LABARIN RAYUWATA CHAPTER 9 BY Ayeshay bee
Www.bankinhausanovels.com.ng
Burj khalifa, Dubai.
United Arab Emirates.+
Wani irin murmushi ne ya sauka kan fuskan shi dai dai lokacin da hannayen shi ke typing Mission accomplished a Email address in ogan shi. Wani iri annashuwa da farin ciki hade da kwanciyar hankali ya ke jin yana mamaye duk ilahirin shi. Ba yau ne na farko da ya fara samun saa akan case in da ya ke dauka ba. Wannan in dai ya kasance daban ne, saboda mahimmanci da ke tattare dashi. Bai ko shakkan komai ya zo karshe. Nan da nan yayi dialling wani numba, visa ya sa a mishi processing. He can’t wait to be finally back in Nigeria. Har ya kwanta, tuno tan da yayi ta sa shi saurin mikewa yana mai lalubo wayan shi. Nan da nan yayi dialling numban ta, kaman Wacce ke jira yana shiga ta dau wayan. Saukan sautin sallaman shi a kunnen ta kadai taji ta gane shi ke magana.
“Faroukh” tayi sauri fada. Sai da yayi murmushin da ya tsaya iya bakin lebba. Sautin muryan ta kadai ya tabbatar mishi she have been longing for the call. Dama ya San dole hakan zai faru, Sai dai Kuma wannan na daya daga cikin punishment inta ne.
“Zan sa a miki processing Visa zuwa jibi you are good to go In Sha Allah, Sai ki zauna cikin shiri” Godiya ta fara yi, Sai dai duk yanda ta so ya tsaya su gaisa da kyau hakan bai faru ba. Duk da haka taji dadin call in nashi, a da tayi tunanin ba zai cika alkawarin ba ya manta da ita. But now it good to feel like Nigeria is safe for her. How she miss her job, Kai Allah ya kiyaye ta a abinda zai sa ta kara shiga dana sani. The good thing, kyautan da ta samu daga wurin su Rawan da ku sunan da bikin ya jawo mata. Ba taji akwai wani Event planner da ke tashe a kasan yanzu kaman ta. One good thing about her, ba ta Nigeria amma hakan bai sa ta samu gargada akan sana’an taba. Saboda hakan ya sa take making sure she work with professional. Mutanen da ke da principle, in kaga harka yayi kasa to tabbas kaddara ce kawai irin ta Ubangiji.
…
Kotu ta cika makil wannan karon fiye da tunani ma. Abun mamaki hadda fuakokin da ba ayi tsammani. Domin dai Hajiya Binta ce zaune a gefe daya, wato uwar gidan Al-mansur, Wacce ake kyautata zaton ita ce ta shigar da karar. Sai cika take tana batsewa, fuskan nan a tamke ko alamun fara’a ba za ka hango. Gefen ta kuwa, Amina ko ince Nainarh ce a zaune. Kana ganin yanayin fuskan ta zaka san ranta a bace yake. Da dukkan alamu ba da son ranta ta halarci wannan wurin ba. Can gefe guda kuma, Umaymah Ameen da mukaraben ta. Kowa dai jira yake yaga ta yanda shari’an zai kasance.
Bayan Alkali ya samu shigowa ne, a ka karanto karar da za a gabatar a wurin kafin Kuma a gurfanar da Wacce ake kara wato Suhaima Adam Bello a gaban kotu.
Suhaima dai kaman yanda kowa ya sani, she plead not guilty akan abinda ake zargin ta dashi. Saboda haka Alkalin ya bama lauyoyin daman su fara gabatar da shari’an.
Barr mustapha ne ya fara magana cikin natsuwa da addu’an neman nasara a bakin shi ya Mike kan kafafun shi. Bayan ya gaida Alkali, ya kara neman a bashi daman tabbatar wa kotu ba Wacce ake zargi bane ta aikata laifin da ake zargin ta dashi.
Kai tsaye Faroukh ya fara Kira, abun mamaki Sai da ya Kira Faroukh inne idanun shi ya fada kan Engr Usman, mijin Antyn shi Kuma yayar matar shi. Bai San yazo ko alama bai sanar mishi da zai shigo Abujan ba ma. Kusa dashi Faroukh in ya miko rashin a hade har ya karaso wurin da ake bukatan ya tsaya.
Cike da kwarewa, Barr mustapha ya kalle shi “Sannu Faroukh, wata yar guntuwan tmby ce nake da bukatan yi maka.” Bai amsa kawun nashi ya cigaba dacewa “Zan so ka sanarwa kotu ina kuka je kai da ranar da staffs in company inku su kayi meeting a guest house in Al-mansur”
Kai tsaye ya bashi amsan inda suka je in da Kuma dalilin da ya Kai su.
“Wa ya fara barin wurin a tsakanin ku?”
“Shine, saboda Kiran shi da aka yi a waya. Sai dai yana fita nima na fita” Sosai Barr ke samun karfin guiwan amsoshin da yake samu gun Dan Yayar tashi. Ba shakka they are going somewhere.
“Ba ka San wa ya Kira shi ba?” Girgiza Kai kayi hade da cije dan lebe.
“Kun ci wani ko shi kadai akwai abinda yaci bayan fitan ku har zuwa rabuwan ku dashi?” Wannan karon ma Aa ya amsa.
“To nagode Faroukh” juyawa wurin Alkali yayi ya sanar mishi iya tmbyn da ya zai mishi kenan. Daga nan aka Sallame shi.
Next hujjar da Barr ya gabatar Kuma, short video clip ne da aka yi connecting aka sa a laptop. Hoton Zayd Al-mansur ne ya bayyan baro baro akan screen in a cikin wani bar, gefen shi Kuma Hafeez wato ogan shine yana faman mishi bayanin cigaban da aka samu game da wani software da suke kokarin creating. Wani magana Zayd yayi akan Faroukh, nan da nan aka hango fuskan Hafeez in ya baci sosai “beware of that guy i don’t like him” murmushi Zayd yayi, har ya dan mike yana fadin “bara naje jewel na jira na” har zai tafi Sai ga daya daga ciki ma’aikaciyyar su pat wato Patricia tayi appearing tana ta faman murmushi. “Oga har zaka tafi, baka sha abinda na maka ordering ba?” Dariya yayi sannan ya dauka ya kurba sau biyu Sai ya ajiye sannan Kuma yayi saurin kara dauka. “This is the best, I need it. Have fun with my oga pat” Yana fadin haka da saurin shi ya bar wurin. A nan clip in ya kare.
Tsit wurin ya dauka kafin Barr mustapha ya tashi ya fara gabatar da bayani kaman haka. “Binciken mu bai tsaya a iya Al-mansur ba kawai, Aa ya Kai har kan duk wani ma’aikacin shi Wanda su ka hadu a ranar dama Wanda bayanan da Kuma duk na kusa dashi. Interestingly, bincike ya nuna mana cewa baya rabuwan zayd da Faroukh, bar ya tafi wurin hafeez a sanadiyyan wayan daya mishi zasu tattauna. A Kuma wannan bar in ne muka samu duk wani rahoto da muke bukata, nagode ya mai shari’a” bayan yan wasu lokutta ne, Alkalin ya bukaci ko akwai magana da lauyan Wanda ke kara zai yi kan batun.
Kai tsaye ya tashi ya fara bayanan shi “Tabbas kwana wata da ya shaidu ya tabbatar da bayanin inda Zayd yake bayan rabuwan su da Faroukh Amma Kuma ba wani kwakwaran hujja da ta bayyana cewa wannan wine in da ya Sha ke dauke da poison in da aka saka mishi ciki. Sannan Kuma har mintuna nawa ya dauka bayanan kafin poison in ya fara attacking in shi? Wannan ba ta isa hujja ba a ganina rakan shi dade, ina fatan kotu tayi duba akan hakan.”
Bayan Kotu ta bawa Barr Mustapha dama ne ya kara tashi yana fadin “Saboda sanin hakan ne yasa binciken mu ya Kai har asibitin da aka Kai Al-mansur da ita Wanda ake zargi bayan gobaran. Shaidan dai da lauyan gwamnati ya bayar kan tabbatar da poison aka sa mishi a abinci ko abin Sha. Sai dai Kuma ina ganin anyi omitting fadin wani irin guba ce wannan. Bayan samun sunan ta da yanayin ta a asibitin, mu ka Kai bincike akan guban research center.” Mikewa Barr mustapha yayi ya amso wani paper ya Mika aka ba wa alkali sannan ya cigaba da cewa “Wannan gubar an tabbatar mana da cewa guba ce Wacce ta ke aiki a hankali a cikin jikin dan Adam a hankali tana mishi illa. Sannan ba ta fara bayyana kan ta har Sai ta Kai kaman wasu awanni a jikin Dan adam. Duba da irin lokuttan da duk abubuwan nan suka faru, za a gane cewa lokacin da guban ya diba bayan cin abincin da Wanda ake kara ta bashi yayi kadan ace a wannna abincin ya samu. Baya da haka daya daga cikin ilolin wannan guba ya kunshe sa yunwa da gaggawa kafin fara aikin ta. Wanda anyi hakan ne saboda an San zai koma wurin ta Kuma wurin ta zai nemi abinci in yunwan ya taso mishi. Nagode ya mai shari’a” gani kake kawai fuskokin dayawa daga cikin kotu ya dau fara’a, musamman wandanda su ke tausayin Suhaiman. Har ko da Nainah, duk da alakan da ta fahimci cewa akawai tsakanin ta da mijin ta, hakan bai sa taji cewa tana jin haushin Suhaiman ba.
Nan da nan kotu ta bukaci ganin Hafeez da Kuma Patricia. Shiru ne ya dau kotu, bayan wani dan lokaci wani force ya shigo, wurin aka samu sanarwar Hafeez na hanyan karaso daga airport saukan su kenan daga UAE Sai Kuma pat da aka tafi dauka ta a ma’aikata.
Lauyan gwamnati ne ya mike domin gabatar da shaidun shi, shi Kuma. Duk biyun magana su ke akan halin girman Kai irin na Suhaima da Kuma yanda aka santa da Amal. Hujjar shi dai daya ce, Wanda tayi haka it so clear she is after something don ta kashe shi bakomai bane. Har ga Allah, bai San haka shari’an zai kasance ba, ya dauka cewa ba ta wani hanya da za a cire ta daga wannan zargin. Musamman ya raina Barr Mustaphan, Yana ganin bai wani kware sosai ba.
Next Wacce aka nemi gani a gaban kotun kafin isowan su Hafeez, Zeenah. Cike da dagawan ta, ta tashi ta karasa wurin. Kotu ta bukaci jin sunan ta da alakan ta da Wacce ake zargi. ” Sunana Zinaru Amma an fi kirana da Zeenah. Suhaima Kuma kawata ce mun hadu a gidan yanci” Hankali kwance ta ke amsa tmbyn da ake mata har aka zo kan shaidan da za ta bada.
Dariya tayi tace “Nasan abinda Suhaima ba ta sani ba. Kuma akan kawarta da tayi sanadiyyan zuwan ta Lagos wato Faree’a. Abinda yasa Faree’a kawo Suhaima Lagos ba dan komai bane Sai don son cimma burin ta akan Zayd Al-mansur da Kuma budurwar shi Amal. Tunda nasan Faree’a nasan ta mutum ce mai buri, Kuma in tayi buri ko ta wani hali Sai ta cika ma kanta. Nasan ta tun farkon da ta fara shiga harka. Haka Kuma nasan tsakanin ta da Hafeez wato abokin aiki Al-mansur, saurayin tane tun kafin Suhaiman ta zo Lagos. Amma tun zuwan ta bai kara zuwa. Burin Faree’a kuwa shine, Al-mansur. A Instagram ta San shi, farko a handle Amal kafin ta fara following in shi. Ta dade tana bibiyar shi saboda yanda ya ke burge ta, hakan Kuma tana tunanin shine dai dai target inta na irin matsayin da take son takawa a rayuwa. A cikin sambatun samun shine, ta hadu da Feedo, yarinyar Umaymah Ameen. A wurin ta, ta samu labarin alakan da ke tsakanin Umaymah da zayd da Kuma irin yanda take neman fansa. To taba ba Feedo aikin Sai dai maimakon ta rama ma ta, ita ma fadawa tayi tsundum a soyyayn zayd, kafin ta ankara ya gama da zamanin ta ya watsar. Faree naji hakan ta tafi nemo Umaymah Ameen, bayan sun saba ta nuna mata cewa tana da wacce zata dau mata fansa wato Suhaima. Tayi Using Inta ne saboda tasan Suhaima na da daman da zata iya daukan attention in Zayd, musamman ma dake sun gane irin macen da ake nema. Da gaske ne akwai plan akan da Suhaima da Umaymah su kayi akan Zayd, sai dai sun fasa Amma abinda basu sani ba dukkansu Faree using insu tayi. Nasan hakan ta hanyan Feedo, Wanda yanzu haka tana cikin kotun nan” To shari’a ya fara juyewa inda ba ayi zato ba. Har ma ga Barr Mustaphan, don ko da Zeenah tace mishi zata gabatar da shaida bai zaton irin wannan kwakwaran shaida gare ta ba. Lauyan gwamnati kam Sai dai zuba ido.
Aka Kira Feedo, duk ta kara maimaita abinda Zeenah ta fada. Kai har pic insu da Zayd sai da ta nuna a matsayin shaida. Mum in Zayd fa ido ya raina fata, Sai dai Nainerh kam jin ikon Allah kawai take. Abunda basu sani ba kuwa shine, Faree’a ba a gun Amal tasan Zayd ba. A gunta tasan shi domin dai da Faree’a aka yi bikin ta. Kuma tayi ta kururuta Zayd, ita Kuma Nainerh tasan halin Faree’a shiyasa ta yanke alakarta da ita. Nan Kuma ta fahimci ta bibiyi Suhaima ne don ta nuna mata bata isa ba tun da tace a kyale ta. Dadi da karawa, Faree ba Zayd kawai ta hango ba harda Amal, don tasan halin a barta musamman da ya kasance ita ma yar kungiyar ce. Sai dai a yanzu ido ne nata.
Tana ji kotu ta nemi Umaymah Ameen, duk tsoron reputation ranar ajiye shi a gefe tayi saboda kwarin guiwar da Umar Faroukh ya bata. Nan ta gabatar da abinda ya faru tsakanin ta da Suhaima da ma Faree’an tiryan tiryan. Mutane sun jinjina abun sannan Kuma dayawa sunyi tur da halin zayd. Ballantana Kuma da kowa ya San mutuwar Amal, Wacce har yanzu ba wanda zai ce ga exact abinda ya faru da ita. Mahaifiyar shi a wurin sosai tayi Dana sanin karar da ta shigar musamman da ta gane ta zubarwa danta mutunci warwas. Nan Kuma tayi godiya ga Allah da yasa ba ta sa an wahalan da yar mutane ba. Domin dai duk ita ta hana.
Da manya jami’an tsaro Faree’a da Hafeez suka iso wurin shari’ar. Zo kaga idanu, duk sun kade. Ga Allah wadai da ke ta faman tashi a cikin kotun kafin a saisaita komai Sai ga Patricia ma an daddago ta.
To zance fa ya Sha kwana. Domin dai asalin dalilin kamo su Faree’a da Hafeez ba wai akan case in Suhaima bane. Aa akan wani bincike ne da aka kungiyan CID na Nigeria bincikawa. Wanda ke hannun dan Nigerian da ke aiki a Egypt as a military intelligence. Sai dai CID inma sun bashi aiki yana musu wato Umar Faroukh Machina. Binciken kuwa akan Al-mansur industry ne Wanda ke hannun Zayd wato na computer. Abu ne kuwa da ta shafi intellectual theft.
Wani Software Industry a can kasan ake ma zagon kasa. Sai sun gama designing abun su kafin su Kai da sakewa Kuma Sai su Al-mansur su saki nasu, banbancin abu daya biyu ne. Anyi hakan kusan sau uku, gashi nasu company in Sai bunkasa yake da abin su. Hakan ya sa su ka shigar da karar a can kasan su, nan Kuma karar ta shigo har cikin Nigeria. Abun da Machina ya fara yi shine samun wani mutum daban ya shiga cikin company in Al-mansur in Yana kawo mishi rahoto. A nan suka gane cewa Hafeez ne mai designing duk wani abu anan wurin. Don haka ake son tafiya dashi domin bincike Amma he have to be cleared here.
Hafeez bayan yaji baki daya zargi da ake mishi, ba wanda ya karyata a ciki Sai na attempting kashe Zayd. “Nasan ina mishi zagon kasa, ina Kuma amfanuwa dashi ta hanyan cuwa cuwa Amma kuma Shirin kashe Zayd ba ya daga cikin tsari na gsky.” Kallon kotun yake cike da nadama a idanun shi, bai zaton duk abinda ya aikata zai bi shi har Dubai ya dawo dashi ba Sai da hakan ya faru. Ya San ba za a yarda akan zancen da ya fada kan Zayd ba, Amma Kuma shi ya San bai aikata hakan ba.
A hankali ya karkata kallon shi kan Umaymah Ameen. “Kiyi Hakuri Umaymah, ba Zayd ya sa miki ciwon da kike dauke dashi ba. Nine” wani irin kallo Umayman ta Kai mishi, idanuwan ta sun yi jajur ba ta Sanda ta silale kasa ba.
“Ba a sanin ki ba nayi amfani dake lokacin Zayd ya shiga wanka, shi inma Kuma bai sani” rasa bakin magana tayi, shi can’t believe all these years da ta dauka tana zargin Zayd tana tsine mishi wai ashe bashi ya sa mata cutan nan ba. Duk da kuwa hakan bai goge cutan son da ya shayar da ita ba. Amma Kuma taji wani Abu daga cikin kullatan shi da tayi ya kau. Sunan Allah ta koma kira kafin aka bukaci Faree’a.
Duk abinda Zeenah ta fada gsky ne Kuma ita ma ta tabbatar da hakan. Yau dai rana ne na fadin gsky da gsky. “Ba a Instagram na san shi ba, mijin kawata be Kuma tun a bikin ta naji ya kwanta min” Abinda ta fada kenan, da ya tabbatar da zargin Nainah. Duk da hankalin ta ya kwanta jin cewan Zayd bai da HIV amma Kuma har zuciyan ta tana jin ba ta cancanci yi ma wani hukunci ba saboda tarin nata irin laifukan ga mahaliccin ta. Musamman ma da likitoci suka kara tabbatar mata ba zata taba haihuwa ba a rayuwan ta domin mahaifan ta ya lalace, karshe ma Baki daya cire shi a kayi. Bayanan wani irin wari take jin Yana fita daga kasan ta, duk da yanzu dai an fara samun sauki saboda ta saduda ta fara komawa ga Ubangiji.
Faree’a ma kiri kiri tayi denying sanin wani abu game da zargin kashe Zayd. “Son shi fa nace nake, domin me zan kashe shi? Haka ma Suhaima ina da tabbacin ba zata taba iya yin kisan Kai ba” Nan fa kotu ta dauka, kowa da irin abinda ke fitowa daga bakin shi. Ba wanda yayi tsammanin shari’an za ta zo da sauki haka. Sai dai Suhaima kam ta riga ta gama yarda ranar addu’a ce kawai ta gani. Ta Kuma kara yarda cewa ba wanda zai rike Allah a rayuwan nan ya taggayara. Sabuwan nadama ne ke shigan ta musamman inta tuna cewa wai yau Amal ba ta duniya. Tana da bukatar haduwa da Zayd, domin sanin asalin abinda ya faru da kawarta.A hanyar fita daga kotun, Suhaima suka hadu da Nainarh. Kallon kallo su ka tsaya yi ma juna kowa ya rasa abun fadi.
“Suhaima” Nainan ta fada cike da abubuwa dayawa daga sautin muryan ta.
Kafin ta hado abinda za tace mata back, taji Dr Fahad yana fadin tazo su wuce. Gabadaya su Engr murna suka dinga taya su. Abun mamakin kuwa wai harda Faroukh. Ikon rabbi kenan, ita dai Suhaima ba ta da wani bakin magana.
A hanya take fadawa Dr Fahad Anty Nainah ce ya gansu a tare. Shi kanshi Sai da ya jinjina abun.
Ranar wani irin kwanan farin ciki tayi duk da in ta tuna ita tayi sanadiyyan Amal Sai taji wani iri a ranta. Za taso taga zayd, tana bukatan ya mata bayani dayawa game da ciwon Amal in. Duk da dai ta riga ta tafi, yanzu Addu’a ne kawai mafita. Kuma tana yawan mata sosai, ta kanyi mafarki da ita tana mata murmushi. Duniya kenan, Allah ya sa mu dace.
Washegari Barr ce ma Suhaima yayi kawai tayi zaman ta a gida ba Sai taje ba Amma fir taki zancen. Da ita aka fara Kuma da ita za a gama shi a cewar ta. Hakanan dai suka isa kotun da ta cika makil, cikan ta har ya fi na jiya sosai. Kowa zuwa yayi ya gane ma idanun shi labarin da ya watsu ko ta ina cikin gari.+
Kai tsaye Patricia aka nemi ta bada nata bayanin. Da farko fir taki bada hadin Kai, Sai da Alkali ya nemi da a mai da ta cell Sai ranar da ta shirya fadin dalilin da tasa Zayd Shan wannan abun bayan har ya manta ya tafi.
Da dai attack in yayi yawa dole ta bude Baki “Hafeez ya dade yana ce min yana so na, ban San ko wasa yake min ba Amma ni kam yayi min ba kadan ba. Don haka mun kasance yana yawan sani wasu aiki da bai kamata ba a cikin company in Kuma ina yi mishi. Ya kan ce zai min duk abinda nake so in nayi mishi, barin ma da ya gane zan iya yin komai saboda shi. Yace zai iya min komai in dai ya samu abinda ya ke so, I can even be his wife. Wannan dalilin yasa nayi tunanin sa ma shi Oga Zayd poison saboda ina ganin if he is no more, Hafeez zai iya samun duk wani abinda yake so tunda na San burin shi kenan. Am the one behind it but is not my fault. Even the fire, Nina kunna gas in Yana fita da kadan kadan sannan na sa igiyan yin leaking so that I will get what I want” nan take wurin ya dau hayaniya Sai da Alkali yayi magana tukun.
“Are you sure you are the only one behind it?” Nan take ta kara tabbatar. Shi kan shi Hafeez never expects this. Turn out Faree is even using Hafeez to gather Information akan Al-mansur. Abun dai duk kwamacala, Sai dai Alhmdlh da komai ya bayyana.
Nan fa Alkali ya fara yan rubuce rubucen shi bayan wani lokaci ya dago ya fara bada verdict in shi kaman haka “Kotu ta yanke hukuncin danka Hafeez a hannun jami’an binciken tsaro na kasa domin su cigaba da gudanar da binciken su. Kafin nan Kotun na Umartar Kulle Company da ake zaton anyi ta’asan a ciki har zuwa lokacin da za a kammala binciken. Bayan haka kuma, za a kiyasta duk wani al-mundahana da Hafeez in yayi ya biya company kudin shi tare da tara da zama kurkuku na wata biyar da Kuma dama da kotun ta bawa Umaymah tana iya shigar da nata karar akan abinda Hafeez in ya mata. Sai Faree’a da aka ci tara dubu dari uku na mutanen da tayi amfani dasu domin cimma wani manufan ta. Batun Rasuwan Amal da lauyan gwamnati yaso ya daga Kuma, dukkan bincike ya tabbatar da ba hannun Suhaima a ciki don haka Kotu ya wanke ta daga dukkan wani zargi da ake mata. Bayan haka dai akwai taran da suma aka cisu ita da Umaymah na kudirin da su kayi akan Zayd Al-mansur. Shi Kuma Zayd in kotu ya bukaci da ya nemi gafarar duk wata yarinya da ya san ya cutar wa rayuwa, Sai duk Wanda bata hakura ba to tana da daman shigar da karar ta.” Bayan ya gama fadin wannan ne ya dago ya kalli jama’an kotun da kyau kafin ya kara maida hankalin shi kan abinda ke gagan shi. “Kaman yanda dokar kasa ta tanada, kotu ta yanke ma Patricia zaman kurkuku na … A sanadiyyan…” Da karfi ya buga guduman da ke kan table in “This is my verdict, kotuuu”1
Ko ta ina Yan jarida kawai kake gani suna kokarin ta yanda za ayi su tattauna da wadanda aka yanke ma hukunci a wannan lokacin. Cike hadda Patricia da ke ta faman zabga kuka tana fadin ita fa taimako taso. Umaymah Kuma Sai faman tmby take ta amsa akan za ta shigar da Hafeez kara ko zata kyale? Murmushi kawai tayi ta shiga motan ta. Rayuwa ta riga da ta nuna mai darasi so ba ta ganin sai ta wani wahalar da kanta da dukiyan da take Shan fama kullum wurin tara su. Bayan haka, she have her own issues to face yanzu haka musamman a yanzu da duniya ta San me take ciki, ta Kuma San asalin ta. Sai dai kowa da irin nashi matsalan don haka bata ganin saboda wannan za ta iya durkushewa.
Faree’a dai Sai zaro idanu take yi, musamman inta tuna cewa ba ta da takamaiman inda zata je. Ko giyan wake ta Sha ta San gidan karuwai ba nata bane a yanzu. Daman Hafeez ne take gani a matsayin mafakan ta to shi Kuma ga yanda ya kasance dashi nan. Shawara daya ne, ta hada kayan ta tayi garin potiskum wurin yan uwan mahaifin ta da a da ta nuna musu su bakomai bane. To tasan duk abinda zasu mata in taje, hannun ka bai rubewa ka cire ka yar don haka tuni ta gama yanke shawaran mafitan ta. Duk bata da wani abun arziki a yanzu, Amma tasan akwai kudin da zai ishe ta biyan taran da ake bin ta sannan sauran taje ta Kama sana’a dashi, tun da shi kadai ne tasan zai zame mata rufin asiri a yanzu.
Hafeez kuwa tuni a ka wuce dashi. Umar ke gaba har Sai da ya tabbatar da an wuce dashi sannan yayi saurin karasawa wurin Barr da ke tsaye. Hannu ya bashi su ka gaisa ya mikawa Dr Fahad dake gefe. “Am Umar Faroukh Machina” kafin yayi wani magana Sai ga Faroukh ya bayyana a gare su. Wani sarawa yayi wa UF Machina sannan ya juya gun Uncle Musty da Dr da suka saki baki suna mishi kallon mamaki.
“Weldone Faroukh” Uf ya fada yana fadada murmushin shi. “Your nephew is my agent, ni ya ma aiki all these while na San you have been suspecting. Ni nasa shi aikin har akan Suhaiman ma” bashi uncle Musty ya kalla ba sai Faroukh da ke ta murmushi. Hararan Barr yayi “Amma Faroukh baka da hankali, you should have told me everything”
“Ai ya sabawa aikin mu In yayi hakan” in an understanding ya amsa Sai dai har lokacin yana mamaki. “Let me get your no, ina so mu hadu dole zamu yi magana” Suhaima da Zeenah ta riga taja ta sun wuce gida bata ma San me ke faruwa. Sai dai daga Barr har Dr sun riga sun gama gane waye UF Machina. Bayan haka suka rabu da zummar zasu yi waya kafin su tafi Kaduna.
Su uku suka tafi Apartment in da Suhaima take. Da taji labarin Faroukh aiki yake ma CID sai da ta girgiza. “El-yas fa?” Tayi saurin tmby saboda ya ma fi mata Kama da jami’in bincike akan Faroukh. “Tare dashi mu ka samu aiki. Secret Investigator ne shi inma. Ta kasa muke aikin mu, har mu ci nasara Kuma ba a gano mu. Sai dai mutum yaga an Kama shi. But aikin ki is personal, shiyasa har kika San ina bibiyan ki.” Rasa abun cewa dai tayi kawai, sai dole shirun ne ta dauka.
Abun da yafi damun ta bai wuce tasan cewa a yanzu zaman Abuja ba zai mata ba, kaman yanda zama gidan wasu ma ba nata bane a yanzu. Don haka take ganin duk yanda ba taso dole ta nemi mahaifanta, da kuma mahaifinta don a yanzu shi kadai ya rage mata. Rokon ta daya Allah yasa wani Abu bai same shi, tana bukatan neman gafaran shi ko ta samu albarka a rayuwan ta.
Washegari, Zeenah ta dau akwatin ta it’s ma ta nufi hanyan nasu garin. Komai dai ji suke ya kare musu, yazo karshe Sai dai duk da haka suna mai gode ma Allah da irin kyautan daman da ya musu. Da sun mutu cikin wannan hali basu San mai zasu sanar ba. Godiya mai yawa Suhaima ta mata tare da dimbin kyauta daga kudin mutum da ya dinga bata kudi a zaman ta gidan yanci a Lagos. Wanda har yau bata sake gani ba, ba Kuma tasan dalilin shi ba. Sauran kudin ko daga wurin Zayd da Amal suka fito. Ko bakomai they owe her, dole ta nemi gafarar su su inma.
Ko da kudin Faree’a ya iso ta. Kiran Faree’an tayi ta maida mata daga ita har Umaymah. A gidan Umayman suka hadu. Suhaima dai daman bata rike ta da komai ba, domin har yanzu tana ganin Umayman kaman wata babban jigo a rayuwan ta. All thanks to her yanzu za ta iya cigaba da karatun ta a inda ta tsaya. Farko dai license Exams za tayi Sai Kuma housemanship Sai tayi service shikenan Kuma Sai abinda Allah yayi. Duk da haka dai Umayman ta nemi gafaran ta. Faree kuwa Sai da ta basu tausayi. A nan take gaya musu gsky ta San Zayd mijin Naina ne tun asali. Sai a lokacin Suhaiman ta tuna ta hanyan ta zata iya ganin Zayd. Don haka ta nemi address inta. Haka suka rabuwa kowa zuciya ba dadi, wannan kadai ya ishe su hukunci saboda duk cikin su ba wanda zai ce Yana jin dadin rayuwan da yake Shirin fuskan ta a yanzu. Karshe dai, duk an hadu an gane duniyan ba komai bane. Allah kenan, mai yanda ya so.
UF Machina, musamman ya nemi su Mustapha da Fahad suka hadu over Dinner. Sun tattauna abubuwa dayawa daga cikin har da yanda ya nuna musu Yana son tafiya da Suhaiman kasar Egypt. Duba da hujjoji da dalilan shi, nan take su ka amince. Amma fa sun shaida mishi Sai taje Kaduna, yazo ya tafi da ita a can. Passport inta ya nema domin yasa a fara mata processing VISA, da duk wani abinda ya dace kafin zuwan lokacin.
Ana gobe zasu tafi Kadunan ta ziyarci Nainah. Duk mamakin ganin ta da Nainah tayi, sosai taji dadin zuwan ta. “Suhaima” kawai take Kira tana rike Baki Amma a hakan Sai da kwalla ya fito mata fuska. Bayan sun dan natsa ne, take ce mata “Kema ashe yanda rayuwa tayi dake kenan? Faree’a ba ta kyauta ba domin nasan da Baki hadu da ita ba da komai bai Kai da hakan ba. Nayi Dana sanin harka da Faree da har hakan ya zama sanadiyyan sanin ki da tayi” tana fadan hakan ne cikin matukar jin zafi. Hakika Suhaima har gobe ba karamin matsayi take dashi a wurin ta ba.
“Bakomai Anty Nainah. Kaddara tace kawai, Kuma ko bata sanadiyyan Faree ba it will happen ba wanda ya Kuma isa ya canja hakan.” Shiru Nainah tayi, kalaman Suhaima na shigan ta. “Hakane Kuma, Allah ya shirye mu baki daya” daganan shiru su kayi. Zuwa can hiran ya karkata kan rayuwan da har tana tmbyn ta Halima. Abun mamaki a wurin Nainahn ta ke jin kawar ta Ajiddah dai zama bai yi dadi a gidan Alhajin da ta aura ba, don haka dole ta fito daga karshe. Yanzu kam wani take aure mai dan rufin asirin shi kawai, matar shi daya da yara biyu. “Rayuwa kenan, in kinga Ajiddah kaman ba ita ba Suhaima. Ba wannan gayun da kwalisa. Baki daya duniya ta gama nuna mata hankali. To gwara ita ma. Ni nawa mijin dani da bbu ai duk daya. Nayi aure ne Amma kaman ban ma taba yi ba” ta fadi hakan tana jin wani kuna na fita daga ranta.
Suhaiman ce ta dan tausar da ita. Ta nuna mata kasa sittin laifin tane ko a baya. Amma yanzu ta zake damtse ta Kama mijin ta hannu bi biyu. Ba ta kara tabbatar wa da gaske laifin nata bane Sai da taji yanda Suhaima ke faman fada mata abinda Zayd ke so, yanda yake so ayi shi da Kuma abinda ya ki jini. Dayawa daga ciki duk zaman ta dashi na shekaru bata sani ba.
“Amma Sai ina gani kaman ko mai zan mishi a yanzu bashi da wani amfani” sanar mata da dukkan abinda ya faru game da marar ta da gaban ta tayi. Nan dai Suhaima ta lallashe ta sannan ta cigaba da nuna mata duk wannan ba zai hana ta kula da shi ba. Amma farko ta fara sanin waye shi tukunna da duk wani takun sa. Tasan tana lacking abubuwa dayawa daga ciki kuwa har da karatun addini. Sai dai ita ma Suhaiman ba ta jin tana da isashen da zata iya ba wani. Ko akwai ma yanzu ba ta da wannan lokacin. Recommending mata inda zata samu Islamic book tayi sannan tasa ta shiga wani group na addini da Dr Fahad yasa aka sata ciki. “Ubangiji ya miki gatan samun miji, gatan aure” tana fadin haka ne tana jin wani zafi a nata ran. Sai lokacin ta gane aure Rahma ne. Gashi dai duk sun gama tsiyan su basu da mafaka. Amma ita Nainah a ba dadi, gata gida auren ta cikin rufin asiri. “Kar kiyi wasa da auren ki yar uwa. Domin baiwa na irin naki. Kar ki damu da duk wani hali na mijin ki. Kiyi ta mishi addu’a kina bin dabarun da Zaki koya. In Sha Komai mai karewa ne da izinin Ubangiji. Sannan Kuma ki rike kaddarar ki hannu biyu, ki yarda dashi sannan ibada Kar ki sake ki taba wasa dashi” Ranar dai Nainah Sai da taji dadin zuwan Suhaima sosai. Sai dai itama Suhaiman tana jin cewa ba ko shakka, Nainah ta mata abubuwa da dama a rayuwa Wanda ba ta iya mantawa. Ta so ta a lokacin da ba Wanda ya maida abun arziki. Allah sarki, Allah ya ji kan Goggon ta. Ita ce ta tsaya mata. Nainah ma Kuma ta bada nata gudunmu wan babba.
Sai can tukunna Suhaima ta bukaci ganin Zayd. “Ba ya kasar, ban Kuma San ranar dawowan shi. Domin Sai muyi wata ba muyi magana ba. Abinda nake fatan canjawa saboda nasihan ki gare ni. Amman in ya dawo zan neme ki. Sai dai zan neme ki wani alfarma”
“Fada inji, I can do a lot for you Anty na” murmushi tayi sannan tace “Why not ki auri Zayd, tunda ya na son ki kuma kema kin fahimce shi fiye dani da nake matan sa ma.” Dariya Suhaima ta dan yi.
“Kiyi Hakuri Anty na, banda wannan. Bazan iya auran zayd ba”
“Why not? Kinga ni ba haihu zan yi ba. Kuma nasan a kwana a tashi dole Zayd zai bukaci yaran shi na kanshi” wani tausayin ta taji ya ratsa ta, kaman ta gaya mata yanzu hakan ma Zayd na bukatan yara. Shi in mai boye wasu abubuwan da yake so ne, in dai ba mace bane. Shiyasa ba ta San da hakan duk da matsayin ta na matan shi.
“Kar ki damu Allah zai kawo muku mafita” Suhaima ta fadi haka, har ranta dai tana tausaya ma ta. Domin da ko yar Zayd sai dai tsarin Ubangiji. Ya riga ya fadi cewa, duk Wanda yayi da matan wani za ayi da nashi haka duk wand aya lalata yar mutane to ya jira yi ganin hakan akan nashi. To Zayd hakin mata nawa ya dauka? Sai dai neman rufin asiri kawai.
Cike da jimami da kewan juna suka rabu. Sai dare Suhaiman ta bar gidan. Tana komawa Kuma ta hau Shirin saboda Barr ya riga ya sanar da ita tafiyan su Kaduna a washegarin ranar.
Washegari tun da safe Dr Fahad ya zo ya dauke ta domin tafiya Kaduna. Kafin su wuce ne ya bukaci tazo su je ta gaida mahaifiyar shi. She wasn’t totally in for the idea Amma Kuma ba ta so ta nuna mishi ba ta son ko dan irin muruncin sa ke tsakanin su. Hakanan dai suka nufi gidan, a ranta tana tunanin wani irin tarba za ayi mata, duba da irin halin Ummin nashi da ya bata labari. Har suka isa ba ta wani tanka shi kan magana da ya ke ta faman mata ba. Already a ranta tana ta fama hada yanda za ta tafi Damaturu, irin tarban da za a mata. Ko Kuma za suki zama da ita ta kara shigowa duniya ne. Musamman jiya bayan ta dawo daga gida Nainarh, Umaymah ta Kira ta wai in ba damuwa tazo su zauna tare mana kawai. She can help in Vows. Ba tayi declining offer in ba, saboda tasan she may need it. Sai dai Kuma ba ta bata amsan ba. Alaman hesitation in da Umayman tayi recognizing in her silence ne yasa tace mata, she should go and think about it.
Har Sai da yayi parking da kyau cikin gidan sannan ta fahimci sun iso. “Bismillah” yace mata. Nan da nan ta fito, tana faman fargaba. Duk da ba wani abu ke tsakanin su da Dr ba a yanzu. Da suka shiga cikin gidan, Yan matan su ka fara iske wa a falon suna hidimomin su. Suna ganin shi, da fara’an ko waccen su suka taso suna gaishe shi. Sannan suka gaida Suhaima.
“Ummi fa?”
Wacce taji an Kira da Laila ne tace “Tana study” hanyan cikin gidan ya kutsa bayan yasa Suhaiman ta zauna. Lailan ce ta kawo mata refreshment. Tana niyyan tmbyn ta Zahra Sai ga ta nan ta shigo. Tana ganin ta, ta fadada fara’an ta. Zahran ma kuwa fara’an take. A mutunce suka gaisa, har suna dan labari kadan kadan.
“Ya Faroukh in ya fasa zuwa ne?” Girgiza Kai tayi tana blushing.
“To shine kika zauna a nan? Aje a shirya tarban shi ko” Suhaima ta fada, cike da kunya zahran ta sadda kan ta a kasa. Sai can Kuma ta tashi da saurin ta, ta koma inda da alamun can ta sauke shi.Ba yabo ba fallasa, Ummin ta amsa gaisuwan Suhaima. Sai dai Kuma ta lura Sai kallon ta take, kaman mai son karanto abu a fuskan ta. Hakan yasa Suhaiman dukan da kanta. Ba su wani dade ba, Dr Fahad yace zasu wuce. “Ba zaku jira lunch ba?” Ummin ta bukata.
“Kai muna kan hanyan Ummi” ya amsa.
“Toh Shknn ba matsala” mikewa tayi ta nufi ciki. Can Sai gata ta fito, da Dan gift nylon a hannun ta. Lailah ta bama wai ta ba Suhaiman. Amsa tayi tai godiya. Abu daya Kuma Suhaima ta fahimta gun Ummin. Ba za ta wani iya tuna Ummin ta sosai ba Amma memories inta na nan cikin kanta. Don haka bata shakkan wasu abubuwan nasu na shige, kaman yanayin takama da rashin son magana duk. Ko dan ba ta manta cewa Dr ya gaya mata ita ma yar kollere bace. Maybe shiyasa abubuwan nasu ke shige.+
Da suka zo fita ne Sai ga mota yayi parking a haraban gida. Surprisingly, Amma to Dr in banda Suhaima. Faroukh ne ya fito, Sai ga El-yas ma. Dukkan su sanye da manyan kaya, which is unusual domin dai ba shigar su bace. Yau Kuma Sai ya musu kyau fiye da tsammani. Kallon su kawai Dr yake ya kasa shiga mota, Suhaima Kuma didn’t offer any explanation. El-yas ya fara ganin shi, dake shi in ba wani sanin shi yayi ba Sai ya tabo Faroukh. “Ahh Dr Fahad ne ai”
“Ga Suhaima a gefen shi ai” a tare suka karasa wurin Dr in. Ya basu hannu suka gaisa. Dr na Shirin tmbyn ko wurin wa su ka zo Sai ga Kiran Zahra ya shiga wayan Faroukh. “Hello zee mun shigo”
“Wurin Zahra kuka zo?” Dr in ya tmby, El-yas ne ya amsa shi. Kafin yayi demanding for more explanation ya shiga cikin big brother mood in shi. Zahra ce ta fito, hakan ya tabbatar mishi da abinda yake tunanin daga yanayin noke noken da Zahran ta fara tana ganin shi.
“Shine F in?” Dr ya bukata, kasa amsawa tayi Sai Laila da ke bayan su ta amsa mai, zo kuga harara gun Zahra.
Irin kallon attack in da Dr ya fara aika mishi yasa Faroukh in dukan da kan dole. “Bani numban ka” kawai yace, El-yas ne ya bashi sannan ya bude mota ya shiga. Suhaima already na shiga don haka kawai ya ja motan su ka bar gidan.
“What ur future plan” kaman daga sama taji tmbyn nashi. Kusan 30 minutes kenan su kayi da barin Abuja, duk lokacin ba Wanda yayi magana Sai yanzun da ya katse shiru da ke ta tashi a tsakanin su.
“Housemanship” ta fada ita ma kaman ba da shi take yi ba.
“Finally, then?”
“Service” ta sake fadi, tana kallon titi. Cikin yan kalilan kwanakin nan, ba tayi zaton cewa zata kara taka wannan hanya ba a rayuwa. Ashe tana da wani sauran farin ciki da sakewa a rayuwa. Ashe tana da sauran dama yin magana hankali kwance kaman ba ta tattare da wani matsala ko damuwa a rayuwa.
“Good, daga nan fa Kuma?”
Tl
Tunani dayawa ne ya fara mata yawo a ka. Zuwa can tace “Work?” Yanayin amsan nata ya sa shi gane kaman by ta ke.
“Nothing special?” Murmushi ta sake sosai, Sai dai yafi Kama da na ciwo akan farin ciki.
“Me kake expecting?”
“Marriage?” Ta gane tmby ne ya mata. Amma Kuma sai ta dan fuske.
“Let me just hope for the best” ta fadi, tana dukan da kanta saboda juyowan da yayi yana kallon ta.
“To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi”
Suna isa Kaduna ya wuce da ita gidan shi. Faran faran su ka gaisa da Rufaida ta mata tarba mai kyau da mutunci. Ta Kuma yaba sosai. Duk da yanayin Rufaidan ta San fuskewa kawai take tana dannewa. Amma dole akwai kishi. Sai dai ta rika tasan cewa ba wani abinda zai shiga tsakanin ta da Dr banda mutunci, bayan nan ita ma ba ta fatan wani Abu. Ba wai Dan ya mata wani abu ba. Aa kawai saboda tana ganin mutum kamili kaman shi bai dace da irin ta ta gurbataciyyar rayuwan ba.
Bayan sun natsa ne Dr in yazo ya same ta da alamun magana ya ke so suyi “Barr ya Kira ni, yace a kaiki gidan Anty, mum insu Faroukh, so yakike gani?” Dan shiru tayi dan bata ma San abun fada ba. Tunanin ta daya bata San wani irin tarba zasu mata ba, musamman ma Antyn. Tun dai yanzu ta San everything is open, kowa ya San komai. An San halin ta na boye da Kuma na zahiri.
“Ba matsala muje” tace saboda sanin banda wani mafita bayan wannan.
Suna shigo Sai ga Anisa dasu Muhibba da gudun su. What she never expect to happen har zuciya ta. “Sis I miss you” Anisa ta fada bayan tayi hugging inta. Da farin cikita duk ta Kama su. Gaskiya yaran nan, Sai dai godiyan Allah Amma akwai zuciya mai kyau.
“Ina mum?” Ta tmby jiki a sanyaye
“Tana ciki, wow sis I thought I will never see you again ma” murmushi tayi, Wanda ta dade ba tana yin shi kawai ba wai ya Kai har kasan zuciya ta bane. Sai dai dan yin is more like an obligation ne kawai.
Mum seems nice and welcoming. Har congratulating ina tayi akan yanda case in yayi turning out. More like she is so over the moon about her son achievement. Ba wanda ya San Faroukh is involved Sai yanzu kawai. Dakin su na da suka tafi da Anisa, the house is still comfortable but God! Ji take kaman she no longer belong there. Haka dai na daure.
Da yamma Faroukh su ka zo da Maryam. Ita ma ba yabo ba fallasa suka gaisa da ita. Sai dai yanayin ta kaman na Rufaida, nasan akwai abinda take dannewa. More especially inta ji Barr na mata tambayoyi.
“Ina so inyi registration for license Exams ina. Amma kafin time in ina son zuwa gida.” Ta amsa mishi tmbyn plans inta da yayi. He seems glad, ganin am finally moving on with my life. He still cares duk ta lura interest in nashi ba Kaman da bane. She likes that he is moving on, dan har ga Allah ba ta shirya wani tashin tashina a gaba ba Kuma.
“Sai dai zan dan katse miki hanzari Suhaima” haka kurum taji gaban ta ya fadi more like tana jin kaman he is about to tell her something huge and demanding.
“Umar yazo ya same ni, ya naso ku tafi tare dashi zuwa can kasan da yake zaune. He tell me his reasons Kuma mun gamsu dasu. Sai dai zan so kije ki ganewa idon ki da kanki zai fi akan in na gaya miki” Confusion ya mamaye ta Baki daya. Na farko tunani ta fari waye Umar? Sannan taya za ta bishi zuwa wani kSa can da ba ta sani ba Kuma su yarda da hakan? Anya ba suna neman hanyan da zasu yi getting rid of her bane?
Ya karanci abinda ke fuskan ta. Dai dai lokacin Kuma Anty ta shigo. Maryam da ke falon Kuma ta fita ganin maganan ba nata bane ba.
“Umar Faroukh Machina or should I say Sanda?” Da sauri ta mike tsaye dai dai lokacin da Antyn ta karaso tana fadin “Lafiya?”2
“A ina ka ganshi Barr?”
“Relax ki zauna muyi magana”
Da kyar ta iya zama sai dai kana ganin zaman kasan tana cikin tension “Ya sanda?” Ta ambata, Sai dai still tana cikin doubt. Musamman in ta tuna Barr ya karanta labarin ta Sai da kawai ka man zolaya ne ma kawai ya ke mata.
“Shi Faroukh ya ke ma a aiki” a hankali ya warware mata komai. Sai dai still komai na zuwa mata kaman almara. Still Sai tace “Ni kam bazan bishi ba, Zan koma gidan Mahaifina duk kuwa kalubalan da zan fuskanta yanzu a can in” Abun mamaki, tana fada zuciyan ta na kara mata wani zafi. Neman yaki da zuciyan kawai take, domin ambaton gidan ma kadai na sa mata wani irin kuna na zuciya. Tana jin kaman ba ta yanda za ta iya abinda ta ke fada. Musamman inta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaya Baba da abokanan su, yanda suka keta mata mutunci. Duk da haka she is willing to overcome duk wani kalubalan da ke Shirin kunno mata.
Cikin hikima da dabara Anty ta fara lallashin ta. Musamman da yake Mustaphan ya gama sanar da ita duk yanda su kayi da Sanda. Itan ne kawai ba ta sani ba, ba Kuma sa so taji a bakin su. “Kije in kin ka sa zama nami alkawari zan sa a dawo dake. Kawai ke neme ni in kinji wani Abu” Abinda Antyn ta fada mata kenan. She is not convinced though, har lokacin ba ta jin za ta iya bin Sandan. Mutum da ta watsar Baki daya a baya. Ba ma haka ba “Amma miye fa’idan hakan? Ba wani abu tsakanin mu dashi fa”
Shiru Antyn tayi ta rasa ta yanda zata bullo mata. “Ba wurin shi Zaki zauna ba, Mahaifiyar shi na can. Ita tace ya Kai mata ke, tasan duk abinda ke faruwa” shiru kawai tayi tana tunani, yanzu abun ya Dan fara mata making sense. Tasan a labarin da take iya tunawa Ummin ta na bata, Maman Sanda mutuniyar tane. Sunyi zaman mutunci da amana kafin ta bar gidan su Sanda. Maybe saboda hakan ta ke son taimaka mata. Shirun da tayi, ya tabbatar musu da sun shawo kan matsalan. Sai dai ita tunani daya ya makale mata. Yanda zata fuskanci shi Sandan.
Is not like she got a solution, don kuwa washegari bayan Anisa ta taya ta shirya kayan ta Baki daya. Cike da jimamin kara rabuwan da zasu yi a karo na biyu. Ita kanta Suhaiman duk da ta girmi Anisan sosai Amma tana jin dadin zama da ita. Yan biyu ne suka shigo da gudu suna fadin “Anty Suhaima wai kizo ya isa”
Dam! Haka taji gaban ta ya buga. Hatta Anisan da ke kusa da ita Sai da ta fahimci hakan. Amma Sai ta hau tausasa ta. Tun daga corridor take jiyo hiran su da Barr. Ga muryan zar Yana tashi, ba ta tunanin zata taba mantawa da wannan muryan kuwa. Jiki na rawa, sanye da hijab inta ta karasa falon tana kallon kasa. Idon nun da ke ji a kanta ne dai, ta kasa tantance na waye. Wuri ta samu a kasa ta fara musu gaisuwan jam’i. “Ina kwananku?” Ta fada tana jin maganan na Shirin makalewa a bakin ta. An dai amsa ba Kuma za tace waye be daga cikin su ya amsan ba saboda hankalin ta da ya fara gushewa.
Zaman shiru ne ya gudana na tsawon minutes. Can Sandan yace “Yakamata mu tafi, banson muyi missing flight duk da dai na dare ne” Yanayin maganan shi kwata kwata bai canja mata ba, Sai dai ta kasa kallon shi taga ya yanayin shi ya koma. Duk da yanda zuciyan ta ke azalzalan ta tayi hakan.
“Aa na dauka za ku tsaya lunch ai. Abujan naga 2 hours drive ne” girgiza Kai Sanda yayi “ban son a samu matsala ne dai kawai”
“No ka bari Dan Allah” Baban su Anisa zai zo ba Sai ku gaisa ba. Kuma Anty ma ba ka gaishe ta ba, let me talk to her. Tashi yayi ya bar su, su biyun a falon. Duk cikin su ba Wanda yayi ma wani magana a haka kowa na harkan gabanshi har Antyn ta fito. Suna cikin gaisawa Sai Engr tare da Faroukh, gaisuwan mutunci su kayi, har da karawa da musu godiya. Su ka nuna mishi bakomai. Duk yanda ya so su wuce, Anty kin yarda tayi. Tilas su ka tsaya aka yi lunch sannan su Anisa su ka fidda ma Suhaima kayan ta. Gabadaya ma ba ta hada wani abun kirki ba, ta dai debi abubuwan da take bukata Sai kaya da basu wuce five set ba duk a trolley saboda Kar tayi kaya dayawa.
Gabadaya su ka fito raka su, ita dai jikin ta a sanyaye ta shiga front seat in. Tana musu Sallama har Umar Sanda ya ja mato su ka bar gidan ba ta it’s dago idanu ta kalle shi ba. Abun ma har da wani irin nauyi da kunya da take ji ya mamaye ta duk a kanshi. Shi inma kala bai ce mata ba ya cigaba da tukin shi cikin kwanciyar hankali. Ba ta San dalili ba taji yayi parking a wani gida.
Sai da ta dago kanta, ta gane gidan Dr ya kawo su. A tsaitsaye su ka shiga, su ka gaisa. Shi inma Sanda godiyan ya mishi. Da suka ki cin abinci, Rufaida ta hado su day snacks da drinks dole Suhaima ta amsa. Dr in dai shima jikin shi duk a sanyaye haka suka bar shi suka Kama hanyan Abuja. Da Shirin yayi yawa a motan, kawai sai yasa wa’azin Sheikh Aminu Daurawa na Kundin tarihi. Shi yake ta tashi a cikin motan. Sai dai zuciyoyin su na dauke da abubuwa dayawa, musamman Suhaima da har yanzu ba ta San the best way da Yakamata tayi reacting wa zaman ta kusa da Sandan ba. Ga tarin tambayoyi a bakin ta, Amma ba ta ita ya kallon shi balle ta ga yanayin fuskan shi, ko ta hasaso yanayin yanda zai amshi tambayan nata. Sai dai Kuma shi inma ba magana ya mata, balle ta gane wani irin yanayi yake ciki game da ita. Fushi yake da ita ko kuwa?
Haka suka isa Abujan ba abinda ya shiga tsakanin su. Wani wuri ya fara zuwa, aka kawo mishi wasu takardu yayi godiya suka tafi. Sai a sannan taji yace “Akwai abinda kike bukata, ko abinci ko dai wani abun?” Sanin bai kallon ta yasa dole ta bude Baki tace “Aa” daganan bai kara cewa komai ba ya dau hanya. Wannan karon wani estate taga sun nufa. A bki wani apartment yayi parking yana fadin “ina zuwa” ya dan dau mintuna a ciki. Sai can Kuma ya fito dauke da jakan baya babba Sai Kuma jaka guda biyu, daya dai tasan na system ne Amma dayan she can’t say. Daganan kam hanyan airport ya dauka, Sai da ya fara tsayawa Immigration office ya amshi abu sannan suka karasa airport in.
Karfe shidda dai dai suka yi checking out sannan Kuma aka fara boarding. Duk abubuwan nan ba wani magana tsakanin su har suka samu wuri cikin jirgin. Sai da jirgin ya tashi tukunna ya fara hidiman gaban shi. Can ya bude side bag in ya dauko wani English novel ya Mika mata.
“Thanks” tace bayan ta amsa. Daman dai ta gaji da zaman shirun. Ai kuwa nan da nan littafin yayi nasarar dauke hankalin ta. Kaman ya sani, she definitely need it ko ba wai don kore zaman shiru ba. Ko Dan saboda current situation in da take ciki. Na rashin sanin mafita a rayuwa.
Karfe bakwai na dare jirgin su yayi landing a babban birnin Egypt wato Cairo. Bayan sun yi getting luggage insu su ka fita haraban airport in. Wani mutum taga Yana faman dagawa Umar in hannu. Suna karasawa wurin shi, suka rungume juna kowanne na fadin “I miss you” a bakin shi. Sai da suka tafa sannan wancan in ya dago kanshi.
“Suhaima?” Ya bukata, da Kai ya amsa mishi. Ai ko Sai washe baki Yana mata fara’a. Da English ya soma mata magana, Yana gaishe ta, ta amsa. She didn’t miss the Arabic accent in his voice.
“Wow! I finally meet you after so many years” bata ce komai ba, Umar in bai fada ba.
“Am Abdallah, I know he never talk to you about me though” murmushi kawai tayi. Suka shiga mota, suka bar Airport in. Tana baya tana jiyo hiran da ke gudana a tsakanin su. Don ma Arabic suke yi, ita Kuma ba ji take ba ma balle hiran ya dau hankalin ta.
Sun dan yi tafiya mai nisa sannan su ka shiga wani babban gidan. Architectural building in baki daya ya tafi da ita.
“Bismillah” wannan karon Umar in ne yayi magana ganin ta tsaya bata motsi. Yana danna ring in aka zo aka bude musu. Wata budurwar yarinya ce, fara sal kyakyawa da ita. Tana ganin shi ta hau murmushi tana fadin “Marhaban brother, where is she?” Dan hararan ta yayi, yace “Who?” Ba ta amsa shi saboda hango Suhaiman da tayi a bayan shi. Da sauri ta karasa wurin ta, hugging inta tayi tana fadin “Oyoyo Adda kun Sha hanya” hook Suhaima tayi, har ga Allah ba ta taba tunanin yarinyar ta iya Hausa ba ma kwata kwata. Ita taja ta suka shiga ciki dukkan su harda Abdallah dake ta tsokanan yarinyar da har yanzu ba ta San sunan ta ba.
Tana ganin matashiyar matar da ta fito tasan cewa mahaifiyar Sanda ne. Da sauri ta tsugunna tana gaishe ta. Dago ta tayi ta rungume ta. “Oyoyo my daughter, welcome home” da kunya Suhaima ta amsa.
“Jidda nuna mata dakin ta mana, can’t you see she looks exhausted. Ki kaita ta huta ko”
“To Hajja” ta amsa. Bin ta Suhaima tayi har zuwa dakin. Bai da wani hayaniya Amma ya dau hankalin ta. Bayin na ciki don haka nan da nan ta shiga ciki. Sai da ta watsa ruwa sannan tayi alwala ta fito. Tana tunanin ta ina ne gabas Sai ga jiddah ta turo kofa. “Wai Hajja tace a kawo miki abinci nan ko Zaki fita falo”
Da dan kunya tace “Bara nayi Sallah, ina ne gabas” nuna mata tayi sannan ta fita ta barta. Da kanta ta fita falon dake ta gane hanyan. Duk suna kan dinning saboda haka ta lallaba kusa da jiddah ta zauna. Ita tayi serving inta, a hankali ta fara tsakuran abincin. Abun mamaki Sai Kuma ta ji kaman ana kallon ta. Tana daga idanun ta, for the first time suka hada ido da Sanda. Kyar ya ke kallon ta ba ko kiftawa, tilas ita ta sauke nata idanun.”Why are you not eating? Ko ba kya son abincin ne?” Da kyar ta it’s bude baki tayi magana “Aa, ina ci” bai ce komai duk da hakan ya maida attention in Jiddah da Abdallah kanta. Wanda zuwa yanzu ta gane cewa shima dan gidan ne, musamman saboda kamannin da taga suna yi da Hajja. Sai dai da tayi Dana sanin fitowa cin abincin duk da ma Hajja ba ta wurin. Don haka kawai taji tana jin wani mahaukacin kunyan ta.
“Adda Suhaima how is Nigeria? And everybody? Na dade ina son ganin ki, Ummi keeps promising to take me there Amma Allah bai yi ba” she is confuse ko da ta amsa jiddan. Dan ba ta ma gane me take nufi bane kwata kwata. Zuwa can aka danna ring bell in. Da sauri Jiddah ta nufi wurin kofan tana fadin “Ina jin Ya Baffah ne, he promise he will come tonight”
“Jidd jidd” taji Wanda ke bakin kofan ya fada. Da sauri ta jawo hannu shi tana fadin “Close your eyes i have a surprise for you Allah” ganin yanda ta matsa mishi ya sa ya rufe idon dole. Wurin Suhaima ta Kai shi dake zaune kan couch yanzu tana ganin drama in da ke unfolding. She didn’t get wai za ayi surprising in Wanda ya zo da ganin ta. Don dai har suka karaso gaban ta bata gane waye ba.
“Now open” jidda ta fada da karfi tana dariya. Ko daya bude idon Sai da ya kifkifta tukunna suka dawo dai dai.
Four eyes su kayi da Suhaiman. Kowa na kokarin fahimtan Wanda yake gani a gaban shi. Da sauri ta mike tsaye tana fadin “Baffah?” Gyade mata Kai yayi, cikin rawan murya yace “Adda ke ce?” Sai Kuma yayi saurin hugging inta. “God i thought i will never see you again” wani irin hawaye taji ya fara cika mata idanu.
“Baffah Kai ne?” Da Kai ya iya amsa mata, shi inma hawayen ne ke fitowa hade da Kuma murmushin tsantsar murna.3
“But wait why are you here? Ina Anty Jamila?”
“Tana can gidan ta. Wait baki gane Jiddah ba wai? Maijiddah ce fa, maijiddan Ummi” da sauri ta sake Baffah tana kallon jiddan. Maijiddah? Kanwar ta? Da Ummi ta tafi da ita tana baby, she can’t even remember her face?” Wani iri hawaye ne ya fara silalo wa daga idanun ta lokacin da jiddan kw cewa “Haba i know she didn’t recognize me, na fada ma Yaya Abdallah da brother sunce wai i talk to much”
Riko hannun ta Suhaima tayi tana kallon fuskan ta sosai. Da sauri ta rungumw ta wasu hawaye na kara silalowa. Dukkan su kukan suke, ita Jiddah ba tasan kukan me suke ba. Halin ta ne in wani na kuka ita ma yi take. “Why are crying? Please tell me” tana fada tana cigaba da kukan.
Umar Sanda ne ya kara so wurin su Yana fadin “it okay please”
Lokacin Kuma Hajja ta shigo falon. Kallon su tayi ta girgiza Kai. Zuwa tayi ta jawo Suhaima gefe, tana lallashin ta. Sai a sannan ta lura Baffah ma yazo. Sai da suka natsa bayan lallashin da Hajja ta Sha. Tukunna Suhaima ta dago da rinannun idon ta, tana kallon Maijiddah “Ina Ummi na?”
“She will back in a weeks, sunje Sudan da baban ku” bata son ta cika tmby shiyasa ba ta tsaya tmbyn waye baban ba. Amma she wonders mai ya kawo Mijiddah da Ummi Egypt, gwara Baffah tasan Yana wurin Anty jamilah ne. Sannan most importantly, miye hadin su da su Umar Sanda.1
“Kije daki ki huta Suhaima, we will talk tomorrow kinj. Jiddah raka ta” mikewa tayi jiki na rawa, da kyar ta it’s musu sai da safe sannan ta lallaba dakin tare da jiddah. A dki jiddan ta sata a gaba tana ta mata tambayoyi, short short amsa take bata. Sai dai ita duk tana bukatan hakan Amma ta kasa tamabayan jiddan abu daya kan Ummin.
“Na kosa Ummi ta dawo, nayi missing Su Aseem. They couldn’t wait to meet you also” dan shiru Suhaima tayi kaman ba zata tanka ba. Sai Kuma tace “who is Aseem?” Rolling eyes Jiddah tayi “Kah Baki sani ba?” Triplets in Ummi ne. Aseem, Areef da Afrah. They are 10 years old, year in nan in sun dawo za su shiga high school”
“Ke fa wani Class kike?”
“University, am in my Second year” murmushi Suhaima tayi a ranta tana tunanin how time flies.
“Baffah fa?”
“About to finish his second degree” Wani irin dai Suhaima ke ji a ranta. Abun yafi karfin farin ciki ma. Dan wani irin feeling na daban take jin Yana shiga jikin ta. Ba ta taba zaton Rana zata zo irin wannan ba in her life. All thanks to Sanda, she owe him.
Ranar kam, ba ta iya bacci ma Sai ma juye juye da ta dinga yi da kyar baccin gajiya ya tafi da ita.
Yau, kusan kwanan ta uku a gidan su Sanda dake kasar Egypt. Tana cikin kwanciyar hankali sannan kwata kwata bata da matsala da daya daga cikin su. Musamman Hajja, matan na da shiga rai haka Kuma akwai sanin muhimmancin dan Adam. Duk yanda Suhaima taso ta dinga zaman daki, hajja ta toshe kofan hakan. Sa wa take a Kira ta, ta fito falo suyi ta hira ko kallon film. Haka lokacin girki, duk da mai aikin su Amma haka Hajjan za ta sata a gaba ita da jidda su shiga kitchen, tare suke aiki Kuma duk da kwarewan ta a girki a dan zaman ta da Hajja ta koyi abubuwa dayawa. Ba abinda yake burge ta kaman yanda matan kwata kwata ba ta wasa da Sallah. Inta fara karatun qur’ani Kuma ko azkar Sai ka dauka bacci take a dakin saboda yanda take daukan lokaci. Musamman ta sasu Jiddah, Abdallah da Baffah su ka Kai ta mall, taje tayi siyayyan abubuwa da dama. Ko taki daukan abu Jiddah dauko mata take yi. Haka su ka dawo da kaya niki niki, tama dauka Hajjan za tayi fada Sai taji yaba ma jiddan ma take akan kokarin da ta mata. Ashe ita ta sata yin hakan. Ai ko ba abinda ta nema ta rasa. Babban abinda ya kayatar da ita, yanda ya zama al’adan gidan, da an idan da sallan Asuba za a zauna karatun qur’ani duk a babban falon gidan kowa na bitan nashi. Ta gode ma Allah, ta Kuma kara gode ma Sanda sannan Dr. Dan da ba don su ba da taji kunya a wurin. Duk da haka Sai da Abdallah ya dinga dan mata ya gyara, don da alama duk cikin su yafi su ilimin addinin sosai. Abincin gidan kuwa ba a taba girki ba olive oil wato Zaitun da Kuma Habbatu sauda a ciki. Domin neman tsari daga cututtuka da dama.
Sai dai tun daga ranar da Sanda ya kawo ta, bata Kara ganin shi ba Kuma. Tana jin nauyin tambaya duk da damuwan da tayi. Ranar tana cikin kallon pictures da Jidda ta kawo mata, tana nuna mata su Aseem da Ummin da baban su. Ummin ta, ta zama babban mace. “Hotunan sunyi kyau sosai”
“Ai brother ne ke daukanmu yawanci. He got a great skill in photography. Kinga wallpaper in da ke courtyard In gidan nan, duk shi ya dauka, yayi enlarging insu suka bada nice view in nan. Shine aka yi printing ya zama wallpapers.
She almost ask waye brother, Sai Kuma ta tuna ashe abinda duk suke fada mishi kenan. Abdallah step brother in shine ashe, two years ke tsakanin su shiyasa they are more like friends.
Satin ta daya, Kuma gabadaya ta saba dasu musamman Jiddah. Hakanan zata zo ta zauna kusa da ita, ta kwantar da cinyan ta kan Suhaima tana fadin “Adda I’ve been dreaming of this moment ashe zai zo” irin maganaganun yana sa ta jin hawaye na Shirin zubo mata. Sai dai ta kan yi kokarin boyewa gudun kar Jidda ta fahimta. Sai dai duk da haka akwai kadaici, saboda duk suna zuwa school. Shi daman Baffah, ashe ba garin ya ke karatu ba, so a campus yake zama, Sai dai weekend ya shigo. Jiddah na zuwa Al-azhar. Abdallah Kuma na zuwa aiki Sai Hajja da ke zuwa wani Islamic College da take lecturing a can. Ganin yanda take zuba larabci, hakan yasa Suhaima ba tayi mamaki ba.
Don haka Hajja tayi deciding ayi enrolling inta a wani school ta dinga zuwa. Da ke tana da interest sosai akan catering, kawai sai ta zabe shi. Itama Sai ta zama occupied, da ta dawo Kuma ta tafi Islamiyya, da it’s da kanta tace ma hajjan tana son shiga. Akwai ranar da suka je gidan Anty Jamila, cousin in su Abbah da ta dauko Baffah. Turn out taga halin da baffan ke ciki ne a maiduguri yasa ta dauko shi da niyyan zata rike shi, itan kawar Ummi ce Kuma ta San abinda ke faruwa. Bayan ta dauko shi Sai ta Kai ma Ummin danta, Ummi tayi farin ciki sosai Amma Sai tayi ma Anty Jamilan kara tace ta rike shi kawai. Haka akayi, a gaban ta ya taso Sai dai Yana yawan zuwa wurin su, ta yanda har suka you sabon ban mamaki.
Taji dadin ganin Suhaiman sosai, harda hawayen ta. Sun dan tattauna da ita Anty Jamilan kafin suka dawo gida. Sai da Suhaima ta shafe wata biyu da kwanaki a gidan Amma ba Sanda. Tana jin dai ana waya dashi Amma ta kasa tmbyn kowa ina yake. Baban Abdallah ma da ya dawo, ashe yaje wani aiki ne Canada. Musamman yasa aka Kira mishi ita suka gaisa, shi inma dai Yana da kirki sosai.
A wani Weekend, taga an tashi gidan gadan gadan da aiki. Abinda ta lura shine aikin yafi focusing akan dayan side in dake gefen wurin da suke zama. Shi inma babban wuri ne sosai, don girman duk kusan daya ne. Bayan gyaran, Sai Kuma Hajja tasa su suka hau girke girke, musamman ita dake catering school ita aka sa a gaba tana ta abubuwa. Duk dai a wancan side in aka shirya su a kayataccen dinning table. Haka kurum Kuma take jin bata jin dadi ranar. Bayan ta gama aiki, ta gaji likis ne ta nufi dakin ta, ta dan watsa ruwa. Sai Kuma ta hau bacci mai nauyi.
Ba ta San iya lokacin da ta dauka tana baccin ba sai dai kawai taji muryoyi sama sama a kanta ana magana. “Ga Addan nan, Ina baku yarda dani ba” da kyar ta iya dagawa, tana bude idanun ta ta hadu da wasu kyawawan yaran guda uku duk suna smiling. Kaman da taga dukkansu suna yi yasa ta gane ba shakka triplets in da jiddah ke basu labari ne.
“Hey dear sis Adda my name is Aseem, this are my siblings Arif and Afra” ya fada yana nuna yan uwan nashi. Murmushi ta masu sosai sannan duk ta Mika musu hannu “nice to meet you little ones”
“Ba nace muku Kar ki tashe ta ba?” Jidda ta shigo tana fada, duk Sai suka juya wannan ya kalli wannan suna murmushin rashin gaskiya. They look so cute to her, nan da nan taji yaran sun shiga ranta. Duk suna Kama da Abdallah hakan yasa take tunanin ko iyayen su na da alaka.
Cewa Jiddah tayi ta daina musu bala’i. Sai bayan sun fita sannan fargaba ya fara kewaye ta. Sai lokacin abun ya sinking in, she is about to meet her mother. Bayan dimbin shekaru masu yawa. Rudu da rashin sanin abun yi ne ya cika mata kwakwalwa. Ba ta San farin ciki ya kamata tayi ba ko akasin shi. Hakan yasa ta kasa ko da mikewa daga kan gadon, baki daya jikin ta rawa yake ga Kuma zufan rikicewa da goshin ta ya fara fiddawa. Ta dade da cire rai da samun wani abu daga mahaifiyar ta, shiyasa ko yanzu bata wani tsammani wani abu mai mahimmanci, illa iyaka ta San idanun ta na matukar bukatan ganin fuskan da ya kawo mata duniya. Kaman yanda zuciyan ta ya dade yana suya akan hakan. Shin mahaifiyar ta, ta mata adalci kuwa a rayuwa? Shine har yanzu abinda ta kasa tantancewa. Shiyasa ta zabi zama a dakin saboda ba ta da ra’ayi akan me yaka mata tayi yayin da idanun ta suka sauka kanta. Ta dai samu wani sauki a ranta, ko don sanin da tayi zuwa Ummin nata ba yawon duniya ta shiga ba Kaman yanda aka dade ana ikirari, ko Kuma tace kaman yanda ita in tayi.
Ta naji aka bude kofa, Sai da gaban ta ya girgiza domin tsoron wanene zata gani. Wani sanyi ta dan ji ganin Baffah ne, jira yake ta bashi izinin karasowa. Da Kai ta amsa mishi, ya tako har zuwa inda take ya zauna daf da ita. Hannuwan ta ya kamo duka biyu, yasa cikin nashi Yana kallon yanayin ta.
“Adda nasan cewa is not easy abinda kike Shirin fuskan ta a yanzu. Ban San me ke zuciyan ki Amma Ina sin sanar dake Ummi ba ta bar ki wurin Abbah don bata sonki, Sai don hakan ne kadai mafita a gare ta a wancan lokacin. Ina so ki mata kyakyawan zato, domin rashin ki a rayuwan ta Abu ne Wanda bai taba gushewa ba. Kana ganin ta, tana cikin wadata da kwanciyar hankali Amma Kuma kallo daya ake mata a San akwai babban abinda ya gushe a rayuwan ta. Ba ta cika ma kowa maganar ki don bata so abun ya dame ta Amma Kuma ya dame ta in, I can assure you daga ni Sai Kuma brother kadai ta iya sanarwa abinda ke damunta. Ki zo muje ku gaisa, Sai ina so in akwai wani kullatan da kika yi don Allah ki min alfarman goge hakan a zuciyan ki” ba ta amsa shi, Sai dai Yana tashi ta Mika mishi hannuwan ta, ya dago ta. Hannun su a hade suka tafi har zuwa sashen Ummin. Su Aseem da Jiddah duk suna side in Hajja, hakan yasa wurin daukan shiru.
Da baban su Aseem suka fara cin karo zai fito falon. Cikin ladabi, Suhaima ta gaishe shi. Yana ganin ta ya gane itace, domin labari ya iske su. Albarka ya sa mata sosai, sannan ya sanar da ita zai fita Amma in ya dawo zai zo suyi zama na musamman.
Baffah ne yayi Sallama a side in, yana jin amsawan Ummi daga cikin dakin ta. Don haka suka cigaba da tafiya har wurin dakin.
“Ki shiga, duk munje mun mata Sannu da zuwa saura ke. Itan tace in shigo da ke” da Kai Suhaima ta amsa me shi. Ya mata wani kallo mai cike da nuna karfin guiwan sannan Sai ya juya.
Tayi seconds a wurin tana contemplating bude kofan. A hankali ta Kai hannun ta kan handle in kofan, ta fara murdawa. Sai dai duk yanda taso jarumtan, kafafun ta sun gaza bata hadin kai. Sam Sam ta kasa matsar dasu gaba, Sai ma ja da baya da ta fara yi a hankali, ita kanta ba zata iya cewa ga direct abinda kanta ke processing ba.
Zuciyan ta da tunanin ta sunyi cunkushewan da bata iya jin Karan bude kofan ba. Sai dai Kawai Mutum ta gani a tsaye a gaban ta. Kallon kallo suka tsaya yima juna, for some seconds, it all feel surreal and too good to be truth.
“Au taso ki yayi daga baccin? Me yake sauri ai Zaki tashi ko” Ummin ce ta fadi haka, kaman ba wani abu da ke damun ta. Suhaima kam ba ta ma amsa, Sai dai wani sanyi da take ji na zagaye dukkanin ilahirin jikin ta. “Shigo mana to” Ummin ta kara fada, ganin Suhaiman ba ta ko motsawa ya sa Ummin jawo hannun ta suka karasa cikin dakin.
A gefen ta, ta zaunar da ita tana kallon ta. She can’t believe Suhaiman tane ta zama haka. Wani irin kwalla take ji sun cika mata idanu, Wanda ta rasa ba dadi ne ko Kuma na bakin cikin rayuwan da yar tata ta tsinci kanta a haka. Kamo hannayen ta, tayi duka biyu tana kallon ta, Sai ta bude bakin ta za tayi magana Sai taji kalaman duk sun bace mata. Ba ta San mai zata ce mata ba, ba ta San abinda ya dace ta fada wa yar tata ba. Taba ta kadai da take yi, ji take wani irin annashuwa hade da fargici na zagaye da ita. Lallashin ta zata yi? Hakuri zata bata ko kuwa? She all deserves them Sai dai Kuma ba ta San taya ba.
Da sauri Kuma ta jata a jikin ta, tana wadata ta da dimin Uwa Wanda tayi rashi a rayuwan ta. A hankali Suhaiman ta zare jikin ta. She can’t resist this, it so good and beautiful. Sai dai duk seconds daya yana tuna mata abinda tayi missing kenan a dukkan rayuwan ta. Kallon Mahaifiyar tata, tayi Ido a raunane tace “Ummina meye sa baki jira ni ba? Islamiyya kawai Zan dawo, shine ya maki tsauri?” Tmbyn da ya dade yana cin ranta kenan, a kullum duniya Sai ta tuna wannan shiyasa a yanzun ma shi inne ya fara zuwa mata.
Girgiza Kai Ummin tayi, tana kallon yar tata “Saboda ban son kika tafiyana da idanun ki, a tunanina hakan zai fi Miki ciwo Kuma Zaki fi rike shi. Ko da na tsayan ma, Mahaifin ki ba zai bari in tafi dake ba, ya riga ya Gina katanga a tsakanin mu” Zuwa yanzu duk hawaye ne ke fita daga idanun su.
“Amma meye sa baki Kara nema na ba? Shin ki manta ina da bukatan hakan a rayuwa ta” Shiru Ummin tayi, a ranta tana mamakin yanda ta dinga jiran wannan ranar da Suhaima za ta sata a gaba tana tuhuman ta. Ashe zai zo? Ta dade da fara fidda rai.
“Nayi tafiyan da ba juyawa a cikin shine Suhaima, ko na dawo ba wani amfani tunda an riga da an min iyaka da ke. Ciwon nake gudu hakan yasa ban waiwaye ki ba, Sai ma hanyan da nake nema inga kin dawo gare ni baki daya. Ashe Allah bai nufa hakan ba”
da sauri sauri Suhaima ta fara girgiza kai “Ki dai nemi wani hujjan Ummi Amma wannan bai isa hujjan da Zaki bani akan bari na da kika yi cikin kunci, wahala da azaban rayuwa. Ashe daman uwa na gudun dan data Haifa? Meye sa kika zabi ki so kanki dayawa? Ki fada min gsky Ummi, dan na kasa daina zargin cewa ba ke kika haife ni ba, a duk yawan da nayi rayuwata, ban taba cin karo da Uwa irin ki ba don …”
“Keh!” Ihun da taji daga bayan tane yasa ta juyawa. Ido hudu su kayi dashi sai huci yake “ashe daman har yanzu da sauran rashin hankali tattare dake?” Umar Sanda ne, wani irin kallon banza yake bin ta dashi kaman Wanda ke Shirin shake ta.Ba ta tashi hakan yasa tayi juyawan ta. Ta riga ta gama gane tsanar ta ne ke gudana a cikin zuciyan shi. Hakan yasa ya watsar da ita, ko maganar arziki bai bari ya shiga tsakanin su ba. Bata ga laifin shi ba, don ko ita ada ta kanji ta tsani kanta. Alhmdlh, tunda ta Mika lamarin ta ga Ubangiji take jin komai na dawo mata dai dai ga Kuma wani irin natsuwa da take samu.
“Ina ke kike yawan maganan Uzuri, shin meyesa itan ba zaki mata ba? Kinsan irin halin da ta shiga a sanadiyyan rashin ki? Rashin hankalin naki har ya Kai ki duba tsaban idon mahaifiyar ki, kina fada mata mugayen kalamai? Ba uwan da ta cancanci hakan, ko da kuwa ba ta hanya aure ta same ki ba, ba dai abinda ya Kai wannan ciwo don haka kisan mekike yi” ba ta amsa shin ba, Amma Kuma kalaman shi ya Kai inda ya Kai a kwakwalwar ta. Tabbas ba ta kyau taba, Amma Kuma ita kanta ba ta San me take fadi ba. Hakan Kuma Yana da alaka da alakanta dukkan wani gurbacewan ta da tayi da rashin mahaifiyar ta a tare da ita tun ba yau ba.
Kalan gaisuwan da Sandan kewa Ummi yasa ta gane ba karamin mutunci ke tsakanin su ba da girmama wa. Bayan nan, ko kallon ta bai yi ba ya fita daga dakin. Hakan yasa ta kara shan jinin jikinta.
“Kiyi Hakuri bansan abinda nake fada ba” gyada Kai Ummin tayi “Na sani Suhaima nasan da ciwo Amma bar na Baki labarin abinda ya hada ni da mahaifin ki. Mahaifin ki mutum ne mai tsatsauran ra’ayi kema kinsan da hakan. Sai dai Kuma tun farko ya San ni ban dau hakan ba, shiyasa duk wani abu nashi Zaki ga ba kasafai yake min ba. Abinda Kuma baki sani ba shine, kafin na hadu dashi da Baffan ku na fara haduwa, shiya fara nema na amma Kuma sabo da irin halayen shi na neman mata shiyasa alakan tamu ba tayi wani nisa ba. Baban su Aseem kuwa shine saurayin da na so har sauran kiris muyi aure rabon ku ya hada ni da Abban ku. Bautan kasa ya kawo shi daga Kano, Kuma yayan Hajja ne, su biyu ne kadai wurin iyayen su. Sai Baban Abdallah daya taso a gidan su. Lokaci yayan babana da nake wurin shi a Borno shi yaki aura min shi, a cewan shi gwara Wanda aka sani domin dai kowa yasan baban mahaifinki a jahan borno da yobe. Nima Sai na hakura na aure shin duk da kuwa nasan kanin baffan ne, na dauka ba wata matsala tunda bashi in bane. Muna cikin kwanciyar hankali, ko a lokacin da na hadu da Hajja bansan cewa yayar baban su Aseem bace. Sai watarana da yazo ya iske ni, na shiga wurinta. Ba wani abunda ya hada ni dashi, har lokacin barin ta gidan da zama yaki dadi, ita kam kishiya tasa ta a gaba. Dole ta hakura da auren, har bayan ta tafi we keep in touch. Har lokacin da na haife ki, su kazo suna, yayan nata ya kawo ta. Lokacin already an hada ta aure da baban Abdallah, hukuncin mahaifin su ne. Bansan ina suka hadu da Baffah ba, Amma ya samu Abban ku ya sanar dashi wai saurayina yazo sunar yar shi, don haka ya bincike ni. A tare suka nemi ni lokacin, so sun San juna. A lokacin Abban ki bai dau abun wani serious ba, Amma a hankali ya dinga zuwa yana fada mishi abubuwa. Dalili kuwa har lokacin yana da ra’ayin ya mallake ni, cikin matan uwargidan tasan ya neme ni, hakan yasa kwata kwata bata kauna ta. Daga baya har waya ya fara min, Sai inki dauka. Tsabagen yawan wayan har Abban ki Sai daya San ana yawan Kira na, yace na bashi ya ma mutumin magana yaki saboda ban son ya gane Dan uwan shi ne. Abinda ya fara sa zargi tsakanin mu kenan. Cikin wannan sarkakiyan na haifi Baffah, tun lokacin ya fara tunanin baffan ba dan shi bane saboda irin text in da ake turo mai a kaina. An ganni a can, an ganni a nan, hakan yasa zargin ya kara yawo har yazo yana bibiyata. Kaman shi da Baffah, yasa shin yardan dan shine. Zuwa lokacin na riga da nasan aure na ya fara samun gargada. Wani Ikon Allah, ban dade da fara koyarwa ba, aka kawo Baban su Aseem University in da nake, ai Kuma lokacin abun ya tsanan ta. Domin dai rahota ake Kai mishi akan ana ganin mu tare dashi, Wlh Suhaima ko gaishe shi banyi saboda gudun matsala. Ya nemi in daina zuwa ko ina, ni Kuma naki. Baban su Aseem kuwa Oga nane, hakan yasa duk yanda naso guje mishi Sai wani abu ya hada mu. Bayan Baffah, na kara Samun wani cikin Amma haka mahaifin ki ya rantse ba nashi bane, muka hau muka fado Amma Ina yaki zancen, daga karshe dai tilasta ni yayi Sai da aka cire cikin nan. Nayi kukan bakin ciki, nayi takaici amma na zabi kare martabar aure na. To Sai dai shi aure ba ayin shi da zargi. Akwai wani zuwana maiduguri, Baffah na kai asibiti Abban ki ya sani zama gidan Baffa duk da ban son haka. Wlh cikin dare ba kunya mutumin nan yaso ya far min, ikon Allah ne ya cece ni a wannan daren. Amma ya min alkawarin ganin bakin ciki mara misaltuwa. Yanda ya fara kuwa shine da amsan Baffah, duk da nasan daga shi har matan shi ba Wanda zai kula min da da, nayi kuka na, nayi bakin ciki Amma hakanan aka Kai shi. Sai Kuma na samu cikin Mai Jiddah, lokacin Kuma bala’i ya taso gadan gadan, domin dai Abban ki cewa yayi Sai dai na kara cire cikin, ni Kuma nace ba Wanda ya isa ya sani kaf duniya. Muka dinga hawa muna sauka, har na haifo ta. Yaki yarda yar tashi ce, musamman ganin ba kamannin. Lokacin ya fara hada ni da yan uwana, har nasiha suke zuwa yi min in rasa abun ce musu. Daga karshe ce min sukayi in na kashe aure na kar na sake na waiwaye su, domin dai labari ya zaga cikin shege nayi da aure na, na haihu. Ban iya zama ana shegan ta min ya, don haka na nemi mahaifin ki da ya gyara abinda ya hada ko Kuma in Kama gabana. Yaki, Sai ma ya kafa min bala’i, wai zai iya hakura ya zauna dani Amma ba tare da Maijiddah ba, in San inda zan kaita, in ko nace zan zauna da ita a bakin aure na. Na gaji da auren zargi, don haka na sama ma kaina mafita domin auren dai ba inda zai Kai ki na zauna tunda ba yarda a tsakanin mu. Labari ya Kai gun yan uwana mun rabu dashi, kowa yace in Kama gabana. Ko na gaya ma Goggo da Goggon Adama illa iyaka za suce nayi Hakuri na zauna ne, ni Kuma ba Zan iya ba. Don haka na hau shirin tafiya, a lokacin Kuma mahaifinki ya sanar min in har na tafi kar na sake na kara tako mai gida, sannan Kar na sake na daukan mishi ya’ya’ bai amince ba. Ko ya fadi hakan ne ya na tunanin zan hakura na zauna, bai San na riga da nayi nisa ba. Wannan shine sanadiyyan rabuwan mu, Kuma direct Kano na tafi na kai ma Hajja kuka na. A wurin ta na gama idda na, har na cigaba da zuwa makaranta baban su Aseem bai ma sani. Sai da nayi shekara biyu ma a wurin ta sannan ya San Ina nan. Auren mu Kuma Sai bayan an mishi transfer Egypt, shi ma ikon Allah ne kawai saboda na hakikance na gama aure a rayuwa ta. Ban Kara waiwayan Damaturu ba, Amma kullum kina raina, dake bake kwana nake tashi. Kullum addu’a ta Allah ya raya min ke. Na barwa Allah ikon shi, nasan Kuma duk abinda ya same ki kaddarar kice Suhaima. Ko Ina tare dake kuwa zai faru, a sannan bakin cikin ma zai fi yawa. Sanda ke kawo min feedback akan ki, har zuwa lokacin da yayi loosing contact dake. Lokacin daga ni har shi mun ahiga tashin hankali, saboda yana da niyyan tun kan ki shiga University ya aure ki ya taho dake nan. Amma yasan baban ki ba zai amince ba, ba mu so ya fahimci wani abu bayan nan Kuma ga Goggo. Ya dade yana neman labarin ki, tukunna ya samu a lagos bayan ansan case akan company in da kike aiki. Tanan ya samo ki, don haka ina fatan Zaki yafe min duk wani abinda kike ganin na Miki” da kuka idanun ta, ta rungume mahaifiyar tata “Ina son ki a kullum Ummi na” rungume ta tayi ita ma, cike da farin cikin dake zagaye su ta ko ina.1
Washegarin ranar, Jiddah tazo ta tmbyn ta. Wai brother yace ta bashi Email address inta. Material ya turo mata na license exams da zata yi, da foams ta cika. Har yanzu dai tana mamakin wai ya so auren ta ada, to meye sa bai taba mata magana ba? Ko dai kawai don Ummin yake yi ne daman? Yanzu ta gane duk sakon da yake cewa an bashi ya bata, daga Ummin suke fitowa.
Ga mamakin ta kaman da haka ya koma mata tambayoyi akan karatun ta. Ba ta San Ina ya amshi numban ta ba, Sai dai Kawai taga mssg Yana tmbyn ta, tana dai karatu ko? Lokacin ya riga ya koma Abuja. So ta chat yake bata feedback kan duk wani abu dake tafiya akan Exams in nasu. Ta dade ba tayi karatu ba, hakan yasa take dan Shan wuyan abun. Daga karshe dole sai ta ajiye catering school in da take zuwa, tayi focusing gu daya. Islamiyyan dai har yanzu tana da zuwa. Ko fuskan tan tana Shan wuyan yayi, kawai sai gani tayi ya turo mata application in online course, Wanda duk yayi covering akan Exams in nata ne. Cikin ikon Allah Sai abun ya fara mata sauki, domin dai sosai ake warware musu komai. A haka ta cigaba da fafatawa har Exams in ya gabato. Ana three days to exam, ta shirya tafiya Abuja. Ummi dai ba wani son tafiyan nata take ba, saboda tana jin kar ta ki dawowa Kuma.
“Kin kwantar da hankalin ki Ummina, in dai nine Sai kin kore ni” hararan ta Ummin tayi “Kaji min yarinya, auren fa?” Dam! Gaban ta ya fadi. Da kyar ta iya basarwa suka cigaba da magana. Sai dai har ga Allah zancen nan Yana damun ta, shin akwai ma Wanda zai iya auren ta kuwa? Ta riga da ta sama ranta, kilan hakan na daga cikin kaddaran tane kawai. Har a jirgi tunanin da ta dinga yi kenan, Sai da kyar ta samu ta kauda shi tukuuna ta iya focusing kan abinda ke gaban ta.
Tana fitowa daga airport in, ta hango shi a haraban wurin yana tsaye kawai yana wasa da key. Kawai sai taji ya burge ta, musamman irin yanda yayi tsayuwan nashi hankali kwance idanuwan shi Kuma na kallon camera in dake hannun shi. Zuwa yanzu tasan his love for photography, saboda duk inda zaka ganshi Yana makale da haddadun camera. To In Sha Allah, Sai ya samu wani abu crearive ya dauka tukunna hankalin shi ke samun kwanciya. Lura da yayi ana kallon shi yasa ya dago idanuwan shi, Sai da jikin ta ya bata wani yarr sanadiyyan haduwan kwayoyin idanun nasu. A kunyace ta saukar da nata, kafin ta ankara kawai sai flash in camera ta gani. Da sauri ta dago, murmushi ya sakan mata “let go” yace yana amsan trolley in dake hannun ta. Ba wani magana tsakanin su har suka Kai mota, Sai da ya fara driving tukunna tace “Ya Sanda ina wuni” da sauri ya taka birki ya fasa tafiyan.
“Kar in Kara ji” ya fada da kakkauran murya, Sai dai taso gane wasa yake ko Kuma da gaske Amma ba alamun hakan.
“Baki San sunana bane? Don’t ever call me that again, am Umar Faroukh of you have to know again” dariya ya so bata, Sai dai yanayin saitin muryan shi ya tabbatar mata har ga Allah da gaske yake.1
“Am sorry” in short ta amsa. Ai kuwa a sittin ya ja motan. Straight bai tsaya ko ina ba ya dau hanyan barin garin. Ta so yin shiru Amma Ina yunwa da ke nukurkusar ta yafi karfin da haka.
“Brother Ina jin yunwa please” kaman ba zai tanka ba Sai Kuma ya Kai u-turn ya juya. A wani restaurant ya tsaya, da saurin ta kuwa ta fito tabi bayan shi. “Take away Zaki yi mu tafi fa, kinsan ai hanyan Abuja-kaduna in yamma yayi bin shi is risk” dole tayi hakan duk da ba ta kauna cin abinci a mota yana tafiya Kuma wai gaban shi. Tana cikin cin abinci taji an rufe mata idanu, it appears so odd to her, like yanzu wake wannan? Kaman dai yanda ake yi sai taga an miko mata hannu, thank God na mace ne. And she can’t forget it da sauri ta juya tana fadin “Anty Nainerh” side hugging juna suka yi, tana daga idanun ta taga Zayd Al-mansur a gefe ya zuba mata idanu. Rasa abun yi tayi for some second suna exchanging looks. Ta ma manta Umar na kusa da ita. “Suhaima” Zayd in ya fada a hankali still idanun shi akan ta. Cike da kunci tace ” I need to know about Amal please” abinda ke ranta kenan, abun da ya kasa ko da almaan bata a kwakwalwar ta.
“We need to talk then”
“Muje ko?” Umar in ya fada bayan an Mika musu order insu. Sai lokacin suka gane tare suke, da sauri Zayd in ya Mika ma Umar hannu su ka gaisa. Hakanan dai suka yi sallama bayan Zayd in ya mata alkawarin zai neme ta.
“Ke kinga tsohon saurayin ki ko?” Abinda yace mata kenan, Sai dai shi kanshi y rasa dalilin fadan haka.
“You should be careful, ban son ki Kara shiga matsala Kuma” dole ta saki murmushi a hankali tace “Thanks” yaji ko bai ji ba, bai dai amsa ba.
A hankali ta fara cin abincin ta, har ta gama ba abinda yace mata. Sai da ya bari ta Sha ruwa tukunna yace “When are you planning on getting married?” Dole gaban nata ya kara faduwa. Ganin Yana jiran jin amsan ta yasa tace “Lokacin da Allah yayi” juyowa yayi ya harare ta “You are not serious, ni da nake tunanin kafin ki fara housemanship ma”
Rasa kan zancen nashi tayi amma Kuma Sai tace “Ban ma fa da tsayaye ni ko saurayi yanzu banda shi” da mamaki kan fuskan shi ya juyo yana kallon ta, kika yi saurayi ai sana ji dalili. Batun tsayaye Kuma, who have i been waiting for?” Sai da notin jikin ta ya kunce baki daya jin kalaman nashi. Bai tsaya la’akari da yanayin da ta shiga ba ya cigaba da cewa “Daman na dade da sanin am alone on this. Kin sani sarai fushi nake dake Amma ko Hakuri kika gaza bani” ta gane in da zancen nashi ya dosa, in akwai abinda ta tsana taso dashi don haka tace “Am sorry to, nasani ban kyauta ba” da Kai ya amsa mata Sai Kuma yace “am not getting any younger, abokaina ba Wanda bai yi aure ba, sun min tsiya har sun gaji, tun abun bai damuna har ya fara. But now tunda you are here, ba Zaki koma Damaturu ba Sai naje wurin Abbah, nd rana kawai za a sa”
Mamaki biyu ya hade mata “Abban zai amince ne?”
“Ai ya dade da bani ke, kuma har gobe alkawarin mu na nan dashi. Saura ke”
“You never told me anything about it” dariya yayi “In Zaki ma kanki adalci Sai na ce wani abu? Shin action ina basu nuna Miki komai ba? Ba abinda bki sani ba so I don’t have any more times to waste” shiru tayi, tana hesitating abinda za ta fada mishi. Can dai ta fuske “ba abinda ba ka sani a kaina ba Ya Umar, why do you still want to marry me?” Murmushi yayi mai ciwo “Waya gaya miki soyayya tana ba mutum zabi? Halan baki taba shiga cikin ta ba? Akwai ta da daci, irin dacin da ba ka iya tauna haka Kuma in taso Zaki you can’t resist it. Sannan ban so ki Kara irin tunanin nan, ban lamunce Miki ba. Ko ba don ke ba, Ummi za ta iya sani yin komai in mata. In Baki manta ba, na taba Baki labarin abinda na aika ta a garin Kano, na yima wata yarinya fyade. A wannan lokacin hatta mahaifiya ta, ta juya min baya. Sai Ummi, ita ta jawo ni ta nuna min kuskure na, da kuma yanda ya kamata in bi dashi. Ita ta ceto ni daga cikin kangin wahalan da na shiga ta Kuma nuna min madaidaiciyan hanya. Ko wannan kadai ya isa in aure ki Suhaima balle Kuma ke kadai ce macen da zuciyata take muradi a kullum. Tabbas nayi takaicin rabuwan da muka yi a baya, da Kuma irin rayuwa da kika jefa kanki bayan nan. Amma na dauki hakan daga cikin kaddara na, abinda na yima yarinyar nan kuwa shike bibiyata. Hakan na daga cikin dalilin abinda ya same ki a ajeyari. Allah ya yafe mana baki daya” da Ameen ta amsa cikin kankanuwar murya. Tabbas, rayuwa kowa da irin tashi jarrabawan, ita kam irin nata kenan Sai dai tana mai gode ma Ubangiji da ya kawo mata yusrah a cikin dukkan tsanani.
Gidan Yan uwan su Hajja ya kaita a Kano, kullum Sai yazo ya duba ta yaji ko tana bukatan wani Abu. Bai so da aikin gaggawa ya Kira shi Abuja, dole ya tafi ya bar ta, dan ma yasan unda ya Kai ta bai da matsalan wani tunani, domin ya San za a mata duk wani abinda ake bukata.1