MAFARI CHAPTER 6 BY UMMU AZAMM
Www.bankinhausanovels.com.ng
A tsorace suka juyo , yakaka tayi arba da wani mutum jikin sa sanye da shuɗin kaya hannun sa ɗaya rike da wani ƙaton kulki , gefen sa kuwa wannan mutumin da take zaton sun yi masauƙi a bakin shagon sa ne+
Nan take ran ta ya aina mata , “, ya ƙira musu jami’in tsaro ne ,” dan haka ta matso falmata gami da sake riƙe hannun ta ƙam-ƙam ,
Daga chan inda yake tsaye yace !
Su waye ku ?
Kuma daga ina kuke ?
Meye kuma kuke tafe da shi a baccon hannu ku ?kuyi gaggawar sanar da mu kafin naje na kira sojoji .

Mukut ! Yakaka ta haɗiye yawun tsoro .
Mu mune su falmata kuma mu ƴan gudun hijira ne daga ƙauyen mairambiri , kayan mu ne a cikin bacco .
Falmata ta amsa musu cikin dakiya .1
Wanne irin kayan ?
Kayan sawar mu .
Suka haɗa baki wurin amsa masa !
Ku buɗe mu gani ?
filla-filla suka yi da suturun nasu , ba tare da gardama ba .
Meyasa kuke yawo da kaya ? Ina ne sansanin ku ? Bai kamata kuna yawo da jakar bacco ba saboda kun san halin da gari yake ciki ba’a yadda da duk wani mutum da aka gan shi da kaya niƙi-niƙi kuma yana nuƙu-nuƙu a cikin taron jama’a bare ma ku yara mata ga kuma irin yanayin ku , kowa ya gan ku dole zai zarge ku har ma ya tsora ta , saboda yadda mafi yawancin lokaci ake amfani da ku ta hanyar rataya muku nakiyar bam ku shiga taro ku tayar ,
Ku godewa Allah ma lokacin da na gan ku a bakin shago na ba jami’an soja ko na ɗan sanda na kira ba mai gadin kasuwa ne , da ace ɗaya daga cikin jimi’an tsaro ne da sai sun hukunta ku dan haka nake baku shawara da ku koma sansanin ku , ku ajiye wannan jakar kayan naku sannan idan ma zaku shigo gari harkokin ku sai ku shigo , yawon ku a haka hatsari ne ga rayuwar ku ,!1
Duk wannan dogon bayanin da mutumin nan yake musu yakaka ta zurfafa cikin tunani , jin ya ambaci komawar su sansanin ƴan gudun hijira ,”
Cikin ran ta ta ƙudurce baza su koma sansanin su ba , saboda tun bata tare da ciki ma ƙuƙaƙƙiyar wahala ce zaman sansani ƴan gudun hijira , sanan ga tozarci uwa uba fyaɗe da ake yi wa mata , to bare fa yanzu da take ɗauke da cikin da bashi da uba , ta koma sansanin su a gan ta da ciki ,? Tace aina ta samo shi ? Alhalin duk wanda ya san ta ya san ta ne a matsayin budurwa wacce bata taɓa aure ba ,3
ai ta tabbatar fanne baza ta bar ta ta kurɓi ruwa ba zagi da aibatawar da zasu dunga mata sai ya samar mata da cuta , dan haka gara sun hakura da zaman sansanin sun nemi wani wurin fakewar ,”
Da wannan tunanin ta ɗago kan ta ta dubi mutumin , da taji falmata na bashi amsa da cewa
Sun ɓata ne sun kuma manta sunan sansanin su .
Malam dan girman Allah ka taimaka mana ka samar mana da wurin da zamu dunga kwana , ” bamu da kowa a garin nan mamar mu da ƙannen mu sun ɓata tun a ƙyauyen mu baban mu ya mutu , mijina ma ba’a san inda yake ba ,”
Ta ƙarasa zancen tana mai sunkui da kai domin gujewa kallon rashin yadda da wannan mutumin yake jifan ta da shi ,” cikin ranta kuwa kunyar sabuwar ƙaryar da ta gilla take yi ,7
Saitin inda take jin tashin sautin muryar yakaka , falmata ta maida fuskar ta , cikin ran ta tana mamakin yaushe su duka suka koyi ƙarya ? ?3
Shiru yayi yana nazari , kwarai zai so ya taimakawa yaran ko dan kasancewar su mata , duk da cewa cikin ran sa ba wai ya gama aminta da zantukan su bane gaba ɗaya ,
toh amma shi ya san ba ƙaramar fitina zai tadawa kan sa ba muddin ya ɗauki yaran nan ya kai su gidan sa ya jefa su tsakanin matan sa uku ,” yana da tabbacin sai an dafa su da ran su , shi kan sa ruwan gidan sai ya gagare shi shaa da kwanciyar hankali , dan haka da muguwar rawa gamma ƙin tashi .3
Story continues below
Yarinya ni bani da wajen da zan kai ku , ku samu wurin kwana saboda yanzu duniya ta lalace ba’a saurin yadda da mutum . Alfarma ɗaya zan muku shine na yadda duk lokacin da dare yayi muku kuna tsakanin nan bakin kasuwa ku gangaro cikin rumfa ta ku kwana bazan hana ku ba ,’ har ma tabarma zan ajiye muku , bayan na sanar da masu gadin kasuwa wanzuwar ku awurin kun ji ko ?
Ya furta hakan yana danne yanayin da yake ji na rashin kyautawa yana taso masa , ya san ba haka ya kamata yayi musu ba yasan taimakon da suke nema ya wuce wannan yasan bai ji tausayin su bai kuma basu kariya ba , toh sai dai yana jin iyakacin taimakon da zai iya basu kenan ,4
Ga mamakin sa godiya suka dunga sauke masa kwando-kwando tamkar wanda ya basu wurin kwana a ƙuryar gidan sa , hakan ya sa tausayin su ya sake baibaye shi ,”
Ku dawo da jakar kayan ku ajiye cikin shago na ,” kuma ku tabbatar kafin cikar karfe huɗu da rabi kun bar duk inda kuke kun dawo kun amshi kayan ku domin ni karfe huɗu da rabi nake rufe shago ,”
Cikin daɗin rai yakaka ta kawo falmata dai-dai wurin da take zaman barar ta ,’ ta ajiye ta bayan sun gaisa haba-haba da ɗan dattijon da yake sayar da kayan miya a gefen wajen wanda suka tarar da shi yana fidda kayan lambu ɗangin su yakuwa , alehu , zogale , rama da sauran kayan lambu yana shirya su akan ɗan teburin sa ga alama bai jima da isowa ba , har yake jajen kwanaki da dama baya ganin falmata ,”
Nan suka ce hana su fitowa aka yi daga sansanin su ,”
Falmata ga naira ɗari ki sayi wake da shinkafa da salat ki ci anjima da rana , kar ki ce zaki zauna da yunwa kin san bana so ,” kuma kar ki tafi ko’ina , nima ba nisa zan yi ba zagayen kasuwar zan kewaya ko Allah zai sa na samu ko dako ne nayi na ɗan samo mana ƴan kuɗi kin ga ƙarshen kuɗin hannu na ne ɗarin da na baki , bayan ita bamu da ko sisi ki kula da kan ki sosai kin ji kou ?2
Naji yakaka
ta furta hakan tana mai miƙewa tsaye daga kan ɗan dutsen da yakakar ta ajiye ta , gaban ɗan teburin mai kayan miyan ta ƙarasa
Baba ɗan Allah ko zamu samu chanji ? Tana mai miƙa masa gudan ɗarin ,
Ƙarɓa yayi , ya bata hansin biyu ,ta ƙarba tare da lalubar hannun yakaka ta danƙa mata gudar hansin ɗaya ,4
Idan kin bani duk kuɗin ke kuma da me zaki ci abincin anjima ? Kin fini buƙatar abinci yakaka , ke da baki da lafiya ,kar kiyi aikin wahala da yawa wanda zai sa ki samu matsala , idan kin shiga matsala ni kuma yaya zan yi yakaka ? Dan Allah ki lallaɓa kan ki , kuma ki dawo da wuri ,”2
Toh madam falmata
ta furta hakan tana murmushi jin yadda falmata ta zage tana bata umarni kamar dai ita ce babba .1
Hanya ta miƙe tana tafe tana raba ido cikin fatan son ganin inda zata ɗan samu wani aiki ta je ta kama ko da ba’a sa ta ba , amma har ta kai kan gadar kasuwar bata ci karo da wani wajen da ake buƙatar ƴan aiki ba , hasalima yanzu ne ƴan kasuwar suke kan buɗe shagunan su , tare da fito da kayayyakin sana’o’in su ,”
Har ta yanke shawarar komawa wurin falmata ta ɗan jira zuwa anjima , sai idanun suka hango mata mattatarar masu niƙa a ƙwarin gadar ,
Sai ta yanke shawarar ta ƙarasa wurin ƙila ta samu aikin yi tun da ta hango wajen a cike ,”
Gangarawa tayi ta sauka wajen , ga mamakin ta masu injinan niƙa ne birjik ta ko’ina a wajen , ƙarar inji kuwa ba’a cewa kome domin ko maganar na kusa da kai baka iya ji sai fa idan yayi ihu ,’1
Da gudu ta ga wasu ƴan matasan yara maza da baza su gaza falmata ba sun nufo ta ,”
Yaya ta niƙa ne ? Ki kawo na kai miki injin mu yau yau muka kai faifan injin washi , laushi luƙui za’a miki ,
Yaya ta injin su mutuwa yake ana cikin niƙa , anjin mu yafi lafiya kuma ga arhar niƙa ,”
Ita dai da ido take bin su da kallo ba sosai take fahimtar su ba , saboda ƙarar injin da ya cika mata kunne ,
Story continues below
Ita ma da ɗan karfi ta amsa musu
Ba niƙa na kawo ba , aiki nake nema ,
Haɗa ido yaran suka yi suka kwashe da dariya , suka maimaita
Wai aiki take nema ? kut wannan ƴar na’u ce ita ma .
Juyawa suka yi suka bar ta nan tsaye ba tare da sun bata ansa ba .
Har sun ɗan yi nisa sai kuma ɗayan ya komo ,
aikin tankaɗe dusa kike nema ??
Batare da ta kai ga fahimtar sa ba ta gyaɗa kai ,
Zo muje injin abokin yayana jiya sun ɓata da mai yin tankaɗen dusar sa ,
Da murna yakaka ta bisa a baya har wata ƴar siririyar hanya , bayan ƴar gajerar tafiya suka bullo a wani babban fili faffaɗa , saɓanin injinan da ta tarar a waje waɗannan manyan injina ne girkakku , ƙaran su mai matuƙar karfin har diri yake a cikin ƙasa ,”
Gaba yaron yayi zuwa wurin wani da yake tsaye a gefen ɗaya daga cikin injinan yana juye hatsi a cikin injin bayan ya gwamtsa shi da ruwa .
A kunne yayi masa maganar yana mai nuna yakaka da ɗan yatsan sa ,”
Bayan sun gama magana ya dawo wurin yakaka ,’
Yace wai shi ba zai biya ki ko sisi ba dusar da zaki tara ita ce ladan aikin ki ,” kin yadda ?
Cikin sanyin jiki yakaka ta gyaɗa kan ta , “bata da zaɓi ! Amma cikin ranta tana tababar ta yaya dusa zata zama ladan aikin ta me zata yi da dusa toh ? Ko suna nufin ta ci ??
Bayan yaron ya faɗa masa amincewar yakaka , da kan sa ya taso ya zo inda take ,
Keh yane ƴar na’u ? Kin gane ne aikin yana da yawa dan haka zaki samu alheri , ina ga nima har sai kin ware min wani abu a ciki , ya ƙarasa zancen yana kwashewa da wata hautsinannan dariya ,
Biyo ni na nuna miki aikin ,
Cikin wata babbar rumfa ya kai ta , wacce take cike da mata tsoffafi da ƴan mata irin ta da ma waɗanda suka fita , wasun su a tsaye suke suna faman zirta hatsi , masara , dawa , alkama , a manyan-manyan turamen da suke watse a cikin rumfar , wasu kuma suna zaune a ƙasa suna ta faman bushe abun da suka zirtan , suna tara dusar a buhun gefen su ,”
Wani babban buhun masara da na hatsi ya nuna mata ,”
Ƴar na’u wannan ne aikin ki yau ake so , kiyi aiki mai kyau dan gaba a neme ki , kuma banda waskiya ai kin gane ? idan masu shi suka kama ki kin waske musu abun su , suka ciya miki ni babu ruwa na ai kin gane ko ?
Na gane
Toh ki zo mu je na baki aron faranti dan naga baki da shi , kuma waɗannan ƴan ciki baki baya kwalta ne , ba baki aro zasu yi ba !
Zungui zungui ta bishi a baya ,’
Daka da surfe ba sabon abu bane wurin yakaka , toh bare wannan da zirtawa ne ba surfawa ba , manyan injinan su ke yin surfe ,” nan take ta kama wani turmi da ta ga babu kowa akan sa , ta ɗauki wata ɓasgararriyar taɓaryar da take jefe a gefe ta kama aikin ta babu tsayawa hira , to ma wa ta sani a wurin da har zasu yi hira?? Babu !1
Kafin la’asar yakaka ta zirce hatsin da masarar tas , ta hau bushe dusar har da gyarawa , la’asar lis ta gama ta tara dusar daban-daban fiye da rabin buhu kowannen su , iyakar gajiya ta gaji , ga yunwa ga kishirwa , nan gefen ɗan buhun ta samu ta zauna tana mayar da numfashi , dayawa daga matan sun gama aiyukan su suna zaman hutawa ,’
Ba’a jima ba masu kayan suka zo ɗauka ƙarƙashin jagorancin “ubangidan ta “mai surfen , nan suka duba kayan su ,” yakaka ta jawo buhun dusar ta nuna musu ,
Ɗan saurayin da ya zo ɗaukar kayan ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata ya ce ta haɗa da dusar ta riƙe kamar yadda suka saba ,
Da murnar ta ta sanya hannu biyu ta ƙarbi kuɗin , cikin ran ta tana tambayar kan ta toh ita kuma me zata yi da dusa ? Ina zata kai ta ?
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga wasu dattawan maza da mata sun fara shigowa , da gudu ta ga kowacce mace tana surar buhun dusar ta tana kaiwa gaban su ,” wannan tace tata ta masara ce , wannan ta ce ta hatsi , wannan ta dawa , alkama , su kuma suna tambayar kwano nawa ne ?? ko kuma daro nawa ?? Sai ta ga an fara cinikin dusar , ita dai tana tsaye tana bin su da ido cikin son fahimtar abun da suke ,
Story continues below
Kafin kace meye wannan tas mutanen sun gama saye dusar nan har sun fara lodawa a wulbaro ana jide musu , fahimtar da tayi masu sayan dusar ne , ya sa ta janyo nata buhun-hunan ta kawo gaban su ,”
Cikin tsanaki ɗan dattijon yake kallon ta duk alamun gajiya da yunwa sun bayyana a gare ta fatar bakin ta har ta bushe , jikin nan busu-busu da ƙurar dusa ,”
Kwano nawa ne ƴan mata ?
Nima ban sani baba
Ungo wannan daron hashimu juye ka auna dusar yarinyar nan kwano nawa ne ,”
Tana tsaye aka auna kwano biyar biyar ne , ta masarar da ta geron ,
Kuɗin ki naira ɗari huɗu ne ƴan mata kowanne kwano murtala biyu muke sayan sa idan dusa mai nawi ce irin taki , idan kuwa faya-faya ce naira ishirin da biyar ne kowanne kwano ,
Ɗari biyar ya miƙa mata tare da buhun ta ,’
Bari na nemo chanji baba ta furta hakan tana jin wani zallar farin ciki kamar tayi tsalle ,”
Ki bar chanji yarinya ki sayi abinci da ruwa ki sha , ki daina zama da yunwa a wannan halin da kike ciki babu kyau , Allah yaye mana talaucin da ya addabi ƙasar mu !4
Har ƙasa yakaka ta sunkuya tana jero kalaman godiya kamar zata kwanta ,”
Sauri sauri ta wanke jikin ta tare da ɗaura alwala da ruwan randunan ƙasa da ta gani birjik a filin wajen , ta lura har babban bayan gida ne a wajen wanda ake shiga a yi wanka da kama ruwa bayan an gama aiki ,
Gudu-gudu tayi sallolin ta na azahar da la’asar , ta ninƙe buhun ta ta cusa shi a ɗan wani lungu , ta fito tana kallon rana yadda ta tafi tana gaf da faɗuwa , hankalin ta baki ɗaya yayi kan falmata ,
A haka ta kama hanyar kasuwar busu-busu da ita sai cin karo take da mutane waɗanda su ma suke cikin sauri domin su bar bakin kasuwar ,1
A zaune ta tarad da falmata inda ta ajiye ta tayi shiru da ita ta sunkui da kai , mafi yawancin mutanen da suke hada-hadar su a wurin duk sun watse hatta baba mai kayan miya baya nan,”
Cikin sauri ta dafa falmata ,”
Falmata na dawo ,
Yakaka kin dawo sannu da zuwa , baki gaji sosai ba koh ? Baki yi aikin wahala ba ko ? Kin ci abinci ? Ya jikin naki ?
Ƴar dariyar ƴake tayi , tana mai jin yadda jiri ke kwasar ta , ƙarfin hali kawai take wurin tsayuwa akan kafafun ta ,
Falmata tashi mu ƙarasa rumfar da zamu kwana kin san fa mutumin nan cewa yayi kar mu wuce karfe huɗu da rabi , yanzu kuma ina ga kamar biyar ma ta ɗan wuce kin ga kar ya fasa taimakon mu da yace zai yi mu dunga kwana a bakin shagon sa ,:
A tSaye suka tadda shi a gaban rumfar shagon sa sai faman duba agogon hannun sa yake ,” ba dan yadda yake jin tausayin yaran ba da tuni yayi tafiyar sa domin a ka’idar sa baya wuce karfe huɗu da rabi a kasuwa , sai ga shi yau har biyar da wajen minti ishirin , cikin ran sa ya aiyana ya ƙara musu mintoci goma idan basu zo ba zai yi tafiyar sa .2
Sai gasu sun iso ,
A gurguje ya ansa gaisuwar su ya shiga shagon sa ya fiddo musu da jakankunan kayan su gami da tabarma mai biyu da kuma wasu robobin abinci da suke rufe guda biyu , sai jakar ruwa ɗaya , yayi musu sallama bayan ya gargaɗe su a Kan su kula da kan su ,”
Ga mamakin yakaka sai ta ga ya sauke musu jibga-jibgan labulen da aka yi da yadin tamfol duk kusurwa uku na rumfar wanda aka yi domin kare zubar ruwan sama zuwa cikin rumfar ,
kirif suka rufu daga barin idanun mutanen da suke kai kawo ba za’a san ma da mutane a ciki ba idan ba leƙawa aka yi ba , yana daga waje yayi musu sallama akan sai da safe , suka bishi da doguwar addu’a tare da godiya !
Cikin jim daɗin karamcin da yayi musu yakaka ta shimfiɗa musu tabarmar tare da kama hannun falmata ta zaunar da ita a gefen jakar kayan su daga jikin bangon shagon sai lokacin ta lura da ledar mai ɗan girma da take hannun falmatan ,”
Story continues below
Falmata menene wannan a cikin ledar hannun ki ??
Abincin ki ne yakaka , naga yanzu kin fi son tuwo miyar yakuwa shine na saya miki lokacin da naji baba mai kayan miya yace mai abinci ta kawo mishi , shine nima na bada kuɗi aka kawo miki , na naira ɗari da hamsin ne , ga sauran kuɗin da na samu yau ƙirga ki gani , “ta miƙa mata ledar da ta tara kudin a ciki ,
Da tarin ƙaunar ta da tausayi ta karɓi kuɗin ta kirga su naira ɗari hudu da sittin ne idan aka haɗa da kuɗin abincin da ta saya mata ya zama ɗari shidda da goma , ai kuwa lalle sun samu kuɗi ita ma ga nata naira ɗari bakwai hansin ɗin safe na abincin ta, kuɗin su sun kama dubu ɗaya da ɗari biyu da goma ,”
Falmata nima na nayi aiki na samu kuɗi har ɗari bakwai kin ji su ,
ta ɗora mata kuɗin akan hannun ta , da murna ta shafa kuɗin
kai yakaka amma wallahi mun ji daɗi kin ga sai muyi ta tara kuɗin da zaki dunga zuwa asibiti ana duba lafiyar yaron mu kamar yadda likita ranar ya faɗa ,” kuma mu dunga ware ko ɗari ɗaya ne kullum muna ajiyewa dan mu sayi kayan jarirai koh ?5
Idon ta cike da ƙwalla ta ce
hakane falmata kin kawo shawara .
Bari na ci abincin yunwa nake ji sosai falmata , ke ma ki ci wanda mutumin nan mai kirki ya bamu ga shi har kwano biyu , ɗayan sai mu bari da safe mu ci koh ?
Ni ban jima sosai da cin abinci ba yau sau biyu na ci abinci na saya da hansin ɗin safen kuma baba mai kayan miya ma ya saya min biski da miyar yakuwa naci ɗazu da la’asar ,’ anjima da dare kafin muyi bacci sai mu ci wannan ɗin , yanzu ni sallah nake so nayi ,!2
******
Dare ya tsala yakaka ta gaza yin baccin kirki daga ta fara sai ta farka, sai juyi take yi ta tattake a cikin abun rufuwar ta tayi matashi da jakar kayan ta ,
Ba kome ne ya hana ta bacci ba illa ciwon baya da kai , ga kuma matsanancin tsoron karnuka da take jiyo kukan su kurkusa da inda suke , zuciyar ta sai dakan lugude take ,3
A hankali ta zira hannu ta lalubi wurin da falmata ke kwance , wayam ta ji bata nan , sake baza hannun ta tayi , ba shiri ta bankaɗa abun rufuwar ta gami da miƙewa zaune , duhu ne bakikkirin a cikin rumfar har ba’a iya ganin tafin hannun , murya ƙasa-ƙasa ta kira sunan falmata ,”
Shiru ta ji
Da ɗan ƙarfi ta sake kiran sunan tana mai miƙewa tsaye ,
Haske ta ga ya ratso rumfar kafin ta ga shigowar falmatan tana lalube , da sauri ta taka ta kamo ta zuwa cikin jikin ta ta riƙe , murya ƙasa-ƙasa tace
Falmata ina kika je ? Meyasa kika fita ? Ke bakya tsoron dare ne ?
Yakaka fitsari na ɗan je baya nan nayi ba nisa sosai ba
Meyasa baki tashe ni ba ,? Kar ki sake irin haka , ba a cikin gida muke ba a bakin kasuwa muke bakin titi cikin rumfa , babu kowa sai mu kaɗai !
Toh ta amsa mata
Daga haka suka kwanta ƙwaƙume da jikin juna ko yaya ɗayan su ya motsa ɗayan zai iya ji ,”1
Asubar fari suka tashi suka yi sallah suka ɗan sake kwanciya zuwa lokacin da gari zai ƙarasa wayewa ai kuwa wani daddaɗan barci ya kwashe su tare da taimakon sanyin asuba ba su suka farka ba sai da hayaniyar jama’ah da ƙarar motoci ya fara yawa wuraren takwas da rabi ,
Yakaka mun yi bacci dayawa , cewar falmata
Mu wanke baki mu ci abincin ALLAH ya sa bai lalace ba , ilai kuwa suna buɗe robar warin lalatatcen wake da shinkafa da miyar ya bigi hancin su ba shiri suka maida murfin ,
Bari na fita na sayo mana abin karyawa me zaki ci ? Fanke ko ƙosai ? Ko doya ko masa ?
Ni kawai duk abinda zaki ci yakaka , ki nuna min wurin da zanje na zubar da abincin nan na wanke masa kwanukan ?
Kwanci tashi suka yi kwanaki a bakin kasuwa suna gudanar da al’amuran su cikin jin dadi , ƴanci tare da walwala , sosai rayuwar da suke yi a bakin kasuwa ta fiye musu duk wata rayuwar da suka taɓa yi a cikin birnin maiduguri daɗi da kwanciyar hankali , zasu ci su sha kuma su adana ƴan kuɗaɗen su , babu ƙyara babu tsangwama ,3
Ka’in da na’in yakaka ta kama aikatau ɗin ta ta riƙe kullum a chan take yini tana aiki chan take cin abincin rana , sai yamma lis take komawa gida , tayi wankan ta fes a banɗakin wurin aikin ta , a hanya zata ɗan saya musu ƴan kayan gwari da ake yayin su lokacin , karas ,lemo ,cashut da sauran su ,2
Falmata kuwa har ta gane hanya daga wurin barar ta zuwa ƴar rumfar kwanan su , dan haka ta daina jiran yakaka ta zo ta mayar ta , daga ta ji kasuwa ta fara alamun watsewa sai ita ma ta tafi bakin rumfar ta jira zuwan yakaka , a hankali har suka fara sabo da jama’ar kewayen wurin ,
Yau an tashi garin a ɗan hargitse sakamakon kwana da aka yi ana ɗauki ba daɗi da ƴan tawayen boko haram da suke neman shigowa garin ta karfi ta wani yanki , sai dai basu samu nasara ba dakarun soji sun tarwatsa su wanda hakan ya jaa dayawa daga cikin su sun fantsama cikin gari da hakan kuma yake babbar barazana ga rayukan al’umma .
Saboda ɗaukar mataki sai soji suka fantsama cikin gari , tare da sanya dokar hana zirga-zirgan motoci akan manyan titunan garin , kasuwar kan ta yau ba’a buɗe ta ba duk inda ka bi motocin soji ne suke kai kawo ,
Jugum-jugum falmata da yakaka suka yi , su sam basa ƙaunar wannan jiniyar ta motar sojoji , tsinka musu zuciya take ta tada musu hankula kamar yadda ya faru a yanzu tun safe sun gaza ko cin abinci sai faman wuri-wuri suke , ko ƙwaƙwarar magana sun gagara yi da junan su , illa hannun su da yake cikin na juna , lokaci zuwa lokaci yakaka tana ɗan leƙawa ta tsaƙanin labulen rumfar su tana ganin yadda garin yake shal tamkar an share .1
Sun kwashe tsawon lokaci a haka , har zuwa lokacin da suka ji an kamo wasu gungun mutane an wuce da su ana ta dukan su ,
Basa fahimtar maganganun da suke tashi a wurin illa dai suna jin ana yawan ambaton kalmar boko haram , boko haram , boko haram !
Yakaka ta so leƙawa ta ga ko su waye ,? Amma sai ta ji falmata ta sake damƙe mata hannu , ƙasa ƙasa ta ji tace
Yakaka kar ki leƙa , tsoro nake ji , zuciya ta bugawa take , yakaka mu yi addu’a kar su gan mu su kashe mu .
Wucewar mutanen bai fi da mintoci biyar ba suka ji ƙarar fashewar bam da matuƙar ƙarfi har sai da rumfar da suke ciki ta girgiza ,
Harbe harben bindigogi ya biyo bayan tashin bam ɗin tare da guje -guje har ta gaban rumfar su suke jin takun gudun mutane tare da wucewar harsashi ,”
Iyakacin ruɗani tare da tashin hankali sun shiga kuka suke yi suna tsaye charko charko cikin rumfar ,”2
Suna nan tsaye falmata ta ji wani ƙaƙƙarfan abu ya bugi kafaɗar ta ya wuce wanda sai da ya sa tayi baya da karfi ta bugu da jikin kofar shagon kafin ta silale ƙasa , cikin wani irin azabar raɗaɗi da take ji yana gauraya illahirin jikin ta takamaimai bata san ina ne yake mata ciwo ba ,
a razane yakaka ta jiyo jin yadda hannun falmata ya kufce daga cikin nata , abun da tayi arba da shi ya sa zuciyar ta ta tsaya da bugawa , bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tare da tallafo falmata wacce jini ke malala daga jikin ta , idanun ta suna rufuwa su buɗu da kan su , jikin ta kuwa babu inda baya rawa ,.’5
Falmataaa
ta kira sunan ta da wata irin murya tamkar ba tata ba , wani irin ihu ta kurma lokacin da ta fahimci abun da ya faru ,…….!6
Masha Allah ina gaida masoyan littafin mafari a duk inda suke !Da gudu ta tako ta fito daga ƴar rumfar , yanayin da ta ga falmata a ciki ya mantar da ita duk wani halin fargaba da tsoron soji da suke ciki ,
Tana kuka ta nufi bakin titin inda ta hango gungun soji da wasu mutane farar hula suna tsaye , tun kafin ta karaso gudun da ta taho da shi ya ɗau hankalin su ,tare da ihun da take faman yi+
Tana ƙarasowa ta zube a gaban su ba tare da ta ji tsoron bakin bindigar da ta ga sojojin suna gyarawa ba tare da saita ta da ita ,”

Da rishin kuka take cewa kun harbi ƙanwa ta , zata mutu , kun kashe min ƙanwa ta me tayi muku ? Mu ba boko haram bane , meyasa zaku harbe ta wayyo Allah ƙanwa ta ,”2
Wasu daga cikin su sun fahimci abun da tace dan haka wani daga cikin su fararen hula ya ɗan matso kusa da ita ,
Ina ƙanwar taki take ?
Waiwayawa tayi tana nuno masa ƴar rumfar da suke ciki , tsabar kuka da ruɗanin da take ciki har numfashin ta sarƙewa yake yi ,2
Su biyu suka nufi rumfar
Yakaka ta take musu baya
Nan take suka fahimci bullet ne ya samu falmata a kafaɗa cikin rashin sani ,”
Da gudu gudu suka koma wajen sojojin tare da neman taimakon su akan a kai yarinyar asibitin kurkusa , ba tare da gaddama ba soja ɗaya ya amince zai jaa su a motar su ta soji .
Dan haka suka ciccibo falmata wacce ta riga ta suma suka ɗora ta bayan hilux ɗin sojin tare da yakaka wacce idan banda sambatun kiran sunan falmata babu abun da take gaba ɗaƴa ta ƙanƙame falmatan a jikin ta .
Da isar su babban asibitin gwamnatin jaha ( general hospital ) wanda bashi da wani tazara mai yawa da bakin kasuwar , aka shige da falmata bangaren bada taimakon gaggawa ( Accident and emergency) nan suka tarar da mutane dayawa da suke cikin hali makamancin na falmatan wanda tarzomar jiya ta ritsa da su birjik , wasu sun ji munanan raunika , wasu babu hannu , wasu ba ƙafa , likitocin da suke kan aiki sai kai kawo suke , da alama sun gaji likis ga har zuwa yanzu akwai waɗanda ko kai ga fara basu taimako ba’a yi ba ,3
Nan suka ajiye falmata akan dandaryar siminti bakin kofar domin duk gadajen da suke cikin ɗakin a cike suke ,1
Bayan sojan ya shiga ciki yayi musu bayani , likitocin suka ce a ajiye ta kawai zasu zo kan ta domin aiki ya musu yawa , ko kuma idan likitocin safe sun zo su duba su tun da sun ce harsashin a kafaɗa ya same ta da sauki akan waɗanda bam ya tashi da su ,5
Tsayuwar da bata fi ta rabin awa ba mutanen da suka kawo su suka yi , suka matso kusa da yakaka wacce har zuwa lokacin idanun ta zubar hawaye suke har sun kumbura ,
Yarinya mu zamu tafi , domin muna da aiyuka a gaban mu , su kuma likitocin nan ƴan walakanci ne basu da niyyar zuwa su duba ta , ki cigaba da jiran su , sannan ki dunga leƙawa kina damun su akan su zo su duba ta , idan kuwa ba haka ba har jinin jikin ta sai ya ƙare ta mutu anan indai likitocin nan ne babu abun da ya dame su , mu mun tafi ,2
ga wannan ki rike a hannun ki ko zasu ce ki sayo wani magani ,suka miƙa mata dubu ɗaya suka kaɗa kan su suka yi ficewar su ba tare da sun sake kallon inda falmata take yashe a ƙasa ba ,”
Wani sabon kuka ta sake fashewa da shi tana tattaɓa fuskar falmata wacce tayi sanyi ƙalau ,”
Falmata na dan Allah kar ki bar ni , Falmata dan Allah ki tashi ,’
Kamar mahaukaciya ta yunƙura ta tashi ta bazama ta faɗa cikin ɗakin da ake duba marasa lafiyan ,”
Tana shiga nurses ɗin da suke taya likitocin aiki suka yi mata chaa ,”
Mata meye hakan ? Baki ga aiki muke ba zaki zo kan mu da ihu ? Ki koma daga waje ki jira a fito da marar lafiyan ku , ba’a shigowa nan idan ba mu muka kira mutum ba fita-fita dallah ,”3
Kuka ta fashe da shi
falmata na zata mutu dan Allah likita ki zo muje ki duba ta jini sai zuba yake daga jikin ta jinin ta zai ƙare ta mutu idan ta mutu bani da kowa ,”1
Story continues below
Kalaman ta suka doki kunnuwan sa yayi tsai daga aikin ɗinkewa wani mutum mummunan rauni da yake yi ,”
Tabbas ita ce , ita ce da kullum damuwar ta yake ga falmata ƙanwar ta ita ce da kullum hawayen ta yake zuba akan ƙanwar ta falmata , bata da wani abu mafi muhimmanci da ya wuce ƙanwar ta falmata , ita ce wacce ya kwashi watanni yana neman ta har ya zo ya haƙura ,2
Cikin nutsuwa ya waiwayo yana duban inda take lokacin da nurse ɗin ta sanya wata security guard da take tsaye daga bakin kofa , tayi waje da ita domin tana son bata musu aiki ,”
Security guard ɗin ta cukuikuyo hijabin ta tana tura ta waje ,
Ita kuma tana sake ƙara karfin kukan ta tare da neman su taimaka mata ƙanwar ta kar ta mutu ,”
Hey jumai let her come in .
Suka tsinkayi muryar babban likitan su da yake duty , ya bada umarni
A tare suka waiwaya da yakaka wacce jin muryar sa ya sa ta waiwayo da fatan son kasancewar shi ne da gaske a wurin ai kuwa tayi arba da shi jikin sa sanye da korayen kaya ,’ɗan siririn farin gilashin da yake ɗore saman karan hancin sa bai isa ya sa ta gaza gane shi ba ,”
Da ƙarfi ta fizge jikin ta daga riƙon da security tayi mata , ta tako da gudun gaske ta ƙurɗo ta tsakanin gadajen marasa lafiya tana zuwa ta kamo hannun sa da yake cikin safar hannu ta duba marasa lafiya ta shiga jaan sa tana cewa
Dakta ƙanwata falmata ai ka san ta ko ? Ita ce harsashin bindiga ya same ta , ta suma kamar ta mutu jini yana ta zuba a jikin ta , dan Allah ka zo muje ka duba ta ,kar ta mutu dan Allah ka taimaka min !2
A hankali ya zame hannun sa daga riƙon da tayi masa , ya maida duban sa ga nurses ɗin da suke tsaye
Ku sa a shigo da ita !
Doctor bamu da gadon da zamu ajiye ta ,”
Yana mai komawa bakin aikin sa yace
A nemo gado a ɗaura ta akai yanzu zan duba ta ,’
Biyu daga cikin nurses ɗin suka fita tare da security guard ɗin , yayin da ɗaya ta aunawa yakaka harara ,
Ai Sai ki fita mata , domin ba’a tsayuwa anan ,’2
Ba tare da ya juyo ba yace
Sister kalsum ki bar ta ta tsaya anan , yanzu za’a shigo da ƙanwar ta ,!1
Tashin hankalin da ya hango a fuskar ta ya taɓa masa zuciya sosai ,”yana jin tausayin ta mai ƙarfi yana taso masa , ita kullum a cikin kuka da wahala take !
Mokaɗe baki nurse kalsum tayi ,
Cikin ran ta tana son sani alaƙar dactor hamza da wannan kucincinannar yarinyar ƙazama !5
Cikin mintoci goma sai ga falmata an turo ta a gadon marasa lafiya an shigo da ita ,” da hakan ya zo dai-dai da kammala aikin da yake yi ,
Ya tako ya zo gaban gadon falmatan ya duba ta tare da yin aune aune , nan ya fahimci ta zubda jini dayawa da ya sa dole sai anyi mata ƙarin jini , bayan an cire harsashin da yake cikin jikin ta
Dan haka yayi umarni a kare gadon falmatan a kuma sauya mata kaya zuwa na tiyata,” sannan ya juyo da ganin sa ga yakaka , cikin tausasa murya tare da sigar lallashi yace ,
Ki nutsu ki daina kuka haka kin ji ko ? Ki samu wuri ki zauna a waje ,ki sayi ruwa ki sha ,insha Allah babu abun da zai samu ƙanwar ki , ɗan rauni kaɗan ta ji kuma yanzu zan cire mata harsashin na ɗinke mata wajen na sa magani zuwa anjima zata farka kuyi magana kin ji ko ?
Gƴaɗa kai tayi tana duban fuskar sa
cikin son samun tabbaci ta ce
” Ka ce zata samu sauki har ta tashi anjima koh ?
Sosai kuwa insha Allah
ya bata ansa yana mai duban ƙwarar idanun ta da tsabar kuka ya sauya musu launi ,”
da jan ƙafa ta fice tana waiwayan inda falmatan take ,
Shi kuma ya juya ya ɗau wata ƴar takadda yayi rubuce rubucen sa ya kira ɗaya daga cikin ma’aikatan da suke tura gadajen marasa lafiya/kujerar marar lafiya , ɗauko file da sauran su , ya miƙa masa takkadar bayan yayi Signature ya buga Stamp .
Ka je blood bank ka kai musu , ka tsaya ka ƙarbo jinin ka kawo .
Toh sir
Cikin gwanancewa ya fara aiki ga falmata !
Story continues below
Bayan awa ɗaya ya kammala ya ɗaura mata jinin da aka kawo leda ɗaya bayan yayi mata allurai ,
Sai da ya sake jaddadawa nurses ɗin da suka karɓi aiki akan su kula da ita Ƙanwar sa ce , bayan yayi bankwana da likitan da ya ƙarbe shi a bakin aiki ya shigar masa da duk wasu bayanai akan marasa lafiyan da ya duba ciki har da falmata da ya roƙi Alfarma a lura da ita da kyau , abokin aikin nasa ya amsa da zai kula da ita sosai .
Cikin takun da yake nuna tsabar gajiyar da yayi ya fito daga ɗakin , yana goge ruwan hannuwan sa da ya wanke da farin ƙyalle .
Tana hango fitowar shi ta miƙe daga inda take durƙushe a jikin bango ta nufo shi ,”
Cikin nazari ya tsaida idanun sa akan ta tana tahowa yana son tabbatar da zargin sa akan alamomin masu juna biyu da yake gani tare da ita alhalin shi a budurwa ya san ta .
Dakta ta farka ? Tana magana ? Jinin ya daina zuba daga jikin ta ? Ko na shiga na gan ta ??
Bin fuskar ta da tayi jazur da kallo yake yana ganin yadda fatar bakin ta ta bushe idanun ta suka kumbura,
Bai amsa mata tambayoyin ba , yace mata
Zo muje !
Ta bishi a baya tana waiwayen ɗakin da falmata take ciki , so take tayi gaddamar bin sa sai dai ta kasa ,
A bakin wani ɗan shagon da ake sayar da kayan sanyi da kayan fulawa irin su Biscuits, cake , meat pie , donut da sauran su , suka tsaya
Duban sa ya mayar kan fuskar ta cikin kulawa yace me zaki ci marar nawi sosai ? Zaki sha Hollondia yogurt ? Ko juice kika fi so ? Cake zaki ci koh meat pie ?
Wani jirkitatcen kallo ta yi masa , falmata tana cikin yanayi irin wannan har shi yana tunanin zata iya cin wani abu ? Ai ita ko ruwa baza ta iya sha ba idan ba ta ga farkawar falmata cikin ƙoshin lafiya ba .
Sunkui da kan ta tayi daga kallon fuskar sa ,’ cikin siririyar murya tace
Bana cin kome bana jin yunwa , dakta dan Allah ya jikin falmata ? Ta samu sauki , ka kai ni na gan ta dan Allah ,
Bai amsa mata ba sai ya maida ganin sa kan mai shagon da yake tsaye ta cikin ɗan shagon sa yana kallon su .2
Bamu hollondia yogurt babbar roba ɗaya da Chii exotics babba ɗaya , meat pie guda uku , tare da ruwan roba guda ɗaya .
Suna tsaye ya haɗa a leda ya miko musu , dakta hamza ya karɓa gami da miƙa kuɗi aka bashi chanjin sa ,
A takaice yace mata
Mu tafi ! Yana mai yin gaba
Cikin ƙosawa ta bi shi a baya .
Wurin da motar sa take ajiye a wajen tsayuwa na musamman ya ƙarasa , gami da buɗe motar ya shiga
Ita ma yayi mata umarni da ta shiga bayan ya buɗe mata ɗayan bangaren ,”
Ta shiga ta zauna gami da mayar da kan ta jikin murfin motar ta kwantar tana jin wani irin yanayi marar daɗi yana taso mata , sam ita bata son takurar da yake yi mata a koyaushe idan suka haɗu ,!
Ledar da kayan da ya sayo suke ciki ya ɗora mata akan cinyar ta .
Bana son musu ko doguwar magana ki cinye kuma ki shanye duk abinda yake cikin ledar nan , ƙanwar ki na mata aiki na bata magunguna yanzu haka bacci take daga ta tashi zaki ganta insha Allah baza ta ɗauki lokaci mai tsawo ba zata warke, idan har kun zauna an bata kulawar da ta dace baku gudu ba !
Sanyin kayan da suke bisa cinyar ta suka haɗu da jin daɗin cewar falmata tana raye an yi mata aiki har ma tana bacci suka tayar mata da kishirwar da ta jima tana ji ,
Ba tace kome ba , ta buɗe ledar gami da ɗaukar gorar ruwan ta kunce bakin ta kafa kai ta fara sha bayan ta muskuɗa ta juya tana fuskantar murfin motar ta bashi baya ,”
Ajiyar zuciya ya sauke yana jin farin cikin sake ganin ta yana ratsa shi , ya zubawa bayan hijabin ta ido da duk jinin falmata ya ɓata , ‘
A garin yaya harsashi ya same ta ?
Ya jefa mata tambayar lokacin da ya ga ta gama shan ruwan ,”
Story continues below
Muna cikin rumfa ne a bakin kasuwa
Bakin kasuwa ? ya maimaita
Me kuke a bakin kasuwa a wannan yanayin da gari yake ciki na hargitsi ?
Daman anan muke zama
Ta amsa masa
Kamar yaya ? Yaushe kuka dawo garin ?
Ɗagowa tayi ta dube shi
Daman muna gari , a bakin kasuwa muke kwana a cikin rumfar mai shago !
Ji yayi kan sa ya wani irin juyawa , take alamun da ya gani na masu ciki a tattare da ita ya faɗo masa cikin rai ! Shi ƙwararren likita ne wanda ya san aikin sa ya kuma faɗaɗa tare da zurfafa bincike cikin duk wani ilmi da ya shafi lafiyar ɗan adam , ba sai wani ya faɗa masa ba ba kuma sai yayi gwaji ba babu shakka cikin kallon tsanaki da yayi wa yarinyar ya fahimci tana da juna biyu , toh amma ta yaya haka ta faru ?
Wani mummunan tashin hankali ya ziyarce shi lokacin da yayi hasashen abun da ya faru ga rayuwar yarinyar , da ta yadda aka yi ta samu cikin
Tare da waye kuke kwana a bakin kasuwa ya tambaye ta yana tsare ta da kallon tuhuma .
Mu kaɗai ni da falmata !
Bai san lokacin da ya birkito da ita tana fuskantar shi ba ,”
Wacce irin rayuwa kuke yi a bakin kasuwar ? Baki da lafiya faɗa min waye yayi miki ciki ?
a tsorace ta ɗago kan ta tana kallon sa , yadda taga jijiyoyin kan sa sun tashi idanun sa sun kaɗa sun yi jaa ya sa ta matuƙar razana ,”
Nan take hawaye suka ɓalle a idanun ta , ta sake maƙure kan ta da jikin kofar motar
Sakin hijabin ta yayi tare da yin baya da kan sa ya ɗora a jikin kujerar da yake zaune bisa ya runtse idanun sa , tunani iri-iri suka rikito masa ,
Wani ƙazamin ɗan iskan ya riga ya bata rayuwar yarinyar tun a ƙaracin shekarun ta , mutanen duniya mafi yawan su azzalumai ne , sun cutar da rayuwar yarinyar saboda rashin galihun ta , ji yayi zuciyar sa ta raurawa idanun sa sun kawo ruwa ,” wani irin tausayin ta da ya danne tasirin bacin ran sa da zafin kishin da yake ji ,ya mamaye ruhin sa ,
Allah sarki talaka !
Ya furta a cikin ran sa ,
Murya ƙasa ƙasa yace
Ki koma ki zauna a inda mutane suke jiran ƴan uwan su marasa lafiya , zan je na dawo ki tabbatar kin ci abinci , kar ki zauna da yunwa ,
Kamar jira take yayi mata umarni ta ɓalle murfin motar ta fita , hankalin ta gaba ɗaya yayi kan falmata , bata damu ba sam da sauyin yanayin da ta gani tare da shi da damuwar da ta bayyana a gare shi , bare har tayi wani dogon nazari akan hakan ,”
Gyara zaman hijabin ta tayi tare da sake riƙo ledar hannun ta da kyau ,ta kama tafiya ,”cikin ran ta tana aiyana baza ta sha wannan kayan daɗin ba falmata zata ajiyewa tana farkawa ta bata ta ci ta sha !9
Tuƙi yake yi akan hanyar sa ta komawar sa gida amma rabin hankalin sa bai tare da shi , yana ga tunanin halin da yarinyar ta tsinci kan ta a ciki , ba zai yiwa kan sa ƙarya ba tun da jimawa ya fahimci ya faɗa tsundum cikin so da ƙaunar yarinyar da ko a mafarki idan aka ce masa shi zai so mace irin ta zai ce ƙarya ne , toh amma tun da ya gagara kaucewa faɗawa a soyayyar ta , sai ya ɗauki hakan a matsayin kaddarar sa ce watakila matar auren sa ce ubangiji ya turo masa ita a haka , dan haka sai ya shiga neman hanyar da zai yi ya gyara ta ta zamto irin macen da shi yake son ta kasance matar aure a gare shi , karatu yake da nufin sa ta a farko bayan ya kai ta gidan su wurin mahaifin sa , tayi karatu mai ɗan zurfi zuwa ko da matakin diploma ne sai ya aure ta ,
Toh sai kuma ƙwatsam ta ɓace masa , ya sha wahalar neman ta bata nan ! , har ya fara dangana da rashin ta sai kuma ta ɓullo da wani al’amari mai girma a tare da ita ,”ciki ba tare da tayi aure ba , baya tunanin ko uban cikin jikin nata ta san shi ,” Al’amarin ba ƙaramin firgita shi yayi ba ya taɓa ran sa fiye da zato , saboda soyayyar gaskiya yake yi mata ,”2
Story continues below
A tun bayan barin ta da yayi yanzu ya kamo hanyar sa yake bincikar kan sa tare da ƙwanƙwasar zuciyar sa ko Allah zai sa ya ji wani sauyi na daga soyayyar da yake mata ta zuwa wani yanayi na ƙi ko kaɗan ne a saboda girman bakon al’amarin da yake tare da ita marar kyau ?
Wanda zai yi amfani da hakan wurin yakice ta daga cikin ran sa baki ɗaya ya shafe babin rayuwar ta daga ran sa ?
Sai dai ko kusa shi ya gagara ya ji alamun ya tsane ta , a maimakon tsanar sai yake jin wani matsanancin tausayin ta yana sake lulluɓar shi , zuciyar sa tana raya masa FYAƊE aka mata , fin ƙarfi aka gwada mata ba da son ran ta bane , ita ɗin abar a tausayawa ce , abar a tallafa ce a bata kulawa , a tsaretar da rayuwar ta daga faɗawa mummunan yanayi dangane da irin halin da ta tsinci kan ta a ciki a ƙarancin shekarun ta ,”3
Sashi mafi rinjaye na zuciyar sa ya ji yana ƙarfafar sa akan Ya tallafe ta , kar ya guje mata , ya zamto gata a gare ta kar ya ƙyamace ta , ya Aure ta ya taya ta riƙo tare da tarbiyyartar da abin da zata haifa HAKAN TAMKAR JAHADI NE a gare shi ,
Da wannan dogon tunanin ya ƙaraso gidan su da yake kan titin danboa road yayi hon maigadi ya buɗe masa kofa ,
kai tsaye falon mahaifin sa yayi wa tsinke bayan ya ajiye motar sa ,
kamar yadda ya saba a zaune ya tarad da shi bisa wheelchair hannun sa riƙe da Alqur’ani mai girma yana ƙarantawa da mabayyanin sauti .
Sai da ya ɗan tsimaye shi ya ƙarasa ayar da ya ɗauko ,
Sannan suka gaisa cikin kulawa da nuna tsantsar ƙauna daga mahaifin sa ,” ƴan tambayoyi yayi masa game da yanayin aikin sa kasantuwar mahaifin na sa professor ne da ya sha ya ƙoshi ya tumbatsa a harar ilmin kimiyya , yanayin rayuwa ya juyar da lamarin sa haka ya kasance zaune bisa kujerar marasa lafiyar ƙafa bai zuwa ko’ina .1
Ji yake batun yakaka yana zungurar sa akan ya faɗawa mahaifin sa , wani sashin ya dakatar da shi da ya bari har ya samu ƙarin bayani daga bakin yarinyar dalla-dallah ta yadda zai ji karfin zuwa da maganar tare da amsa duk wasu tambayoyi da ka iya zo mar daga baban sa !
Dan haka ya miƙe yana mai yin sallama da baban nasa ,
Har ya ɗauki hanyar sashin sa , sai kuma ya dawo ya kutsa kai zuwa ainahin cikin gidan sashin mahaifiyar su da yanzu ƙannen sa ne ke rayuwa a ciki ,
A babban falon ya tarar da su suna harkokin su , ƴan mata ne su uku ya da ƙanwa , babbar cikin su zata yi kimanin shekaru ishirin da biyar sai mai bin ta sai kuma ƙaramar su ,2
Har suna rige-rige wurin gaishe da yayan nasu inda shi kuma ya amsa musu da yalwatatciyar fara’a bisa fuskar sa ,’
Girls , so nake ayi girki mai kyau wanda marar lafiya zai ji daɗin ɗanɗanon sa a bakin sa , kamar girki kala biyu haka , a dafa tea da kunu nan da awa biyu zan shigo na ɗauka ,”
Toh company
Suka haɗa baki wurin amsa masa tare da barin abun da suke suna nufar hanyar kitchen , ta cikin falon
Ƴar dariya yayi yana girgiza ,”
Nace muku sunan nan ya fita a bakin ku ko ? Ya furta hakan yana mai nufar hanyar barin falon
Har ya fita , ya dawo ,”
Rahima !
Ƙaramar su ta amsa gami da dawowa baya ,
Na’am big bro
Nace ba ! a cikin kayan ki ki ware kamar kala biyar masu kyau ki ajiye idan na zo ɗaukar abincin marar lafiyar zan haɗa da kayan na kai musu ,
Toh big bro zan ɗauko yanzu , biyar sun isa ko ?
Sun isa! ya ansa yana barin falon .
A duk ranar da ya kwana a asibiti toh yini yake yana bacci idan ya dawo , sallah kaɗai ke tashin sa sai ko cin abinci , kafin zuwan wani daren , saɓanin yau da sam ya gaza yin bacci sai juye juye yake yana kallon agogo , zuciyar sa ta zurfafa wurin son samar masa da mafita , shin daga ta haihu ne zai aure ta ko kuwa zai bari tayi karatu kamar yadda yake da buri ??1
Tunowa yayi bai san matsayin sa ba ma tukun a gurin yarinyar duk wannan tsare-tsaren iska yake , daga ta nuna ƙin amincewa kome ya rushe ,2
ba shiri ya miƙe daga kwanciyar da ya samu kusan awanni biyu yana yi ,
Karfe ɗaya da mintuna goma agogon ɗakin ya nuna , lokacin sallar azahar ya shigo ,
Kai tsaye ya sake shiga banɗaki ya sakarwa kan sa ruwa tare da sake ɗaura alwala ya fito ,”
Mai ya shafa sama-sama ya buɗe ma’ajiyar kayan sa , ya ɗauko wani shuɗin yadi marar nawi mai haske ya saka , ƴar saisayayyar sumar sa ya taje har zuwa ɗan zagayayyen sajen da ya ajiye a gefe da gefen fuskar sa , ya ɗauko turarukan sa ya fashe jikin sa .
Ya zurara bakaken takalman sa yana ɗora igiyar ɓakin agogon hannun sa ,
Ficewa yayi a ƙafa ya nufi babban masallacin da yake bakin titin shigowa unguwar su domin yin sallar azahar .
Ƙarfe biyu dai-dai tayi masa a harabar asibitin , kai tsaye ya nufi emergency ward , hannun sa riƙe da ɗan kyakkyawan gwandon roba mai ɗan girma da aka zubo kulolin abinci zuwa ƴan ƙananun flask guda biyu da cups biyu , chokula biyu da plates guda biyu sai serving spoon , ɗayan hannun nasa kuma ya riƙo ɗan ƙaramin akwati ,
Da gudu security ya taso ya karɓi kayan hannun nasa yana masa sannu da zuwa ,”
Yana shiga ya tarar da babu gadon falmata , ya tambayi likitan ina yarinyar da take gado mai lamba goma ?
Nan yake sanar da shi ta farka har an mata chanjin ɗaki zuwa cikin ward , dan haka ya nufi ward , security biye da shi .
Tun yana shiga ya hango su falmata daga ƙuryar ɗakin gado na ƙarshe , tana kishingiɗe an ɗago mata gadon ta wajen kan ta domin ta ji daɗin kwanciya ,”
Yakaka tana ɗosane a bakin gadon ta tattara hankalin ta baki ɗaya ga falmata tana shayar da ita hollandia yogurt sannu-sannu ,
Tana labarta mata irin jimawar sa tayi a sume da taimakon da dakta hamza yayi musu ,”
Sannu patient ɗina kin tashi ? Ah lalle jiki yayi kyau tunda ga shi har kina shan yogurt , to yaya me kike ji yanzu a jikin ki ? Akwai inda yake miki ciwo ?
Da ƴar fara’ar ta ta waigo inda take jin tashin muryar sa ,
Da sauki dakta , dai-dai wurin raunin kawai shine yake min zogi , sai kuma kaina da yake min ciwo kaɗan-kaɗan , mun gode dakta Allah ya saka da aljanna ,”
Murmushi ya mata , cikin ran sa yana jin tausayin makantar ta ,”
Babu kome ɗan pain ɗin da kike ji saboda sabon rauni ne , daga ya ɗan yi kwana biyu zaki daina ji , ciwon kan da kike ji saboda sabon jinin da ya shiga jikin ki ne , zai daina da zarar jikin ki ya dai-dai ta ,’ akwai magungunan ɗauke zogin ciwo za’a kawo miki ,” ki dunga cin abinci sosai saboda ki samu ƙarfin jiki ,”
Duban sa ya mayar ga yakaka wacce tun da ya ƙaraso ƙamshin turaren sa ya bigi hancin ta ta ji zuciyar ta ta hautsina , sam ƙamshin bai mata ba , dan haka ta koma daga gefe ta tsaya tana yatsina fuska gaba ɗaya gumi keto mata yake amai yana sasuƙar ta sai dai kuma babu kome a cikin ta idan banda ruwa ,”
Ga abinci nan ku ci , kiyi wanka ki sauya kayan jikin ki , ga kaya nan na taho miki da shi a cikin nan ,
Ya mata nuni da kayan da security ya ajiye a gefen gadon ya tafi, “
Kai ta gyaɗa kafin ta ce
Mun gode Allah ya biya ,” cikin ran ta tana Allah-Allah ya tafi saboda warin turaren sa da ke neman kai ta ƙasa , babu abun da take so a yanzu irin ta shaƙi ƙamshin turaren bature kam silum , wanda ta san babu damar hakan domin kayan su yana kulle cikin shagon “, Abuwar mai yadi ,” dan haka ta Kai hannun ta biyu ta sa ta rufe rabin fuskar ta daga kan hancin ta zuwa ƙasa ,”9
Ware idanun sa yayi sosai yana kallon ta , yadda ta toshe hanci ya sa shi ɗan shaƙo numfashi ko zai ji inda wari yake tasowa amma shi bai ji ba ,”
Bai ce kome ba ya juya ya fara tafiya , tare da cewa watakila zan dawo zuwa yamma ,” !
Gaskiya kwana biyu ina mutunci kut! 😂
Watau rubutu nake muku babu kakkautawa, duk domin na Baku nishadi. 😍17
Da fatan nima zaku bani tukuici , ta hanyar fada min ra’ayoyin ku, / Me kuka tsinkayo zai faru nan gaba? 12
Wai shin bakwa cigiyar biyamuradi YOUSSOUFA ne? ? 😂Cikin sati guda da suka yi a asibiti sun ga gata tare da kulawa daga wurin doctor hamza , har ma da ƙanwar sa rahima, domin kuwa kusan kullum sai ta zo da yamma ta taho musu da abincin da take girka musu na dare , shi kuma doctor hamza ke zowa da na safen ,” da rana kuma ya yo musu take away daga sidic’s ,ruwa kan sa na roba suke sha , ga lemuka da kayan shayi irin na garari , biscuits, cake , lokar gadon su cike take taf da cimaka iri-iri , tamkar dai wasu ɗiyan attajirai ,+
Rahima tana da matuƙar surutu da wayon tsiya, yarinya ce da kaɗan ta girmewa yakaka , bai wuce shekaru biyu ta bata ba , ita ce ƙarama a ƙannen doctor hamza ,” a halin yanzu ta gama secondry sch tana jiran sakamako , “
doctor hamza shi yace mata ta dunga zuwa ta na ɗan taya su hira ko da ta awa biyu ce , bayan ya nemi iznin mahaifin su , yayi masa bayanin su falmata da ƙudirin sa akan su na taimaka musu, sai dai ya boye masa cikin jikin yakaka na banza ne ,maimakon ya fadi gaskiya sai ya ce masa boko haram ne suka kashe mijin ta tun a garin su ,”

Maifinsa bai ƙi ya kawo su gidan su zauna ba , sai dai yayi masa gargaɗi mai karfi kamar yadda ya saba yi masa a kullum cewar ,”Ya tsoraci MATA tare da ƙaidin su yayi hankali da lamarin mata domin sau dayawa su ɗin ba’a gane gaskiyar su , wanda duk ya bada gaskiyar sa a gare su tabbas zasu takaita shi watarana ,”
Kamar koyaushe ya amsa masa yana jin yadda wani ɗaci ke yawo a zuciyar sa , sam bai so ba da mahaifiyar su ta zamto silar da ya sa mahaifin su ya samu mummunan tabo akan mace da yakasance kullum kalaman sa masu tsauri ne akan MATA ,3
*********
Yau yake da niyyar kai yakaka ayi mata scan tare da gwaje-gwajen da ya kamata ayi wa mata a tun farkon samuwar cikin su , duk da cewa har kawo yau bai sake tada maganar cikin ga ita yakakar ba wacce ya lura ita bata da wata damuwa da zaman cikin a jikin ta ,
abun da bai kai ma ga gama fahimta ba kamar son cikin take sosai , saɓanin sauran matan da ya sani da suke shiga damuwa tare da ƙin abun da yake cikin nasu a duk lokacin da suka samu cikin ta haramtatciyar hanya irin nata ,
sai dai ya danganta hakan da kasancewar yakaka yarinya ce kuma akwai ƙarancin wayewa da rashin ilmi a tare da ita , ko ma menene shi daman ba shi da burin raba ta da cikin jikin ta wanda ya riga ya fahimci yayi ƙwari a mahaifar ta .
Ya zaɓi ya kaita wani asibitin daban a duba ta ne a saboda ƙoƙarin sa na kare martabar ta ko da anan gaba ya aure ta , domin a halin yanzu kowa ya san ba shi da mata , to kuma duk sauran likitocin da zai iya haɗa yakaka da su , abokanen aikin sa ne da suka riga suka san juna sosai ,ya kai ta wurin su a zuwan matsayin me take a gare shi ?
Bai son a kodayaushe ya dunga yin ƙarya dan haka ya fi son ya kaucewa duk wani abun da zai sa shi yayi ƙaryar ,”
Sai da ya bari rahima ta zo misalin karfe huɗu da rabi , ta hau sama ofishin sa tare da ajiye masa na shi abincin , nan yake sanar da ita zata Zauna tare da falmata , shi da yakaka zasu je wani waje su dawo ,”
Tare suka shiga ward ɗin inda suka tarar da su suna ƴar hirar su , babu laifi cikin sati guda falmata ta ji sauki sosai saboda kulawar magunguna masu kyau da take samu zuwa abinci mai inganci , uwa uba kwanciyar hankalin da ta samu , yini take a kan gado iskar fanka tana kaɗa ta , ga ta ga yakakar ta a gefen ta , wanda hakan shi yafi kome sanya ta farin ciki ,
Cikin fara’ar da jin muryar su ya sanya ta take gaishe da doctor hamza da zuwa yanzu take matuƙar girmama shi tare da ganin ƙimar sa har ma take jin sa a matsayin wani jigo cikin rayuwar su ita da yakaka ,3
Shima faram-faram ya amsa mata yana mai sake tambayar ta yanayin jikin nata , kafin ya maida duban sa ga yakaka wacce take zaune bisa kujerar gaban gadon , “suna gaisawa ita da rahima wacce suka yi sabo da juna cikin ƴan kwanakin ,”
Story continues below
Duban ta ta mayar kan doctor hamza tana mai gaishe shi , cikin ƴar siririyar muryar ta ,
Fuskar sa a sake ya amsa mata yana mai kallon fuskar ta da take fayau babu ko ɗigon kwalliya sai ƴan siraran shunkuran ta “zane” da suke tarwai akan farar fuskar ta ,
Fatima zamu je na kai yayar ki wani wuri baza mu daɗe ba zamu dawo ga rahima nan zata kula da ke kafin dawowar mu kin ji koh?
Toh yaya dakta sai kun dawo ! Yakaka sai kun dawo !
Zo mu tafi ,”
yace da ita yana mai fara taku ,”
Tiris ! tayi akan kujerar , ina kuma za su ? ? Ita fa sam bata son kaɗaicewa da shi , duk ya bi ya ishe ta da kallo ga warin wannan ƙaƙƙarfan turaren nasa da ba so take yi ba ,”
Kallon fuskar rahima tayi wacce ita ma ɗin ita take kallo cikin nazari , dan haka ta miƙe a sanyaye gami da yi musu sallama bayan ta jaddadawa falmata akan yanzu zata dawo !
A motar sa suka fita a asibitin , duk da cewa har zuwa yanzu bai faɗa mata inda zasu ba ,” sai da ya hau titi ɗoɗar tukun ya juyo ga kallon sa kan ta da ita kuma ta juya fuskar ta ga kallon titi ,”
Ƴar kwantatciyar sumar da take gefen kunnuwan ta zuwa gaban goshin ta da tayi luf-luf yayi wa kallon daƙiƙai kafin ya maida kallon sa ga titin gami da yin gyaran murya ,”
Asibiti zan kai ki a auna ki tare da duba lafiyar abun da yake cikin ki , dan haka ina son sanin sunan ki mai kyau , domin ayi amfani da shi wurin buɗe miki file ,”
A hankali ta juyo da ganin ta kan shi ,”
Cikin ran ta tana jin daɗin yau karo na farko bayan ita da falmata wani ɗan adam ya nuna kulawar sa akan cikin jikin ta har ma zai kai a duba lafiyar abun da yake cikin , “
Sai dai tambayar sa ta ƙarshe ta bata mamaki daman duk zaman su bai taɓa sanin sunan ta ba ???1
Babu shakka ita bata taɓa ji ya kira sunan ta ba , ko magana zai mata kawai yana jefa maganar sa ne a saitin ta kai tsaye ba tare da ya kama sunan ta ba ,” amma ai yana ji koyaushe falmata tana kama sunan ta a gaban shi , sai dai idan wani walakanci ne hakan ,” zai ce bai san sunan ta ba .
Kamar ya san tunanin da take
Ba tare da ya dube ta ba yace ,”
Sunan ki mai kyau nace ,”wannan sunan da ake kiran ki da shi ba suna mai kyau bane dole akwai ainahin sunan ki ,
Bani da wani suna bayan wanda ake kira na da shi ,”
Ta bashi amsa ƙasa-ƙasa , a ran ta Kuwa tana jin haushin kalmomin sa ya za’a yi yace sunan ta bashi da kyau ??
Ba wanda ya sake cewa ƙala har suka ƙaraso ɗan ƙawatatcen asibitin mai zaman kan sa da yake cikin unguwar G.R.A ,
Jerowa suka yi suna tafe tamkar sabbin ma’aurata , ta wutsiyar ido ya kalle ta tana sanye ne da wata atamfa ruwan ɗorawa da aka yiwa dinkin doguwar riga wacce ta buɗe daga ƙasa , ɗaya daga cikin kayan da rahima ta ba su ne ,” nan ya ga yadda ɗankwalin kan ta yayi baya sosai har ya bayyana lallausar sumar da take gaban kan ta , gyalen ta da ta rufu da shi daga kafaɗar ta iskar juyin yanayi da ake na ta kaɗa shi ,”
gani yayi ta yi masa kyau ba kaɗan ba ,”
Sam baza’a ce mace mai ciki bace , domin idan ban da cikar da ta sake yi tayi ƴar ƙiba kaɗan tare da ƙarin haske , babu wani alamun ciki , cikin bai bayyana a sarari ba ,”
Ki gyara ɗan kwalin ki , kuma ki rufa gyalen zuwa kan ki ,”
Ta tsinkayi muryar shi yana bata umarni ,”
ba tare da ta ce uffan ba tayi yadda yace lokacin da suke ƙarasawa cikin ainahin asibitin ,
Ba tare da ɗaukar lokaci ba ya shige gaba ya kammala kome da ake yi a dokar asibitin kafin a ga likita , wanda kuɗaɗe ne tsababa saboda asibitin na manya ne ,
Wurin bada sunan ta ne ya so shiga ruɗani kafin lokacin da zuciyar sa ta yanke masa shawarar abun da ya kamata ,”
Aka yi musu jagora zuwa wajen ainahin babban likitan mata da yakasance shine mamallakin asibitin baki ɗaya ,”
Story continues below
Nan ya tare su da fara’a duk da cewa ba wai ya san doctor hamza bane amma yanayin sa ya bayyana masa wayewar sa tare da ilmin da ya hango tare da shi , “
Bayan bayanin da doctor hamza yayi masa akan a duba lafiyar uwar da abun da yake cikin ta tare da son sanin ranar da zata iya kasancewa ranar haihuwar ta ,”
Likitan ya fara aikin sa cikin gwanancewa, nan ya fara da ɗaukar jinin ta domin yin gwaje gwaje , ya kuma bata wata ƴar roba yace ta kawo fitsarin ta tare da ƙiran ɗaya daga cikin nurses akan ta gwada mata banɗaki , bayan ta dawo yayi mata awun blood pressure, ya ga jinin ta dai-dai ne , sai yayi umarni da ta hau wani ɗan gadon duba marasa lafiya da yake gefe guda cikin ofishin domin yayi mata scanning ,”
Da jaan ƙafa ta ƙarasa bakin gadon ta hau ta zauna ,”
Kallon ta likitan yayi lokacin da yake jona na’urar da jikin babban tv da yake kafe a gefe ,”
Amarya gyarawa zaki yi ki kwanta mai kyau ki miƙe kafafun ki ,”
A ɗarare tayi yadda ya umarce ta tana mai sake gyara rigar jikin ta da kyau ,”
Da ido doctor ya yi wa hamza alama akan ya mata bayani yadda zata gane ,”
Ki ɗaga rigar ki , ki buɗe cikin ki hoton jariri za’a yi ta haka za’a gane lafiyar sa ,” ya furta hakan yana mai maida ganin sa ga fuskar wayar sa ,”
Hoton jariri??
Ai kuwa zata so ta ga hoton abun da yake cikin nata ,” wataƙila yayi kama sosai da baban sa ? ,” tuno da hakan da tayi ya sa wani siririn murmushi ya bayyana kan fuskar ta ,
ta tashi tsaye ta tattara doguwar rigar ta , dogon wondon da ta sa ta ciki ya bayyana ,”
Cikin nutsuwa ya fara mata scanning ɗin , yayin da shi da dakta hamza suka maida hankalin su baki ɗaya ga fuskar tv lokacin da ƴar jaririyar da take cikin mahaifiyar ta ta bayyana tana ta hidimar ta hankali kwance, a yau tana da sati goma sha tara da kwanaki biyar , “komen ta yana lafiya ƙalau a yanayin da ya dace ,hasashen ranar haihuwar ta ya nuna biyar ga watan goma ,” nan da watanni huɗu da ƴan kwanaki kenan ,”
Wow what a beautiful busy baby girl , ? See those wee fingers are very close to the mouth,!
Doctor ya karasa zancen da ƴar dariya a fuskar sa yana mai maida duban sa ga fuskar doctor hamza ,”wanda shima ya ga wutsilliyar da ƴar jaririyar take da hannuwan ta,”wani abu yaji ya taɓa ran sa , fuskar sa kadaran-kadahan yace ,”4
Yeah the baby looking super comfy and growing perfectly ,1
ya furta hakan yana mai jefa kallon sa ga yakaka wacce ko kalma guda bata gane ba cikin ƴar gajeruwar mahawar da suka yi , sai faman raba ido take tana daga kwance ,
Congratulations once again Mr and Mrs Hamza Mustapha Dilmari1
Likitan ya furta haka tare da miƙawa doctor hamza hannu suka yi musabaha , dai-dai lokacin da suka tashi domin tafiya , bayan da likitan ya kammala shigar da duk wasu bayanan da ya tattara akan yakaka da abun da yaje cikin ta zuwa cikin computer Ya aika da shi ainahin wurin wanda zasu cigaba da yi mata anti-natal , bayan ya duba duk wasu gwaje-gwajen da ya yi mata , yaga bata tare da wata babbar matsala ,” nan ya miƙa musu takaddar magungunan da ya kamata ta dunga sha tare da wani ɗan kati wanda da shi zata dunga amfani wurin zuwa awo ,”
Har sun yi taku biyu , yakaka ta tsaya tare da juyowa ta fuskanci likitan , bayan ta sauke idanun ta ƙasa tace ,”
Likita toh ina hoton jaririn da ka ɗauka ?
Ta furta hakan tana mai jin ƙwalla na cika idanun ta domin ta so ƙwarai ta ga jaririn , sai kuma ta ga har zasu tafi bata ga hoton na sa ba ,
Tiris likitan yayi yana duban ta , domin shi a idanun sa bai ga alamun ƙyauyanci har haka a tare da ita ba ,1
Wani takaici ne ya rufe hamza , shi dai gidadancin yakaka na ci masa tuwo a ƙwarya ,”
Lokacin da ake hoton ina hankalin ki yake ?? Wuce mu tafi gaba idan mun sake zuwa kya ga hoton , ya furta hakan yana mai kokarin danne ɓacin ran sa akan tsantsar son cikin da yake hangowa cikin idanun yakaka ,
Waye uban cikin ?tabbas yawan soyayyar ɗa wurin uwar sa tana da alaƙa da son da take yiwa mahaifin sa ,”
Story continues below
Bayan sun kama hanyar komawa gida yakaka ta katse shirun da suka yi da faɗin ,”
Inaso na je bakin kasuwa na ɗauko kayan mu da suke shagon da muke kwana a bakin sa ,”
Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba saboda zuciyar sa da take ta kai kawo akan son sanin ko yarinyar tana da wata alaƙa da uban cikin jikin ta ,? ko zaton sa ba gaskiya bane , ? ko dai da amincewar ta ta bada kan ta ga wani ƙato ??
Babu buƙatar ki ɗauko kayan , ki bar su kawai zan saya muku wasu nan gaba !
Ta bar kayan ? Yana nufin rabuwar ta da duk wani abu da ya shafi bature kam silum ɗin ta ,!’ bata jin zata iya ,’domin kome da ya shafe sa abun so da ƙauna ne a wurin ta , baya ga haka kuma ba ƙaramin taimakawa suke wurin ɗebe mata kewar sa da ke cin zuciyar ta a kullum ba ,
Ni dai Dan Allah ka kai ni na ɗauko , akwai abu masu muhimmanci a cikin jaka ta,”
Duban sa ya mayar kan ta
Abu masu muhimanci , meye su ?
Agogon sa da hoton sa ta amsa masa kai tsaye babu ƙunbiya-ƙunbiya ,!3
Gangarawa yayi gefen titi ya tsaya , tare da maida hankalin sa baki ɗaya kan ta ,”
Agogo da hoton wa ??
Ya jefa mata tambayar yana mai tsare ta da idanu ,”
Ɗago da kan ta tayi tana kallon tsakiyar idanun sa , ƙwarai yayi mata kwarjini kuma tun farko shi ɗin bai taɓa zuwa mata da sigar wasa ba , uwa uba zuwa yanzu ta san cewa abun da suka aikata da bature kam silum har ta kai ga samun ciki ba abu ne mai kyau ba , dan haka ya zama dole ta koyi boye ainahin yadda kome ya faru da dangantakar ta da shi ,”
Da inda-inda tace masa
Hoton baa-baban mu ne da agogon sa ,
Tsai yayi yana kallon cikin ƙwarar idanun ta a koƙarin sa na son gano gaskiyar ta ,”
Dan Allah ka kai ni
Ta sake yi masa magiya tana marairaicewa,”
Ɗauke kan sa yayi tare da tada motar , sashi guda na ran sa na tabbatar masa da bata da wayo da wayewar kan da zata iya masa ƙarya , sam alamun ta bai yi kama da na wacce zata iya lanƙwasa zance ta sauya masa launi ba ,”1
A dai-dai ƙofar shagon ya tsaida motar ƙarkashin umarnin ta da tace masa nan ne shagon ,”
Ba ƙaramin farin ciki abuwar mai shago yayi ba da ganin yakaka cikin ƙoshin lafiya , ya ɗora da tambayar ta falmata , domin labari ya isar masa na abun da ya same ta , ya kuma ga shaidar jini a bakin shagon sa washegarin ranar da abun ya faru ,
Ya shiga dumuwa sosai ta yadda yake ganin har da rashin taimakawar sa ya sa suka afkama masifa ,” ga yadda suka samu labari falmata ta riga ta mutu , hakan ne ma ya sa bai ko je neman su asibiti ba ,”
Bayan gaisuwa tare da jajantawa yakaka ta buƙaci ya bata jakar baccon su , nan kuwa ya fiddo mata da su , suna nan yadda suka bar su , ” a cewar sa yayi niyyar cigaba da ajiyer su domin ya san zata dawo ɗauka , nan dai suka rabu suna mutunta juna ,!
Daga yanzu baza ku sake dawowa bakin kasuwa da sunan zaman kan ku ba ,” idan ƙanwar ki ta samu sauƙi zan tafi da ku gidan mu ku zauna tare da su rahima , har zuwa ….
sai kuma yayi shiru gami da juyowa ya dube ta , ta nutsu tana saurarar sa ,”
maida duban sa yayi ga tukin kafin ya jefa mata tambaya
ko baza ku bini gidan mu ?
da sauri ta ɗago kan ta , ita kuwa da daman kullum da tunanin inda zasu samu mafaka bayan barin su asibitin take kwana take tashi ,Ta yaya zata ce baza su bi sa ba ? To ina zasu da ya wuce inda zai kai su ?? Babu !
zamu bika yaya dakta , kuma mun gode Allah ya saka da alheri ya baka abun da kake so duniya da lahira , yadda ka taimaka mana kai ma Allah ya ɗaukaka ka ,!1
sosai kalaman ta suka burge shi tare da dadaɗa masa rai , a yadda yake mata ganin bagidajiya bai taɓa zaton ta iya kalamai masu nutsuwa haka ba ,”
da murmushi a fuskar sa ya amsa a bayyane da ,
Ameen Nurii .5
Story continues below
Bayan sati biyu
Falmata ta warke ras kamar ba ita ake sallama daga gadon asibiti a yau ɗin ba , tayi ƴar ƙiba mul-mul , fatar ta mai ɗan haske ta sake washewa , fes da ita cikin jar doguwar rigar da yaya dakta ya saya mata , kafafun ta sanye cikin sabon farin silafa ɗan madina , ta ɗora ɗan bakin hijabi akan ta ,”1
Duk wani abun da ake kafin a ba wa mutum sallama daga gadon asibiti doctor hamza ya gama yi inda likitocin ta suka buƙaci ta dawo bayan sati shidda su sake duba ta , “
Rahima ita ta taya su suka harhaɗa ƴan kayan su domin tafiya da su gida , sai dai da zuwan doctor hamza yace duk su bada bokitaye zuwa buta tabarma da sauran tarkacen kayan ciye-ciyen da basu riga sun cinye ba ga marasa lafiyan da ba’a riga an sallame su ba masu ƙaramin ƙarfi ,
daga su sai ɗan ƙaramin akwatin da rahima ta basu wanda suka juye duk ƴan kayan su a ciki suka fito ,” zuwa jikin motar sa da yace su tsumaye shi a wurin , bai ɗauki lokaci ba yazo ya buɗe motar yayi musu iznin shiga , yakaka da falmata suna mazaunin baya yayin da ƙanwar sa take daga gefen sa , sannan ya tada motar suna masu barin harabar asibitin ,”
Kai tsaye ya wuce da su shagon telan da yake yiwa rahima ɗinkunan ta da shi doctor hamza ya saya atamfofi , yadiddika da ƴan lesuka , ya bata yace ta kaiwa telan ta ya ɗinkewa su yakaka , kowaccen su shiga takwas-takwas ,”
Telan ne ya buƙaci a kawo su ya gwada su domin gujewa kuskure ,”3
Da rahima ya haɗa su yace su shiga a gwada su , ya kuma faɗa musu ranar da za’a zo ɗaukar ɗinki saboda ya riga ya biya sa kuɗin ɗinkin baki ɗaya ! Har sun fara taku ya kira ta
Rahima ki sake jaddadawa tailor kar fa yayi musu ƙaramin ɗinki , ita babbar ma kawai duk yayi mata dogayen riguna buɗaɗɗu ,”
Toh ! ta amsa masa
Ba’a ɗauki lokaci ba suka fito daga shagon , rahima sai faman dariya take tana tsokanar falmata ,”
Fatima da kuɗi goggagun mata suke zuwa a maida musu fasalin jikin su irin naki , kin gan ki kuwa kamar wata “Kim Kardashian “ta ƙarasa zancen da dariya ,’2
Da murmushi akan fuskar su suka haɗa baki wurin tambayar ta wacece kuma , “kimkadarshia”???
Wata celeb ce
Ta amsa musu Tana ƙara ƙarfin dariyar ta jin yadda suka kira sunan a hargitse,”4
Yana daga cikin motar yake hango fararen haƙoran ta tana darawa , tsawon ta da takun kafar ta yana daga cikin abun da yake daɗa jaan hankalin sa akan ta , duk da cewa yanzu da cikin ya shige watan sa na biyar ya fara bayyanuwa da ya sa tafiyar ta ta tafara sauyawa zuwa irin ta mata masu ciki ,
Shima tsintar kan sa yayi yana mai murmusawa a saboda ganin fara’ar ta , ƙwarai ya fuskance ta ita ma’abociyar murmushi da haƙora ce , kusan koyaushe fuskar ta da haskakken murmushi ƙwarsi ta dace da sunan da zuciyar sa ta raɗa mata watau nurii .
Daga nan hanyar gida ya ɗauka , suna isa suka fiffito daga motar , inda yakaka take bin illahirin gidan da kallon baƙunta ,
Ku zo muje ku fara gaishe da Baban mu ,
Suka tsinakayi muryar sa bayan ya kulle motar “
Shi ya shige gaba suka doshi kyakkyawan ginin da yake tsaye a saitin su , a bakin kofar ya ce su tsaya ya shiga ya sanar da shi tukun ,”
Nan suka tsaya duk su ukun har da rahima ,”
Bai jima ba yayi musu iznin su shigo yana daga ciki,’
Tsayawa suka yi daga baya har sai da rahima ta fara shiga sannan suka bi bayan ta hannuwan su a sarƙe ,”
Babban falo ne tafkeke , dan haka suna shiga taku biyu suka yi yakaka ta ɗurƙusa bisa kafet ɗin da yake malale a ɗakin tana mai fuskantar sa fahimtar hakan da falmata tayi ya sa ita ma ta zube guiwar ta a ƙasa , suna masu gaishe shi ,”
Da murmushi a fuskar sa yace
Ku shigo , ku shigo , kar ku tsaya daga chan ku zo daga nan , ” ya musu nuni da kusa da shi a ƙasa inda rahima ta zauna ,”
Tasowa suka yi suka dawo inda ya nuna musu ,” sannan suka sake gaishe sa kan su a sunkuye ,”
Ya amsa musu fuskar sa a sake yana mai musu kallon tsanaki ,”
Daga wanne gari kuke ? Ya tambaye su ,”
Mairambiri ,” yakaka ta amsa masa ,
Mairambiri , ya maimaita tamkar yana nazarin sunan ,!
Ina iyayen ku ?
Nan yakaka ta bashi takaitatcen tarihin rayuwar su ,”
Ya tausaya musu sosai ,”
A ƙarshe yace su saki jikin su , insha Allah zai kula da rayuwar su gwargwadon ikon da Allah ya bashi , muddin suka tsaya akan gaskiya ɗa ai na kowa ne ,!
Daga haka ya basu umarnin tafiya !
Ɗakin da yake gefen na rahima wanda a da yake rufe babu kome cikin sa sai shimfiɗar kafet , nan doctor hamza ya gyara musu , aka sa musu labule da katifu madaidaita biyu , sai ƙaton wardrobe mai kofa shidda , sai fanka da bulb, akwai banɗaki a ciki , babu laifi ɗakin yayi kyau musamman a wurin su yakaka da basu taɓa shiga ɗakin da ya kai haka sun kwana ba tun da suke , dan haka su yau ran su fes zasu yi kwanan ƙarƙashin fanka bisa lallausar sabuwar katifar da ta ji sababbin shimfiɗu har da tausasan matasai ,!2
Biyamuradi youssouf ne a tsaye kan ɗan wani dutse , waya ce a hannun sa yana ta faman neman layin hajiya umma fiye da mintoci ashirin amma ya gagara samun ta , yau kwanaki biyu kenan rabon da su gaisa da gida , ya san duk inda take yanzu hankalin ta yana gare shi ,
Duk da ta san cewa a yanayin aikin su akwai haka , wani lokaci su kan rasa samun layin wayar sa muddin anka tura shi wurin da yake da matsalar hanyoyin sadarwa , kamar dai yadda ya fatu a yanzu , wajen da aka matso da su sam babu kyaun hanyar sadarwa , saboda ya sake nesa sosai da cikin gari , cikin surƙuƙin daji ne da yake gaf da bakin bodar da ta raba tsakanin niger da nigeria , babu mahalukin da ya isa ya san da mutane a gurin sai fa jami’an tsaro ƴan uwan su ,”
Motsin da yaji daga ƙasan ɗan dutsen da yake tsaye bisan sa wanda ruwa yake ɓulɓula ta tsakanin sa ya sanya shi ɗan rankwafawa ya leƙa ,zuwa ɗan kwarin da ruwan ke bi , da yake lulluɓe da bishiyoyi da Koren tsirrai shar ,
nan ya hango wata barewa tana tsaye akan ƴar ta wacce alamu ya nuna yanzu ta haife ta , domin sai faman lashe ƴar take tana ƙoƙarin ɗago ta ta tsaya bisa kafafun ta ,
Mafarkin da yake yi a jere kwanaki biyu mai yanayin kama da halin da yaga barewar nan ciki shine ya dawo cikin tunanin sa ,”
Kwanaki biyu kenan a jere yake mafarki da wata barewa tare da ƙaramar ƴar ta , maharba sun biyo su , sai faman gudu suke a sanadin haka ya sa uwar ta faɗa a rami ƴar kuma ta wuce da matsanancin gudun da ya wuce na ƴar jaririyar barewa kamar ta ,” gaban sa ƴar kyakyawar barewar take zuwa ta tsaya , shi kuma ya sunkuya ya ɗauke ta zuwa jikin sa tare da juyawa ya fara gudu da ita maharban na sake bin sa a ƙokarin su na son ganin sun karɓe ƴar barewar daga hannun sa ,’ !
Tsumu yayi ya tsirawa barewar idanu ,” yana son samun fassarar mafarkin sa ,
Ƙarar wayar sa ita ta jaa hankalin sa ga barin kallon barewar ya maida duban sa ga fuskar wayar da fatan ganin ƙiran daga hajiya umma ne ,”
Sunan tafeeda ne ke yawo bisa fuskar wayar , da ƴar fara’a bisa fuskar sa ya kara wayar a kunnen sa
Gaisuwa suka yi irin ta aminan junan da suke tsantsar ƙaunar junan su , daga nan suka ɗora hirar su akan lamuran da suka shafi aikin su ,”
Biyamuradi youssouf ke tambayar tafeedah , yaya yaga number sa ta nijer ce maimakon ta sudan ?saboda shi ma watanni biyu da suka wuce an tura su sudan akan aiki ,”
Ya bashi amsa da cewar ya gama satittikan da aka tura sa ya yi , har wani ya amshi bakin aikin sa ,”
Nan Biyamuradi youssouf ya tambayi lafiyar mutanen fada baki ɗaya a ƙarshe ya nemi da tafeedah ya haɗa shi da hajiya umma su gaisa idan ya shiga gidan saboda ya gagara samun ta a waya kwana biyu ,”
Ya ce masa shi ma tun jiya yake gwada layukan na youssouf dakyar ya samu nasarar samun sa a yanzu ,
Nan suka tsaya akan zai tafi fada ya kira shi ya haɗa su da hajiya umma , idan kuma har bai same shi ba zai isar da saƙon gaisuwar sa gare ta tare da mai martaba baki ɗaƴa ,”
Har sun yi sallama ya sake tsinkayo muryar tafeedah inda yake cewa ,”
Da farko nayi niyyar nai maka bazzata tou amma na gaza hakurewa , watanni biyu masu zouwa , zan shigo nigeria bikin iliyas wanda za’a yi cikin babban birnin nigeria abuja ,”
Da murna youssof yake bayyana farin cikin sa , ya san iliyas abokin aikin tafeedah ne da suka taɓa aiki tare a magadishu , asalin sa ɗan nigeria ne , da yakasance babban sojin sama , “
Shi ma zai so halartar bikin iliyas ɗin kwarai da gaske , tare da farin cikin haɗuwar da zasu yi da aminin sa wanda suka kwashe kusan watanni bakwai basa tare ,”
Sauke wayar yayi daga kunnen sa bayan sun yi sallama da tafeedah , bai sake bi ta kan barewar nan ba ya kaɗa kan sa ya bar wurin ,”Kwanakin da suka biyo bayan zaman Su yakaka a gidan su doctor hamza , kwanaki ne mafiya jin daɗi da walwala agare su a bakiɗayan rayuwar su ,sun gyagije sun yi fes da su tamkar da ɗai basu taɓa shan wata wahalar rayuwa ba ,1
Doctor hamza yayi bajinta sosai ta yadda ya ɗau nawin duk wasu lamuran su na yau da kullum babu gajiyawa babu ƙorafi ko tozarci irin na wasu mutanen, a gefe kuma ya gama shirin sa na sanya su a makarantu , inda ita yakaka yayi mata rajista da wata makarantar matan aure ta jeka/ka dawo boko zallah , zata fara zuwa bayan ta haihu ,1
Falmata kuma yana fafutukar nema mata wata makarantar makafi mai zaman kan ta , wanda su a shekara mutane 70 kachal suke ɗauka , yana sa ran za’a samu gurbin sanya falmata , ‘

Amma a halin yanzu su duk biyun ya ɗauka musu wasu malamai biyu mata ɗayar tana zuwa da rana kamar karfe sha biyu bayan ta taso daga makarantar islamiyyar da take koyarwa , sai ta zo ta koyar da su karatun addini , zuwa karfe biyun rana , wacce take koyar da su boko kuma zata iso karfe huɗu na yamma zuwa karfe shidda take tafiya , ita falmata kome da baki ake koya mata tana saurara a halin yanzu tun da ba makarantar su ta makafi aka kai ta ba , yayin da ita kuma yakaka ake koya mata har da rubutu ,
Kuma babu laifi ƙwarai suna da saurin fahimta musamman ma falmata , ba’a maimaita mata karatu , daga an fadi ta haddace sa kenan, ga ta da baiwar harce iya fidda lafuza Sam bata da tsamin baki, “hakan ba ƙaramin farantawa doctor hamza yake ba , da alama yaran baza’a sha wahalar sauya musu rayuwa ba !2
Ta ɓangaren ƙannan sa ma basu da wata matsala , zainab da hafsa sune manya kuma sun girme musu sosai zainab tana da ishirin da biyar hafsa tana da ishirin da uku ,dan haka tsakanin su da su yakaka gaisuwa ce kawai bayan haka ko kula sabgar su basa yi , basu ma cika zaman gidan ba domin a halin yanzu ma shirye shiryen bikin zainab ɗin ake nan da sati uku inda zata auri wani babban sojin sama ,4
ita kuwa hafsa boko yayi zafi domin yanzu ne take matakin ƙarshe a jami’a ga kuma taya ƴar uwar ta shirye shiryen biki da suke , tunda ba uwa bace da su a kusa , kusan su biyun suke duk wasu tsare-tsaren su na ƴan mata , sai kuma ƙannen mahaifin su uku mata da su kuma suke gudanar da sauran lamuran da yakamata iyaye mata suyi ,”
dan haka daga su sai rahima da ta zama ƙawar su su duka biyun suke gudanar da lamuran su , domin ta biye musu sosai tana kwasar duk wasu gidancin su da ƙauyencin su da suke yi sumfuri-sumfuri kuma dai-dai gwargodo tana iyakar yin ta wurin wayar musu da kai a duk lokacin da suka yi wata katoɓarar .1
A halin yanzu sun samu kusan watanni biyu kenan a gidan ,
Kamar kullum bayan dawowar sa daga aikin sa da ya wuni yana yi , ya shigo bangaren sa bayan ya baro bangaren baba inda ya daɗe suna tattaunawa mafi yawa muhawarar ta su akan sha’anin auren zainab ɗin ne , suna tsare-tsaren yadda kome zai tafi cikin tsari mai kyau , sai kuma a ƙarshe kamar koyaushe idan suka yi zama irin wannan sai hamza ya shigo da batun mahaifiyar su ko da a fakaice ne , a yau ma nema yayi da mahaifin nasu ya amince a sanyo ta cikin lamuran bikin zainab ɗin kasancewar ta babbar ɗiyar ta mace da a karon farko za’a aurar , a wannan lokacin fiye da lokutan baya ya ga bacin ran baban su , inda ya rufe ido yayi ta faɗa a ƙarshe yace kar hamza ya sake sako mahaifiyar su cikin lamuran bikin zainab , shine mahaifin su shi Allah ya ɗorawa alhakin aurar da ƴaƴan sa , ba wata chan daban ba wacce ta zaɓi rayuwar kororo akan zaman aure ,”4
Idanun sa taf da hawaye ya baro sashin yana jin zuciyar sa na ƙara bunƙasa girman laifin ta ,
Kai tsaye banɗaki ya shiga yayi wanka gami da ɗauro alwalar sallar magariba da ta gabato , ya zira jallabiyar sa tare da sanya ɗan silifa ya rufe sashin nasa ya nufi cikin gidan ,” hannun sa riƙe da wata ledar da ya biya ya ɗauko a mota mai tambarin “down town” , tare da wata bakar leda .
Story continues below
A zaune ya tadda su , suna sake biya karatun su da malamar su ta boko ta yi musu yanzu ta tafi ,’ Rahima na yi musu gyaran ƴan ƙananun kalmomin english da ma’anonin su da aka fara koya musu bayan sun gama haddace Alphabet ,”..
Cikin idanun yakaka ya fara jefa kallon sa, lokacin da ya ƙaraso cikin falon ,
Da sauri rahima ta miƙe gami da karɓar ledar hannun sa suna masu haɗa baki su ukun wurin yi masa barka da zuwa tare da gaishe shi ,”
Yana daga tsaye yana ɗaura agogon da ya zaro daga aljihun wandan sa yake amsa gaisuwar su , “
Da fatan suna muku karatun yadda kuke ganewa ?
Ya tambaye su yana mai nacewa kallon fuskar ta ,
A tare suka haɗa baki su biyun wurin amsa masa ,”
Muna ganewa sosai yaya dakta ,”
Toh madallah a cigaba da dagewa ,”babu dai wata matsala ko ?
Babu matsalar kome yaya mungode,!
Daga haka ya fice jin an fara kiran sallah ,
Da zumiɗin su suka buɗe ledar da ya kawo musu duk da sun riga sun san abunda yake ciki , ilai kuwa shawarma ce naɗi biyar , kowaccen su ta ɗau ɗaya suna murna, ɗaya ledar kuwa agwaluma ce manya-manya nunannu har cikin ledar , ai kuwa yakaka tana ganin agwalumar ta ajiye ƙunshin shawarmar ta gami da sunkutar ledar agwalumar baki ɗaya ,
da sauri ta yunƙura tana tura cikin ta wanda zuwa yanzu har ya shige watanni shidda , kitchen ta je ta wanko musu , ta miƙawa rahima da tace zata sanya musu a firiji ta ɗan yi sanyi kafin su idar da sallah ,
Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha’i , kamar yadda yake ka’idar sa idan ya shiga masallaci sallar magariba bai fitowa sai yayi isha’i muddin ba wani aiki ne mai girma a gaban sa ba , zama yake yayi ta karatun Alqur’ani .
Rahima , yakaka da hafsa ya tarar suna zaune a ainahin babban falon suna hira tare da kallon wani shirin larabawa da ake nunawa a tv , hannun kowaccen su riƙe da agwalumar tana shaa ,
Da murmushi a kan fuskokin su suka masa sannu da shigowa , hafsa ta miƙe ta shiga kitchen ta fito hannun ta riƙe da babban faranti wanda aka jera kuloli bisa ,
Miƙa masa tayi ,ya karɓa tare da maida ganin sa sashin da yakaka take zaune ,”
Ki shirya gobe ne ranar komawar ki asibiti su duba ki , da safe zan kai ki saboda ina da aikin safe ,”
Charaf hafsa ta karɓi zance ,”
Big bro kayi tafiyar ka kawai aikin ni zan kaita , ko ba Galaxy hospital ba?
Nan ne , amma nafi son na kaita da kaina saboda akwai wata matsala da muke kan tattaunata da likitan ta ,”
Ki ƙira min zainab ku zo sashi na tare inason yin magana da ku ,!1
Daga haka ya juya yana barin wurin ,
Ya bar hafsa nan tsaye da tarin wasi-wasin da take yi akan alaƙar yayan su da wannan ƴar gudun hijirar , kulawar da ta lura yana bata yayi yawa ya wuce na taimako ,” meye a tsakanin su ? Tasan yayan su kamili ne kuma managarci bata zargin zai aikata wani mummunan abu , tunanin ta yafi karkata akan wani yanayi da take hangowa a kan fuskar sa a duk lokacin da ya ga yarinyar da kuma tsantsar kulawar da yake mata duk a sunan taimako ,” ko ma menene a sannu zata kai ga fahimta fatan ta Allah ya sa ba abun da take zato bane , ,”1
Cikin sati biyun da suka biyo baya shiri ake gadan-gadan na bikin zainab shi da kan sa hamza bai zauna ba , shirye shirye suke ka’in da na’in kasantuwar wannan ne biki na farko da za’a yi a gidan nasu , ƴan uwan su na nesa nesa duk sun fara isowa , haka ma wasu ƙawayen zainab ɗin sun fara sintiri ganin cewa an shigo satin fara bikin sam ƙafa bata ɗaukewa a gidan , ƴan aiki huɗu mata doctor hamza ya kawo amma duk da haka aiki da aike chakuɗe musu yake ,’
Yakaka da Falmata duk a takure suke , ko falon basu cika son fitowa ba suna ƙunshe cikin ɗaki sai fa idan rahima ta tuno su tazo ta ishe su da surutu tare da mitar meyasa basa son fitowa cikin jama’a ,” ??
Story continues below
Yau ya rage saura kwanaki uku ayi ɗaurin aure kuma a yau ne za’a fara gabatar da shagulgulan bikin , inda a yau ɗin ne suke shirin yin arabs day dan haka gidan danƙam yake da ƴan mata kawayen ita amaryar da yawancin su daga nesa suke , sun yi guzurin manyan jakankunan su da suke cike da suturun su zuwa kayan kwalliyar su da takalma , dukkanin su gogaggu ne kuma wayayyu , kuma ƴaƴan manya irin ta, yawan su ya sa ɗakin ta ya gaza ɗaukar su , dan haka suka rarrabu wasun su suka samu wuri a ɗakin hafsa , da rahima , sauran ukun kuma suka sauƙa a ɗakin su yakaka ,
Tashin farko lokacin da suka shiga ɗakin da suka ga su yakaka , ɗaya daga cikin su ta tambayi zainab ɗin da ta rako su ɗakin da kan ta
Friend Waɗannan ɗin su waye ?
Ƴan gudun hijira ne ,’ ta basu amsa kai tsaye
Yakaka ga ƙawaye na dallah ku ɗan ara musu shimfiɗun ku kafin …..
Tun kafin ta ƙarasa babbar ƙawar ta da tun da suka shigo ɗakin take yatsina tana ƙarewa ɗakin kallo , tace
Zee mekike nufi ? Kaddai kice min kan shimfiɗar da ƴan gudun hijira suka gama birgima zamu kwanta ? Kalan mu ɗauki wata cutar ,? Ko kuwa kwarkwata ta maƙale mana ko amosani ?
Wata ƴar iskar dariya suka kwashe da shi ,”kai sofi baki da kyau ,kuma fa da gaskiyar ki ,”
Ɗan murmushin ƴake zainab tayi2
Kai haba dai sofi , baki ga sun waye bane ? Ai kin ga babu alamun ƙazanta har haka tattare da su ,” amma bari na samo sabbbin bedsheets idan ya so sai ayi sauya muku, sai su kuma su koma falo suna kwanciya kawai haka yayi ko ? Ta furta hakan tana mai barin ɗakin cikin sauri domun ta kawo bedsheets ɗin , har tayi nisa ta tsinkayi muryar ɗayar su tana cewa ,”
Ki zo da germs kill/anti bacteria dan a wanke bathroom ma sosai da kuma room freshener ,”
Ta amsa da toh ,”tana ƙara sauri .
Sai kuwa ga ta da duk abubuwan da suka lissafa ,’
Su kuma har lokacin suna tsaye akan kafafun su , suna hirararrakin su tare da latse-latsen waya ,2
Nan ta zube kayan a gefe ,
To wa zai gyara ɗakin ina housemaid ?
Cikin ƙosawa zainab tace duk basu nan sun tafi kasuwa ,”
Duban ta ta mayar kan su yakaka da suke zaune daga gefen wardrobe sun yi shiru kamar ruwa ya cisu , duk suna jin maganganun su ,”
Ke fatima tashi ki je ki wanke musu bathroom ke kuma yakaka ki sauya bedsheets ɗin tare da share musu ɗakin ya fita da kyau ki fesa turaren nan , ” ta mayar da duban ta kan ƙawayen ta , muje ɗaki na kafin su gama aikin sai ku zo ku shirya , “
Daga haka suka kama barin ɗakin suna masu cigaba da dararrakin su ,”
Ɗan shiru ne ya ratsa ɗakin , kamar haɗin baki kowaccen su ta ce
Bari ni zan yi aikin yakaka ke baki da lafiya ,’
Bari ni nayi duk aiyukan falmata ke ki zauna anan ki jirani ,”
Nan suka kama musu ƙarshe a dole falmata ta sakarwa yakaka dukkanin aiyukan ganin har ran ta ya fara ɓaci ,”1
Bata ɗau lokaci ba ta gama , zuwa tayi ta kama hannun falmatan zo muje mu faɗa musu mun gama sai mu samu wurin zama ko ta waje ne mu zauna ,”
Sama-sama zainab ɗin ta amsa musu lokacin da suke sanar da ita sun gyara ɗakin ,’ saboda hayaniyar ƙawayen ta da ta cika ɗakin ,”
Nan suka kamo da baya tare da kama hanyar barin falon , kichiɓus suka yi da hafsa tare da wata ƙanwar baban su da ta titsiye ta tana mitar ta ƙira mata hamza ya zo ya ƙaro musu ma’aikata ,’domin aikin yayi yawa yafi ƙarfin ƴan aiki huɗu baza su iya bada abunda suke so ba ,”
Wayar ta sa taƙi shiga ga alama a kashe take watakila yana kan aiki ne ,”
Auntie hajja wayar ta sa bata shiga , amma ga waɗannan su biyun su ma ƴan gudun hijira ne kawai aje da su wajen da ake aikin su kama , kafin a ƙaro wasun ,” ta furta hakan tana mai nuna mata su yakaka da suke ƙarasowa wurin ,’
Kallon su tayi sama-da-ƙasa , kafin ta ce
Toh su zo mu je ,”1
Story continues below
Ku bita zaku je wurin aiki , ta furta musu hakan tana mai shigewa cikin falon ba tare da ta ko sake waiwayo su ba ,’
Jikin su ba ƙwari suka bi bayan wacce aka ce su bitan , har zuwa wani faffaɗan fili da yake ta chan baya ƙarshen gidan , inda aka kafa babbar rumfa aka kakkafa manyan murhu da takwane , gefe guda ga manya-manyan kasko da aka cika shi fal da mai ana suyar dubulan da alkaki , ga kuma manyan daruna an cika su fal da ruwan narkakken sugar ,”
aiki dai kacha-kacha ta ko’ina , da kallo yakaka ta bi hamshaƙan matan su kusan rai shida da suke tsaitsaye akan aikin , daga wuya zuwa kunne da hannuwan su sai ƙyallin gwalagwalai suke , yayin da daga sun buɗe baki hasken haƙoran gwal da suka yi ado da su a hakoran su yake ɗauke ido ,”
ko alama hannun su bai taɓa aikin ba , illa wasu jikkatattun manya mata su huɗu da suke yin duk wasu aiyukan wajen suna ta faman kai kawo ,”
Ga wasu masu aikin biyu ƴan mata an ƙaro su ,”
Cewar wacce suka biyo ɗin ,’
Waɗannan ai yara ne wane aikin kirki zasu yi da ya wuce wanke wanke da aike ? Inji ɗaya daga cikin matan ,”
Ko shi ɗin ma dai su yi , ai kuma zasu iya irin su soya abubuwa ma , “
Ke babbar ki zauna anan ki cigaba da suyar dubulan ɗin nan , ƙaramar kuma ga wanke wanken abubuwan da aka yi ƙwabin fulawar a ciki ki wanke ki kawo mana zamu sake yin amfani da su , cewar ɗays daga cikin ƴan aikin ,’
Cikin ƙasƙantar da kai suka haɗa baki wurin amsawa da toh ,’ aiki ba sabon abu bane a wurin su , kuma basu jin tsoron aiki kome yawan sa ,”
Yakaka ta kama hannun falmata ta kaita wurin da aka tara wanke wanken manyan darunan silver da farantan silver manya da a zahiri sun fi ƙarfin hannun falmata ,
Ga bakin fanfo falmata ta sanya mata bakin tiyo ɗin da yake zubar ruwa akan hannun ta , kuma ga omo ga soso , ki wanke da kyau kin ji ?idan kin gama ki min magana kar ki taso ke ɗaya kin ga gurin akwai murhu ,!
Toh yakaka
Daga haka ta je ta kama aikin da ita ma aka sa ta ,
Yakaka ta kama wannan aikin ta gama ta hau wancen , falmata tayi wanke wanke ta ƙara , har yamma suna wannan wurin , nan suka ci abincin rana da yin sallolin , gajiya tilis sun yi ta musamman ma yakaka da bayan ta ya riƙe ƙam , ‘kawai karfin hali take amma a zahiri aikin yayi mata yawa , ‘ daga inda suke suna jiyo yadda ƙidan wakokin larabawa suke tashi ta cikin gida tare da tsinkayo hayaniyar jama’ah ,”
Karfe biyar aka sake kawo wani aikin wanda girki ne za’ayi na abincin dare a ainahin babban kitchen ɗin gidan , nan aka bar su yakaka suyi zaman gadi a wurin tare da ƙarasa tsoma sauran dubbulun da alkakin a ruwan sugar kafin a zo a juye su a ma’adanai a killace su,
Har karfe takwas na dare suna wajen , zuwa lokacin hayaniya ta ɗan ragu a gidan ,saboda ɗaukewar kiɗa , sai dai shewa da dararrakin jama’a , falmata har ta fara gyanyaɗi saboda tsabar gajiya ,”babu abun da take so irin ta ji ta kwance bisa ƴar katifar ta amma ta san yau kam babu damar hawa wannan katifar ,
Chan sai ga hamshaƙan matan nan sun zo tare da wasu mata da alama su ma ma’aikata ne , nan suka ce su juye kome a manyan robobin tara ruwa , bayan sun sallami su yakaka babu ko sannu bare nagode , ! To meye ƴan aiki ne fa ? !1
A gajiye liƙis suke cire takun kafafun su , duk sun yi laushi ,’ ko magana sun gaza yi da juna burin kowaccen su ta samu muhallin ajiye haƙarƙarin ta
Tun daga bullowar su farfajiyar gidan hasken da yake wadace gal a wurin ya haske fuskokin su , babbar mashigar kofar gidan a buɗe take motoci sai kai kawo suke ,
Sun kawo tsakiyar farfajiyar kusa da ƴar hanyar da zata sada su da cikin sashin kwanan su , ya sanyo kan motar sa cikin gidan ,’ idanun sa suka sauka a kan su , me suke yi a nan da daren nan wajen karfe tara ? Da sauri ya ajiye motar sa a mazaunin ta ya fito dags cikin motar yana bin su da kallo nan ya hango yadda suke duk a hargitse , kasan zanin falmata duk a jiƙe ,”
Ya taka da niyyar bin su , sai wasu ƴan uwan su mata su kusan rai biyar suka kutso kai cikin gidan , suna hango shi kuwa suka nufo shi suna gaishe shi tare da tsokanar shi kasantuwar su abokan wasa , nan dai dole suka tsayar da shi da ƴar hirar su ta zumunci ,
Zuwa lokacin da suka wuce su yakaka sun riga sun shige sun ɓacewa ganin sa ,
Story continues below
Shiru yayi a tsaye yana sake tunano yanayin da ya gan su ciki , ” ba dai aiki aka sanya su ba ? Ya tambayi kan sa ,”
Nufar sashin sa yayi yana haɗa kamannin da ya gan su ciki da wanda yanzu ya ga yaran matan nan ƴan uwan sa a ciki , hakan ya tuno masa da abunda baki ɗaya ya manta “watau yiwa su yakaka ɗinkin fitar biki,” al’amura sun haɗu sun chakuɗe masa , yanzu haka fita zai sake yi domin yana so ya ƙarasa shirye-shiryen kome kafin jibi da tawagar masu neman auren zasu iso daga garin abuja ,” a ɗaura a basu matar su juya da ita bayan anyi walima ,” sauran bukukuwan chan a abuja zasu ƙarasa bikin irin na su na soji ,”
Sannan a daren na yau yana so ƙwarai ya je yaga mahaifitar sa a unguwar da tayi bigire,’2
Duk yadda za’a yi dai goben zai samu ya saya musu kayan fitar bikin ko da ready made ne saboda lokacin yin ɗinki ya ƙure ,” da wannan tunanin ya ƙarasa shigewa sashin sa ,’
Su yakaka a cike suka tarad da falon duk kuwa da girman sa ,”yaran mata ne masu aure da marasa aure birjik a falon su da ƴaƴan su ,kowacce tana wace wance ,” kaf ɗin su dangin juna ne , saboda ta bangaren mahaifin su manyan gida ne kuma shahararrun masu kuɗi kaf garin ansa kakan su wanda ya haifi baban su ,’
Kamar jiran shigowar su hafsa take wacce take tsaye suna magana da wata ƙawar su ,” tace
Yauwa yakaka dan Allah ɗauki Mopper nan ki goge duk illahirin cikin falon nan saboda akwai ruwa-ruwa kar a tattaka a faɗi ,”
Cikin juriya yakaka ta amsa
toh anti hafsa ,
Tas ta goge faffaɗan tiles ɗin ta ɗauraye mopper ta ajiye , ta dawo inda ta bar falmata a tsaye ,daga bakin kofa ,
Falmata zo muje ki gani na gano mana wurin kwana ,”
Wata ƴar siririyar hanya ta kai su da take bangaren hagu na falon da wata ƴar kofa ɗaya jal ta karfe , ta tsakanin karafunan kofar yakaka ta hango step ɗin bene , da yayi sama wanda a duk zaman ta a gidan kusan watanni biyu bata san cewa akwai bene ba ta cikin falon ,”
Kinga sai muyi kwanciyar mu anan tunda babu kowa , koh ?
********
Daidai da rana guda bai taɓa mantawa da ƙanƙanuwar yarinyar da ya lalatawa rayuwa ba , kullum sake ganin laifin kan sa yake a duk lokacin da yayi hasashen irin halin da ya bar ta da wanda a yanzu zata iya kasancewa a ciki ya kan shiga zullumin da yake kai ga hana shi walwala ,,
Yayi nadama marar iyaka da ta sa har yau yana laluben neman sanin haƙiƙanin abunda ya same shi a wancen lokacin da har ya aikata abunda ko a mafarkin sa bai taɓa nuna masa shi youssouf zai aikata ba ,’ idan akwai abunda yake bashi mamaki da sanya shi hamdala bai wuce wucewar wannan lamarin ko kuwa yace warkewar ciwon da ya kai shi ga aikata mummunan aikin ba , tun daga ranar da ya bar ta bai sake jin son kasancewa da wata mace a irin wannan yanayin ba , ya koma youssouf ɗin sa da ya san kan sa ,”1
Ko ruwan burkutu yanzu ba sosai ya cika neman ta ba , sai jifa jifa jarabar sa da burkutun ya ragu da kusan kaso shidda cikin goma , kuma a lokuta da dama ko giyar company ma ya samu ya ɗan kurɓa yana jin kwaɗayin sa da barasar ya kau ,
Bulayin neman abunda zai sa shi ya goge laifin sa ko kuwa ya gyara barnan da yayi a wurin yarinyar , ya sanya shi ɗaukar tsawon lokaci bai sake waiwayar ta ba duk da cewa sau da dama a farkon rabuwar su ya sha ganin kiran ta ta layin da ya saya mata , kafin daga baya ya daina ganin kiran ,
Ya shiga damuwa da har ya sashi fara neman layin nata sai dai amsa guda yake samu kullum daga computer shine wayar tata a kashe take ,” meya same ta ? Wane hali take ciki ? Wacce irin rayuwa take yi ?? Bai sani ba !
Story continues below
Zuwa lokacin da ya samar da abun da yake ganin zai taimaka mishi gurin gyaro ɓarnar da yayi , kuma sai yanayin aiki ya tsaida shi ,tare da sake yin nisa da inda take , amma ya ƙudurce ba zai bar kasar ba har sai ya gyaro barnar da yayi ta hanyar da shi yake ganin ya dace ,”
Dan haka da yanzu ya samu damar da zai iya fita daga wajen aikin ya taka zuwa cikin garin da take , domin a jiya da suka yi waya da tafeeda ya sanar da shi cewa ya shigo ƙasar nigeria a halin yanzu yana abuja , ‘
biyamuradin ya tabbatar masa da cewa zai halarci wurin ɗaurin auren , aina za’a yi bikin ɗaurin auren ? Amsar da ya bashi faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama domin ya tabbatar masa da auran a jahar borno za’a ɗaura shi cikin birnin na maiduguri ,”
shikenan ma ba sai na zo har abuja ba , zan tsumaye ku cikin birnin maiduguri domun ai cikin garin nai bigire ,” amsar da youssouf ya bawa tafeeda kenan !
Washegari , tun sassafe aka kaɗa kan su yakaka zuwa wurin aiki , ba’a ko bar su sun karya ba , sune shara wanke-wanke goge-goge basu nan basu chan , sai misalin sha ɗayan rana aikin ya dan tsahirta musu , suka shigo gidan suna rarrakaɓewa saboda kallon hadarin kaji da ake bin su da shi ,
Wanka suke so suyi su sauya kaya domin rabon su da wanka tun shekaran jiya , amma ko da suka shiga ɗakin da yake a zaman nasu , kawayen zainab da suke ta faman harƙƴallar su a ɗakin wasu na wanka wasu na karin kumallo koro su suka yi basu ko saurari zantukan da suke da nufin faɗi ba ,
haka suka fito jiki a sanyaye suka dawo bakin kofa suka rakaɓe ,”
Suna nan tsaye ya danno kan sa cikin sashin , yayi wankan sa fes cikin wani brown ɗin yadi mai shara-shara , sosai kayan suka ƙarbi kalar fatar jikin sa mai ɗan haske kaɗan ,
Akan su ya fara ɗora ido ,”
Me kuke anan fatima ?
Ya na gan ku haka wani iri ?
Anyi muku wani abu ne ?
Kun kuwa ci abinci ?
Ƙwallar da tuntuni take taruwa a idanun falmata suka tsiyayo ,” lokacin da take saita idanun ta a sashin da ta ji tashin muryar sa
Mun ci abinci yaya dakta , kuma ba’a mana kome ba , cikin ne babu wurin zama sosai shiyasa muke tsaye anan ‘yakaka ta amsa masa ,
Wanne irin babu wurin zama ?ba ga ɗakin ku ba ku shiga ciki kuyi zaman ku mana ko kun fi son zaman parlour ne??
Wannan Karon falmata ce tayi karaf ta amsa
Ai ƙawayen auntie zainab sun cika ɗakin , korar mu ma suka yi da muka shiga muna son muyi wanka mu chanja kayan mu ,” ta furta hakan tana turo ɗan ƙaramin bakin ta bayan ta kumbura kumatu ,”irin su da ɗakin su ɗin nan,” ( su falmata samun sarari tusar asuba )4
Da kallon nazari yake bin su , yana ƙoƙarin boye ɓacin ran sa a gaban su kan abunda aka musu ,
To wai ya na gan ku kun yi datti haka ,? Ba dai aiki kika je kina ta faman yi ba a wannan yanayin da kike ciki ?
Tun jiya muke aiki yaya dakta yanzu ma muka gama na safe , cewar falmata , irin su a dole ga garkuwar su ,( ja’ira falmata an samu wuri )4
Gabaɗaya bacin ran da yake ji ya bayyana saman fuskar sa , wanne irin aiki zasu sa ƴar mutane da ciki ?
Har ya taka da nufin shiga gidan sai kuma ya jaa ya tsaya ,
Ina rahima ?
Story continues below
Ya tambaye su ,”
Cikin rashin jin daɗin yadda falmata ta bayyana masa laifin ƴan uwan sa , yakaka ta amsa a sanyaye
Tun jiya ban gan ta ba yaya !
Baice kome ba ya zaro wayar sa daga aljihu ya shiga neman layin rahima ,”
Bugu ɗaya ta ɗauka
Hello big bro ina kwana ?
Rahima kina ina kizo yanzu ina kofar sashin ku ,”
Toh ,” ta amsa
Ba’a cika mintuna huɗu ba sai ga ta ta fito daga cikin gidan ,”
Gani big bro ,” ta furta hakan tana mai washewa yakaka haƙora gami da kashe ido ɗaya irin na shakiyanci ,”
Ki je da su ɗakin su suyi wanka su shirya ku zo tare ke da su ,” ya bata umarni fuskar sa babu alamun wasa ,”
Toh ta amsa tana mamakin ɗakin nasu kuma zata raka su ? Kai big bro yana ji da baƙin nan nasa anya anya anya kuwa ,” tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yace ,”
Kice ga duk wanda ya nemi hana su yin abun da nace , umarnina ne a bar su suyi wanka su shirya ,” nan ta fahimci akwai abunda ya faru ƙila hana su wanka aka yi , to wa ya hana su ?
Tana shiga ɗakin ta samu amsar tambayar ta domin suna sanyo kafa cikin ɗakin sofi wacce take rangaɗa kwalliya tace ,”
Kai kai ku koma , wai meye kuke mana sintiri kalen ku baɗa mana ƙwarƙwata ?? Daga kun zo wuri sai kun sauya kalan ƙanshin sa ,”cikin ran ta tana ji haka kawai ta tsani yaran ,” ( karfin hali )1
Da hannu biyu rahima ta dafe bakin ta kafin ta ce
lalala anty sofi baƙin big bro ne fa kuma ma daƙin su ne ,” yanzu ma shi yace na rako su suyi wanka su chanja kayan su ,”
Baƙin ƴan gudun hijira ko dai bakin doctor ?
Wallahi baƙin sa ne shi ya kawo su ,”
Yakaka ku shiga kuyi wanka , ba kowa a bathroom ɗin ko ? Ta furta hakan tare da ɗan kwankwasa kofar banɗakin ,”
Falmata shiga ki fara yi ta furta hakan tana mai kaucewa mugun kallon da sofi take watsa musu ,”
Wata purple and black ɗin atamfa yakaka ta cirowa falmata daga cikin kayan su , sabuwa ce dal falmatan bata ko taɓa sawa ba , ta miƙa mata banɗakin lokacin da tace ta gama wanka , ita kuma ta fiddo wani pink colour ɗin yadi ɗinkin doguwar riga ta riƙe a hannun ta ,
Tsaf falmata ta fito cikin kayan da ɗinkin sun bala’in karɓar ta dinkin riga da siket ne na yayi wanda rahima ta zaɓar mata style ɗin ya zauna ɗas a kyakyawan jikin ta , baki ɗayan ƴan matan ɗakin suka bita da kallo lokacin da take wuce su tana nufar inda ta ji muryar rahima ta ƙira ta ,”
“,surar jikin fatima abar kallo ce
shine abun da rahima ta ambata aran ta lokacin da ta lura da kallon sake bakin da wayayyun ƴan matan suka bita da shi1
Gyara mata ɗaurin ɗankwalin rahima tayi gami da rufa mata bakin mayafin akan kafaɗun ta wanda ta zame daga jikin ta ,”
Cikin ran ta tana dariyar shirun da ɗakin ya ɗauka ,” a hankali ta furta
Duk ta sumar da su ,!2
a gurguje yakaka ta yi wankan ta shirya ta fito , ta sanya ɗan madaidaicin hijabin ta fari mai hannu akan doguwar rigar da ɗankwalin ta fuskar ta fayau ko mai babu ,
Story continues below
Suka bar ɗakin ƙarƙashin rakiyar dogon tsakin da sofi ta bisu da shi ,” a sarari rahima ta furta kya ji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa , big bro dai kwalelen ki , ko dan wannan mugun halin naki ma zai sa ya tsane ki ,”aikin banza ,1
Yana hango su ya nufi motar sa ya buɗe ya shiga ,”
Tare da rahima suka ƙaraso jikin motar ,”
Ta sunkuyo saitin sa ,
Big bro na cika aiki na , ?
Baki cika ba rahima , ki shigo mu tafi ,
Ɗan jimm tayi , ” bata son fitar domin tare da ƙawayen ta take suna shirye shiryen yadda anjima zasu tsantsare a wurin sisters day ,”
Shikenan je ki abin ki tunda baki son fitar ,”
Ta marairaice murya Big bro kayi hakuri ƙawayena zasu je nayi musu walakanci idan na tafi na bar su ,”
Toh rahima mai jama’a , agaida kawayen ,!
Ya furta haka yana tayar da motar sa bayan yakaka ta shiga gaba ta zauna rahima ta kamawa falmata ta shiga baya ,”
Kai tsaye ya nufi tata saloons da bashi da wani nisa sosai da gidan su ,”
Tun da suka tsaya gaban shagon bugun zuciyar yakaka ya sauya ,” mikin da yake ciwo cikin ran ta ya dawo ɗanye , hotunan al’amuran da suka gudana a tsakanin su ya fara dawo mata , gata da soyayyar da ya gwada mata na ɗan lokaci suka bijiro mata son da take mishi ya yunƙuro da wani irin ƙarfin da ya sauya bugun zuciyar ta da har hakan ya jawo abun da ke cikin ta ya motsa da ƙarfi ,”1
Har abada baza ta so wani namiji makancin son da take masa ba ita ta sani ta kuma haƙiƙance da hakan ,” shi ɗin na daban ne cikin rayuwar ta kamar yadda son shi yake da wani irin ɗanɗano na daban a cikin ran ta ,” wanda yake bata nishaɗi tare da kashe mata jiki a lokaci guda ,”
A hankali ta ɗaga kai tana kallon ƙaton board ɗin da yake kafe a gaba kaɗan da inda suka tsaya da motar su a gaban shagon ,” karon farko da tayi ƙoƙarin haɗa baki ,”tunda aka fara koyar da su
A hankali leɓen bakin ta suka motsa
TA-TA
sunan wajen da yake ɗaya daga cikin wuraren da baza ta manta su ba a tarihin soyayyar su , wurin da ya sha gwada mata ƙaunar sa batare da jin nawin mutanen da suke kallon su ba , a gaban su ya nuna ita ɗin abar son shi ce abar ƙaunar sa wacce ya zaɓa ,”3
kafin zuwa lokacin da kome ya sauya , kome kuma ya ƙare ya tsaya ƙem har zuwa lokacin da komen ya ruguje ,
rugujewar da ta samar da mummunan rauni a zuciya da gangar jikin ta , sai dai tana ji a jikin ta zuciyar ta kuma tana faɗa mata , komen bai ƙare ba kuma kome zai sabunta kan sa a watarana ,1
sai dai abunda ta kasa samun tabbaci akan sa shine yau ne ko gobe ne komen zai dawo ?bata da tabbacin dawowar sa alhalin kuma shine komen da zuciyar ta ke ɓida a kowanne daƙiƙa bayan daƙiƙa .
Wani irin farin ciki yaji lokacin da ya fahimci ta iya karanta sunan wurin da ya kawo su ,” idan hakane tabbas kwakwalar ta mai saurin ɗaukar karatu ce , ƙwarai zasu shirya shi da ita , wata rana kuma zsi yi alfahari da ita , da alama ƴaƴan sa zasu samu haziƙar uwa ,”
Yes sunan wurin kenan
Tata saloons ,” ya furta mata hakan da murmushi ɗaure kan laɓɓan sa ,3
Da ido ta bishi tana mai jin haushin katse mata ɗan daddaɗan yanayin shauƙin da ta tsinci kan ta a ciki na tunanini abun son ta ,
Rufe motar suka yi bayan sun sun fiffito , yakaka ta kamo hannun falmata ta riƙe cikin nata , ,”
Bissmillah muje
Yace da su ,” yana yin gaba ,”
Story continues below
Kamar yadda suka tsanmata gurin akwai mutane ,amma kasantuwar akwai wadatar ma’aikata nan take biyu daga cikin ma’aikatan suka taso taryar su , ɗaya daga cikin ma ta gane yakaka domin ta sha yi mata gyaran jiki ,”
Madam sannu da zuwa ta furta hakan tana mai yiwa yakaka murmushin sanayya ,
Ɗan yaƙe yakaka tayi a ranta tana furta ,’na shiga uku Allah ya sa kar su nuna sun sanni ,”
Madam kin kwana biyu baki zo ba , ma’aikaciyar ta furta haka daidai lokacin da take basu wurin zama ,”
Shiru yakaka tayi tana satar kallon doctor hamza wanda shi kuma hankalin sa ya tafi ga ɗayar ma’aikaciyar inda yake faɗa mata yana son ganin ainahin ita shugabar su ,”
Cikin girmamawa tace bari ta shiga ta sanar mata ,”
Ƴar wata ƙofar gilashi da take daga gefe a cikin shagon nan ma’aikaciyar ta shiga ,’ bata ɗauki lokaci ba ta fito tace zai iya shiga wurin shugabar ta su ,”
A cikin mutunci suka gaisa da hajiya Ruma’yassa’u, nan ya shaida mata kaya yake nema ready made na ƴan mata ,”
Ta tabbatar masa da suna da kaya masu kyau da inganci domin a jiya ma wasu ɗinkakkun kayan suka iso , dan haka sai wanda ya zaɓa tsakanin atamfa , leshi , shadda , yadi da sauran nau’ikan suturun mata , kawai abun buƙatar a zo da magnitude ɗin mai kayan ko kuwa shi kan sa , ya sanar da ita tare suke da waɗanda zasu sa kayan ,” nan tace a shigo da su ,
Kallon sani take yiwa fuskar yakaka amma kasantuwar its ƴat kasuwa ce da take chuɗanya da mutane da dama ssi ta watsar da laluben inda ta san fuskar yarinyar , ta miƙe gami da cewa su biyo ta su da ma’aikaciya ɗaya dake tare da su ,”
Har ta ɗsn yi taku ta jiyo da murmushin nan nata mai haiba tana gyara mayafin kan ta tace ,” akwai iyakacin adadin na kuɗin da keke so su ɗauka ne ?? Kuma shiga nawa zasu ɗauka ,”
Su ɗauki duk wanda suke so kuma kika ga ya dace da kowaccen su , ” ki zaɓa musu ,” shiga uku uku ,”
Toh shikenan ranka ya dade ,”
Ta cikin shagon suka ɓulla ta wata ƴar kofa zuwa wani kawatatcen shago mai zaman kan sa , ta ko’ina kayayyaki ne wasu a rarrataye wasu a cikin closets ɗin gilashi , kaya dai na kece raini tare da ɗaukar hankalin mai kallon su ,
Wurin zama ta basu akan wata doguwar kujera , bayan ta umarci ma’aikaciyar da ta gwada mata su mataki-mataki na jikin su , kai tsaye ta nufi faffaɗar closets ɗin ta shiga zaro wasu tsantsara tsantsaran lesuka masu ƙananun huji duk jikin su da mabanbantan kaloli da aka yiwa ɗinkin wasu kyawawan dogayen riguna , buɗaɗɗu da tsukakku , gajerun hannu da dogaye ,
Tana daga inda take ta tambayi size ɗin su nan ma’aikaciyar ta sanar da ita ,” a take ta zaro huɗu daga cikin lesukan masu size ɗin da aka faɗa mata ,”
Bayan nazarin da tayi a matsayin ta na cikakkiyar malamar kwalliya wacce kuma ta san takan kwalliya da ado , ta zaɓarwa yakaka wata buɗaɗɗiyar doguwar riga mai rufaffen wuya turquoise color, ( ban San sunan launin a hausa ba ) mai adon wasu siraran zare silver ,
Falmata kuma ta zaɓar mata ita ma wata doguwar riga da ta tsuke tum daga sama har zuwa cinyoyin ta ta ɓuɗe ta kasa , mai buɗaɗɗen wuya scarlet color, ” da adon golden.
Kowaccen su dai-dai da tsawo da jikin ta , sannan ta zaɓar musu wasu atamfofi da aka yiwa ɗinkin riga da siraran siket sai dai ita yakaka tata rigar har kusan guiwar ta take yayin da ta falmata ta tsaya iyakar cinya , ta yakaka background din ta dark red pattern din kuma aka yi da salmon and moss color , ta Falmata kuma background din fari ne pattern din kuma freesh grass and carnation color,
Sai yadika da suka ɗauka su duk biyu iri ɗaya see grean da aka yiwa ɗinkin buba da single zane ,’
Iyakar kyau kayan sun yi kyau , domin shi da kan sa doctor hamza ya yaba ya kuma ji daɗin gani zaɓin da hajiya ruma tayi musu , dan haka bai ji ƙyashi ba ko kadan ya lale makudan kuɗaɗen ya biya kuɗin kayan da ko a mafarki su yakaka basu taɓa hararo kan su a cikin irin su ba ,” aka haɗa musu kayan har da gyalalluka bibbiyu da takalma masu kyau kafa biyu da ya sake saya musu aka sanya musu cikin babbar ledar mai ɗauke da tambarin TATA SALONS ,
Story continues below
Har zasu tafi ma’aikaciyar nan da ta gane yakaka tace
madam yau ba gyaran jiki ne da gyaran kai ??
Cikin tsanaki doctor hamza ya mayar da ganin sa kan yakaka wacce ta langwaɓe kai tana kifkifta ido duk wasu alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskar ta ,”
Bai hango kome ba bai kuma fahimci komen ba illah hasashen sa ya bashi tabbacin tana so ayi mata gyaran jikin ita ma ,’bisa ga kallon da take masa mai kama da roƙo ,” ,
Ayi musu gyaran jikin da wankin kai amma kar ayi musu kwalliyar nan ni ban cika son ta ba ,” yace da wacce ta nace sai ta fasa ƙwan yakaka ,”3
Toh yallabai
ta amsa tana mai shiga rudu ,
da tayi zaton wani ɗan uwan mijin yakakar ne kamar yadda suka yi zaton biyamuradi mijin yakaka ne , sai dai kuma kalaman wannan na yanzu ya sata wasi wasi da chanki-chankin wanne ne mijin tsakanin farin dogon kyakyawan bamarɗen mai cike da ginshiri da ƙasaita irin na saraki , ”
da kuma wannan matsakaicin mutumin wanda tarin nutsuwa da kamala gami da tsantsar ilmi suka bayyana kan su a tattare da shi ,” ????? ( toh nima dai tambayar da nake yiwa masu karatu kenan ??? )3
Gata dai ta gan ta har da ciki bayan tsawon watannin da suka yi rabo da ganin ta tabbas matar aure ce ,’
Tattara gulmammakin ta tayi ta adana su gefe suka fara goge tare da sumulmule jiki , daga kafafu har kan su yakaka da falmata ,”
Basu suka bar wajen ba sai misalin karfe uku na yamma, iya wankuwa sun wanku fuskar su har sheƙi take , babu wata kwalliya da aka musu a fuskokin su sai fa siraran lallen da aka tsantsara musu yiryir a ƴan hannayen su da ƙafafu karkashin umarnin hajiya ruma a zuwan tukuicin da tayi musu na cinikin da aka mata tare da karrama abokan ciniki irin nata ,”
Kyau kam sun yi shi ƙamshi kuma sai tashi yake a sassan jikin su , falmata jin ta take kamar mai yawo a gajimare saboda yadda iska yake ratsa kowanne sako na jikin ta , yakaka kuwa lumshe ido tayi akan hanyar su ta komawa gida tana tuno wani yanayi irin wannan a tsakanin ta da biyamuradi , da hakan yake sanya ta sakin murmushi lokaci-zuwa-lokaci saboda hotunan fuskar sa da suke ta gilmawa ta idanun zuciyar ta
Yayin da shi kuma doctor hamza yanayin da ya gan ta ciki ya sanya shi nishaɗi har shagala yake wurin satar kallon ta ya manta da tukin da yake yi ,’ sai fa idan motocin bayan sa sun matsa masa ham ,3
Sun dawo sun tarar da gidan kamar yadda suka zata a cike danƙam motoci sai fita suke da ƴan matan da mata domin tayi party ,
Ganin cinkoson ya sanya doctor hamza sauke su daga bakin babbar kofar yace su shiga shi zai juya , su bar kayayyakin a cikin mota da daddare zai shigo musu da shi , su tabbatae sun samu wani wuri sun ɓuya daga idanun masu sanya su aiki ,
Duk da kusan kowa harkar gaban sa yake a farfajiyar wurin amma hakan bai hana falmata fahimtar yawan idanuwan jama’ah da yake yawo akan ta ba ta hanyar jin tsikar jikin ta na ta miƙewa , hakan ya sanya ta sake ƙanƙame hannun falmata
Wacce itama ta sunkui da kan ta cikin jin nawin idanun mutane da ta gani a kan su ,
Tun da suka ratso wurin take bin su da kallon mamaki , tabbas sune toh me kuma ya kawo su yaks gidan bikin zainab ?? Wai daman ashe da yaks ta gudu wani wurin daɗi ta samu ya sanya ta ji ta shiru da a farko ta dunga zaton wahala zai dawo da su da kafafun su ,” bata buƙatar a sanar da ita tabbas yakaka da falmata suna cikin kin daɗi domin kuwa ta ga sauyi a tattare da su a zahiri1
,” shegiya yaks farar mace alkyabbar mata kyakkyawar mace kadara ,’ babbar haja da ba’a raba ta da masu tayin saya ,” ta furta a zahiri ,”
Kafin ta daddage ta kwalla mata kira daga inda take tsaye a jikin motar ƙawar su1
Yaks Yaks Yaks ,
Chak suka tsaya daga ita har falmata kirjin su yana dakan sha tara ,”didif-didif-didifdif ,.