MAFARI CHAPTER 4 BY UMMU AZAMM
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tuki Hamza yake cikin rashin kuzari wanda ba domin kan titin shal yake babu kowa ba a sakamakon gudun da kowa yayi , da tabbas babu abunda zai hana ya samu tukuicin zagi daga wurin sauran direbobi saboda sam ya gaza yin sauri , zuciyar sa taƙi aminta da ya tafi ya bar ta cikin halin da take ciki , wani sashi na zuciyar na son sanin me ma ya kai ta wannan unguwar wacce take cike da hatsari .?
Gangarawa yayi gefen titin ya tsaya dai-dai lokacin da tunanin abun da zai iya samun ta marar kyau idan har dare yayi mata a wannan unguwar ya gitta masa , da hakan ya sa ba shiri ya karya kan motar ya juya batare da la’akarin ba akan hannun da yakamata ya juya bane .
Wannan shine karo na biyar da take safaa-da-marwaa a bakin babban titin tana mai kwalla kiran sunan falmata , wanda zuwa yanzu da ta kawo tsakiyar hanyar ta ji juya ya fara kwasar ta a sakamakon muguwar yunwa da kishirwa gami da tsantsar sanyin da yake ratsa bargo da kasusuwan ta ta jikin jiƙaƙkun kayan ta da iska ta fara busar da su ,
Ba shiri ta dira guwowin ta duk biyu a ƙasa tare da sake fashewa da wani matsanancin kukan da baya fitowa sosai a sakamakon kwalla kiran da take ya fara dusar da karfin muryar ta .1
Kuka take bilhakki tana kiran sunan falmatan a hankali cikin ƙaramar murya ,”
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Falmata nyi dan3? ( falmata kina ina ?)
Allahgammama falmata are3 nyi baa maa range3 kindaa dikkin3 baa ,” (Dan Allah falmata ki dawo idan babu ke bazan iya rayuwa ba )
Ƙarasa bajewa tayi daɓas a cikin guntun ruwan da yake wajen idanun ta na fara ganin bibbiyu ,
Daf da ita ta bayan ta ya zo yayi birki , kallon ta yayi ya ɗauke kai gami da matsa mata hon ,
Taji ƙarar motar sarai a daf da ita amma bata yi wani alamu na motsawa ba hasalima wani ɗan guntun tunani ne ya gifta mata na ina ma da motar nan zata take ta ta mutu ita ma kamar yadda mahaifin su ya mutu take kuma hasashen mahaifiyar su da sauran kannen ta ciki har da mafi soyuwa a gareta “falmata” duk sun riga sun mutu sun bar ta ,” tunanin hakan da tayi ya sa ta sake muskuɗawa ta matsa kan titi sosai yadda zata bawa motar da ta taho damar bi ta kan ta ,”
Wani dogon tsaki ya saki ganin yadda ta rarrafo ta hau kan titi a maimakon ta taso ta zo su tafi kamar yadda yake nufi ,
Balle murfin motar yayi ya fito laɓɓan bakin sa suna furta kalmar “sokuwar banza ƴar kauye “,
Tsayuwa yayi a kan ta ya zuba mata ido yana nazarin ta cikin tantamar samuwar cikakken hankali a gareta , gefe guda na zuciyar sa na yaba kyaun dogayen fararen yatsun kafafu da na hannayen ta da suke zara-zara kuma fasalin yatsun hannayen nata kamar an feƙe fansiri haka suke da ɗan tsini ta saman su , gwanin ɗaukar hankali duk da ɗauɗa da maikon miya da suka bata su .
Tsayuwar sa akan ta bai sa ta ɗago kan ta da ta ɗora bisa hannayen ta dake kan guwaowin ta ba wanda hakan ya bata ɗamar dunkulewa guri guda tana jiran motar tayi awon gaba da ita ,”
Ganin taƙi ɗago kan nata ya sanya ransa sake ɗugunzuma ganin sa tana neman ɓata masa lokaci alhalin shi taimakon ta kawai yake son yi wanda har zuwa yanzu ya rasa dalilin da ya sa yake son taimaka mata ,”
Ke duba bana son wawanci ki taso na mayar da ke sansanin ku tun kafin dare yayi miki anan karnuka su yagalgala ki ,
STORY CONTINUES BELOW
Hamza ke furta hakan yana yi yana yamutsa fuska tamkar an sanya shi yin maganar a dole ,”
Har illa yau dai yakaka taƙi ɗago kan ta taƙi cewa koh uffan duk da cewa ta gane shi ,a ranta kuwa ta gama yankewa kan ta shawara a dalilin zancen karnai da ta ji ya ambata wanda take taji hanyar mutuwar ta mafi sauki shine kawai ta kwana a nan wurin domin tana da tabbacin idan har tayi ido biyu da karnuka a sulusin dare babu abun da zai hana jijiyoyin da ke kai jini cikin zuciyar ta su tsinke ta mutu nan take ,” tunanin hakan ya sa ta sake gyara kwanciyar kan ta ta maida fuskar ta zuwa ɗayan bangaren cikin sallamawa.
Wanda hakan ya bawa hamza damar ganin fuskar ta da jijiyoyin kan ta daga goshin ta da na gefe-gefen idanun ta suka taso raɗa-raɗa koraye shar “kasancewar ta fara sol “
Firgita yayi da ganin ta a haka wanda a take ya fahimci rangwamen lafiya a gare ta kasancewar sa cikakken likita kuma kwararre wanda gwamnatin jaha ta amince da shi har ya zama ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da marasa lafiyan dake sansanin ƴan gudun hijira .
Sunkuyawa yayi a gaban ta gami da kai hannu ya taɓa goshin ta ,” a ɗan tsorace ta ɗago da idanun ta da suka ƙanƙance gami da sake zurmawa ciki ainahin launin su na zaiba-zaiba kamar gilashi suka bayyana tar ,”
Da sauri ya janye idanun sa daga cikin nata sakamakon ji da yayi kamar akwai wani ɗigo dake sashi cikin wani yanayi tun daga ƙasan ruhin sa a tare da idanun yarinyar .
Ya janye hannun sa tare da miƙewa ya tsaya ,”
Baki da lafiya , ki taso mu tafi na mayar da ke sansanin ku a duba ki a baki magani zaman ki anan hatsari ne ,”
Kin ji koh ?
Jin ta sake yin shiru a karo na biyu ya sa shi shafa sumar kan sa cikin gundura da halin ta ,”gefe guda na ran shi yana mamakin kan sa ta yadda ya damu har yake rarrashin ƴar gudun hijirar da bai san ma daga wanne ƙauye take ba.
Ke idan baza ki tashi ba zan cicciɓe ki koh da bakya so na kai ki saboda hakki na ne na kula da lafiyar ku , ( haka kou ? naga alama 😂 )5
Ji da tayi yace zai ɗauke ta ya sa ta miƙewa tsaye batare da ta bari sun sake haɗa ido ba , ta nufi cigaba da tafiya ,
Idan kika sake kika sake taku biyu da waɗannan ramammun siraran kafafun naki zan ɗaga ki sama na jefa ki cikin mota ,”idan ya so ki karye ma ke kika sani doluwa kawai , “dan ma kin samu ina sauke hakki na na taimakon ki da Allah ya ɗora min shine zaki dunga min iskanci da reni ,???2
Tare da rashin jin dadi danganta ta da yayi da mai reni ta koma da baya ta tsaya a jikin motar ,’ tana mai riƙe kan ta da hannu bibbiyu wanda yake masifar yi mata ciwo tamkar zai faɗo ,”
Da sauri ya buɗe mata murfin motar
Shiga muje ! ?
Tafiyar kurame ita ta biyo bayan gudun da hamza yake shararawa akan titunan da babu wani wadatar motoci , cikin mintuna goma sha biyu ya karaso bakin sansanin nasu ,”
Sauke gilashin motar yayi gami da gaisawa da sojojin da suke gadin sansanin da hakan ya sanya yakaka ɗago kan ta da tun da ta shiga cikin motar yake sunkuye ,”
STORY CONTINUES BELOW
Karaf ta sauke kwarar idanun ta akan ta tana tsugunne a tsakiya tana fuskantar duk wanda zai shigo sansanin ,”daga inda take tana hango yadda take rawar sanyi da jikakkun kayan jikin ta ,”
Wani irin numfashi ta sauke mai tafe da nishin jin daɗi bata yi wani jinkiri ba ta fara tura murfin kofar da kokarin ɓalla ta ta fita ,’cikin sautin da yake bayyana tsantsar murna da farin cikin ta take jera kiran sunan ƙanwar ta ta ,”
Falmata nah !
Falmata nah !
Mayar da duban sa yayi inda yaga idanun ta suna kallo ,’ yamutsa fuska yayi tamakar ya ga kashi ,”domin haushin yakaka da yake ji kaɗan ne akan irin tsanar da yayi wa falmata.3
Ke dallah ki nutsu kar ki ballamin murfin mota ,” ke da baki da lafiya ina zaki fita da gudu ki je ??
Tun kafin ya rufe baki ta amsa masa cikin siririyar muryar ta da take gauraye da sautin farin cikin da ya gaza boyuwa har akan siririyar fuskar ta da siraran laɓɓan ta suke ɗauke da dariyar da har ya bayyana gajejjerun hakoran ta irin na ƴar uwar ta ,”
Na warke wallahi na warke falmata na ashe ta dawo bata mutu ba ,”bata ɓata ba dan Allah ka buɗe min kofa naje wajen ta wallahi na daina jin kowwane ciwo a jikina .2
Shagala yayi wurin sauraran sassanyar muryar ta da koh kaɗan bata tare da hayaniya uwa uba ɗan bakin ta da yake bayyana baki sidik ɗin dasashin ta da ya kawatu kwarai akan farar fuskar ta ,”
Jijjiga kofar tayi da ɗan karfi cikin nuna alamun ƙosawa
Dan Allah ka buɗe min !
Cikin sanyi jiki da sabon yanayin da yake ji yana ratsa kowanne sashi na zuciyar sa ya miƙa hannu a kasalance ya matsa ɗan mubuɗin kofar ta bude , fit ta fita a guje har tana koƙarin faɗuwa ,”
Takun gudun kafafun ta shi ya fara isowa ga kunnuwan ta kafin taji sautin muryar ta ,”
Zuruf ta miƙe tsaye ita ma tana ambaton sunan ta ,” tare da nufar inda take jiyo tahowar ta ,”
Kyakyawar runguma suka yi wa juna zuciyoyin su suna masu cika da farin cikin ganin junan su cikin koshin lafiya bayan taraddadi tare da zullumin da kowaccen su ta shiga na tunanin rasa ƴar uwar ta ,”
Hannu bibbiyu yakaka ta tallafo fuskar falmata ,” da take dariya
Falmata ya akayi kika dawo ? Waye ya dawo da ke ? Meyasa baki jira ni ba a wurin kamar yadda muka yi yarjejeniya? falmata kin tayar min da hankali dan Allah nan gaba kar ki sake tafiya wani waje mai nisa ki barni ,”
Yakaka nima ba’a son raina na matsa daga gurin da kuka ajiyeni ba , bom ne ya tashi yakaka , duk mutane suka dunga gudu ,” kowa yana neman wajen tsira ,” na rasa yadda zan yi , inaso naje inda kuke ban san wajen ba kuma bani da ido bare nima na gudu , Allah ne ya taimaka min , wannan mutumin da kuka ajiye ni a gefen rumfar sa shi ya kama hannu na ya kawo ni tasha , da nufin mu nemi ƴan uwa na tun da na gaya masa kuna kurkusa da wajen ya san za ku zo tasha ,” sai dai wajen minti talatin babu wanda ya zo daga cikin ku ga gaf ake da fara ruwa , har ya yanke shawarar zai tafi da ni gidan sa , sai naji muryar “Kolo” tana kiran suna na , nayi murna sosai domin a tsorace nake ina ta kuka ,”
Na tambayi kolo ina kuke ke da yagana ta tabbatar min da kuna tare kuma zaku dawo ,” sai dai hankali na bai kwanta ba tun da muka dawo na kasa zama ina tsoron kar ku ɓata yakaka ku kasa gane sansanin mu ,”zuciya ta baza ta jure rashin ki ba yakaka “, domin bani da kowa bayan Alllah sai ke yakaka ,”3
STORY CONTINUES BELOW
ta ƙarashe zancen ta tana mai kai hannunwan ta ta ɗaura akan na yakakan da take tallafe da kumatun ta ta zubawa ƴar kewayayyiyar fuskar kanwar ta ta idanu,” kamar yadda fararen idanun kanwar ta ta ma suke fes akan fuskar ta tamkar dai tana kallon ta ,”
Murmushi tayi tana mai sake jin yadda zuciyar ta take narkewa da ƙaunar ƙanwar ta ,gefe guda tana sake jin zuciyar ta tana ƙarfi da ɗaukar ƙudirin zamantowa GARKUWA ga falmata ..!!1
********
Kai kawo yake yi a gaban gungun zaratan sojojin cikin matsancin bacin rai yake magana da maɗaukakiyar murya ,”
Matsayin mu na jami’an tsaro ba shi ne zai bamu damar cin zarafin Al’umma tare da mayar da rayukan su ba a bakin kome ba ,” ba’a bamu kaki da makamai domin naɗa mu jagorancin zalinci ga fararen hula ba ,” sai domin mu basu kariya da tsaro tare da kwato musu hakkokin su ,” sai dai yadda kuka tafiyar da mutanen ƙaramin ƙauyen da yake tsakanin yankin difa da birnin maiduguri ya sha banban da rantsuwar kare martabar jama’ah da muka yi ,” labari ya zo min na yadda kuka ci zarafin mutanen ƙauyen ta hanyar yi musu kisan kiyashi ƙona dukiyoyin su da yi wa matan su fyaɗe dan kawai an sanar da mu akwai ƴan tawayen boko haram daga cikin su , ni a matsayina na shugaban rundunar ku ba haka na tura ku kuyi ba ,”gwamnati ba mutanen ƙasa ta turo mu mu yaka ba face ƴan tawayen boko haram ,
ɗan tsagaitawa yayi yana mayar da numfashi ,”
Wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zaku hau kan mutanen gari da kisa a zuwan kuna yakar ƴan tawayen boko haram .
Jaan kafafu suka yi suka buɗa gami da ƙamewa su sara masa da hakan yake nuni da sun karbi umarnin sa ,”
Shigewa yayi cikin ɗaya daga cikin manyan tantunan da suke kakkafe a sararin faffaɗan filin da yake cikin daji sosai daga gefen birnin na maiduguri .
Zama yayi a bakin ƙatuwar katifar da take yashe cikin tantin gami da kama kan sa da hannu biyu , wani iri yake jin kan nasa yayi masa matuƙar nawi kamar ba nasa ba , ga zuciyar sa da tayi wani irin cunkushewa sam sam ba ya jin sa dai-dai da ya riga ya danganta abubuwan da yake ji da rashin shan abar sa “Burkutu” har na tsawon kwanaki biyu yau ana yinin na uku ,
Miƙewa yayi ya nufi wurin da jakankunan sa ke jibge ya jawo ɗaya daga cikin su gami da buɗe ta sai ga tarin kwalaben giya sumfuri daban daban da yayi guzurin su, ɗaukar ɗaya daga cikin kwalbaben yayi ya riƙe a hannun sa yana jujjuya ta ,”
Kwarai yana da bukatar son ya sha giya sai dai shi sam ba giyar turawa yake sha ba , hasalima idan ya sha giyar turawa birkita masa jiki take yayi ta haraswa tare da matsanancin ciwon kai ,” giyar gargajiya ta burkutu ita ce abar shan sa .
Mayar da kwalbar giyar yayi cikin sauran ƴan uwan ta gami da rufe jakar yana me miƙewa cikin ransa yana jin ya zama dole ya nemo burkutu duk inda take idan har yana so ya iya cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali ya kuma gabatar da aikin da ya zo yi cikin nasara , tabbas burkutu ta zama mahaɗin rayuwar sa domin ji yake kamar zai iya rasa ran sa idan ya ƙara wasu awanni bai zubawa cikin sa ruwan zafin burkutun ba ,”2
Da sauri ya fita daga tantin yana jin yadda kan sa yake jujjuyawa ,” a take sojojin dake da alhakin kula da shi , kama daga tuƙa shi idan zai fita da masu rakiyar sa ,zuwa masu yi masa wanki da girki da sauran aikace aikace duk suka taso ,”
dakatar da su yayi ya kira direban sa kawai tare da yi masa umarnin ya tuƙa sa zuwa cikin birnin maiduguri ,” .Babban Barikin soja dake tsakiyar birnin maiduguri nan direban youssouf ya dakata ,+
Karo na uku biyamuradi youssouf yana yunkurin faɗawa takwaran aikin sa kuma sabon aboki agare shi wanda ya kasance babban sojan nigeria mai matsayi irin na biyamuradi ( colonel ) amma sai ya ji ya kasa , saboda shi da kan sa yana jin kunyar mummunar ɗabi’ar sa duk da cewa kusan hakan ba bakon abu bane wurin su soji , amma yadda yake da kamala da nutsuwa a zahiri ,uwa uba kasantuwar sa ɗan nasaba da akan san su da kyaun tarbiyyah , tashin farko zai yi wuya ayi hasashen yana kurɓar burkutu ,”
Sake ƙutawa yayi a karo na barkatai yana me jin duk ya gundura da hirarrakin da abokin nasa mai suna “colonel nuhu ” yake yi masa , ya kai ɗan yatsan sa ɗaya gami da sosa ƙeyar sa .
Taɓo sa nuhu yayi lokacin da ya lura baki ɗaya youssouf ɗin bai bashi amsar hirar da yake yi masa tamkar ma hankalin sa bai tare da shi yayi zurfi cikin tunani .
Abokina yaya dai ?
Meye yake damun ka haka da har ka zurfafa cikin tunani ?
Ɗan ƙaramin tsaki youssouf ɗin yayi kafin ya ce
Bari kawai abokina akwai abun da nake bukata ne ,
Wani shu’umin murmushi nuhu yayi domin shi tun tuni ya harbo jirgin youssouf ɗin duba da yadda duk yake a birkice ga fuskar sa da take bayyana matsanancin halin da yake ciki ,” amma dan ya sake tabbatarwa tare da son ya tsokani youssouf ɗin ganin kamar yana son boye masa cikin sa , ba tare da ya san shi da shi dukkanin su ƙwaryar sama da ta ƙasa ne ( duk kanwar jaa ce )
Me kake bukata haka abokina ??
Ɗago kan sa yayi da yake a sunkuye ya wara idanun sa da suka sauya launi zuwa jaa yana jin yadda nawin da ya tokare shi a kirji akan rashin samun kurbar burkutun yana sake ƙaruwa ta yadda yake jin tamkar matse masa jikin sa ake da dukkanin hanyoƴin jinin sa ,” cikin wata irin sarƙaƙƙiyar murya yace ,”
Burkutu ,” Burkutu zan sha nuhu ,’ dan Allah ka taimaka ka kaini inda zan samu burkut da farko , zan yi maka bayani daga baya ,”
Wata shu’umar dariya nuhu ya kwashe da ita ,’
haba abokina ai ba ma sai ka min wani bayani daga baya ba duk su biyun za’a tanadar maka a lokaci guda , kaga daga ka gama kora ruwa sai kuma a faɗa harka ,”
Shi dai biyamuradi youssouf bai ce kome ba hasalima bai kai gano ba cikin kalaman nuhu illah kawai ya ji ya fara samun nutsuwa tun da nuhu ya ce zai samar masa da abun da yake muradi ,”
Direban sa yayi niyyar kira amma sai youssouf ɗin ya dakatar da shi tare da faɗa masa shi yana bukatar sirri ne dan haka so yake su tafi su biyu kawai ‘, a cikin ran sa yana ƙudurtawa zai sanya ido sosai ya gane hanyar domin duk lokacin da ya bukata kawai ya tafi shi ɗaya ya shaa abar sa ba tare da rakiyar kowa ba , ba kuma tare da kowa ya sani ba. ( mai kowa me kome ya sani kuma yana ganin ka youssouf amm )
STORY CONTINUES BELOW
Haka suka kama hanya tare nuhu shi ke jaan motar suka keto titi tare da bullowa ta bayan kasuwa suka gangara zuwa cikin unguwar BULABURIN wacce kaf cikin garin anan kaɗai ake iya samun giyar gargajiya gangariya ƴar asali ,”
Suna yin fakin a harabar wurin da ya cika ya tumbatsa da mutane zuwa ababen hawan su sakamakon yamma da tayi ,” kiɗa yana tashi ta cikin manyan sifikokin da suke a kusurwa huɗu na zagayen filin ,ga matan banza da shigar fitsara burjik suna kai kawo cikin sigar tafiyar tallata baiwar jikin su , kowacce taci bilicin tare da izgar doki a tume a kan ta yayi tozo kamar na tsohon rakumi ,”
Juyowa nuhu yayi tare da kallon youssouf da ya lura yana ƙarewa matan wurin kallo , cikin yanayin da shi nuhu bai kai ga fahimta ba ,”amma sai ya fassara kallon da na tsantsar zalama da nuna muradi ,”
Abokina duba waɗannan ba irin naka bane waɗannan duk ajawos ne na kananan yara ,” daina ma kallon su irin naka suna daga ciki a adane ba kowa ke hayar su ba sai ire-iren mu manyan yara ,”
Yana kammala faɗin hakan bai jira cewar youssouf ɗin ba ya balle murfin motar gami da fita ,
Kutsa nan bulla ta chan suka bullo ainahin wurin da ake sayar da burkutun da mashayan ta suka tabbatar da tafi ta ko’ina inganci a cikin da’irar wajen watau ( burkutun madam saly )
Suna doso wurin youssouf ya shaƙi ƙaƙƙarfan warin burkutun ya lumshe idanu yana sake jin nutsuwa tare da matsuwar ya ji ya kwankwaɗa , dan haka ya sake sauri ,inda suka tadda mutane akan kujeru gaban tebura ,
Ɗaya daga cikin ƴan matan wajen da suke da alhakin rabawar ga masu saya wacce take raƙube a gefe ita ce ta zaburo ta nufo wurin su ,’
Tun da ta nufo su nuhu yake mata kallon sheƙeƙe , saboda sam ba ita yayi zato ba , ba kuma ita ya so gani ba ,” budurwar sa ko kuwa ace farkar sa samy baby , yarinyar da take tashe a da’irar ta su ita yake son ganin kamar yadda ta saba taryar sa kaf ƴan matan wurin sun san shi kwastoman samy baby ne ,
saɓanin ta sai yaga wata yagwalgwalalliyar ƴar yarinya tana tahowa gare su hasalima shi tun da yake zuwa rumfar madam saly bai taɓa ganin wannan ƴar ƙwailar ba ,”
Da zuwan yakaka wurin ta ɗan rage tsawo tare da tambayar su kofi nawa zata kawo musu ,” ɗauke kai nuhu yayi yana wani hura hanci domin shi gaba ɗaya ma ransa ya gama baci ,”
Biyamuradi youssouf da yayi baya da jikin sa akan kujera tare da yin ƙasa-ƙasa da idon sa tamkar dai yana gudun wani ya gan shi a wurin “,alhalin nan kuwa shauƙin burkutun ne ke kwasar sa da kamshin ta suka haɗu suka samar mishi da mutuwar jiki ,” shine ya amsa mata cikin hausar shi ta bamarɗe ,”
” Ki ɓido min mai auki kawai “
Kasaƙe yayaka tayi a tsaye cikin rashin fahimtar abun da ya faɗi ,” hasalima hausar da ake yi cikin maiduguri ma da bata da nisa ba gane ta take yi sosai ba bare fa wannan gangariyar hausar sam bata tsinci koh kalma guda ba ,”
Sake rusunawa tayi tana me sake maimaita tambayar da tayi masu cikin gurbatatciyar hausar ta ,”
Wannan karon nuhu ne ya amsa mata a fusace ,’ke dallah cewa aka yi ki kawo dayawa ,”
Sum-sum yakaka ta juya da nufin zuwa ta kawo musu,
‘conole youssouf ya bi takun kafafun ta da kallo yana saƙe ƙagauta,”
” dai-dai tahowar samy baby wacce shigowar ta kenan wurin aka yi dace idanun ta suka sauka kan yakaka tana abun da ta ayyana shi a taɗi da gwarzon ta na wannnan wattanni “conole nuhu” wanda a yanzu kaf samarin ta babu kamar shi a kuɗi da shi take tinƙaho ,”
A take wutar kishi ta ruru a ƙarƙashin ran ta ,” wata irin bangaza tayi wa kafaɗun yakaka tare da sanya tsinin dogon takalmin kafar ta , ta take mata kan yatsun ta biyu tare da tsayuwa akan yatsun kafar sannan cikin raɗa bayan ta kawo bakin ta kusa da kunnuwan yakakan wacce ta ɗimauce cikin jin azabar takun da samy baby tayi mata tace
STORY CONTINUES BELOW
,” yarinya ki kiyaye wannan ɗan itacen marmari nane zan iya kashe wacce ta shiga gona ta har tayi gigin taɓa ɗan itaciya ta ,’
Duk tsayuwar samy baby akan ƙafar yakaka biyamuradi youssouf yana ankare da hakan saboda idanun sa da suke wurin daman ,” ji yayi tausayin wacce aka takewa kafar ya ɗan kama shi wanda tun daga kan kafafun nasu ya fahimci banbancin da ke tsakanin su ,ganin kafar yakakan duk dadbare-dadbaren datti ,ga manyan tsagun faso da datti ya samu mazauni na dindin-din wanda idan aka kwatanta da kafar samy baby da take a wanke a goge sumul-sumul tashin farko za’a fahimci baiwa ce da uwargijiyar ta , dan haka yayi tunanin yakakan wani laifi tayi wa samy take hukuntata ,” sai dai duk da haka yaji haushin samy saboda shi mutum ne wanda sam baya son zalinci ,” take yaji ya tsane ta ,
Ɗago idanun sa yayi ya sauke su akan fuskar samy baby wacce idanun ta da hankalin ta baki ɗaya yake kan “ɗan itaciyar ta nuhu “😁
da sauri yakakan ta wuce lokacin da ta ji samy ta janye kafar ta tare da yin gaba ,”
Kichibis tayi da madam saly wacce ta sawo kai kallon ta sama da ƙasa madam.saly ta jefa mata,”
yanzu yaks dan ubanki ban baki kayayyaki nace ki daina yawo cikin waɗannan shegun tsunmokaran ba , ace tsawon sati kenan yau da kuka fara zuwa min nan amma shegu ƙazaman banza kullum da daƙalkalallun kaya ɗaya? Kalen ku dunga sa min kostomomi amai ? Kuna yawo yarkace yarkace uwa sabbin mahaukata ? A haka waye zai karbi abun hannun ki ya shaa ? Aaa ah ku ji min shegiyar yarinya zata min kashin kasuwa ta janyo min hasara ? Toh dan uwarki wuce maza ki je ki sauya kayan nan kamar yadda ƴar uwar ki ta sauya nata ,’idan ba haka ba a bakin aikin ki kin ji ko baki ji ba ?1
Da sauri yakaka take gyaɗa kai daga inda take rakaɓe ,”
Sake ɗaga kayan yakaka take tana jujjuya su tare da ɗora su a jikin ta tana gwada tsawon rigar wacce take ƴar ɗigil da kaɗan zata rufe mata cibiyar ta da ƴan guntayen hannu maƙale hammata , tare da ɗan siririn siket ɗin da ya shaa tsagu a gefe da gefen sa har fiye da rabin tsawon siket ɗin ,
Niyyar ta ta kaiwa falmata a ɗinke mata wuraren da suka yayyage a tunanin ta ,” sakamakon ganin kayan ƙanana ne tunanin ta sun ɗangale mata , dan haka ta yanke shawarar kaiwa ƙanwar ta ,” duk da tayi tunanin kayan zasu matse falmata kasantuwar ta ɗan fi ta kaurin jiki ,” gefe guda na zuciyar ta tana jin zata fi samun farin ciki idan falmata ta samu sauyin sutura fiye da karan kan ta ,”
Zabura tayi tare da fara kokarin zare kayan jikin ta sauya , jin motsi da tayi yana nufo ɗakin da yake zaman mallakin ƴan aikin madam saly a nan masu kwana a gidan suke kwana su kuma da suke yini su tafi anan suke cin abincin su , ita da yagana da suke duddungura sallalolin su suyi sallah a ɗakin ,” domin bayan su babu wacce ta damu da sallah cikin sauran ma’aikatan manyan su da yaran su da tsoffin su ,”
STORY CONTINUES BELOW
Juyowa tayi bayan ta sanya rigar a zaton ta madam saly ce ta leƙo ta ga koh ta shirya ,”
Karaf suka haɗa ido da ɗanliti wanda ya ɗaga labulen bayan ya tokare hannayen sa da jikin kofar yana ƙare mata kallo da jajayen idanun sa da suke cikin maye ,”
A firgice yakaka ta rarumi chukuikuyayyen hijabin ta ta suturta jikin ta “, tsaki ɗanliti ya jaa tare da ƙarasa shigowa ɗakin .,’
Aikin banza da wofi toh yarinya meye zaki boye min iyee ? Baya koh gaba ?? Baya dai kin san nima ina da shi , gaban ma idan naƴi niyya zan taso su ehe ,”
Jin tayi shiru ya sa ɗanliti buga tsaki dai-dai lokacin da yake zama a gefen wata yamutsatsiyar tsohuwar katifar da take yashe cikin babban ɗakin ,”
Ƙwaila ma irin ki me zan gani a wannan busasshen jikin naki da bana zaton koh nonon kirki kina da shi ,” duk abun da zan gani na riga na gani a jikin jigajigan manyan mata ƴan uwana ,” ya ƙarashe zance yana wani jijjiga da girgiza gwangonin kirjin sa da yake a bushe ƙaranbau,”1
Raɓar jikin bangon yakaka tayi bayan ta sunkuya ta ɗauki tsohuwar rigar ta da sabon siket ɗin , ta suɗaɗa ta fice a ɗakin tare da nufar bayan gida domin ta sa siket ɗin ,”
Bayan ta ya bi da kallo ,”
Wai sunan wata kalma”, Luwai ,” yau naga ƴar kauye da lafiyayyar farar fata luwai-luwai,”ji yadda fatar ta take sheƙi da wani ɗan uban su fari na ainahi babu algus irin na su madam saly ,” yarinyar nan idan ta samu hutu tabbas zata jaa gayu ahaayyee ,”gwara da babu ni a harkar ƴan maza ai da ganin da nayi wa bayan yarinyar nan da ace ina harkar maza da yau babu zaman lafiya,.”
Da raɓe-raɓe ta fito daga banɗakin tana tafe tana sake sauke siket ɗin ƙasa-kasa sakamakon tsagun sa da yake har ya zarta gwuiwar ta ,
Wurin karɓar burkutun suka haɗu ita da yagana da tun safe madam saly ta sata gyara mata cikin ɗakin ta ,”amma tsabar shirgin da yake cikin ɗakin bata samu damar kammala gyaran ba sai yanzu ,”
Kallon kallo suka yi da ita da yagana wacce ita ma take tsuke cikin sabuwar shigar da madam saly ta bata na wani chasasshen wondon jins da yake a ɓarƙe ta wurin cinyoyin sa da wata ƴar ɗangalalliyar riga mai siririn hannu ,” fuskar yagana ta kalla kawai ta fahimci ita ma tirsasa ta madam saly tayi ,ta sa ta sanya kayan a dole kamar yadda tayi mata ,”1
Ba wacce tace ga ƴar uwar ta ƙala suka ƙarbi manyan farantan silver da larki da hema suka ciccika musu ruwan burkutu a kofuna tare da jerawa akan farantan ,”
STORY CONTINUES BELOW
Tana shigowa ƴar rumfar ta doshi gurin da ɗazu wasu mutane biyu suka bukaci ta kawo musu burkutun dayawa ,”
Turus ta yi lokacin da ta tadda kujerun da ta bar su akai wayam babu kowa ,”
Ɗan waiwayawa tayi tana dube-duben wurin da zata hango su ,ga zaton ta kou sun sauya waje ne ,”
Sai dai jajayen idanun mazan da taci karo da su suna kallon ta ya sa nan take ta diririce saura kiris ta saki farantin hannun ta ,”fiye da rabin maxan wurin kallon farar doguwar yarinyar da take sanye cikin jaan yadin da ya sake fidda kyau tare da hasken fatar ta suke,” giyar da suka shaa suka yi tatil tana sake ƙawata musu tare da girmama musu sassan halittar jikin ta daga yar ƙanƙanuwar yarinya zuwa cikakkiyar babbar budurwa ,” nan take suka fara kawo mata wawura da chafka cikin tamɓelen su na mashaya,”
Zilliya da zamiya ta haɗa Allah ya bata ikon tsalleke farmaƙin da suke kawo mata , ” dan haka gudu-gudu ta maida tiren burkutun tare da shaida wa larki, masu neman burkutun sun tafi .
Ganin lokacin tashin su ya riga yayi “karfe biyar tayi ” ya sa ita da yagana suka nufi ainahin cikin gidan inda anan ɗaki da falo gami da banɗakin madam saly yake ,”
Suna isa kamar kullum iwar haka suka tadda cikin falon nata a cike da manyan ƴan matan da suke ji da kan su ire-iren su samy baby ,” sai karta suke da cha-cha suna yi suna haɗiyar ƙwayoyi tare da kora ruwan maganin mura da yake mahaɗin ƙwayar da suke sha ,”
Madam saly tana daga gefe zaune tsakanin wasu manyan Alhazawa biyu da alama wata magana mai muhimmanci suke yi ,”
Ɗan rakuɓewa suka yi daga bakin kofar a durkushe sannan suka sanar da madam saly lokacin tafiyar su gida yayi ,”
Kallon hadarin kaji madam saly ta watsa musu kafin ta balbale su da masifar basa ganin tana tare da baƙi ne ? Su waɗanne irin wawaye ne ?
Hakuri suka bata tare da cigaba da tsugunno nan bakin kofar suna jiran ta ta kammala da bakin nata ,”
Sai da aka kwashe fiye da mintuna arba’in har duhu ya ɗan fara shigowa karfe shidda ta gabato , zuwa lokacin kuwa har kafafuwan su sun sage duk sun muzanta tsabar gajiya .,”
Sai da suka kammala maganganun da su basa iya jin me suke faɗi daga inda suke a sakamakon hayaniyar da take sake cika illahirin da’irar wajen ,” basu ankara ba suka ji ta watso musu kuɗin aikin nasu ,”
Ga shi nan ,’ ku tabbatar gobe kun zo akan lokaci sannan ku tabbatar baku dawo min nan wajen da waɗannan shegun tsunmokaran kayan naku ba ,” idan kuwa kuka yadda kuka doso min nan wajen da wannan shigar taku uwa masu kwana akan bola toh kuwa a bakin aikin ku ,” ni bana son ƙazanta ,”ta karashe zancen tana jawo wata jakar bagco ta tura musu a gaban su ,” ga kaya nan kowaccen ku shiga bibbiyu da su nake so na dunga ganin ku ,” kun ji koh baku ji ba ???
Cikin sauri su ka amsa da toh !
Sauri-sauri suka haura tudu tare da barin unguwar suka tadda falmata wacce har ta fara gundura da jiran su tare da fara jin tsoron rashin dawowar su har zuwa yanzu da take jin hayaniya ta ragu a bakin kasuwar alamar an watse domin tun ɗazu baba modu ,”mutumin da take zama a gefen rumfar sa ,” ya tattara kayan sa tare da sauke rumfar ta sa yayi mata sallama ya wuce gida ,”
Ajiyar zuciya ta saki a take fuskar ta ta yalwatu da murmushi sakamakon jin muryoyin su yakaka ,”
Yakaka yau kun daɗe a wajen aikin da fatan dai lafiya ? Dan har na fara tsorata .
Kamo hannun ta yakaka tayi tare da sarƙafe yatsun su cikin na juna,
Lafiya lau falmata uwarɗakin mu ce yau tayi baƙi shiyasa bata sallame mu ba da wuri , kin ci abincin rana dai koh falmata ?
STORY CONTINUES BELOW
Naci gƴaɗar naira ashirin yakaka ,” ta furta hakan tare da miƙa mata ɗaurin bakar leɗar da take tara kuɗin barar ta a ciki ,”
Wannan karon yagana ce tace ,”
Gyaɗar naira ashirin ba abinci bace falmata ina ma laifin ki sayi koh ƴar awarar hamsin ,”ki daina zama da yunwa kullum muna faɗa miki ,ai yunwa tana daga cikin dalilin da yasa muka fito nema , toh me yasa zaki sake zama tare da yunwar bayan kuma akwai kuɗin sayan abincin a tare da ke ,”
Shiru falmata tayi ba tare da tace ƙala ba cikin ran ta kuwa tana sake kuɗurce niyyar cigaba da tara kuɗin barar ta , har sai ta samarwa da yakaka iya adadin kuɗin da zai isa ta jaa jarin kowacce irin ƙaramar sana’a ce da zasu iya dogara da ita ba tare da yakaka taje tayi aikatau ba ,”
Yakaka kuwa da ita ma bata ce kome ɗin ba idanun ta ne yake bisa kan wata mata da take soya doya da kwai daga gefen bakin tashar ,” sakin hannun falmatan tayi ba tare da ta amsa tambayar da falmatan take yi mata ba na “ina zata” ?
Ta nufi me sayar da doyar , ta miƙa naira ɗari daga cikin kuɗin aikin ta ɗari uku ,”ta ce a bata doya ,”
Kamo hannun falmatan tayi tare da zaunar da ita akan wani ɗan fasasshen buluk ta tsugunna ta buɗe ledar doyar tare da ɗaukar yanka ɗaya ta nufi bakin ta da shi
,”buɗe bakin ki kici zaman ki tare da yunwa barazana ce ga kwanciyar hankalina falmata , babu amfanin wuni da nake ina aikayau idan har ke zaki wuni tare da yunwa , alhalin kina zaune a bakin hanya cikin rana kina bara , na kasa baki kulawar da ta dace , rashin amfanina zai yawaita a gare ki falmata idan har ya zama na kara miki da yunwa daga yau kar ki sake zama da yunwa duk kuɗin da aka baki na sadaka ki daina ajiye ko sisi duk ki sayi abinci ki ci , ki ƙara girma ki zama ƙatuwa ko bakya so idan mama ta gan ki ta ji daɗi tare da yaba min akan na kular mata da falmata mafi soyuwa agare ta cikin ƴaƴa ??”,
Tun da ta fara maganar take taunar doyar da ta sanya mata cikin baki tana murmushi , kammala maganar ta ya zo dai-dai da fitowar ƴar siririyar dariyar da tayi jin an ambaci kalma mafi daɗin sauraro agare ta watau ” dawowar mahaifiyar su”
Nagode yakaka a kullum ina alfahari da yawan ƙaunar ki gareni ina kuma rokon Allah nima ya bani damar da zan nuna miki kulawa koh da bata kai yawan wacce kike min ba ,Allah ya bayyana mana mama tare da su baana cikin ƙoshin lafiya ,”
Su duka suka amsa da ameen har yagana da take kallon su cikin sha’awar yawan kaunar da suke yiwa junan su ,”
A gijiye likis suka dawo sansanin nasu amma hakan bai sa ,”fanna da ajus sun tsahirta musu ba domin tamkar jira suke su sanyo kafafun su cikin camp ɗin su tare su da lodin aiyukan su da ƙyuiya tare da sanin cewa akwai waɗanda suka maida bayun su ya sanya suka ƙi motsawa suyi aikin ,”1
Da ɗibo ruwa da suka tadda an tada injin yamma kenan suka fara , kafin yakaka ta ɗora da wankin kayan yaran fanne na kashi da fitsari , ita kuma falmata ta tafi aiken da ajus tayi mata wurin saurayin ta wanda shi ma a cikin sansanin nasu dai yake amma yana ta bangaren maza da yake chan-ciki inda tantunan maza yake ,”
Wannan shine karo na huɗu da ajus take aiken falmata ta karbo mata kuɗi koh kuwa ta tambayo mata saurayin nata kou zasu samu damar haduwa a wannan ranar idan dare yayi ,” wanda ita kuma sam falmata bata son zuwa wurin tantunan samarin saboda wani da bata kai ga sanin sa ba da yake biyo ta a baya ta tsakankanin manyan bishiyun darbejiyar yana taɓa mata jiki ,” yana faɗin wai tsarin jikin ta tun tana ƙarama yana da kyau ,”1
Sai dai tsoron ajus ya hana falmata tayi wani yunƙuri na samarwa kanta damar kaucewa zuwa aikin ,
Cikin sanyin jiki ta kama hanya bayan ta biya ta sanarwa yakaka wacce take ta faman gurzar wanki ta gefen ɗakunan su duk da duhun dare da ya riga ya shigo domin har an idar da sallar magariba ina shirye-shiryen yin isha’i amma su koh sallar magaribar ma basu samu damar yi ba kamar yadda a yawancin lokuta haka take faruwa sai dai su haɗa magariba da isha’i suyi tare , abincin dare kuwa ba kullum.suke samun damar ci ba saboda ana idar da magariba ake zubo shi a daka wawaso kamar yadda aka saba , su kuwa a mafi yawancin lokuta basu kammala aiyukan bautar da ake basu ba ,”dan haka zuwa yanzu sai rana ɗaiɗaiku suke cin abincin sansanin kuma basu wani damu sosai ba sakamakon suna da ƴan kuɗaɗen su a kulle ,” kou yagana da take take da damar cin abincin ma bata cika shiga cikin turmutsutsun ayi kokawar ɗibar loma da ita ba , a cewar ta daman dole ne ta sa take cin wannan cinkusasshen abincin marar daɗin ɗanɗano ,”
Tafe take tana juya jikin ta a hankali kamar yadda yake halittar jikin ta , duk da ƙarancin shekarun ta da yanzu ne ta fara fidda alamun budurci ,” amma haka halittar ta take irin matayen da suke da maɗaukakin kyaun diri da ɗan madaidaicin tsawo ,” tafiya take cikin nutsuwa baza a taɓa zaton makauniya bace ,” saboda yadda take tafe babu ɗan jagora kuma babu sanda sai dai lokaci-zuwa-lokaci ta kan ɗan lalubi hanyar wanda hakan yake babbar baiwar da Allah ya yi mata , tana daga cikin makafin da Allah ya basu ikon gani da zuci , wanda kai tsaye baza’a kira hakan da gani ba domin ba ganin suke ba sai dai wata irin baiwa ce da ɗaukakar ubangiji da ya yi musu daga kwakwalwa zuwa zuciyar su ,”
Ta tsakanin dattin ganyen bishiyar ta ratso har ta bullo a gaban tantunan da suke duk a rurrufe saboda ɗan sanyi sanyin damina uwa uba tsoron kar muggan ƙwarin damina su buwaye su , “
Tsayuwa tayi a dai-dai bakin tantin da take hasashen nasu saurayin ajus ɗin ne tare da yin sallama cikin maɗaukakiyar murya ta kwala kiran sunan sa kamar yadda ta saba ,”
Daga ciki ya jiyo tare da shaida muryar ta nan take ya fito , nan ta isar masa da sakon ajus ɗin da take tambayar neman sanin kou yau zasu haɗu su zanta ? Inda shi kuma ya faɗawa falmata ta sanar da ita shi yau bai jin daɗi .
Tana kammala jin amsar sa ta juya tare da nufar hanyar komawa , signal saurayin ajus yayi wa wani saurayi ɗan uwan sa da yake tsaƴe a gefe wanda kuma tare suka fito daga tantin ,” shafa shukurkuɗaɗɗan daddauɗan gemunsa daya saurayin yayi lokaci guda suka yunƙura tare da rufawa falmata wacce ta ɗan fara nisa daga da’irar su ,”
Ta cikin takun su da yake sauka akan busassun ganyayyakin ta fahimci akwai mutane fiye da ɗaya a bayan ta wanda bata kawo hakan a zuwan wani abu ba cikin ranta ,”
Cigaba tayi da tafiyar ta , sai dai kome ya tsaya mata ne lokacin da taji anyi sama da ita an ɗaga ta cak lokaci guda ana me sanya hannu a toshe mata bakin ta , kafin taji an zura da gudu da ita zuwa wani bigire da bata san ina bane duk kuwa da wuntsil-wuntsil da ƙoƙarin sauka da take daga kafaɗun wanda ya ɗaga ta da bata kai ga nasarar saukar ba ,,” sauke ta aka yi akan wani abu da tashin hankalin bai bari ta fahimci menene ba , kafin kuma tayi aune taji an fara ƙoƙarin raba ta da suturar ta alhalin bakin ta yana danne cikin hannunwan wani daban , an hana ta damar ihu , wani irin bugawa zuciyar tayi tamkar zata fashe lokacin da ta fahimci mummunan nufin da suke son aiwatarwa a gare ta ,”
Bugawar zuciyar ta ya zo dai-dai da na yakaka da tata zuciyar ta fara sauya salon aikinta tun daga barin falmatan gaban ta zuwa yanzu da zuciyar tayi mummunan bugawa, ” zuruf ta miƙe tare da zare hannun ta daga ruwan wankin ta kai hannayen nata duk biyu ta dafe kirjin ta ,”……!Dafe da kirjin ta da yake cigaba da bugu ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakunan kwanan mazan sansanin su , domin haka kawai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da rashin ganin ɓullowar falmata har yanzu dan haka ta tafi domin ta taro ta su dawo tare,’
Sai dai har ta cimma ɗakunan bata ga falmatan ba , sai tsirarun mutane da suke giftawa ta cikin duhuwar ,” turus ta jaa ta tsaya saƙe-saƙe ta fara yi a zuci ,”
Toh ina falmata tayi ?
Koh dai ta koma ɗakin su ne wurin ajus ?
Ganin bata ga koh alamar ta ba kuma ga shi babu wadatar kafafun mutane a wurin bare ta cigita , ga kuma duhun dare da take tsorace da shi , sai ta juyo gami da kamo hanyar komawa da nufin zuwa ta duba ɗakin su falmata ,
A sanyaye take taku saboda har yanzu zuciyar ta bata bar tsinkewa ba sai ma ƙara dukan uku uku da take yi ,”
Bata yi nisa ba ta tsinkayo wani rishi da alamun fitowar kukan da aka ƙi bada dama ya fito ,’ kiƙam ta jaa ta tsaya tare da sake kasa kunne lokacin da ta sake jin irin rishin ,” a firgice ta juya laɓɓan bakin ta suna furta sunan ,”Falmata”
Tayi diri-diri cikin rarraba idanun ta a kewayen wurin ,tana neman inda zata gan ta domin tabbas kunnuwan ta muryar falmata suka jiye mata ,”
Cikin rashin sanin gaba zata yi ko baya ta taka da gudu tare da hawa kan barandar wasu tsoffin ajizuwan da suke gefe da ita waɗanda kou rufi babu a kan su ta wasu wuraren ma sun fara zaftarewa da alamun sun zama kango ,”
Da gudu take shiga cikin ajizuwan tare da kwala kiran sunan falmata , sai dai bata tarar da kome cikin ajizuwan sai tarin bola tare da yanar gizo-gizo da tayi dafifi a ciki , cikin tashin hankali ta jaa ta tsaya daga karshen barandar da take daf da katangar makarantar , daddagewa tayi ta sake ƙwala kiran sunan falmatan , sai dai bata kai ga rufe bakin ta ba taji an ɗauke ta da wani kakkarfan mari , kafin ta farga taji an shatile kafufuwan ta , ta tafi ta baya ta faɗi ƙasa tare da bige ƙeyar ta da katangar makaranta ,
zuruf ta miƙe bata koh ji alamun zafi ba lokacin da tashi sautin muryar falmata ya fito tar cikin wani irin kukan wahala tana ambaton sunan ta a kurkusa da ita ,”
Taku biyu ta ƙara ta ci karo da ita a kwance cikin tarin busassun ganyayyakin da ake sharewa a tara a wurin ya zamto tamkar bolar zuba ganye ,”
Ɗago ta tayi ta tarairayo ta tare da rungumo ta zuwa cikin jikin ta tana yi tana waige-waigen jin ta inda waɗan da suka bige ta zasu bullo wanda take da tabbacin sune suke shirin cutar mata da falmata cikin ran ta tana jin karfin yin ɗauki ba daɗi da ko su waye domin ta tseratar da falmata ,”
Tunanin ta ya tsaya chak ! Lokacin da ta ji gaba ɗaya kukan da falmatan take yi ya gauraye da wani irin numfashi tamkar na me shiɗewa , jijjigata ta fara yi tare da kokarin tayar da ita tsaye ,tana cewa
“sannu falmata me suka yi miki ? Duka ? Kin ji ciwo ne falmata tashi muje ki shaa ruwa ,”
Rinjayar ta falmatan tayi a domin ta gaza tsayuwa sakamakon numfashin ta da yake sarƙewa , su duka biyu suka zube ragwaf a ƙasa kafin falmata tayi baya lau ta tafi zata kwanta cikin sauri yakaka ta riƙo ta kwakwalwar ta na son fahimtar me ke shirin faruwa da ƙanwar ta ?
Jijjigata ta fara yi cikin zubar hawayen da suka balle sakamakon tashin hankalin ganin falmatan a kwance bata motsi sai wani irin shiƙar numfashi take ,”
Cicciɓar falmatan take son yi amma ta kasa saboda tayi mata girma da nawi baza ta iya ba , kwantar da ita tayi ta taka da nufin zuwa ta kira mutane su taimaka mata , har ta yi taku biyu a gigice ta sake juyowa , zuciyar ta na bijiro mata da hoton gawar mahaifinta da ta bari a wuri makamancin wannan cikin “gona babu kowa ,”
STORY CONTINUES BELOW
Da gudu ta taho gami da sake durƙusawa tare da ɗago falmatan da dukkanin karfin ta , ta rungumo ta a kirjin ta , ta yunkura da kyar ta miƙe gami da ciccibar falmata da jikin ta yake a sake bata motsi , kiki-kiki ta fara kokarin jaan ta ta tafi da ita , sai dai kou taku uku mai kyau bata yi tayi tuntube da wani ɗan kankanin dutse ta baya kafar ta ta zame takalmin ta ya tsinke , suka tafi baki ɗaya suka faɗi ta baya kan falmatan ya bigi haɓar ta nan take hakoranta suka datse laɓɓan ta na ƙasa ya fashe ,”
Da hanzari ta sake sunkuyowa kan falmata hawayen ta na ɗiga akan fuskar falmatan ta ɗago ta ta fara jaan ta cikin sautin kuka ta fara ƙwalla kiran naiman taimako , domin zuwa yanzu ta fahimci mutanen da suka jefa ƙanwar ta cikin wannan mummunan yanayin da zuciyar ta taki aminta da falmatan ta mutu kamar yadda ta ga alamu , mutanen sun gudu basa wajen ,”
Da faɗuwa da tashi ta fiddo ta tsakiyar hanyar da ake wucewa , sunkuyowa tayi tare da tallafo kan falmata tana cigaba da girgiza fuskar ta ,”
Meƴe ya same ki falmata ?
Falmata ki tashi dan Allah
Ki tashi falmata ? Ki tashi
Hasken tocila ne ya fara hasko su daga nesa kafin mutanen su ƙaraso ,” tun kafin tayi magana suka yunƙuro da hanzari suna tambayar ta me ya samu ta kwancen kuma me suke anan ?
Cikin kuka take rokon su akan su taimaka su ɗauki ƙanwar ta zuwa asibiti , basu yi ƙasa a guiwa ba suka ɗauki falmatan chak tare da kai ta ɗan ƙaramin ofishin da aka tanada a matsayin ƙaramin asibitin bada taimakon gaggawa ,’
Yana zaune yana kammala shigar da wasu muhimman bayanai da suka shafi aikin sa ta computer suka faɗo masa duuu babu sallama bare neman izni ,”
Da ido ya bisu har suka shimfiɗe ta akan ɗan siririn gadon da aka tanadar domin marasa lafiya ,” suka yi tsaye charko-charko sun tasamma mutane ishirin a cikin ofishin a tsai-tsaye banda waɗan da suke daga wajen baranda da idan aka haɗa zasu kai rai hamsi duk ƴan rakiya ne ,”
Cikin nazari yake kallon su ɗai-ɗaya ta cikin farin gilashin da yake manne akan fuskar sa bayan ya rufe computer gami da tokare hannuwan sa biyu akan teburin ya ɗago haɓar sa da su , cikin ranshi yana jimanta rashin hankali da gidadanci na wasu mutanen ƙauye ,”
Chan daga waje yake jiyo tashin ƴar siririyar muryar ta cikin kuka tana ambaton sunan “Falmata”wanda hakan ya sa da sassarfa ya nufo marar lafiyar da aka kwantar da bai kai ga sanin meye ya faru da ita ba ,”
Da taimakon hasken ƙwan lantarki fari sol da ya haske ofishin ya shaida fuskar ta duk da cewa ta ɗan kunbura a sakamakon shatin yatsu da suka kwanta tar a gefen da gefen fuskar ta ta da kuma laɓɓan ta da suka ɗan kumbura ,”amma hakan bai hana shi gane ta ba ,”
Me ya same ta ??
Ita ce tambayar da ya jefo musu a dai-dai lokacin da ya ɗauko abun auna bugun numfashi ya ɗaura shi a saitin kirjin ta ,’ kallon-kallo aka shiga yi tsakanin mutanen da suke a cike a ɗakin domin duk cikin su babu wanda ya san takamaimai meye ya faru ga falmatan
Ganin sun yi shiru ya sa shi sake cewa ” ina ƴan uwan ta ?
Mutane biyun da suka ɗauko ta suka ce ƴar uwar ta tana waje ,”
” Ku ƙira ta”
Da kyar ta samu hanya ta kutso cikin ɗakin idanun ta na yararin ruwan hawaye har ya jiƙe gaban hijabin ta ,
Gaban gadon da falmatan take kai ta zo ta tsaya ba tare da ta lura da wanene likitan ba ita dai babban burin ta , ta ga falmata ta motsa tsoron ta tare da taraddadin ta kar ace mata wani mummunan abu ya faru ga ƴar uwar ta ,
Tun da ta shigo yake bin ƴar siririyar fuskar ta da kallo , daga ƙarƙashin ruhin sa yana zumuɗin kallon cikin ƙwarar idanun ta ,”
Me ya same ta ? ,”
Itace tambayar da ya jefa mata bayan yaƴi umarnin ga sauran jama’ar akan su basu wuri zai yi aikin sa , maida duban ta tayi gare shi ,”karaf suka haɗa ido ,”
STORY CONTINUES BELOW
Tiryan-tiryan ta shiga bashi labari , yayin da shi kuma ya duƙufa wurin bada dukkanin taimakon gaggawar da yake ganin yakamata ga falmata sai dai falmata bata motsa ba ,”
Zama yayi tare da ɗaukar wayar sa kira yayi tare da bada umarnin tahowa da motar asibiti domin ya fahimci matsalar falmata ta zarce ƴan kayan aikin da suke nan ,” kallon sa ya mayar ga fuskar yakaka wacce tayi jazir sakamakon kukan da take ta faman yi ,”
Kiyi hakuri ki daina kuka ƙanwar ki ta samu attack ne na ciwon ta a sakamakon toshe mata hanyar numfashi da aka yi wanda ya jawo huhunta ya wahalta kasantuwar daman tana ɗauke da cutar asthma amma insha Allah zata samu sauki numfashin ta zai dai-daita yanzu motar asibiti zata zo akai ta babban asibiti domin bata cikakkiyar kulawar da ta dace da masu irin ciwon ta sannan kuma jami’an kiwon lafiya mata su duba ta domin cikin bayanin ki ina zargin ta faɗa hannun ƴan ɓata gari ne,”
Tun da ya fara bayani yakaka take ƙara sautin kukan ta zuwa lokacin da ya gama mata bayani kuwa sosai take kuka har tana shiɗewa sakamakon ji da tayi falmata tana ɗauke da wata cutar da har sai an dangana ga babban asibiti ,’kuka take bilhakk .
Komawa yayi ya zauna tare da jingina da jikin kujerar sa bayan ya rintse ƙwarar idanun sa , saboda sosai kukan ta yake taɓa masa ruhi , gashi kuma bai san yaya zai yi da ita tayi shiru ba ,
Cikin abunda yake ƙasa da mintuna sha biyar motar asibitin ta iso aka shigar da falmata cikin motar tare da yakaka wacce taƙi fur ta saki jikin falmatan da zuwa yanzu numfashin ta ya fara komowa amma sama-sama ,
Suna zuwa babban asibitin gwamnatin jaha ,aka ƙarbe ta tare da shigar da ita ɗakin bada taimakon gaggawa karkashin ƙulawar dakta hamza da daman ya kasance babban likita ne shi a asibitin , zama dirshan yakaka tayi akan tiles ɗin wurin tare da dunƙulewa wuri guda ,bata ko damu da mutanen da ta zo ta tadda a wurin da su ma suka kawo marasa lafiyan su da kuma sauran mutane masu wucewa da suke mata kallon tausayawa ba ,
Bayan share zaman mintoci arba’in da ƴan kai , wanda yakaka baza ta iya fasalta iyakacin ruɗani da hargitsin rayuwar da ta shiga ba a ƴan mintocin , dakta hamza ya fito cikin alhini da rashin kuzarin da fargaba suka haddasa mata ta ɗago idanun ta da suka kumbura tana tuhumar sa da su domin ta gaza buɗe baki ma tayi magana ,”
Ɗan lallausan murmushi yayi tare da yafitar ta da hannu ,” a sanyaye ta miƙe tana gama hanya ta bi bayan sa zuwa cikin ainahin ɗakin ,”
Daga bakin kofar ta jaa ta tsaya lokacin da ta hango falmatan ras a zaune a bakin gadon asibitin,wata irin dariyar murna ce ta subce mata kafin ta taka da gudu ta tsalleƙe ƴar tazarar da take tsakanin su tare da rungumo falmatan wacce ita ma ta washe ƴan haƙoran tana dariya da jin sautin dariyar yakakan da take nema tun da ta farfaɗo , fuskar ta sayau da alamun rashin kuzari a tare da ita sakamakon allurorin da ta shaa har da ƙarin ruwa ,”
Falmata nah sannu , sannu sannu dan Allah me suka miki ?? Wacce irin cuta ce take damun ki falmata ciwon ki ya tsorata ni , irin tsoron da zan iya mutuwa idan ya zarta haka dan Allah falmata kar ki sake irin wannan rashin lafiyar ,” gaya min ina ne yake yi miki ciwo yanzu , meye suka miki ??
STORY CONTINUES BELOW
Dakta hamza wanda yake tsaye ya harɗe hannunwan sa a kirji yana kallon su , karon farko da yaga wata irin tsaftatatciyar zallar ƙauna a tsakanin ƴan uwan biyu ,”shi ya amsa mata dukkan tambayoyin ta .
Cutar asthma ce take damun ta , asthma cuta ce da take kama huhun mutum ya zamana huhun mutum yana kumburi tsokar huhun tana matsewa tare da rurrufe hanyoyin da iska take shiga wanda hakan yake bada matsala wurin shiga da fitar iska / numfashin ɗan adam , alamomin cutar sun haɗa da tsananin tari musamman cikin dare zuwa wayewar gari , gwarnaki , da kuma ɗaukewar numfashi ko kuma yin ƙarancin sa , ana iya gadon cutar asthma ta iyaye , ana kuma iya samun cutar ta hanyar ƙura idan tayi yawa , ko ta hanyar shaƙar iskar gas , ko kuma tsananin sanyi , cutar asthma bata da wani maganin warkar da ita baki ɗaya sai dai akwai magungunan hana samun farmaƙi daga cutar ,” sannan ya zama dole me cutar ya kiyaye kan sa daga shaƙar ƙura ,shaƙar iskar gas ,zama cikin wurin da yake da tsananin sanyi ko kuwa shan abu mai matsanancin sanyi domin bawa kansa kariya daga samun farmaƙin ciwon ,”
Numfasawa yayi yana me gauraye idanun sa cikin na yakaka wacce tayi kasaƙe tana sauraran sa idanun ta tar akan fuskar sa , lumshe idanun sa ya sake yi lokacin da ya ji wani yanayin shauƙi yana fusgar sa a sakamakon kallon cikin idanun ta da hasken ƙaton farin ƙwan wutar da yake cikin ɗakin ya haska su suke wani irin sheƙi tamkar ba yanzu suka gama ambaliyar hawaye ruwan ba ,”
Sannan ƴan bata gari sun yi yunƙurin lalata ƴar uwar ki ta hanyar yi mata fyaɗe sai dai a binciken da muka gudanar basu riga sun cimma nasara ba ,Allah ya kiyaye ta sai ku kula da gaba , ga sister zahra zata sake yi muku bayani dalla-dalla , zaku kwana anan zuwa gobe da safe muga yanayin jikin nata sai mu sallame ku ,
Duk da cewa ba duka kalmomin sa yakaka da falmata suka gane ba amma sun fahimci dai falmata tana da wani ciwo wanda yake riƙe numfashi a irin fahimtar su , sai dai daga yakaka har falmata babu wacce ta wani damu sosai saboda suna ganin ta samu sauki saboda falmatan ta bada tabbacin bata jin kome a halin yanzu lafiyar ta ƙalau sai ko ɗan rashin karfin jiki dan haka su ran su yau ƙwal zasu yi kwanan sabon wuri kwanan ƴanci , kwanan cikin haske , ga falmata kwanan kan gado da katifa duk da ba wani taushi bane da katifar asibitin amma ga falmata abun daɗi ne tun da kuwa yau ne karon farko da ta hau gado da katifa a gaba ɗaya tarihin rayuwar ta ,”dan haka da walwala akan fuskokin su suke yiwa dakta hamza godiya wanda yake bin su kawai da ido tare da gƴaɗa kan sa ,”ya kuma juya yana mai sake jaddadawa wata ma’aikaciyar jinya wacce ya kira da suna zahra akan ta tabbatar tayi musu bayanin kalmar fyaɗe tare da nisantar hulɗa da duk wani ɗa namijin da ba muharramin su ba , “wanda shi da kan sa bai san dalilin da ya sa yaji ya damu akan son su nisanci hulɗa da maza har yake jin da yana da dama da ya killace yaran , sai dai kawai ya ɗauki hakan a zuwan tausaya musu da ya fara yi da fahimtar da yayi basu da wani gata bayan Allah sai su biyun da junan su suka dogara ,’
STORY CONTINUES BELOW
Har ya taka ya nufi bakin kofar ficewa daga ɗakin bayan yayi musu sallama domin barin asibitin , sai kuma ya juyo gami da nufo wurin da yakaka take zaune akan kujera daga gaban gadon falmatan ,”
Janyo wata kujerar yayi tare da zama a daf da yakaka wacce tayi wuri wuri tana tunanin me kuma zai sake zaunar da shi ? Domin ita dai sam bata sakewa idan yana wurin wani irin nawi take ji daga ƙarƙashin ran ta da zuwa yanzu ta kasa fahimtar menene , abu ɗaya ta sani shine daga farkon haɗuwar su da tsiya suka faro ta tare da kullatar shi gami da jin tsanar sa cikin ruhin ta, sai dai daga ranar da ya fara taimakon ta zuwa yau ,ta kasa sanin takamaimai a wane mizani ta ajiye shi , ta dai san ƙwarai ta fara ganin girman sa daga haka baza ta ɗorar da kome ba bayan faɗuwar gaban da take ji a duk lokacin da idanun su suka sarƙe cikin na juna , shi yasa sam bata son kallon idon sa ,
Umarni ya bada aka miƙo masa ƴan kananun kayayyakin wankin ciwo idanun sa akan laɓɓan ta da na ƙasan ya kumbura ,”
Da kansa ya wanke mata ciwon da ta ji a sanadin dartse laɓɓan , yana yi yana kallon idanun ta da suke runtse gam a saboda ɗan radaɗin maganin wanke ciwo , a hankali kalmar , “sannu” ta subto daga bakin sa bayan da ya gama wanke mata ciwon ,yana bin fuskar ta da kallo
,” ya daina zafi ko ?
A hankali tana me kaucewa kallon idanun sa ta ‘gyaɗa kan ta ,” nagode
Miƙewa yayi ,”ki zo ki sayo muku wani abinda zaku ɗan ci a waje ,”
Tare suka jero duk inda suka wuce tsirarun ma’aikatan asibitin da suke aikin dare , sai sun isar da gaisuwar su , har suka fito bakin asibitin babu me cewa ƙala a tsakanin su ,” zaro gudan dubu ɗaya yayi a aljihun sa ya miƙa mata tare da gwada mata tsallaken titi wurin wasu mata masu toye-toye da kuma masu sayar da shayi ,
Tare da ɗan durkusawa ta miƙa hannu biyu ta karbi kuɗin tana godiya , bin bayan ta yayi da kallo har sai da ta tsallaka titin kafin ya juya cikin asibitin inda ya ajiye motar sa ya shiga gami da bata wuta ya bar harabar asibitin ,’
Bayan sun ci masa/waina tare da ruwan bunu shayin da yakaka ta sayo musu a waje , sai suka tattara hankulan su baki ɗaya ga sister zahra da take yi musu bayani dallah-dallah game da fyaɗe ta kuma tsoratar da su sosai game da yin tarayya koh wasannin banza da maza , sun kuwa tsoratu har cikin rayukan su fiye da zaton ta domin su dukkanin su biyu kwana suka yi tare da tunanin maganganun da ta faɗa musu , wanda ya sa suka ji baki ɗaya zaman sansanin nasu ya fita akan su , ga zaton falmata mazan sansanin su ne kaɗai suke iya yiwa mace fyaɗe su yi mata ciki ,”
Yakaka nikam bazan koma sansanin mu ba dan Allah mu samu wani waje mu dunga kwana koh aina ne ‘ cewar falmata kenan lokacin da gari ya waye likitocin aikin safe suka zo suka duba su tare da basu sallama bayan sun tabbatar da ta samu lafiya ,bata kuma cikin hatsari ,”
Nisawa yakaka tayi wacce itama har ga Allah bata son komawar sun sansanin su , ko kusa bata son abun da zai ɓata rayuwar falmata , duk wani abun da ya shafi falmata bata ɗaukar sa da wasa ,”
Falmata nima bana so mu koma sansanin mu , toh amma bamu da wurin zuwa da ya fi chan ɗin , bamu da kowa ba mu san kowa ba ,”
Mu tafi wurin uwarɗakin ku yakaka , mu roƙe ta , ta yadda ta bamu wurin kwana koh da a zaure ne ,
Zubawa falmata ido tayi tana juya shawarar ta ta cikin nazari , tana hasashen madam saly baza ta ƙi taimakon su ba toh amma gidan madam saly ma ai sansanin maza ne , mazan ma tambaɗaɗɗu ƴan iska , har ma gwara na sansanin su ,”
Girgiza hannun ta falmata tayi , ta ɗago ta dubi fuskar falmatan da hawaye ya silmiyo ,”
Yakaka dan Allah kar mu koma sansani , ajus baza ta daina aikena wurin ƴan maza ba ni kuma tsoro nake ji yakaka dan Allah kar mu koma ,”
Da sauri ta sanya hannu ta goge mata hawayen ,”kiyi shiru falmata baza mu koma ba ,”
A hankali suka tako zuwa wajen asibitin , duk da cewa yakaka ta so su jira dawowar dakta hamza domin ta bashi chanjin sa naira ɗari takwas da yake hannun ta , toh amma kukan falmata ya kaɗa mata hankali bata jure damuwar falmata , sai dai har zuwa yanzu da suka fito bakin titin suka jaa suka tsaya hankalin ta ya kasa kwanciya da zama a gidan madam saly tare da ƙanwar ta ,
Kamo hannun falmatan tayi ta zaunar da ita lokacin da wani tunani ya ɗarsu a ran ta ,”
Zamu je gidan madam saly mu roƙe ta mu zauna zuwa wani ɗan lokaci , sai dai da sharaɗi falmata ,
Sharaɗi ?
Eh sharaɗi falmata , gidan madam saly matattarar ƴan maza ne , ba kamar yadda kike zato bane falmata , gidan madam saly gidan ƴan iska ne , kin ga ke kuma falmata baki da lafiyar idanu zasu iya cutar da ke kamar yadda na sansanin mu suka so yi , dan haka na samo mana wata dabara , idan zaki yadda ,
Zan yadda koma menene yakaka idan har baza mu koma sansanin mu ba ,”
Zaki koma namiji falmata
Zaki koma saka kayan maza
Zan aske miki kan ki , domin ta haka ne kaɗai a yanzu zan iya kare ki daga ƴan maza kin yadda ??5
Baki buɗe falmata ta ware manyan idanun ta tana juya su a saitin wurin da take jiyo sautin muryar yakaka tamkar dai tana kallon ta ,’ !!!!
.Tafe suke su biyu akan hanyar su ta zuwa gidan madam saly , idan ba wanda yayi musu farin sani tar-tar ba , babu ta yadda za’a yi a gane falmata mace ce , sakamakon askin tal kwabo da yakaka tayi mata da sabuwar rezar da ta saya , sai walwali da ƙƴalli mummulallen kan ta yake , jikin ta kuwa sanye take da wasu afarangiya da wondo na maza da suka yi mata bururum-bururum wanda yakaka ta saya mata a kasuwar tsaye da sauran chanjin dakta hamza ,1
Fuskar falmata sam babu walwala saboda dole kawai yakaka tayi mata har ta amince kan ta ya sha askin da tun da aka yi mata shi take jin kan ta sakayau tamkar zai faɗo ga uwar ranar damina da ta fara ɗagawa “hantsi ya dubi ludayi” , wannan karon hantsin kan falmata ya duba ,”11
Yakaka nikam gaskiya bazan iya sake yadda ki min wani askin ba idan har gashi na ya sake fitowa kamar yadda kika ce ,”saboda gaskiya zafin rana tana ƙona min fatar kai ,sannan kin ga kullum a rana nake wuni a zaune ,”
Cikin tausayawa tare da ganin laifin kan ta yakaka tace ,”
Ki daure kiyi hakuri falmata ni da kaina ba’a son raina ba ne na aske miki suma ,bamu da wani zaɓi ne bayan hakan ,kina sane dai da yadda mazan gari nan suke ƴan iska ,” kiyi hakuri nan gaba bazan sake suɗe miki kai tal kamar haka ba zan dunga bar miki kaɗan ,”3
Me zai hana ki saya min hula kawai ?? Ki barmin kaina ba tare da kin aske ba idan ya so na cigaba da sanya kayan mazan a zuwan ni tamiji ce , tunda ba wanda ya san mu a gidan madam ɗin sai yagana da kolo ,”
Yakaka bata samu zarafin amsa mata ba sobada sun kawo gidan madam saly ,
Cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace kiyi shiru falmata mun zo gidan , kar kiyi wani abun da zai sa wani ya fahimci ke mace ce ,”
Fuska a turɓune falmata tace ” toh”
Tun kafin su ƙaraso ainahin cikin gidan suka soma tsinkayo muryar madam saly wacce take ta bala’i da dure-duren ashariya akan satar da ta wayi gari an ɗunguma mata har ta naira duba ishirin ,”
Ƙarasowar su ta zo dai-dai da cewar madam saly
,” kuma na rantse daga yau duk wasu ƴan zaman fara ƴan zaman alfarma su nemi inda dare yayi musu tun da abun ma ya zama haka , kayi wa mutum rana yayi maka sulusin dare , ji min ganin arhar gabas ? daga yau babu shegiyar ƙaramar karuwa da zata sake kwanan min cikin gida kun dai ji na rantse ai daman kome aka yi da sabara sai ta yi kere,”2
STORY CONTINUES BELOW
ta karasa tana sake shigar da mici-micin idanun ta da suka yi jaa domin bala’i !
Duk da yakaka ba duk kalaman madam saly ta kai ga fahimta ba , amma ganin ta cikin maɗaukakin bacin rai ya haka , yayi matuƙar tsorata ta tare da dukushe mata ƴar ƙwarin guiwar tunkarar ta da batun dawowar su zama a wurin ta ,”
A fusace ta juya ga su yakaka lokacin da taji yakakan tana gaida ta bayan ta ɗurkusa guiwar ta biyu a ƙasa ,”
Ba tare da ta amsa mata ba ta maida ganin ta kan falmata wacce take tsaye kiƙam tana jujjuya idanun ta kan nan sai sheƙi yake tare da ɗaukar idanu.,’
Wannan ɗan ƙolon fa ? Shi kuma daga ina ??9
Cikin sanyin murya da inda-inda yakaka tace” ƙani na ne ” tana mai sanya hannu ta jawo hannu falmata ta ɗurkusar da ita ,”
Ina kwa…..
Ko kafin falmata ta ƙarasa kalmar gaisuwar da ta ɗauko nufin yiwa madam saly , tsawar ta ta katse mata hanzari ,”
Miƙe miƙe maza-maza ka kama gaban ka , ka tafi barar ka ni nan bani da buƙatar irin ku , ke yaks ɗan uwar ki wane ɗan iskan ne yace ki kawo min ƙanin ki nan ? Ko nace miki ina bukatar almajiri ne ? Oya kama hanyar ka kayi tafiyar ka kwa haɗu a mahaɗar ku kar na sake ganin ka a gidan nan ,”
Gaba ɗayan su sun firgita da tsawar da tayi musu musamman ma falmata wacce kalma korar da aka yi mata ta sanya ta jin ruwan hawaye ya fara taruwa a gurbin idanun ta ,”
Madam kiyi hakuri , shima na kawo shi ne ko akwai aikin da zai dunga yi miki ,?
Aikin ubanki wannan ɗan tatsitsin yaron zai min ? ,”
Kai tashi kayi naka guri nace ,” ta furta hakan tana zazzarowa falmata ido ,wacce dirin muryar madam saly cikin faɗa duk ya bi ya diririta ta tare da dasa tsoron ta cikin ran ta anan take har ma ta ji ta fara nadamar zaɓar gidan ta a matsayin wurin mafakar ta ,
Cikin muryar kukan da ya bayyana kansa yakaka tace ,”
Makaho ne madam dan Allah ki taimaka mana ki bamu wurin da zamu dunga kwana wallahi zan dunga yi miki aiki daga safe har dare koh baki biyani ba ni dai kawai ki taimake mu ni da ƙani na ki bamu wurin kwana ,?
Kallon hadarin kaji madam saly take yi ma ta ,”
Yau ji min gantalallun yara ke yanzu ni ce zan baku masauki ke da musaƙin ƙanin ki ?? Dan uban ki yaks kin ga gida na yayi kama da masaukin baƙin ƴan gudun hijira ?? Ciki ma har da muskinai ? Ke ma ai kin sa wanan abun bazai yi yu bane “auren mage da ɓera ” an faɗa miki nan gidan sarkin unguwa ne koh kuwa gidan mai gari ?? To bari kiji ni bani da wurin ajiye ke kan ki bare miskinin ƙanin ki , toh na ci uwar me da ku ??gayyar na ayya gayyar tsiya gayyar ƙwarƙwata da tsumma, dan aikin da kike min daga na ɗaga murya nayi cigiya zan samu madadin ki , dan haka tun wuri ki maida ƙanin ki inda kika ɗauko sa ,ki zo ki kama min aiki na , kina cin lokacin aiki kin kuma san dai doka ta ban yadda da asara ba ,”
STORY CONTINUES BELOW
Ɗan liti wanda tun shigowar su yake tsaye a gefe ya kafe yakaka da falmatan da idanu ,yana nazarin ɗan dirarren yaron mai ƴar kyakkyawar zagayayyar fuska da yakaka ta kira da kanin ta ,” yayi charaf ya chafe zancen jin ana shirin korar masa hanyar samun abebaɗan arziki !3
Haba haba madam saly tayaya arziki yana bin ki kina guje masa ,” kuma ai a so kare har bindin sa !
Ya furta hakan yana farfari da ido
A harzuƙe madam saly wacce ta koma daga bakin kofar ɗakin da ƴan matan ciki ke tattataro ƴan kayayyakin su suna fitowa ta juyo
,’ waɗan nan ne hanyar arzikin liti bana son ƙazamar kalma,” wai me kuke jira ne ?? Ta wurga tambayar ga yakaka wacce zuwa lokacin kuka take yif-yif suna durkushe cikin rana ,”
Ke dai mutuniyar mu sanya labule ki ji bayani , kiji nufi na kar ki yanken hukunci baki ji hujja ta ba ,!”idan ban da abun ki ai Abun da ke ga amarya shi ta kan ba ango ” Ya furta hakan yana jan hannu madam saly wacce take wurga masa harara ,tamkar idanuwan ta zasu faɗo ,”
Bayan shuɗewar mintoci sha biyar madam saly da ɗan liti suka dawo ,”
Ke yaks na yadda ki zauna anan tare da su larki a ɗakin su , zasu ɗan matsa miki wajen kwana domin wannan babban ɗakin kulle sa zan yi , ƙanin naki kuma zai bi ɗan liti su dunga kwana tare idan ya so kullum da safe ya dunga zuwa nan yana min wanke-wanke kafin ya tafi barar sa ,” daga yanzu bazan biya ki ko sisi ba domin zan dunga ciyar da ku sau uku a rana da ke da ƙanin naki ,idan kin yadda toh idan kuwa baki yadda ba sai a bi wani sarkin ,!
Ba tare da tunanin kome ba yakaka da falmata suka amince bayan sun bi ɗan liti da madam saly da doguwar godiya tare da addu’o’i ,2
Toh sai ƙanin naki ya biyo ni yaga ɗakin kwanan koh ? duk da dai ba gani yake yi ba amma ya ɗan tattara wajen da zai sa ƴan haƙarƙarin sa ,” ni ya ma sunan sa ne ??
sunan sa kachalla !
Ah kachallari ne toh tashi zo mu tafi mikon hannun ka ,”3
Tare da rashin sakewa falmata ta jefa hannun ta cikin na ɗan liti , wanda ɗumi tare da laushin fatar hannun falmata tuɓus-tuɓus , suka nemi ruɗar da shi a karon farko ,”1
STORY CONTINUES BELOW
Da ido yakaka ta raka su cikin ranta tana fatan Allah ya sa madam saly ta zamto gatan su ,!
Kichibus yagana suka yi ita da su falmata wacce ɗan liti ya matse mata hannu gam cikin nasa yana ɗan luguiguitawa , a ɗan fisge ta dube su tare da gaishe da ɗan liti sai dai kuma fuskar falmata da ta gani a fisge ya sanya ta sake waiwayowa da zabari sai dai bata ci nasarar sake kallon fuskar yaron ba sai bayan sa ‘,
Tana shigowa ta ci karo da yakaka cikin mamakin ganin ta a wurin aikin tare da alhinin abun da ya faru da su a daren jiya wanda duk a zaton ta har yanzu su yakaka suna asibitin ne ta kamo hannun yakaka ,
Yakaka ya jikin falmata ??tana ina ? Ta samu sauki da fatan babu abun da ya same ta ??
Sai da yakaka ta ɗan hah-hanga ta ga babu kowa a cikin rumfar da suke saida burkutu wanda a halin yanzu take kan tattarawa tare da goge gujeru da teburan da masu saye ke zama ,” tace
Yagana jikin falmata da sauki , kuma a halin yanzu tana gidan nan mun taho tare , yagana dan Allah ki rufa mana asiri domin a saboda abun da ya so faruwa ga falnata jiya mun bar sansanin mu mun dawo nan gidan da zama sai dai a matsayin falmata namiji , zaki ganta cikin shigar maza da askakken kai tana amsa sunan kachalla , domin Allah kar ki faɗawa kowa ita mace ce kin ji ? Ki rufa mana asiri !
Tare da maɗaukakin mamaki yagana take kallon ta ,
falmata ta koma namiji kuma ??kuma kun dawo nan gidan da zama ? Anya yakaka wannan hanyar mai billewa da kyau ce ? Kin san fa gidan nan cike yake da ƴan iska da ma unguwar baki ɗaya , ke da kan ki hatsari ne kwanan ki cikin gidan nan kina dai ganin yadda da ƙyar muke kwatar kan mu a hannun ƴan iskan nan idan suka sha kunun madam saly , ni a ganina gwara mazan sansanin mu basa shan wannan ruwan da ke fitar da mutum a hankali ya sa hauka, ni dai idan har kin ɗauki shawara ta ku koma sansani duk lalacewar sa yafi nan ,
Yagana falmata tace baza ta koma ba , ta riga ta tsorata , sanin halin mazan gidan nan ya sa na ɗauki matakin mayar da falmata namiji domin kare ta daga idanun su ,”
Katse ta yagana tayi ,”
Toh idan kin kare falmata ke kuma fa ?? Bakya tsoron su cutar da ke ??
Ɗan murmushi yakaka tayi ,”
Zan iya sadaukar da kome nawa domin na bada kariya ga falmata , falmata miskiniya ce bata da kowa daga Allah sai ni ,” ki mana addu’a kawai yagana kuma ki rufa mana asiri ,’
Kallon ta yagana tayi na ƴan dakikai ,
STORY CONTINUES BELOW
shikenan dan ta ni kam baku da matsala koh cewa kika yi kar na nuna na san falmata bazan nuna ba , me ma kika ce sabon sunan ta ??
Kachallah
Kachallah , ta maimaita
Suka haɗa ido gami da kwashewa da dariya , ga alama zuciyar yakaka ta samu ƴar nutsuwa a karon farko tun bayan barowar su garin su .
Niamey Niger
Yau kwanakin su siyama da gnala goma sha huɗu wanda kuma a gobe ne suke da niyyar komawa maraɗi saboda hutun da ta ɗauka a wurin aikin ta gobe yake ƙarewa ,
Zaune suke a ɗakin ubboh wacce ta kama kan siyamar tana kitsewa kamar yadda ta saba yi mata tun siyamar tana ƙanƙanuwa ,har ɗan tasawar ta kafin a aurar da ubboh ,”
Ho addah ke kouwa yaushe ne zaki bar mini kitson hittoɓe ? Haba mana adda baki ganin na girma da wannan kitson ??
Ɗan murmushi ubboh tayi tana me kallon fuskar siyama da ta shagwaɓe fuskar ta ta jikin mudubi ,”
Kauna ta kin kouwa san yadda kitson hittoɓe yake fidda kyauwou tare da cikar surar ki ?? Na kou jima ina faɗi miki babu kitson da ke haska ki yaa shi ina mai tabbatar miki akwai wani sirri cikin kitson ga ki riƙe shi da kyawou har gidan amren ki,”
Shiru siyama tayi domin ubboh ta fama mata ciwon da ke nuƙurƙusar ta cikin rayi ,” da nazarin sauyin da ya bayyana akan fuskar ta ubboh ta tsaida kitson da ta fara yi ,”
Ban san yauhe ne munka fara ƴar haka da ke ba kaunata ,?? Yauhe ne kin ka fara boye mini damuwar da ke a zuciyar ki ? Yanzu duniya da gaskiya siyama kina da ƴar uwa da ta fice ni ?? Tuno da kusancin da ya wanzu tsakanin mu tun tsawon lokacci shin kou kuowa dai matsayi na ya sauyu gare ki ?
Juyowa siyama tayi ta fuskanci ubboh , fuskar ta da alamun rashin jin daɗin maganganun ubboh ,”
Kou kussa adda matsayin ki gareni wallah basshi sauyuowa , ke kou me zai sanya ki wagga irin tounani adda amm ??
Shafar fuskar ta ubbo tayi ,” cikin ranta ƙaunar siyama na sake linkuwa,
Tun zouwar ki nan wurina na fahimci kina tare da damuwa amma juyin duniya nayi da ke ki faɗi min me ke ad damun ki kin ki faɗi mini toh ƙaƙa kike so in yi da rayi na ? Shin kou kuwa dai a chan gida an ka bata miki rayi ??
STORY CONTINUES BELOW
Ajiyar zuciya siyama tayi domin ta ga wannan ce damar da zata yi amfani da ita wurin fidda abun da ke boye cikin ran ta , sake marairaice fuska tare da shagwaɓe ta tayi bayan ta karya wuya ,”
Adda amm ni kam ban san dalili guda wadda ya sa hamma youssouf ya ƙi jini na ba , tun tasowa ta nake hangen ƙiyayyar da ke mini cikin idanouwan sa
Da sauri ubboh ta kai hannu ta ɗan make bakin siyamar , tare da maɗaukakin bacin rai akan fuskar ta tace ,”
Wanne irin kalami kike haka ga ɗan ouwan ki siyama ? Shi youssouf ɗin ne basshi ƙamnar ki ? Ƙaƙa kin kai ga fahimtar hakan ,? Ƙou kouwa shi da baki nay ya furta hakan gare ki ? yi samri ki sanar da ni ƙaƙa anka yi wagga mummunan tounani ya kai ga ɗarsuwa cikin rayin ki ?
Hawayen da daman suna kurkusa sune suka samu dalilin ballowa da gudu akan kumatun siyama ,” cikin ranta tana faɗin “ayi a ƙare yafi a bari sai gobe ,”
Hamma youssouf bai ɗaouke ni matsayin kauna gare shi ba , har ya gaza boye hakan a gare shi Shi ɗai , sai da ta kai ya bayyana ga bayun masarauta agades , inda ya danganta ni da baƙuwa garai a gaba gare su ,”sun ka maishe ni marar muhimmanci ga har ta kai bayun sun nemi taka ni ,’
Cikin takaicin jin abun da youssouf ɗin ya aikata ga ƴar lelen ta ubboh tace ,”
Yi shirun ki kaunata ki kuma daina wagga mummuna tounani , youssouf yana dawouwa ya iske ni nan cikin gida na zan kuma yi masa magana , yo a rabe magirbin yakuwa ne da na rama ?? Bar ni da shi ,”
Cikin sanyin murya da cikin ran ta ba haka ta so ba , tace
Adda kar ki masa faɗa bissa dilili na bani son ko ƙaƙa ran sa ya baci a sanadiyya ta , bacin ran sa ba zaya dadaɗa mini ba ,”
Cikin son fahimtar abun da ta hango tattare da siyamar ,”ubboh” tace
Ke ko ƙauna ta faɗi min gaskiya ƙou kouwa dai son hamman naki kike ?? Kou amren dangin kike so ?
STORY CONTINUES BELOW
sunkui da kan ta tayi a lokaci guda tana wani ɗan kyakkyawan murmushin da tun zowar ta ubboh take son ganin irin sa a fuskar ta , kamo haɓar ta tayi ta ɗago fuskar ta ,tana dariya tace
“ni ƴar uwa nake gare ki bai kyautu ba ki boye min kome idan Allah ya yarda youssouf sai ya zama miji gare ki , ina bayan ameren ku ɗari cikin ɗari , ai ba domin lamurran sa da wagga ɗiyar buzouwa ya kankama ba ai da ba’a bawa dawa ba gida ba ta ƙoshi ba ,” ki kauda wagga mummunan tounani naki , youssouf ɗan ouwan ki ne kuma zai zamto miji gare ki bisa yarda Allah , ki samu kusanci da shi , kin ji kou ? Ni zan yi maganar ku da hajiya umma ,”
Cikin matsanancin farin cikin da siyama ta gaza boye shi ta miƙe bisa kan guiwar ta tare da rungume ubboh wacce ke zaune bisa bakin gadon ta na alfarma ,” zuciyar ta cike da farin cikin da ta daɗe rabon ta da jin irin sa tamkar dai ubboh ta riga ta ɗaura mata aure ne da biyamuradi youssouf ɗin ,”
Nagode nagode nagode , kawai ita ce kalmar da take fitowa bakin ta saboda ta gaza doguwar magana
Cikin sanɗa saɗaf-saɗaf gnala ta koma da baya wacce ta taho domin kawo wa siyama lamurjen da ta sanya ta haɗa mata , ta zo bakin kofar ta tsinkayi tattaunawar su da ta jaa hankalin ta har ta tsaya daga bakin kofar ta ji kome ,”
Sai dai kan ta ya ƙulle ashe daman siyama ba ƙanwa take ba ga biyamuradi youssouf ??ashe kishiya take ga uwargijiyar ta ? To amma ya aka yi gimbiya maimouna bata kai ga sanin hakan ba ??
Jikin ta har rawa yake lokacin da ta mayar da lamurjen ɗakin girki tare da komawa cikin ɗakin da aka yi mata masauki ta murza ɗan makulli , cikin ujila ta fiddo wayar ta tare da danna kiran uwargijiyar ta tana me zumuɗin sanar da ita wannan labarin , domin tun zuwan su sau uku gimbiya maimouna na kiran ta a waya tana tambayar ta ko akwai wani labari koh sun koma maraɗi ??ita kuma Tana shaida mata har yanzu suna niamey ɗin kuma bata ci karo da wani abun da ke bukatar fashin ɓaki ba ,”sai tsantsar ƙaunar da ta fahimci tana tsakanin ƴa da ƙanwar, wanda gimbiya maimouna ta gwatsale ta tare da cewa bata tambaye ta wannan ba ta kuma sake gargaɗin ta tare da jaan kunne akan ta kula da abun da ya kai ta kaɗai ,!
Sai dai har wayar ta gama karaɗin ta daga chan wurin gimbiyar bata ɗaga ba , “tana kuma jin tsoron sake kiran ta kar tayi laifi , dan haka ta maida wayar tare da dasa zaman jiran kira daga gimbiyar ,!3
Maraɗi
Lokaci yayi kusa da zaki iddasa aykin da kin ka faro shi saratu , koh kin manta cikin watan ga mai kamawa youssouf yake cika shekarun sa talatin cif ne ? Kou kouwa dai kin manta da abun da zai faru a ranar zagayowar haihuwar sa na cikon shekarun sa talatin ,
Ban manta ba hajiya uwa ba kuma zan manta ba tou ƙaƙa ma za’a yi na mance wannan lokaci ?bayan shi zai zamto shiri na na karshe akan tarwatsa rayuwar safiyyah tare da duk wasu masu ƙaunar ta ??
Ke dai Allah shi kai mu karfe 23:59h na ranar goma ga wattan biyu ,”