LABARIN RAYUWATA CHAPTER 2 BY Ayeshay bee

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 2 BY Ayeshay bee

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

A hankali Suhaima ke samu sauki,  da ke akwai orthopaedic  doctor in da ke zuww asibitin yana duba ta. Abin yana zuwa da sauki sosai don har an fara koya mata taka kafan.  Qur’ani kuwa tun ranar da su ka fara da Dr Fahad bai yarda an tsaya ba,  har ma sunyi nisa. Ganin tana saurin dauka ya sa ya ke dan hada Mata da wasu littatafai gabadaya. Suhaima ko jinta ta ke wani fayau kaman ba ita ba saboda azkar in da ta sa gaba d istigfari. Hakanan kawai ta ke jin ta cikin annashuwa,  kaman rayuwar ta ya canja gabadaya, sai yanzun ta gane ba abinda ya kai ka koma wa Allah dadi.

+

A gidan su Rufaida ko tuni su ka fara shiryen shiryen bikin da ya rage sauran wata uku sai dai ba tare da sa hannun ango ko Amaryan ba. Wani zuwan mahaifin Fahad da su ke Kira Abbah Kaduna ne ya ga irin ramar da Rufaida tayi gabadaya ta yi baki ta rame. Ganin hakan ya sa ya Kira ta gefe don Jin ko aiko abinda ke damun ta game da auren amma ta tabbatar mishi bbu, Fahad inma sai da ya tuhume shi ko akwai abinda ya ke mata shi ma dai babun ne. Mahaifin ta Baffah ya samu akan ko su hakura da auren tunda yaran kaman ba su so. Aiko ya ga bacin rai gun Baffah, kaca kaca ya mishi da ke daman shine Yaya, ya tabbatar mishi da ba abinda zai sa a fasa wannan auren. Don Haka Dr Fahad da Sister Rufaida sai hakuri.

“Oh yau dai ya kamata muje mu duba Suhaima gsky” Anty Ke maganan tana typing a system inta, Zaune su ke gabadaya a parlor suna kallo Amma as a workaholic ba ta iya Zama hakanan. Lecturer a Kaduna polytechnic da ke tudun wada, tana koyarwa da Course in SLT wato Science and laboratory technology. Mace mai ilimi sosai da ta San mahimmanci karatun boko Kuma ta daraja shi. Haka yaranta gabadaya ta daura su akai domin ko gabadayan su ba dakiki, da kanta ta ke sparing time ma ta musu lesson. sai dai Kuma Kash! Bata ba Ya’ya’n ta karatun addini kaman yanda ta basu na bokon ba. Ba Wai ba suyi bane gabadaya, Aa suna zuwa islamiyya kullum sai dai ko kadan ba ta damu da ta tmby su abinda aka koya musu koma ta koyar dasu kaman yanda ta ke wa na bokon.

Da murna Anisa ta tashi “Yauwa daman 2 days nayi missing inta so Zan biki”

“Nima zanje” Muhibba ta fada hankalin ta na Kan littafin da take dubawa. Kusan ita ce ta dauka gabadaya halin Antyn a gidan, kullum ka ganta da littafi gaban ta.

Nan fa Kulsoom da twins su ke ihun su ma zasu je har sai da Faroukh ya daka musu tsawa sannan su ka natsu.

Siririn tsaki ya ja “Za ku Wani cika ma mutane kunne”

“Ehm ehm Faroukh ban son zalunci fa”

“Allah Mummy sai ana musu haka ne. Ni wai Mummy wai wannan yarinyar ba zaku nemi iyayen ta bane ko Kuma Zaku huta haba!”

“Amma ai kana ganin kokarin da babanka da Uncle Musty ke yi ko”

“Mummy mutanen tunda fa kuka ji haka ba zasu fito ba, may be bata dasu ne”

“Ni dai yanzu tashi ka shirya da Kai zamu fita” tashin yayi ya nufi hanyan dakin shi yana gunguni “Duk Mimin nan ta jawa mutane”

“Haka kace a kunnen Uncle Musty” Da sauri ya juyo ya daga hannayen shi alaman surrender “Wai mommy ki rufa min asiri kisa aji mu da Uncle”

Mustapha ba ya gari so Maryam da Haydar kawai ta nufi asibitin. A haraban asibitin su ka hadu, da gudu Kulsoom ta je wurin ta daman ita ce mutuniyar ta, a daddafe su ka gaisa kafin su karasa cikin asibitin.

Dr Fahad da Suhaiman ne kawai a daki yana mata bayanin wani hadisin sahihul bukhari. Yana ganin su ya ajiye littafin kafin ya juyo gaida Anty “sannnun ku da zuwa, Anty Ina Kwana” Ya kirata kaman yanda yaji Su Mustapha na kiranta. Da murmushi kwance a fuskan ta ta amsa hadda zolayan shi”Dr naga alamun ka Saba sosai da patient in nan naka, anya za ka sallamo mana ita kuwa?”

“Ai Anty Ina ganin nan da 2 weeks ma za ayi discharging in nata”

“Ah Ma Sha Allah jiki kam yayi sauki Alhmdlh”

Gabadayan su suka gaisa da Suhaima hade da Mata ya jiki bayan Dr ya fita Amma banda Faroukh da ya maida hankalin shi gabadaya Kan wayan shi. Sai daga baya Anty ta lura sannan ta zungure shi “Kai wa Faroukh lafiyan ka, ba ka iya gaida mara lafiya bane” tabe baki yayi kafin ya juya ya watsa mata wani mugun kallo “sannu ya jiki?” “Alhmdlh” kawai ta bashi amsa ba tare da ko Kallon shi tayi ba. Ganin Anty ta cigaba da yin fadan ya sa yayi saurin mikewa zai bar dakin.

“Yauwa Faroukh please dan siyo airtime tunda fita zaka yi” Maryam ta fada.

“Ai ni ba bawan ki bane ba” Bai jira Jin wani comment ba ya rufe kofan dakin “Allah ya shirya” Anty ta fada tana girgiza Kai. sai dai Muhibba ce ta je ta siyo mata credit in.

Ba su wani Jima ba su ka bar asibitin amma sun bar Maryam a nan da ita ba lokacin za ta tafi ba.

Dr Fahad ko Yana barin dakin ya hadu da Rufaida idanuwan ta sun kumbura sun yi ja alamun kuka tayi. “Me ya same ki?” Ya tambaye ta cike da mamaki. Kauda kanta tayi saurin yi sannan ta maida idanuwan ta kasa. “Kai na ke ciwo” kallo daya ya mata ya San ba asalin abinda ke damun ta kenan ba, Ya mata sanin da zai iya gane ta inta yi karya ko Kuma tana kokarin boye wani abu. Shaking Kan shi yayi “Kar ki fada min abinda ba shi bane don kin San zan iya gane ki” wannan karon Kam shiru tayi domin ta San magana daya zata yi ta rushe da kuka. Wayan da ke hannun ta ya bi da kallo da alamun waya ta gama. “Mu ga wayanki” ba musu ta mika mishi, Yana amsa yayi sliding cikin call logs inta. Sunan Fa’iza ya gani karshe “Wani abu ya faru a gida ne?” Girgiza kanta tayi. “Okay Zan wuce gida tunda am now a stranger to you baki iya fada min damuwanki, karfe nawa za ki gama schedules inki na asibitin” “Four” ta bashi amsa.

“Shknn Zan zo in dauke ki” ya fada kafin ya wuce abin shi.

Aiko Yana komawa gida ya tarar da abinda ya sata kukan. Daga kofan falon ya ke jiyo Muryar Dada tana ta wa Aliyu fada cikin natsuwa “Haba Aliyu zagi za ka ja min, ni dai nasan ban baka wannan tarbiyyan ba”

“Ki yi hakuri Dada na bata Miki rai amma ba Zan iya Kallon ana ci Miki fuska ba inyi shiru” girgiza Kai tayi cike da takaici “Allah ko Ali? Amma har kana iya maidawa Mahaifiyar ka magana ko bakomai ai ta ci darajan Abbanku da yayanku ko balle Kuma ta haifeka”

“Toh Dada Kiyi hakuri ba Zan sake ba” badan ranshi yaso ba ya fada bai jira ma amsan ta ba ya tashi ya fita daga Falon kaman zai fashe, ba ta dakatar dashi ba sanin irin zuciyan shi. Ai ko a kofan falon su ka ci karo da Fahad, kallo daya ya Mai ya kauda Kai ya wuce dakin shi. Fahad ko jiki a sanyaye ya karasa Falon.

“Dada sannu da gida”

“Ushe binga am har en yattake? Noi kude?” (Sannu dana har ka dawo? Ya aiki)

“Alhamdulillah, Dada Ummi ta Zo ko?” Idon shi kasa ya ke magana, kana Jin kasan ya shiga wani Irin hali. Tausayi ma ya bawa Dadan sai dai ba sai ta bashi amsa ba yanayin shi kadai ya tabbatar mata da ya riga ya sani.

“Dada Kiyi hakuri Dan Allah, In Sha Allah watarana za ta gane”

“Bakomai Dana Nima ban taba riketa ba. Yanzun ma akan aurenka da Rufaida ne. Ni nace ma ko za a hakura domin zaman lafiya yafi zama dan sarki amma Baffanku ya ki zancen” murmushi ya kakalo Wanda ya tsaya iya labba kawai “Kar ki damu In Sha Allah aurena da Rufaida za ayi shi cikin kwanciyar hankali.”

“Ehm ehm Binga am, kasan bakin uwa kuwa? Kar kazo ka samu matsala daga baya Ina jiye maka tsoro”

“Allah ya San ba biyayya na ki Mata ba Dada Kuma bata da kwakwaron hujja a addinance da za ta hana aurena da Rufaida” shiru Dada tayi don ka tasan gsky Aliyun ke fadi.

Faizah ya kwala wa Kira ta fito “ki same ni a sashen mu” kawai yace kafin yayi wa Dada Sallama ya bar falon.

Tun kafin ya karasa sashen nasu ya ji Karan shigowan text wayan shi ko daya duba Ummi ce: Hamma i’ve warned her so consider the marriage cancelled. Murmushin takaici kawai yayi a ranshi Yana fadin “its not that easy Ummi” don ita acewarta Dada ke sa Baffah yin komai ta mallake shi, unknown to her Baffah mutum ne murdade da in yayi niyyan abu to fa ba Wanda ya Isa ya canja mai.

A hankali ya juyo ya kana Kallon Faizah da tayi five minutes tana jiran ya mata magana. “Meye sa Kika Kira Rufaida Kika fada mata abinda ke faruwa a gida?” Gabadaya jikin ta rawa ya ke sanin ba ya musu wasa har gumin wahala ta fara hadawa “ba magana na ke Miki ba?”

“Yayah ka yi hakuri pls” wani irin harara ya bita dashi “ba abinda na tambayeki ba kenan”

“Kawai kawai fa na kirata ne sai na bata lbr”

“Saboda gaki parrot ko? Ba ki San asibiti ta ke ba tana treating patient in ta je tayi mistake fa rai nawa Kika wahalar? Bayan kinsan halin Faidah da Saurin rudewa” wannan karon gabadaya kasa ta zube tana bashi hakuri ganin yanda ya ke fada sosai. Tsaki ya ja “infact me ya dawo da ke gida?”

“Weekend nazo”

“Weekend tun ran Thursday? Ki hada kayanki you are going back right now maza” da sauri ta bar dakin. Aliyu da ke zaune yana sauraran su ne ya ja dogon tsaki “ba fa ita ta Kar zomon ba” Yana fada ya fuske ya cigaba da danne danne a wayan shi.

“Aliyu ni kake wa magana haka?”

“Yi hakuri ba da Kai nake ba?”

“Da Mahaifiya ta?” Shiru Aliyu yayi kafin ya tashi ya shige cikin dakin shi.

Sai da ya Kai Faizah har cikin KASU sannan ya nufi asibitin dauko Rufaida.

Suhaima ya fara zuwa dubawa ya samu tana ta bacci abun ta. Nan da nan ya ji ran shi yayi sanyi. Lallai fa sauki ya samu, ya dan Jima a dakin Yana Kallon sleepy face inta. Tsintar kanshi yayi da ciro waya ya fara snapping inta. Ya dauka kusan biyar sannan ya bar dakin yayi dialling numban Rufaida. Daman ta gama shiryawa so tana ganin numban shi ta yima Nabeela sallama ta fita haraban asibitin.

Tana fita ta hango shi suna magana da Dr Najib, kawai sai ta wuce wurin motan shi. Ta Kai five minutes tana jira kafin ya taho “Sorry Amarya na barki ko?” Bata tanka shi ba har ya tada motan su ka bar asibitin.

“Ina zamu je?”

“Gida” ta amsa a takaice

“No not there, let go somewhere”

“Ya Fad fa na gaji, I’ve been working since morning”

“Inda Zaki huta Zan Kai ki and I guess tomorrow is ur day off”

Turo baki tayi kaman za ta fashe shi abin ma dariya ya bashi, wato Faidah ba zata taba canjawa ba.

“Pardon me” kawai ya ce ya cigaba da driving.

A crystal garden yayi parking, wani open space su ka nufa, the place scream peace and beautiful!

“You still come here?” Ta fada with some suprise expression.

“Why not? I like it comfort, Bismillah nasan you are hungry”

“I can’t eat here”

“Ni kadai ke Kallon ki”

“Still”

“Come on I’ve feed you with my own hands” sanin ba zai yi giving up ba yasa ta fara cin snacks in.

“Rufaida” ya Kira sounding serious, ganin haka ta Mika mishi attention in ta gabadaya.

“Are you willing to marry me?” Shiru tayi for some seconds tana tunain Mai zata fada mishi, a hankali ta fara magana “is not like I have a choice”

“Ina saurayin ki”

Shiru tayi gabadaya jikin ta yayi sanyi, ba ta San sanda kwalla ya fara cika Mata idanu ba “Ya fad he dumped and betrayed me, he cheats on me” zuwa yanzu Kam kuka ta ke sosai, shi dai Fahad ka Sa ce Mata komai yayi sai kallo da ya ke binta dashi, ya najin kaman ya ja ta jikin shi ya rarrashe ta Amma he can’t, ba da bane. She looks hurt and pale, hanky ya ciro da ga cikin aljihu ya Mika Mata “can you please stop crying for him”

“Ya fad am am hurting inside” ta fada with a stutter.

“I understand but share hawayen ki kiji” yi tayi kaman yanda yace in tana ajiyan zuciya, tsaya yayi har sai da tayi calming kanta sannan ya ce “tell me me ya faru? Spit it”

“He used me, Yayi succeeding ya sa na fara son shi but he ends up betraying me claiming me that Ina resembling Ex in shi da ta yaudara shi and that’s why he choose me ya rama abinda ta mishi. Is it fair? I don’t even know her fa, ba laifina bane and I can believe me he say it to my face” by now she is mercilessly sobbing.

“karki damu maybe daman shi in ba alkhairi bane a gareki don haka ina fatan zaki fawwalawa ALLAH dukkan lamuranki”

“Bakomai ya fad, i feel ease now that i share it out”

“you should have done that since. by the way, meye sa baki kawaye”

“i have some little”

“Ina nufin ƙawar da zaki iya tunƙara kin sanar da ita da mun ki, hakan yana da amfani sosai”

“you have always been my friend since from time”

“still, Kinsan ance ciwon mace na ƴa mace. ina ganin kaman za tafi fahimtar ki fiye dani. you even have trust issue Faidah”

“Ya Fad kawayen nan sai a slow kananun maganganu da gutsiri tsoma bai taba karewa”

“Just one ma ta isa and if you can consider Nabeela, she likes you” dago kanta tayi tana kallon shi cike da mamaki, aiko four eyes su kayi maimakon ya dauke winking ma ya mata, saurin saukar dana ta tayi”

“That aside for now let give an us a chance”

“you mean”

“i mean let make this relationship works, we don’t even have another option” da dariya ya ida zancen nashi making her smile.

“okay”

“you mean YES!” Nodding kanta tayi in affirmative.

“That will be good” shiru yayi yana nazarin abin da zai fada mata, ya kuma zata dauki maganar tashi.

“Ya fad you want to talk”

“waya fada miki?”

“i can read you”

“okay! ehmm faida maganan Ummi nake son miki, kinsan despite all her flaws i still love her ko”

“nasani” kanta a kasa ta bashi amsan.

“so please ina son kiyi hakuri kuma kar ki raina min ita, mahaifiyata ce she deserves my respect”

“bakomai ya fad, Allah ya bani iko”

“Ameen, in har kika min hakan kin gama min komai. NAGODE”

murmushi tayi har sai dai dimples inta ya lotsa.

wannan kenan!

Cike da sha’awa ya Kallon ta har sai da ta Kai karshen Aya.

“Ma Sha Allah Suhaima, you are very brilliant, Allah ya Kara basira, ya sa ki amfana da karatun gabadaya, Ina fatan Zaki yi aiki da abinda muka karanta Kuma kema ki koya ma wani domin ko Manzon Allah SAW Yana ce ‘khairukun man ta’allamal Qur’ana wa’alamahu’ mafificin ku shine Wanda ya San Al-qur’ani Kuma ya sanar dashi”

Unknown to him hawaye kaman famfo ke fitowa daga idon ta sai dai sunkuyar da kanta kasa da tayi Bai bashi daman gane hakan ba. Ba shakka ta taba irin wannan a baya da mutumin da ta ke wa Kallon shakikinta unknown to her shi ne zaman su na karshe.

“Kaman yanda na fada Miki” Dr Fahad ya katse Mata tunanin “Gobe za a sallame ki, Ina Mai baki Shawaran yarda da kaddara a dukkan halin da Zaki tsinci kanki ki gode wa Allah sannan Kuma ki rike addini kar kiyi Wasa dashi” shiru yayi Jin sheshekan kukan ta.

“My God! Don’t tell me you are crying Suhaima”

“Sorry Dr, kana nufin shikenan kenan”

“What? No No no, akwai zumunci Mai karfi tsakanin mu, I will always check on you”

“Are you sure”

“I mean it, I will be leaving for Abuja now”

“Allah ya kiyaye hanya, Thank you for everything Dr, I really appreciate …”

“Shhhh Kar ki fara fa na fada Miki ke kanwata ce ko” murmushi tayi kawai kafin ta sa hanky ta goge sauran kwallan da ya rage a fuskan ta.

“Toh ko kefa, gwara ma ki daina kukan nan Dan ba kyau ya ke Miki ba and I hate it when my sister looks ugly” dariya tayi sosai wannan karon kafin ya Mata sallama ya wuce kamar ba zai bar dakin ba, he knows that dole haduwan su zai ragu da ga rana irin wannan and he will surely miss her, sabo turken Wawa.

A kofan dakin nata ya ci karo da Faroukh da alamun ya Dade a kofan dakin. Hannu ya Mika mishi “You have been here”

“Ehmm nazo Naga Kuna magana so shiyasa na baka space”

“Oh Thank you” ya fada yana wuce wa. Saurin kamo hannuwan shi Faroukh ya yi “Zan so in baka shawara”

“Shawara Kuma?”

“Ehmm, Dr how can you let a stranger have that effect on you, she is just a patient and someone you hardly knows for God sake its better if you stay away. Am warning you”

“Ehmm really? So waye Kai da za ka bani wannan Shawaran Young man? Ka koyi fita daga abinda ba ruwan ka” Bai tsaya Jin Mai zai fada ba yayi tafiyan shi. Murmushi Faroukh yayi kawai hade da girgiza Kai “it seems like they will never understand what he is trying to warn them”

Da karfi ya tura kofan dakin nata, tana zaune a kasa still tana karanta wani littatafai da Mustapha ya kawo Mata domin ta dinga rage kewa. “Sannu da zuwa” ta ce mishi. Tsaki ya ja mai karfi “munafukar Allah ta’ala, nazo ne in Miki gargadi, na ji cewa gobe za a sallame ki so ina mai baki Shawaran tattarawa ki koma inda Kika fito Kar ki sake ki ce zaki zauna cikin family inmu,  in ba haka ba ki kiyaye abinda zai biyo baya. Saboda ni dai kinsan bazan taba yarda da ke kaman yanda sauran su ka amince miki ba.” Kala ba ta ce mishi ba har ya gama fadin abinda ke ranshi ya bar dakin. Wani kuka mai karfi ta rushe dashi.

Wata Sabuwa inji Yan caca…

A bakin wani hadadden gida da aka mishi ado da flowers tunda ga waje ta ga Barr Mustapha ya tsaya da motan kafin ya danna hon. Nan da nan mai gadin gidan ya bude yana mishi sannu da zuwa, Sai da ya tsaya su ka gaisa sannan ya karasa cikin gidan yayi parking.
+
Anisa ce ta taimaka ma Suhaiman su karasa cikin gidan. Da gudu Maryam ta fito daga cikin dakin ta Jin muryar su “Welcome home Suhaima” ta fada tana murmushi, Suhaiman ma murmushin ta Mata “thank you” ta furta a hankali. “Sannun ku Anee”
“Yauwa Anty Maryam ni dai yunwa na ke ji”
“Ai Kya bari kiyi Sallah Koh?”
“Nayi a asibiti” ta amsa tana nufan hanyar kitchen.
“Uncle Musty sannu da zuwa” Maryam ta fada cike da tsokana. Harara ya bita dashi “rike kayan ki banso sai yanzu ki ka ganni?”
“Am sorrrrrrrrrry!” sai da ta daidaici saitin kunnen shi sannan tayi maganan da karfi saurin rufe kunnen yayi yana mata nuni da Suhaima da ke Falon. Anisa ta kwala wa Kira ta umurce ta da ta Kai Suhaima dakin da suka shirya mata.
“Ina Haidar” ya bukata
“Sun fita da Hadiza” girgiza Kai kawai yayi “me aka dafa?”
“Ban son Mai hadiza ta dafa ba but let me check”
“Oh ni Mimi ke dai you will never change”
Shagwabe fuska tayi, yasan yanzu zata fara complain da sauri ya katse ta “kawo Mana abincin please Kinga muna tare da patient”
Nodding Kan ta tayi sannan ta tafi kitchen ta iske Anisa na ta zubawa Suhaima za ta Kai Mata.
Kwana Anisa uku a gidan ta koma gidan su saboda zata fara zuwa computer school Aiko ta bar Suhaima da kewa don ita ke Taya ta Hira da abubuwa da dama.
Satin ta daya a da kwana uku a gidan Mai aikin Maryam, Hadiza ta sanar da ita tana da bako a waje. Ba kowa a gidan sai hadizan da Haidar. Barr na wurin aiki Maryam Kuma ta tafi islamiyya. Hijabi dogo ta sa har ta fita tsakar gidan. A Kan bench in kusa da dakin Mai gadin ta hango shi zaune Yana wasa da key in motan shi. Jikin shi ne ya bashi ana Kallon ya dago Aiko four eyes su kayi da ita tana tsaye da crunches a hannu ta.
Tasowa yayi ya karaso har inda take ya ja fararan kujeran da ya gani a wurin ya zauna bakin wani bishiyan da ke ta buso iska. “Bismillah” ya nuna Mata dayan kujeran da ke kusa da ita. Kaman wacce aka dasa haka ta yi ta bin shi da kallo, sai yau ta ke Kara ganin kamanin su da sanda sosai har yanda su ke abubuwa ma Kama yake. “Ki zauna Mana na fanshe ki kice bakuwar bani ba” Zama ta yi akan kujeran still tana Kallon shi “Shine sai yau za ka neme ni” ta fada kasa kasa.
Murmushin Nan nashi yayi Mata har dimples in shi su ka bayyana “am sorry Suhaima na Kara komawa Abuja ne gashi ke baki da waya bare in Kira ki”
“Ya shirye shiryen biki?”
“Lafiya kalau, nace wa Rufaida Zan zo duba biki tace tana Miko gaisuwa”
“Amarya Ina amsawa sosai, ka gaishe ta”
“Kinga tunda da hijab Kika fito mu tafi kawai, we are going out”
Zaro ido tayi tana Kallon shi shiko sai murmushi ya ke Mata.
“Muje Mana da wani Abu ne?”
“Dr Ina zamu je? Kuma ma ai ban fada wa masu gidan ba”
“Munyi magana da Mustapha”
“Toh Ina za mu je”
“Zaki gani kedai”
Bin shi tayi, ba ta gane inda suke ba sai da tagan su a bakin garkuwa hospital, “sorry I have to check on a patient ki bani minti goma”
“Asibiti nawa kake aiki Dr?”.
“Many, Zo ki rakani ma” ba musu ta biyo shi. A haraban asibitin su ka hadu da wata Nurse. Ganin Dr Fahad ya gaishe ta ya sa Suhaima tsayawa ita ma ta gaishe tan “Ah doctor Amarya ka kawo Mana ne?” Da fara’a tayi maganan.
“No Dr kanwata ce wannan”
“Oh Allah sarki! Sannu beautiful lady” ita dai smiling kawai ta Mata kafin su ka karasa cikin ward in da zai duba patient in.
Wani Elderly man ne akan gadon, ko da Dr Fahad ya gaishe shi Nodding kawai yayi. A hankali Nurse in da ke tare ya radawa Dr Fahad. “he is not hearing clearly but he pretends to be well” murmushi Dr yayi.
“Baba me ke damun ka right now?”
“naci abinci Mana Dan Nan” da mamaki Suhaima ta bi tsohon da kallo.
“Da kyau, am ina ke maka ciwo yanzu”
“Na ci na ci abinci Mana ba Zan muku karya ba ai ko, Tun dazu abinda kuke tambayan mutum kenan” cike da baccin rai ya karasa zancen. Dafe Kai Dr Fahad ya yi, he have no idea ya zai bullo mishi.
“Where is his guardian” ya tambayi nurse in.
“Sir shi ya kawo shi Amma he left since, he complained about the same thing, shi ma ya fada min Bai Jin sosai, Yana ta tambayan shi Amma Bai fada mishi me ke damun shi”
“So why do you call me? I thought case in field Ina ne”
“No sir, all the doctors here are in the Theater room, Kuma Kai kadai ne Zan kira ka Zo that’s why, pardon me sir”
“I have an idea” Suhaima tare da mikawa Dr Fahad hannu.
“Me za kiyi”
“Watch and see, pass me the stethoscope”
“Young lady you are not a doctor”
“I know Kai Dai ka bani” Mika Mata yayi ya tsaya Yana Kallon ikon Allah.
Ear tubes in ta sa mishi a kunne, Sannan ta dago chest piece wurin bakin ta. “Baba ka na jina” kallo tsohon ya bita dashi har da murmushin gamsuwa “sosai ma kuwa”
“Ko za ka iya fada min me ke damun ka?”
“Haba ko kufa da Kun ishe ni akan abinci” murmushi tayi kawai ta mikawa Dr Fahad su ka cika gaba da magana. shi Kan mamaki ma ya Hana shi magana har sai da su ya gama duba patient in tukunna su ka bar asibitin.
“Am so suprised like a wani wuri Kika samo wannan idea in”
“Don’t you know I was a medical student you never asked”
” Seriously? I can believe this. Amma kin gama karatun?”
“Nagama, Housemanship ne dai banyi ba”
“Am now more interested in knowing who really are you”
“Suhaima Adam Bello, a lady with full of mysteries. I have a long story by the way”
“I will love to hear…” Ringing in wayan shi ne ya katse maganan tasu, ganin Wanda ke Kiran ya sa shi dole ya dauka. Ummin shi ce sun Dade suna magana ta fulatanci, gabadaya ran shi ya baci kaman zai sa ihu su ka Isa haliems.
Kala Bai iya furta ba bayan ya gama wayan sai ko abubuwan da ya musu ordering.
“Sorry Fa, actually cinema na kawo ki kiyi kallo, you must be bored indoors always”
Nodding Kan ta tayi in affirmative “surely, nagode sosai but let’s go back, you are not in a good mood” ba ta jira me sai ce ba tayi saurin Mikewa. Bai San sanda ya rike hannun ta ba, laushin Mai hade da shock in da yaji ne yasa yayi realizing abinda yayi “am sorry please Amma ki zauna” saurin zaman tayi tana Kallon shi.
A hankali ya fara Magana though jikin shi har rawa ya ke. Ruwa Suhaima ta Mika mishi ya Sha kafin ya cigaba.
“Ban San meyesa nake sharing personal life Ina da ke but whenever I do I felt comfortable” Dan Jim yayi kafin ya cigaba Ina son in fasa auren Rufaida Amma I can’t saboda parents inta ga Kuma Ummi na on the other side. I need an advice from a lady this time other than Ummi and Dada, I got attached Suhaima I think I’ve start to like you. Ki bani shawara even though ban sanki ba ban San kowa naki ba still zuciya ta ta aminta da addini da kyawawan halayen ki, Am sorry if I may sound offended but I think i have a strong feelings for you”
Turus tayi tana Kallon shi cike da mamaki, seriously she never expect this from him. How can’t he even love her? Ba shakka halayen ta ke rudar shi da Kuma situation in da ya ke ciki. Dr Fahad a yanzu ko shakka bbu wani jigo ne a rayuwarta sai dai Kuma ba ta wannan fannin ba domin kuwa zuciya ta a rufe take da ko wani irin soyayya na Dan Adam illa mutum dayan da ta ke da tabbacin ba zai taba iya fita a cikin ta domin an halicce sa ne domin shi.
Shirun da tayi ne ya bashi daman cigaba da maganan shi ko ince labarin Rayuwar shi.
Mahaifin Rufaida wan Mahaifi nane uwa Daya uba daya. Mahaifin nata da muke Kira Baffah yayi aure Mahaifiyar ta wato Dada shekaran su Biyar da aure Amma Allah Bai azurta su da haihuwa ba. Dada bafulatanar Gombe ce, mace ce Mai mutunci, kirki, hankali da sanin yakama ta, kyawawan halayen ta shi ya jawo Mata soyayya a cikin dangin mahaifan maza kowa alfahari ya ke da ita. A shekaran da su ka cika biyar da auren Abba wato mahaifina ya auro Ummi. zuwan shi Yobe service ya hadu da ita. Ummi na mace ce Mai zafi ga Kuma zuciya irin ta bafulatanin mutum. Still tana da kirki Amma sai dai ba ta Kama kafan Dada.
Zaman lfy ne tsakanin su da Dadan da dukkan dangin Abba na. Bayan shekara daya ta samu ciki na. Tun Ina ciki Abba ya yanke Shawaran bawa Dada da Baffah ni ba Dan komai ba sai dan irin tausayin Dan uwanshi da yake, mutum ne Mai matukar son haihuwa Amma Allah bai bashi ba. Duk Yana wannan Shawaran ne ba tare da ya sanar da Ummi ba sai bayan an haife ni ya sanar Mata, Nan ta ke Ummi ta ki amincewa, Tace ba yanda za ayi a rabata da Dan ta na fari domin ko Ummi ko kunyan Dan fari da fulani ke ji ita ba tayi. Ba ta yadda cewa Abba dagaske ya ke ba sai bayan an dawo Dani daga Yobe, can ta Kai ni yaye wurin mamanta har sai da nayi shekara uku aka maido ni. Wata na daya a gunta Abbah ya Kara tuna Mata kudirinsa. Fir Ummi ta nuna ba ta San zancen ba don haka Abba ya share sai bayan kwanaki ta fita Unguwa ya hada kayana gabadaya da ni ya kaini gidan Baffah inda ya sanar mishi kudirinsa. Dan farinciki Baffah har kukan murna yayi haka ma Dada har sujada tayi ta gode ma Allah, yanda ta rungume ni ko kaman za a kwace ni daga gun ta.
Abbah ko kwata kwata ba su wanye ta lfy da Ummi ba har ya kai da Rantsuwa ta yi sai ta je ta dauko ni, cikin fushi Abbah ya ce Mata matukar ta je gidan wan shi da niyar dauko ni shi Kuma a bakin auren ta. Rigima su ka you sosai Amma Bai hana Washegari Ummi ta je gun Dada dauko ni ba. Ba irin kwantar Mata da hankali da Dada ba ta yi ba Amma Sam Ummi ta ki ji, Dada na kuka ta dauke ni ta Bata saboda Ummi ba rashin kunya ta Mata kawai dai ta bukaci a Bata nine Mu koma gida.
Hakan yayi sanadiyar Rabuwan auren su. Dani Ummi ta tafi kolere Amma fir iyayen ta suka ki su ka maido ni wurin mahaifina Wanda ya maida ni gun Dada. Tun daganan Ummi ta fara kin Dadan sanadiyar raba ta da Danta da Kuma auren da ta ke matukar so. Abbah ya Sha so ya maida ta Amma fir taki amincewa a cewarta sai dai in ya yarda zai maido ni hannun ta.
Ba karamin gata na samu gun Dada ba, ba irin kaunar da Bata nuna min ba fiye ma da Ya’ya’n da ta Haifa. Ina Five years ta haifi Aliyu bayan shekara biyu ta Kara haifan Sadiq tun daga Nan Kuma sai bayan wani five years in ta haifi Rufaida. Allah yayi ni da son kanwa mace saboda haka tunda na kyalle ido Naga Rufaida a gida mu na ke matukar kaunar ta, tare ma mu ke rainon ta da Dada” dan dakata wa yayi yana murmushi da alamun ya tuno Lokacin ne sannan ya cigaba. “Kusan Nina raini Rufaida don kullum tana wuri na. Ko da ta fara magana da suna na ta fara bude baki. Ya fad, Nina sa Mata Faidah saboda a cewata yafi kama da suna na. Ko bayan da aka haifi kannen ta Mata still na fi shakuwa da ita duk abinda na samu to tabbas rabi da kwata na Rufaida ne. Gabadaya yaran gidanmu tsoro na suke ji saboda bana musu wasa har ko su Aliyu da Sadiq Amma Banda Rufaida don in har suna son abu guna ma ita su ke aikowa.”
“Ta San cewa ba iyayen ta bane su ka haife ni saboda yawancin hutu Ina zuwa hutu kolere har bayan Ummi ta yi aure a Abuja ban daina zuwa ba daga Yoben har Abujan. Ina tausayin Ummi na saboda irin son da ta ke min fiye da duk wani da da ta haifa a duniya. Musamman ta ke zuwa Taraba ganina Amma ba ta zuwa gidan Dada sai ta je gun Goggo Fatume kanwar Su Baffah ita Kee zuwa ta dauko Mata ni har sai ta tafi a maida ni. Tun Ina karami Dada ta sanar dani ita ce Mahaifiya ta hakan ya sa Nima na taso da soyayyar ta a raina. Ba abun duniya da Ummi na ba ta min har bayan mun dawo Kaduna a sanadiyar transfer inda akawa Baffah, Abbah ko daman ya Dade Yana aiki a Abuja.
Ina final year a secondary school Iyayena su ka dawo da auren su bayan Allah yayi ma mijin Ummin rasuwa. Ya’ya’n su biyu duka Mata, Shaheeda da Zahra sai Kuma bayan ta koma gidan Abbah ta haifi Fu’ad, Mukhtar da Rukayya. Akwai Matan Abban da mu ke Kira da Mami ita Kuma Ya’ya’n ta uku. Sulaiman, Abdallah da auta Mamah.
Ko bayan Nan Ummi ta nemi in koma Abbah ya ki zancen ba dan ta so ba ta hakura.
Alaka ta da Rufaida ko sai abinda yayi gaba, shakuwar mu ko har ta wuce misali kowa kwatancen mu yake. Ban son Lokacin da na fara son ta ba” da sauri ta dago ta kalle shi, daga Mata Kai kawai yayi sannan ya cigaba “Tun Ina karami ake tsokana ta ko Yar gida za ayi ne? Sai dai kawai inyi murmushi. Tun ana fada Ina murmushin har ban son Lokacin da na fara Jin maganan nasu na Zama a kwakwalwa ta ba, har ya ke da na sawa Raina ba ni da wata Mata a duniya inba Rufaida ba. A bangaren ta ko a nawa shirmen gani nake banda matsala domin nasan ba za ta ki ni ba. Aliyu kadai yasan da wannan sirrin nawa domin duk wata shawara wurin shi na ke nema duk da na girme mishi Amma shi mutum ne Mai matukar hankali da sanin Yakama ta just like Dada, sosai ya dauko ta ta wannan fannin.
A India nayi karatun likitan, gabadaya Baffah yayi sponsoring karatuna da komai da komai. Tsakani na da Daddy ko sai dai kyautatawa Amma komai nawa Baffah ya tsare min. Bayan tafiya ta Rufaida har ciwo ta yi, ba ta wa kowa magana sai da Dada ta Kira ni na dinga lallashin ta kuwa. Still kullum sai na Kira Dada da murnar ta za ta amshi wayan mu yi ta hira da ita, musamman saboda ita na ke dawowa hutu duk shekara haka kuma tsaraban ta sai yafi na kowa yawa.
Bayan Naga karatuna sai da na tsaya one year nayi wani course kafin na dawo Nigeria Housemanship. A ABUTH shika nayi. Duka duka ban cika 1 month da farawa ba Ummi na ta fara min maganar aure, Kai tsaye nace Mata Kar ta damu kwanan zan je Abujan mu yi maganan. Ni fa duk ana wa zaton Zan jira Rufaida ne ta gama secondary School muyi aure, Lokacin ta na SS3 ma ne.
Tana gama secondary da kaina na siya waya Mai kyau na bata as gift. Ba karamin farin cikin samun wayan tayi ba Saboda Baffah Bai taba barin ta ta rike waya ba. Ba dadewa ba ta samu admission a ABU Zaria su ka bata Nursing, Ni na Mata registration da komai da komai hakanan Lokacin na kusan gama Housemanship Ina Saboda haka na yanke Shawaran yi residence ina a Nan ABUTH.
A Lokacin Ummi ta fara matsa min da batun aure abun Kuma kaman hadin baki Baffah, Dada da Abbah duk su ka fara min maganar duk da dai shi Abbah hanya hanya kawai ya ke min Bai fito fili ya fada ba.
Ba Wanda ya San abinda ke zuciya ta a Lokacin sai Aliyu yayanta saboda haka Kai tsaye na tunkare shi da zancen ganin Rufaidan har ta fara University.
“Haba Ya Fad ai Nasha ka fasa ne” ya fada cike da tsokana, harara na bishi dashi ba shiri ya natsu.
“Afuwan Yaya Fahad Amma ni ai da Naga har ka Bari ta fara makaranta ba Ka yi zancen ba na dauka ka canja ra’ayi ne. Gsky gwara ka tunkare ta tunda wuri kafin wani ya hure Mata kunne ta ki sauraran ka” wani irin tsoro naji saboda maganganun Shi, a Lokacin na nufi zaria. Tun akan hanya na sanar da ita Ina nazo za muyi magana da ita, ita ma ko cike da murna ta ke fada min akwai labarin da zata bani. Nan ta ke naji gaba na ya fadi…
Da la’asar na isa Zaria, Kai tsaye na wuce samaru. Sai da na tsaya nayi Sallan la’asar kafin na nemi Rufaida. A mota na dauke ta Mika wuce wurin Dam in da ke cikin ABU in, Dama tun can ni Allah yayi da so wuraren shuke shuke, they always gives me comfort. Sai da muka gaisa sannan na taso Mata da zancen da nace Mata zamuyi. “Oh! Ya fad am dying to tell you this” da mamaki na bita da kallo, Kar de itama tana Jin abinda na ke ji but she gave the suprise of my life “Ya fad na yi saurayi har yace Yana so ya je samu Baffah” hmm! Ji nayi gabadaya numfashi na ya dauke for some seconds kafin ya dawo, har na fara hada gumi Lokaci da ya annurin fuskana ya dauke. “Are you not happy? Am getting married fa”
“Faidah am not” Kai tsaye na fada mata “am disappointed rather”
“Ya fad ba Ka son inyi aure ne?” Kaman za ta yi kuka ta ke magana “Ya fad Yana Sona fa and he even promised to take good care of me, I mean he is very nice and I love him too” Ya Isa! Na yi saurin dakatar. “Haba Faidah, are you telling me baki taba sanin Ina son ki ba? I thought its even a mutual feeling” fara’ar fuskan ta gabadaya daukewa yayi tana dubana da mamaki “Kana so na fa kece? Haba ya Fahad you are my brother”
“And? Ai kinsan ba haram bane right?”
“But ya Fahad I can’t marry you, Kallon yayana ya ke maka who is always there for his little sister and nothing more.” To say i was dumbstruck is an underestimate wlh. “Meaning?” I asked her.
“I love someone else and we are even talking of taking our relationship forward” kasa cewa komai nayi for I can’t still believe I was rejected on the first trial, Rufaida rejected me.
Miyan baki na gabadaya kafewa yayi, a hankali nayi yunkuran jawo ruwan da ke kusa Dani nayi gulping. And can you believe that Rufaida kuka ta ke, I feel like slapping her don ji nake dama ni na samu nayi wannan kukan nata da nagode. Kala ban kara ce Mata ba har tayi kukan ta ta gama sannan na Mike nace Mata ta tashi mu tafi. Har na sauke ta a hostel ba maganan da ya shiga tsakanin mu sannan na koma hotel in da na sauka. Da da dare ta turo sms Wai tana bani hakuri claiming that she is taken. Wlh ban taba tunanin Faidah za ta min haka ba. Abinda yayi shattering kyakyawan alakan mu da ita kenan. Da safe na koma Kaduna, Aliyu ya fahimci halin da na ke ciki don Haka na warware mishi halin da ake ciki. He insists on talking but still yarinyar Nan ta bijire. Har ta gama University Saurayin nata Bai turo ba, kullum sai an dauko magana sai ya rushe tunda ga Nan na gane yaudaran ta ya ke you but I can’t tell her saboda gabadaya ma maganan arziki daina shiga tsakanin mu yayi sai ko in ya Kama, Kai gaisuwa ma sai ta ga dama ta ke min saboda gabadaya harkar ta na fita na daina sakan Mata fuska, I was so disappointed in her. I can’t still get to tell her he is getting married in two weeks time. Recently, Dada ta samu labari which I believe Aliyu ne ya fada Mata, ita ta gaya wa Baffah and they arranged the marriage. Ina so ince musu na hakura but Baffah ya rantse sai anyi sai dai ko mu mutu, that’s why I give in but I still don’t think ina son Rufaida kaman da even though we agreed on making it work.
So Suhaima this is my story. can I hear yours?. Kiran Sallan magreeb ya ji. Murmushi su ka saki a tare “I guess it will be for another day then, mu je in ajiye ki gida ko, are you even comfortable living with them” nodding kanta tayi “okay remember am just a call away and thats remind, I bought you a phone, I will send it tomorrow”
“You shouldn’t have done that”
“Shhhh” ya fada making her chuckled “remember you are my sister” and he never talks about the confession he makes earlier on….Karfe Tara da rabi dai dai Suhaima ta gama duk wani abinda za tayi a dakin, ta share shi tayi mopping, ta wanke bayi, sai da ko Mai yayi tsaf sannan ta kunna burner ta fito falo.+
A falo ta samu matar gidan da Kayan bacci a jikin ta tana zaune tana Kallo, Haidar ko na bacci akan kujeran da ta ke zaune “Ina kwana Maman Haidar”
“Lafiya kalau Suhaima an tashi lafiya? Ya kafan?”
“Alhamdulillah”
“Gashi kin tashi ko breakfast ba a dora ba, akwai ruwan zafi a flask ko Zaki Sha kafin Baban Haidar ya fita ya siyo mana breakfast”
“Ah bara na yi mana, ba akwai kayan abincin ba”
“Eh akwai kinsan Hadiza ba ta Nan so sai a slow”
“Ba matsala bara na yi in” Suhaima ta fada tana nufan hanyan kitchen, can kasan zuciyan ta ko tana mamakin hali irin na Maryam, gabadaya ta gama fahimtan ta a sati biyun da suka zauna tare. Kiwuya gare ta na bala’i ba ta iya komai na gidan in ba yi Mata za ayi ba to Bata damu ya zauna hakan ba.
Da tunanin hali irin na Maryam ta shiga kitchen in Wanda shima din kacha kacha ya ke kaman zai yi ihu. Saurin girgiza kanta tayi, a fili ko ta furta “No” ma’ajiyan tsintsiya ta nufa ta share kitchen ta tattare shi ta yi wanke wanke sannan ta goge ko Ina. In 20 minutes kitchen ya dawo hayyacin shi ita ma Kuma sai a Nan tayi feeling satisfied ta fara Shirin girkin.
Golden yam da sauce ta musu sannan ta daura ruwan shayi da ya Sha kayan kamshi kaman yanda ta ga anayi kullum a ajiye a dinning, may be maigidan ke sha. Nan ta gama ta je tayi setting dinning in, dai dai fitowan Mustapha daga bedroom yana daura cuplinks, cike da girmama wa Suhaima ta dan durkusa sannan ta gaishe shi. “Ah Malama Suhaima yau ke ki Mana girki kenan” murmushi kawai tayi ba tare da ta amsa ba. “Ai ko kin kyauta Kinga I don’t have to waste my time and money” ita dai ba tace komai ba sai daukan nata share in da tayi ta nufi dakin ta. “Ah Suhaima ya za ki shiga ciki” Maryam tayi maganan tana Kallon ta.
  “No bar ta Kila za tafi sakewa a can in ne” Mustapha ya fada Yana zuba ruwan shayin a cup inshi.
Tun da ya Kai abincin bakin shi ya ke ta yabon girkin. Tun Maryam na mishi dariyan Santi har ta hade Rai ko yayi magana ba ta tankawa, lura da hakan yayi ya sa yayi magana “mimi dear ya dai, wa ya taba min ke?” Banza tayi dashi ganin haka yasa yayi saurin ajiye cup in shayin da ke hannun shi ya tattara hankalin shi gabadaya ya maida kanta, Sa’a Daya da Maryam ta ci a rayuwar ta kenan, soyayyar da Mustapha ya ke Mata kaman zai lashe ta ko kadan bai son yaga baccin ranta.
“Kinga Dan Allah fada min Mana ko ni na bata Miki rai”
Ganin yanda ya marairaice ya sa ta dan saki fuskan ta “Ji fa yanda kake ta yabon girkin ta as if ba Ka taba cin abincin da ya Kai shi ba”
“No ba Haka bane Mimi na, na kwana biyu ban ci abincin da yayi dadi like wannan bane kinsan ba wai Ina son abincin restaurant bane and Mai aikin am not enjoying her food but you insist a bar ta”
“Whatever am very sure Zan iya Wanda ya fi wannan ma”
“Ba kiyi karya ba mimi, you are a very good cook but ba ki son you so i have to manage since i love my queen” murmushi farinciki ne yayi appearing a fuskan ta har ta manta wa abinda ta ke wa fushi.
Roudah watch da ke hannun shi ya dubo “I’ve to go mimi, shari’an mu will Soon starts”
“Okay dear Allah ya bada Sa’a”
“Ameen, wait ba za ki rakani” ya fada Yana Kallon idon ta yanda tayi kicikicin da fuska kaman za ta yi kuka. Da kyar ta daure ta Mike ta bi bayan shi har gun motan.
Sai da ya shiga motan ta Mika mishi briefcase inshi da ta amsa. Murmushi Mai kayatarwa ya sakan Mata kafin ya tada motan. Waving ya Mata kafin ya ja motan ya fita ya bar Mimi na blushing.
Da ga Window dakin Suhaima ta  ke Kallon su, wani irin sha’awa su ka bata, she didn’t missed  affectionate looks in da Mustapha ya ke bin Maryam dashi, it’s so obvious how he loves and care for his wife. Wani irin hawaye Mai hade da murmushi ya saukowa Suhaima. She can’t believe smiling and crying at the same time reminiscing her passed moment, she wonders how he is doing now, the love of her life, the man behind her mystery. Saurin goge hawayen ta tayi kafin ta yi answering call in Dr Fahad da ya shigo phone in da ya Bata.
Just like everyday tambayan ta yayi ya ta ke? Hope ba abinda ke damun ta da Kuma zaman shirun da take. Murmushi ta yi kawai ta amsa da she is enjoying every bit of her life now and she meant it. She has always been lonely… Tambayan shi tayi Amarya and gladly they are really trying to makes it work as they plan, sai da ya tuna Mata da ranar da za a fara events in bikin nashi kafin su kayi sallama.
Musamman Dr Fahad yasa kanwar shi Shahida ta siyo Kaya ya sa aka Dinka ma Suhaima. Duk a zaton ta Karin kayan Amarya ne shiyasa ba ta ce komai ba. Ummi dai ta yi shirun tana ganin ikon Allah don ko an Fi karfin ta ta ko Ina, sai dai ta dau aniyar Hana Rufaida Jin dadin zaman aure da danta. Su Shaheeda da Zahra sun Sha fahimtar da ita Amma Ina Ummi ta you nisa a kiyayyar Dada da Ya’ya’n ta.
Maryam da Yan uwanta ma ba baya sun yi Suhaima abubuwan alkhairi iri iri har rasa bakin gode musu ta ke. Kaya Kam wata Yar gatan da take wurin iyayen ta ba sa nuna Mata ba.
Yanzu Kam Suhaima kusan ita ke komai na gidan Hadiza ta fi rainon haydar shi ma ta Kan rike shi. Maryam ta so Hana ta Amma Sam ta ki ta nuna Mata bakomai. Ita Kam na ta jam Gidan ta kullum tsatsaf ba ta da matsala dama wurin gyaran jiki ba ta da matsala, tsaf za ka ganta kullum tana kamshi sai da ba ta iya Zama ta gyara muhallinta Kam Amma danta ma tsaf yake. Kusan kullum ko sai ta samu inda zata ba su hada hanya da yawan zaman gida, da kullum tana wurin Anty. Tsawata Mata da Anty ta ke Mata ne akan hakan yasa ta daina yawan zuwa gidan gabadaya, don ko ita mace ce da ta tsani fada ko Kuma a Sata Abu. Aa abinda ta ga dama shi ta ke yi ba Mai Hana ta shiyasa ma Antyn ta zuba Mata ido said ya Kama za kaji tana mata fada shima ko Mustapha Bai son laifin matar shi.
Hadiza Mai aikin su irin yan matan Nan ne na kauye masu fama da rawan Kai. Shiyasa Maryam na fita ita ma za ta Sabi hijab ta Sabi haydar sai makota.
Yau ma hakan ne ya kasance Maryam na fita ita ma ta dauki hijab za ta fita. Dakatar da ita Suhaima ta yi “Ina Kuma Zaki Hadiza da Yaron da yamma Nan ana sanyi”
“Makota Zan leka Kuma tunda Mahaifiyar shi ba ta damu dashi ba ta ke fita ta bar shi Nima dole na fita dashi” girgiza Kai kawai Suhaima tayi, ko kadan ta San hadizan ba ta iya magana ba “kawo shi to sai ki tafi” ba musu ta Mika Mata shi, Daman abinda ta ke so kenan ta yi waje da wuri.
  Har  ta gama abincin dare haydar na zaune abin shi Yana wasan shi, yaro ne Mai hakuri har tausayi ya ke Bata. Sai da tayi Sallan magreeb ya fara gyangyadi kawai ta goya shi. Wani English novel da ta gani a Falon Mai suna may be someday na Colleen Hoover da ta gani a book shelf in da ke falon ta dauka tana karan ta wa ita daman ta fi preparing karanta novels akan Kallon film.
Har ta gama chapter one ta ji takun mutum a Falon. Maigidan ne ya shigo “sannu da zuwa” ta fadi kanta a kasa. “Yauwa karatu kike Ina ta sallama baki ji ba” shiru tayi tana mamaki ya akayi ba ta ji ba “Mimi fa?” Ya katse Mata tunanin nata. “Ta fita” ta bashi amsa, “har yanzu ba ta dawo ba” ya tambaya kanshi hade da girgiza Kai. Sai a sannan Hadiza ta shigo ta na Yan noke noke sanin ya Hana ta yawo. Ko Kallon ta Bai yi ba ya nufi daki, he never like the girl, ta cika surutu ga rawan Kan tsiya, shirmen abincin ta kuwa bai da case tunda Suhaima ta fara girki.
Sai da ya fita Sallan isha’i ya dawo sannan ya nufi dinning ya fara cin abinci. meanwhile Suhaima da Hadiza na small parlour in da ke farko and they can all see him ta transparent glass in da ya raba tsakanin parlours in. He is completely enjoying the food sai dai during the process Yana ta trying numban Amma ya ki shiga, tsaki ya ja mai karfi kafin ya tashi ya dauko car key in shi.
Haydar zai fita ya sa ihu Yana Mika mishi hannu, cike da tausayin Yaron ya karasa gare shi. “Sorry son ba dadewa Zan yi ba kaji” sai ka rantse da Allah Yaron naji abinda ke fada sai dai Yana matsawa zai wuce haydar ya saki wani Kara da ya gigita su gabadaya, an tabo mai hakuri. Still dai kuka ya ke yi. Juyowa Barr yayi Yana Kallon Suhaima “gidan Anty zani ko za muje ki gaishe ta ba Zan Dade ba” shiru tayi tana tunanin ganin har yanzu haydar bai daina kukan ba ya sa tayi saurin daukan hijab in da ke kusa da ita ta amshi haydar a wurin Hadiza. “Ki kula da gidan saura Kuma ki fita” Barr ya fadawa hadiza kafin su ka nufi mota.
Sun yi two minutes da fita daga gidan Amma ba Wanda yayi magana a motan sai haydar da ke ta wasan shi. “Dan naki dai da alamu yawo ke so” ya fadi Yana Kallon kwanan da zai yi. Ita ko a zuciyan ta fadi ta ke Dan Maryam Kuma ai dole ya so yawo. Kaman daga sama ta ji ya na fadin “so you are a bookworm?” Nodding Kan ta tayi in affirmative looking interesting “wow! I love books too”
“They are interesting” ta fada ba ta so ta bar shi kadai Yana surutu.
“How many novels have you read so far?”
“Countless” ta bashi amsa.
“That’s great, hope kina enjoying wannan in”
“Sosai ma, na karanta may be now online time in ta riga ta cire may be someday so am happy to finds it finally”
“Haba no wonder, na yi mamakin me yasa out  of all the books Kika dauke shi. You have been wondering how ridge ya fara son Sydney har yayi breaking up da Maggie right?”
“Exactly, Naga storm and silence ai. I will love to read that book again its awesome” she can’t believe ta sake tana lbr dashi but he is talking books, for crying out loud he can’t ignore him.
A haka su ka Isa gidan Anty. Cike da farin ciki su Anisa su ka tare su haydar sai washi baki ya ke yaga yan’uwan shi.  Anisa ko sai faman Jan Suhaima da hira ta ke, ita dai Allah ya hada jinin su tana matukar son Suhaima though ta San ta girme Mata, Ringing in wayan tane ya katse musu hiran nasu da su ke tayi. Da murna Anisa ta dauki wayan tana ihun “waw! Ya Faroukh i can’t believe ka Kira ni. Ya ya zayd ya ke? Hope he is fine?” Daram dam Suhaima ta ji gaban ta ya buga a sanadiyan jin sunayen mutanen da Anisa ta ambata. Ba ta ma ji Mai su ke cewa bayan Nan illa ta ji Anisan na fadin “sun ma sallame ta since yanzu ma su ka Zo da Uncle musty, ayt” ta ce kafin ta Mika wa Suhaima wayan.
She wants to reject but Anisa ta zuba mata pleading eyes, ba yanda ta iya haka Nan ta amsan jikin ta na rawa ta Kai kunnen. “Hello” ta fadi a hankali.
“Wato ba kiji warning in da na Miki ba ko?” Abinda ya fada ke ne ba tare da ya amsa ta ba.
“Suhaima is better ki fita daga rayuwar Yan uwana kafin na dawo na same ki, in ba Haka ba za kiyi Dana sani, wannan ne warning na karshe da Zan Miki and mind you I will be returning in 3 weeks” dif ya kashe wayan.
A tsorace ta juya ta Mika wa Anisa wayanta sai dai hankalin ta ma gabadaya bai wurin tana can suna musu da Yan uwanta. Tana Mika Mata wayan Uncle musty ya Kira ta don su wuce gida.
Tana zaune a falo ta daura kafa Daya Kan daya su ka yi sallama, fuskan Nan nata murtuk kaman ita aka yi wa laifi. Da kyar ta amsa Sallaman tana binsu da wani mugun kallo.
Haydar na ganin ta ya fara mutsu mutsun Yana so ya je wurin ta sai dai ko Kallon shi ba ta yi balle ta tanka. Suhaima ce ta fara magana “Maman haydar kin dawo?”
“Ehmm Ina kuka je ne?” She is calm kodan ba mijin ke Mata magana ba.
“Munje gidan Anty ne ta ce a gaishe ki”
“Emhmmm” kawai ta ce ta tashi ta tafi daki ko haydar in bata tsaya ta amsa sai Barr ne ya amshe shi ya wuce dashi.
Baiwar Allah Suhaima ji tayi gabadaya jikin ta yayi sanyi kodai maryam ta fara gajiya da zaman ta a gidan ne? Tambayan da ta ke ta wa kanta kenan but littafin da ke hannun ta ya taimaka wurin Kore Mata damuwa.
Washegari ko da ta tashi har ta shiga kitchen ta fara hada musu breakfast basu fito ba, Dan wake tayi tana cikin yanka cabbage Hadiza ta shigo kitchen in tana Hamma. Wani tsaki ta ja ganin Suhaima tsaye tana faman aiki “Ayi dai mu gani” ta fada tana nufan sink. Kala ba ta ce Mata ba domin ko Hadiza ba sa’ar yinta baccin instead juyawa tayi tace “an tashi lfy”
“Lfy garas ni ke” ta fada hade da rike kugu, ita kam dariya ma ta bata ganin yanda ta ke son tsiran fada da ita.
Ba ta Kara tanka ta ba kawai ta cigaba da abinda take ita Kuma ta fara wanke wanken ta tana ta sakin habaici cin Waka “Komin bakin cikin tanda sai na ci Wa’ina ahhayye ni dije hadizatu Yar gidan malam abdu, a ganni a kyale Ni”
Allah ya tsare mu da jahilci, shine abinda Suhaima ta fada cikin ranta daga baya ma istigfari ta fara yi a zuciyan ta. She is far more than responding to that village girl, ko bakin cikin Mai zata Mata oho.
Tana gamawa ta shirya warmers in a dinning table sannan ta nufi daki. After Forty minutes taji Barr na kwala Mata Kira don haka kawai ta Sabi dogon hijab inta ta fita. Suna zaune Kan dinning in suna magana da matar tashi, haydar ko bai riga da ya tashi ba. “Ina kwana”
“Lfy kalau” su ka amsa a tare both of them are smiling at her.
“Sorry Suhaima na taso ki ko” Barr ya fada his gaze directly on her face, shaking kanta tayi ba tare da tayi magana ba “Ehmm Dan Allah Zan Zo da friends Ina anjima, Zan samu dambu kin iya ko?” Yana dariya ya fadi maganan sai dai ita hankalin ta na Kan Maryam da smile in da ke fuskan ta ya fara fading.
“Na iya” ta amsa
“Irin fa mai gyada da zogalen Nan, they love traditional things”
“Zan yi” ta amsa in short realizing yanda Maryam ke faman zabga mishi harara. “So i can’t even know now if your friends are coming?” Bata jira amsan shi ba ta taci a zuciye ta wuce daki ba tare da ta Kara Kallon daya daga cikin su ba leaving them dumbstruck. Dariyan da Hadiza ta kwashe dashi ne ya dawo da hankalin su jikin su, Kallo Daya Barr ya juya ya Mata ta bar gun. Siririn tsaki ya ja hade da dafe kanshi. “Suhaima bara na tafi am getting late” briefcase inshi ya dauka ya nufi motan shi. Ita Kam Suhaima ta yi mamakin tafiyan da yayi ba tare da ya lallashi Maryam ba, it so unlike him ko kadan bai so ya ga abu ya taba ta but its like she enjoys giving him headache and it like he is getting feeds up with her attitude.
Ba ta dade da shiga daki ba Dr Fahad ya Kira ta akan ya tuna Mata shopping inda ya ce za ta raka shi,  ita kam har ranta ba ta son zuwan amma bata son yaga kaman ba ta son hulda dashi ne.Ana idar da Sallan Azahar Dr Fahad ya iso gidan, Sai da ta tabbatar da ta gama abincin da Barr ya sata ta hada musu da abin Sha sannan ta fita, ko da taje fadawa maryam, toh kawai ta amsa Mata ba tare da ko ta kalle ta ba. Jikin ta a sanyaye ta fita wurin Dr.
+
Gaisawa su kayi kawai ya ja motan su ka tafi. A wani katon super market taga sun tsaya “mu je ko ko ba Zaki tayani zabo kayan lefen bane?”
“Kai za ka hada?” She asked with a suprise expression plastered on her face.
“Mu je kedai kawai ya ce Mata ta ko bishi” siyayya su ka yi sosai na atamfofi, laces, bags, shoes, undies da cosmetics. Maimakon ta ga ya dau hanyar gida sai taga ya bi wani gun Kallon shi ta yi da mamaki yayi saurin ce Mata “shhhh” ai ko shirun ta yi.
Wani madaidai cin gida ta ga ya nufa Yana ta horn, Nan da Nan maigadi ya bude Mai Yana Mai sannu da zuwa. Shiru gidan kaman bakowa hakan yasa ta fara bin shi da Kallon tsoro. “Hey, i don’t bite” ya fada Yana dariya. Ba Wai Dan tayi trusting in shi completely ba ta bishi Aa ta dai tsaya ta ga gudun ruwan shi. Sai dai taga yayi sallama taji muryar mace ta amsa sannan hankalin ta ya dan kwanta.
“Ah Fahad har ka iso?” Wata Mata da ba zata wuce 35 ba ta fito tana maganan hade da wata yarinya a bayan ta. Gaishe ta Suhaima ta yi ta amsa faran faran haka ma Dr in.
“Anty ga Suhaima Nan na kawo ta gaishe ki Kinga ita ma ta Taya ni muka karasa siyayyan” murmushi tayi cike da kunya don ko wani iri ta ke ji in Fahad in ya Kira ta da Anty don ta San da kadan ta fishi.
Suhaima dai Kallon da ake ta bin ta dashi ya sa ta tsargu, four eyes su kayi da Zahra Nan da Nan ko kirjin ta ya bada kulululu “Sannu fa kin Sha jiki” Wacce su ka Kira da Antyn ta fadi sai a sannan Zahra ta Mata sannu sai dai da alamun ita ba ta gane ta ba kaman yanda Zahraun ta gane. “Ga sis ita Zahra da nake baki lbr” Dr Fahad ya fada ita ko Suhaima murmushin karfin hali kawai ta sakan Mata cike da mamakin yanda zahran ba ta gane ta ba Amma sai ta barwa zuciyan ta. Sun Dan taba hira sama sama kafin a Kira Zahra a waya tayi saurin dauka tana fadin “F sai yanzu za ka kirani? Nayi fushi” Nan ta ke Suhaima ta gane da Faroukh ta ke waya don ko haka ta ke Kiran shi. Ihun da ta sa ne ya dawo da Suhaima daga tunanin da ta tafi “are you in your senses Zahra?”
“Sorry ya fad, F ne fa yace min In 5 days zai yi Landing a Lagos, nayi missing in shi”
Tsaki Fahad ya ja “I wonder if this guy is even going to marry you kin tsaya kina hauka akan shi” turo baki tayi kaman za tayi kuka “Anty Kinga brother ko”
“Kyaleta Fahad Ikon Allah ne”
“Aa Anty in Sha Allah ma ni shi Zan aura” murmushi su kayi gabadayan su.
Sai bayan la’asar bayan Fahad ya dawo daga masallaci su ka bar gidan, haddadun bokhoor Anty ta bada, zahra Kuma ta Bata bracelet taso ta ki amsa but she insisted, Dr Fahad ko da ya sauke ta a gida wasu haddadun Arabian gowns ya Bata guda biyu da jewelries a cewan shi tukuicin Siyayyan da ta Taya shi ne, ba ta Musa ba ta amsa don ko ta ki ma fada za suyi daga karshe ya sata dole.
Ko da ta shiga gidan as usual Matan gidan ba ta Nan sai Hadiza da haydar, Yaron har murmushi ya dinga yi ya ganta ita ma ko da sauri ta dauki shi sannan ta bashi tsaraban Bobo in da ta siyo Mai, Nan da Nan ya hau Sha, Yaron har tausayi ya ke bata har ya sa da wuni da yunwa tun Yana karamin shi Yana Shan abubuwan da Nanon Mahaifiyar shi ba da gabadaya ba ta da time in Shi, daga yau tana islamiyya sai gobe kasuwa gata gidan kawa kullum dai da inda ta hara, don da har weekend ta ke hadawa ta tafi gidan Anty sai da Antyn ta hada su da Mustaphan ta musu ta tas tukunna su ka shiga hankalin su. Shi dai ba wai Yana so bane Amma ya tsani abinda zai Bata Mata Rai Yana mugun gudun fushin ta.
Sai bayan magreeb Barr ya shigo tana daki ya kwala Mata Kira don ko kadan bai son abinda zai hada shi da Hadiza, he hate the girl ba ta Mai ba. “Sannu da gida, kin dawo?” Nodding kanta tayi “Ya outing in, hope you enjoy it?”
“Ehmm” kawai ta ce Mai Nan da Nan ya hade Rai “Suhaima na lura har fa yanzu ba ki saki jiki da ni ba come on am your brother” murmushi kawai tayi sannan ta Mika haydar da ke ta kokarin zuwa wurin Baban shi. “Allah sarki my boy mum ta barka da yunwa ko?” Yaron dai sai kananun rigima ya ke don Yana ma da hakuri “Ni ko in tambaye ki, akwai wani abu tsakanin ki da Dr ne?” Kallon mamaki ta bishi dashi sannan ta yi murmushi hade da girgiza Kai “We are just good”
“Em em fa for the first time Naga murmushin ki Sosai daga Kiran Dr ki dai fada min gsky”
“Haba dai bbu komai, aure fa zai yi soon”
“Nasani fa, namiji ne fa ba mace ba infact you are not that easy mutum ya Bari ki kubuce Mai” saurin Kallon shi tayi kafin ta Mai da Kai kasa “Babu komai kawai Allah ya hada jinin mu ne?”
“Then Allah ya samu a danshi shi muma ko a dan da sa damu, he is damn lucky!” Suhaima dai barin kanta tayi a kasa ta kasa magana, maza dai sai a slow ji fa soyayyan da ya ke gwada wa matar shi Amma ya zo zai cika ta da dadin baki.
“And ban fada Miki ba girki yayi Dadi sosai Abokanai na duk sun yaba sunce za su kawo tukuici Amma Bari na bada nawa kafin na sun ya iso” hannu ya Kai cikin aljihu ya fiddo Rafan 2 hundred ya Mika Mata, nodding Kan tayi alamar Aa “kin amsa Mana come on ban son haka fa ni”
“Aa Allah ka bar shi”
“Ranki zai baci fa ki amsa nace maza” cike da fada yayi maganan this time around hakan ya sa ta sa hannu ta amsa hade da godiya, daga Mata hannu yayi da sauri alamun Bai so and she smile. “Ah ah Anty Ashe kin dawo” Hadiza ta fada tana Kallon Maryam da ta saki baki tana Kallon dilemma in da ke faruwa a gabanta. Dukan su Kan one seater da ke kusa da juna su ke zaune sai dai ita Suhaima ta yi gefe. “Mimi kin dawo? Ba ki yi sallama ba fa”
Tabe baki tayi “Daman ya za ayi kaji”
“Sannu da dawowa” Suhaima ta fada
“Sannunki” kawai Maryam ta amsa Mata fuskan Nan a hade kaman zata fashe ta nufi dakin ta.
“Mimi Yar rigima” ya fadi hade da girgiza Kai sannan ya dauki haydar su ka bita dakin.
Hadiza da ke kallo ta matso kusa da Suhaima a hankali ta fara magana “a dai ji tsoron Allah Kar a raba auran so da Allah ya hada” kallo Daya ma Suhaima ba tayi sparing inta ba ta tashi ta dau littafin ta ta bar falon.
A cikin daki Mustapha ya kura wa matar shi da ke ta faman kuka Ido, abin ko ba karamin Kona Mata Rai yayi ba da da dane ya dinga rudewa kenan Yana tambayan ta damuwan ta. Da kanta tayi shiru ta fara shesheka “tashi ki wanko idonki muyi magana” ba musu ta tashi ta yi abinda ya ce in ta dawo ta zauna “tell me me ke damun ki”
“Kai ne Ya Musty”
“Me na miki Mimi?”
“You love her right?”
“Wai Suhaima?” Murmushi ya saki “haba Mimi har Zaki zarge ni don na fada son wata macen bayan ki after all you gave the room for that to happen”
“Okay dan nayi taimako shi ne laifina ya Musty?”
“Meyesa da nace ki kaita gidan Anty Kika ki”
“I want to help myself and I trust you” ta fada tana Kara fashewa da wani kukan, yayi lallashin har ya gaji ya kyaleta. Tun daga ranar ta fara daure dauren fuska a gidan, sai ta wuni a waje sai dare ta dawo, haydar ko a gida ta ke barin shi, a cewarta ta bar mishi dan yayi abinda zai yi tunda ta San ya tsani hakan, tsakanin ta da Suhaima sai Kallon banza, baiwar Allah duk ta tsangwame kanta, she is feeling guilty ga Barr sai faman kara shige Mata ya ke ya dinga Jan ta da hira kenan tana kaucewa, Maryam ko ko bi ta kanta Bai yi ta Kai ta kawo ma kowa a dakin shi ya ke kwana.
Da dai ta lura da gasken Fushi ya ke da ita sosai,  ita kuma ba ta saba da fushin shi ba kwata kwata sai ta fara karaya. A hankali ta fara jure zaman gidan, ba ta cika fita sai dai duk da hakan zaman bai sauya zamani ba saboda wuni ta ke tana kallon series, wanda daman a gidan kawayen ta ta ke kallo saboda ya ki mata subscription tun asali ganin ba ta da aikin yin sai kallon a gidan shine fa ta dauke kafan ta gabadaya daga gidan dan zaman da ta ke ma ta daina. Yanzu kam da kanta ta je ta yi subscription in DSTV in ta zo ta cigaba da kallon ta. Mustapha yayi tunanin sauya wa tayi da yaga ta fara zaman gidan amma sai ya zuba mata ido ya gani. Ya ko gani in,  ba ta sisin fari ko baki a gidan nan banda ta yi bacci,  chatting, ta ci abinci sai ko kallo. Don ko haydar in ba nono za ta bashi ba to hadiza ta ke ba ma wa, aikin gidan kam Suhaima ke fama in ta gama ta karbi haydar.
Duk cikin su ba mai jin dadin zaman gidan hatta ita maryam in,  ba ta saba zama da sabon halin da barr ke ma ta ba wanda ta ke tunanin duk akan Suhaima ne. Daman dai kawayen ta sun sha gaya mata ba a yarda da namiji dari bisa dari sai yau ta yarda da hakan. Shi ko Mustapha lallabawa yayi ya dauke key in motan ta ya ma tafi dashi office ya boye gabadaya don a ganin shi zama kallon series in yafi mishi yawon gidan mutane. Ya ko kara sa Mimin nashi a wani hali,  dan fitan da ta ke yi ma ya zama bbu. Gashi ita kuma tana ganin kaman raini ne kaman ita a ganta a napep, anya har yanzu barr na sonta kuwa? Girman kai ya hana ta mishi maganan dauke ma ta key in da yayi, ba ta son ya zamana ita ce ta fara karaya. Tsakanin ta da Suhaima kam abun yanzu ba kyau, ta na dai amsa gaisuwan ta shima darajan yaron da ta ke kula mata dashi, kunsan ance mai da wawa saboda haka ta ma fi daura laifin kan mijin ta akan Suhaiman.
Yau ma in dai kaman kullum zaune ta ke a falon daga tana kallon Indian Series in da ta sa a gaba. Gabadaya ya dauke mata hankali,  sam ba taji sallaman mustapha ma da ya shigo gidan ba. Maimakon ya kalle ta gani tayi yayi cikin gidan da sauri. Ita ma in sai a lokacin taji kukan haydar da ke ta tashi, tabbas taji shi yana kuka sai dai cewa tayi ba ta da lokacin shi in ya gaji yayi shiru. Bin bayan Mustaphan tayi har zuwa corridor in da ta jiyo kukan yaron. Yana hannun suhaima tana faman jijiga shi, fuskan shi yayi ja tsabagen kuka har shidewa ya ke domin da alama yau kam ya ki jin lallashi. Ko da baban shi ya mika hannu kin zuwa yayi yana tirje wa “wai me ya same shi haka Suhaima?” Sai a lokacin ya ga hadiza da ke ta faman sinne kai alamun rashin gaskiya. “Wlh fa fadi yayi a hannu na ban sani ba shine ya buge kai” tsaki barr yaja yana girgiza kai
“saboda ke mahaukaciya ce yaron zai fadi a hannun ki ba ki sani ba ko?” Maryam ce ke maganan tana shirin yin wani ya mata wani kallon da ya sa ta yin shiru “Ki amshi danki” kawai ya ce ya kama hanyan bari wurin. Ai ko yaro da saurin shi ya zo wurin mamanshi yana kara kankame ta. Saurin zama tayi ta sa mishi nono a baki,  wannan karon kam kin amsa yayi ya janye kan shi, sai ta lallashe shi tukkuna ya amsa hat da sakin ajiyan zuciya, ita kanta tabbas ta san tana shiga hakkin yaron sosai.
Mustapha kam falon ya nufa direct ya cire DSTV in yayi disconnecting ma gabadaya har TV in. Mota ya nufa ya ajiye ya bar ma gidan gabadaya, tun maryam tana tsammanin zai dawo har ta gaji ta hakura. Shi ko ranar har kukan bakin ciki yayi, bai yi zaton za ta iya saka mishi da abinda ta ke mishi yanzun ba. A ganin shi ya fi karfin abinda ta ke mishi a wurin ta. Sai wuraren goma ya dawo gidan, ya samu haydar yayi bacci ita ko sai faman chatting ga ke a wayan ta. Wani irin nauyi yaji kanshi ya dauka, shin ba ta idan zai bullo wa alamarin maryam yayi nasara ne? Shi kam lamarin ta ya fara kai shi makura domin a kwanakin nan har aikin shi ya fara affecting. Har ya gama abinda zai yi ba ta mishi magana ba,  hakan ya kara tunzura shi. Yanda ya ke ganin ta bakikirin hakan ya ke jin zuciyan shi bakikirin, shi kanshi bai san inda ya ke nufa ba sai da yaga kanshi a gaban ta. Tsabagen chatting sai da taji mutum a gaban ta sannan ta ankara da shi, tun kafin ta gama gane yanin shi yayi nasaran wafce wayan a hannun ta. Kafin ta gama bude baki domin furta magana,  wani kara ta ji a cikin dakin. Saurin mai da idanun ta tayi kan wayan da ya wulla jikin bango da dukkan iya karfin shi sannan ya fado kasa. A rikice ta nufi wurin wayan, a bushe ta ke jin zuciyan ta ita ma. Kallon arziki ba ta yi wa wayan da ya dagargaje ba illa ma sims inta da m card da ta dauka kawai ta sama musu ma’adana ta nemi wuri tayi kwanciyan ta, a ranta tana fadin “Sai me? Kaine dai zaka kara siya” Tabbas ya san halin mimin da taurin kai amma bai zata za ta iya mishi abinda ta mishi yanzun ba. Da dukkan sakwanin duniya tana kara tabbatar mishi itan ba ta dauke shi a yanda ya dauke tan ba. A daren da kyar yayi yaki da zuciyan shi wurin ganin bai sa hannu a jikin ta ba domin haka ba halin shi bane. Kallo daya ya mata yana jin dukkan zuciyan shi na mai ciwo ya dauke idanuwan shi,  saurin barin dakin yayi domin yanda ya ke jin shi in har ya cigaba da kallon ta a ranar ba abinda zai hana bai fidda ma ta jini ba. Ya san yana da mugun hakuri amma kuma zuciyan shi tabbas ba abu bane mai kyau ba, ya kan dau lokaci kafin yayj fushi amma in yayin shi kan shi yana tsoron abinda zai iya aikatawan. Daren ranar kam bai runtsa ba,  saukin shi washegari weekend don haka yana sallan Asuba ya samu wani bacci mai karfi ya kwashe shi. Ringing in wayan shi ne ya tashe shi daga bacci,  da kyar ya iya bude idon yana dubawa ko yaga anty ne.
“Little come home now and ka taho da Suhaima”
A rude ya tambayeta “Anty lafiya?”
“Just come yanzu nan fa, it’s urgent” da sauri ya tashi ya dauki key in mota kafin ya kwalawa Suhaima kira “ina haydar?” Ya bukata
“Yana bacci”
“Maman shi fa?”
“Ai ta fita “
“Oya dauko shi maza we are going out” ganin yanda ya ke a rude he didn’t give room to intrude ya sa ta dauka haydar in kawai su ka nufi mota.
Sallama su kayi a Falon aiko four eyes Barr ya yi da Maryam da ke zaune gaban Dad insu Aneesa, kallo Daya ya Mata ya gane ta Sha kuka don ko idanuwan ta har sun kada sun yi ja.
Sai da suka zauna sannan su ka gagaisa, bawan Allah haydar ya hango uwarshi tuni ya fara kiciniyar zai je wurin ta ita ko Kallon shi ba ta yi ba kanta a kasa.
“Kawo shi Suhaima” Dad insu Aneesan ya fada, Anty ta Mika ma wa sannan ta ba wa Dad in “Maryam amshi danki Mana ko ba ki ga Yana son zuwa wurin ki bane” kaman za ta fashe ta amshe shi ai ko lafewa yayi a jikin ta. “Tashi ki je ki bashi abinci ya Sha ki dawo muna jiran ki” Toh kawai ta ce sannan ta tashi ta basu gu, sai bayan 5 minutes ta dawo kaman yanda ta bar su haka ta iske su, bawan Allah ko da ya koshi bacci yayi abin shi sai kawai ta kwantar dashi.
Addu’an bude taro Dad in yayi sannan ya juya ya kalli Mustapha “Massa me ya hada ka da matar ka tace ka daina kulata more like gaba ma kuke kawai” with a blank expression ya ke maganan cike da natsuwa. Barr Sunkuyar da kanshi kasa yayi a hankali yace “Abbah tace na Mata wani Abu?” Yanda yayi maganan kadai ya Isa tabbatar maka da yanda ya ke girmama Wanda ya ke maganan dashi bai ma iya dago Kan nashi ba.
“Shiyasa na nema ka ai don inji dalilin gaban da kuke da junan ku a cikin gidan ku na sunna”
“Ni ban gaba da ita Allah, ita ce dai Naga tana fushi dani ko na Mata magana ba ta tanka ni shiyasa na fita harkar ta for some time”
“Saboda duk ku taru ku Zama Daya ko? Haba lil sai kace ba namiji ba?” Wannan karon Anty ce ta yi maganan.
“Allah ba fa abinda ya faru ba kenan Abbah, ya fadi gsky man kullum fa samun shi na ke Yana hira da Suhaima infact komai yanzu ya ke bukata ita ya ke cewa ta Mai har fita tare su ke yi har kudi ya ke Bata hakanan yayi ta siyo Mata abubuwa Kuma duk bai fada min.” da sauri Mustapha dauke Kai.
“Toh Maryam tsakani ga Allah in zai yi kyauta dole sai ya fada Miki? A takaice dai Kishin ki na Mata kike right?”
“Abbah ba Haka bane gsky ne fa Yana faruwa”
“Naji ai ko ma Yana faruwan shin tun farko Antyn ku ba tace Miki Kar ki tafi da ita gidanki a barta a Nan Kika ki? Ke Mai taurin Kai ko?” Rau rau tayi da Ido kaman za ta yi kuka.
A hankali Barr ya fara magana “Abbah maganan fita da ita wlh sau Daya ne ku Nan mu ka Zo da dare ranar Zan fito haydar ya sa Kuka nace ta dauko shi mu zo, Zan iya Rantsuwa Banda kudin da Kika Zo ranar Kika ga Ina ba Suhaima ban taba Mata kyautan da baki sani ba Mimi” shiru yayi saboda takaicin abinda zai fada but this is his only choice, a hankali ya fara magana da kaji kasan Yana Jin zafin abinda ya ke fadan “Abbah miye laifina don na bukaci abu gun wacce da na sa za ta mun, Abbah kaga Mimi fa ba ta San ta tashi ta dafa min abinci ba Aa sai dai Mai aikin ta ne za ta yi in na ga dama in ci ko in barshi ba damuwan ta bane, ba ta San ci na ba balle Kuma batun sutaran na a tsaftace min su, ba ta San ta gyara gidan ta in ma Mai aikin Bata Nan sai dai a bar shi kaca kace Bai dame ta ba indai za ta gyara jikin ta, dakin ta ma ba ta gyarawa balle Kuma nawa duk sai dai Mai aikin ta tayi har kananan Kaya na fa sai taba Mai aikin ta ta wanke da na gane na fara wanke abu na, Abbah Mimi ce a matsayin ta na matar aure ina fita zata sa kafa ta bar gidan ita ma har in dawo ba ta Nan sai isha’i ta ke dawo min gida a matsayin ta na Matan aure ta bar min yaro a gidan Yana wahala sai dai ta sa a bashi kunu ko Madara ita Kam ba ta da Lokacin Dan da ta Haifa to shin miye laifina don nasa Suhaima ta min abu ta min Kuma alhalin ke ko nasa ki ba yi za ki yi ba Saboda Sam Sam ke ba ki gudun baccin rai na sai dai ni ne ma ke gudun naki kuma har kalaman Nan za su fito daga bakin ki Mimi ba ki min adalci ba ai yau ko auren Suhaima nace zan yi a ganina ba ki da bakin yin magana Kai wlh Ni ko ba ita ba Mimi in dai haka Zaki cigaba Ina Mai tabbatar Miki ba abinda zai hanani Kara aure kwanan, sannan Kuma ban tsamman Zaki Zo ki hada min sharri ba, you are more than this haba,  Abbah fa banda yawo,  kallo da chatting ba abinda ta ke tsinana wa a gidan nan.” gabadaya jikin su yayi sanyi, Ganin yanda Mustaphan sam bai son laifin matar shi har ya iya bude baki ya fada da kanshi Kam abin ba karamin Kai shi makura yayi ba.
Ita Kam Mimi tun da ya ambato kara aure jikin ta ya fara rawa “Ni ni fa ba sharri na maka ba ba Hadiza ba ce ta fada min?” Gabadaya jikin ta karkarwa ta ke yi.
“Ke kuma sai Kika ga yadda, Nagode Amma wlh yarinyar can sai ta bar gidana Kuma ban son wata Mai aikin cikin gida Kam in ba za kiyi ba zanyi abu na”
“Ya Isa dukkan ku kuyi shiru” tsit ko su kayi dukkansu kafin Abbah yayi wa maryam ta tas, da kanshi ya umurci in har ba ta gyaran ban ya Zo ya fada Mai aure ko ba fashi, sannan ya sa Mata dokan rashin fita kwata kwata In ba da wata kwakwaran hujja ba har Islamiyyan ko sauke ta yayi don a cewar shi bai ga amafanin Islamiyyan ba tunda ba ta yi koyi da yanda ya kamata a yi zamantakewar aure a musulunce ba. Sai kuka ta ke tayi shi dai Mustapha Kan shi a kasa zuciyan shi sai zafi ta ke yi. A hankali ya fara tuno tun farkon soyayyan su da maryam abinda har ya Kai su da aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *