MAFARI CHAPTER 2 BY UMMU AZAMM

 MAFARI CHAPTER 2 BY UMMU AZAMM

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yakaka yakaka ,” da sauri yakaka wacce ta maida hankalin ta gaba ɗaya ga mutanen da suke kai kawo a wurin tana nazarin su,”cikin ranta tana hango musu irin rayuwar rashin sakewar da zasu yi ita da ƙanwar ta a cikin waɗannan ɗaruruwan mutanen da basu taɓa sanin koh ɗaya daga cikin su ba ,sanin da tayi su ɗin ba mutane ne waɗan da suka saba da shiga cikin jama’a ba , hasalima su ko a garin su a ƙebe da su da mahaifiyar suke , basa shiga cikin taron jama’a saboda wasu dalilai ,”+

Da sauri ta juya gami da miƙewa tsaye hankali a tashe take duban yagana wacce ta ƙaraso gaban ta yanzu tana ta haki a sakamakon ɗan gudun da tayi ,” yagana lafiya ta furta hakan hannun ta ɗaya dafe da kirjin ta ?

Lafiya lau yakaka Albishirin ku , ?

Da sauri falmata wacce ita ma ta miƙe tsaye ,”

Da sauri kuma cikin zumiɗi tace goro ? ta zarce da cewa…kin ga maman mu ne ?2

Ɗan kallon ta da gefen ido yagana tayi cikin ran ta kuwa tausayin su ne ya kawo mata ,! ,” Falmata kin manta ni ban san mama ba ?,”ta ɗora da sake faɗaɗa fara’ar ta tace ,”wai yau gwamna ne zai zo wannan sansanin , Yakaka-falmata mu yau mun shigo maiduguri a sa’a ,wallahi yau zamu ga gwamna ta ƙarasa zancen tare da yin ɗan tsallen murna,”

Ɗan guntun tsaki falmata tayi ,’ kana cikin sanyi jiki ta silale tare da lalubar inda ta tashi ta sake zama tare da rafka tagumi hannu bi-biyu , sam a gareta wannan ba Albishir ba ne ,” toh ita ina ruwan ta da wani ganin gwamna ? Tukun da wanne idanun zata ga gwamnan ? Sannan koh da tana gani ma a halin da take ciki a yanzu bata jin ganin gwamna zai iya ƙarar da ita wani abu da ya shafi farin ciki da har za’a yi mata albishir a kan sa ,’ a halin yanzu jin ɗumin mahaifiyar ta tare da sauraron gwalatun maganar ta ,irin ta kurame shine kaɗai abun da zai sanya ta farin ciki ,” hawaye ne ya silalo daga gurbin idanun ta sakamakon amsa kuwwar muryar mahaifiyar ta da taji yana shawagi da yi mata gizo a kunnuwan ta ,”6

Da ɗan guntun murmushi ɗauke akan fuskar yakaka ta koma ta zauna ita ma ,” kai yagana saboda haka ne kike ta ihun ƙira na har kika tsinka min zuciya ?

Ɗan yaƙe yagana tayi ganin yadda ya da ƙanwar suka gwale ta ,” cikin ranta tana cewe ku ai daman alamu sun nuna ba’a yi muku gwaninta2

Yakaka ni kam ki kaini banɗaki fitsari nake ji kuma fa har yanzu ba mu yi sallar azhar ba har ga shi kamar kunnuwa na suna jiyo kiran sallar la’asar ,”

Da sauri yakaka ta sake miƙewa lokaci guda tana kai duban ta ga yagana wacce tsabar murna ta gaza tsayuwa guri guda ,” yagana inane banɗakin ne ?

Ɗan diri-diri yagana tayi domin ita har ga Allah ta ma manta ina aka gwada mata banɗakin yake ,”saboda tsabar ɗoki ,” amma ganin wani mutum ya fito daga wani ɗan ɗaki da yake daura da ɗakin da suka fara cin karo da shi a wurin (office ɗin mutumin nan ) hannun sa riƙe da buta ga alama kama ruwa yayi , hakan yasa yagana tayi nuni da wurin ta ɗora da faɗin ,’ Kamar cewa aka yi nan baya haka yake koh ,?

Bin inda ta nuna da ɗan yatsanta manuniya yakaka tayi ,”cikin shakku take kallon inda yagana ke gwada mata ,” domin dai ɗakin da yake gefe da ɗakin (office) ɗin mutumin nan da yayi musu korar kare take nunawa ,”

Yagana nan baya kika ce kuma gashi kina nuna gaba ? Anya kuwa can ne banɗakin ?

Yakaka kina gani dai mutum ya fito daga banɗakin hannun sa riƙe da buta kin dai gan shi ai koh ?,”

Toh muje falmata ,” yakaka ta furta hakan dai-dai lokacin da take kamo hannun falmatan suka jera har bakin barandar ,” mu karasa bakin kofar sai na jira ki ,”

Ɗan turus yakaka tayi lokacin da falmata ta ce toh ina ruwan da zan yi amfani da shi yakaka ?

Bari na tambayo matan can inda ake ɗibar ruwa , ta furta hakan lokacin da take mayar da kallon ta kan wasu gungun matan da suke tsaitsaye hannuwan su riƙe da wasu manyan farantai irin na rabawa jama’ar gidan biki abinci ,

Toh ni zan shiga dan gaskiya a matse nake yakaka idan kin kawo ruwan ki ajiyemin a bakin kofar ,” falmata ke furta hakan a lokacin da take laluban ƙyauren kofar ,” ɗan bin ta da kallo yakaka tayi cikin ran ta fal tausayi da ƙaunar ƙanwar ta ke ƙaraƙaina ,”

STORY CONTINUES BELOW

falmata koh na kama ki mu shiga tare saboda koh banɗakin bashi da kyau sosai ,” ?

Yakaka zan kula da kaina ki kawo min ruwan da sauri dan Allah kar wasu su shigo kaina ,” falmata ta furta hakan a lokacin da ta tura kofar ,”

Da sassarfa yakaka ta juya ta dumfari matan nan cikin ranta tana jinjina irin karfin zuciyar falmata da kuma yadda a koyaushe take boye tsaraicin ta sosai ,bata taɓa ganin mutum a shekarun falmata da yake da kunya tare da suturce jikin sa irin ta ba ,” tun falmata na da kananun shekarun da yakamata a dunga kula da ita irin su wanka ,tsarki da sauran su ,” ita bata yadda , sai dai tayi da kan ta duk kuwa da naƙasar da take tare da ita ,” tun mahaifiyar su na dukan falmatan idan taƙi yadda tayi mata wanka ,” har ta haƙura ta kyale ta .

********

Da lalube take bin bangon banɗakin tana shaƙar wani daddaɗan kamshin da yake game da wurin ,tsam ta tsaya lokacin da ta ji ƙafar ta da koh takalmu babu ta sauka akan wani lallausan abu ,”kamar shimfiɗa ? Da sauri ta ɗan janye ƙafar ta , cikin ranta tana tunanin toh shi banɗakin birni haka yake da laushi kamar anyi shimfiɗa ?1

Koh da yake ance gidan gwamnati muke ,zata iya yiwuwa ma ayi shimfiɗar a banɗakin dan jin dadi ,” Fitsarin da ya sake mintsilin marar ta shi ya sa ba shiri ta ɗan ƙara gaba kaɗan ta sunkuya da nufin tsugunnawa lokacin da taji kan ta yayi karo da wani abun da bata tantance ko menene ba ,” ɗan shafa goshin ta tayi lokacin da ta fara sauke larurar ta ,’cikin ranta tana mitar su mutanen birni sai a bar su yanzu me ya kawo tarkace cikin banɗaki ?

Ji tayi ana ƙokarin turo kofar da saurin ta tayi gyaran murya cikin siririyar muryar ta tace ” a dakata akwai mutum ,”4

Turus yayi sakamakon jin muryar mace da yayi a cikin office ɗin sa ,” waiwayawa yayi ya dubi ɗayan saurayin da suke tare da basu wuce sa’o’in juna ba yace ,” suleiman ko kaji kamar muryar mutum a cikin office ɗin nan yana dakatar da ni ? ,” eh hamza naji mana muryar mace ba ,? “wanda aka kira da suleiman ke furta hakan fuskar sa ɗauke da ɗan siririn murmushin da ya yi kyau akan madaidaiciyar fuskar sa ,”1

Ba tare da jinkiri ba hamza ya murɗa hannun kƴauren gami da danna kan sa ciki”

Jikinta babu inda baya rawa a saboda duk ta riga ta gama jin zantukan su , cikin office nake ba banɗaki ba toh inane office ɗin ? kar dai wani wuri ne na musamman wanda bai da alaƙa da banɗaki ni falmata na shiga uku yau ,” shine kalaman da suke ta maimaituwa a cikin ranta lokaci guda kuma tana gyara zaman zanin ta da rigar ta har ma da adikon da ke kan ta bayan ta miƙe tsaye ,”

Ware idanun sa sosai yayi yana kallon ta tamkar dai yaga sabuwar halitta ,tun daga sama har ƙasa , wata irin zabura yayi ya jaa baya sakamakon ganin ruwan da yake kwance male-male akan tattausan shuɗin kafet ( Carpet ) ɗin ofishin daga gefen kafafun ta ,

tattare fatar goshin sa yayi tare da ƙanƙance idanun sa a lokacin da tunanin sa tare da abun da yake gani suka tabbatar masa da abun da ta aikata masa a office ɗin sa da dazu-ɗazun nan masu shara suka share kowanne lungu da saƙo tare da goge shi haɗi da feshe shi da turare a saboda manyan ɓakin da suke tafe,3

Da gudu-gudu ta ƙaraso wurin hannun ta rike da zundumemiyar gorar ruwa wacce koh murfi babu , a cike taf da ruwa har yana ɗiga ,” ɗan satar kallon saurayin da ta tadda a bakin kofar banɗakin tayi ,” da sauri ta ɗauke kan ta sakamakon haɗa idanu da suka yi ta ga yana bin ta da wani kallon da yake nuna alamun kƴamata ,

Cikin sanyin murya da gurbatatciyar hausar ta tace kayi hakuri yanzu zata fito ɗan ƙwanƙwasa kofar tayi ,” falmata ga ruwan kiyi sauri ki fito akwai mai jira ,” yakaka ke furta hakan ,”1

Jin ihun fashewar kukan falmata ya sanya ba shiri yakaka ta danna kanta cikin wajen da suke zaton banɗaki ne ,”

Suman tsaye tayi lokacin da tayi arba da kyakyawan ofishin da yake tashin kamshi ,’ hasaso abun da ƙanwar ta ta aikata a ofishin ya sanya ta jin numfashin ta na mata wuyar shaƙa .1

STORY CONTINUES BELOW

Muryar sa ta dawo da ita cikin hankalin ta wanda a farko bata lura da wanzuwar sa ba ma a wurin

Banza ƴar ƙauye dakikiya , dan ke dabba ce zaki shigo office kiyi min fitsari akan Carpet , ? Ke mahaukaciyar ina ce ? Koh a can ƙauyen ku kin taɓa cin karo da banɗaki da irin wannan tsarin ?

Cikin razana yakaka ta maida duban ta ga falmata , ganin ƙanwar ta ɗurkushe dafe da kumatun ta duka biyu ya sanya ba shiri ta saki robar ruwan , nan kuwa take ruwan ya tuntsure ya fara malala a wajen , amma koh ta kan ruwan yakaka bata bi ba ta karasa ga falmata wacce take ta shishiƙar kuka ta ɗago ta tare da rungumo ta baki ɗaya zuwa cikin jikin ta .

Falmata meye ya miki ? Dukan ki yayi me ya same ki ? Waɗan nan sune tambayoyin da yakaka take ta faman furta su ga falmata,”

Ɗagowa tayi tare da falmatan da ta kama jikin rigar yakakan ta maƙalƙale kamar zata koma cikin ta saboda tsabar tsoro da zafin marukan da ta sha , wanda tun da take ba’a taɓa yi mata makamanta su ba ,” sai shishiƙar kuka take ta kasa buɗe baki ta bawa yakaka amsoshin tambayoyin da take jero mata, ita burin ta ɗaya kawai su bar cikin wurin da aka kira da offishi ,”

Da matsanancin bacin rai yakaka ta ɗago idanun ta ta sauke akan fuskar sa wanda yayi kicin-kicin da ita kamar zai kurma ihu hannun sa harɗe a kirjin sa yana ɗosane daga baki-bakin kofar da alama baki ɗaya ma kyamar offishin yake ji a yanzu ,”

Sauke idanun ta tayi ba domin ta ji raguwar bacin ran da ta tsinci kan ta aciki ba a dalilin fahimtar da tayi ya dokar mata kanwa sai dan wani girma tare da kwarjini da ta ga ya yi mata , gefe ɗaya kuma zuciyar ta na tunasar da ita tare da girmama mata girman laifin da kanwar ta ta aikata da ya sa har wannan gabjejen ƙaton ya mare ta.

Ka-kayi hakuri dan Allah bamu sani ba ne , ‘ shine kalmar da yakaka ta furta a dai-dai lokacin da ƙara taku biyu cikin son ficewa daga offishin ,

Wani sabon bacin rai ne ya taso masa ganin yadda falmata ta wani ƙwaƙume a jikin yakakan ta ƙi ko da duban sa bare ta bashi hakuri duk kuwa da cewa ita ce mai ɗauke da kaso chasa’in cikin ɗari na girman laifin ,

Ganin bai motsa ba bare yayi magana ya sa yakaka tayi zaton koh ya haƙura ne ,’ dan haka ta saƙalo hannun falmata suka fara taku da shirin barin wajen , sun zo dai-dai ficewa daga offishin

Cikin bazata ta ji ya fizgo wuyan rigar falmata ta baya da nan take rigar ta bada sautin ɓarr alamun ɓarkewa , wurgi da ita yayi cikin fitsarin ta faɗa ciki ragwaf ,

Mahaukaciya waye zaki bar wa aikin goge fitsarin da kika yi min ? Sunkuya maza ki goge shi tas idan ma kuma zuƙewa zaki yi da bakin ki ki maida abun ki inda ya fito ya rage naki , bukata ta kawai kar na ga damshi ,”1

Ke ma kuma ya juya ga yakaka wacce fuskar ta tayi jawur , tare da wani irin mabayyanin bacin rai da har ya sa laɓɓan bakin ta karkarwa , ki sunkuya ki goge ruwan da kika tuttular a nan kafin na kira sojoji su baku horo ,( ya tsora ta su )

Ai kuwa koh dakika ɗaya ba’a ƙara ba falmata ta tattara fiye da rabin zanin ta tare da sanya hannayen ta duk biyu tana laluben daga inda ta fi jin damshin fitsarin ta sanya zanen ta tana guza gurin tare da gogewa da dukkanin ƙarfin ta , idanun ta suna zubar kwallar buguwar da raunin ƙafar ta yayi dalilin wurgi da ita da aka yi , “

Da gudu yakaka ta karaso ta sanya hannayen ta biyu ta ɗauke hannun falmatan , ” falmata ki bari zaki yaga zanen ki bari na goge ,” ba tare da jinkirin kome ba ta warware ɗankwalin kan ta , ” tare da sanya guiwar ta a ƙasa ta fara goge wurin ,” lokaci guda hawayen da suka taru cikin gurbin idanun ta suka fara sauka , “

Yakaka zan iya gogewa nima dai-dai lokacin da ta kai hannun ta tana lalubar jikin yakakan , ” zan iya… Sauran kalmomin bakin ta suka maƙale lokacin da hannuwan ta suka sauka akan lallausan yala-yalan gashin ƴar uwar ta, Yakaka ina ɗankwalin ki ? A gaban namiji kike zaune babu rufin kai ? Kwance ɗankwalin kan ta tayi lokaci guda ta rufawa yakakan a bisa kan ta , cikin sauri kuma ta sake tattara bakin zanen ta tare da cigaba da goge kafet ɗin tun karfin ta ,

STORY CONTINUES BELOW

Ji yayi idanun sa na son zowa da ruwa , baya raba ɗaya biyu tausayin su ne ya mamaye ransa , sanin da ya yi yana daga cikin mutane masu raunin zuciya ,” a hankali ya fara taku har ya ƙaraso cikin office ɗin ,”ba tare da ya dubi fuskar hamza ba ya ce kai ku tashi haka ku tafi abun ku ya isa , nan gaba kuma ku dunga lura da wurare kun ji koh ?

Da sauri yakaka take gyaɗa kai lokaci guda kuma ta fara yi masa godiya ,” ɗan gyaɗa kan sa yayi idanun sa yana kan fuskar falma da shatin marin da ta sha ya kwanta rudu-rudu .

Kamo hannun falmata tayi ta ɗago ta lokaci guda kuma ta zare ɗankwalin falmata daga kan ta tare da rufa mata shi daga kan ta zuwa kafaɗun ta,( da yake ɗankwalin na da girma kaɗan )

Yakaka ke da me zaki rufe kai ? Ba tare da ta jira amsar yakakan ba ta ɗaura hannu da nufin sake cire ɗankwalin ta mayar mata ,”dafe hannun falmata yakakan tayi , idanun ta na cigaba da son taro ƙwalla saboda kumburar da taga fuskar kanwar ta yayi , ba tare da tace kome ba ta dora hannun falmatan bisa kan ta , anan falmatan taji jikakken ɗankwalin da yakaka ta ɗaura akan ta wanda ta goge wurin nan da shi ,” da sauri falmata ta buɗe baki da niyyar sake cewa wani abun ,” katse ta yakaka tayi cikin cewa mu tafi falmata ,”

Taku suka fara yi hannayen su saƙale da na juna ,” sun zo dai-dai kofar yakaka ta maida duban ta , kan sa sarƙewa idanun su yayi cikin na juna ,” kallon-kallo suka yi na ƴan dakiƙai ,’kowannen su zuciyar sa na bugawa da yanayin da take ciki , “2

A bangaren sa haushin su duka biyun ne fal a ran sa! Tare kuma da jin takaicin me ya sa suleiman bai bar shi ya hora waɗan nan gidadawan ba son ran sa ta yadda gaba baza su sake gigin yin ganganci makamancin wanda suka yi a yanzu ba , yayin da wani bangare me rangwamen rinjaye yake jin wani abu me kama da bai fa kyauta ba , musamman a yanzu da ya kalli cikin ƙwarar idanun ta masu ruwan zaiba-zaiba ,sai ya ji wannan yanayin kamar yana sake ƙarfafa acikin ran sa ,! Tsaki ya jaa a lokaci guda yana mai kau da kan sa ,

Ga yakaka kuwa ,’ lokacin da take kallon ƙwarar idanun sa baƙar shaida take yi masa tare da jin tsanar sa tana mamaye baki ɗayan zuciyar ta tana jin shine mutum na farko da ta fara tsana a cikin rayuwar ta , sakamakon rashin tausayi ƙarara da ya nuna a gare su uwa uba , shi ɗin ne mutum na farko da ya taɓa lafiyar ƙanwar ta abar ƙaunar ta akan kuskuren da ta aikata shi cikin rashin sani ,ba tare da ya dubi naƙasar da ke tare da ita ba ,” ɗauke kan ta tayi lokacin da suke sanya kafafun su domin barin ofishin ,1

Baku ji ba ,” waiwayowa yakaka tayi lokaci guda tana me jin faɗuwar gaba ,” a hankali ya ƙaraso hannun sa a aljihu , zare hannun sa yayi daga aljihun ya fiddo da sabuwar naira dubu ɗaya ,” ungo ku sayi hijabi ku dunga sanyawa ,” ganin basu ƙarba ba ya sanya yayi ƙasa da hannun sa dai-dai hannun falmata ya taɓa hannun nata da kuɗin cikin buɗe muryar sa yace ,”

Ƙarbi mana ,’ duk da cewa falmatan ba gani take ba hakan bai hana ta juya fuskar ta inda take jin hucin numfashin yakaka ba ,” da alamun neman izni bisa fuskar ta ,”

Mungode Allah ya saka da Alkhairi amma baza mu karbi kuɗin ka ba a wurin Allah muke neman taimako ta hannun gwamnati muna tunanin gwamnati ke da Alhakin ɗaukar nawin mu ,? Dan haka baza mu ƙarbi kudin ka ba mun gode sosai ,” cewar yakaka daga haka ta jaa hannun falmata suka ƙarasa barin wajen.

Ɗan murmushi suleiman yayi lokacin da yake bin bayan su da kallo , lokaci guda yana jin tausayin su yana ratsa shi , gefe guda na ran shi ji yayi kyakyawar tarbiyyar da ya ga alamun ta a tare da su ta burge shi , juyawar sa yayi bayan ya maida kuɗin sa aljihu ,”

Amma wallahi hamza baka kyautawa a wasu lokutan ,abun da kayi ga waɗan nan yaran sam bai kamata ba , baka ganin ƙauyawa ne ? Ya kamata ka dunga rage zafin zuciya tare da tausayawa na ƙasa da kai Dan Allah .

Mts toh uba na idan ka gama min faɗan sai ka fita ka samo Cleaner ya zo ya goge wurin tun da ka sallami masu ɗauke da alhakin gyaran kaji koh waliyyin Allah ?

STORY CONTINUES BELOW

Yakaka , Falmata wanka kuka yi ne naga jikin ku du a jiƙe haka ? Falmata meya ya same ki haka fuskar ki a kumbure faɗuwa kika yi a banɗakin ?

Ganin sun wuce basu tanka mata ba ya sa yagana bin bayan su tana me sake ƙare musu kallo daga sama har ƙasa ,” a ranta kuwa ta fara jin haushin irin halayyar da suke gwada mata a wasu lokutan ,’ musamman ma dai falmata ,2

Yagana meyasa kike yin ƙarya ? Tun muna yara maman mu ta nusar da mu rashin kyaun faɗar zancen da ba gaskiya ba ,meyasa kika ce mana can wurin banɗaki ne alhalin kin san ba haka bane ? Dubi jikina dubi jikin falmata kuma ki dubi fuskar ta ? Duk sanadin kin faɗa mana zancen da ba gaskiya bane kika jawo mana wannan masifar ya zaki ji idan mu ne muka tura ki cikin haɗari irin haka ,?

Cikin nadama yagana take kallon fuskar yakaka wacce take bayyana tsantsar bacin rai a lokacin da take sanya sauran guntun ruwan da ta ɗibo tana wankewa falmata jikin zanin ta ,”

Kuyi hakuri yakaka na ɗauka banɗaki ne ganin wani mutum ya fito daga ɗakin yana gyara wondon sa da buta riƙe a hannun sa ,

A fusace falmata ta katse ta wacce ta zo har wuya da bacin ran yagana domin ita ce ainahin sanadin faruwar kome ,” amma ai yagana cewa kika da farko an gwada miki can wurin ne banɗakin ? Meyasa kike haka tun farkon fara tafiyar mu tare zantukan ki dayawa ba gaskiƴa kike faɗa ba, haka kika ce mana kin san hanyar maiduguri ? Ba domin Allah ya haɗa mu da mutanen dajin nan ba(fulanin da suka taimake su ) da ba mu san halin da zamu shiga ba ,” yagana yana da kyau mutum ya dunga faɗin gaskiya kome wuyan ta .

Cikin takaici yagana take kallon falmata wacce take daga zaune idanun ta suna kallon gefe ,” tayaya za’a yi ƴar karamar yarinyar da ta girmewa , ta zauna tana gaya mata magana son ran ta ? Tana yi mata tsawa da ihu irin haka kuma ƙarin abun takaicin ma makauniya ce miskiniya ,”

Dakata falmata daga yau sai yau ni ba sa’ar ki bace dan haka kar ki sake cewa zaki min faɗa da tsawa ,” meyasa ku da kuka shiga wajen kuka ga ba banɗakin bane ba ku fito ba ,? Koh kuwa ba tare muka zo wurin ba ɗazun nan ? Da dan kawai nayi kuskure zaku hau kaina da faɗa yayar ki tana min ke ma kuma kice zaki min kamar ku kuka kawo ni garin ?

Cikin sanyin jiki yakaka ta bi bayan yagana da kallo wacce bayan ta gama mayar musu da magana ta kaɗa kan ta ta bar wajen ba tare da ta sake ce musu ƙala ba , ta koma nesa da su ta zauna , alamu sun nuna taji haushin faɗa mata laifin ta da suka yi ,

Wanda ita kuma yakaka sam hakan bai mata daɗi ko babu kome cikin kwanaki biyun da suka yi tare da yagana taji daɗin samun ta a matsayin ƙawar da suka shigo sabuwar rayuwar su a tare , kuma ƙwarai yagana tana kokari wurin kyautata musu musamman ma dai falmata ,” toh sai dai har ga Allah ita bata son hallayar da ta lura yagana ta na da ita na ƙarya , ba dan kome tayi mata magana ba sai dan tana son yagana ta bar hallayar dan ba hallaya bace mai kyau , duk da haka cikin ran ta ta ƙudurci aniyar bata hakuri tun da ta ga tayi fushi, sam ita baza ta so rabuwar su ba ,ƙwarai take bukatar ƙawa cikin rayuwar ta a yanzu wanda a tun tashin ta bata damu da ƙawaye ba , falmata ita ce ƙawar ta abokiyar wasan ta , amma a yanzu da girma ya hau kan ta ya zama dole ta nemi wata ƙawar bayan falmata da zata dunga taya ta koh da da shawarwari ne domin inganta rayuwar falmatan .

ƙamshin abincin ne ya daki hancin su da ya sa ba shiri yakaka ta bi manyan farantan da aka wuce da su da kallo nan take yawun bakin ta ya tsinke ganin shinkafar da aka wadata kan ta da baƙar miyar da tashin farko ba za’a tantance jar miya ce koh kuwa wacce irin miya bace , amma da yake cikin su ya jima rabon sa da abinci sai abincin yayi kyau matuƙa a idon yakaka ,”

Yakaka ƙamshin abinci nake ji ? Muje mu ci mana koh ba namu bane ? Falmata ta ƙarasa zance tare da haɗiyar yawun da kamshin abincin nan ya sanya shi tsinkewa ,”

Wucewa aka yi da abincin inaga rabawa ake dan naga gashi sai kaiwa ake wuri-wuri ,” inaga mu ɗan jira za’a zo kan mu ,”

Miƙewa tsaye yagana tayi tare da ƙarasawa bakin kofar ɗakin da ɗazu ta shiga tayi tambaya wanda yanzu ta ga an shiga da farantan abinci huɗu ,”

Dogarewa tayi daga bakin ƙofar tana ganin yadda matan nan kusan su arba’in da ƴaƴan su ,suka tasamman farantan abincin nan huɗu haiƙan da suke tashin tiririn zafi .

Hannu baka hannun ƙwarya suke auna abincin nan zuwa cikin bakunan su yayin da ƴaƴan su waɗan da wasun su basu wuce ƴan shekaru biyu ba zuwa ƙasa , su ma ba’a bar su a baya ba, kokawa suke da tiren abincin nan wasun su hannu bi-biyu suke jefawa cikin tiren basa koh nuna alamun jin zafin abincin , na bakin su yana komawa ciki sakamakon ƙona musu harcen da abincin ya ke ,

Cikin mintocin da suke ƙasa da biyar babu abincin nan babu alamun sa tamkar dai gonar hatsin da mayunwatan tsuntsaye suka sauka a kai suka tashi , haka kan farantan nan suke babu koh ƙwarar shinkafa ɗai , sai tashin tiririn da har yanzu da suka kammala cin abincin bai kai ga hucewa ba , ƴaƴan su suna ta sanya harce suna tanɗar jikin faranti tamkar zasu haɗa da farantin su lanƙwame .1

Sauke ajiyar zuci yagana tayi lokacin da suka haɗa ido huɗu da matar da ta yi mata kwatancen banɗaki a ɗazu “tana ta faman tanɗar yatsun hannun ta lungu da sako tana zura harshe tana zaƙulo duk wata guntuwar miyar da ta rage mata a hannu ,” yarinya ke ba anan za ki ci abinci ba ki tafi ta can bayan tantunan da suke farfajiya anan ƴan mata sa’o’in ki suke kiyi sauri ki tafi kar a cinye a bar ki , cewar matar nan da yanzu ta kammala suɗe hannun nata ta goge hannun akan ta .

Ba tare da tace kome ba ta juya gami da kai hangen ta ga harabar wajen can ta hango masu rabon abincin nan sun nufi manyan tantuna biyun da suke haɗe da junan su daga gefe ,” da sauri ta ɗiro daga kan dakalin barandar har ta ɗaga kafafun tayi taku biyu sai ta waiwaya karaf suka haɗa idanu da yakaka wacce duk ta bi ta damu da fushin yagana , hakan ya sa duk wani motsin yaganan yake kan idanun ta ,”

Yafitar su tayi da hannu lokaci guda ta buɗe murya “, Yakaka ku zo mu je mu ci abinci a can ,” ba tare da ta jira amsar su ba ta ɗaga ƙafafun ta cikin sauri ta nufi tantin da ta ga an kai abincin nan cikin ran ta cike da addu’ar Allah ya sa ba’a riga an fara ci ba .

Da sauri ta ruƙo hannun falmata da jin zancen abincin nan ya sa cikin ta ya sake yin ƙarar yunwa ,

Mu yi sauri mu je falmata !Jugum suka yi a ɗosane tsakankanin matsin ƴan mata sa’o’in su da waɗanda suka fi su , da ma ƙasa da shekarun falmata kaɗan “bayan kammala baɗakalar wawason abincin,.

Yakaka ni fa koh rabin-rabin yunwar da nake ji bata mutu ba ,wannan abincin sam bai isa ga uwar hanji na ba , me zai hana mu nemi wurin sayar da abinci mu sayi wani da kuɗin hannun mu ?2

Kiyi hakuri falmata mu jira na dare tun da kin ga yanzu la’asar yayi ,idan yaso da daren sai mu shirya salon cin abinci , tun da kin ga dai yadda muka sha gumurzun kokuwa kafin mu samu ƴan lomomin da yanzu suke cikin mu .

Toh yakaka ,Allah ya kaimu ɗaren .

Cikin wani irin yanayi na tausayawa yagana take kallon yakaka wacce koh lomar abinci ɗaya bata sa cikin bakin ta ba , domin duk kokuwar da ta sha idan ta ɗebo abincin maimakon ta sanya a bakin ta , lalubar hannun ƙanwar ta take ta zuba mata ,

Cikin neman son su shirya bayan ƴar hatsaniyar da ta shiga tsakanin su ,”yakaka ta sakarwa yagana murmushi tare da riƙo hannun ta , mun gode yagana ba domin kin kira mu ba ,”da baza mu samu abincin ba”

Murmushi yagana ta mayar mata ,”babu kome yakaka mun riga mun zama ƴan uwa “

Waiwayawa tayi ga wata budurwar da take zaune kusa da ita “ta ɗuƙufa sosai wurin soka allura da zarewa a jikin hular da take ɗinkawa “,

Dan Allah kawata koh zaki gwada mana banɗaki muna so muyi sallah? Cewar yagana

Ba tare da ta ɗago daga yin ɗinkin da take ba tace ,idan kuka fita kuyi hannun ku na dama ku miƙe sosai zaku tarar da banɗaki a jere amma ku kula hudu daga cikin takwas ɗin basu da kyau duk sun tsage sun farfashe ba’a amfani da su dan gudun su rufta da mutum .

Godiya sosai suka yi mata dai-dai lokacin da suke miƙewa .

Da ido yakaka take bin farfajiyar da take dauke da banɗakunan da kallo cikin wani irin yanayi na tsantsar kyankami domin duk da kasancewar su mutanen ƙauye ,” suna da wadatar tsafta basa barin muhallin su cikin dagwalon ƙazanta ,”

Cikin ɗaukewar numfashi falmata tace kai yakaka wannan banɗaki da wari yake da alama babu wadatuwar tsafta , ni dai gwada min inda zan yi alwalar .

Koh kafin ta buɗe baki “yagana ta karaso wurin hannun ta riƙe da manyan gorar ruwan roba wanda mafi akasarin mutanen wurin suke amfani da ita a madadin buta .

Itama turus tayi ganin tsimi-tsimin “bahaya” a farfajiyar wurin wasu an turbuɗe da ƙasa wasu kuwa muraran suke a sarari ƙudaje tare da sauran ƙwari suna sukuwa a kai .

Da sauri ta kawar da kai tare da tsirtar da wani mugun yawun da taji ya taru mata a baki tace ,”yakaka anya wurin nan kuwa ya dace da wajen alwala ? Gaskiya ku zo mu koma

Bata gama rufe baki ba ,”taga wata mata da goyon ƴar ta,  ta zo tayi ƴar tsallaƙe ta tsallake tarin kazantar dake wurin tare da shiga ɗaya daga cikin banɗakin wajen ,”cikin ƴan dakikai kuma wata mace ta fito daga ɗayan banɗakin .

Yagana babu yadda zamu yi kin ga kowa dake nan wurin da nan ɗin suke amfani , dan haka muma dole mu bi ayari .

Tana rufe baki ta saki hannun falmata gami da tattare zanen ta , ta tsallaƙa cikin dauke numfashi ta nufi bandakin ,”tare da cewa falmata ki jira ni anan kar ki motsa “,

Bayan sun idar da sallolin da ke kan su da suka yi ta a ɗanɗaryar ƙasar kan baranda ,cikin rashin wadatuwar suturar da zasu suturce jikin su kamar yadda ya kamata a yayin sallar ,” duk da daman ba wani sani suke da shi sosai game da ibadar ba .

Tsumu suka yi kowaccen su cikin taɗin zuci ,”

Ƙarar jiniya da tayi musu kama da ta motar sojojin nan da suka ji ya dumfaro farfajiyar masaukin nasu ,shi ya firgitar da su suka miƙe ba shiri cikin ransu kuwa cike da taraddadin da me jiniyar ta sake zuwa musu a karo na biyu cikin ƙasa da sa’o’in su biyar a cikin birnin na maiduguri ?

STORY CONTINUES BELOW

Sai dai sabanin tunanin su a yanzu ba daga motar sojojin da suke zato bane ƙarar jiniyar take fitowa ba ,” daga wasu jerun gwanon manyan bakaƙen motoci masu daukar ido tare da kyallin sabuntar dake nuni da tsadar su , karar take fitowa “,

Buɗe baki da hanci yakaka,da yagana suka yi suna bin motocin da kallo waɗanda har matukan su suka riga suka sama masu matsaya ,”

Sai dai basu kai ga sauke numfashin farin cikin da suka riƙe na ganin cewa ba waɗannan sojojin da ganin su ba alheri bane a wurin su ,suka dawo ba , idanun su suka yi arangama da jerin gwanon motocin sojojin daga baya da ma na wasu jami’an tsaron masu mabanbantan kayan sawa wadanda basu kai ga rarrabewa da banbancin su da sojojin ba  ,”

Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoron da ya cika mata zuciya fal ! Lalubar hannun ta falmata tayi cikin maƙyarkyatar murya take cewa ” yakaka, yagana kun ga abun da nake faɗa muku koh ? Ni daman nasan da kyar idan ba gidan bayar da horo sojojin nan suka kawo mu ba ,” ai tun daga horon yunwar da aka fara yi mana ɗazu ya ci ace kun fahimci irin kurkukun da muka shigo ,” kawai ban faɗa miki bane yakaka , amma tun sanya kafafuna cikin garin maiduguri naji ajikina babu alheri cikin sa , naji cewa akwai wani babban al’amari marar daɗi da zai same mu a cikin sa ,”1

Kuwwar mutane tare da dararrakin su da ya cika musu kunnuwa shi ya katse surutun da falmata take yi cikin ɗimaucewa ta koma cewa “menene yakaka ? Harbi ake ? Kashe mu muma zasu yi ? Toh ku zo mu gudu mana tsayuwar me muke ?

Ki nutsu falmata ! Yagana ta furta “cikin ɗan ɗaga murya” a sakamakon surutun da hargowar da falmatan take yi musu cikin ruɗewa ya hana ta , ta gano abun da take hasashe , ganin yadda taga fuskokin kowa a wurin ya yalwatu da fara ,”ta ko’ina bullowa jama’a suke suna tururuwa a harabar wajen ,”

Da gudu yagana ta dira daga kan baranda kafin ta waiwayo cikin tsantsar farin cikin da kamar anyi mata babban bisharara ,”yakaka falmata ga gwamna wallahi gwamna ne yazo ,gwamnan jahar borno “, kuyi sauri ku taho kar wajen tsayuwa ya cika ,” daga haka ta kara da gudu kamar yadda taga sauran jama’a maza da mata suna kwasar gudun zuwa gaban dandamalin da jami’an tsaro suka kewaye ta ko’ina wanda da alama anan gwamnan yake tsaye .

Saƙare suka yi a tsaye  cikin rashin sanin takamaimai halin da suke ciki na farin ciki koh saɓanin hakan , a zahiri basa jin wani farin ciki a dan saboda zuwan gwamnan musamman ma ga falmata ,” wacce ta sauke boyayyar ajiyar zuciyar samun kwanciyar hankali jin ba zuwa aka yi domin azabtar da su ba kamar yadda ta zata ,” sai dai ita bata wani farin ciki da zuwan gwamnan domin rashin sanin muhimmancin zuwan nasa .

A hankali yakaka ta fara jaan hannun falmata cikin cewa mu ma muje falmata muga gwamnan kuma muji bayanin sa kin ga duk mutane sun tafi .

Bayan gajeren bayanin da gwamnan ya gabatar musu cikin yaren su wanda duk na ban hakuri ne game da halin da suke ciki tare da yi musu alkawurwukan kyautata musu da ababen more rayuwa , sannan a karshe yayi musu albishirin tarin kayan abinci da suke tafe da shi , gidajen sauro , butoci da kuma bargunan rufuwa , ya kuma ƙara da albishirin za’a ƙara musu matakan kula da lafiyar su da sauran bukatun su na yau da kullum,

a karshe kuma ya basu dama wasu daga cikin su suka faɗi irin matsalolin da suke ciki a sansanin nasu , inda mafi yawan korafe-korafen nasu ya tafi akan ƙarancin abinci da ruwan shaa,  uwa uba da cizon da sauro da ƙwarin gurin suke musu wanda cizon sauron yake kawo musu mummunar masassarar da har take iya kaiwa ga rasa rayuka idan ya zo da ajali musamman ga mata masu ciki da kananan yara .

Bankwana yayi musu bayan da ya basu tabbacin za’a samu sauyi daga yanzu inda ya nemi da a naɗa kwamiti da shuwagabanni a tsakanin su kashi-kashi domin lura da matsalolin su .

Nan take aka shiga ihu da kalmomin yabo ga gwamna da tawagar sa har zuwa lokacin da ƙurar motocin su suka bace .

Babu laifi , ziyartar da gwamna ya kawo musu sosai ta saisaita ciwukan da suke cikin rayukan al’ummar sansanin yayin da ya haifar da farin ciki a cikin zukatan kashi tamanin na cikin ɗarin mutanen.

STORY CONTINUES BELOW

Idan aka ɗauke falmata wacce har kawo yanzu da ake kammala raba musu gidajen sauro tare da barguna, inda ake haɗa mutum biyu da gidan sauro guda bayan an damƙa musu bargunan su ɗai-ɗaya da buta ɗaya ,” dukkanin su ba’a haɗa su da juna ba ,an ware su ne daban-daban yayin da aka haɗa yagana da wannan budurwar wacce ta basu kwatancen inda banɗaki yake , yakaka kuwa da wata yarinyar mace mai yara biyu ƙanana aka haɗa ta , falmata kuma da wata mata wacce take yanayi da zaurawa ,”domin ta wuce a sata sawun ƴan mata ƙanana irin su ,”kuma ita bata da ɗa ,” babbar budurwa dai .

Babu yadda yakaka bata yi da wannan babbar budurwa da aka haɗa su da falmata akan tayi musu lamini ta bar musu ita da falmata gidan sauron idan ya so sai itama yakaka ta bar mata wajen ta ,”ma’ana suyi musanye wuri,” saboda a zahiri ta shiga tashin hankali ganin za’a raba musu wurin kwana da ƙanwar ta ,” Amma fir budurwar nan taƙi ,tace ita gaskiya baza ta iya kwana cikin gidan sauro guda tare da mai yara ba , karshe ma ta fatattaki yakaka ta kuma ce idan har ta matsa toh fa sai dai falmatan ta bita su tafi chan su ƙarata “ta bar mata gidan sauron ita ɗaya “

Da farko yakaka tayi tunanin su haƙura kawai da kwanan cikin gidan sauron su haɗu su dunga kwanan su tare, sai dai tunowa da korafe korafen da taji ɗazu sun yi da suke faɗin illar da cizon sauron yake yi da har yake iya kisa , yasa taji babu yadda zasu yi dole ta kiyaye lafiyar falmata , dan haka tana ji tana gani aka raba musu wurin kwana da ɗaki ita da ƙanwar ta .

Dare ya raba tsakiya idan banda juyi babu abun da falmata take yi gaba daya ta kasa bacci saboda tsananin takurar ta da budurwar da ake kira da “ajus” taƴi duk ta bi ta ture ta, tare da janye mata bargonta ta rufu da shi ,sakamakon sanyin damina tare da raɓa irin na tsakiyar daren yanayin damina ,”

sakamakon turo ta da ta dunga yi yasa gidan sauron nasu duk ya buɗe sauro da cinnaku masu fiffike sun samu damar shiga ciki sai faman ɗallara mata cizo suke ,”sau biyu tana yunƙurin jaan bargon ta amma sai ajus ta ɗallara mata mintsini tare da haure ta da ƙafa ,”2

Lalubawa tayi ta tashi ta zauna tayi tsumu , gefe ɗaya na zuciyar ta cike taf ! da kewar mahaifan ta da ƴan uwan ta ,”kamar yadda take sake ganin daren na yau ma kamar sauran ukun da suka wuce babu mahaifiyar ta babu mahaifin ta babu ƙannen ta ,” duk wani buri da take da shi na samun gamuwa da mahaifiyar ta da sauran ƴan uwan ta taji yana barin ran ta , wani sashi na ranta yana raɗa mata tare da bata tabbacin sun rabu kenan har abada,” fashewa tayi da kuka dai-dai lokacin da wata gwarzuwar cinnaka ta sake mallara mata cizo a dokin wuya ,”cikin zubar hawaye take tuno irin kulawar da mahaifiyar su ke basu a irin wannan yanayin na yawaitar muggan kananan kwarin damina sam bata bari su cutar da su ,”toshe kunnuwan ta tayi da hannayen ta biyu a sakamakon rugugin hadarin da taji wanda take da tabbacin ruwan sama gaf yake da tsinkewa

A hankali yakaka ta sauke ɗan jaririn mai kimanin watanni biyu zuwa uku daga kan kafaɗun ta a yadda take durƙushe cikin gidan sauron tana ta faman jijjiga shi ,”tayi niyyar kwantar da shi a gaban uwar sa wacce take bararraje , tayi wawiyar kwanciya cinyoyi duk a buɗe kai ba ɗankwali ,” cikin addu’ar Allah yasa kar ya farka domin hakika ta gaji da rainon sa tun farkon dare yake hannun ta lokacin da uwar sa ta dungura mata shi tace ta jijjiga shi yayi bacci,  ita ta gaji bacci take ji ,ta jaa ɗayan ɗan nata gaban ta suke shaƙar baccin su ,”sau uku tana ajiye shi amma daga yaji an ajiye shi baya yin minti ɗaya yake sake challara kuka ,” cikin gigin bacci da hargowa uwar sa zata ce dallah ta ɗauke sa zai hana sauran mutane bacci .1

Cikin sa’a har ta kwantar da shi bai tashi ba ,” tsurawa kofar ɗakin ido tayi tana ganin yadda walƙiya take haskawa tare da rugugin hadari nan take hankalin ta ya tashi tunowa da falmata da tayi koh a wane hali take ciki a ɗakin da take ? Ji tayi baza ta iya kwanciya ba idan bata ganta ba .1

A hankali ta ɗaga gidan sauron da suke ciki da niyyar fita dai-dai lokacin da aka yi wani tsawa da rugugin tasowar hadari da ya sa jaririn nan ya firgice tare da tsanyara kuka ,” a daburce uwar sa ta farka gami da fara cewa ke ke keh kina ina ne kika bar shi yana ta irin wannan ihun ji min ƴar banzar yarinya ,”muguwa ,cikin sanyin murya yakaka tace wallahi yanzu na ajiye shi koh kwanciya ban kai ga yi ba , kuma ma da alama kamar yunwa yake ji “, ta furta hakan cikin fatan Allah yasa uwar ta ɗauke shi ,”mts ta jaa tsaki tare da surar ɗan jaririn kamar ta suri yaro mai shekaru biyu ,” ta koma ta kwanta tare da shi tare da ciro abincin sa ta cusa mar a baki ,ɗif yayi shiru .1

STORY CONTINUES BELOW

Sauke ajiyar zuci yakaka tayi ganin uwar da ɗan sun koma bacci ,”ta siɗaɗa ta fita dai-dai lokacin da kakkarfan ruwan saman ya tsinke kamar da bakin ƙwarya ,” gudu-gudu ta tsallaka ɗayan barandar ɗakin da falmata take ,’ba tare da ta damu da duhu tare da shirun da harabar wajen ya ɗauka ba ,ga ƙarar ruwan sama ,”

Tana shiga ta fara yawata idanun ta ,” a hankali ta fara jin ƴar siririyar muryar ta tana kuka ,”ɗas-ɗas zuciyar ta ta buga tare da taruwar ƙwalla cikin gurbin idon ta,  cikin sauri ta fara taku tana kewaye gidajen sauron jama’ah tare da tsallaƙe su cikin taka tsantsan ,” tana nufar inda take jin sautin ta domin bata son yin magana kar ta tashi mutane

Cak ta tsaya da kukan jin takun sawayen ƴar uwar ta ,”yakaka ta furta cikin sanyin murya dai-dai lokacin da ta ƙaraso tare da durƙusawa a bakin “shingen”(gidan sauro) .

Ƙasa-ƙasa tace falmata meye yasa ki kuka ? Me aka miki ,” da shishiƙar kuka tace babu kome yakaka na tuno da su mama ne ,”yakaka cikin daren nan kika fito kuma ana ruwan sama ? Meyasa ?  ki koma ki kwanta dan Allah

cikin ƙura ido tare da taimakon hasken walkiya ta fahimci a dandaryar ƙasa kanwar ta take takure a zaune ,” cikin takaici ta maida duban ta ga ajus da take ajiye numfashi ɗaya bayan ɗaya tare da sake duƙunƙunewa cikin jin daɗin barcin ta ,take ta fahimci abun da yake faruwa ,”1

Zuruf ta miƙe cikin cewa ina zuwa falmata ,” bata saurari amsar falmatan ba ta fita ,

Jim kaɗan ta dawo tare da bargon ta a hannun ta zura hannu  ta miƙawa falmatan bargon,”ungo falmata buɗa shi ki kwanta akan rabi ki rufu da rabin duk da ma dai fitsarin yaron matar chan ya taɓa jiki amma ki kwanta a haka ,”

Jin falmatan tayi shiru yasa tace matsa na shinfiɗa miki kin ji ,”? Cikin rawar murya tace yakaka ke kuma ki koma ki kwanta akan me ?

Shittt ,” falmata lafiyar ki tafi min kome , bamu da kowa a yanzu daga Allah sai junan mu , menene amfani na idan har ban zamar miki garkuwa ba falmata ,”  tana furta hakan ne dai-dai lokacin da take gyara mata bargon tana shimfiɗa mata ,” kama mata tayi ta kwanta ,”

Yauwa toh bari ruwan ya ɗan tsagaita sai na koma ɗakin mu kiyi baccin ki kin ji ?

Gyaɗa mata kai tayi domin kuwa idanun ta har yaji-yaji suke mata tsabar baccin da ya cika su ,

Sauke sassanyan numfashi tayi , tare da share guntun hawayen da ya cika mata gurbin ido nisawa tayi tana tunanin ƙalubalen da suke a farkon sa yanzu wanda basu da sani akan iyakar sa ,karshen sa babu abun da yafi tsaya mata a zuci irin tausayin ƙanwar ta a yin rayuwa cikin wannan sansanin da ta lura kowa kan sa ya sani kan sa yake so “rayuwar daga ƙawri sai gwaiwa “,  zuciyoyin mutane cike take da mugunta da son kai .. Yaa Allah ga ni ga miskiniyar kanwata Allah ka taimake mu .2

               Maraɗi jamhuriyar niger 

A karo na biyar ta kama ta sauko daga kan murfin sunduƙin yin “bahaya”( Toilet- Toilette ) da yake cikin banɗakin ta ,” kai kawo ta shiga yi tare da duban agogon fuskar wayar ta “

Yau har karfe biyu da mintuna arba’in biyamuradi bai dawo ba kamar yadda ya saba fita sha biyu da rabi na dare ya kuma dawo karfe biyun dare ,”

Meye ya tsayar da shi ? Jin motsi tayi kamar an taɓa kofar sirrin da take bangaren biyamuradin wacce kuma da ita yake amfani wurin fita da shigar sa gidan a dai-dai wannan lokutan da ba wanda ya taɓa sanin yana fita daga Allah sai shi sai ita , 

Cikin sauri ta sake ɗarewa kan sunduƙin tayi ƴar ɗage ta leƙa ta ɗan siririn huɗar da aka yi ta a can saman banɗakin domin ado wanda aka liƙa kwan lantarki a jiki, sai dai a halin yanzu babu ƙwan lantarkin sai dai huɗar da ta fito sarari ake iya ganin abun da ke waje ta wurin ,

Tar ta hango shi a cikin hasken lantarkin da ya ƙawata lambun bayan ɗakunan sa ,” yana layi tare da tamɓele jikin farar rigar sa da shuɗin wandon jins ɗin sa dumu-dumu da abun da bata iya tantance shi daga inda take ,”1

Ji tayi ruwan hawaye ya silmiyo daga gurbin idanun ta da gudu sun fara tsere akan siriryar fuskar ta ,”

Wani faɗuwar ƴan bori da yayi rigijib shi yasa ta kusa zamewa ta silmiyo daga kan toilet ɗin ,  da sauri ta ɗiro cikin gudu-gudu ta bullo ɗakin ta tare da fitowa cikin parlour kai tsaye ta nufi kofa ta kama mariƙin kofar ta murɗa , zuciyar ta tana zafi tare da ingiza ta , idanun ta suna hango mata faɗuwar da abun kaunar ta yayi .1

Sai dai turus ta jaa ta tsaya lokacin ta tuno da fitar ta a wannan lokacin zuwa bangaren biyamuradi zai jawo , me zata cewa masu tsaron gidan ? Wanda ta san basu san halin da yake ciki ba , basu taba sani ba , idan kuwa har ta fita war haka dole su sani .

Hakan yana nufin fallasuwar mummunar fuskar masoyin ta , hakan yana nufin kunyatar masoyin ta , hakan yana nufin dasuwar bakin ciki cikin zuciyar uwar goyon ta , hakan yana nufin samar da wanzazjen bakin ciki cikin zuciyar uban goyon ta kuma kawun ta , hakan yana nufin tozartuwar ƴan uwan ta ,hakan kuma yana dai-dai da zubewar girma da mutuncin masarautar su baki ɗaya .

Kamar walƙiya ta juya ta koma da sassarfa ta shiga ɗakin ta gami da murza mukulli lokaci guda ta nufi gadon ta gami da fadawa rubda ciki ta sanya kanta tsakanin filo gami da fashewa da wani irin kukan da ya tuƙo tun daga karkashin zuciyar ta , kuka ne irin wanda mutum yake yi idan bakin ciki yayi masa yawa .

4

Hoooooo hoooo hooooJuyi ya sake yi a karo na barkatai bisa makeken gadon nasa na alfarma, tare da runtse idanu yana mai sake jin yadda kan sa yayi masa mugun nawi har baya iya buɗe idanun sa sosai , ɗan ƙaramin tsaki ya jaa da yayi sanadin juyowar Tafeedah wanda yake zaune bisa doguwar ƙawatatciyar kujerar da take gaba ƙadan da gadon .

Cikin takaici yake duban biyamuradi yousouf ɗin , kafin ya ɗan yi gyaran murya ! “cikin kowanne daƙiƙa ɗaya da yake wucewa yana sake nisanta ka da lokacin sauke farillah ” tafeedan ya furta kalmomin masu nuni da tunasarwa , cikin nuna halin ko in kula ga biyamuradi yousouf , wanda koh kafin tafeedah ya idasa bayanin sa ya buɗe idanun sa tarwai da jijiyoyin cikin suka yi jaa , kammala bayanin nasa ya zo dai-dai da miƙewar sa zumbur daga kan gadon .

Bai yi wani jinkiri ba ya fara taku cikin sassarfa lokaci ɗaya yana sauke idanun sa akan tagar ɗakin sa wanda hasken rana ya riga ya hudo ta tsakanin labulen .

Bayan tsawon mintoci fiye da talatin da biyamuradi youssouf ya ɗauka yana addu’a da neman gafarar mahaliccin sa bayan ya idar da sallah ,

sadda kansa ƙasa yayi yana me jin kunyar ɗago kansa ya dubi aminin nasa wanda ya tabbatar idanun sa a kafe suke a kan sa , yayin da sashi guda na zuciyar sa yana me son tuno da wani abu .

A firgice ya dago kan sa a sakamakon tunowa da yayi dawowar sa daren jiya da faduwar da yayi a harabar lambun sa wanda daga nan bai sake sanin inda yake ba a sakamakon kakkarfan baccin da yayi awon gaba da shi a wurin a yashe , da hakan baya rasa nasaba da sabuwar sumfurin dahuwar burkutun da ya sha a jiyan wanda gaba ɗaya ta hargitsa masa ƙwanya .

Aina ka tarar da ni ?

Shine kawai tambaƴar daya jefawa tafeedah bai koh kula da irin kallon da tafeedan ke jifan sa da shi ba mai cike da tarin ma’anoni .

A jefa a inda kaga yafi dacewa da kai cikin kuma irin yanayin da ka zabarwa kan ka .”amsar da tafeedah ya bashi kenan ” yana me miƙewa cikin yanayi na nuna alamun tafiya yake da niyyar yi ,”

Wani boyayyar ajiyar zuciya biyamuradi youssouf ya sauke a sakamakon fahimtar da yayi cewa tafeedah ne ya kawo sa ɗakin nasa ,”

Da misalin karfe nawa ka shigo gidan ? Su wa ka tarar a haraba ta ina nufin ma’aikata na sun yi chanji ?

Mts! Idan kasan kana gudun zubewar mutuncin ka me zai sa ka jefa kan ka cikin rayuwar da kake youssouf ,” tafeedah ya furta hakan cikin ƙufula yana me komawa ya zauna a inda ya tashi ,”

Cigaba yayi da cewa karfe uku na asubah na shigo sashin ka bayan tasowata daga wurin taron mu (meeting) ,inda masu tsaron gidan suka tabbatar min kana ciki tun farkon dare ,”

Amma abun mamaki nazo na gama neman ka ƙasa koh sama baka nan har nayi niyyar fita na sanar da masu tsaron ka , sai nayi tunanin zagayawa har cikin lanbu inda na tarar da kai kwance a ƙasa , da farko na tsorata amma daga baya na fahimci abun da ka min alkawarin ka daina sha kayi min rantsuwa da Allah akan baza ka sake sha ba ita ka sha youssof , ƙarin abun takaicin ma a cikin gidan nan , bayan ka san duk cikin ahalin gidan nan babu wanda ya taɓa sanin kana ta’amali da barasa ,” kafi kuma kowa sanin masifun da fallasuwar wannan mummunar ɗabi’ar taka zata iya jawowa a garemu baki ɗaya ,”haba youssof , haba youssof , duk cikin tarin ababen zubda mutunci da jawo tozarta ka rasa wanda zaka zaɓa sai BARASA ? Bayan kasan itace shugaba ummul’aba’isi na jaan ɗan adam ga aikata kowanne irin sabon ubangijin mu ,”

tsagaitawa yayi lokacin da yaji muryar sa ta fara karkarwa alamun gaf yake da fara kuka sakamakon ƙona masa zuciya da wannan ɗabi’ar ta abokinsa ,amininsa kuma ɗan uwan sa youssouf da ya jefa kansa a ciki tun yana da ƙarancin shekaru sosai domin shi da kan sa ba zai iya cewa ga lokacin da youssof ɗin ya fara shan barasa ba , kawai dai ya farga ya gane ne shi da kan sa a saboda kusancin da suke da shi da juna ta yadda wasu lokutan dayawa zai taradda da youssouf ɗin cikin maye ,”

STORY CONTINUES BELOW

wanda tun yana ƙaryata kan sa cewa youssouf giya yake sha ,a dalilin tsawaita bincike da yayi bai taradda alamun barasa ba a duk inda youssouf ɗin yayi bigire da kuma boye masa tare da waskewar da ya dunga yi , har dai ya zo ya yadda, kuma yayi amanna aminin sa mashayin giya ne , ya kuma tabbatar lokacin da ya bi shi har zuwa wani tsohon kuchakin gidan saida burkutu wanda yake chan tsakiyar unguwannin talakawan gari inda anan youssouf yake zuwa yayi tatul , amma baya guzurin ta .

A ranar yayi kuka har kan sa yayi ciwo ,kuma ya girgiza matuka musamman da yayi duba ga matsayin youssouf a garin na kasancewar sa ɗan sarki mai jiran gado , wanda ake sa ran watarana shi zai jagoranci dubannan al’ummar yankin ya zama shugaba a gare su abun koyi ,

Yaya hajiya umma (mahaifiyar sa) da mai martaba ,haɗi da ƴan uwan sa zasu ji a lokacin da suka farga , uwa uba yaya al’ummar gari zasu dubi lamarin yayin da labarin ya bazu ga kunnuwan su , haƙiƙa maƙiƴan sarari da na boye zasu ji daɗi suyi murna , sannan kuma da akwai yiwuwar subucewar samuwar mulkin jahar maraɗi daga hannun sa domin rashin chanchantar sa ta wannan fuskar ! Wane irin mulki ake zato ga mashayin sarki ????

Tun daga lokacin tafeedah ya nuna cikar amintakar dake tsakanin su da biyamuradi youssof ta hanyar yi masa faɗa da nasiha mai tsanani a kullum, gami da boye masa sirrin sa tare kuma da toshe duk wata hanyar da zata iya sa asirin youssof ɗin ya tonu , sosai yake koƙarin kare masa martabar sa da mutuncin sa , ta inda har ta kai yasamu nasara a wani dare shekaru biyu da suka wuce ,biyamuradi youssouf ɗin yayi masa alkawarin daga ranar ya daina shan barasa bayan fada da suka yi kacha-kacha inda tafeedah har yayi wa youssouf ɗin barazanar daina shiga sabgar sa idan har ba zai daina ta’amali da barasa ba .

Farin ciki tare da kwanciyar hankali suka wadata ga tafeedah bayan jin alkawarin da youssof yayi masa “,cikin rashin sanin tuban muzuru youssouf ɗin yayi ya kuma ninke sa a baibai domin daga ranar ya sauya lokutan shan barasar sa muddin yana cikin garin maraɗi , ta yadda ya maida tsakanin sulusin dare lokacin fitar sa ya sha abar sa , yayin da idan yana wata ƙasar koh wata jahar a duk lokacin da ya samu sarari yake zuwa ko’ina ne ya nemo barasar gargajiya da aka fi sanin ta da “BURKUTU” zazzafa ya sha iya shan sa babu abun da ya fasa .

Janye idanun sa da suka ciko da ƙwallar takaici tafeedah yayi , cikin rashin kuzari ya sake miƙe jin youssof ɗin ya rasa abun faɗa , toh me ma zai faɗa masa ? Soke hannayen sa yayi cikin wondon sa ,”ni zan shiga na gaishe da hajiya umma daga chan zan wuce ,sai kuma Allah ya kaddara saduwar mu , ina mai fatan Allah ya kiyaye ka ya baka nasara akan waɗanda zaka tunkara ,”

Daga haka ya sanya kan sa gaba da sauri youssof ɗin ya miƙe daga kan dardumar da ya idar da sallar sa ,”Jira ni nima babu abun da zan yi da wuce wanka sai mu fita tare ,” bai jira amsawar sa ba kamar yadda shima tafeedah bai tsaya domin saurarar sa ba ya sanya kai yana me ƙarasa barin katafaren ɗakin youssouf ɗin .

Yana shiryawa yana tunanin maganganun aminin sa tabbas duk wasu kalmomin da ya ɗauki shekaru yana furtawa agare shi gaskiya ne ,” kuma shima a karan kansa yana mai bakin cikin halin da ya wayi gari ya tsinci kan sa a ciki sannan yayi iyakacin kokarin sa dan ganin ya daina shan burkutu amma hakan ya gagareshi duk kuwa da addu’o’in da yake yi a koyaushe yayi sallah akan Allah ya yaye masa, amma abun kamar tiri ,

ji yake idan bai sha burkutu ba a kowacce rana , yana iya rasa numfashin sa , burkutu ta zama jinin jikin sa , mahaɗin rayuwar sa kuma abar dake samar da nutsuwa da farin ciki a rayuwar sa ( a ganin sa kenan )

Ajiye matajin hannun sa yayi bayan ya kammala taje ƙwantatciyar sumar sa wanda yake yawan yi mata saisaye luf-luf da ita ,” yayi yawo da idanun sa a ɗakin cikin son gamsuwa da bai bar wani abun sa mai muhimmanci ba ,”duk da cewa tun a daren jiya sojan dake kula da shirye-shiryen tafiyar tasa ya kammala haɗa masa kome cikin umarnin sa da yake zaune a gefe yana gwada masa abubuwan da yake bukatar tafiya da su ,”ya shirya su tsaf tare da kai su motar da aka shirya zai yi tafiya zuwa Niamey inda daga nan zasu daga zuwa Nigeria.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin takun sa na ƙasaita wanda yake bayyana cikar jarumtar sa irin na gwarzon soja , jaan tunga yayi ya tsaya “ɗan mitsitsin murmushi yayi ganin tafeedah da yayi a zaune cikin ɗaya daga cikin kujerun falon fuskar sa kadaran kadahan ya dago ya dube shi gami da miƙewa tsaye yayi gaba ,” da sauri ya bi bayan sa suka jera .

Cikin nutsuwa suka yi sallama a babban falon hajiya umma , da ya jawo hankalin siyama da merama aisha da suke zaune bisa wadatattciyar darduma suna ƙarin kumallo ,” gefe guda masu hidimar zuba musu abincin da tsaftace wurin ne suke durƙushe zaman jiran su kammala , zumbur aisha ta miƙe

Da ɗan gudu da tsalle ta ƙaraso gare su dai-dai lokacin da suke yiwa kan su mazauni akan jerun kujerun falon ,”zama tayi a gefen biyamuradi gami da ɗaura kan ta bisa kafaɗun sa “,barka da safiya hamma nah ,

nayi kewar ku sosai na same ku lafiya . ?

Shafa kan ta yayi lokaci ɗaya fuskar sa tana sake faɗaɗa da yalwatatcen murmushin da yake bayyana tsananin  ƙaunar sa ga ƙanwar tasa yace “,

lafiya lau meramar mai martaba yaya karatu ?

Yaushe kika zo ?

anyi muku hutu koh ?

Anyi hutu hamma jiya da yamma nazo .

Ɗan gyaran murya tafeedah yayi ,

Murmushi ta sake yi tana me sunne kanta a jikin hamman nata tace ,”ina kwana hamma tafeedah na same ku lafiya ,” ?

    Bazan amsa ba tunda abun ma wariyar launin fata ce ,”

    Leƙo shi tayi ta bayan biyamuradi tana ɗan murmushi tace yi hakuri hamma tafeedah kasan nayi kewar hamma na watanni uku fa ,”

    Kallo yake mata me kama da harara amma kuma fuskar sa ɗauke da sassayan murmushi wanda sai shi ya san ma’anar sa , sai kuma ita da duk lokacin da yayi mata irin wannan murmushin da kallon take tsintar kanta cikin wani irin yanayi na fargaba da mutuwar jiki ,”

Cikin sanyin jiki siyama ta ɗago idanun ta tana mai sauke su akan abun ƙaunar ta ,” hamma youssof antashi lafiya ,? Hamma tafeedah barka da asuba ,?

Ciki-ciki ya amsa mata da “lafiya” saɓanin tafeedah da suka gaisa sosai cikin sakewa har ma yake tambayar ta akan lamarin aikin ta inda ta tabbatar masa da ta ɗauki hutu na tsawon sati uku ,”

cigaba tayi da satar kallon biyamuradi da aisha wanda suke hirar su ƙasa-ƙasa cikin tsantsar shaƙuwa da kulawa da junan su da alama wata matsala ce da aishan wanda ta ƙagautu ta haɗu da yayan nata ta faɗa masa kasancewar ta rainon sa kuma abokin shawarar ta ,

cikin nazari take kallon sa bata samu ƙwanciyar hankali na sosai ba sai da ta fahimci faɗuwar sa ta jiya da dare bata haifar masa da wani rauni ba ,”ta sauke boyayyar ajiyar zuci , tana me Ƙwaɗaitawa a ranta ina ma ita ce maƙale da kafaɗun biyamuradin yana sauraren ta cike da kulawa da ƙauna kamar yadda yake yi wa ƴar ƙanwar ta sa ,”2

lokaci zuwa lokaci suna sakarwa juna murmushin yaƙe ita da tafeedah da rabin hankalin sa yake kan wayar sa domin idan da sabo yaci ace ya saba da yadda yake zama saniyar ware a duk lokacin da biyamuradi da aisha merama suka haɗu .

Da yalwatacciyar fara’ar ganin ƴaƴan nata ta ƙaraso falon , cikin hanzari bayun suka yi jerin gwano suna masu isar da gaisuwar su ɗaya bayan ɗaya , kafin cikar mintuna biyu sun cika babbar dardumar da suka shimfiɗa da kawatattun kwanukan abinci na alfarma ,ficewa suka fara yi ɗaya bayan ɗaya bayan sun sake kai gaisuwa .

Da murmushi take amsa gaisuwar yaran nata tare da tambayar su yaya suke ,”

Umartar aisha tayi da ta zubawa yayun nata abinci ,” ita kuma tuni siyama ta zuba mata abubuwan da take tunanin zata so ,”ta ɗebo ruwa a wani kyakkyawan mazuɓi tare da kamo hannun umma ta hau wanke mata su ,” cike da so da kauna take sanya mata albarka ,” tana me sunkui da kai take amsawa da ameen umman mu .

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun kammala cin abincin ne tafeedah ya miƙe bayan amsa wayar da yayi wanda saƙo ya iso gare shi ana neman sa ,” ƙarasawa gaban umma yayi tare da yi mata sallama addu’a tayi masa tare da ɗaurawa da nasiha ta ƙare da gargaɗin sa akan idan har yana cikin garin maraɗi kar ya yanƙe zuwa wurin ta kullum koh da bayan tafiyar aminin sa ,

Tare da ladabi yake amsa mata da yi mata alkawarin ba zai ɗauke ƙafar sa daga sashin ta ba koh da youssof baya nan , sallama yayi mata tare da miƙewa ya fice bayan sun yi musabaha da aminin nasa .

Bin sa yake son yi domin ya shawo kan sa amma bashi da kuzari koh kuwa bai tanadi kalmomin da zai yi amfani da su wurin wanke fushin da yake hangowa a idon tafeedan ba , dan haka ya bar shi ya sarara zasu  shirya a waya , domin sanin da yayi cewa shi da aminin nasa basa iya wani dogon fushi da juna , duk saɓanin ra’ayin su bai taɓa jawo musu fushi da junan da ya wuce awanni ishirin da huɗu ba , dole daya zai nemi daya koh da ta waya ne koh ta hanyar sakon kar ta kwana su shirya ,” kaunar junan su daga Allah take ,”

Cikin son fahimtar samun saɓani a tsakanin su umma take bin su da kallo har lokacin da tafeedan ya bacewa ganin ta ,” tasowa biyamuradi youssouf yayi gami da dawowa daf da ita tamakar zai hau cinya ,”riko hannayen sa tayi tana me murmushi tace ,”yarona tun kafin ka tafi ka fara bani kewa ƙwarai zan yi kewar ka bani kaɗai ba har mai martaba ma jiya ya ɗauki lokaci yana mitar nisan da zaka yi mana alamu sun nuna kiris yake jira ya janye alfarmar da yayi na barin ka tafiyar nan ,”1

Tare da tsananin ƙaunar iyayen nasa da yake taso masa yana kokarin dannewa yace “umma na shekara tamkar kwana ce kamar yau zaku ga Allah ya dawo muku da ni ,’kuma a jiya mai martaba ya sanar da ni cewa duk lokacin da yaga dacewa zai dunga tashin mutane daga nan musamman suna zuwa dubo masa ni ,ko da shi da kan sa bai samu damar zuwa ba ,”

umma na nima zan yi kewar ku ya karashe zancen sa yana me “ɗaga tafin hannunuwan ta ya sunbata tare da sanya kumatun sa a tsakanin hannun ta ,”ya cigaba da cewa addu’ar ku ita nafi bukata domin ita zata min jagora zuwa kan dukkanin wasu matakan nasara akan tafiyar da na sa gaba ,”

Murmushi tayi tana jin yadda kowacce ɗakika ɗaya take ƙaruwa da yawan kaunar ta ga gudan jinin zuciyar ta “, baza mu gushe ba muna masu yi muku addu’a har sai lokacin da mai rabawa ta raba tsakani ,” ta furta hakan tana me kokarin maida ƙwallar da take son cika mata gurbin idanu ,” yi maza kayi harama yarona .

Waiwayawa tayi ta dubi sashin da siyama take zaune wacce a zahiri take shafa fuskar wayar ta da ta jiƙe sharkaf da ruwan hawayen da yake ta ɗiga a bisa fuskar wayar ,”a dalilin matsananciyar kewar biyamuradi tare da wani karfin son sa da yake hanƙoro a cikin zuciyar ta , uwa uba damuwar ta da halin da biyamuradin zai iya kasancewa a ciki bayan tafiyar sa zuwa wata ƙasar , duk da cewa ba wannan ne karon sa na farko ba ,amma ita a gareta a duk lokacin da zai yi nesa da yin tozali ga idanun ta rauni ne sabo zuciyar ta take yi .

Siyama ta kira sunan ta ,”na’am umma ,!

Yi maza ki sa a fito miki da kayan naki a kai mota ku zo ku kama hanya kar rana tayi sosai ,”

Ta juya ga biyamuradi youssof wanda bai kai ga fahimtar kalaman mahaifiyar tasa ba , tace “, koh zaka yi magana ga hadiman naka “sojojin sa” tun da su suka san shirin motocin tafiyar ta ku , zu zo su ɗauki jakar siyama zata bi ka ku tafi tare zuwa niamey ɗin , ku kaita har gidan “ubbo”

Cikin jirkituwar fara’ar fuskar sa yake kallon bakin mahaifiyar tasa lokacin da take rattabo masa bayanin , amma kuwa lalle yarinyar nan tayi bala’in raina sa , watau ma da shi zata haɗa hanyar ta duk tarin direbobi da motocin da suke jibge a gidan nan ta rasa waye zata nema haɗa hanya da  sai shi ? A fusace ya waiwaya bangaren da yake zaton take da niyyar gargaɗin ta da idanun sa amma wayam yaga bata nan .

STORY CONTINUES BELOW

Cikin kwantar da kai yace ,”amma umma ni ba kai tsaye zan tafi zuwa niamey ba zamu tsaya a wasu wuraren me zai hana direba ya kai ta ?

Cikin ɗan ɗaure fuska umma tace ,”ko ma ina zaka biya tun da dai niamey ɗin ka nufa tare zaku tafi hankalina zai fi kwanciya sanin tana tare da kai cikin tsaro fiye da idan direban gida ne zai kai ta ,” kayi musu umarni a zo a fito da kayan ta ,

Bai samu zarafin amsa mata ba ya hango fitowar siyama wacce ta sauya shigar ta daga doguwar rigar da take jikin ta a ɗazu ,zuwa wani sassalkan leshi ruwan madara wanda aka yi masa ɗinki riga buba da zane ta ɗaura ɗankwalin ta ya zauna mata ɗas akan tarin bakin gashin ta irin na fulanin usul , sosai kayan suka haska mata fatar ta me dauke da matsaicin haske ,zanen kuwa ya zauna ɗabas a cikakken kunkumin ta ,kafafun ta sanye cikin takalma marasa dunduniya bakake , hannun ta ɗaya rike da bakin mayafin ta ɗaya hannun kuma ƴar ƙaramar jaka ce da kallo daya za’a musu asan tare aka ƙera su da takalman kafafun ta ,

Cikin takun ta na rangaji wanda ya dace sosai da zubin ta na doguwar mace samɓal take takowa bayan ta bayun ta ne biyu biye da ita ɗayar rike da jakar kayan ta ɗayar kuma ta riko jakar da take ɗauke da computer ta da kuma wasu tarkacen takaddun su na likitoci ,”

Wani banzan kallo me tafe da sumfurin harara iri daban-daban da biyamuradin ya watsa mata lokacin da take ƙarasowa falon shi ya sa ta kusa faduwa ba shiri ta ɗauke idanun ta da tsautsayi yasa ta jefa su cikin nasa ta mayar da hankalin ta kan ummu wacce take ta faman sakar mata murmushi ,”umma na fito ,”

A fusace biyamuradi ya miƙe gami da yiwa umman sallama tare da tabbatar mata cewa zasu kasance akan waya a kodayaushe ,” ba tare da ya sake kallon sashin da take tsaye ba ya sanya kai ya fita a karkashin rakiyar addu’o’in mahaifiyar sa .

Risnawa tayi tare da yiwa umman sallama wacce take jaddada mata da ta kula kan ta , kuma ta tabbatar bata wuce iyakacin kwanakin da ta ɗiba zata yi ba a karshe ta ɗora mata da tarin addu’o’i ,”maza je ki kar su jira ki Allah ya kiyaye hanya ,”

Da gudun ta , ta karaso har tana ɗan haki jikinta rigar wankan ce sai katon tawul ɗin da ta rufu da shi ,”kar dai hamma nah ya tafi ta furta hakan tana mai taro ƙwalla cikin idanun ta ,”

Ba tare da siyaman ta amsa mata ba ta ɗaga kafafun ta tana me ƙarasa ficewa daga falon tana jin lokacin da hajiya umma ta fara rarrashin aishan wacce ta ɗauke ta tamkar ƴar cikin ta ba ƴar kishiya ba ,”

Ta ɗauki tsawon mintoci biyar a tsaye gaban jerun gwanon motocin su biyar bayan da tun fitowar ta wani soja ya amshi jakankunan hannun bayun ta ya sanya su a bayan mota, bayun suka koma suka tsaya daga bayan ta sanin cewa basu da ikon tafiya su bar wajen har sai idan ita tayi musu umarni koh kuwa sun ga tafiyar ta .

Bangaren sojojin su ma suna ƙarƙashin umarnin ubangidan su ne wanda yake cikin ɓakar motar sumfurin ( purchase ) mai ɗauke da ɓakaken gilasai daga shi sai direban shi , ya shaƙa har iya wuya , a saboda haɗa hanyar sa da ta siyama , sosai yake jin zafin yarinyar shi da kan sa kuma ya rasa dalilin hakan kullum abun sake gaba yake ,

Sai da ya mula dan kan sa ya ɗago ya kalle ta yadda har ta fara haɗa gumi a ƙwaleliyar ranar damina ,” yayiwa direban sa umarni da ya buɗe mata gidan gaba ,”1

Cikin nutsuwa tayiwa kanta matsugunni a gaban motar tana me sauke ajiyar zucin wahalar tsayuwar da tayi , karaf suka haɗa ido ta mudubin gaban motar , da hanzari ta janye idon ta , dai-dai lokacin da direban ya tada motar ,sauran motocin suka bi bayan su ,1

Suna gaf da barin gari ya cewa direban nasa ,”agades muka nufa “,  cikin cika umarnin ubangidan sa ya amsa gami da karya kan motar ya ɗauki hanyar da zata kai su ga hawa titin katsina ,zuwa zender ,sannan yankin agades ,”

Ɗas ! Kirjin ta ya buga ta maimaita kalmar ‘,Agades ‘ me kuma zasu je yi agades su da suka nufi niamey wannan wane irin bahaguwar tafiya ce mai kwan gaba kwan baya ,a maimakon ayi gaba an sake nausawa baya ,? Gimbiya maimouna ta garin agades “, sunan da yayi amsa kuwwa kenan cikin ƙwaƙwalwar ta ,1

Tabbas yankin su maimouna suka nufa , hakan yana nufin biyamuradi wurin budurwar sa yake nufin zuwa tare da ita ,!

Tunanin ta ya katse lokacin da ta tsinkayi muryar sa yana yin waya ” hello Princess ,

dan kyakkawan murmushi ta hango saman fuskar sa,”da ya bata tabbacin wata kalma aka furta masa me daɗi,”

“Gamu bisa hanya,’

“, ameen sai mun iso je t’aime “,

.

  Ji tayi ran ta yana tuƙuƙi ,kwantar da kan ta tayi gami da lumshe idanun ta ranta cike taf da tunanin gamuwar su da gimbiya maimouna tana kuma saƙawa da warware yadda zata yi amfani da duk wata damar da zata iya zuwa mata wurin yaƙin neman ƙwato biyamuradi youssof daga wurin kowacce mace , kamar yadda tun farko ta tsara wannan tafiyar tata zuwa wurin ‘ubbo’ da nufin fara dasa harsashin ginin ta … Toh fah!Miƙa tayi bayan ta ya bada sautin “ƙaƙas” sakamakon zaman awanni baƙwai da tayi wanda zata iya cewa wannan ne karon ta na farko da tayi doguwar tafiya irin haka a mota ,”+

Wara idanun ta tayi sosai tana bin jerin gwanon bayin da ba sai an mata bayani ba tasan bayun yankin masarautar agades ne ,”cikin ranta kuwa mamaki fal take na ganin irin didima tare da sarewar da ake busa masu ,”wanda ya bata tabbacin anyi shiri sosai domin taryar biyamuradi, nan take taji wani malolon bacin rai ya tokare ta a maƙoshi .,

Bata fargar ba sai gani tayi bayun nan sun jagoranci biyamuradi zuwa ainahin cikin ginin masarautar wasu ta baya wasu ta gefe da gefen sa ,” yayin da sojojin sa suka dakata daga inda suke ,”

Ganin haka ya sa cikin sassarfa ta soma taku tana bin bayan su da har suka riga suka danna kan su cikin shigifofin gidan ,”cikin ranta kuwa tarin nadama tare da bakin cikin biyo biyamuradi take ,”wanda duk da sanin cewa da tayi basa shiri amma bata zaci kiyayyar sa da walakancin sa sun kai har haka ba a gare ta , duba da cewa tun da suka ɗauko hanyar tafiyar awanni bakwai koh kalmar sannu bata sake haɗa su ba ,”sai ita da take ta faman satar kallon sa haɗi da sauraron amon muryar sa ,”

Basu yi wata tafiya mai nisa ba a faffaɗan filin da yake mazaunin harabar gidan sarautar wanda yake rairayi ne tas-tas lallausa ,da ya ɗauki yanayin damina da sanyin la’asar yake bada wani irin sanyin ni’ima da kamshin ƙasa mai sanya nishaɗi a zukata .,

Amon sautin muryar biyamuradi taji ,”wanda ba ta kai ga fahimtar abun da yake faɗi ba , sai dai ta fahimci umarni ne ya basu ganin wasu tsiraru daga cikin su sun juyo gami da ƙarasowa gaban ta da take da ɗan tazara da su ƙadan ,”

“Ranki shi daɗe yarima yai umarni da a sada baƙuwathei ga shigifar gimbiya “

Gyaɗa kai tayi yayin da dogarawan nan uku suka shige gaba ta juya ta bisu a baya tana waiwayar tawagar biyamuradi wanɗanda suka nausa shiyar gabas ba tare da ta samu arzikin da zata samu koh da kalma guda daga gwarzon nata ba ,”

Fiye da yadda tayi zato gini da tsarin masarautar agades ya tafi da hankalin ta tare da burgeta sosai da sosai ,”ware idanu tayi tana bin kowanne zane da taswirun da aka ƙawata bangon kowacce shigifa da ita ,da kallo mai bayyana shauƙi tare da burgewa ,” kafafun ta da suke babu takalma tun a shigifar farko suna waɗakata cikin lallausan shimfiɗun alfarmar da suke ƙwance a kowacce shigifa,”

Cikin kowacce shigifar da zasu gifta bayu mata ne su huɗu suke zubewa gami da kai gaisuwa tare da tambayar inda suka nufa ,”amsa guda dogarawan suke badawa .”

Wagga diya baƙuwace da suke tafe tare da yarima biyamuradi ,kuma wurin gimbiya aka biɗa da a sada ta ,”

Har zuwa ga shigifar da tafi kowacce tsaruwa inda daga nan dogarawan suka juya bayan sun damƙa ta a hannun wata baiwa wacce tayi mata umarnin zama akan ɗaya daga cikin shimfiɗun alfarmar dake wurin ,tare da sanar mata ta jira gimbiya na nan fitowa bayan almuru ,”

Cikin takaici take duban baiwar da ta miƙe bayan kammala bayanin ta ,”

“Tou ki sada ni da inda zan yi alwala na kimtsa domin ina da bukatar yin haka ,

Siyama ta furta hakan ba tare da ta kai duban ta ga baiwar ba domin zuwa lokacin ta fara shaƙar takaicin halin ko’in kula da rashin girmamawan da ta fara hango alamun su ga hadiman gidan wanda ta hakikance ba kowa ya jawo mata hakan ba illa biyamuradi da ya danganta ta da matsayin Baƙuwa a gareshi a maimakon ƙanwar sa ƴar uwa ,” domin ta tabbatar da ace ya kiraye ta da matsayin ƙanwa agareshi da tabbas ya samar mata da girma tare da matsayi a idanun hadiman gidan .,1

STORY CONTINUES BELOW

Bayan idar da sallar ta “na magarib” tayi kimanin mintuna talatin tana zaune ,wanda har zuwa lokacin babu wacce ta sake bi ta kan ta cikin tarin bayun da suke ta kai kawo da manyan tire da tasoshi na alfarma a hannayen su waɗanda suke rufe ruf da mayafai iri guda masu launin ruwan sararin samaniya “, suna nufar wani sashi da ƙofar sa take rufe ta hannun dama ,

Cikin ta kuwa idan ban da ƙugin yunwa babu abun da yake ,”yayin da ita kuma ta sha alwashin baza ta sake tuntubar hadiman gidan kan wata bukata tata ba ,” hasalima kishingiɗa tayi gami da lumshe fararen idanun ta ,gefe guda na zuciyar ta tana nazarin yadda lamuran suke tafiya .,1

Wani sassanyan ƙamshin turare ne ya fara bugar hancin ta kafin taji tashin muryoyin hadiman da suke cikin shigifar suna kirari tare da ƙwarzanta uwargijiyar su ,”

Ta ɗauki kimanin mintuna biyu kafin ta buɗe idanun ta a hankali ,”fes suka sauka cikin manyan idanun kyakkyawar budurwa da take zaune cikin shiga ta alfarma akan wata shimfida da ita bata san lokacin da aka samar da ita ba ,”kallon – kallo suka yi na adadin wasu daƙiƙai kafin siyama ta mayar da nata fatar idanun ta lumshe zuciyar ta kuwa bugawa take ɗas,ɗas,ɗas ,

tabbas wannan ce gimbiya maimouna , babu shakka ta amsa sunan ta ,’ ganin ta kuma ya zo dai-dai da jin labarin ta ,” sai dai koh kusa bata ji ta karaya ba bata ji ta tsorata ba ,sam ƙwarjinin ta bai ɗimautata ba ,” hakan ya sa ta cigaba da lumshe idanun ta tamkar mai bacci wanda babu wanda ya lura da buɗesu da tayi ta rufe sai ita gimbiya maimouna wacce hasken lantarkin da yake tarwai ya bata damar hango cikin ƙwarar idanun siyama wacce bata kai ga sanin wacece ba hasalima bata san da zuwan ta ba ,”1

Gnala wagga ɗiya daga ina ta tahou ?

Wacece ita ? Gimbiya maimouna ta furta hakan tana mai kai duba ga inda siyama take kishingiɗe

Cikin girmamawa wacce aka kira da “gnala” ta amsa

“afuwa take biɗa , wagga ɗiya baƙuwa ce da suke tafe tare da mai girma yariman maraɗi tun da yammaci ta samu isowa nan ƙarƙashin rakiƴar dogarai su sunka isar da sakon wanzuwar ta anan daga bakin yarima ,”

Mayar da duban ta ta sake yi ga kyakyawar hausa/fulanin fuskar siyama ,” nan take ta hango yanayin kamannin masoyin ta akan fuskar siyamar da take da tabbacin ba bacci take ba ,”ginshiri ne kawai tare da ƙasaita wanda ta danganta hakan ga kasancewar ita ma siyamar ɗiyan sarki ce kamar yadda tayi zato ,”siyamar ƙanwar youssouf ce wacce bata kai ga sanin ta ba , domin duk cikin tarin ƙannen sa da ta hakiƙance yana da su bai taɓa yi mata zancen kowa ba sai na “Aisha merama” ta kuma tabbatar ba ita bace wannan domin ya sha gwada mata hoton meramar maraɗi ,”

Nan take ta hango kuskuren da hadiman ta suka aykata na barin gimbiyar maraɗi bisa wannan shimfiɗar da bata kai ba a wurin ta .1

Gyaran murya tayi cikin yaren su na azbinawa tace ,”

Gnala a samarwa gimbiyar maraɗi kyakyawar shimfiɗa a wadata ta da abin sha da na ci haɗi da bigire mai kyau domin tayi wanka ta sauya kaya ta huta kafin mu gaisa ,wagga ɗiya gimbiyar maraɗi ce , kar a sake ayi wani abu na rashin ɗa’a da zai taɓa martabar mu har zuwa tafiyar ta ,ɗiyar girma ce maza a girmamata,”

Duk da cewar siyama bata jin yaren su na azbinawa amma ta fahimci zancen ta aka yi jin an ambaci “maraɗi “

Tunanin ta ya katse lokacin da taji hadima ngala wacce ga alamu ita ce shugabar bayin gimbiya maimouna,” duba da cewa tun da gimbiyar ta fito duk sauran bayin suka kai gaisuwa tare da ficewa daga shigifar sai ita ta rage”, ta ɗurkusa tana ahuwa cikin girmamawa take neman iznin ta jagorance ta zuwa wata shigifar ,”

STORY CONTINUES BELOW

Ware ido tayi tana me sake tsuƙe fuska ta gƴaɗa kai ,” abun mamaki kunnuwan ta sai suka tsinkayo mata ngala na mata ƙirari “ɗan murmushin gefen baki tayi tana mai bin bayan ta ,”1

Cak ta tsaya sakamakon sallamar sa da ta tsinta cikin amon muryar sa mai samar mata da kasala ,”

Waiwayowa tayi suka dubi juna ido cikin ido ,”dai-dai lokacin da gimbiya maimouna ta miƙe tana mai nufar sa cikin takun ta ,” fuskar ta ɗauke da tattausan murmushin da duk cikin maza shi yayi zarrar samun irin sa ,”

Juyawa tayi cikin sauri ,kafin idanun ta su hango mata irin tarɓar da zasu yi wa juna wanda zai haifar mata da damuwar da zata hana ta bacci ,”

Cikin nutsuwa ta sauya kayan ta zuwa na barci bayan taci abinci ta getse ta sake yin wani wankan duk cikin ƙarƙashin kulawar gnala da take hidima da ita cikin girmamawa hatta ruwan wanka da kayan baccin ita ta haɗo mata ,” yayin da a halin yanzu take kishingiɗe kan makeken gaɗon kwatankwacin nata sai dai wannan ya fi shi girma , gnala tana daga ƙasa ta miƙe bisa guiwarta tana tausa mata kafafu ,”1

Tare da nazari take kallon ta tana son samo bakin zaren ta inda zata fara yi mata maganar da take son yi wato yi mata tambayoyi akan uwargijiyar ta ,” sai dai kuma tana shakka akan koh zata samu haɗin kan gnala ɗin ,”

A hankali ta murɗa kofar ɗakin gami da shigowa ƙarƙashin rakiyar sassanyan kamshin ta mai shiga zuci ,cikin sabuwar shiga mai banbanci da ta ɗazu domin a halin yanzu sanye take da doguwar rigar siliki ruwan zaiba da duwatsun jiki suke ta faman ɗaukar ido ,miƙaƙƙen gashin ta ya zubo har gadon bayan ta yayin da madaidaiciyar fuskar ta mai ɗauke da manyan fararen idanu ta faɗaɗa da lallausan murmushi ,”

Sallama tayi musu tare da zama bisa gefen gadon da siyama take a zaune bisa a halin yanzu ,” maida duban ta tayi ga gnala ,”

daɗa a bamu wuri mu zanta tare da ƙauna ta ,”

Toh ranki shi ɗaɗe ku tashi lafiya ɗiyan saraki ,

Barka da zuwa ƙauna ta siyama kin iso lafiya ? Yaya umma da fatan kun baro kowa lafiya kun iske mu lafiya ?

Cikin murmushi siyama take amsa mata kafin daga bisani hira ta fara gudana cikin taka tsantsan daga kowaccen su ,” domin ita ma gimbiya maimouna koh da ta tambayi biyamuradi youssouf wacece wacce suke tare ya tabbatar mata ƙanwar sa ce kuma sunan ta siyama ,sannan ita ma niamey ta nufa shiyasa tafiyar su ta zo guda ,”

Daga haka bai wani bata fuskar da zata sake zouwa mar da batun siyaman ba ,” yayin da ita kuma hankalin ta yafi karkata ga batun tafiyar sa da yayi ta faman rarrashin ta da kyar ta amince suka rabu cikin aminci tare da alkawarin kasancewa akan wayar tafi da gidan ka a har kullum ,”

Ƙauna ta daga shigowar ki cikin garin mu zuwa saduwar ki da masarautar mu menene yafi burge ki yafi baki sha’awa ?

Ɗan jimm siyama tayi tana nazari “ga dama ta samu ,” murmushi tayi tsarin ginin masarautar ku sosai ya burgeni , sannan na biyu girke-girken ku na gargajiya sun ƙawatar da ni kuma sun min daɗin ɗanɗano wanda har zan so na dunga samun irin girkin lokaci zuwa lokaci

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi maimouna tayi jin siyamar ta yabi masarautar su ,idan kuwa haka ne zan baki baiwa ƙwararriya ɗaya daga cikin masu min girki ki tafi da ita zuwa duk inda zaki ta dunga yi miki irin girkin mu a duk lokacin da kika biɗa ,”

Cikin farin cikin ganin tarkon da ta ɗana yayi kamuwa kuma zuwan ta yayi alfanu domin zata tafi da wani bangare na kusa da gimbiya maimouna tayi mata godiya tare da yabawa akan karamcin da tayi mata ,”2

Tare da nishaɗi gimbiya maimouna ta amsa tana mai jin daɗin zuwan siyamar domin ta daɗe tana son ta samu dama irin haka da zata tura wani na kurkusa da ita zuwa maraɗi “saboda wani boyayyan dalili nata “, tunani ta fara yi cikin amintattun bayun ta wa zata tura ?1

GNALA

Hasken alfijir ya fara haskowa ta tsakanin labulen tagar ɗakin nata ,tana zaune daga bakin wata doguwar kujera jal da take ɗakin nata da ta sha shimfiɗun alfarma , gefe daga ƙasa baiwar ta ce ngala

“zaki tahi zuowa maraɗi a matsayin kyautatciyar baiwa da na ba da ki ga ɗiyan sarkin maraɗi siyama ,”zaki tahi a matsayin mai yi mata girke girken gargajiya irin namu ,” zaki yi duk wani kokari ganin kin samu mazauni mai kyau wurin sabuwar uwargijiƴar ki ,”ta yadda zata sau miki jiki ki samu shiga cikin lamuran ta wanda ta haka zamu san lamuran da suke gudana baki ɗaya a cikin gidan tun kafin wanzuwa ta ,”wanda hakan shi zai sa naji saukin tafiyar da dukkanin lamurana idan naje cikin su ,” ba akan mutum guda zaki sanya ido ba akan duk wasu makusanta biyamuradi youssouf , nasan tsawon shekara guda zai ishe ki kammala aykin da na aike ki ,” idan na zo babu wahala zan sauyawa siyama ke da wata baiwa daban ,amma a yanzu ke yafi chanchanta da ki tahi ,” ki kula sosai bana so a samu matsala zan dunga tuntuɓar ki lokaci zuowa lokaci ,”

Cikin girmamawa da miƙa wuya baiwa gnala ta amsawa uwargijiyar ta ,”cikin ran ta kuwa tana tunanin wanne lamurra uwargijiyar ta ke son aiwatarwa a masarautar na maraɗi da har zai kai ta zaman aure da magajin garin ,????????

Kafin karfe baƙwai na safe siyama ta gama shirin ta ,an yi mata jagora zuwa sashin matan sarkin ɗaya bayan ɗaya ta kai gaisuwa inda a karshe tayi zango a fadar mai martaba sarkin agades inda nan ma ta kai gaisuwa tare da biyamuradi youssouf wanda shima yake shirye tsaf cikin shirin sa na tafiya,”

Ƙarƙashin rakiyar dogarai suka sadu da wurin da motocin su suke batare da bata lokaci ba suka shiga , sai dai a yau saɓanin jiya baiwa gnala ita ce a mazaunin mai zaman banza yayin da siyama take maƙale daga jikin kofa gefen biyamuradi wanda tun bayan gaisuwar su da ya amsa ita da gnala ɗin bai sake bi ta kan su ba bai kuma tambayi siyama wacece gnala ɗin ba ,”domin gimbiya maimouna ta gama yi masa bayanin kome ,”inda ta bayyana masa ayken ngla ɗin tayi zuwa niamey ,???( koh meyasa ta boye masa gaskiya )2

_______

Tafiya yankin azaba tabbas haka ne domin ba su suka sami isa niamey ba sai bayan magarib ,” yayin da kai tsaye ya sa suka wuce gidan “ubboh” wacce tun jiyan take ɗokin zuwan ƙanwar ta mafi soyuwa agare ta ,”

Da gudu-gudun su suka fito ita da ƴan kyawawan yaran ta huɗu ,” suka tarɓe su tare da jagorantar su zuwa ciki , inda ta miƙawa mai kula da hidimar gidan namiji ,”mukullin sashin da suke sauƙar baƙi ya buɗewa youssouf da muƙarabban sa sai dai biyamuradi youssouf ɗin ya dakatar da ita ta hanyar sanar mata da cewa karfe takwas suke da taro (meeting) kuma zuwa asubahin yau jirgin su zai ɗaga zuwa nigeria dan haka basu da isashen lokaci ,” hakuri ya bata ganin yadda tayi kicin-kicin da fuska tana mitar bata lokutan da aka yi wurin shirya musu abinci shi da muƙarabban sa ,”ƙarshe dai dole ta sa suka kwashi abincin bayan ta sa anfito musu da shi ,suka yi sallama cike da ƙaunar junan su ,”domin duk da kasancewar su abokan faɗan juna amma wannan tsabtatatciyar ƙaunar ta tsakanin saƙo da saƙo tana nan tana gudana a tsakanin su ,” koh sun yi faɗa basa jimawa suke shiryawa ba’a shiga tsakanin su ,”

Har ta ga ficewar motocin sa daga gidan tana ɗaga masa hannu zuciyar ta cike da ƙauna tare da tausayin ƙanin nata ganin irin aikin wahala da bautawa ƙasa da ya zaɓarwa kan sa ,”

Gefe guda kuma tana tinanin damuwar da ta hango kwance a ƙwarar idanun siyama cikin sassarfa ta juya gami da nufar cikin gidan ,” koma meye dole zata magance mata matsalar ta saboda ita kam duniya bayan mahaifan ta bata da kamar mahaifiyar siyaman har abada baza ta mance da ƙaunar ta ba ,”1

_____

Karfe huɗu da rabi na asubahi agogon niamey jirgin su biyamuraɗi youssouf ya ɗaga Daga “Diori Hammani international airport ” zuwa nigeria ,inda karfe shiddah da mintuna arba’in suna cikin tashar jirgin sama na “Nnamdi Azikiwe international airport Abuja Nigeria “,……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *