kuma na aurene nakowa

da muhallinsa shiyasa ma bahushe yace

KWARYA TABI KWARYA!.

KWARYA TABI KWARYA8⃣

Na UMMI A’ISHA

Tunda yafara maganarsa mahaifin nasa kawai

kallonsa yakeyi har yagama, amma acikin

zuciyarsa fadi yake yaro yarone yaro man kaza,

gyaran murya yayi shikenan awwab naji abinda

kace kuma naji duk bayanin da kayi to amma ita

yarinyar yar inace? Abba yan kanone amma

acikin garin nan suke da zama yanzu haka

tagama karatunta a London dawowa kawai

zatayi, to Allah yadawo da ita lfy, amin abba,

tashi yayi yafito yanata cika yana batsewa haka

kawai wata yar secondary akan me? Yanzu duk

ajin nan nawa ace wai kamar ni na auri yar

secondary wlh bazai yiyuba ni yarinyar da zan

aura me class ce sannan kuma mai degree ce

amma ba illiterate ba da wannan zancen zucin

yakarasa falon umma tana zaune wannan

yarinyar tana zuba mata abinci, barshi haka

NIHAL yaji umma tafada cikin sauri yabi yarinyar

da kallo au dama wannan ce da yarinyar da

abba yake so ya aura? Mts shikuwa me zaiyi da

wannan yar mitsitsiyar yarinyar? Wuce nan

wannan ai sai abokansa ma suyi masa dariya.

Wata irin harara ya wurga mata da mamakinsa

sai yaga itama ta harareshi gamida murguda

masa baki,idonsa yabude cikeda mamaki ya

kalleta a haife bazata fi shekaru 20 ba aduniya

makewa yayi yaje kusa da umma ya zauna yana

babbata rai, kallonsa tayi awwab ya akayi? Kai

da waye? Umma nida abba ne wai wata yarinya

ya zaba min bayan kuma ni inada yarinyar da

zan aura, murmushi umman tayi kar ka damu

awwab abinda kake so shi mahaifinka yake so

nasan bazai taba matsa maka ka auri yarinyar

da baka soba, sai alokacin yayi murmushi

hakane umma amma kema ki kara fada masa

yanda nake din nan ba kowacce kuchakar

yarinya zan aura ba kallon wannan yarinyar

yasake yi saboda dama dan ita yafada harar sa

ta sakeyi akaro na biyu tsaki yaja umma ni

yanzu bana burin nayi auren jahila sam sam nafi

son wayayyiya yar makaranta

KWARYA TABI KWARYA9⃣

Na UMMI A’ISHA

Murmushi umman sa tayi wannan haka yake

awwab Allah yabaka wacce kakeso, me zaka ci

nihal ta zuba maka? Yatsina fuska yayi babu

abinda zanci kuma idanma inaso to da kaina

zan zuba basai an zuba min ba, kallonsa

yarinyar tayi tare mikewa ta fice daga falon,

shima mikewar yayi tareda bin bayanta da

harara fita yayi yaje dakinsa ya dauko key din

motar sa yafice daga gidan sai Rossy Guest villa

yana zuwa yasamu anata chasu mata da maza

sai rawa suke masu shan giya suna sha, masu

rawa sunayi masu rungume rungume suma

sunayi can gefe yakoma ya zauna yana kallon

masu shige da fice kafin daga bisani yayi order

kwalbar giya guda daya Ana kawo masa ya

shanye amma bata bugar dashi ba agogon

hannunsa ya kalla karfe 10:30 gida ya hara

saboda washe gari yake son komawa yana zuwa

yashige dakinsa yaja birki a falo yazauna akan

kujera yana kallon silin, bacci ne yadauke shi

mafarkin wannan yarinyar yafara ta biyo shi

aguje, gudu yake iya karfinsa amma sai da ta

kamashi wukar hannunta tadaga sai sheki take

alamar kaifi cikin karaji tace yau zan

kasheka,zan rama abinda kayi min wukar tadaga

zata luma masa firgit ya farka cikeda firgita

amma dayake soja ne bai wani damuba kawai

dai duniyar tunani ya shiga yana son gano

wacce yarinya ce wannan kuma shin meyayi

mata da har take son rayuwarsa wannan shine

karo na 3 dayayi mafarkinta gashi kuma yanzu

tayi nasarar kamashi, daga kansa yayi ya kalli

agogon dake manne acikin falon karfe 3:30

nadare mikewa yayi tare da lalubar bindigarsa

yawuce cikin dakinsa.

KWARYA TABI KWARYA1⃣0⃣

Na UMMI A’ISHA

Yana shiga yacire kayan jikinsa yazauna iskar

a.c tana shigarsa yana nan zaune yana nazari

har 4 tayi wanka yashiga yayi yafito lokacin

anata kiran salla a massalaci, salla yayi yatafi

dakin mahaifinsa yayi masa sallama yafito

yashiga wurin umma itama sallamar yayi mata

yatafi garin ibadan lokacin dayaje karfe 7 tayi

agurguje ya shiga gidansa ya dauko wasu

takardu yafita zuwa office dinsa. Sai la’asar

yadawo yashiga gidansa yayi wanka ya ahirya

tsaf yafito gidan yakub abokinsa yatafi yana

shiga ya sameshi zaune da wasu yan mata sun

sakashi a tsakiya sai masha’a suke aikatawa

tsaki awwab yayi yasamu kujera yazauna,

kallonsa yakub yayi canal yau zamuje club ne?

Yeah hakan dai zai fi kazo muje ka kyale

wadannan yaran, kana ta bata lokacinka akan

wadannan matan marassa aji kallonsa yakub

yayi yace sorry canal bari nazo mutafi fita waje

yayi yazauna cikin motarsa yana jiran fitowar

yakub, bai jimaba yafito suka tafi akan hanyarsu

ne yakub yadubi anwar yace canal wai me

yafaru ne naga kamar yanzu baka fiya kula yan

mataba? Wani dan karamin tsaki awwab yayi

wlh yakub ni kaina ban san menene dalili ba,

amma kuma ina ji ajikina cewa akwai gagarumin

abunda yake tunkaro rayuwata akwai wani abu

wanda zai faru dani nan bada jimawa ba but

ban san yaushe ne ba, kallonsa yakub yayi cike

da mamaki taya kasan haka? Wlh yakub akwai

wasu mafarkai dana jima inayi kuma har yau

ban daina ba sannan akwanakin baya akwai

wani abu da yataba faruwa wanda bai yiyuwa

na iya fada maka domin sirrine wanda ya shafi

rayuwata,yanzu gaba daya jina nakeyi a wani

irin yanayi, sanin kanka ne ina son mata kuma

ina nemansu aduk inda nasan zan samesu to

yanzun ma dai ba dainawa nayi ba amma inajin

wani irin abune a tare dani, ahalin yanzu nafi

son nasha giya akan nakula mata sai dai zan

kulasu suma nan da wani dan lokaci dai dai

lokacin suka karasa club din, nidai ummi A’isha

nakosa naji wannan labarin na awwab masu

karatu nasan kuma kun kosa ko? Ko baku kosa

ba.

[1/12, 8:28 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:21 AM]

Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA1⃣1⃣

Na UMMI A’ISHA

Suna isa awwab yayi packing adai dai inda

aka tanada domin packing din motoci, kashe

motar yayi suka firfito suka shiga cikin club din,

nanfa suka fara gwangwajewa sai da dare yayi

sosai sannan suka dawo gida. Ranar juma’a da

misalin karfe 4 na yamma awwab yabar ibadan

ya nufi abuja karfe 4:30 ya isa gida falon

ummansa ya fara zuwa suka gaisa sannan

yafito yashiga dakinsa, wanka yayi yafito

yashirya cikin wani dafaffen boyel baki yasa hula

zannabukar itama baka agogon azurfa na Gucci

ya daura a hannunsa yafesa turaren ice hot

yasa bakin takalmi harp cover yafito hakika yayi

kyau na daukar hankali gashi yanada kwarjini

sosai, side din umma yakoma lokacin da yashiga

ita kuma tana kokarin fita ganinsa da tayi yasa

taja da baya tareda komawa kusa da umma ta

zauna, shigowa ciki yayi take falon ya gauraye

da daddadan kamshin turarensa, umma ya kalla

yace umma zanje gidansu basma,au basman ta

dawo ne? Eh umma tadawo tun shekaran jiya

saboda itama nazo garin yau, to kagaisheta,

zataji umma yafada yana dan murmushi, ta

gefen idonta ta kalleshi yayi kyau mutuka taba

baki tayi acikin zuciyarta tace danma dai adon

iya najiki ne daki kaca kaca yake, shiko awwab

ko kallonta bai yiba yafice daga falon yaje

yadauki wata motarshi black yafita yanufi zone

2 unguwar su basma. Gidansu basma gidane

babba kuma iyayenta yan boko ne nakarshe

asalima su rayuwar turai sukeyi agidansu, yana

zuwa aka bude masa yashiga yaje ya ajiye

motarsa a inda aka tanada, yafito ya shiga

gidan wanda yayi mutukar tsaruwa a falon

manyan baki ya zauna yana jiran isowarta, sai

da yashafe samada minti 20 sannan tafito taci

uwar kwalliya cikin wata bakar doguwar riga ga

uban gashin kanti har gadon bayanta ayangance

take takunta bakace sosai marar tsayi kuma

bata da hanci, oh ikon Allah masu karatu nazata

basma zatafi haka haduwa amma sai naga abin

ba haka yake ba, tana zuwa inda yake ta zauna

ajikinsa tana fadin welcome my man! Kallon so

awwab ya jefa mata sannan yace thank you my

dear! murmushi basma tayi sannan tace

yakake? Lfy my dear ya sch dafatan an gama

lfy? Lfy tafada kamar wadda bakinta yayi mata

nauyi.

KWARYA TABI KWARYA1⃣2⃣

Na UMMI A’ISHA

Kallonta awwab yayi gashi yanzu kin gama

sch saura me? Murmushi tayi saura aurenmu

kuma, yawwa my dear haka nake son ji so

yanzu zan sanar da dad dina cewar yazo suyi

magana da dad dinku ko? Eh hakan yayi,

ammafa inada wani uzuri,name? Ya tambayeta

agaskiya awwab ina son zanyi aiki kuma sannan

duk lokacin dana samu admission zan koma sch

nayi masters dina, to ai duk wannan ba problem

bane ni awajena, babu matsala zakiyi aikinki

kuma zakiyi karatu ai duk mai saukine ni dama

babban burina shine na auri mace mai class

kamar ke domin ke ta dabance, wani malalacin

murmushi tayi thanks my canal, bari naje

nadawo tafada tareda mikewa ta shige gidan

tana cike da farin ciki domin samun miji kamar

awwab tasan sai mace mai sa’ar gaske, kuma

yana da fuskar mutanen kirki dan idan basani

kayiba baka taba cewa yana shan giya balle har

kayi tunanin zai nemi matan banza, shigowa tayi

hannunta rikeda tiren silva ta zubo masa kayan

motsa baki kamar ba acikinsa shi daya zai zuba

ba, agabansa tazo ta dire farantin tana

murmushin jin dadi, tana farin cikin zata auri

awwab duk da cewa ita tasan yana shan giya da

neman mata amma hakan bai sa taji tsanarsa a

ranta ba asalima itace taganshi tana so,kusa

dashi tazauna my man amma idan munyi aure a

anan zaka barni na zauna ko inyaso Kai sai ka

rinka zuwa? Yes haka nake tunani my dear

saboda akwai gidan da dad dina yabani kyauta a

nan kusa da gidanmu so i think anan zamu

zauna saboda dad baya so nayi nisa dashi, kai

amma fa naji dadi sosai, mikewa yayi bari

nawuce gida sai munyi waya ko, tashi tayi tabi

bayansa har zuwa compound din gidan.

KWARYA TABI KWARYA1⃣3⃣

Na UMMI A’ISHA

Tsayawa tayi ta zuba masa idanu komai na

shi burgeta yakeyi domin ya hadu iya haduwa

ita kanta tasan awwab ba ajinta bane yafi karfin

level dinta kawai dai Allah ne yadorata akansa

har ya amince da soyayyarta yake sonta, kofar

motar ya bude yashiga yayi mata sallama tafara

daga masa hannu har yafice daga cikin gidan

sai da taga fitarsa sannan tayi ajiyar zuciya

tareda furta awwab kenan nida kai aurene

zamuyi irin na KWARYA TABI KWARYA tana

gama fadin haka ta shige gida. Shi kuwa awwab

gida yakoma yana zuwa yashiga wajen umma

ya tarar da ita zaune tana cin apple gefe daya

kuma nihal ce take mammatsa mata

kafafuwanta wanda ta dorasu asaman tumtum,

kusa da umma yaje ya zauna tareda cire hular

kansa juice din dake gaban umman ya dauka ya

balle murfin yafara sha amma sai yaji dandanon

baiyi masa dadi ba, dan shi yanzu giya ce take

yimasa dadi abaki amma komai dadin juice idan

yasha sai yaji babu dadi, ajiyewa yayi umma ta

kalleshi awwab kasha juice din mana, no umma

ya isheni inada juice adakina idan naje zansha,

kallonsa nihal tayi ta taba baki, kamar hadin

baki shima ita ya kalla gabansa yaji ya fadi, to

shi wai meyake faruwa ne? Duk tun lokacin

dayafara ganin yarinyar nan yaji gabansa yana

faduwa.

KWARYA TABI KWARYA1⃣4⃣

Na UMMI A’ISHA

Kallonta yasakeyi sosai kamar dai yasan ta

awani wuri amma ya kasa tuna ko a inane,

hakama muryarta kamar yatabaji sai dai ya

manta a inda yaji hararta yayi aransa yana fadin

yarinya karama sai iyayin tsiya da kwainane,

dagowa dara daran idanuwanta tayi ta wurga

masa harara, hararta shima yayi yana daddanna

wayarsa chtn yake da basma ta palm chat,

kallonta yasakeyi baki yaga ta murguda shi abin

nata ma dariya kuma yake neman bashi yarinya

sai kace tababbiya baiyi mata komai ba ta ringa

harararsa? Remote din tv ya dauka ya kamo

MBC Action yafara kallon wrestling ita kuma

nihal tanata aikin daddannawa umma kafafunta

yana nan zaune yana kallo har 9 tayi umma ya

kalla umma kira talatu ta zubo min tuwo dan

kadan,a’a ga nihal ta zuba maka mana, a’a

umma kira talatu dan Allah kira umma ta

kwallawa talatun sai gata dasaurinta tazo ta

durkusa, talatu zubawa awwab tuwo sai dai kin

san cin abincinsa dan kadan zaki zuba masa, to

ranki yadade da saurinta ta tashi zubo masa ta

kawo masa yakarba da cokali yake cin tuwon

yanaci yana kallo, jifa jifa kuma yana duba

sakonnin daketa shigowa cikin wayarsa, dahaka

har ya gama cin abincin ya tashi, dakinsa

yashiga yacire kayan jikinsa domin shi bai cika

mu’amula da manyan kayaba sai dai idan ranar

Friday ne abbansa yayi fadan har yagaji bashida

kaya sai jeans da t.shirt ko kuma boxer, wanka

yashiga yayi yafito yayi salla yaje yabude fridge

dinsa zai dauko giya amma wayam babu ita

babu alamunta tsaki yaja yasan wannan

figigiyar yarinyar ce ta kwashe masa to amma

me zatayi da ita? Wata zuciyar tace babu abinda

zatayi da ita kawai tsabar mugunta ne yasata

kwashe maka, zama yayi afalon zuciyarsa

cikeda kunci, tsaki yayi taja gashi yau baya son

fita club domin so yake yayi bacci ya huta,

dakinsa yashiga ya kwanta dakyar bacci ya

kwasheshi. Washe gari basma tayi masa waya

ta sanar dashi cewa zatazo ta gaisheda

ummansa, tashi yayi yashiga cikin gidan dakin

umma lokacin 11 dai dai yasameta suna yin

breakfast itada abbansa, tsugunnawa yayi

yagaishesu sannan yahau kan dining din shima

yahada tea yafara sha, kallon abbansa umma

tayi tace Alhaji dama ina son fada maka ka

shirya kaje gidansu yarinyar da awwab yake so

ka tambayo masa aurenta saboda iyayenta sun

bashi dama.

KWARYA TABI KWARYA1⃣5⃣

Na UMMI A’ISHA

Dan haka yanzu abin yi yarage garemu sai

mu nemo masa aurenta, kallonsa abba yayi wai

hakane my son? Yes abba hakane murmushi

abbansa yayi ato alhamdulillah insha Allahu

zanje gidansu yarinyar in Allah ya yarda, mikewa

abban yayi to ni zan tafi office hajiya Sadiya

babu wani abu ko? Mikewa tayi tabishi tana

cewa babu komai abba, kallo awwab yabisu

dashi har suka fice, dai dai lokacin nihal tashigo

falon tana sanye da doguwar riga ta shadda, ke

ina abinda kika dauka min acikin fridge?? Wani

mugun kallo ta watsa masa mai nuna alamun

baka isaba, ke nifa ba sa’anki bane kin gane?

Bana son raini idan kin saba rashin kunya kisan

a inda zakiyita amma ba anan ba, dankwalin

kanta ta turo gaban goshinta ma’ana gayawa

keya dan kwali yabaka amsa, nan da nan ya

sake kuluwa dan dai kawai shi baya dukan

matane amma da babu abinda zai hanashi

babballata tashi yayi yabar falon yakoma

dakinsa, sai waya ya yiwa umma ya sanar mata

da zuwan basma anjima. Yamma tanayi basma

tazo gidansu awwab cikin shiga tasu ta yayan

manya, an bazo gashin kanti awwab ne yafito

yayi mata jagora har cikin falon suna shiga

umma tana zaune akan sallaya da alama salla

takeyi ita kuma nihal tana lallatsa wayar umma

sallama basma tayi tanemi wuri ta zauna kamar

ba zata amsa ba ta amsa sallamar tareda

dagowa kanta ta kallesu, tsaki taja acikin

zuciyarta wai dama wannan ce basman? Lallai

ashe jinta yafi ganinta tab su awwab angamu da

aiki akan wannan yake wani rawar kafa? Harara

ta watsa musu daga shi har basman, itama

basman sai faman harare harare take tayi kamar

wacce aka zaga, maganar umma ce ta katsesu

sannu da zuwa basma cikeda yanga tace yawwa

sannu umma ina wuni? Lfy lau umma ta amsa

cikin fara’a ta dubi nihal wacce taketa faman

yatsina fuska da harare harare tace nihal kawo

mata ruwa da lemo, to umma tafada batare da

ta tashi ba sai da tagama jan ajinta sannan ta

tashi hakan ba karamin batawa basma da

awwab rai yayi ba, ruwa roba daya ta dauko da

lemo gwangwani daya sai tsurar cup guda daya

ko a faranti bata doro ba tazo gabansu ta ajiye

akan center table takoma mazauninta wato

kujerar datake kallonsu ta zauna ta dauki wayar

umma taci gaba da lallatsawa awwab ya kulu

ya kulu, ita kuwa basma haushin nihal ne ya

cika ranta kamar taje ta shaketa takeji, kuma ita

a iya saninta awwab bashida kanwa su 2 ne

kadai awurin iyayensu daga shi sai yayarsa Anty

jamila to a ina suka samo wannan yarinyar mai

kama da aljana? Wani kishi taji ya turnuketa

marar misaltuwa kara daga idonta tayi takalli

awwab wanda shi kuma nihal yake kallo cikeda

tsana da jin haushinta itama nihal din su duka

biyun haushin su takeji in banda harara babu

abinda datake aika musu, to meye dalili? Nidai

ummi A’isha banida amsa.

[1/12, 8:36 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:29 AM]

Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA1⃣6⃣

Na UMMI A’ISHA

Daure fuska awwab yayi yayin da itama

basma ta daure tata fuskar, umma ce tayi

magana tace basma kisha ruwa, to umma

nagode tafada tana mai cigaba da hararar nihal

ita kuwa nihal basu ma isheta kallo ba daga

basman har awwab din gani take bata da

lokacinsu amma haka kawai taji basman nan

bata burgeta ba kamar yadda itama basman taji

sam nihal bata yi mata ba shirune ya dan gitta

afalon kafin umma tace basma ashe kuma an

kammala karatu ko? Washe baki tayi wlh kuwa

umma nagama yanzu sai maganar aiki kuma,

kallonta nihal tayi tareda taba baki daidai

lokacin awwab ya kalleta ya harareta bata

kyaleshi ba itama ta watsa masa harara, ganin

abin yayi yawa yasa basma mikewa umma ni

zan tafi tashi umma tayi to jirani ina zuwa

dakinta tashiga ita kuma nihal ta dubesu ta kara

tabe baki azuciyarta tana cewa wlh sam baku

wani dace da juna ba, umma ce tafito hannunta

rikeda leda wadda tasako turarrurruka da man

shafawa aciki tabawa basma, gashi basma

nagode kigaida mutanen gida Allah yayi albarka,

amin nadawo tafada tana murmushi wucewa

tayi awwab yana binta abaya sai da sukaje daf

da kofa nihal tace agaida gida bakuwa, ko

waiwayowa basuyi ba bare su tanka mata ita

dinma dama tafada ne domin ta tsokane su to

kuma sai akayi sa’a basu kulata ba. Suna

fitowa harabar gidan basma ta dubi awwab my

man wacce yarinya ce waccan? Meye alakarku

da ita? Kai ya girgiza wlh yadda kika ganta haka

nima naganta ban san wacece ba, sai dai ina

son nasan meye alakarmu da ita amma jinina

bai hadu da ita ba saboda bata da kunya

fitsararriya ce ta karshe, baki basma ta taba ai

naga alamar marar kunya ce sai wani kallon

banza take yimana sai kace wasu sa’anninta,

wlh dan kawai nice nazo ne badan haka ba da

sai na tsinka mata mari murmushi awwab yayi

babu ruwanki da ita ki barni da ita ni zan koya

mata hankali,kallonsa basma tayi ina fata dai

baka sakar mata fuska? Haba ina ruwana da ita

nifa sau 2 kawai nataba yimata magana tun

zuwanta gidan nan tsakanina da ita harara ce.

KWARYA TABI KWARYA1⃣7⃣

Na UMMI A’ISHA

Yawwa my man haka nakeso saboda dama

bana so kabata fuska ko kadan domin idan taga

fuska zata iya cewa tana sonka, no no kima

daina wannan tunanin mezanyi da wannan

karamar yarinyar, yarinyar da har yanzu bata

gama cika mace ba murmushin farin ciki basma

tayi shiyasa ko yaushe sonka karawa yake

acikin zuciyata domin kai acikin maza na

dabanne you are special one, kanada class da

iya taku ba irin sauran maza bane murmushi

yayi to yanzu sai yaushe ni kinga gobe nake son

komawa Ibadan, ok to shikenan Allah ya kaika

lfy zamuyi waya later, motarta ta bude tashiga

ta tadata tadaga masa hannu ta fita daga

gidan, juyawa yayi yakoma side din umma,

zaune ya hango nihal tana yankewa umma

farcenta tsaki yaja yaje kan kujera ya zauna

yakalli umma,umma wai me aka dafa agidan nan

ne? Awwab dashishi akayi, to ai umma ni bana

son wannan abin dan Allah sa talatu ta dafa min

indomie duk da ba lallai ne ma in iya ciba ni kin

sanni da tsantsami, to bari nihal ta dafa maka

shiru yayi yadauki remote ya kunna tv, nihal bar

min yankan farcen kije kitchen dina ki dafawa

awwab indomie inji umma, tashi tayi har zata

fita umma tace nihal kar kisa yaji dayawa

saboda awwab bai son yaji, to umma tafita ta

shiga kitchen, acikin mintunan da bazasu fi 5 ba

ta shigo da plate a hannunta da spoon tazo ta

ajiye agabansa ko kallonta bai yiba itama bata

kalleshi ba, kusa da umma takoma ta zauna

lokacin umman har tagama yanke farcen, kamar

kada yaci amma ganin yana jin yunwa yasa

yadauki cokalin yadebi indomien yafara ci jin

harshensa yayi kamar zai cire saboda yadda

tasha attaruhu, ajiye spoon din yayi yatashi

yabude fridge ya dauko juice din gwangwani ya

dan kurba ya ajiye dakyar ya iya magana umma

bari naje naci abinci a restaurant daga can zan

wuce nasha lemo harararsa nihal tayi aranta

tace zakaje kasha giya dai ba lemo ba, to

awwab adawo lfy inji umma.

KWARYA TABI KWARYA1⃣8⃣

Na UMMI A’ISHA

Sai da ya harari nihal sannan yafita cikeda da

jin haushin nihal yanufi dakinsa yayi wanka ya

sake kaya, dark purple din riga mai dogon hannu

da bakin wando jeans yafesa turarensa na ice

hot tadauki gun dinsa yanufi motarsa BMW blue

wadda takasance mai dark black din glass, yana

shiga yadaga kujerarsa ya ajiye bindigar sannan

yatasheta ya fita,nihal kuwa lokacin da awwab

yafita ta kalli umma tace umma bafa Lemo zaije

yasha ba, wlh.. Umma ce ta katseta hanyar

cewa bana son surutu nihal kar nakarajin

wannan maganar a bakinki, shiru nihal tayi

tareda tashi ta wuce dakin umma. Yana fita ya

saki kida a motarsa wakar d banj ya kunna cikin

before in love, a hankali kidan yake tashi har ya

isa wani katafaren wurin cin abinci hot pot

restaurant and catering services, a kan titin mai

tama,a waje yayi packing din motarsa yafito

yashiga,shinkafa da miya yayi order sai dan

salad aka kawo masa yaci ya biya, yana shirin

fitane yaci karo da zaituna, zaituna yarinyarsa

tunda dadewa, kallonta yayi cikin mamaki

zaituna kece? Murmushin jan hankali tayi nice

ranka ya dade, yakake? Normal yagida, gida lfy,

yanzu ina zakije? Zanje gidane ko kana so ne

narakaka?. Yes idan kikayi haka zanji dadi, ok to

muje,jerawa sukayi har inda ya ajiye motarsa

suka shiga bai zame da su ako ina ba sai Dan

Musa guest lodge,suna zuwa yakarbi mukullin

daki suka shiga dubansa zaituna tayi canal

dama bakayi aure ba? Ke yakamata nayiwa

wannan tambayar dan tuntuni nayi zaton kinyi

aure, gefen fuskarsa ta shafa no ina tareda kai

tayaya zan iya auren wani, ai duk maza ganinsu

nake kamar mata yan uwana kai kadaine kawai

namiji a wurina, murmushi yayi tareda riko

kugunta kar fa ki yaudareni zaituna idonta ta

fara sannan tace babu yaudara tsakanina dakai

ka yarda da abinda na fada, janta yayi suka

fada gado. Sai wurin karfe 5 sannan suka dawo

hayyacinsu alokacin awwab bacci kawai yake ita

kuma zaituna tazuba masa ido cikeda so inama

ace awwab mijin tane haka kawai take rayawa

acikin zuciyarta motsi yayi yafarka daga dan

baccin da yayi yatashi yashiga toilet yayi wanka

yafito tareda fara tashin zaituna hannunsa tariko

tareda kara jawoshi jikinta nanfa suka koma

ruwa

KWARYA TABI KWARYA1⃣9⃣

Na UMMI A’ISHA

Sai da suka dada shafe awanni suna

shedancinsu sannan suka shirya suka fito,

abakin wani titi yayi dropping din zaituna tare da

rubuta mata cheque na wasu makudan kudi

masu yawan gaske. Wani gidan saida giya ya

zarce yasiyi wata yar karamar robar giya yafito

yashiga motarsa yadan kurbi giyar kadan

sannan ya rufe ya boye sauran akasan kujera,

gidansu ya wuce lokacin karfe 8 nadare yana

shiga ya wuce wurin abbansa yagaisheshi anan

ne abban yake yi masa albishir da cewa yaje

gidansu basma sun ganada mahaifinta, dadi

awwab yaji domin shidai yana son basma

saboda iya jan ajinta, mikewa yayi yafito zuwa

sashen umma nan ya taradda ita zaune da

fitsararriyar yarinyar nan nihal yana shiga suka

hada ido da nihal take ya dalla mata harara

itama ta rama kujerar da umma take kai yaje ya

zauna kamar wanda zai shige cikinta, awwab

kadawo? Eh umma yanzu daga wurin abba nake

yace min yaje gidansu basma dazu harma sun

gama magana da mahaifinta murmushi umma

tayi eh haka yagaya min ai yanzun nan yafita

daga cikin falon nan, komai ya daidaita saura

yanke ranar aure kawai kansa ya kwantar ajikin

kujera, oh nima nakusa zama mai gida kenan,

dariya umma tayi dadina dakai rashin kunya,

yanzu agabana kake fadar zaka zama maigida?

Dariya awwab yayi sorry ummana ai gani nayi

kece abokiyar shawarata kuma abokiyar zancena

shiyasa kikaji na fadi haka, to ai shikenan

awwab Allah yakaimu lokacin, amin umma

wayar hannun nihal ce tayi kara taduba tareda

dagawa cikeda yanga tafara magana hello

hamid, ok bari zan kiraka anjima, awwab ne yaji

gabansa yafadi kallonta yasakeyi tana sanye da

leshi fari mai ratsin baki ajiki, ta turo dan

kwalinta gaban goshi hakan yabashi damar

hango tulin gashin kanta data tufke,harara ya

jefata mata sannan acikin zuciyarsa yace

wannan yarinyar yar duniyace da alama, ita

kuwa nihal sam bata ma san yanayi ba domin

hankalinta yana ga wayar umma datake

hannunta sai lallatsawa takeyi, ko hararta da

yayi bata gani ba domin da tagani shikansa

yasan sai ta rama.

KWARYA TABI KWARYA2⃣0⃣

Na UMMI A’ISHA

Kallonta yaci gaba dayi ita kuma tanata

daddana wayar dake hannunta da alama sakon

txt massage take turawa, she’s very cute and

beautiful yafada acikin zuciyarsa wata zuciyar

tace yes is true ammafa muguwa ce da alama

saboda dazu taji umma tace bakason yaji shine

tacika attaruhu a girkin dan kar kaci dai dai

lokacin ta dago dakanta ta kalleshi harara ta

cilla masa amma shi sai yayi murmushi karo na

farko dataji ya burgeta domin tun farkon ranar

data fara ganinsa bai taba yimata murmushi ba

sai dai aikin harara amma yau gashi abin

mamaki itace ta harareshi bai ramaba a

maimakon ya rama ma sai ya aika mata da

sakon murmushi mai tausasa zuciya, hararsa

takara yi aranta tace good naji dadi tunda yanzu

ka gane nima ba kanwar lasa bace da alama

kagane cewa u are d one that loose d game

shiyasa kafara sakkowa but naso ace munci

gaba da buga wasan so that sai agane waye

winner, maganarsa mai dadi tajiyo yana yiwa

umma magana, umma wai ni kwana 2 ina baba

mai gadine? Tunda nazo ban ganshi ba, eh wlh

awwab yazo yayi min sallama cewa zaije gida

dansa bashida lafiya, ayya umma inane kauyen

nasu? Wlh awwab sai dai ka tambayi idi mai

gadi ni ban san garinsu ba, ok to idan idin

yasani sai kawai na aikeshi ma ya kai masa

sako, murmushi umma tayi Allah yasaka da

alkhairi Allah yayi maka albarka Allah ya biya

bukata, amin ummana kinyi min babbar addu’a

domin inada wani babban buri arayuwata kuma

inada muhimmiyar bukata awurin ubangijina,

kallonsa nihal tayi ta taba baki ta dauke

kanta,murmushi yayi acikin zuciyarsa yace

yarinya zanyi maganinki ni banida time din da

zan tsaya ina musayar harara dake,umma ya

kalla umma zan sha tea da sauri ta kalli nihal,

nihal tashi ki hadowa awwab tea, mikewa tayi

tana cikeda takaici kinga kisa min lemon tsami

aciki kuma iya sugar da Lipton kawai zakisa

bata kulashi ba tafita tashiga kitchen, lallai

gayen nan dan rainin hankaline nifa ba yar aikin

gidansu bace da zai rinka sani bauta amma

zanyi maganinsa dariyar mugunta tayi dai dai

lokacin data gama hada tea din tadauka acikin

glass cup takai masa yana nan zaune a inda

tabarshi amma umma bata wurin ta tashi, akan

stool din dake gabansa ta dire tea din takoma ta

zauna tazubawa tv idanu tana kallon drama

sahrul asmar a tashar MBC Bollywood sai da

awwab yagama jan ajinsa sannan ya dauki tea

din yakai bakinsa kurba daya yayi yadawo dashi

saboda gafin gishiri da yaji kamar zaiyi magana

dariya nihal tafara kamar me sannan tace yadai?

Murmushi yayi yafara kwalawa umma kira

umma! Umma!.

[1/12, 8:47 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:40 AM]

Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA

2⃣6⃣

Na UMMI A’ISHA

Shirin biki akeyi sosai agidajen biyu

musamman ma gidan su basma,basma ansha

bleaching anyi fari dau ga tarkacen gyara da

aka tanada domin a damfari awwab, shikuwa

awwab yana can Ibadan bai samu damar zuwa

ba. Ita kuwa nihal bakin ciki kawai takeyi da

wannan auren na awwab domin haka kawai bata

san dalili ba taji ta tsani wannan auren, amma

gidan kullum kaya ake shigowa dasu wadanda

za abukata alokacin hidimar bikin, yanzu ma

kwance take akan dan madaidaicin gadonta duk

ranta abace yake har wata yar rama tayi, karar

saukewa kaya take jiyowa a falo da alama irin

kayan da ake kawo wane na bikin tsaki taja

takara gyara kwanciyarta wato awwab shi

wannan yarinyar burgeshi take? Hmm dama ai

duk namijin da yafiya yaudara to akarshe

mummuna yake aura kwanciyarta ta sake

gyarawa duk tarasa abinda yake yimata dadi.

Satin biki yana kamawa awwab yazo lokacin

nihal ta tattara tabar gidan tayi tafiyarta,an

shirya karya abikin kuma an kashe kudi sosai,

ranar juma’a aka daura auren awwab da basma,

abokansa sojoji suka shirya masa fareti a aminu

kano square agarin abuja, ana tashi aka tafi

dinner akaci aka sha daga nan aka watse.

Washe gari gidajen biyu sukayi wuni da daddare

aka kawo amarya gidanta, gidan dayasha kayan

alatun more rayuwa kamar a turai domin an

kashewa gidan kudin gaske kuma gidan ya tsaru

matuka, ajikin gidansu awwab gidan yake, yan

kai amarya suna watsewa awwab ya shigo inda

amaryarsa take nan suka gabatar da dukkan

abubuwan da Ma’aurata suke gabatarwa adaren

farko, suna gamawa awwab yaje gareta ya fara

nuna mata soyayya amma kuma sai ya sameta

ba a budurwa ba tsaki yaja yatashi ya zauna

yafara nazari, cikin tuhuma basma ta kalleshi

my man meya faru? Banza yayi da ita hannunsa

tajawo ya fisge, haba awwab ya zaka min haka?

Idan kai ka gamsu ai ni ban gamsu ba, harara

ya watsa mata ke malama ki rabu dani kinji, wlh

kin bani mamaki ashe dama ke yar iska ce?

Zabura tayi ta tashi me kake son fada ne? Kaga

awwab kar ka yarda kayi min sharrin zina, to ai

ba karya nayi miki ba kinyi ne domin ba a

cikakkiyar mace kika zo min ba yafada cikin

bacin rai.

KWARYA TABI KWARYA2⃣7⃣

Na UMMI A’ISHA

Mamakine ya kamata yanzu duk wadannan

abubuwan da tayi amfani dasu sai da awwab ya

gane? Boye mamakinta tayi tace look awwab

agaskiya bazan juri wulakanci ba kuma ashe

kenan kaima manemin matane shiyasa kagane

ni ba budurwa bace, domin idan kai cikakken

saurayi ne baka taba kusantar wata mace ba

tayaya zaka san na rasa budurcina? Tashi

awwab yayi yafice yabar mata dakin yakoma

dayan ransa abace zuciyarsa sai faman

tafarfasa takeyi, shidai yasan basma bata zo

masa da martabar ta gidansa ba haka ya zauna

yana cikeda takaici, ita kuwa basma koda

awwab ya fita komawa tayi tai kwanciyarta

babu abinda yadameta ba tareda damuwar

komai ba tafara shakar baccinta yayinda shi

kuma awwab baccin ya gagari idonsa yanda

yaga rana haka yaga dare. Washe da safe aka

turowa da basma yan aiki guda uku daga gidan

iyayenta shi dai awwab bai ce komai ba amma

yasan yafara samun matsala da basma tun

daga daren jiya, mai shara da wanke wanke

daban mai yimata girki daban sannan mai

yimata wanki da guga da sauran ayyuka daban,

kowaccensu aikin da zatayi tafada, yatsina fuska

basma tayi tareda nuna musu B/Q tace suje can

sukai kayansu dan acan zasu zauna babu musu

suka kinkimi kayansu suka fita, suna fita ta

koma ta kwanta yayinda shi kuma awwab yafice

daga gidan yana cikeda damuwa da bacin rai

kansa tsaye ya wuce wani guest lodge yana

zuwa yasiyi giya roba biyu ya karbi mukullin

daki yashiga ya rinka shan giyar nan har sai da

ya shanye sannan ya kwanta akan gadon dakin

yakama bacci. Abagangaren gidansu kuwa baki

sun fara bajewa masu sanya albarka sunyi sun

tafi, alokacin gidansu basma suka aiko da kayan

gara mota guda wanda yawansu zai iya cika

store daya, godiya iyayen awwab sukayi tareda

bada tukwici. Sai da yamma tayi sannan awwab

yafarka daga baccin daya daukeshi yadawo gida

yayi wanka yashiga cikin gidansu umma ya gani

da sauran bakin da basu tafiba, gaisheta yayi

yawuce side din abbansa suka gaisa nan abban

yafara yi masa nasiha kan ya zauna lafiya da

matarsa kuma yayi hakuri akan duk abinda

zatayi masa domin mata sai da hakuri kuma

yazama mai rufe sirrin iyalinsa, kansa ya dukar

akasa yace insha Allahu abba zan kiyaye kuma

zanyi aiki da dukkan abubuwan daka fada min,

Allah yayi maka albarka awwab sannan kuma

dan Allah karage wannan shan giyar da neman

matan da kakeyi domin kaga yanzu ka girma

nan ba da jimawa ba zaka zama mahaifin wasu

to kaga yanada kyau kazama uba nagari irin

uban da kowanne da zai yi alfahari dashi kaji?

Eh naji abba in sha Allah zan kasance mutum

nagari kamar yadda kake min fata.

KWARYA TABI KWARYA2⃣8⃣

Na UMMI A’ISHA

Dafa kansa mahaifin nasa yayi tareda fadin

Allah yayi maka albarka awwab Allah ya

albarkaci rayuwarka, amin abba yafada yana

murmushi tashi yayi yafita yakoma gidansa yana

shiga yasamu basma zaune afalo tana shan

juice ko kallonta bai yiba yashige daki, sai da

tagama shan juice din sannan ta tashi tabishi

cikin dakin tasameshi kwance kan gado yayi

rigingine kansa tafada gamida sakin kukan kissa

dan Allah awwab kayi hakuri wlh ni ban taba

aikata iskanci ba ina jin dai hawan keken da

rinka yine lokacin ina yarinya yaja min haka,

takarasa maganar cikin kuka, rungumeta yayi

yafara share mata hawayen dahaka ta samu

nasarar rudashi har ya amince da ita. Zama

sukeyi na babu yabo babu fallasa har na tsawon

sati 1 alokacin awwab ya shirya zai koma

ibadan itama basman asatin da zai kama zata

fara fita aiki, wanka yayi yafito lokacin basma

tana kwance akan gado ta bararraje shiryawa

yafarayi ya kalleta basma yunwa fa nake ji ki

tashi ki sama min abinda zanci, oh sorry my

man bari nakira mary ta dafa maka indomie, a’a

kibari nadawo tukunna yanzu gidan umma zanje,

brown colour din jeans yasaka da bakar t.shirt

mai kyau an rubuta its a new day agaban rigar,

turaren touch me yafesa yafito kallon burgewa

basma tabishi dashi hakika ka hadu mijina

tafada tana dariya, gidan umma yashiga babban

falon yafara shiga yatarar da yan aikin gidan sai

kai da komo sukeyi, sama ya hau falon umma

anan ya sameta itada nihal suna zaune, sallama

yayi yashiga yazauna yadan duka ya gaida

umma, ina basman? Tana nan lfy ? Lfy lau take

umma yafada yana mai kallon nihal wacce tayi

kicin kicin ta bata rai tareda daure fuska, kanta

ta dauke ta mayar kan tv, murmushi awwab yayi

aransa yace sarkin tsiwa kin dawo kenan, umma

nima gobe nake son komawa ibadan,ah har

hutun naka ya kare awwab? Eh umma itama

basman nxt week zata fara zuwa aiki tasamu

aiki a nta, to Allah ya sanya alkhairi, amin

umma, dan Allah umma arinka dai kulawa da ita

tunda ni kinga ni bana gari, jiyowa nihal tayi ta

harareshi acikin zuciyarta tana cewa kijishi sai

kace wata karamar yarinya wai arinka kulawa

da ita hararshi taci gaba dayi tana mai jin

haushinsa shida basman, dan tsaki taja acikin

ranta kema umma kece kike biyashi ai shiyasa

yake samun damar yiwa mutane iyayi.

KWARYA TABI KWARYA2⃣9⃣

Na UMMI A’ISHA

Kallonta kawai awwab yakeyi shidai a duniya

yarasa me yayi wa yarinyar nan da yasa take jin

haushinsa,hada ido sukayi ta wurga masa

harara,umma ya kalla umma dan Allah bakida

garin kunu? Wlh kunu nakeso, da akwai awwab,

kunun zakasha?eh umma, kallon nihal umma

tayi nihal maza jeki ki damawa awwab kunu

garin kullun yana nan acikin farin dan karamin

bokitin nan, tashi nihal tayi ta wuce binta da

kallo awwab yayi tana sanye da atamfa yelluwa

anyi mata dinkin bubu na zamani tasaka bakar

hula akanta wanda ta bayyanar da gashin kanta

kitchen tashiga ta kunna gas ta dora ruwan zafi,

minti biyar yatafasa tadama kunun gyadar ta sa

sugar tazuba peak milk gwangwani daya tazuba

masa acikin dan madaidaicin kofin tangaram

tanayi tana mita shi wannan mutumin sai son

saka mutane aiki,idan kunun yakeso yaje

matarsa ta dama masa mana dahaka tagama ta

dauko tashigo falon yana zaune inda ta barshi

yanata faman lallatsa wayarsa gaba daya

hankalinsa ya tattarashi akan wayar, mika masa

kofin tayi batareda tayi masa magana ba

shikuma sam bai kula da ita ba tsaiwar taci

gaba dayi shikuma yanata daddanna waya ganin

yaki karba yasata juyawa kitchen tamayar da

kunun ta ajiye itadai bazata yi masa magana ba

balle ya yarfata,domin bazata taba manta

wulakancin da yayi mata ba ranar data

gaisheshi, falon ta dawo zata zauna taji yace ina

kunun? Fasa zaman tayi takoma kitchen ta

dauko takawo masa batareda tayi masa magana

ba karba yayi yace thanks yakai kunun ya kurba

wani irin gardi da dadi yaji kunun yayi masa,

yanasha yana chtn bai san lokacin da ya shanye

ba sai da ya kalli cikin kofin yaga wayam,

kallonta yayi lokacin tana canja tashar satellite

daga tashar zee tv zuwa zee cinema tana

kamowa taga ana rungume rungume baki ta rike

tareda saurin canja tashar zuwa sunna tv hakan

datayi ba karamin bawa awwab dariya yayi ba,

kinga ungo kofin nan mayar kitchen tashi tayi ta

karba ta wuce daga nan bata dawo falon ba tabi

ta kofar baya ta fice takoma dakinta tana cewa

bari yanzu kuma naga wacce zaka aika, nan

awwab yasha zamasa har umma tafito suka yi

hira sai da aka kira salla sannan yayi mata

sallama yakoma side din Abba shima sallamar

yayi masa kasancewar gobe jirgin karfe 7 nasafe

zai bi. Gidansa yakoma yayi sallar mangraruba

yashiga dakin basma tana kwance tana waya da

mominta kusa da ita yaje yazauna yakama

hannunta ya rike cikin nashi, sallama tayiwa

mominta takwanta ajikinsa my man ya akayi

ne? Gobe iwar haka sai ni kadai ka tafi ka barni,

fuskarta ya shafa karki damu my dear babu

komai zan dawo bazan dade ba.

KWARYA TABI KWARYA3⃣0⃣

Na UMMI A’ISHA

Wuyansa ta shafo Allah yadawo min dakai

lfy, amin my dear yafada yana mai nutsa

hannunsa cikin tulin gashin kantin dake kanta.

Washe gari da sassafe awwab yatafi ibadan

aranar da yamma basma tashiga gidansu

awwab dan ta gaishe da umma tana shiga ta

hango nihal afalo ta mike akan kujera tana

kallon wani Indian film mai suna vadaraha, film

din yayi mutukar burgeta tana sanye da bakar

doguwar riga yar kanti mai santsi rigar tayi

mata das kamar dan ita aka dinkata kanta babu

dankwali ta tufke gashin kanta sannan ga wata

katuwar kalaba datayi kwaya daya a gaba tana

daga kwance takamo gashin tayi kalabar, cikin

jin haushinta basma tasamu wuri ta zauna jin

motsin mutum yasa nihal waiwayowa basma

tagani zaune sai cika take tana batsewa mayar

da kanta tayi takwanta taci gaba da kallonta

batareda tayi mata magana ba, suna nan zaune

shiru babu wanda yakula wani har umma

tasauko ganin basma yasa tafara murmushi

barka da zuwa yata, yanzu kika shigo? Eh

umma ban jima da zuwa ba nazo naga falon

babu kowa ne shiyasa nace bari nazauna

najiraki, ayya ai da kin hawo saman ina nan

afalo babu abinda nake saukowa kasa tayi

tagaida umma sannan takoma saman kujera

tazauna taci gaba da aikawa da nihal harara

wadda ita nihal din bata san tanayi ba, shiru

shiru batace zata tafi ba ita kuma nihal burinta

taji tace sai anjima amma shiru dan haka sai ta

tashi tahau sama takoma falon umma takwanta

taci gaba da kallonta ita kuwa basma sai da ta

dade sosai sannan tayiwa umma sallama. Batun

awwab kuwa tun lokacin daya koma ibadan yaci

gaba da shan giyarsa da bibiyar mata duk inda

yaga kykkyawa sai ya bita wasu kuma sune

suke kawo masa kansu da kansu amma duk

wanda yake cikin barikin nan yasan awwab

mugun manemin matane kuma cikakken dan

giya, sai dayayi sati 2 bai zoba asati na uku ne

yashiryo yanufo abuja jirgin karfe shida yabiyo

dan haka shida da rabi agarin abuja tayi masa.

Yana zuwa ya shiga gidansa daga shi sai kayan

jikinsa sky blue din riga t.shirt mai gajeren

hannu da bakin jeans sai yar karamar bindigarsa

wacce baya rabo da ita kamar koda yaushe

kamshin touch me yakeyi, dakinsa yafara shiga

kaca kaca babu gyara sannan yafito ya shiga

dakin basma itama dakin nata ba a kimtse

yakeba kuma da alama bata gidan, falo yadawo

yazauna ya danna kararrawa dagudu mary tazo

tazube agabansa, ina basma? Sir bata dawo

daga office ba, tun yaushe tafita? Sir since

around 11 in d morning tashi kije yafada tareda

mikewa yatafi zuwa gidan umma, amma fa yaji

haushin rashin samun basma ga wata irin

yunwa da yakeji, bari tadawo bazan yarda da

wannan yawon ba.

[1/12, 8:48 AM] Ummi A’isha: [10:21AM,

10/22/2015] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

Na UMMI A’ISHA

3⃣1⃣

Fitowa yayi ransa gaba daya yagama baci

da lamarin basma yana shirin fita yaga motarta

ta kunno kai fasa fitar yayi yakoma cikin gidan

ya tsaya yana jiran shigowarta ahankali tafito

daga motarta tabishi cikin gidan, zaune ta

taredda shi afalo welcome my man tafada tana

farfara idanuwanta thank you yafada yana

kallonta, daga ina kike? Cikin murmushi tace

daga aiki nake, wannan wanne irin aiki ne tun

safe har la’asar? Haba awwab kaima fa kasan

yadda aiki yake dole wani lokacin sai mutum

yayi overtime, look basma agaskiya yakamata ki

canja tsarin aikinki yana dakyau kiyi adjusting

din time dinki, oh sorry my man insha Allahu zan

gyara, to yanzu ni yunwa nakeji me zan samu

naci? Wash nima wlh da yunwar nadawo amma

bari nakira selesina ta sama mana abinda zamu

ci, kararrawa ta danna sai mary dagudu tazo,

mary bake nake nema ba ki turo min selesina

yes ma! Tafada tareda mikewa tafice shidai

awwab shiru yayi yana tunanin halayyar basma

sam bata son yin aiki ko kayanta idan tacire nan

zata watsar dasu sai dai su mary su dauke su

gyara tunda tazo gidan nan bata taba yin wani

aiki ba balle girki hatta ruwan zafi sai dai adafa

akawo mata bata da aiki sai bacci, selesina ce

tashigo tadurkusa gani anty, selesina kije ki dafa

min indomie guda 3 kisa kifin gwangwani guda

daya ok ma! Dasauri tamike tafita ita kuma

basma ta dauki handbag dinta tashiga dakinta

yayinda awwab yamike akujera yafara daddanna

wayarsa shidai mutum ne mai kyankyami da aji

sannan kuma duk inda dan gayu yakai cikakken

namiji mai class da kwarjini to awwab yakai

amma sai gashi basma tana neman maidashi

mai araha.

KWARYA TABI KWARYA

3⃣2⃣ Na UMMI A’ISHA

Yana nan zaune har selesina tagama

takawo tana kwallawa basma kira cewar

tagama, fitowa tayi daga dakin tana daure da

zani daurin kirji tajawo abincin ta ajiye agaban

awwab man muci tashi yayi yasa cokali yadiba

yaci gishiri mal kamar zai yi magana spoon din

ya ajiye yace zaije gidan umma kallonsa basma

tayi, abincin fa? Nakoshi yafada tareda ficewa

yanufi gidansu yana shiga falon umma yatarar

da ita zaune nihal tana yimata tsifar kai, sannu

umma yafada yazauna akusa da ita yawwa

awwab sannu da zuwa, gaisawa sukayi yadan

saci kallon nihal duk tabi ta bata rai kamar

wadda taga mutuwarta ita tunda yayi auren nan

take mitukar jin haushinsa duk taji ta washe shi

sam bata son ganinshi shida mummunar

matarsa,hankalinsa ya maida kan umma, umma

yunwa nakeji wlh, cikin kulawa umma tace to ai

da abinci akwai shinkafa da miya akwai dambun

shinkafa wanda nihal tayiwa abba, wanne

zakaci? Umma abani dambun, to nihal maza

kawowa yayanki abinci tashi tayi ta harareshi

tafita taje ta zubo masa tahado da ruwa da juice

takawo masa ta ajiye, budewa yayi dambun yayi

kyau gashi washar washar dashi sannan yasha

albasa da zogale dambune irin nagargajiya diba

yayi yafara aikawa cikinsa gaskiya dambun yayi

yafada acikin ransa baifi rabi yaci ba yature filet

din domin baya da cin abinci dayawa ruwan

kawai ya kurba amma juice din ko tabashi bai

yiba dan baya shansa sosai, kallonsa umma tayi

har ka koshi? Yakamata ka rinka cin abinci

gaskiya, wlh umma ahakan ma naci dayawa

yafada yana ciro cingum daga cikin aljihun

wandonsa yabare yajefa cikin bakinsa yafara

tauna ahanlali, baki nihal ta tabe azuciyarta

tana cewa jishi sai kace wani mace, kana namiji

kana abu sai kace mace ni nayi mamakin ma ta

yadda ka iya zama soja domin dukkan

kamanninka na yan hutune marassa aikin

wahala, domin kallo daya za ayi maka agane kai

dan hutune, tashi yayi yana maida wayarshi

aljihun jeans dinsa yacewa umma bari naje

wurin abba amma zan dawo kallonsa nihal tayi

ya wani rausayar da kai yafita, yana fita ta kalli

umma, wai umma shi wannan yaushe yazama

soja? Murmushi umma tayi tun shekaru 3 baya

lokacin yagama degree dinshi yana zama soja

kuma yakoma ya iyo masters dinshi,ba karamin

soja bane a babba yafito shiyasa idan kin ganshi

bazaki taba cewa soja bane.

KWAARYA TABI KWARYA

Na UMMI A’ISHA

3⃣3⃣

Girgiza kai tayi hakane kam umma sai dai

idan kaganshi da kaki sannan zakasan sojane,

kuma yadace da zama sojan sai dai shi dan

hutune tafadi hakan acikin zuciyarta suna nan

zaune yadawo ko zama baiyi ba yayiwa umma

sallama yace zai koma gida kuma gobe da

sassafe zai tafi ibadan akwai aikin da zaije yayi

addu’ar neman tsari umma tayi masa sannan

tace adawo lfy, amin umma yafada yajuya

yafita, bayansa nihal tabi da kallo oh kai kam

badai tsayi ba sa’arka daya bakada rama

dayawa, yana fita ko cikin gidan bai shiga ba

yadauki mota yafita bai zame ako ina ba sai

gidan giya anan yadamu ya dan ragewa kansa

zafi injishi da fada, giyar roba yasha yayi tatil

sannan ya dawo gidansa lokacin basma ta dade

da yin bacci, afalo ya zube cikin kujera yafara

bacci irin na mashaya barasa can acikin barcin

nasa yafara wani irin mafarki wannan yarinyar

tana binsa da gudu ga wuka a hannunta suna

cikin gudunne suka shiga wani bakin daji gashi

yagaji ana cikin haka sai ga wata mummunar

mata ta bullo masa hannunta rikeda takobi tana

zuwa ta daga zata sara masa sai ga wannan

yarinyar tazo, tana zuwa ta kareshi suka fara

fada da daya matar har Allah yabawa yarinyar

nasarar kashe wannan matar, tana kasheta ta

juyo gareshi dama alla alla yake ta jiyo domin

ya samu damar ganin fuskarta amma tana

jiyowa yayi firgigit ya farka zama yayi duk ya

jike sharkaf da gumi duk kuwa da cewa falon

katange yake da na’urar sanyaya daki wato a.c

tunani yafara yi aransa wannan mafarkin me

yake nufi? Kodai matan da nake bini? To ai dole

ne nabi mata domin mata ababan sone kuma

sun cancanci abisu, sai dai wannan mafarkin na

yau yafi na kullum razanashi, agogon falon ya

kalla karfe 1 dai dai nadare sai alokacin yatuna

cewa bai yi salla ba tashi yayi yashiga dakinsa

wanda yake a hargitse kamar ba nasa ba wai

duk gayun nan nasa amma dakinsa kamar na

umbo umbo dan rashin gyara shi kansa toilet

din akazance yake haka ya daure yayi wankan

yadauro alwala yafito.

KWARYA TABI KWARYA

Na UMMI A’ISHA

3⃣4⃣

Shiryawa yayi ya gabatar da sallar da take

kansa yatashi ya koma falo domin kyankyamin

dakin yake ji, yana nan zaune yanata faman

tunani har asuba tayi yatashi yayi salla sannan

yafara shirin tafiya, sai da ya shirya tsaf sannan

ya nufi dakin basma inda take kwance sai kace

macacciya sai bacci take yi tabata yayi tareda

girgizata basma! Basma! Cikin magagin bacci ta

bude idonta my man har ka tashi? Eh ni zan tafi

sai munyi waya, ok to Allah ya kiyaye hanya

tafada tajuya ta gyara kwanciyarta, fita yayi

daga dakin babu abinda yadauka in banda

bindigarsa da phones dinsa yanufi airport. Tunda

yakoma ibadan yaci gaba da harkokinsa kullum

sai yaje club, ga neman matan tsiya kamar me

tuni ya manta da basma ko waya baya yi mata

sai dai idan itace takirashi kuma kullum idan

yahau online sai yaganta tana online ya rasa da

wadanda take chtn dan sai takai karfe dayan

dare tana chtn wani lokacin sai yayi mata

magana sannan zata sauka, wasa wasa sai da

yayi wata daya a ibadan bai dawo abuja domin

yasan idan yadawo babu abinda zai yi domin

shi ahalin yanzu baya tunanin zai sake kusantar

basma kwana kusa har yanzu fushi yake sai ya

huce, abbansa ne yayi masa waya yafara

yimasa fada dan me zai ajiye yarinya yatafi

yabarta lallai lallai yazo abuja acikin satin nan

hakuri yabawa abba tareda cewa yana nan

zuwa. Ranar friday da yamma yashirya yabaro

ibadan zuwa abuja 3:30 yazo gida amma kuma

basma bata nan sai yan aikinta, zama yayi

yafara jan tsaki bai dade da zama sai gata

tashigo in banda kamshi babu abinda takeyi, ga

wata uwar kwalliya da taci sannu da zuwa dear,

cikeda takaici yakalleta basma wannan wacce

irin rayuwa ce? Kullum bazaki zauna agidan ki

ba kamar ke kikafi kowa aiki, yanzu kiduba

dakina tun waccan zuwan danayi yake kaca

kaca amma har yau baki gyara ba, am sorry my

man bari nakira mary tazo ta gyara maka, kar ki

kirata kece zaki gyara da kanki, kallonsa tayi

wlh bazan iyaba domin ni banma san yadda ake

yin shara ba balle moping, kuma agajiye nake

wlh kabari kawai mary ta gyara maka, nace miki

a’a ki barshi kawai.

[1/12, 8:48 AM] Ummi A’isha: [12:48PM,

10/22/2015] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

Na

UMMI A’ISHA

3⃣5⃣

Fita yayi daga falon ita kuma basma

cikeda rashin damuwa tawuce dakinta. Gidansu

yawuce kai tsaye yashiga falon umma amma

babu kowa da alama tana sama, benen yahau

anan kuwa yasamesu ita da nihal, umma tana

yiwa nihal kalaba akanta sallama yayi yashiga

cikin murnar ganinsa umma ta amsa nihal tana

jin shine tajawo dankwalinta tarufe kanta umma

bar min haka zan karasa ta tashi tazauna akan

kujera, russunawa yayi yagaida umma sannan

ya nemi wuri yazauna sai da akayi yan mintuna

sannan yace umma dama mata masu fita aiki

haka suke barin gidansu kaca kaca? Kallonsa

umma tayi a’a awwab suna gyarawa, to umma

banda basma domin dakina yana nan kamar

bola nayi nayi ta gyara min taki wai sai dai yar

aiki zatasa nikuma bazan amince mai aiki ta

rinka shigar min daki ba, murmushi umma tayi

to yi hakuri soja ni bana son ka rinka gwada

zuciyar nan taka akan basma saboda macece

mata kuma sai da hakuri, nihal saka hijabinki

kije gidan ki gyara mishi dakin kidawo kallon

umma tayi amma babu damar tayi mata musu

tashi tayi tadau hijab dinta tafita wannan shine

karo na farko da zata shiga gidan dan tunda

akayi auren bata taba sha’awar shiga gidan ba,

cigaba da yiwa awwab fada umma tayi kasan

basma agidansu babu abinda takeyi komai yi

mata akeyi kaga anan ma dole kayi hakuri tunda

tun farko da haka ta taso, to umma bayan

wannan ma hatta girki sai dai mai aiki tayi ita

ko tea bata iya hadawa ba, duk da haka dai kaci

gaba da hakuri, tashi umma tayi dakanta taje ta

hado masa abinci ta kawo masa. Ahankali nihal

take tafiya har tashiga gidan babu kowa afalon

amma duk yadda akayi dakin farko shine na

awwab dan haka shi tashiga taganshi gaje gaje

babu kyan gani har wani karni dakin yake, hijab

dinta ta cire ta shiga bathroom din ta tari ruwa

ta wankeshi tas tadawo dakin ta yaye bedsheet

din kan gadon da alama tun wanda aka shimfida

lokacin biki ne domin gashi nan yayi bakikkirin,

drower ta buda tagansu gasu nan kala kala

wani ruwan toka ta dauko ta shimfida tafara

share dakin tana cikin sharar basma ta shigo

dakin wa zata gani? Nihal tagani tana shara

nanfa basma tasha kunu.

3⃣6⃣

Itama nihal kunun tasha ta daure fuskarta ta

hade girar sama data kasa domin dama bata

son ganin basma ko kadan ,juyawa basman tayi

tafice daga dakin batare da tace komai ba

ammafa aranta masifa ce fal awwab kawai take

jira yashigo dan ta tsattsage shi, nihal kuwa

cigaba da aikinta tayi tagyara dakin sosai yayi

kyau sai kamshi yake domin ga airfeshener nan

sunfi kala 5 amma dan tsabar rashin gyara ba

atabasu balle ayi amfani dasu tsayawa tayi tana

kallon dakin ita kanta dakin ya burgeta yanzu

domin ta ajiye komai a muhallinsa, hijab dinta ta

dauka tafito lokacin basma tana zaune afalon

tacika tacika tayi fam kamar zata fashe ko

kallon inda take nihal batayiba tafita nan fa

basma takara kuluwa, ita kuwa nihal gida

takoma inda tabarsu shi da umma anan ta

samesu kallonta ya danyi ta gefen ido yaga

ranta abace yake dama yasan za ayi haka,

zama tayi umma tana cewa kin dawo, um umma

nadawo satar kallon awwab tayi ya tsurawa

wayarsa ido da alama akwai abinda yakeyi

kallonsa taci gaba dayi yana sanye cikin bakar

t.shirt mai dogon hannu da botira agaban rigar

yasa bakin trouser hannunsa na hagu daure da

agogon azurfa na Gucci dan yatsansa na tsakiya

sanye cikin zoben azurfa mai kyau, agaskiya

awwab ya hadu iya haduwa, girgiza kanta tayi

wlh bakayi sa’ar mataba kwata kwata tafada

acikin zuciyarta me za ayi da basma? Cases

tafada ahankali dagowa da kansa yayi ya kalleta

caraf suka hada idanu gabanta taji yafadi tayi

saurin dauke nata idon shima awwab jin

gabansa yayi yafadi,dama shi ya saba jin

wannan faduwar gaban tun lokacin da yafara

ganinta, tashi yayi yace da umma shi zai tafi

sunkuyar da kanta nihal tayi aranta tana cewa

agaida mummuna fita yayi ya nufi gidansa yana

shiga ya tarar da basma afalo dama shi take jira

yana zuwa ta mike tsaye tafara masifa

3⃣7⃣Kadawo daga yawon tona min asirin?

Shine zakaje ka turo min wannan ficiciyar

yarinyar tazo min gida, to wlh wannan yazama

na karshe duk ranar da tasake gigin zuwar min

gida sai nafasa bakinta aikin banza aikin wofi,

wuri awwab yasamu ya zauna bai tanka mata

ba har sai da tagama sannan yace basma ya

mukayi dake? Saifa dana rokeki kan kigyara min

dakin nan amma kika ki, to da ban gyara ba ai

nace maka zan sa mary tagyara kaki ko?

Yazanyi maka? To ai shiyasa naturo wata ta

gyara min, ai kuwa duk ranar da takara zuwa

sai nadauki mataki akanta wlh kallo yabita

dashi kin nuna min aikinki yafini muhimmanci

ko? Kibar aikin nan kizauna ki kula da gidanki

da mijinki,a’a awwab kada ma kasoma fadar

haka domin alqawari mukayi dakai cewa zanyi

aiki kuma zan cigaba da karatu to shikenan

tunda haka kika zaba kije kiyi, daki ta wuce ta

barshi zaune a falon oh! Mata matsala ne

yafada tareda dafe kansa sai da yadade azaune

sannan yashiga dakinsa yana shiga yaganshi

tsaf fes fes in banda kamshi babu abinda yake

tashi acikin daki gefen gadon yaje yakwanta

haba ai komai yana son gyara yafada tareda

mike kafaduwansa akan gadon, yau baya ra’ayin

zuwa club amma dai yasan yanada giyar kwalba

daya acikin mota.

3⃣8⃣ Da hanzarinsa yafita inda motarsa take

yabude ya dauko yadawo dakinsa ya bude

kwalbar ya shanye ta tas sannan ya tura

kwalbar kasan gadonsa duk da cewa yasan

basma tasan yana dan kurbawa bararrajewa

yayi akan gadon nan bacci ya sureshi bashi

yatashi ba sai tsakiyar dare nan kuma ya zauna

har asuba tayi sai da aka kira salla yayi sannan

ya koma bacci, 11 yatashi yayi wanka ya sanya

kananan kaya wanda sukayi mutukar yi masa

kyau yafito dakin basma yashiga amma bata

nan har tafita aiki wato su aikinsu babu asabar

babu lahadi kenan ransa ne yabaci sosai yafito

babu komai akan dining table da alama dama

bata ajiye masa komaiba cikin bacin rai yafito

yatafi gidan umma, agaskiya lamarin basma da

gyara sai ya seta mata zama zasu daidaita

dakin umma yashiga saboda falon babu umma

tana zaune abakin gadonta tana waya nihal har

kinje malam madorin? Eh to shikenan Allah ya

kaimu sai kindawo, Malam madori kuma?

Yatambayi kansa nikuwa ai nataba zuwa Malam

madori a rayuwata, bazan taba mantawa da

wannan garin ba

3⃣9⃣ Zama yayi agefen gadon umma, umma

ina kwana? Lfy awwab, anfito? Eh umma,kayi

break? Wlh umma banyiba to kaje kan dining

akwai abinci yana nan, to umma godiya nake

tashi yayi yafita yakoma falo ya hau kan dining

yafara zuba farfesun kayan ciki ya hada tea

yasha can kasan ransa kuma tuna garin malam

madori yakeyi, ai kuwa bazai taba manta malam

madori ba da wannan tunanin yagama yin break

din yadawo falon ya zauna acikin kujera

yakunna tashar kwallo yafara kallo. Sai yamma

yakoma gidansa yayi wanka ya shirya yafita har

lokacin basma bata dawo gidan ba shima fitarsa

yayi yatafi club tun lokacin club din acike yake

da yayan manya yan duniya said sharholiyarsu

suke nan shima yashiga sahu anan kuma

yasamu sabuwar budurwa zahar tun daga nan

suka fara holewa bashi yadawo gidansa ba sai

12 nadare lokacin itama basma bata dade da

shigowa ba dakinsa yawuce ya kwanta basma

tana jinsa amma bata tashi ba taci gaba da

kwanciyarta. Washe gari ma lokacin da yatashi

basma ta dade da fita har yamma bata dawo ba

ganin bata dawo ba yasashi shiryawa yaje

yayiwa umma sallama yayi tafiyarsa abuja, ita

basma bata san yatafi ba sai dataga 12 ta wuce

sannan tasan baya gari jijjiga kai tayi tace Allah

ya raka taki gona dama idan ka zauna ma

bawata uwar kake tsinana min ba.

4⃣0⃣Tunda awwab yatafi bai kara

waiwayowa abuja ba sai bayan sati 3 aranar da

yadira basma bata gidan kwanciyar sa yayi yai

bacci domin shigowar dare yayi, ba ita tashigo

ba sai wurin 9 kaji ma’aikata tana zuwa tayi

kwanciyarta da alama bata san awwab yadawo

ba. Wayewar garin sai 11 awwab yatashi yayi

wanka yahade cikin wata Orange din riga t.shirt

yasa blue din jeans yadora jacket asaman rigar

kasancewar garin kwana akayi ana sheka ruwa

gashi weather din ta canja sanyi ya juyo, falo

yafito basma na zaune sannan ga wasu maza

guda 2 suma suna zaune akan daya kujerar cikin

mamaki basma ta kalleshi my man dama kana

nan? Banza yayi da ita? Suwaye wadannan

kuma? Abokan aikina ne akwai abinda muke

tattaunawa dasu ne tsawa ya daka musu tareda

nuna musu kofa sim sim suka tashi suka fice

sannan yadawo gareta ke wacce irin

mahaukaciya ce, dabba marar tunani? Kwata

kwata bakya daraja aurenki saboda tsabar

rashin sanin yakamata cikin masifa itama ta

mike kar ka kara aibantani ai dama sai da

nafada maka zanyi aiki kuma ka aminta dan

haka yanzu baka isa ka hanani ba kallonta yayi

ai kuwa dole sai kin bar aikin nan ko kuma ki

hakura da zaman aurena, wlh bazan bar aikiba

tunda mun yita da bajewa dama kai ka fada min

auren yanzu kwarya tabi kwaryane ma’ana

yimin inyi maka, ka fita aiki nafita aiki, juyawa

yayi yafita yabar mata gidan, gidansu yanufa

yasamu umma itada nihal suna yin break a falo

cikin bacin rai ya gaida umma yafara fada mata

abinda basma tayi masa tareda fadin wlh umma

nagaji da halinta sakinta zanyi dai dai lokacin

abba ya shigo falon yaji abinda awwab yafada

hakuri umma tasoma bashi shikuma abba ya

zauna yana sauraren har suka gama gyaran

murya abba yayi yace awwab! Na’am abba!

Awwab nabaka nihal akaro na 2 ka aura kamar a

mafarki awwab yaji maganar itama nihal kamar

mafarki taji, nima ummi A’isha kamar a mafarkin

naji

[1/12, 8:52 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:50 AM]

Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA

4⃣1⃣

Na UMMI A’ISHA

Shiru nihal tayi tana son jin yadda awwab zai

karbi zancen amma abin mamaki sai ta jiyo

muryarsa yana yiwa abba godiya tareda addu’ar

Allah yasa yin Allah ne harda cewa abba nagode

nagode Allah yabaka aljanna hakika nasan duk

inda ake neman uba nagari to ka kai Allah

yasaka maka da mafificin alheri, amin awwab

inji umma sannan tajuya ga abba tace nan da

yaushe kake ganin za ayi bikin? Nan da 3

months ai yayi ko? A’a gaskiya ayi nan da

karshen this month domin ba wani taro zamuyi

ba duba da yadda jama’a zasu ga bai wani jima

da aure ba kar azo anayi damu agari, kinyi

gaskiya hajiya aisha hakika kinyi tunani mai

kyau yawwa kaga da zarar an daura aure sai mu

bashi matarsa ya dauketa su tafi, wannan haka

yake hajiya Allah yakaimu lokacin amin, tashi

abba yayi yafita daga falon shima awwab din

tashi yayi yabi bayansa ita dai nihal kanta yana

kasa tunda aka fara maganar ta sunkuyar

dakanta sai da taji fitarsa da abba sannan ta iya

daga kanta ta kalli umma wadda farin ciki

yagama cikata shiru tayi tofa! Awwab zai zama

mijinta basma kuma zata zama kiahiyarta wani

bacin rai ne ya ziyarci zuciyarta ashe dama miji

daya zasu aura da basma? Shiyasa taji ta

tsaneta tsana mai yawa tashi tayi tashige

dakinta ta kwanta. Abangaren awwab kuwa

abba yabi ya sake yimasa godiya sannan yafita

zuwa golden touch hotel anan ya Shafe awanni

yana holewarsa sai daf da magriba yadawo gida

ko lokacin da yashiga bai samu basma ba dan

har yanzu bata dawo daga aiki ba, bai damuba

yashiga yayi wanka yashirya yafito yau wankan

nasa na daban ne kamar wanda zai je zance

farar shadda mai mutukar tsada yasaka tareda

saka farar hula ga agogon fata fari ya daura

sannan yasanya harp cover dinsa shima fari,

turaren secret amber yafesa nan yadauki kamshi

kamar wani sabon ango.

[1/12, 8:51 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

4⃣2⃣

Na UMMI A’ISHA

Gidansu ya hara yana tafe yana waya da ogansa

da haka yashiga gidan, falon umma yayiwa

tsinke tana zaune itada su talatu mai aiki gefe

kuma nihal ce ta mike akan doguwar kujera

idanuwanta arufe kujerar kusa da ta umma yaje

yazauna tuni masu aikin suka firfice, hira suka

farayi da umma sama sama nihal taji

sanyayyiyar muryarsa ahankali ta bude

idanuwanta tafara kallonsa yayi kyau sosai

kamar bafulatani gashi kayan da yasa sun

amshe shi sosai, yaune karo nafarko da tayi

masa kallon kurulla dataji zai zama

mijinta,komai nashi acikin sanyi yake yi ita

kanta maganar sa asanyaye take kallonsa taci

gaba dayi daga kansa har zuwa kafarsa

agaskiya yayi bala’in haduwa matsalarsa daya

shan giyar da yakeyi domin bata san yana

neman mataba, sai da yashafe sama da minti

40 sannan yayiwa umma sallama tareda fadin

tunda ita wannan bacci take umma natafi da

sauri ta rufe idanunta yatashi yafita. Gari yana

wayewa aka kirashi a ibadan dole ya shirya

yatafi lokacin karfe 6 nasafe ko umma ma sai

awaya yafada mata dan bai samu damar shiga

gidan ba. Tunda yatafi ayyuka sukayi masa

yawa bai samu damar zuwa abuja ba ganin

bashida isasshen lokaci yasa yayiwa yayarsa

waya tareda tura mata kudi mai yawan gaske

domin ta hadowa nihal lefe,dama umma ta

sanar da ita komai dan haka babu bata lokaci

taje ta iyo siyayya Kaya masu tsada ta tarkato

akwati takwas da dan karamin kit nacikon tara

dayake ba wani taro zasuyi ba ita kadai takawo

kayan gidan umma lokacin nihal tana gyarawa

umma dakinta sai kawai gani tayi anata shigo

da akwatina masu kyau ko ba afada mata ba

tasan nata ne aka kawo sai dai gidan tsit babu

wata hayaniya hakan ya tabbatar mata da cewa

iya anty jamila ce ita kadai ta kawo kayan har

kasa ta tsugunna tagaida ta kamarsu daya da

awwab sai dai ita tafishi hasken fata, tashi tayi

tafita daga falon taje dakinta tafada gado wai

dagaske itace zata zama matar awwab? Ganin

abin take kamar a mafarki tunanin irin zaman da

zasuyi da basma tashiga yi saboda ta tabbatar

shi awwab bashida matsala domin baima cika

son hayaniya ba balle ya tsaya zaman fada da

mace dan a yadda ta fuskanta ma basma itace

take cutar dashi bashine ke cutarta ba, Allah dai

ya sausauta min zuciyata domin nayi mutukar

tsanar basma tafada aranta.

[1/12, 8:51 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

4⃣3⃣

Na UMMI A’ISHA

Umma ce ta leko tace taje ga kayanta can

na lefe tagani cikin jin kunya tace umma ni basai

nagani ba kyaleta umma tayi tafita tana cewa

kya gani ai idan Jamilan ta tafi ita dai nihal

shiru tayi takwanta. Sai da biki ya rage saura

sati 1 sannan awwab yasamu kansa yakarbi

hutu nasati biyu yadawo abuja yana zuwa

gidansa yafara shiga yauma komai a hargitse

babu gyara kamar babu masu aiki agidan gashi

basman bata nan itadai ta barwa masu aiki

gidan bata dawowa sai dare kuma tun safe take

fita dakinsa yawuce yayi wanka yasake dressing

ya shirya cikin kananan kaya dark brown din

riga da light brown din wando yafeshe jikinsa da

turaren touch me yafito yanufi gidan umma tuni

ita ta dade dafara shirye shiryen bikin duk da

cewa dai bawani taro zatayi ba sai nakusa ne

kawai zasu zo falon abbansa yaje suka gaisa

daga nan yafito yashiga falon umma babu kowa

afalon sai nihal datake kwance akan doguwar

kujera take bacci tana sanye cikin atanfa mai

box kalarta yeluwa da baki kanta ba dankwali

tasa dantsen hannunta ta rufe fuskarta kallonta

yatsaya yi gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce

sosai gata da gashi waje yasamu ya zauna yaci

gaba da yimata kallon kurulla sai da yashafe

wajen minti goma yana kallonta sannan ta dan

motsa ahankali ta dauke hannunta tabude

idonta caraf suka hada ido sake kallonsa tayi

kamar a mafarki ta ganshi kamshinsa duk ya

baibayeta tashi tayi taja dan kwalinta ta daura

ahankali tace sannu da zuwa, yawwa sannu

yafada yana kallon tv, ina wuni? Lfy yagida? Lfy

tafada ta tashi tashiga kitchen ta dauko masa

ruwa da lemo tazubo masa dambun nama ta

doro akan tire takawo masa hakan datayi ba

karamin dadi yaji ba, yanzu yaga wani

girmamashi take tun lokacin dataji an bashi ita

tadaina yi masa tsiwa wadannan harare hararen

ma duk ta daina yimasa thank you yafada

ahankali sama tahau taje dakin umma takirata,

tare suka dawo falon, yaci dambun naman

kadan yasha ruwa amma bai sha lemon ba

domin shi baya harka da lemo babbar harka

yake sha gaisawa sukayi da umma anan take

tambayarsa ko ya sanar da basma zancen

aurenshi? A’a umma ban fada mata ba amma

yau dai nake son sanar da ita, tashi nihal tayi

tabar falon shi kuma suka cigaba da tattauna

maganar shida umma.

[1/12, 8:51 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

4⃣4⃣

Na UMMI A’ISHA

Sai wurin karfe 8 awwab yabar gidansu yayi

niyyar yaje club amma yafasa yashiga gidansa

lokacin basma tadawo tana zaune da yar best

da dogon wando baki tana cin indomie tana

kallo sallama awwab yayi yashiga cikeda

mamaki ta amsa tana kallonsa my man yaushe

ka sauka agari? Akusa da ita yazauna yana

cewa tun yamma nashigo lokacin bakya nan,

ayya wlh gidan bikin friend dina naje shiyasa,

kallonta yayi shine baki fada min ba? Oh sorry

nakira wayarka bata shiga ba, murmushi yayi ok

no problem yanzu kin san me nakeso dake?

Girgiza kanta tayi dan Allah ki rinka gyara

dakina da naki,oh my man munyi maganar nan

fa wlh banida time din gyarawa kuma ban iya

bama amma nace maka zansa Mary tashare, no

nace miki ban yarda suna shigar min dakina ba

haba basma ni shikenan banida sirri komai nawa

sai mai aiki tasani? To amma ai naga wannan

yarinyar ma tashiga dakin naka ita kuma

awanne matsayi take? Ni yanzu duk ma ba

wannan ba gobe zan tura miki 5 hundred

thousands acikin account dinki, murmushi tayi

kai amma fa nagode, ki sai dukkan abinda

kikeso domin zan kara aure ne, zumbur ta tashi

kamar wadda aka mintsina aure awwab? Me

kake nufi? Wulakancin naka har yakai kamin

kishiya tun yanzu? Yaufa watanmu 5 da aure

kwata kwata, me kakeso duniya tadaukeni?

Domin duk matar da akayi mata kishiya bata

shekara ba dole axargeta, look basma ki

kwantar da hankalinki babu wanda zai zargeki

domin duk duniya babu wanda yasan sirrin dake

tsakanina dake wlh babu wanda nataba yunkurin

fadawa kuma kar ki damu kanki bawata bakuwa

zan aura ba nihal ce kuma abba ne yabani ita

kinga bani da halin da zan musanta abinda yace,

cikeda masifa basma ta dubeshi dama ai

nadade da sanin haka zata faru tunda kana

zaune da munafukai, zunbur shima ya mike

suwaye munafukan? Su wadanda suka hada

auren tas! Yadauketa da mari iyayen nawa ne

munafukai basma? Dama bakida mutunci? Gaka

nan marar mutunci macuci wlh idan kayi auren

nan sai nakasheku kai da ita domin natsaneta

natsaneta bana son ganinta amma saboda

tsabar rashin adalci ace da ita za ahada ni

kishi? Wlh bazan yafeba Allah ya isa tsakanina

daku Allah ya dora maka masifa da bala’i acikin

rayuwarka, bai sake kulata ba yajuya yashiga

dakinsa, dakin ta bishi tana mai ci gaba da tsine

masa amma ba saurareta ba yashige toilet don

yin wanka duk da haka bata fasa zaginsa shida

iyayensa ba har yafito duk da haka rabuwa da

ita yayi saboda shi baya son fada da mace da

maza yasaba fada sune daidai shi amma yaushe

zai wani zauna yana kace nace da Mace sai

kace wani soko? Shi aganinsa duk mai musayar

yawu da mace bai cika namiji ba.

[1/12, 8:51 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

4⃣5⃣

Na UMMI A’ISHA

Kayan baccinsa ya saka yahau gado ya

kwanta amma basma bata barshi yayi baccin ba

saboda ruwan rashin mutuncin da tayita xuba

masa, munafuki shiyasa ka turota tagyara maka

daki saboda kana so ka nuna mata banida kima

da daraja a idonka to wlh sai kayi nadama, ashe

dama an san abinda ake kullawa shiyasa tunda

nazo gidan nan sau daya kataba hada gado dani

daga karshe kabini da sharrin cewa ni ba

budurwa bace, to ai kaima ba saurayi bane

tunda manemin mata ne kuma mashayin giya

rayuwar auren yanzu kuwa sunanta KWARYA

TABI KWARYA kayi min inyi maka, haka taci

gaba da maganganu da zage zage har gari

yawaye, tana ganin yafita masallaci tashiga

dakinta tasa kayanta tadauki wayarta tafito

tadau motar ta tanufi gidan iyayenta. Tana

zuwa tafada jikin momynta tafashe da kuka

tafara labarta mata abinda yafaru, cikeda masifa

momy tace wulakancin dazai yimana kenan?

Yayi miki kishiya tun yanzu salon a rainaki to

wlh bai isaba zai zo gidan nan yasameni wlh sai

naci mutuncinsa sai naga waye ya tsaya masa

kuma ma ai da laifin iyayensa dan me zasu

kyaleshi yayi aure tun yanzu? Cikin kuka basma

tace wlh momy sune ma suka sashi yin auren

amma da bashida ra’ayin ajiye mata 2,kiyi shiru

basma nasan laifin uwarsa ne itace zata sashi

to wlh bazaki koma gidansa ba har sai yagane

kurensa, kuma aiki ne dole sai kinyi ko yaki ko

yaso karatu ma kina samun admission zaki

koma, sannan ko agidan nan bakya yin shara da

gyaran daki dan haka bazaki fara agidansa ba,

dafatan kin sanar dashi ke ko agidanku bakya

dafa ruwan zafi bare girki? Eh momy duk nafada

masa yawwa kinyi min dai dai shalele na dan

haka kishare hawayenki daidai lokacin dadynta

yashigo ai nan ya tambayi abinda yafaru momy

tasanar dashi fada shima yafara ni alh mansur

zai ciwa mutunci? Yayi kyau zamu hadu dasu

wlh sai nadau mataki akansu. Agidansu awwab

shirin biki kawai aka sa agaba kuma awwab bai

sanar daasu umma cewar basma bata nan ba

shi kansa shareta yayi duk kuwa da cewa

mahaifinta yayi masa waya yace yazo yana son

ganinsa bayan ya zazzaga masa masifa dan

hatta gaisuwar da yayi masa bai amsa ba ganin

haka yasa awwab ya sharesu, shirin aurensa

kawai yasa agaba wanda yanzu ya rage saura

kwana 2 kacal.

[1/12, 8:55 AM] Ummi A’isha: [1:29PM,

10/25/2015] Ummi A’isha: [10:05AM,

10/25/2015] Ummi A’isha: KWARYA TABI

KWARYA

4⃣6⃣

Na UMMI A’ISHA

Ranar juma’a bayan an taso daga

masallaci da misalin karfe 2 aka daura auren

awwab da nihal akan sadaki naira dubu 50

babban limamin masallacin shine yayiwa awwab

walinci yayin da abba yayiwa nihal walinci,

awwab yasha kyau sosai cikin farin yadi mai

mutukar tsada komai mai tsada yasa tundaga

yadin jikinsa har agogon hannunsa da

takalminsa kamar auren fari dan idan ba sani

kayi ba zata zakayi wannan shine aurensa

nafarko, ana dawowa daga wurin daurin auren

yawuce gidansa amma sai me? Gidan duk anbi

an kukkulle ko ina da manyan padlocks babu

inda aka bari abude nan fa yaji yakulu yafito ya

tambayi mai gadin gidan ina masu aikin?. Alh

yanzu duk hajiya da mahaifiyarta sukazo suka

rufe gidan suka debesu suka tafi juyawa kawai

yayi yafita yashiga gidansu babu kowa agidan

sai yayarsa jamila da umma da nihal cikin

takaici yafara fadawa umma,umma kinga

yarinyar nan ita da mahaifiyarta sunzo sun rufe

min gida ko? Yi hakuri awwab bari na tura nihal

ta gyara maka side dinka nada tunda ba wani

dadewa zakayi ba kwana nawane, wuri yasamu

ya zauna yana huci, tashi nihal tayi tatafi side

din nasa ta gyara masa tadawo tawuce dakinta

daga nan bata sake ganinsa ba sai dare tana

zaune afalo wayar umma nakusa da ita yakira

tadaga hello umma ahankali tace ba umma bace

ok to ki kawo min abinci dan Allah to tafada ta

ajiye wayar tashiga kitchen tahado masa akan

tire takoma dakinta ta fesa turare dama tafi

amfani da Arabian perform irinsu nashwa,

aroosa, shaikah, lailatul sahara da sultan abyad

duk sai da fesa su ta yafa gyale tafito tadauki

tiren tanufi side dinsa. Ahankali ta tura kofar

falon tashiga yana zaune yana waya takai kayan

gabansa ta ajiye takoma kujerar nesa dashi ta

zauna. Kusan minti 5 sannan yagama wayar

yajuyo ya kalleta dawo nan ki zauna yanuna

mata kusa dashi, babu musu tadawo kusa dashi

ta zauna kamshinta kawai yaji yajishi ya rude

ahankali yashiga jikinta, hawayene suka fara fita

daga idonta shar shar da sauri ya kalleta meye

abin kuka? Dan Allah kayi hakuri da abinda

zakaji daga bakina sannan dan Allah kayi min

alkawari bazaka sakeni ba kallonta yayi yaga

jikinta sai rawa yake hannunta yakama kar ki

damu wlh nayi miki alkawari bazan sakeki ba

kuma bazan rabu dake ba kome zanji daga

gareki i promise you! Cikin kuka tace ni ba

budurwa bace wlh wanine yayi min fyade

shekaru uku da suka wuce awani dare nataso

daga islamiyar dare ina cikin tafiya naci karo da

wani saurayi dayake duhu ne ban ganshi ba

nataka shi kawai sai ji nayi ya mareni zafin

marin yasa nazageshi nace Allah ya isa ban

yafeba shege mugu yana jin yajani wani kango

ya toshe min bakina yace yau sai yayi maganin

rashin kunyata anan yayi min fyade dayake duhu

ne banga fuskarsa ba.

[10:45AM, 10/25/2015] Ummi A’isha: KWARYA

TABI KWARYA

4⃣7⃣

Na UMMI A’ISHA

Ji tayi awwab ya rungumeta ahankali ya

lalubi kunnenta yace lallai Allah shine gwanin iya

hikima, nine saurayin da nayi miki fyade dayake

Allah gwanin hikima ne sai yahadani dake anan

yabani ke a matsayin matata, zunbur ta tashi

tafara ja da baya dama kaine macuci azzalumin

da ya bata min rayuwata? Yayi sanadiyar barina

gidan ubana, yayi sanadin da ubana ya tsine

min albarka yayi tir dani mutanen gari suka

tsaneni, wlh bazan zauna dakai ba kai mugune

sai ka sakeni sai ka rabu dani natsaneka

natsaneka bana son ganin kome kama dakai

bazan zauna dakai ba kuma wlh sai kaima ka

dandana bakin ciki kamar yadda ka dandana

min,alkawari nayi duk ranar danaga wanda ya

gurbata min rayuwa sai na kasheshi kuma har

yanzu ina nan aka bakana yanda ka rusa min

rayuwata kaima sai narusa taka idonta ne yakai

kan yar karamar bindigarsa wacce baya rabuwa

da ita zaraf ta dauka ta riketa taseta shi wlh

kaima sai na nakasa ka kamar yadda ka nakasa

ni sai alokacin awwab yayi magana ki kasheni

sai ki huce amma wlh bazan sakeki ba domin

nayi alkawari bazan rabuda ke ba duk tsanani

bindigar ta danna ji kake tau ta harbeshi a cinya

duk dauriya irin tashi sai dayayi yar kara tuni

harsashin ya huda cinyar sa jini ya fara fita tana

ganin haka ta yarda bindigar tafice da gudu

shikuma awwab dakyar ya dau wayarsa yafara

kiran abbansa yasanar dashi nan da nan sai

gashi arude,ya taimaka masa suka fito suka

shiga mota sai wani private hospital anan aka

shiga dashi theatre kwararrun likitoci suka yi

masa chaaa!. Acan gida kuwa nihal tana fita

dakin umma tashiga tana kuka tafada jikin

umma tana fadin wlh umma bazan zauna

dashiba sai ya sakeni shine mutumin da ya cuci

rayuwata wlh natsaneshi bana sonsa cikin bacin

rai umma tace dama awwab ne yayi miki fyade?

Wlh bazai taba yiyuwa domin nafi son farin cikin

yata akan dan wani, ni ina nan ina tattalin

rayuwarsa ashe shikuma yana can ya rusar

dataki rayuwa yazama dole na kwato miki

yancinki yata.

[12:13PM, 10/25/2015] Ummi A’isha: KWARYA

TABI KWARYA

4⃣8⃣

Na UMMI A’ISHA

Cikin kuka nihal tace umma nidai kawai

kisa yasakeni domin bazan zauna dashi ba

kanta umma tashafa itama hawayen take nihal

sai yasakeki mutukar hakan zai samar miki farin

ciki domin nafi son farin cikinki dana sa.

*********************** Acan asibiti kuwa cikin

mintuna kalilan likitoci sukayi nasarar cire

harsashin sukayi masa allurar bacci awwab

yasha wahala mutuka, baccin minti goma sha

biyar yayi yafarka abbansa ne ya matso wurinsa

ji yake kamar yafashe da kuka dan tausayin

dansa hannun awwab yakama son waye ya

harbeka? Hawaye ne yaziraro daga idon awwab

abba ka taimaka min bazan iya rabuwa da nihal

ba wlh ina tsananin sonta idan narabu da ita

mutuwa zanyi, kadaina kuka my son kaifa soja

ne ko kamanta ne? Kai yagirgiza abba kar

karabani da nihal dan Allah bamai rabaka da ita

son mutukar bakai ne ka saketa ba wayarsa

yadauka yakira umma yafada mata asibitin da

suke yace tazo yanzu yanzu, mintuna kadan sai

gata lokacin awwab yasake komawa bacci tana

shigowa tace Alh ina fata dai takardar sakin

nihal ya rubuta min shiyasa ka kirani? Cikeda

mamaki abba yace haba hajiya aisha awwab fa

bashida lfy harbinsa akayi gashi kuma yanata

yimin wasu maganganu cewar kar narabashi da

nihal,ai kuwa dolensa yasaketa dan tace bazata

zauna dashi ba kallonta abba yayi kin san kuwa

abinda kike fada? Eh nasani ko kana nufin zan

goyi bayan danka nafaranta wa danka na

kuntatawa tawa yar? To wlh bazan taba bawa

danka farinciki na kuntatawa yata ba domin

yanda kake son danka haka nima nake son yata

nama fika sonta domin son da nakewa yata

baka yiwa danka dai dai lokacin awwab yafarka

yabude idanunsa yana kallonsu abba ne

yakalleta cikin takaici yace hajiya aisha baki

isaba babu mai raba awwab da nihal duk kuwa

da cewa kina takamar kece kika haifeta to wlh

nafi son farin cikin dana fiyeda nakowa zan iya

yin komai domin naga na sama masa farin ciki,

cikin daga murya tace haka zalika nima zan iya

sadaukar da rayuwata domin naga nayiwa yata

abinda takeso, yanda kake son danka haka nake

son yata wata tara nayi ina dauke da ita acikin

cikina tafasa jikina tafito kaga kuwa ta cancanci

nayi mata dukkanin soyayya, kai kuwa baka san

ciwon nakuda ba baka san zafin haihuwa ba,

bazan taba raya naka dan ni nakashe tawa ba,

to wlh duk abinda yasamu dana sai na daure

yarki indai tayi sanadiyar mutuwar dana, wlh

kana daure min yata nima sai nakama danka na

daure duk abinda kake takama dashi nima ina

dashi.

[12:37PM, 10/25/2015] Ummi A’isha: KWARYA

TABI KWARYA

4⃣9⃣

Na UMMI A’ISHA

Badai dukiya da mukami da mulki kake

takama dashi ba? Kai kanka kasan nafika dukiya

nafika hanya nafika yawan masu daurin gindi,

yanda kake takama kana rikeda mukamin

minster nima na rike wannan mukamin dan haka

dani dakai kar wanda yafasa, KWARYA TABI

KWARYA amma ina mai tabbatar maka nihal

bazata zauna da awwab ba kuma sai nayi

kararsa dalilin keta mata haddi da yayi, cikin

zafin rai abba yace karki fasa kiyi kararsa sai

me? Kidau lawyer nadau lawyer inyaso sai aga

wanda zai yi nasara amma duk fitinarki awwab

bazai saketa ba sai dai idan shine yayi ra’ayin

hakan, ai kuwa dolensa domin yata bazata

zauna da dan giya ba manemin mata tas! Kakeji

abba ya dauke umma da mari kar ki kuskura Ki

sake muzanta dana, karya nayi masa? Duk

wanda yasan danka yasan cikakken mashayin

giya ne kuma kwararre afannin neman mata

wasu hawaye ne suka fara sintiri akan kumatun

awwab gaba daya ji yayi ya tsani rayuwar,da

ace yana iyawa to da yasaki nihal ko dan

yaraba gardamar dake tsakanin umma da abba

amma bazai iya ba jin sonta yake yana ratsa

bargonsa kuma sai yau yasan ashe nihal yar

ummance muryar abba ce tadawo dashi hajiya

aisha ina iya yimiki saki uku akan dana wlh kar

ki yarda ki kureni, cikin kuka awwab yace

umma! Abba! Dan Allah kuyi hakuri, nahadaku

da girman Allah da kuyi hakuri dan Allah kar ku

rabu akan wannan maganar ko kallonsa umman

batayi ba tajuya tafice daga dakin, hawaye

awwab yaci gaba da zubarwa wanda ni kaina

ummi A’isha sai da nayi mamaki ganin soja

kamar awwab yana kuka, kusa dashi abbansa

yazo yazauna yafara shafa kansa awwab kayi

shiru kadaina kuka rabona danaga kukanka tun

ranar da mahaifiyarka ta rasu kayi hakuri kaji?

Abba kar kasaki umma akaina nasan umma

akan gaskiyar ta take duk uwa tagari bazata

aura min yarta ba domin ni bana gari bane ni

mashayin giya ne, manemin mata, ban tsayar da

salla ba bana tasbihi bana istigfari bana salatin

annabi duk wata dabi’a ta mutanen kwarai

banida ita lallai dan kuka shi yake jawa uwarsa

jifa yau gashi ata dalilina ana yimaka gori abba,

tir da hali irin nawa yafada yana kuka kamar

karamin yaro.

[1:14PM, 10/25/2015] Ummi A’isha: KWARYA

TABI KWARYA

5⃣0⃣

Na UMMI A’ISHA

Kadaina kuka awwab bana son kukanka,

kaima da nagari ne kaji kar ka damu kanka bari

nayiwa yayarka jamila waya nasanar da ita halin

da kake ciki fita yayi domin kiran anty jamila

awaya shi kuma awwab ya runtse idonsa yana

jin haushin kansa domin tun lokacin da abba ya

auro umma bai taba jin kansu ba ko musu

basayi amma yau gashi abba ya mari umma

agabansa sabodashi yana ikararin saki, hawaye

ne suka biyo kumatunsa oh! Allah saukaka

wannan masifa badan halina ba ya Allah yana

nan zaune in banda hawaye babu abinda yake

sai kace wani ragon maza har su abba suka

shigo shida anty jamila dasauri takaraso bakin

gadon sannu awwab amma gaskiya umma

tabani mamaki datayi haka amma babu komai

nihal dai bazaka saketa ba sai dai idan ita abba

zai saka kuma wlh idan wani abu yasamu dan

uwana bazan yarda ba tana cewa zataje kotu

ko? To sai gareta muna nan muna jiran

sammaci ko ta manta mijina shine shugaban

alkalan Nigeria gaba daya? Ai bata isa tayi

mana komai ba babu abinda zata iyayi dan tana

takamar ta taba zama minister? Wlh munfi

karfin dauri a kasar nan bazamu dauru ba,

hannu awwab yadaga mata dan Allah anty

jamila kar ki maida hannun agogo baya, kai

awwab kana tunanin zan kyaleta ne taciwa

ubana da kanina mutunci? Wlh bata isa ba ba a

halacci matar da zata zagi ubana na kyaleta ba

yanzu daga nan gidan zanje na mayar mata da

martanin abinda datayi kuma wlh sai tabar

gidanmu dan bata isa tazauna tana yiwa

mahaifinmu rashin mutunci ba shiru awwab yayi

anty jamila kuwa sai fada take tayi tana nan

zaune masu aikinta da driver dinta suka kawo

abinci wurin kala 5 sai wurin 9 tayiwa abba da

awwab sallama tafita bata tsaya ako ina sai

gidan abba tana shiga tasamu umma zaune

afalo hannunta rikeda faranti da fruits akai tana

shan apple ko sallama batayiba ta shiga ta rike

kugu ta tsaya tafara yiwa umma kallon banza

tareda fadin naji sakonki zakiyi karar dan uwana

ko? To ba hakuri nazo nabaki ba illa nazo

nasanar dake cewa har yanzu bakiyi kudin da

zaki iya daure awwab ba sannan bakida arzikin

da zaki tozarta zuri’armu domin munyi miki

nisa! Tashi umma tayi shi uban naki ne yaturo

ki kiyi min rashin kunya? To ki koma ki sanar

dashi karace ban fasa ba sai nayi karar dansa

yasaki yata kuma sai an kwato mata hakkinta

na fyaden da yayi mata, saki yazama dole dan

bazata zauna dashi ba duk wanda yasan dansa

yasan dan giya ne manemin mata haka kawai

yaje ya dauko cuta yasaka mata bazata taba

yuyuwa, cikin rashin kunya jamila tace haka fa,

me za ayi da matar uba? Allah yatsinewa matar

uba aduk inda take sannan awwab zai saki yarki

in yaso ki jikata ki shanye, mari umma

takawowa anty jamila cikin zafin nama tarike

hannun umma wlh kina marina ramawa zanyi

bar ganin kina matar ubana, cikin masifa umma

tace badake zanyi ba da ubanki zanyi me za ayi

da yayan miji? Gayyar masifa sakin hannunta

anty jamila tayi tajuya tafita tana fadin muna

jiran sammaci, tana fita umma tadau hadaddiyar

wayarta tafara kiran wata kawarta wadda ta

kasance babbar lauya mai zaman kanta tare

sukayi school a university of akwaibom inda take

karantar low ita kuma tana karantar medicine.

[6:17PM, 10/25/2015] Ummi A’isha: Nasan

wannan sako zai isa ga mai amfani da wannan

pin din na bbm chat (56523C1F ) duk da ban

sanka/sanki ba naga kin/ka canza min labarina

na MACE GUDA DAYA TILO duk da gargadin

danayi akarshen littafin amma sai da kuka

canza min to ina mai fada da babbar murya

ALLAH YA ISA domin labarin mace guda daya

tilo kirkirarren labarine da nazauna nabata

lokacina nashirya shi amma ki/ ka canza min, to

ban yafe maka/maki ba.

Ummi A’isha

[1/12, 8:56 AM] Ummi A’isha: [7:45AM,

10/27/2015] UMMI A’ISHA: KWARYA TABI

KWARYA

5⃣1⃣

Na UMMI A’ISHA

Kiran barrister laure tafara yi ringing 2

tadauka tana gaidata cikin bacin rai umma tace

barrister kina ina ne? Ranki yadade ina birnin

kebbi ayanzu haka naje wani case amma next

week zan shigo abuja, wani abune yafaru? Yes

barrister yaron mijina nayanzu ne yayiwa

yarinyata fyade kuma yanzu ya aureta ita kuma

tace bazata zauna dashi ba shine nake so ki

kaimin case din kotunku, to ranki yadade kidai

bari nadawo zan zo gidanki mu tattauna, ok

thank you barrister sai naganki, ajiye wayar tayi

tana faman hucin bacin rai.

***********************

Acan asibiti kuwa awwab yana can kwance yau

kimanin kwanansa 5 kenan abbansa shine yake

zama dashi dan yanzu ko office baya zuwa

sa’arsu daya asibitin sune suke kulawa da

patients dinsu ba a bukatar yan zaman jinya,

yayinda anty jamila itama kullum sai tazo itace

take kawo musu abinci da duk abinda zasu

bukata, ita kuwa umma tun ranar da abin yafaru

bata kara dawowa asibitin ba balle taga halin da

awwab yake ciki, yau jikin nasa da sauki don har

yatashi zaune suna hira da abba, turo kofa akayi

aka shigo anty jamila ce dauke da wani food

flask mai dankaren kyau sannu abba, awwab

yajikin takaraso tana murmushi, jiki yayi sauki

anty jamila nan da gobe za a sallamemu, to

Allah yakara sauki amma awwab yazama tilas

ka saki wannan yarinyar dan tunda tayi maka

haka zata iya kasheka watarana,anty jamila

kidaina fadin haka wlh ina son nihal har cikin

raina, taba baki tayi kai dai kasani tunda kaji

abinda uwarta tace sotake ta tozarta mu kuma

wlh bata isaba idan tayi wasa kafin ta daureka

ni sai na daureta,kiyi hakuri anty dan Allah wuri

tasamu tazauna tana fadin ita za abawa hakuri

ai tunda ita aka batawa, shi dai abba yana jinsu

bai ce musu komai ba.

********-*-********-*

Umma ce zaune acikin kasaitaccen

falonta taci ado cikin wata jar atanfa super

tasha gwalagwalai a hannunta da kunnenta da

wuyanta abinka da farar mace nan tafito das da

ita, sallamar barrister laure ce tacika falon

tashigo tana barka da hutawa ranki ya dade,

cikin murmushi umma tace yawwa sunnu da

zuwa barrister, bisimilla ga wurin Zama,zama

tayi suka gaisa tadubi umma tace ranki yadade

ina sauraronki cikin damuwa umma tayi mata

bayani sannan takara da cewa ni yanzu so nake

akwatowa yata hakkinta kuma kotu tasa

yasaketa don bazata zauna dashiba, murmushi

barrister laure tayi tace ranki yadade a shawarce

wannan case din bai kamata akaishi kotu ba

saboda family issue ne zuwa kotu babu alfanu

acikin wannan case din abinda nake so dake

shine kiyi hakuri ki bani dama ni zanyi muku

sulhu, yanzu ina awwab din yake? Awwab yana

asibiti shida mahaifinsa kuma barrister nifa babu

sulhun da za ayi mana domin yayarsa jamila har

gidan nan tabiyo ni taci min mutunci dan haka ni

bazan yarda ba, ranki yadade hakan dana fada

miki shine masalaha domin a ka’ida dama shine

yafi dacewa daya aureta domin ko a kotu

hukuncin da za ayanke kenan kuma hajiya aisha

ai hakan shine babban rufin asirinku domin idan

kukaje kotu to kun tonawa kanku asiri sannan

kuma duk ranar da nihal tayi aure zata fuskanci

matsala dan haka dan Allah kibani dama nida

kaina zanyi solving din wannan case din, girgiza

kai umma tayi shikenan barrister nabaki dama,

sallama barrister laure tayiwa umma tatafi.

[8:09AM, 10/27/2015] UMMI A’ISHA: KWARYA

TABI KWARYA

5⃣2⃣

Na UMMI A’ISHA

Barrister laure bata zame ko ina ba sai

asibitin dasu awwab suke, bayan ta dubashi tayi

musu bayanin cewa gobe zatazo gida tasamesu

tana son ganinsu har anty jamila, babu damuwa

Allah yakaimu inji anty jamila. Washe gari aka

sallamesu daga asibiti awwab yawarke misalin

9:30 suka isa gida lokacin barrister laure har

taje gidan, suna zuwa suka shiga falon anan

suka tarar da umma da barrister laure zaune,

babu wanda yayiwa umma magana acikinsu illa

gaida barrister da sukayi, kallonsu barrister laure

tayi tafara jawabi ranki yadade babu maganar

tashin tashina dan Allah, abinda nakeso daku

shine kubar awwab yaci gaba da zama da

matarsa domin babu wanda ya san tsakaninsu,

maganar fyade dama duk wanda muka samu

yayiwa yarinya fyade to dole ne ya aureta sai

dai idan yaki ne muke kaishi kotu ayi masa

hukunci dan haka ni ina ganin shaidan ne

yashiga tsakaninku ya bata maganar amma

maganar gaskiya shine bai cancanci awwab ya

saketa ba, hajiya Aisha kibawa alhaji mansur

hakuri bisa abinda yafaru umma batayi musu ba

tace Allah yabaka hakuri alh, kallonta barrister

tayi yawwa ke kuma jamila abinda kikayi baki

kyauta ba tsakaninki da hajiya bai kamata ayi

hakaba, kema kibata hakuri domin ada kin

dauketa a matsayin uwa kuma itama ta daukeku

a matsayin yaya idan mutum basani yayiba

bazai taba cewa ba itace mahaifiyarku ba cikin

karamar murya anty jamila tace Allah yabaki

hakuri umma, babu komai jamila Allah yakara

hada kanmu murmushi barrister tayi to komai ya

wuce yanzu abawa awwab matarsa murmushi

umma tayi ai tana malam madori tun ranar da

abin yafaru ta tafi, tashi abba yayi yafada yana

yiwa barrister godiya yawuce side dinsa kallon

umma awwab yayi to umma ai kuwa gobe zan je

nadaukota dariya anty jamila tayi ai kuwa zaka

hadu da basma yaro, ai kuwa dai inji umma, ni

wlh harma namanta da ita, to ai kuwa jiya

momynta takirani amma ban dauka ba inji

umma, garama dabaki dauka ba anty jamila

tafada tana dariya ita dai barrister laure tashi

tayi tai musu sallama ta tafi tabarsu sunata

hirarsu kamar wani abu bai faruba. Daren ranar

awwab bai runtsa ba tunani yake tayi haba

shiyasa yarasa a inda yasan nihal ashe itace

yarinyar daya yiwa fyade lokacin yaje wurin

abokinsa musaddik yanzu ma abokin nasa

yarasu, tun lokacin dayayiwa nihal fyade yashiga

harkar neman mata domin akanta yafara sanin

mace amma har yau baiyi dace da mai ni ‘ima

kamarta ba kullum tunanin yanda zai ganta yake

ashe itace nihal, Allah nagode maka yafada

insha Allah gobe zanzo gareki matata.

[8:28AM, 10/27/2015] UMMI A’ISHA: KWARYA

TABI KWARYA

5⃣3⃣

Na UMMI A’ISHA

Da misalin karfe 9 nasafe awwab yafito

zuwa dakin umma yayi kyau sosai cikin blue din

wagambarin da yasa, yasa hula blue da agogon

azurfa na guess watch, kamshin turaren touch

me da catch me sai tashi yake daga jikinsa, a

daddafe yasha tea da wainar kwai bayan sun

gaisa da umma yayi mata sallama bayan yakarbi

address din gidansu nihal yanufi side din

mahaifinsa suka gaisa yayi masa sallama yafito

yashiga motarsa kirar BMW blue mai bakin glass

yafita, gudu yayi sosai daga abuja zuwa jihar

jigawa daf da azahar ya shiga garin malam

madori awani masallaci ya tsaya yayi salla

yafito yashiga cikin garin bai wani sha wahala

ba yasamu gidansu nihal babban gidane da

alama itama mahaifinta babban mutum ne,

fitowa yayi yashiga gidan mai gadi yayi masa

jagora har falon mahaifinta, shiga awwab yayi

yasamu babanta zaune yana cin abinci kwara ne

kana ganinsa zaka gane hakan domin idan

kaganshi baza ka zata yana jin hausa ba saboda

basu da maraba da indiyawa shi kansa gashin

kansa yalo yalo yake, cikin girmamawa awwab

ya duka ya gaisheshi ya amsa cikin fara’a,

bayani awwab yayi masa na cewar yazo wurin

nihal ne shine mijinta, nan da nan mahaifinta ya

gintse fuska, dama Kaine ka auri yata batare da

sanina ba? Saboda tsabar Aisha bata daukeni da

daraja ba shine ta aurar min da yarinya bata

sanar dani ba to dama ina jirane kazo kabata

takardar ta dan tun dadewa nayi mata miji da

wani yaron kirki, hakuri awwab yafara bashi

amma yaki ya saurareshi daga karshe ma tashi

yayi yashigewarsa gida nanfa awwab yadade

azaune daga karshe shima yatashi yafita yanufi

wani guest house yakama daki ransa adagule,

sallar la’asar yayi, yayi order abinci aka kawo

masa harda kwalbar giya, daukar giyar yayi

yabude har yakai bakinsa zuciyarsa tace amma

idan kasha kacika marar zuciya karfa kamanta

gorin da akayi maka akan kana shan giya,

ajiyewa yayi yaja tsaki domin shi aka’idarsa

indai aka yimasa gori akan abu to yabar abin

nan kenan har abada.

[12:20PM, 10/27/2015] UMMI A’ISHA: KWARYA

TABI KWARYA

5⃣4⃣

Na UMMI A’ISHA

Daren ranar awwab bai iya runtsawa ba

kamar yadda itama nihal batasamu damar yin

bacci ba tunda mahaifinta yasanar da ita zuwan

mijinta, hankalinta yagama tashi kawai addu’a

take Allah yasa kar awwab yayi fushi ya saketa

kuka tasawa mahaifinta cikin sigar lallashi

yafara kwantar mata da hankali ta hanyar cewa

yasan awwab koda yatafi to zai dawo ita dai

shiru tayi dan gani take kamar awwab yatafi

kenan gashi yanzu tana tsananin sonshi, har

aka kira assalatu bata runtsaba. Tunda sassafe

awwab yatashi ya shirya karfe takwas dai dai

yaje gidansu nihal yauma kamar jiya mahaifinta

na nan zaune acikin wani babban falo, har kasa

awwab ya durkasa ya gaidashi kafin yafara

bashi hakuri akan ya kyaleshi da nihal,

murmushin abban nihal yayi yace yaro babu

komai haka Allah ya shirya kuma haka ya

kaddara, nabaka nihal kuma ina so kariketa da

amana idan ka cutar da ita ban yafe maka ba,

awwab kamar zai yi kuka yace insha Allah zan

rike nihal da amana kuma nayi alqawari bazan

cutar da itaba, murmushi mahaifin nata yayi

shikenan, nihal ita kadai ce yata dana mallaka

mun rabu da mahaifiyarta tun tana yar shekara

7 a duniya awurina ta taso amma gashi aure zai

rabani da ita yanzu duk da haka nayi farin ciki

Allah yabaku zuri’a dayyaba shiru awwab yayi

baice amin ba dan yana jin kunyar abban nihal,

tashi yayi yace bari nashiga ciki na sanar da ita

zuwanka domin ta kimtsa tafito kutafi,to abba

nagode madalla Allah yakara girma, mintuna

kadan sai ga wata yarinya da tire tazo ta ajiye

agabansa tareda gaida shi tiren yabude wainar

shinkafa ce da miyar agushi murmushi yayi

wannan shine best food dinsa amma yau dakyar

in zai iya ci saboda dokin ganin matarsa domin

nihal wani bangarece ta rayuwarsa itace mace

tafarko daya fara sani kuma tun daga ita bai

kara jin dadin sex ba gashi dai alokacin ba ta

dadin rai yayi mata ba asalima bai je inda

yakamata yaje ba ga ciwo da ya jijjimata amma

duk da haka yaji sweet shiyasa yadade yana

burin sake kasancewa da ita, ashe itace yarinyar

da yayita mafarki da ita sai yanzu yagano

fassarar mafarkinsa, yana nan zaune shiru yana

jiran fitowarta, ita kuma tana can gida

mahaifinta yana yimata nasiha tunda taji awwab

yazo taji wani sanyi acikin zuciyarta dama tun

jiya tagama shirya kayanta komai yazama

ready,idonta cikeda hawayen rabuwa da abbanta

tafito da katuwar trolley dinta taje jikin motar

awwab ta tsaya, abbanta ne ya leka yasanar da

awwab fitowarta tasowa yayi yafito shima ganin

awwab bai ci abincin ba yasa abbanta yasa aka

saka musu amota saci ahanya, awwab yana

fitowa tafara kallonsa tagefen ido lokacin yana

yiwa abba godiya, yayi kyau yana sanye da milk

colour din dafaffen boyel mai kyau yasa hula

kalarta milk sai kamshi yake kallonsa taci gaba

dayi aboye har yagama yiwa abba sallama yazo

ya bude kofar motar yashiga itama tashiga

tazauna dan kallonta yayi tasa bakar doguwar

riga da dan karamin hijab iya kafadarta shima

baki sai hawayen rabuwa da mahaifinta.

[12:47PM, 10/27/2015] UMMI A’ISHA: KWARYA

TABI KWARYA

5⃣5⃣

Na UMMI A’ISHA

Dan murmushi mai ban sha’awa yayi

yadaura belt yafara driving, har sukayi nisa bata

daina kuka ba kuma bata kalleshi ba murmushi

yasakeyi yasan dama fushi take yi dashi sai da

akayi tafiya mai nisa sannan tayi shiru tashare

hawayenta, dai dai wata bishiya yayi packing

gaba jeji baya jeji yacire belt din yace kifito kiyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *