MAFARI CHAPTER 8 BY UMMU AZAMM

MAFARI CHAPTER 8 BY UMMU AZAMM

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari da misalin tara na safe , jirgi ya ɗaga da Tafeeda zuwa birnin Lagos inda ta chan zai wuce ƙasar su ,+

Dukkanin su shi da Biyamuradi babu mai isashiyar walwala suka yi sallama , alhalin basu kai ga cimma matsaya guda kan matsalar su ba ,

Duk da cewa bangaren youssouf ya ji kaso sittin cikin ɗari na damuwar sa ta tafi , saboda ya bayyana ta ga aminin nasa , ya kuma san Tafeeda zai yi duk yadda zai yi ya ga ya dai-daita kome a gida kafin komawar sa , yanzu babbar matsalar sa ita ce rayuwar ɗiyar sa ,

A daren jiya kwana yayi yana dogon nazari akan yadda zai yi ya ga ya bata ingantatciyar rayuwa ba tare da gurbatatciyar hanyar da aka samar da ita ta zama ƙalulabe a gare ta ba , da mutum yana iya sauya kaddarar sa da a daren na jiya ya juya , ya gyaro hanyar da aka yi ƴar nan ta sa ta zo duniya , amma ya riga ya san bakin Alƙalami ya bushe ,

hakan ya sa ya ɗau ƙuɗirin zai jajirce akan duk wani ƙalubale da shi zai iya cin karo da shi cikin rayuwar sa wajen ganin ya inganta tare da kyautata rayuwar ɗiyar sa ta FARKO a duniya ,”

Tafeeda kuwa ya bar ƙasar ran sa cike taf da tunanin yaya zai yi yaga ya boyewa hajiya umma musabbin shiga damuwar yarima ? Ya zai yi ya boye mata irin mummunan aikin da yarima ya aikata ? Yaya zai boye mata samuwar wata haramtatciyar ɗiya daga tsatson ta ? Kome yana neman kubce masa , shi ya kasance a tsakiya ne , ɗan aike ne shi , sai dai saƙon da zai koma da shi a yau me nawi ne wanda ya fi ƙarfin fitowa daga kan harshen sa ,1

Cikin awanni (2) da tashin jirgin su daga Murtala Mohammed International Airport Lagos, Ya samu dira a Diori Hammani International Airport Niamey , duk yadda ya so ya tsaya wajen ‘ubbo’ su gaisa kamar yadda ya tsara , ya gagara saboda rashin nutsuwar zuci , Allah-Allah ya ke ya samu isa wajen hajiya umma ,”

Jirgin da zai sada shi da Maraɗi kai tsaye ya hau , yana isa gidan su wanka kawai yayi ya sauya kaya ,ko abinci bai duba ba ya yiwa fada tsinke , nan ya nemi iso ga hajiya umma , aka yi masa ba tare da jinkiri ba ,”

Bayan ya gaishe ta yayi shiru yana son samun ƙarfin guiwar faɗin abinda ya shirya ,”

Yayin da ita kuwa hajiya umma baki ɗaya ta tattara hankalin ta gare shi , tana nazarin sa ,” ita ta katse shirun da tambayar sa ,’

Yaya kun ka ƙarƙe da yarima ? Shin ya sanar da kai damouwar sa ? Ko kouwa ?

Ƙwarai ranki ya dade yarima ya shaida min basshi da watta damouwa da ta wucce , na rashin aboukiyar zama , inda har ya nouna ra’ayi da zai yiwu ma yana buƙatar a amra masa mataye biyu a rana gouda wanna shine ɗai guda damouwar yarima , sai kouma yace ayi albishir yana nan tafe nan da ƙarshen wata me kamawa, bayan haka yarima yana nan lafiya cikin yanayi mai kyau !

Tafeda ya ƙarasa zancen sa yana sunkui da kai da jin kunyar ƙaryar da ya gilla , wacce rashin mafita ya ja sa ga aikata ta ,”

A take fuskar hajiya umma ta yalwatu da fara’a zuciyar ta ta haskaka , har haƙoran ta suka bayyana ,”3

Alhamdulillah , Madallah da kai Tafeeda yaron kirki , tashi maza ka tahi ka sanya a fara shiri tare da gyara ga bangaren da anka gina na wagga ɗiya ƴar mutan agades , zan yi magana da mai martaba akan buƙatar da yarima ya tado da ita , amsa zai isar maka , Madallah da kai ,Madallah !

Godiya Tafeeda yayi tare da miƙewa yana barin shigifar , yana sake ganin dacewar shawarar da ya bayar na aurawa Yarima mataye ganin sa hakan ne mataki na farko na dakile sa daga sake faɗawa cikin wata musibar a gaba , domin ya ƙare nazari kaf rashin aure shine dalili na farko da har ya sa Yarima faɗawa ga zina ,2

Yana fatan yadda ya rufa asirin mummunan labarin nan a nan gaban hajiya umma , Youssouf ma ya rufawa kan sa asiri ya bar ɗiyar chan a Nigeria kamar yadda ya faɗa masa , idan kouwa har ya ƙi jin shawarar sa babu shakka jiki magayi ,”duka da ɗanyen kara ,” tsuntsun da ya jaa ruwa kuma shi ruwa kan doka , shi dai yayi iya yin sa ,”

STORY CONTINUES BELOW

Faɗuwa ta zo dai-dai da zama , shine abunda hajiya umma take kitsimawa cikin ran ta , ganin cewa a saukaƙe tare kuma da haɗin kan yarima auren sa da Siyama zai tabbata , kai wannan Al’amari yayi kyau gwanin daɗi , cikar gata da martaba ne ga ɗan nata ya auri mataye biyu a rana gouda , tabbas maƙiya zasu cija yatsa , girma da martaba kouwa zasu tabbata ga Yarima Youssouf ,”

Nan ta kudurce sanar da maimartaba a daren na yau da ita ke da turakar !2

*****

Biyamuradi Youssouf yana barin airport inda ya raka Tafeeda gidan su Dr Hamza ya nufa , maigadi shi ya nema masa izni,

Yana shiga ya tadda prof yana karin kumallo , suka gaisa faram-faram nan ya masa umarnin ya matso su ci abincin ,

Babu musu ya wanke hannun sa ya matso suka fara cin abun ƙarin ,”Fankaso ne da miyar ganyen alayyahu , sai kuma danderun tsokar ƙaramar dabba , gefe guda kuma kwaɗon zogale ne da yake mahaɗin kowanne cin abinci na prof ,sai kuma green tea ,

Sosai ya nutsu ya ci abincin yana yabawa girkin maiduguri , bayan sun gama cin abincin ne prof ya gyara zama yana fuskantar Youssouf ɗin ,cikin nazari yace

Zan so ka sanar da ni takaitatcen tarihin ka da kuma halin da ka kasance a ciki bayan rabuwar ka da iyalin ka da ta sanar da mu cewa ka mutu sanadin ƴan tawayen nan na boko haram ,”

Shiru yayi yana jin yadda tausayin ta ke sake mamayar sa , Allah sarki ashe ta rufe kome , ta rufa musu asiri , ta lulluɓe laifin sa , ta gyara masa asalin ɗiyar sa a idanun jama’ar ta , idan haka ne shi kuwa zai cigaba da kare martabar ta a idanun su har abada , shi ma bazai taɓa tono laifin su da ta binne ba ,

Asali na ni mutumin niger dagga yankin ,”Malbaza Uzine,” dake ƙassar Tahoua ,” ni sojja ne aiki ya shiggo da ni nan nigeria har munka yi amre da itta , bayan amren mu bada jimawa ba boko haram sunka kawo hari mahaɗar mu inda sunka far mouna da yakin da yayi sanadiyyar rabouwar mu har ta kai ga tayi zaton na moutu, sun ka yi gudun hijira zouwa nan ,”

Lokacin da kuka yi aure a hannun iyayen ta ta karbi auren ta ?

Mukut ! Biyamuradi ya haɗiyi yawu , shi wannan mutumin matsayin me yake gare ta ? Zaton sa ɗan ouwa ne ga mahaifi ko mahaifiyar yarinyar ,”1

Cikin ƙosawa yace

Mahaifi gare ta ya rassu , sai dangin ta ,”

Kayi hakuri ina maka tambayoyi ne domin mu tabbatar da gaskiyar Alaƙar ku saboda yau duniya babu gaskiya ,”

Mu ma ta shaida mana mahaifin ta ya rasu sanadin tarzomar boko haram , mahaifiyar ta tare da sauran dangin ta sun bata , ta zo nan mun ƙarbe ta tare da ƴar uwar ta sai kuma juna biyu tare da ita wanda ta rasu wajen haihuwar ƴar, ɗan waje na shine ya kawo su nan bayan ya tsince su suna walagigi cikin wahalar rayuwa a bakin titi ,

Ya tsahirta ,

Yana duban Youssouf wanda idanun sa suka yi jaa saboda jin tausayin Yakaka da ahalin ta,

Idan har dattijon nan da ya ɗauka wani jigo ne ga yakaka , yace shi bashi da wata alaƙa da su asalima taimakon su ɗan sa yayi suka kasance ƙarƙashin inuwar su , shi kuwa ai babu dalili ɗaya da zai sa ya bar ɗiyar sa hannun su , wajibi ne ya tafi da ƴar sa ,

Kamar Prof ya san tunanin da Youssouf ɗin yake yi , sai yace da shi

Idan ka shirya tafiya da ƴar ka , koyaushe zaka iya zuwa ka amshe ta , tana tare ne da ƳAR UWA ga mahaifiyar ta wacce ka gan ta riƙe da ita jiya ,”

A hankali ya ɗago kan sa , yace zan iya ganin su ?

Ƙwarai kuwa bari a ƙira su ,”

Cikin mintuna kaɗan falmata riƙe da baby mama ƙarƙashin jagorancin hajja mai wurya suka bayyana a falon , fuskar falmata babu walwala , saboda ƙiran da aka mata na cewa ta kawo baby mutumin jiya ya dawo ganin ta , tambayar kan ta take yi wanene wannan mutumin da yake ta zaryar ganin baby mama ,? Ita fa sam bata ƙaunar abunda zai ratsa tsakanin ta da ƴar kome ƙanƙantar sa ,

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ta gaishe da prof da take jin tashin muryar sa tun shigowar ta falon ,

Yace da hajja mai wurya

Ƙarbi ƴar ki miƙa ta ga mahaifin ta , mun riga dai mun mata hudhuba tare da yanka kamar yadda addini ya zartar , ƙarƙashin yaddar uwar riƙon ta kuma ƴar uwa ta jini ɗaya da muka sani tare da yarinyar kafin bayyanar ka , amma kana da ikon sauyawa ƴar ka suna !

Janye ƴar falmata tayi ta hana hajja mai wurya damar ɗaukar ta ,”

Waye baban baby ? Waye yace shine baban baby ? Baby ƴar mu ce ni da yakaka na , mu kaɗai muka haife ta , yanzu da babu yakaka ni ce mama , baba , yaya , kanwa , da gabaɗayan danginta , ko waye ma yace shine baban ta ƙarya yake muku wallahi ƙarya ne , ta ƙarasa zancen tana fashewa da kuka !2

Turus !

Biyamuradi Youssouf yayi yana bin fuskar ta da kallo , ƙwarai ya shaida waɗannan idanuwan nata masu girma , ita ce wannan ƴar yarinyar da ta nemi yi masa faleƙe lokacin da ya fara tako kafafun sa cikin wannan gidan , biki , a watanni baya , ashe rashin sani shi yafi dare duhu , ashe ya tako har gidan da take lokacin da yake bulayin neman ta ? Allah ya raba ganawa a tsakanin su ,1

Wani tsoro ne ya ji yana taso masa daga ƙarƙashin ran sa , tsoron kar ƙanwar ta ta san kome ? Kar ta tona asirin da shi da yakaka suka binne ,! Kar ta furta kalmar da zai shata layi tsakanin sa da mallakar ƴar sa , dan haka cikin sarƙewar harce yace ,

Du-duba kin ka ce baki shaida ni ba ? Baki gane ni ba ?

Cikin hargagin kuka tace waye kai ? ni ban san muryar ka ba , aina ka san mu ? Ni da yakaka bamu da kowa a duniya kowann mu sun mutu , sai mu biyu a karshe Yakaka ma ta mutu ta bar ni tare da baby , bamu da kowa ni da baby , Baba wallahi ƙarya yake yana so ya ƙwace min baby dan Allah ku hana shi taɓa ta ,

Wani kallon yatsutsu hajja mai wurya da daman cike take da halin ƙwalafaci da rashin yardar da falmata take gwadawa kowa akan baby mama , tace

Ji min karfin hali ?? Ji min abun mamaki ƙurege da faɗa wa zomo daɗin ƙanzo , yanzu ke saboda Allah yarinyar nan un un un Falmata kike da suna ko wa ?? Yanzu ke uba zaki hanawa ɗaukar ƴar sa ?? Ina kika taɓa jin anyi haka ? Ina kika taɓa jin ɗa ya zama ɗan mace da dangin ta ita kaɗai ?? A rashin yardar taki da kowa kuma har da uban ƴar ?? Ni dalla bani ƴa na miƙata ga uban ta , har akwai martabar da ta zarta ta mahaifi ga ɗan sa , ?1

Kukan da falmata ta fashe da shi wanda ya ja ƴar jaririyar ma ta tsanyara kuka shi ya sa Youssouf zabura akan kafafun sa ya miƙe ya tsaye ,

Kyale matta ɗiyar , batta ta cigaba da riƙon ta ,

Fatima zahra, yi shiru abun ki babu mai raba ki da ɗiyar nan , ɗiya ai taki ce , ki daina kuka kin ga ita ma kuka take ,

Lallashin ƴar ta shiga yi tana yi tana share hawayen ta , ‘

Duban sa ya maida kan prof da yake yawo da idanun sa a kan su, cikin ruɗani yana son fahimtar mai gaskiya a tsakanin su ,”

Baba Fatima ta samou watta larura ne ?

Ya furta hakan da sigar tambaya cikin son cire zargin da ya fara hangowa a idanun prof ɗin ,

Bata da wata larura bayan wacce muka gan ta da ita ta rashin gani , sai dai ko rashin ƴar uwar ta ya sa ta a ruɗani ,!

Hamdala Youssouf yayi a cikin ran sa , ashe ma makauniya ce , idan haka ne kome zai zo masa da sauƙi ,

Babu shakka ta shiga ɗimuwa da yassa ta gaza gane ni , a bar ta kar ayi mata zancen kome har zouwa lokacin da zan dawo bayan kammaluwar aiki na ,

Toh babu damuwa Allah ya kai mu lokacin ,

Fatima ku koma ciki tunda dai kin ƙi a bashi ƴar ,

Falmata da bata saurarar zantukan su ta himmatu wurin rarrashin ɗiyar da take gaba da sauran mutanen da suke wajen a wurin ta ,

cimak! ta miƙe tsaye , riƙe da jaririyar da take ƙoƙarin komawa baccin ta ,

Hajja mayar da ni ciki

Tace ga hajja mai wurya wacce take ta faman kyeɓe baki ,

Yanzu Allah baza ki bada ƴar nan ba Baban ta ya gan ta falmata ?

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Youssouf da har lokacin bai zauna ba yace , ƙƴale mata ɗiyar nan Babaa , batta ta cigaba da riƙon ta , ita ma ɗiyar ai tata ce ,”

Ta gaban sa suka zo giftawa , yana bin su da kallon ƙwalafacin son ya ga ko ƴar fuskar ƴar ta sa, yadda falmata ta kumburo fuska ta haɗe girar sama da ta ƙasa yaso bashi dariya ,ita a dole kar a taɓa mata ƴar ta ,

ƙwarai sai ya ji ta burge shi , yadda ta jajirce take ƙoƙarin bada kariya ga ɗiyar sa ya motso shauƙi daga ƙasan ran sa , ashe ba shi kaɗai bane yake jarumi akan ƴar ta sa , ashe ba shi kaɗai bane yake Ƙoƙarin bata kariya , ashe bayan shi ƴar sa tana da wata ƴar ƙaramar katangar da take kare da ita , da idan ta bunƙasa zata iya zama dangar dutse da babu saran da ya isa ya samu na bayan ta , madallah da ke FATIMA ZAHRA .1

A gurguje Youssouf yayiwa Prof sallama da zummar dawowa nan da ƙasa da kwanaki arba’in lokacin da zai kammala aikin sa , zai dawo tafiya da ƴar sa ,

Zaro damin kuɗi yayi daga Aljihun sa ya ajiye a gaban prof ,

Baba ga wannan a ƙara cikin hidimar gida madallah nagode da karamcin ku ina nan dawowa ba da jimawa ba !

Kul ,

Ɗauki kuɗin ka , bazan karba ba , hidimar fatima da jaririya zai cigaba daga aljihuna kamar yadda yake a tun farkon zuwan su har sai lokacin da riƙon su ya bar hannun na , dan haka ka ɗauki kuɗin ka , Nagode

Ganin ba fuska ya sa Youssouf ɗaukar kuɗin sa , godiya mai tarin yawa yayi masa kafin ya miƙe yana barin gidan

Cikin ran sa da addu’ar Allah ya sa har ya dawo yarinyar nan da aka ƙira da suna fatima bata ɓata masa shiri ba , sai dai yana jin bama zata iya ba saboda ganin sa yafi kowa iko da ɗiyar sa nan duniya !1

******

Abuja

Cikin sati biyu duk wani shirin makaranta ya kammala ga Yakaka , inda samy baby ta zaɓar mata ,”Eyes Scholars School ,”wacce take makarantar boko da take chakuɗe da arabi tsantsa, a matsayin makarantar da take so yakaka ta dunga karatu ,

Duk da cewa Alhaji Gali attajiri ne kuma fitatcen ɗan kwangila amma sai da aka samu tsaiko gurin ɗaukar yakaka a makarantar , domin a cewar hukumar makarantar yakaka bata chanchanta da shiga ajin gaba da primary ba bayan interview ɗin da aka mata kamar yadda samy baby ta so a sanya ta , hukumar makarantar ta tabbatar musu da cewa ko ɗaliban su ƴan primary school sun wuce yakaka a matakin karatu ,

Bayan kai kawo da Alhaji Gali da shi ke ɗauke da nawin kome na dangane da karatun yakaka , ya dunga yi

Kuɗi da Alfarma suka yi aikin su inda hukumar makaranta ta amince da shigowar yakaka cikin jerin ɗaliban su ƴan matakin ajin farko na secondry school jss1 , tare da sharaɗin Alhaji Gali zai ɗauki mai yiwa yakaka ,”extra lesson”,koyarwa na mussaman daga cikin malaman su na makarantar da kuma zai dunga biyan malamar a duk wata , domin a cewar su chakuɗa irin yakaka da bata san kome ba tare da sauran ɗaliban su zai iya kawo naƙasu ga karatun sauran ɗaliban su da suke aji guda da ita wanda a ƙarshe zai tado da ƙorafi daga iyayen yaran da zai iya kaiwa ga duƙushe tasirin ingancin makaranta a idanun jama’a ,1

Ba tare da ƙorafin kome ba Alhaji Gali ya amincewa sharaɗin su , ganin sa ai duk abunda yayiwa samy baby bai faɗi ba , tana biyan sa dan haka bashi da asara ,1

Nan take ya lale ya biya kuɗin malamar da zata dunga yin extra lesson ɗin inda aka zaɓar mata wata yarinyar mace da ashekaru zata haifi yakakar , tana tsakanin shekaru 36-38 , malama maryam ita ke ɗaukar su yakaka fannin I.R.K , ( Isalamic Religion knowledge ) abunda kuwa ya sa hukumar makaranta ta zaɓe ta shine domin zamantowar ta jajirtatciyar malama da ta kware a harkar koyarwa , duk da cewa fannin addini take koyarwa amma sun san zata iya koyar da yakaka English da Arabic sosai ta yadda gaba zata fara gane karatu da kan ta , bugu da ƙari gani da suka yi location ɗin gidan ta da na su yakaka duk ɗaya ne , dan haka suka ɗora mata wannan nawin ,2

STORY CONTINUES BELOW

Babu musu malama maryam ta ƙarbi form ta cike a matsayin ta na malamar da zata dunga extra lesson na musamman ga sabuwar ɗaliba yakaka , ranta cike taf da farin cikin samun wannan damar na amsar wani ƙarin kuɗi akan albashin ta na kowanne wata wanda kusan da shi rayuwar su ita da ƴaƴan ta da mijin ta suka dogara , zuciyar ta cike da burin zage ƙwanji ta koyar da yakaka da dukkanin iyawar ta har sai watarana anyi mamaki , .1

Ga bangaren yakaka bata jin kowanne irin yanayi dangane da sabuwar rayuwar ta na jin daɗi ko akasin sa , iyaka ta san har zuwa yanzu da take samun wajen sati uku a sabuwar rayuwar ta , kewa tare da so gami da tausayin rayukan nan biyu da ta bari a bayan ta yana nuƙurƙusar zuciyar ta tare da yiwa walwalar ta kisan mummike ,1

Ko yaushe kewar falmata ta dame ta takan zauna tayi kuka iya kuka , tana son sanin a wanne hali suke ciki ita da ƴar jaririyar da ta bari ? Tana son jin tashin muryar falmata ,

Sai dai a ɗan tsukin zaman da ta fara yi a gidan samy baby da irin mutanen da take gani a gidan tare da saurarar wasu daga cikin hirarrakin su da fiye da rabin sa ba ganewa take ba , ya sa ta sake kafa naci akan neman ilmi ya kuma sa ta fahimci shi ilmin ashe muhimmancin sa ya kai sai ya wadata ga mutum sannan mutum yake samun cigaba da kaiwa ga wani matsayi a rayuwa ,1

dan haka ta kuɗurta cikin ran ta a yanzu komawar ta ga su falmata bai da amfani , zata tsaya ne ta nemi ilmi iya yin ta , tunda dama ta samu gare ta , ta yadda ita ma zata tsaya da kafafun ta , ta koma rayuwar ta ta baya ta gyaro kuskuren ta , ta ɗauke ƙanwar ta da ƴar ta , su ma ta tsaya musu suyi karatu su samu ilmi ,3

bata tunanin akwai azal , bata tunanin lokacin ba a hannun ta yake ba , bata tunanin shi lokaci juyawa yake yana wucewa cikin kowacce daƙiƙa da idan kuma har ya wuce baya dawowa , shin ko lokaci zai jira yakaka har zuwa cikar burin ta kome yana nan yadda yake kamar yadda ta tsara shi take kuma buri ???7

Duk yadda yakaka tayi zaton samun ilmi na da sauki ta tadda abun ba haka nan yake ba domin tun ranar da ta sanya kafafun ta cikin makarantar da awanni kaɗan da suka wuce daga ta tuno da kusantowar ta ga fara zuwa makaranta neman ilmi ji take farinciki na mata lulluɓi , da har take sakin murmushi akai akai ,

Labarin ya sha banban lokacin da yakaka ta sanya ƙafafun ta cikin ajin da aka mata jagora tare da bata tabbacin nan ne ajin karatun ta ,

Tayi zaton zata tadda ƴan mata sa’o’in ta ne a ajin a matsayin abokan karatun ta , sai ta tarar da yara ƙanana da manyan cikin su ma Falmata zata iya girme musu ,

Jiki a sanyaye ta bi bayan mai mata jagora inda ya kai ta chan ƙarshen ajin ya nuna mata wajen zama ,

Zama tayi tana satar kallon yaran da kusan su dukkanin su suka waigo suna bin su da ido ,,alamun mamaki ɗauke akan fuskokin su har wasu daga ciki na magana da junan su ƙus-ƙus1

Hankalin ta bai sake tashi ba sai da ta ga malami ya shigo yayi koyarwar sa ya gama , bata kai ga fahimtar ko kalma guda ba saboda bata jin yaren da yayi magana da shi , cikin rashin sanin ta bayan darasin da malamin integrated science ɗin ya koyar da su har ,”class work/aikin cikin aji ,”ya bayar yana jiran su kammala ya bi ya duba ,1

Ɗaya bayan ɗaya ya dunga bin ɗalibai yana duba class work ɗin da ya basu , ya yabawa wasu , wasu kuma ya gargaɗe su , duk dai cikin yaren da yakaka ba fahimtar sa take ba , har ya zo kan ta ,

Wani kallon gargaɗi yake jefa mata

Hey what are you doing here? Go back to your class now ,”

STORY CONTINUES BELOW

Ƙifin-ƙifin da ido yakaka take yi tana kallon sa , tare da wasa da bakin ɗan madaidaicin hijabin ta,

I say Go back to your class,!

Ya daka mata tsawar da ta firgita ta

Dariyar da mafi yawan yaran ajin suka kwashe da ita shi ya sa malamin mayar da hankalin sa gare su ,

Hey what’s wrong with you class ?

Uncle she is our classmate , she’s a new comer,

Wasu yara kusan su hudu suka haɗa baki wajen faɗi , suna cigaba da dilliƙar dariyar da tun shigowar yakaka suke son yin ta ,1

Ya buɗe baki da nufin sake yin wata maganar shigowar malama Maryam ta katse shi ,

Ɗalibai suka miƙe domin gaishe ta ta dakatar da su ,suka koma suka zauna tana jefa musu tambaya cikin harshen larabci tace

Aina huwa ɗalib jadid Yakaka Gali ?

Da hannun su suka yi mata nuni da inda yakaka take zaune ta sunkui da kai idanun ta taf ƙwalla , tana jin yadda idanun malamin nan ke yawo akan ta da kallo mai ɗauke da ƙasƙanci ,

Ɗan takaitatcen bayani malama maryam tayiwa malamin nan akan yakaka a ƙarshe ta nemi alfarmar tana so tayi magana da yakaka a wajen class ,

Ya bata izni yana shaida mata shi ya gama da ajin ma , lokacin sa ya fita , sai na malamin darasin gaba ,

Da hausa malama maryam tayiwa yakaka tausasan kalamai tare da gabatar mata da kan ta a matsayin malamar ta da zata dunga koyar da ita inda ta nemi da ta jajirce akan duk wani ƙalubale da zata fuskanta a yayin neman ilmi , ta kuma dage ta buɗe kwakwalwar ta ya zama tana maida hankali tana koyon duk abunda ake koyar da ita , har ma tayi mata albishir a gaba idan ta dage ta iya karatu za’a mata chanjin aji zuwa na manya sa’annin ta , a ƙarshe kuma ta gargaɗe ta akan ko kusa kar ta bada ƙofar da yaran nan zasu raina ta , ta tsayar da karfe 7am na safe zuwa 8am a matsayin lokacin da zata dunga koyar da yakaka darussan da suke cikin yaren English , karfe 4pm zuwa 5pm kuma ta koyar da ita Arabic da littatafan addini ,

Godiya mai tarin yawa yakaka tayi mata tana share ƙwallar idon ta da hannuwan ta biyu ,

Kafin ta juya ta koma cikin ajin ƙarƙashin umarnin umarnin malama maryam !

Cikin kwanakin da suka biyo baya yakaka ta kafa naci ta ƙarfi da yaji so take ta ga tayi ilmi ,” bata da wani lokaci sai na karatu ta tattara duk wasu al’amuran da suka shafi rayuwar ta na baya ajiye shi a waje guda cikin zuciya ta ta killace su gefe , da gaske so take ta yaƙi jahilci , so take ta ci gajiyar ilmi so take ta goge kalmar wawanci da aka mata laƙabi da shi , so take lokaci yayi saurin juyawa wanda zai zo mata da sauyi daga JAHILA ZUWA MALAMA .1

Gidan malama Maryam bayan layin gidan samy baby ne , ɗan madaidaicin gida ne inda suke rayuwa ita da mijin ta da ƴaƴan su uku , babbar ƴar ta lubna zasu iya zuwa sa’anni da yakaka , sai maza biyu faruq da sadiq , a halin yanzu Lubna tana ss2 , faruq yana ss1 sai sadiq da yake jss3 , mahaifinsu ƙaramin ma’aikaci ne da yake aiki da wani company ,”

Rayuwar gidan Malama maryam abun sha’awa ce duba da yadda suke masu ƙaramin ƙarfi amma rayuwar su cike take da wadatar zuci , soyayya da shaƙuwa gami da tausayin juna a tsakanin iyayen da ƴaƴan su ya yawaita , da hakan ya zama abu mafi muhimmanci da ya haifar da ingantatciyar tarbiyya a wajen ƴaƴan su ,

STORY CONTINUES BELOW

tare da taimakon tsayayyar uwa da suka samu , malama maryam mace ce wacce ilmin addini ya wadace ta , take kuma aiki da shi, a yanzu matakin karatun ta degree ne a fanni Arabic And Islamic Studies , sai dai mai fadadawa tare da zurfafawa cikin neman ilmi ce musamman ma na addini, a bangaren bokon ma ba baya bace ,

Yanayin ɗabi’un ta su ke sanya take birge duk wasu mutanen da suka mu’amalance ta , komen ta cikin tsari da nutsuwa take yin sa , bayan wadatatciyar tsaftar da ta bayyana kan ta agare ta a duk inda ta kasance ,

A tun ganin farko da Malama Maryam tayiwa Yakaka yadda ta tarar yara na yi mata dariya , ta ji tausayin yarinyar ya tsirga mata , ta san babu shakka wani shamaƙi mai girma ne ya tauye yarinyar ya hana ta samun ilmi akan kari , dan haka ta ƙudiri aniyar jan ta a jiki , ta yadda zata tunga taimaka mata tare da ƙarfafa mata akan harkar karatu ,

Ganin suna kaiwa har kusan magariba kafin su dawo gida idan ta tsaya yiwa yakaka lesson saboda nisan dake tsakanin makarantar da unguwar su , yasa ta cewa yakaka su dunga komawa gida tare idan kowaccen su ta je gida tayi sallah ta ci abinci , sai yakaka ta zo har gidan ta suyi lesson ɗin , wanda lokacin da take ɗauka tana yi mata lesson ɗin ma ya zarce awa ɗayan da makarantar ta sharɗanta mata ,

Sannu sannu saboda nacin karatu irin na yakaka da kuma samun fuska da tayi wajen malama maryam da take kira ,”anty,” wacce ta sake mata sosai babu tsangwama ko kyara a yayin da take koyar da ita , ya sa har ranakun da babu makaranta ma yakaka zuwa take su ɗauki lokaci ana mata lesson ko na arabi ko na boko , wanda malama maryam ta lura yakakar tafi kafa naci akan na bokon tamkar dai tana da wani lulluɓaɓɓen burin da take son cikawa ta hanyar karatun bokon , babu laifi ƙwaƙwalwar yakaka tana da saurin fahimta hakan ya sa take jin daɗin koyar da ita ,1

A hankali sabo ya fara shiga tsakanin yakaka da lubna wacce take yarinya mai tsananin wayo , hankali da manyance , cikin abunda bai fi sati uku ba da fara zuwan yakaka gidan su ƙawance ya ƙullu tsakanin su kasancewar halin su na nacin karatu da ya zo ɗaya , saboda lubna mai naci da ƙwazon karatu ce duk kuwa da cewa makaranta mai sauƙin kuɗi suke karatu ita da ƙannen ta , amma saboda kaifin ƙwaƙwalwar su , da kuma tsayuwar iyayen su akan fannin karatun su ya sa ko yaran da suke karatu a shararrun makarantu kuɗi baza su fi su ilmi ba ,”

Nacin karatu biyu ta haɗu dan haka bayan lesson ɗin malama maryam , lubna ma ta na koyawa yakaka wasu abubuwan da suke ma sunfi matakin karatun ta , a cewar lubna lokacin da yakakar zata kai matakin ta riga ta koya baza ta ji wahalar karatu ba ,

A wani yammaci lubna da yakakar suna zaune kan ƴar darduma a tsakar gida bayan lubna ta gama koya mata karatu , suna ƴar hirar su kafin malama maryam ta gama ƴan aikace-aikacen da take yi a ɗakin baban su ,

Lubna ta dubi yakaka wacce ta duƙufa tana kwafar rubutu daga jikin textbook ɗin ta ,

Yakaka ku ƴan wanne gari ne ? Naga zane a fuskar ki , kuma hausar ki ma wata iri ?

Ba tare da ta ɗago ba tace

Ni ƴar maiduguri ce !

Su maman ku da ƴan uwan ku duk suna maiduguri ne , ? Kin ce nan da antyn ki kike zaune ,

Tsam yakaka tayi ta bar rubutun da take ,”

Ganin shirun ta ya ɗauki lokaci ya sa malama maryam fitowa daga ɗaki da duk hirarrakin nasu daman a kunnen ta yake ,

Lubna tashi maza ki ɗora girki , yakaka kawo textbooks ɗin ki mu fara karatu ,

Babu kuzari tare da walwala a gare ta suka yi karatun suka gama da bata wani fahimta ba ko kusa , da malama maryam ta lura da kyau ma sai ta ga taruwar hawaye a gurbin idon yakakar lokacin da suke yin sallama zata tafi gida , bata ko jira rakiyar lubna da take raka ta kofar gida ba , tayi tafiyar ta ,

Tana fita malama maryam ta ƙira lubna ta zaunar da ita tayi mata faɗa sosai akan bincikar mutum game da abunda ya shafi rayuwar sa kai tsaye ba tare da shi wannan mutumin shi yayi ra’ayin kan sa , ya bata labari ba,

STORY CONTINUES BELOW

Nan tayi ta ba wa mamar ta hakuri tace baza ta sake ba, malama maryam tace ita ba ita zata bawa hakuri ba , yakaka zata ba wa ,”

nan tayi alƙawarin gobe idan yakaka ta zo zata bata haƙuri ,

Tun a hanya yakaka take kuka shaɓe shaɓe da hawaye har ta ƙarasa gida , tana shiga kai tsaye ta wuce samy baby tare da ƙawayen ta da suke baje a falo suna hirar su , kowacce ta bararraje kai ba ɗankwali sai tilin izgar roba da aka yi musu kitso da shi a ka ,

Chan lungun gado ta samu ta Zauna gami da haɗa kan ta da jikin gadon ta fashe da kuka me fidda sauti , kukan tausayin rayuwar da ta bari a baya , kukan ƙewa da famuwar ciwon da ke binne a ƙasan ran ta , kukan tunowa da iyayen ta , ƴan uwan ta ,garin ta , asalin ta , kukan rashin kowa na ta da tayi ,

Yaks kukan me kike haka ? Cewa nake yanzu lokacin kuka ya wuce a wajen ki ? Ashe har yanzu baki san cewa kuka baya maganin kome ba ? Baya sawa bare ya hana ?

Ko kuwa wani abun malamar ta ki tayi miki yanzu na je na ci mata mutunci ? Ki min magana mana ?

Idanun ta jazur ta ɗago kai , anty samy na tuno da su mama , baba , falmata da baby mama , bani da kowa anty samy , ni bani da kowa !

Da wata irin murya mai ɗauke da tausayi , samy baby tace ,

Kina da ni yaks , ni zan cike miki gurbin su , har zuwa lokacin da zaki koma musu ,1

Wasu sabbin hawaye ne suka zubowa yakaka ,

Falmata fa ? Waye zai zama madadi na a wajen ta ? Falmata bata da kowa ita ma idan gidan su rahima suka gaji suka kore ta ina zata je ita da baby mama ? Anty samy ina son komawa na zo da su ,!

Babu wanda zai kore su a gidan su doctor , doctor da baban sa mutanen kirki ne , ki kwantar da hankalin ki , ba yanzu bane lokacin da ya kamata ki ɗauki nawin su lokacin na nan zuwa kin ji ko ?

Naji anty samy ,

Yauwa ko ke fa ? Yakaka matar Yarima ta furta hakan tana juyawa ga barin ɗakin ,1

Da wani irin kallo yakaka ta bita ,

Yarima

Ta maimaita !

****

Kwanakin kammaluwar aikin Biyamuradi Youssouf Tare da komawa ƙasar sa suna sake kusantowa , aiki yana sake zafafa a gare su , inda cikin ƙasa da wata ɗaya aka samu asarar fiye da sojoji hamsin cikin rundunar sa , wanda hakan ko kusa ba abu ne mai dadi ba wajen su da ma gwamnatin ƙasar su baki ɗaya , duk kuwa da cewa aikin soja daman ya gaji haka , sadauƙarwa ne a bakin rayukan su ,

Dan haka duk yadda ya so ya samu damar zuwa sake ganin ɗiyar sa abu ya gagara dole ya haƙure har zuwa nan da kwanaki goma da wa’adin su yake ƙarewa ,

Baby mama sai girma take tana daɗa wayo , har ta wuce kwanaki arba’in tana neman cika watanni biyu , kome ƙin ka da jariri idan ka ga baby mama sai ta burge ka , ka ji kana son ɗaukar ta , idan kuwa ka ɗauke ta ji zaka yi ina ma a baka ita , ina ma ƴar ka ce ? Yarinya ce mai tsananin ruwan kyau bayan kyaun kan sa da take da shi , ƴar bul-bul da ita fara tas gwanin sha’awa madarar jariran da ake bata ta karbe ta ba’a ce jaririyar da ta barranta da shan nonon uwa bace ba ,1

Bugu da ƙari kulawa da lelen da Falmata take yi mata domin duk da kasancewar falmata makauniya , tsafta yana daga halittar ta ce , dan haka ko yaya ta ji wani yanayi da bai gamsar da ita ba a tare da baby mama , take zata tuɓe ta ta goge mata jiki da wiper , ko ruwan ɗumi da tawul ta sauya mata diaper da kaya , bayan wanka sau biyu da hajja mai wurya take mata safe da yamma ,” dan haka koyaushe baby mama cikin ƙamshi take da wankakkun kaya tsaf-tsaf ,

STORY CONTINUES BELOW

So da ƙaunar baby mama a bayan kowacce daƙiƙa sake ninkuwa yake cikin ran falmata , ta ɗauki duk wani so ƙauna da tausayi na duk wasu mutanen da ta taɓa so a rayuwar ta rashin su ya sa ta juye su akan ƴar jaririyar , tamkar ran ta aka taɓa haka take ji idan tace ‘uhun’ da sautin kuka ,

bata taɓa gajiyawa da hidimar baby mama , ta kan manta da yunwar cikin ta ko ƙishirwa idan ta shagaltu cikin tarairayar ta , son baby mama haɗe yake da bugun zuciyar falmata !1

Waƙoƙi iri iri take rera mata da ƴar daddaɗar muryar ta cikin yaren su , sai kuwa ƴar jaririyar tayi luf , ƙulus a kwance tana kallon fuskar falmata da tunda ta fara kallon abubuwa ta himmantu gurin tsare fuskar falmatan da idanun ta a duk lokacin da take farke , ga alama bada jimawa ba zata haddace kamannin ta tare da ɗaukar yanayin ɗumin jikin ta , ta kuma gane warin jikin uwar goyon ta da ta buɗi ido tun ranar farko ta gan ta a matsayin UWA a gare ta ,”1

******

Duk abunda aka sanyawa lokaci aka zana iyakar sa to fa babu shakka zai zo ya wuce tamkar da ɗai ba’a taɓa fara farkon sa ba ,

Yau shabiyu ga watan goma sha biyu ita tazo dai-dai da ranar kammaluwar aikin tawagar rundunar sojojin niger da suka kawo tallafi wurin yakar ƴan tawayen Boko Haram zuwa cikin yankin nigeria ta kan boda inda yankunan biyu suka haɗu na niger da nigeria ,

ƙarƙashin jagorancin Colonel Youssouf Abdul-Azizou Baskore , a kuma yau gwamnatin ƙasar su ta bada umarnin su fara janyewa daga filin daga inda waɗanda aka turo su maye gurbin su zasu samu isowa bakin dagar a yau , ‘ dan haka baki ɗayan sojojin gurin idan ka dubi fuskokin su a yalwace suke da fara’a , inda dayawa daga cikin su suke ta ihu da wasanni a tsakiyar dajin domin bayyana murnar su a fili kan komawar da zasu yi ƙasar su cikin dangi da iyalan su , bayan kwashe fiye da tsawan watanni goma sha biyu da suka yi cikin daji ,

Colonel Youssouf ya bi jerin ƴan uwan sa soji wajen bayyana farin cikin sa bisa ga wannan nasarar da suka samu na tsallake hare-haren ƴan tawayen boko haram ɗin da suka sha far musu , da kuma nasarorin da suka samu wajen fatattakar ƴan tawayen boko haram ɗin ta hanyar kashe wasu tare da kama wasu da dama , hakan a gare su babban nasara ne da dukkanin su suke sanya samun ƙarin girman matsayi daga gwamnatin ƙasar su ,

Gefe guda kuma zuciyar sa cike taf da murnar sake ganin ɗiyar sa da zai yi a yau , sosai ya zaƙu yake kuma ɗora idanun sa akan fuskar ta , dan haka duk wani abunda yake cikin ƙuzari da karsashi yake yin sa ,

Sha biyun rana tawagar sojin da zasu karbi aiki suka iso ba tare da ɗaukar dogon lokaci ba bayan musayar gaisuwa da wasu bayanai na sirri irin na tsaro da ya shiga tsakanin manyan sojojin gurin da zasu tafi da sabbin da zasu maye gurbin su ,

Motocin da suka kawo sabbin sojin suka fara juyawa da tawagar masu komawa inda zasu ajiye su a babban barikin garin maiduguri zuwa gobe da zasu wuce ƙasar su ta jirgi da zai tashi ta abuja !

Biyamuradi Youssouf bai jira rana tayi sanyi ba , da isar su barikin maiduguri , wanka kawai yayi ya sauya kayan sa daga uniform ɗin soji ,

Ɗaya daga cikin direbobin su ya ja sa zuwa unguwar da ƴar sa take ,

Ƙarfe ɗaya na rana ta gota suka isa gidan nan ya tadda prof tare da wasu baƙin sa ,dan haka ya jira su har suka gama ganawa sannan ya shiga falon ,

Bayan gaisuwa da suka yi prof bai bari ya ɗora kome ba yace bari suyi sallah su ci abinci ,

Bayan sun ɗan taɓa abincin da ba sosai Biyamuradi Youssouf ya ci ba ,

STORY CONTINUES BELOW

Prof ya tattara hankalin sa ga Youssouf yana saurarar sa inda yake sanar da shi ,

Yana so gobe ya zo ya ɗauki ɗiyar sa saboda a goben yake son komawa ƙasar su domin aikin sa ya kammala ,’

Shiru prof yayi yana ɗan nazari

yayin da zuciyar yarima ta cika taf da taraddadi tare da fatan kar wata matsala ta taso domin zuwa yanzu ya gama tsara kome game da makomar rikon ƴar sa a tare da shi , ya gama tsara inda zai kai ta tayi rayuwa irin wacce yake so ƙarƙashin inuwar kulawar sa da kuma kariyar sa ,

dan haka baya jin akwai wani abunda ya isa ya hana shi ɗauke ɗiyar sa daga hannun waɗannan mutanen da bai kai ga sanin su ba basu kuma da kowacce irin alaƙa da shi da har zai iya barin jinin sa tare da su , ya shirya tsaf ko ta tsiya ko ta arziki zai tafi da ƴar sa !1

Gyaran murya prof yayi kafin ya ɗora da cewa ,

Ɗa na mai zai hana idan har ka amince ka bar jaririyar nan a hannun ƴar uwar mahaifiyar ta har zuwa lokacin da ta ɗan tasa tayi wayo shekaru biyu zuwa uku sai ka dawo ka ɗau ƴar ka , baka ganin yanzu idan aka raba yarinyar nan ƙanwa ga mahaifiyar ƴar , zata shiga damuwa me tarin yawa ganin cewa har zuwa yanzu ba ta kai ga gyagijewa daga ruɗanin da mutuwar yayar ta ya jaza mata ba ,bugu da ƙari bata da kowa nata a halin yanzu sai ita wannan ƴar ta ka , ka duba magana ta da kyau ,

Ya ƙarasa zancen da bada zaɓi ga Biyamuradi ,

Ba domin tun ganin farko da Youssouf ɗin ya yiwa prof ɗin ya riga ya cika masa ido da ƙwarjinin sa tare da cikar kamalar sa ba , sannan halin dattaku da mutuntaka da ya dunga nuna masa a kowacce haɗuwar su , mafi muhimmanci kula da rayuwar ƴar sa da yayi na wani lokaci ,

bayan haka da babu abunda zai hana ya kartawa prof rashin mutunci , ya kuma gwada ƙarfin ikon sa na soja , sannan da ƙafafar su ta sarakai da koyaushe abunda suka so shi ake mu su ba’a musa mu su , ya ɗauke ƴar sa yayi tafiyar sa , to amma girma prof nada yawa a idanun sa dan haka ya sassauta murya tare da saita nutsuwar sa yace

Baba nan ba kassa ta ba , sannan ni kuma ai ma’aikaci ne , idan na tafi na bar ɗiya ta nan hankali na basshi kwanciya , chan inda zan tahi da ita nan ai shi tushe da assalin ta , kayi haƙuri baba zan tahi da ɗiya ta na ɗau Alƙawarin zan wanzu ina kawo ta lokaci zuwou lokkaci ta ga innon ta da yardar Allah ,

Shiru prof yayi yana jin tausayin falmata na kawo masa , bashi da wani ƙarfin iko akan yaran , bai haɗa kome da su ba idan banda taimakon su da ya biyo ta hannun sa dan haka shi baya da ƙarfin hanawa Biyamuradi ɗiyar sa ,

Toh bari a ƙira ita uwar riƙon ƴar ta ji daga bakin ka , kafin gobe da zaka dawo ɗaukar ƴar ,

Rahima ce ta rako falmata a yau da kallo ɗaya za’a mata a gane gaf take da ɓarkewa da kuka saboda ƙiran da aka mata ta kawo baby mama

Daga gefe ta gurfana bayan ta gaishe da prof , tayi shiru ,

Fatima ga baban jaririya nan ya sake dawowa yau , miƙa masa ƴar sa ya gan ta ,

shiru tayi bata ce ƙala ba

A hankali Rahima ta zare baby mama daga hannun ta wacce take ta wasa da hannuwan ta idanun ta tar a buɗe , shirye take tsaf cikin jar riga ta jarirai mai haɗe da wondo da safa , kan ta lulluɓe da farar hular sanyi mai ratsin ado da fulawoyi jajaye ,

Hannun Youssouf har rawa yake lokacin da yake ƙarbar yar jaririyar , yana ƙarbar ta ya zarce da ita zuwa fuskar sa inda ya sumbanci kumatun ta zuwa goshin ta , bakin sa ɗauke da addu’o’i ya kama wannan ya Sake waccen ,

STORY CONTINUES BELOW

Farin cikin sa ya yawaita da har ya gaza boyuwa ya bayyana akan fuskar sa dake ɗauke da murmushi mai bayyana haƙora ,

maida ita ƙirjin sa yayi ya rungume ta rungumar da ke bayyana tsantsar so da ƙaunar da yake mata , ji yake kamar ya buɗe cikin ƙirjin sa ya ɓoye ta ,

Da dariya akan fuskar sa ya ɗago cikin cewa

Ɗiya ta girma sossai , hala wanni sinadarin ƙara wa jarirai girma da lafiya kuke bata ? Madallah Madallah da ku , “

Ɗan murmushi prof yayi , kafin ya maida ganin sa kan falmata wacce ta ƙagu a miƙo mata baby mama suyi tafiyar su ,1

Fatima kina ji na ko ?

Ina ji Baba

Ta amsa da ladabi cikin muryar ta ,

Baban jaririyar nan ne ya zo yau yake shaida mana ya gama aikin sa da ya kawo shi nigeria nan ƙasar mu , dan haka gobe yake son komawa tare da ƴar sa , a shiryawa jaririya kayan ta kafin gobe ,

Tamkar kunnen ta ya toshe haka ta ji dumm , cikin kan ta , tana jin yadda kalmar a haɗa kayan baby mama za’a tafi da ita gobe yana bin duk wata gaɓɓa mai kuzari a jikin ta yana kassarawa ,

wanne azzalumi ne yake neman ta ƙarfi da yaji sai ya raba ta da jinin ta ɗaya tal da ta rage mata a duniya , ?

Da wani nisasshen yanayi cikin muryar ta ta ɗago kan ta tana saita idanun ta inda ta ji tashin muryar youssouf ɗin a ɗazu tace

Wanene kai ? Me muka maka kake son raba mu ? Aina kasan yakaka na ?meyasa kake ƙarya ?

Shiru tayi tana jin yadda fitar numfashin ta ke sauyawa kafin ta ce cikin ƙarajin kukan da ya taho mata ,

ƙarya kake baby mama bata da BABA kai ba baban ta bane , yakaka ita kaɗai ta haifi baby mama , ina kake lokacin da yakaka take rashin lafiya akan cikin baby mama ? Ina kake lokacin da yakaka take shan wahala alhali baby mama tana cikin ta ? Aina kake lokacin da Yakaka na ta mutu sanadin haihuwar baby mama ?? Ƙarya kake kai mugu ne , ba kai bane baban baby kana so ne ka gudu da ita ,

rarrafawa tayi inda ta ji sautin baba prof yana ƙoƙarin son katse mata maganganun ta ,

Illahirin jikin ta rawa yake lokacin da ta dangana da jikin kujerar da yake zaune ,

ba-ba-Baba bani da kowa sai baby yakaka dan Allah kar ku bari ya raba ni da ita wallahi ƙarya yake yi maka , Baba ni miskiniya ce dan Allah kar ka bari ya zalunce mu ni da baby yakaka dan Allah Baba ,!

Wani irin yanayi me wuyar fassara prof ya tsinci kan sa a ciki ƙwarai da yana da iko da yau ya hana youssouf ɗaukar jaririyar nan ya bar ta a hannun yarinyar nan , “

Idon sa ya sauke akan Youssouf ɗin wanda kan sa yake sunkuye yana kallon fuskar ƴar sa ,tamkar bai san da bulayin da Falmata ke yi ba, sam baya so tausayin falmata da ya fara tsirga masa ya sanya shi barin ƴar da Allah ya jarabbe shi akan ta hannun mutanen da ba shi da tabbacin zasu iya riƙon ta har tsawon rayuwar ta ba , kar watarana ta walakanta ko ta sha wuyar rayuwa , ƴar sa mace ce ƙwarai tana buƙatar uba a halin tafiyar rayuwar ta nan duniya ,1

shi ya barranta daga samari irin sa waɗanda zasu samu haihuwa ta haramtatciyar hanya su ƙarawa kan su zunubi ta hanyar yin watsi da abunda suka haifa ko ma su kashe baki ɗaya , yana so ya ubangiji ya yafe masa akan zunubin da yayi ma ta hanyar samar da ita baya fatan shaiɗan ya sake jaan sa ya aikata wani zunubin da yafi wanda ya aikata a baya muni ,

Mayar da ganin sa prof yayi ga Falmata cikin sigar rarrashi yace fatima ki daina cewa jaririyar nan bata da Baba , alhalin ga baban ta nan a zaune yana jin ki babu kyau haka , kiyi haƙuri ki bari ya tafi da ƴar sa yayi alƙawarin zai dunga kawo ta nan gidan gurin ki kin ji ko ?

STORY CONTINUES BELOW

sai lokacin Youssouf ya ɗago kan sa ya dube ta ,

Ƙwarai nayi alƙawari ƙanwa ta, zan dunga kawo ta zouwa gare ki har girman ta , ke ai har abada uwa kike a gare ta ,

Zumbur ta miƙe tsaye , cikin takun da kafafun ta ke harɗewa ta nufi inda take jin tashin muryar sa ,

Hannun ta duka biyu ta miƙa da zummar riƙe sa yayi saurin kaucewa yana sake boye baby mama cikin ƙirjin sa ,

Gefen rigar sa tayi wa wani ƙaƙƙarfan riƙo ba da wasa ba , Cewa take

Dan Allah ! Dan Allah ka ji tausayi na ka bar min baby , Dan Allah kar ka raba ni da ita , zan mutu idan ka ɗauke ta , dan Allah …..

Numfashin ta ne ya fara tsarƙewa dai-dai da ƙarasowar Rahima wacce prof ya yiwa umarni da ta janye Falmata , hawayen tausayin Falmatan suna zarya a kumatun ta ,

Luuuu ta tafi baya ta faɗi bisa jikin rahima suka ƙarasa bajewa a ƙasa tare babu alamun numfashi ga Falmata ,

subahannalahi innalillahi wa inna ilaihi raji’oon sune kalmomin da prof ke jerowa

Rahima ƙira direba maza a kai ta asibiti ,

Da sauri Youssouf ya waigo tare da sunkuyowa kan falmata ya tabbatar dai bata numfashi nan take ya sanya hannu a aljihun sa yana ƙiran direban sa , lokaci guda fuskar sa na bayyana ruɗanin da yake ciki yake cewa

Daman bata da lafiya ne Baba ??

Prof bai amsa masa ba ,

Direban youssouf shi ya fara shigowa dan haka rahima ta fara ƙoƙarin ɗaga falmata sai dai ta kasa , saboda tayi mata nawi ,

Baby mama Youssouf ya miƙawa Rahima ,

Lokaci guda ya sanya hannunwan sa biyu ya ɗaga falmata wacce take sume ya fice da ita wajen motar su , direban sa ya buɗe gidan baya ya shimfiɗe ta ,

Ya karɓi baby mama daga hannun rahima tare da yi mata umarnin ta shiga su tafi ta gwada musu asibiti mafi kusa da zasu kai falmata ,

tafiyar mintoci biyar suka isa wani asibiti mai zaman kan sa , inda nan take likitoci suka rufu akan falmata suna ƙoƙarin dawo da numfashin ta dai-dai ,

Hankalin Youssouf baki ɗaya a tashe yake ya kasa zaune ya kasa tsaye , sai zirga zirga yake tsakanin kofar ɗakin da Falmata take yana rungume da baby mama , tsoron sa ɗaya kar yarinyar nan ta mutu a sanadin raba ta da yace zai yi da ƴar sa , idan haka ta faru bai san inda damuwar sa zata kai ba , ” ko kusa bai san haka take ƙaunar ƴar sa ba ,

ya kasa kintata yawan ƙaunar da ke tsakanin ta da yayar ta wanda yake da tabbacin son da take mata ne ya shafi ƴar ta , idan kuwa haka ne lalle falmata abar a tausayawa ce , ƙwarai ya kamata yayi adalci ya kuma duba anya idan ya raba ƴar sa da ita ya kyauta kuwa ?? Anya bai so kan sa dayawa ba kuwa ?1

mintoci arba’in da shigar da ita ɗakin suka fara jiyo gunjin kukan ta , tana surutai ,

Da sauri Biyamuradi youssouf ya ƙarasa gaban ɗakin dai-dai da fitowar babban likitan ,

Mun samu numfashin ta ya dai-daita kamar yadda muke zaton kun sani tana da asthma , toh ta samu attack ne , yakamata a dunga kiyayewa da duk wani abu da zai iya kawo mata wahalar numfashi , yanzu ku shiga akwai wanda take son gani a tsakanin ku , nan da ɗan wani lokaci kaɗan ma zaku iya tafiya gida ko awa ɗaya haka nan gaba !

Biyamuradi youssouf ne a gaba sai Rahima biye da shi , suna shiga rahima ta ƙarasa ta rike hannun ta , tace ga ita

Ki daina kuka haka fatima , ai ga baby nan ba’a tafi da ita ko ina ba ,

STORY CONTINUES BELOW

Tana ina ??

Tace tana lalube da hannuwan ta biyu idanun ta har sun rine tsabar kuka ,

A hankali biyamuradi youssouf ya tako zuwa gaban gadon ya ɗora mata baby mama a cinyar ta tare da cewa

Ungo ta ! karɓe ta fatima daina kuka , ke ai uwa ce a gare ta ,

Chak ta ɗauke ta ta rungume ta tana ajiyar zuci tare da shafa bayan baby mama tana ɗan bubbugawa ,

Juyawa yayi ya fita yana jin yadda tsananin tausayin ta yake ratsa kowanne saƙo da lungu na zuciyar sa yana samun mazauni , ji yake kome yana neman kunce masa , tausayin ta kuma yana neman yin tasiri akan sa , mafita yake nema ,

Zuwa yayi ya biya kuɗin magungunan da aka mata ,

Daga nan ya sake ganin likitan da ya bata taimako , ya sake yi masa bayani tare da sake jaddada masa a kula da lafiyar ta, nan ya rubuta musu sallama zasu iya tafiya daga zarar an sake duba yanayin numfashin ta ,

A bakin ƙofa ɗakin ya tarar da rahima tana zaune ,

Da sauri ya tura ƙofar ya shiga idanun sa suka sauƙa akan ta , har yanzu tana zaune rungume da jaririyar da take ta bacci abin ta ,

waye anan ? Tace tana sake rungume ƴar ,

Fatima ,

ya ƙira sunan ta muryar sa babu amo ,

Ƙwalla ce ta sake kawo mata a ido , ita dai wannan mutumin ya fi ƙarfin ta ,1

Dan Allah , Dan Allah ka bar min ita , kar ka raba ni da ita ,

Shiru yayi yana kallon ta , idan har yace zuciyar sa bata yi laushi ba akan tausayin yarinyar ya faɗi ƙarya ,

Fatima za ki bi ni mu tafi ?? Za ki bi ni na tafi tare da ku ke da ɗiyar ki ?? ?

Inda take jin sautin muryar sa ta saita idanun ta tamkar tana ganin sa ,

Muryar ta ƙasa-ƙasa , ta juya tambayar kan sa ,

Za ka yadda na bi ka , ? Idan na bi ka za ka bar min baby a tare da ni ??

Idan za ki bi ni zan bar ki miki ita har abada a hannoun ki , babu mai raba ku ,!

NA YARDA ZAN BI KA ,!3

****

ƙarfe huɗu suka dawo gida , numfashin falmata ya samu daidaito , tana maƙale da ƴar ta tsam , lokaci zuwa lokaci tana ɗan jijjiga ta saboda kukan yunwa da ta fara ,

Suna shigowa prof wanda tunda suka tafi yake ƙiran rahima ya ji halin da suke ciki , ya ji hankalin sa ya kwanta da ya ga falmata ta warware ,

kai tsaye falmata da rahima suka wuce cikin gida domin su haɗawa baby madarar ta ,

Shi kuma Biyamuradi ya shiga wajen prof ,

Cikin nutsuwa youssouf ya yiwa prof bayanin yadda suka yi da falmata akan amincewa da tayi zata bi shi , ya ɗora da cewa

Na ɗauki Alƙawarin zan kula da ita tamkar yadda zan kula da ɗiya ta , da yardar Allah ,

Gyaran murya prof yayi bayan ya gama jin sa ,

Ɗana ka so kan ka dayawa , kuma a wannan gaɓar inada ikon yin hani , saboda yarinya amanar Allah ce a hannu na , shi ɗa na kowa ne , abunda baza ka so ya samu ɗan ka ba idan kana da ikon hanawa kar ka bari ya samu ɗan wani ,

ni a matsayina na wanda wannan yarinya take a ƙarƙashin iko na a yanzu , bazan amince maka ka ɗauke ta ka tafi da ita ko ina ba , tana matsayin ƴa mace , kai ko namiji ce bazan yadda ba bare ƴa mace , to a wanne dalili ? Ka tafi da ƴar ka wannan ƴar ka ce ,kana da iko da ita amma fatima kam baza ta bi ka ko’ina ba !

Shiru youssouf yayi kan sa a ƙasa , shi tausayin falmata yake ji matuƙa , sannan yana da kyakkyawar niyyar sauke ƙudirin sa na tun farko da ya so cikawa akan yakaka , a yanzu da bata nan zai so ya tallafi falmata , ko da babu baby mama zata samu taimakon sa sanadin yakaka ,!

Baba ayi haƙuri a duba da kyau dai ita ɗiyar nan idan an raba su da jaririyar nan matsala ce babba zata auku , lafiyar ta abun dubawa ce ,

Babu alamun sassauci a muryar prof ya ce idan ka ga na bar ka , ka tafi da fatima , to ka ɗauke ta ne ƙarƙashin amincewar shara’a

amincewar shara’a ?

Youssouf ya maimaita

Ƙwarai ina nufin igiyar AURE ta ƙullu a tsakanim ƙu , ta zama halalin ka , ta maye gurbin ƴar uwar ta a gurin ka , to a lokacin kana da ikon da zaka tafi da ita tare da ƴar ka duk inda kake so cikin duniya ,bazan hana ba, idan kuwa ba haka ba ka janye batun zuwa da ita ko’ina idan Allah ya kai mu gobe ka zo ka ɗau ƴar ka kamar yadda ka ce , na gama magana !6

Ɗago kan sa yayi yana kallon prof tamkar sassaƙen mutum mutumi ,

AURE ?

AURE TSAKANIN sa da wa ? Wannan ƴar ficiciyar yarinyar ? Ƙanwar yarinyar da yayiwa ciki ? Makauniya ƴar gudun hijira ? Marar gata marar galihu marar dangi ??

Wani irin yanayi yake ciki akan tunowa da yayi da wacece ita , ?

Bugu ƙirjin sa ya shiga yi gumi yana tsattsafo masa har yana ɗiga daga goshin sa duk kuwa da sanyin ac da ya wadaci falon , “

Youssouf mutum ne da yake jajirtatce mai kafiya akan cikar burin sa bai cika duban yadda gaba zata kasance ba idan yaso aiwatar da wani ƙudiri nasa , a yanzu tafiya da ƴar sa shine a gaban sa , so yake ya tsira da ƴar sa ba tare da ya bar baya da ƙura ba , ba tare da ya ci karo da wani abu da zai iya yi masa shamaƙi ba ,

raba fatima da baby mama wani abu ne da idan yayi , har abada baya jin zai iya mantawa kamar yadda ya riga ya san cewa tabbas idan ya tafi ƙasar su dawowar sa nigeria wani abu ne da yake gani da wuya ya kasance to ya dawo yayi me ?? Waye nasa a nigeria ? Ba shi da kome a nan , bai taɓa zuwa ba sai ta dalilin aikin sa ,

Kalmomin da zuciyar sa ta riga ta amince masa da hukuncin da ya yanke sune suka jero kan su suka fito ta tsakanin laɓɓan sa ,

NA AMINCE DA AUREN TA !2

a take fuskar prof ta yalwatu da haske da fara’a

Masha Allah Masha Allah haƙar sa ta cimma ruwa ,

Ka amince zaka auri fatima ƙanwar matar ka ??

NA AMINCE ZAN AURE TA !Babu kowa a harabar barikin sai masu gadi da suke daga kowacce kusurwa , sakamakon dare da ya raba tsaka 2am , sai Biyamuradi youssouf da ke kai kawo a cikin hunturun sanyin da yake ratsa har ɓargon mutum gami da iska mai ƙura da take toshe ƙofofin hancin ɗan adam , a tsaye yake tsakiyar filin ya sunkui da kan sa jikin sa sanye da ƴar baƙar riga mai gajeren hannu da dogon wondon uniform ɗin su na soji ,2

Ya zurfafa a tunanin makomar Auren da yake shirin karɓarwa kan sa nan da wasu ƴan awanni zuwa wayewar gari ,

Ina zai dosa da auren yarinyar ?? Yarinya ce ƙanƙanuwa , sannan kuma miskiniya , ta wacce hanya zai fara tallafar ta , domin ƙwarai take buƙatar matallafi cikin rayuwar ta da bata da kowa sai ƴar jaririyar sa ,

Me zai cewa iyayen sa su fahimce sa da dalilin sa na auren ta? Wanne irin hukunci maimartaba da hajiya umma zasu yanke masa idan suka ji ainahin abunda ya aikata da har ya kai shi ga auren yarinyar ?? Zasu su yi fushi mai tsanani da shi irin fushin da baya fatan ya gitta tsakanin sa da iyayen sa duk tsawon rayuwar sa ,

Me zai wakana tsakanin sa da gimbiya maimunatu lokacin da ta san ya auri wata mace kafin ita , Yana riƙe da auren wata bayan ita ? Zata iya yi masa kallon mayaudari kuma munafuki , a ƙarshe soyayyar su zata gurgunce da zai iya datse alaƙar su shi da ita , bai fatan haka saboda ya shaida irin tarin ƙaunar da zuciyar sa ke yiwa gimbiya maimounatu,

Kalaman prof ya tuno inda yake ce da shi ,

Madallah tunda ka amince da auren Fatima , ka zo da wakilan/waliyan ka, a gobe zan baka auren ta , daga nan idan kana buƙata a goben zaka iya tafiya da ita tare da ƴar ka ,

A lokacin ya amsa masa da

Toh na Amince

Har ya tashi zai tafi prof ya tsaida shi ,

To amma akwai wani lamari guda ɗaya , lamarin kuwa shine bazan iya ɗaukar yarinyar nan na baka ita , ka tafi da ita, ita kaɗai ba dole zan haɗa ka da mutum ɗaya wanda za ku tafi tare chan ƙasar ta ku domin a gano inda zaku zauna saboda sha’anin duniya , ta ka zo ta kan zo ko watarana wasu daga cikin dangin su zasu ɓullo su zo neman sanin inda ƴar su take , da fatan ka fahimceni da kyau kuma ka amince ?2

Jim yayi a ƙarshe ya sake amsawa da

NA AMINCE

Waje ya samu ya zauna akan ɗaya daga cikin dakalin da aka yi su domin zama dake a watse cikin barikin ,

Da farko yayi niyyar idan ya ɗauke ta ya kai su Niamey gidan ubbo a matsayin ƴar gudun hijirar da ya taimaka ita da baby mama idan ya so su kasance ƙarƙashin kulawar ubbo tare da shi har zuwa lokacin da zai samawa kan sa hanyar da zai bi ya bayyana su ga dangin sa ba tare da abubuwa sun rinchaɓe masa ba ,1

Sai dai batun haɗa su tafiya da wani ya rusa wannan nufin nasa domin ko kusa ba zai so a san wasu dangi nasa ba , ba zai so asan ko shi wanene ba saboda kar watarana kome ya bayyana , a biyo sawu ba tare da sanin sa ba , kome ya lalace masa a lokacin ,

Idan kuwa har ya nuna ƙin amincewar sa , hakan zai sa a dasa ayar tambaya akan sa , ayi masa zaton marar gaskiya , wanda zai iya sa pro ya tsananta bincike akan sa wataƙila a ƙarshe kome ya isa ga masarautar su , bai fatan haka ,

Idan kuwa haka ne dolen sa ya yarda ya tafi da su da me rakiyar su ,

Ƙaunar ƴar sa da Allah ya jarrabe shi da shi ya sa duk yana ƙoƙarin fuskantar duk wani ƙalubale , burin sa ya tsira da ita , dan haka a ƙarshen tunanin sa ya ture duk wani ƙalubale gefe ya amince da mallakar baby mama tare da uwar goyon ta a lokaci guda da me rakiyar su ,

Yana tsaye a wajen aka yi ƙiran sallan farƙo na karfe 3:30am , kai tsaye ya nufi babban masallacin cikin barikin ya ɗaura alwala da sassanyan ruwan da iskar hunturu ta gama hura sa ya shiga masallaci ya fara jero nafilfili , yana roƙon Allah ya bashi nasara akan manufar sa ya kuma rufa masa asiri ya kawo masa warwaruwar al’amuran sa a sauƙaƙe , “toh ameen,”3

STORY CONTINUES BELOW

ALƘAWARIN UBANGIJI ( MATAR MUTUM DAGA GARE SHI TAKE )

Da misalin ƙarfe goma na safiyar ranar Alhamis ɗin karshen sati , ƴan tsirarun mutanen da prof ya ƙira na cikin unguwa da basu wuce goma ba tare da wasu ƙarin mutane biyar da youssouf ya kawo a matsayin wakilan sa wanɗanda a zahiri abokan aikin sa ne daga ƙasar su , suka haɗu suka shaida ɗaurin auren FATIMA DILMARI , tare da YOUSSOUF ABDUL-AZIZOU BASKORE , wanda ya sauya suna zuwa youssouf Garba Malbaza Uzine,

Bayan ɗaurin auren babu ɓata lokaci su abokan aikin youssouf suka yi komawar su domin ɗaura shirin tashin su zuwa Abuja inda zasu wuce ƙasar su ta jirgin sama a yau ɗin ,,

da shi kuma youssouf ya shigar da neman iznin a bada mota guda cikin motocin su na soji tare da direba da zai tuƙa su zuwa Niamey ta hanya , ba’a tsananta bincike ba aka bashi izni tare da shaida masa ya tabbatar ya samu isa niamey kafin ranar litinin inda za’a yi bikin dawowar su tare da yi musu ƙarin girma ,

Hajja me wurya,” ita ce dattijuwar da prof ya zaɓa a matsayin wacce zata raka fatima ɗakin mijin ta daganan ta gano garin da zasu zauna a niger , kasancewar ita hajja mai wurya dattijuwa ce da a ƙalla ta tasamma shekaru hamsin , sannan kuma a halin yanzu bata da wani jigo cikin rayuwar ta iyaye duk sun mutu dangin kuwa kowa ta kai ta kai yake sannan tun asali bata da haula ɗan ta ɗaya ne tal da ta haife shi a shekarun girma bayan aure auren da tayi ta yi domin neman haihuwa ,

tana tsakiyar fara cin moriyar ɗan nata da ya ɗan fara tasawa shekarun sa ishirin da huɗu , ƴan tawayen boko haram suka shigo har gida suka yanka mata shi , a cewar su yana zagin su tare da sukar akidar su , dan haka suka kawar da shi,2

Tun daga nan rayuwa ta fara yi mata wahala , ƙunci da talauci suka dirar mata , zamani ne da kowa yake gudun wahala ba’a duban zuminci , tunda ta fahimci haka ta daina yin raragefe gidan ƴan uwa ta bazama neman na kan ta sanin da tayi da ɗan sauran karfin ta bata zama ƙarƙashin dangina ana zuba mata sharar walakancin ,

aikatau ta fara a gidajen saida abincin ,kasancewar ta gwanar girki iri iri ,musamman ma na ƙasar camaru da tayi farkon zaman auren ta a chan , amma sakamakon tsaurin ta da kuma tsayuwar ta kan gaskiya ya sa ba ta cika daɗewa a wajen aikin ake sallamar ta , saboda bata zuru duk ta ga zalau sai ta tsinka ,”

daga baya ta koma aiki a gidajen masu hali nan ma gida biyu tana barin aiki saboda yadda take gwadawa uwargida iyakar ta a cikin gidan ta idan har ta ga abunda bai dace ba, sai fa wannan karon da tayi dace ta samu aiki gidan Professor Mustspha dilmari

Allah ya tsawaita zaman ta a gidan da taimakon tarbiyyar yaran gidan da basu cika raini da walakanci irin na sauran ƴaƴan masu hali takwarorin su ba , babu kuma matar gidan shekaru biyu take nema da fara aiki a gidan a matsayin mai yin girki , musamman ma na shi prof .

A jiya da prof ya ƙira su ita da falmata ya faɗa musu hukuncin da yake ƙoƙarin yankewa har ma ya tuntunɓi ita falmata akan jin ra’ayin ta , ta amince zata auri baban ƴar da take riƙo su tafi ita da shi da ƴar chan ƙasar sa ko kuwa ??

Ga mamakin sa ba tare da shayin kome ba

Falmata ta amsa da ta amince zata auri baban baby ya tafi da ita tare da baby ,

Ƙwarai prof ya ji daɗin amsar Falmata domin da farko har yana fargabar ko yarinyar zata ƙi gatan da yake son yi mata na aurar da ita tunda ƙuruciyar ta , ga mutumin da yake iya hango nagartar sa a cikin yanayin sa da mu’amalar sa , yana hasashen mutum ne na ƙwarai !

STORY CONTINUES BELOW

A sarari ya nuna jin daɗin sa tare da yi mata addu’o’in samun nasara a rayuwa , sannan ya juya ga hajja mai wurya wacce ita ma take durƙushe daga gefen falmata ,

Hajja Alfarma zan nema a gurin ki akan ki raka fatima ɗakin mijin ta ki gano min wajen da zasu zauna ita da mijin ta a chan niger ɗin daga baya sai ki dawo. Da fatan zaki min alfarma ?

Dariya hajja me wurya ta sa !

Babu kome Alhaji zamu tafi tare , me zaman aure ma ta amince bare ni ƴar rakiya ?? Ai ko gaba da binnin sin ne Alhaji ba na ƙi raka ƴar marainiyar Allahn nan ba , kai shima dai wannan dogon balaraben nijar ɗin Allah yayi masa Albarka da duk da kyan nan nasa da cikar zati irin ta ɗa namiji amma haka ya runtse ido ya ce ya amince zai auri wannan murɗaɗɗiyar bahaguwar yarinyar , ai dole ayi masa godiya bawan Allah .7

Nan dai Alhaji ya sallame su yana sake musu godiya akan biyayyar da suka ma sa ,

Kan hanyar su ta komawa hajja mai wurya tana riƙe da hannun falmata tace

Ke ƴar nan Allah ya dube ki ya tarfawa garin ki nono , irin wannan zankaɗeɗen miji da Allah ya wanke ya ba ki ?? Ai ko ɗiyar masu mulki ba ta ƙi shi ba , to zan fara faɗa miki tun wuri tun yanzu , ki zubar da waɗannan hargitsatsun halayen naki tun a nan nigeria kar ki ce zaki tafi gidan auren ki da su , saboda wannan dai miji naki wallahi kin yi sa’a wanke hannun ka taɓa Allah dai shi sa yadda surar nan tasa take halin sa yafi haka kyau ,

Ai bazan bar gidan nan naki ba sai na ga kamun ludayin zaman naki da shi , ato sai ki shirya ni ɗin dai da kika tsana kike ƙin bani riƙon jaririya , nice dai me miki zaman ɗaki sai dai muyi wacce za mu yi mahaukaci ya ɗau rigar kurma …3

Zame hannun ta tayi daga cikin na hajja tayi gaba ta miƙa hanya , ƙalau tamkar me gani saboda yau da gobe ta fara haddace hanyar a ƙwaƙwalwar ta,

Sasakai hajja me wurya tayi

Au aikin banza kenan hanci ba ƙafa , to ki fi ruwa tafiya , nace ki fi ruwa tafiya , wannan yarinyar sai na dage kafin ta shiga hanya ta ɗau haske ta san me duniya take ciki kan ta hayaƙi yake ,!

Falmata ko sauraron ta bata yi ba hasalima ji tayi hayaniyar hajja me wurya ta hana kwakwalwar ta sakewa tayi tunanin da ya kamata shi yasa ta zame hannun ta ta rabu da ita ,

Aure da ita da shi ?? Wanene shi da yace baban baby ne ? Da gaske shine baban baby ? Wanne irin aure zasu yi ? Ina ne ƙasar ta su ? Idan suka tafi zasu dawo ? Bata son barin nan inda take , burin ta watarana dr hamza ya nemo mata maman su , to amma yanzu kuma ga shi zata tafi ta bar nan ɗin ,

Abun da ta sani zata yi kome , zata tafi ko ina zata kuma ta shiga kowannen wahala domin ta tsira da baby mama , domin ta tsaya tare da baby mama , domin baby mama kar ta sha wuya , naƙasun ta miskinancin ta , rashin idanu ,

da ace ita lafiyar ta ƙalau , bata buƙatar abokin tayi wajen gina rayuwar ƴar ta , da zata gudu da baby mama ta ɓuya wani waje tana kula da ita , to amma ita ɗin ma miskiniya ce dole ne ta bi baban baby da yace zai kula da mama ƴar sa ce !

Ƙarfe biyu cif aka fara fito da jakar bocco ɗin falmata wacce ta haɗe kayan ta da na yakaka kakaf a cikin babbar baccon yakakar , sai kuma kayan baby mama shima a cikin babbar jaka , duk aka zuba su a bayan dunƙulalliyar motar soji me ƙirar golf kofa biyu ,

Biyamuradi youssouf ya taka zuwa cikin gidan falon prof , suka yi sallama inda prof ɗin ya bi shi da kalaman godiya ya kuma ɗora da damƙa masa amanar fatima tare da roƙon sa akan ya kula da ita , ita ɗin abar a tausayawa ce ,

STORY CONTINUES BELOW

Nan youssouf ɗin ya amsa tare da ɗaukar Alƙawarin zai kula da ita ,

Yana zaune hajja me wurya da falmata rike da mama haɗi da rahima suka shigo , falmata tana shirye tsaf cikin sabuwar atamfar ta ruwan ganye da adon furanni farare, ta saka farin hijabi har guiwar ta ,

Daga gefe suka tsugunna , nan prof yayi musu addu’o’i tare da ƴan nasihu ya sake ɗanƙa amanar falmata a hannun hajja me wurya har lau ,

Daga ƙarshe ya zaro kuɗin sadakin falmata naira dubu ishirin sabbin bandir ɗin ƴan ɗari biyu ,

Ungo Rahima ,

miƙawa fatima kuɗin sadakin ta hakkin ta , fatima ina me baki haƙuri akan yadda auren ya zo a ƙurarren lokaci ban miki kome ba da iyaye ke yiwa ƴaƴan su idan zasu kai su gidan miji , amma na miki alƙawari na kuma yi magana da shi mijin naki akan idan kun isa ya tura min account number zan tura da kuɗin da za’a saya miki kayan ɗaki da na amfanin gida a chan kin ji ko ? Ki riƙe wannan sadakin auren ki ne ,

Da sauri falmata wacce idanun ta suka kawo ruwan hawaye akan irin ƙaunar da prof ke musu tare da sanin cewa yau zata bar gidan shi zuwa wani waje da bata da sani akan me zata je ta tarar , tace

Baba na bar maka kuɗin ni babu abunda zan yi da su ,

A ah fatima ki karɓa nace hakkin ki ne , watarana zaki samu abun saya da su ,

Muryar ta na karkarwar kukan da ta soma tace

Baba to ka riƙe min idan na dawo zan karɓa ,

Ba shiri hajja me wurya ta zungure ta , tana satar kallon youssouf da yayi shiru yana sauraran ta ,

Ƙasa-ƙasa tace

Ka ji min sakarya auren da tun baki kai gidan ba kike fatan ki dawo , ??

Kawo ƙuɗin na riƙe mata Rahima, irin kunyar nan ce ta amare take gwada mana ,

Rahima da take murmushi a hankali ta miƙawa hajja me wurya kuɗin ,

Madallah Allah ya sanyawa auren ku Albarka Allah ya sa abokiyar arziki ce , Allah ya kauda shaiɗanun aljanu da na mutane a tsakanin ku , Allah ya sa mutuwa ɗai ita zata raba ku, Allah kuma ya baku zuri’a masu albarka irin wacce manzo Allah zai yi alfahari da ita !2

Laɓɓan Youssouf ne suka motsa a hankali da ,”Ameen .

Rahima ita ta raka su har bakin mota tana jin yadda kewar su take taso mata , ai anyi sabo zaman watanni tare , duk da cewa ta so tafiyar su tafi haka tsawo sai dai damar bata samu ba , amma ko babu kome tayiwa fatima murnar samun ɗanɗasheshen mijin da ya ƙere sa’an auren ta ta ko’ina hakkun fatima me sa’a ce .

Da wannan tunanin ta rufe musu ƙofar motar bangaren da falmata ta shiga inda suke zaune tare ita da hajja me wurya a bayan motar , Biyamuradi da direban sa suna gaba ,” .

*****

Tafiya ce suka ɗora ta miƙaƙƙiya tun daga maiduguri zuwa sokoto , inda basu samu isa sokoto ba sai cikin dare misalin sha biyu da rabi , alamun gajiya da suka bayyana baro-baro ga falmata tare da baby mama wacce ta ke yin ƙananun rikici na gajiya da rikon hannun ya sa youssouf ya kama musu ƴan ɗakuna a wani ƙaramin guess inn da yake cikin garin na sokoto zuwa wayewar gari sun huta sun kuma sake shiri sai kuma su faɗa yankin niger ta,” ilela ,” su ɗau hanya ta birnin N’konni da zai ɗaura su kan kodoben da za su sadu da birnin Niamey ɗin niger ….!

STORY CONTINUES BELOW

Ba su suka samu isa Niamey ba sai ranar Asabat da misalin ƙarfe bakwai na dare duk kuwa da gudun da direban ya dunga shararawa tun da suka faɗa yankin niger kasancewar sun shigo ƙasar su , kowa yaga gilmawar motar su basu hanya ake ,

Kai tsaye direban ya wuce da su ( Radisson Blue hotel,) ƙarƙashin umarnin youssof , kasancewar shahararren hotel ɗin mafi yawan lokuta nan ne wajen sauƙar sa idan wani aiki ya kawo shi Niamey ɗin kasantuwar hotel ɗin kusa yake da manyan ma’aikatu masu muhimmanci na ƙasar da ke babban birnin Niamey ,

Babu ɓata lokaci ya kama musu ɗakuna inda hajja me wurya da falmata zasu zauna a ɗaki guda , (one bedroom Residence ) dake ƙasa shi kuma ya Kama nasa ɗakin a sama ( royal suite ) inda ya saba zama idan ya zo otel ɗin yayin da direba yayi tafiyar sa inda sauran abokanan aikin su suke , ya bar masa mukullin tare da motar , ‘

Bayan yayi wanka ya sallaci isha’i , misalin ƙarfe takwas da rabi ya sauko ƙasa , ɗakin da suke ya tasamma , ƙwanƙwas musu ƙofa yayi ,

Hajja me wurya tana sallar isha’i lokacin , falmata kuwa ta idar tana kwance bisa faffaɗan gadon ta sanya baby mama a gaba wacce take ta baccin gajiya bayan an cika mata ciki da madarar ta me ɗumi ,

Sake ƙwanƙwasa ƙofar yayi a karo na biyu yana sake kallon number ɗakin da take rubuce a jikin wani ɗan katako dake sakale a jikin ƙofar ,”nan ne dai ɗakin nasu ,”

Miƙewa zaune tayi

Hajja kamar ana buga ƙofa ko ?

Ƙyat ! Ƙyat

Hajja ta mata alama da hannu

Oho sallah kike ?

Sake bugun ƙofar aka yi da ɗan ƙarfi da ya sanyata miƙewa a hankali bayan ta zura hijabin ta ,

Ƙasantuwar ɗakin ba wani babba sosai bane taku kaɗan tayi ta isa jikin bango , dan haka ta fara shafawa bata sha wahala ba hannun ta ya sauka jikin ƙofar,

Waye ne ?

Ni ne buɗe min ƙofa

Ta shaida muryar sa

kama mariƙar ƙofar tayi ta murɗa sai dai bata ji alamun ƙofar ta buɗu ba ,

Ban iya ba

tace da shi cikin ƴar ƙaramar muryar ta ,

,’Bata iya buɗe ƙofa ba ? Ya tambayi kan sa ,”

Hajiya batta cikin ɗakin ??

Tana sallah ,

ta ce masa

Bai ce kome ba ya gyara tsayuwa gami da jingina da jikin bangon ɗakin ,

Cigaba tayi da tsayuwa tana ɗan laluba jikin ƙofar ko zata ji wajen buɗewa ,

Ba’a ɗauki lokaci ba hajja ta idar da sallah ,

Ke kam wannan yarinya anyi bagidajiya , yanzu ace buɗe ƙofa ma kin kasa ? Ni gusa ki ban guri ,

buɗe masa ƙofar tayi ya shigo suka gaisa ,

Hajja akwai abunda kuke buƙata ne ?

Babu abunda muke buƙata ɗan nan , mun gode ƙwarai da hidima ,

Idon sa ya ɗora kan baby mama ,

Ta daina rigimou kou ? Ba ku buƙatar kome kou ?

Shiru falmata tayi domin bata ma san da ita yake ba ,

Hajja ta ce

fatima maigidan na magana

Wanne maigida hajja ??

Wata ƙatuwar harara hajja ta wurga mata , tamkar falmatan tana ganin ta a ƙufule tace

Baban jaririyar ta ki1

A sanyaye ta ce me yace ? Wai zai tafi da baby ?

Da sauri youssouf yace

Ban faɗi hakka ba fatima cewa nayi ba ku buƙatar kome ?

Eh !

Ta bashi amsa tana zama bakin gado ta shiga laluben baby mama, hannun ta ya sauka bisa kan ta ta shiga shafawa a hankali ,

Ya juya ga hajja , ni zan shiga gari wajen aiki na , akwai yiwuwar gobe sai yammaci zan shigo , duk idan kun buƙaci wanni abu ku ƙira ma’aikatan otel ɗin ta kan wayar tarho ,

Ga ta nan ,”

ya nuna mata telphone ɗin dake ajiye daga saman ƴar durowar gefen gado “

madallah hajiya ina sake godiya

STORY CONTINUES BELOW

Mune da godiya ai ɗan nan mune da godiya , to to babu kome Allah shi taimaka muna nan muna addu’a

Ameen hajja sai gobe

Ya juya yana barin ɗakin

Da sauri hajja ta zunguri falmata ,

Ke baki san ki gaishe da miji ko kiyiwa miji addu’a bane ? yau ni hauwa’u na ga abunda ya fi ƙarfi na me zan gani haka ? Yanzu ashe haka za ki dunga gwada rashin hankali a gidan auren na ki ? Ko kuwa taƙamar yarinta kike ? To bari ki ji na faɗa miki ni lokacin da aka min auren fari ma ban kai ki cika ba , kin fini ƙugu da ƙirji da sharaɓa da kome ke har shekaru ma domin ni lokacin da aka min aure ma sha huɗu nake ko nonon arziƙi bani da su , amma billahil azeem ban yi irin wannan haukar da na hango somi-somin ta a tare da ke ba ,

Ke kenan sai ƙwalafacin ƴa , alhalin kina gwadawa uban ta halin ko in kula , idan taƙamar ki son ƴaƴa ai sai ki kwantar da kai kema ki samu ki tara naki ba ki dunga gwada naci akan ƴar wasu ba ,

Falmata wacce ta fara jin haushin hajja akan takurar da ta ke mata, muryar ta a cunkushe tace ,

To a ta ya zan tara nawa ƴaƴan ??

Sororo hajja tayi ,

Ah lalle abun naki na yi ne, ‘an biyawa bazaura hajji , to sai ki cigaba da tambaya ta , ranar bada amsa tana zuwa , aikin banza yarinya sai sokonci kika iya ,.

Washegari biyamuradi youssouf bashi zaune bashh&

har sai da ya samu wani ɗan madai-daicin gida irin wanda yake so a unguwar ,(Banifandou 2) ya kamawa su falmata hayar sa ya biya kuɗin shekara guda cif ,

Ƙarfe hudu tayi masa a shahararren company ƙera kayan katako da shirya gida ,(sunwe) inda ya faɗa musu buƙatar sa na son a kai masa kaya dai-dai da tsari da fasalin gidan sa ,

Basu yi ƙasa a guiwa ba suka tashi ma’aikatan su har su huɗu suka je ganin gidan ,

Hotunan gadaje , kujeru da sauran kayan adon gida aka dunga nuna masa tare da kuɗaɗen su ,

Bai yi zari ba ya zabi dai-dai kudin sa , tare da matsayin Falmata a wajen sa ,

Ma’aikatan da kan su suka kwashi kayan a motar su zuwa gidan inda gobe zasu je su shirya kayan da safe ,

Sai sha biyun dare Youssouf ya koma hotel ɗin saboda tun ƙarfe takwas na dare yana tare da manyan su suna wata ganawa ta musamman da lieutenant-Gènèral da Major Général , waɗanda sune ƙashin bayan samun ɗaukakar sa a fannin aiki ,

Ya so ya je ya ga ɗiyar sa da yadda suka wuni amma ganin yadda dare ya riga yayi sai ya yi wucewar ɗakin sa kai tsaye , da zummar gobe zai gana da su cikin rashin sanin sa yini baby mama tayi da matsanancin zazzabi tare da mura , banda kuka babu abunda take , tun falmata na rarrashi ita kaɗai har hajja ma ta karɓa , duk da haka ta ƙi shiru , zuwa dare har shiɗewa take gaba ɗaya hankalin su ya gama tashi banda kuka babu abunda falmata take ko abinci sun gagara ci ,

Ganin duhu ya sawo kai ga youssouf bai zo ba ya sa hajja me wurya fitowa daga ɗakin ba tare da ta san takamaimai ina zata nufa ba , Allah ya taikaita mata wahala ya gama ta da ɗaya daga cikin ma’aikatan otel ɗin da ya kawo musu abincin rana ,

Nan ta tsaida shi ta tambaye shi ina ne ɗakin wanda ya kawo su ? Suna buƙatar taimakon sa , bai gane inda ta dosa a maganar ta ba saboda haka ya yi mata jagora zuwa gun manyan su , inda cikin kwatancen hajja me wurya tare da duba sunan ainahin wanda ya kama musu ɗakin da suke suka fahimci colonel youssouf take nema ,

basu da number wayar sa dan haka suka shiga ƙiran layin telfo na ɗakin sa nan ma basu ci nasara ba domin wayar tana ta ƙara ba’a ɗauka alamun da ke bayyana babu mutum a ɗakin .

Ganin yadda hajja ta damu tare da sanin matsayin wanda ya kawo su ya sa suka tambaye ta matsalar su ?

Nan ta shaida musu ƴar shi wanda ya kawo sun ne jaririya bata da lafiya suna neman a kai ta asibiti ,

STORY CONTINUES BELOW

Nan take ma’aikatan hotel ɗin suka jagorance su zuwa wani asibiti me zaman kan sa mafi kusa duba da halin da ƴar jaririyar take ciki na wahalar numfashi,

bayan sun haɗa su da likitoci da nan take suka karɓi baby mama suka fara bata taimakon da ya dace ,

Sai suka dawo suka cigaba da ƙiran layin ɗakin youssouf lokaci-lokaci ko ya dawo ?

Dan haka da shigar sa ɗakin bai rufa mintoci goma ba fitowar sa daga wanka kenan , kan wayar ɗakin ta fara ƙara ,

Nan ya ɗauka bayan sun gaisa suka sanar da shi halin da ƴar sa ke ciki tare da asibitin da suka kai ta ,

A gigice youssouf ya sanya kayan sa gami da ɗaukar ɗan mukullin motar sa , kai tsaye ya tasamma asibitin da ba baƙon sa bane domin fitatcen asibiti ne da duk ƙasar aka san sunan sa ,!

Bai wani sha wahala ba illa tashin hankalin da yake ciki lokacin da ya samu ganin babban likitan da aka tabbatar masa shi ya kula da jaririyar a daren ,

A kiɗime youssouf ke tambayar sa ina ƴar ta sa take ? Kuma a wanne hali take ciki ? Nan likitan ya kwantar masa da hankali inda ya shiga yi masa bayanin abunda ke damun ƴar sa tana da ,( single pneumonia ) wanda kuma shi ya kawo mata wannan wahalar numfashin tare da zazzaɓi me tsanani , sanadin shaƙar ƙura me ɗauke da ƙwayoyin cuta da tayi,

Dan haka likitan yayi ƙira da a kiyaye sosai a kula da ita , a ƙarshe ya sanar da shi an shawo kan matsalar ta a halin yanzu har ma ta samu bacci zuwa gobe idan aka ga yanayin jikin ta ana iya sallamar ta ,

Tare da likitan suka nufi ɗakin da aka kwantar da baby mama ɗaki ne na musamman ( side room ) inda falmata da hajja suke tare da ita ,

Lokacin ƙarfe ɗaya saura na dare dan haka nuna masa ɗakin ya yi , ya juya ,

A hankali ya murɗa kofar ɗakin ya shiga , da haske wal a ɗakin dan haka ya hango falmata daga kan gadon tana zaune ta jingina bayan ta da jikin ƙarfen gadon tana riƙe da baby mama a hannun ta , ga alama bacci take ,

Hajja kuwa tana kwance akan ƴar shimfiɗar da ma’aikatan asibitin suka bata sai sharar bacci take saboda gajiya da tayi da kuma jikin girma !

A hankali ya tako cikin ɗakin ya ƙarasa bakin gaɗon gami da rage tsawo ya leƙa fuskar baby mama , ya yi haka ne saboda baya son tashin su a bacci,

Falmata kuwa tun taɓa ƙofar da yayi ta ji sa , hasalima ba nisa baccin na ta yayi ba saboda sam yanayin wajen da yayi shiru sosai yana bata tsoro , tun tana ƙiran sunan hajja lokaci zuwa lokaci tana amsa mata har dai ta ji hajjan tana mitar ta dame ta da ƙira cikin magagin bacci dan haka ta haƙura ta ƙyale ta , Tayi shiru tana sauraran sauƙar numfashin baby mama da take yin sa cikin nutsuwa alamun sauƙi ya samu gare ta ,

Hannun sa ya kai a hankali da nufin ƙara rufe jikin baby mama da ya ɗan buɗu kaɗan ba tare da sanin falmata ba ,

Yana ajiye hannun sa ta maida nata akan nasa ,

Ɗago kan sa yayi ya dubi fuskar ta , manyan idanun ta da suka ɗan yi jaa kaɗan sun kafe fuskar sa da kallo tamkar tana ganin sa ,

Haɗa baki suka yi wajen yin magana ƙasa-ƙasa

Ita tana tambayar wanene ?

Shi kuma yana cewa ni ne fatima !

A hankali ta ɗauke hannun ta daga kan nasa ,

Shi kuma ya gyarawa baby rufuwa tamkar yadda yayi niya cikin ran sa yana mamaki tare da girmama nisan kunnen ta tare da yadda take kaffa-kaffa da ƴar baby , da ɗai bai taɓa cin karo da uwa irin ta ba , duk da ƙarancin shekarun ta

STORY CONTINUES BELOW

Komawa yayi ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana duban fuskar ta cikin nazari , kallon ƙurr yake mata tsaf yana wasu tunaninnika masu nissa ,

A jikin ta take jin idanun sa suna yawo saboda tsikar jikin ta da ta ji tana mimmiƙewa,!

ya tsinkayi muryar ta da ɗan karfi tace .

Ka ɗaina kallo na haka bana so !

Ware idanu yayi da ɗan mamaki a fuskar sa ,”ya aka yi tasan ina kallon ta ,”? kafin yayi murmushi kaɗan ganin yadda ta turɓune fuska ,

,’Ƴar baiwa ce,” ya aiyana haka cikin ran sa , a sarari kuwa cewa yayi

Ki kwantar da itta ke ma ki kwanta dare yayi ,!

Yayi baya da kan sa tare da miƙe dogayen kafafun sa ya ɗan zame kaɗan akan kujerar yana jin yadda tunanin lamura suke yi masa rubdugu tamkar yadda ya saba duk dare tunda abubuwa suka fara haɗe masa !

*****

Stade Général Seyni kountchê ( SGSK ) nan ne babban filin da gwamnati ta shirya gudanar da bikin karamma sojojin ta waɗanda ta tura nigeria tare da yi musu ƙarin girma , har ma da kyautuka ga waɗanda suka chanchanta , !

Mai martaba sarkin Maradi tare da Mommoudou , ‘wanda hajiya mama ta tilasta masa zuwa taron ƙarin girman ,” sai Tafeeda ƙarƙashin rakiyar tawagar maimartaba , suna cikin mutanen da suka halarci wannan taron da suka samu isowa a yau ,

sai kuma Ubbo tare da Siyama wacce ita ma ta iso Niamey tun ranar asabat tayi zango a gidan ubbo tare da cigaba da tsara yadda zata fara bin matakin farko na kusanta kan ta ga Biyamuradi muradin zuciyar ta !

Da wasanni irin na soji , kiɗe-kiɗen su zuwa faretin su , aka fara buɗe taron da kai tsaye ake watsa shi a gidajen tv dake baki ɗayan ƙasar Niger ,

Kafin a bada dama ga maigirma Shugaban ƙasa yayi jawabin yabo da jinjinawa ga sojojin ƙasar sa , sannan shugaban rundunar sojojin ƙasa na ƙasar ma yayi nasa bayanin , har zuwa kan wasu manyan kusoshin gwamnatin ƙasar da manyan soji da duk dai yabo ne suke yi ga sojojin su da suka dawo daga bakin daga ,

Youssof Abdul-azizou shine wanda aka fara ƙira domin martaba shi tare da yi masa ƙarin girma ,

Da faretin su na soji ya fito filin ya ƙarasa har zuwa gaban shugaban ƙasa ya sara masa ya juya gaban manya-manyan sojojin su na ƙasa nan ma ya sara musu kafin ya ƙarasa kan ɗan tudun da aka tanada domin tsayuwar sa inda shugaban sojin su na ƙasa yake tsaye , daga gefen sa wasu sojoji biyu ne a ƙame da ƙwali rike a hannuwan su ,

Sara masa yayi ya ƙame ,

cikin takun sa na soja lieutenant General ya ƙaraso gaban youssouf tare da kai hannun sa ya warware ɗan yadin dake ɗauke da tambarin girman matsayin youssouf ɗin a soja , ya miƙa sa ga ɗayan sojan dake hannun sa na hagu ya sa a kwalin hannun sa ,

lokaci guda ya waiga ga ɗayan sojan ya ɗauki sabon rank ɗin da ke ɗauke da zanen yellow layi huɗu wanda yake ninke cikin kwalin hannun sojan ya maƙala a gefen kafaɗar youssouf ɗin dai-dai inda ya cire na farkon ,

Da hakan yake nuni da sabon matsayin Youssouf Abdul-azizou Baskore da ya tashi daga colonèl ya koma Brigadier youssof Abdul-Azizou baskore ,

A take gurin ya ɗauki tafi tare da sarewa da gangunan su na soji , wani irin yanayi ne ya bayyana a fuskar mommodou da take kirtiɓ ya haɗe girar sama da ta ƙasa , idanun tafeeda da ya sauƙa cikin nasa shi ya sa shi gyara yanayin fuskar sa tare da haɗa hannunwan sa biyu cikin yanayi na dole ya ɗan tafa su ,!

STORY CONTINUES BELOW

Da fareti major youssouf ya dunga bin su ɗaya bayan ɗaya tun daga kan shugaban ƙasa har zuwa shuwagabannin sa wajen aiki yana sake sara musu , masu camera na aikin haska shi da masu ɗaukar sa a video , ƙarshe ya dire a gaban mahaifin sa da yake hakimce cikin shigar su ta sarakuna , idanun sa da suke sakaye cikin farin gilashin ƙarin ƙarfin ido suna bayyana tsantsar farin cikin da yake ciki , yayin da bakin sa da yake rufe ta cikin rawanin sa yaƙi daina murmushi ,

Ƙamewa yayi ya sarawa mahaifin sa , ga jin daɗin sa sai maimartaba ya miƙe gami da miƙa masa hannu suka yi musabaha idanun su na musayar zallar ƙauna , ya rungumo shi zuwa jikin sa ,

Bakin sa na furta kalmar

MADALLAH DA KAI MAJOR YOUSSOUF KAI KA KASANCE ABUN ALFAHARI NA ,

Kunnuwan youssouf kaɗai suka jiyo me mahaifin nasa ke cewa .

Yayin da fuskar mommodou tayi jaa tana tsattsafo da gumi .

Ware idanu sosai hajja me wurya take cikin son tabbatar da fuskar wanda take gani tarwai a fuskar ƴar tv da take kunne cikin ɗakin su na hotel da basu fi mintoci ishirin da dawowa cikin sa ba daga asibiti da aka sallamo baby mama wacce tayi sumul da ita tana ƴan wasanni ta tamkar ba ita ce jiya ta sha wahala ba ,

Ke fatima wannan ba mijin naki bane ake masa ƙarin girma a wajen aikin sa? Ga shi nan ana nuna sa a tv,? ashe babban SOJA kike aure , ah ki ce shiyasa kike firirita , ashe matar soja ce ,

SOJA ?

waye ne sojan ? Ita fa bata ƙaunar soja ko jin sunan su ta yi zuciyar ta tsinkewa take , mutanen da suke da bindigogi da jiragen yaƙi ita kuwa ai bata manta bama-baman da sojoji suka dunga sakar musu a daji ba, da har ya sa ta gurɗe ƙafar ta gurin gudun ceton rai ,

Saitin inda take jin tashin tv ta maida hankalin ta kafin ta ce

Hajja waye ne soja ?

Shi baban jaririyar taki ,

Gwalalo idanu tayi

Soja ne daman ? Soja masu ƴaki da bindiga da jirgin ƴaki hajja ?

Au daman baki ma san irin aikin mijin naki ba ? Hunm abun naki sai ido , bebiya ta auri makaɗi ,3

Shiru falmata tayi tana jin wani tsoron sa sabo dal yana ɗarsuwa a ran ta , baban baby SOJA ne ?, “

****

La’asar tayi musu a gidan da yake matsayin na biyamuradi youssouf da falmata , sojan da ya kawo su niamey shine ya je ya ɗauko su daga hotel ɗin ƙarƙashin umarnin youssouf da tun safe suke tare da maimartaba tare da wasu manyan ƙusoshin ƙasar a ainahin cikin gidan gwamnatin tarayya ,

Tunda suka shigo gidan da bayan sojan ya gama shigar musu da kayan ya danƙa ƴan mukullayen ga hajja me wurya ,

Santin gidan hajja take tana bin kowanne lungu da saƙo tana leƙawa tare da addu’o’i tana jere su iri iri ,

Gidan ba wani babba bane amma tsarin sa me kyau ne dai-dai da rayuwar mai rufin asiri kuma ƴan gayu , ɗakuna uku ne a cikin dan madaidaicin falon sai kuma kitchen da yake ta cikin falon sai keɓantatcen wajen cin abinci , ko’ina an sanya kayan da suka dace ,

cikin ɗakuna biyun gadaje ne iri ɗaya tare da wardrobe ɗin su, sai dai ɗaya ɗakin akwai set ɗin gadon jarirai har da ƴar kwabet ɗin jera kayan jarirai da yake mallakin baby mama , gidan kam yayi kyau sai sa albarka hajja me wurya take , ita kaɗai ba tare da falmata ta kula ta tanka mata ba ,

yammaci lis biyamuradi Youssouf ya iso gidan tare da shi akwai sabon direban da gwamnati ta ba shi , bayan motar su cike taf da kayan abinci zuwa ƴan kananun kayan buƙatu na gida irin su , omo , sabulai , toothpaste

da sauran su,

STORY CONTINUES BELOW

Kai tsaye ya shiga gidan bayan ya ƙwanƙwasa ƙofa hajja ta buɗe masa , kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna bayan sun gaisa da hajja wacce take ta shi masa albarka har ma ta taya shi murnar ƙarin girman da ya ssmu wajen aiki ,

Dumm ! Yayi , ƙaƙa ankayi ta san an masa ƙarin girma ?1

Kamar ta san tunanin da yake cikin dariya tace ma sa

Ɗazu na gani a tv , gaskiya ɗan nan ka sha hotuna , anya hasken majigin hoto bai kashe ma karfin gani ba ? Yadda ka ƙware a rawar nan ta ku ta soji ka burgeni ai naso ita ma wannan matar ta ka tana gani ,da ta ga yadda kake shan juyi a fili nasan dole ka burge ta , hahaha

Ɗan murmushi yarima yayi yana maida kallon sa ga falmata wacce take gefe a ƙasa riƙe da baby mama , alamun rashin kuzari duk sun bayyana agare ta ,

Fatima miƙo min ɗiyar ki na ga fuskar ta ko kouwa har yau kina mini rowar ta ne ??

Cikin sauri ta girgiza kan ta , “

Hajja miƙa ma sa ita !

Hajja me wurya ta karbi baby ta bashi ,

Ya karbe ta yana tambayar yanayin lafiyar jikin ta a yanzu ?

Hajja ta amsa masa da samun tabbatuwar lafiya ga baby mama ,

ya shagaltu da yiwa ƴar sa wasa daga shi sai falmata da ke rakuɓe daga chan gefe ,

Hajja tana cikin kitchen tana aikin gyarawa tare da sanya duk wasu kayan abinci a inda suka dace ,

bata yi aune ba ta ji ƙarar bindigogi da sauti iri iri ya karaɗe falon da ya sa ta yunƙura da gudu tana neman wajen tsira , rashin sanin kan falon ya sa ta dunga cin karo da kujeru ,

Wani mummunan karo ta ci da doguwar kujerar falon da yasa tayi baya tare da sakin ihun da yasa biyamuradi miƙewa a zabari ya taro ta da hannun sa ɗaya , jin mutum a kusa da ita da ƙara kusantowar harbe harben da take ji ya sa ta ƙwaƙumewa a jikin sa ta zagaye dukkanin hannunwan ta biyu zuwa bayan sa ,

Hajja da ta fito da gudu saboda jin ihun falmata da ƙarar harbe-harben bindiga , sai ta ɗan yi turus tana yawo da ido neman bindigar take ,

Miƙa mata baby mama yayi ganin yadda take ƙoƙarin sanya kuka saboda ƙaƙƙarfar rungumar da falmata tayi masa ya sa ta firgita ,

Hajja ta karɓe ta tana cewa ƙarar bindiga nake ji ɗan nan , ince dai ba wai yaƙi aka soma ba ??

Bai amsa mata ba illa zaro wayar sa da yayi daga cikin aljihun sa bai duba waye ke ƙiran ba ya katse kiran ,

Hajja ku yi haƙuri sautin ƙiran téléphone ne hakka ba wani abou bane ya kai ga faruwa ba ,

Au to to , ai cewa nake yaƙin ne ya biyo mu har nan , !1

Wucewa tayi da baby mama ɗaki tana neman abin goyo ,!

Fatima

Sakar ni haka nan , na faɗi miki ƙarar talfo ne …

Wayar sa da ta sake ɗaukar ruri ita ta sa falmata ƙara sanya ihu tana sake shigewa jikin sa idan banda ƙyarma babu abunda jikin ta ke yi ,

Sauri yayi ya ɗaga kiran ganin sunan me ƙiran na sa

princesse

Allô ma jolie fille.1

Ya furta dai-dai lokacin da yake yin baya ya zauna akan kujerar da ya tashi tare da falmata wacce har lokacin riƙe take da shi tsam ta runtse idanun ta ,

Allo Mon amour !

tu me manques mon amour comment vas-tu aujourd’hui?1

STORY CONTINUES BELOW

Gimbiyar maimouna ta amsa masa cikin salon sautin ta na gogaggun matan da suke tsakiyar ganiyar su ,

Je vais très bien et tu me manques aussi,

Ya amsa mata yana jin yadda daɗin sautin ta yake ratsa jikin sa ,

Ma princes , Albishirin ka ?

Tace da shi .

Ɗauke da amon murmushin da ya bayyana har a fuskar sa yace ,

Gorro farare gimbiya !

Ko kassan yanzou jakka ( jakadiya ) ke sanar mouna saƙo ya taho dagga masarautar ku maigirma , ɗauke da gorron tsayar da ranar amren mu , gomma ga wata me kamawa , tabbas sa’a zata tabbata gare ni ranar da anka ɗamra amren mu da kai biyamuradin maraɗawa !

Wani irin daɗi ne marar misaltuwa ya ji yana ratsa zuciyar sa , tabbas zuciyar sa na ƙaunar maimounatu fiye da kowacce ɗiya mace , samun ta kuma nasara ce maigirma saboda a ta suffa da ƙawa tayiwa sauran mata zarra a wajen sa ,

Cikin shauƙi ya sake riƙe wayar sa da kyau yana ɗan bubbuga bayan falmata wacce ta fara dawowa hayyacin ta , da ɗayan hannun nasa ,

Wannan albishir naki mai girmou ne tauraruwar Agades , votre histoire a fait son chemin dans mon cœur, s’enfonçant dans mon âme.

tamkar Falmata ta ji abunda ya faɗi , sai ta ɗago kan ta daga jikin sa , a hankali ta zare jikin ta daga nasa , ta miƙe tana taku sannu-sannu da ƙoƙarin barin falon , zuciyar ta shaƙare da haushin sa , ita shiyasa ta tsani soja ,1

kome na su akwai sumfurin mugunta a ciki bayan haka tayaya sautin ƙiran waya da ta san ƴar ƙara ce mutane ke sawa a wayoyin su amma sai ga shi ta shi wayar ruwan alburusai take har da tashin boma bomai ,”4

Cigaba yayi da hirar sa cikin nishaɗi yana jin yadda albishirin da tayi masa yake ƙara masa kuzari , lalle maimartaba yayi masa attaque par surprise

Fiye da mintoci ishirin suna hirar su sannan suka yi sallama ya aje wayar sa ,

Bankwana yayi da hajja wacce har lokacin tana kitchen goye da mama tana girka musu ɗan abinda zasu ci kafin kwanciyar bacci ,

Har ƙofa ta raka shi tana masa addu’a da godiya

Inda yake sanar da ita gobe zai wuce garin su zai iya kaiwa sati biyu zuwa kwanaki ishirin idan ya tafi saboda haka zuwa goben su masa lissafin abubuwan da zasu iya buƙata baki ɗaya ,

Bayan fitar sa ta kulle ƙofar ta dawo ciki zuciyar ta cike da wasi-wasi akan hirar da ta ji youssouf ɗin na yi da wata wacce bata kai ga sanin wacece ba , sai dai cikin hirar su da mafi yawa da faransanci shi youssouf ɗin yake bada amsa , ta fahimci mafi yawan maganganun nasa na soyayya ne saboda zaman da tayi a ƙasar kamaru , kurtun ɗan sanda ne mijin nata a bariki suka yi rayuwar su dan haka sosai take tsintar wasu kalmomin faransanci duk da dai shekaru ya sa ta manta yaren sosai !

A fahimtar ta youssouf yana da wata mace wacce yake tsanananin so da a kowanne lokaci zata iya cuso kan ta cikin rayuwar sa ta mallake shi wanda hakan yake babbar barazana ga rayuwar auren sa da yarinya falmata miskiniya ,

STORY CONTINUES BELOW

Hodijan !

Kai tsaye ɗakin da falmata ta shiga nan ta tasamma ,

A zaune ta tarar da falmatan daga ƙasa a bakin ƙofar ɗakin ta takure ,

Kallon ta tayi ta ji tausayin ta ya tsirga mata , hakkun ta fara hango ƙalubale a rayuwar auren yarinyar da ko fahimtar kalmar auren ma ba ta kai ga yi ba ,

mutuniyar kina zaune anan ne ??

da sauri falmata ta ɗago kan ta ,

Hajja ya tafi ?? Mama tana hannun ki ?

Eh ya tafi ga kuma mama a baya na , taso nan muyi wata magana kin ji ƙawalliye roman jaɓa !1

******

Abuja Nigeria

Yakaka ta dage da neman ilmi tun ana koya mata haruffa ,A ,B,C,D , da kuma ا ب ،ت ،ث، sannu sannu ta haddace su tare da iya rubutun su , aka fara haɗa mata jimla , tana koyan rubutun su tare da sanin ma’anar su ,1

ba ƙaramin daɗin koyar da yakaka malama maryam take ji ba saboda wankakkiyar ƙwaƙwalwa me saurin ɗauke abu da yakaka take da ita ,

A hankali ta fara lura da ƙarancin wayon da yake ga yakaka tare da gidadanci , sai tayi ƙoƙari tana gyara mata duk lokacin da ta ga tayi wani abunda bai kamata ba , tare da yawaita yi mata ƴan nasihu akan duk wasu manya da ƙananun zunubai .

Gefe guda lubna na ƙara zage damtse ita a dole sai yakaka ta iya English da arabic ta iya magana da yarukan kamar yadda ta iya , dan haka sai ta tsiri yiwa yakaka magana da English ko Arabic ta daina yawan yi mata magana da hausa koyaushe ,

ga bangaren yakaka ita ma ƙwarai ƙwarai take jin daɗin haɗuwar ta da malama maryam da ƴaƴan ta , domin sun ja ta a jiki suna kuma gwada mata ƙauna hatta mahaifin su da ba sosai ma suke haɗuwa ba , amma duk lokacin da suka haɗu yana amsa gaisuwar ta faram-faram babu nuna tsangwama ,

Dan haka gidan su nan ne wajen yinin ta idan babu makaranta , ranakun makarantar ma daga ta baro makarantar gida zata tayi sallah ta ci abinci ta sauya uniform ɗin ta , ta dawo gidan ta kama musu ƴan aikace aikace kafin malama maryam tayi sallah ta ɗan huta , zaman ta da samy baby sai ya ƙaranta ,

Ranar wata litinin an tashi da hazo sosai tare da sanyi mai tsanani tun safe , zuwa yamma sai hazon ya ƙaru sararin samaniya yayi jawur iska me ƙura tare da tsananin sanyi yana kaɗa jikin al’umma , kusan kowa sauri-sauri yake ya gama abunda yake a titi ya koma gida

Bayan tashin su yakaka a makaranta tare suka dawo da malama maryam ita ta wuce gida da zummar yin sallar la’asar ta ci abinci ta sauya kaya ta koma gidan malama maryam wacce ta sake jaddada mata kan lalle fa ta zo su yi darasi kar ganin yanayin garin ya sa ta ƙi zuwa , cikin ladabi ta amsa da

To zan zo Anty !

Da sallama ta tura ƙofar falon samy baby tare da danna kan ta kai tsaye , abunda ta gani ya sa jakar hannun ta saɓulewa zuwa ƙasa ,

Ɗaya daga cikin ƙawayen samy baby ne tare da saurayin ta suke yin masha’ar su nan kan kujerar falon babu kunyar ubangiji ko shakkar za’a iya shigowa agan su haka ,

Da sauri yakaka ta kawar da ganin ta daga kan su , tare da sunkuyawa ta ɗau jakar ta da sauri ta wuce ɗaki ba tare da ta sake kallon su ba tana jin yadda jikin ta baki ɗaya ya ɗau rawa da tasowar sabon yanayin da take ji cikin illahirin wata jijiyar jikin ta ,”

A kasalance ta gama kome hatta cin abincin ta da samy baby take ajiye mata shi a ɗakin ta,

ta shiryo ta fito falon da fatan son sake ganin su , saboda ganin su na ɗazu da ya tayar mata da wani yanayi cikin jikin ta tare da bijiro mata da guguwar begen yarima da ta ɗan kwanta sakamakon mayar da hankalin ta da tayi kan karatu ,2

STORY CONTINUES BELOW

sai dai ganin da ta yiwa waɗanan fasiƙan ya sa ta fara tuno da wasu abubuwa masu kamanceceniya da wanda ta ga suna aikatawa , da abunda ya shiga tsakanin ta da bature kam silum ,

ba ta tarar da su a falon ba , dan haka ta sanya ƙafafu ta bar gidan , tana tafe tana jin ƙewar bature kam silum na sake lulluɓar ta , ko yana ina yanzu ? Wataƙila ma ya manta da ita ! , ruwan hawaye ta ji suna taruwa a idanun ta ,daidai lokacin da take tura babbar ƙofar gidan su malama maryam ta shiga ,1

karaf suka ci karo da lubna wacce take ƙoƙarin fitowa daga gidan hannun ta riƙe da wata leda ,

Yauwa ƙawata Dan Allah zo ki raka ni wancan gidan ummi ta aike ni ,

Tana mata nuni da wani babban gidan da yake chan kusa da ƙarshen layin su ,

Ba musu ta bi bayan ta , lokacin da lubnan take jan hannun ta ,

Saƙo lubna ta kaiwa matar gidan tana bata saƙon suka mata sallama suka yi fitowar su ,

Sun zo dai-dai tsakiyar harabar babban gidan , yakaka ta ga wani ɗan dogon saurayi ɗan gayu ya sha gaban lubna fuskar sa a marairaice idanun sa fes akan ta ,

Lubna Haba dan Allah ki saurareni , yau wajen watanni bakwai kenan ina bin ki da soyayya ta amma kina min walakanci , dan Allah ki TAIMAKA MIN ki yadda da soyayya ta wallahi ina tsananin son ki ,

Ba tare da lubna ta ɗaga ido ta dube shi ba ta kewaye shi ta wuce tana sake jan hannun yakaka ,

Charaf ! Ya riƙo hannun ta Lubna Dan Allah ki taimak….

Wani irin ƙara lubna ta sa kamar ya jona mata wuta , ta warce hannun ta da matuƙar ƙarfi cikin abinda bai wuci daƙiƙai ba ta cire hannun ta ta wanke shi da mari , kafin cikin muryar ta da take karkarwar kuka ta tace

Kar ka kuskura ka sake taɓa ni , ni ba ƴar iska karuwa ba ce ,

Kukan da ya zo mata ya sa ta kasa ƙarass zancen ta da gudun gaske ta juya tana barin gidan ,

Yakaka wacce take sakakai a tsaye ta bi shi da kallon tausayi a hankali ta furta kalmar

Kayi hakuri

Gƴaɗa mata kai yayi

Cikin sanyin jiki ta juya ta bar shi a wajen ta nufi gida ,

Tana shiga cikin gidan ta tarar da lubna rungume jikin mamar ta banda kuka babu abunda take , malama maryam sai tambayar ta take me ya same ta ? Me aka mata ? Ta gaza bata amsa ,

Kallo mai bayyana haushi yakaka tayi mata lokacin da take zama a gefen malama maryam ,

Anty wai fa dan kawai wani mutum ya kama hannun ta yace ta taimaka masa yana son ta shine ta mare shi ta gudo gida tana wannan kukan ,

Ta ƙarasa zancen muryar ta na nuna jin haushin abunda lubna tayi ,

Waye ya kama hannun ta ? Wanne mutum ne , ke lubna ɗago ki dube ni waye ne ya riƙe miki hannu meye tsakanin ku da shi ? Ki faɗa min gaskiya ,

cikin shisshiƙar kuka lubna tace ummi , Mukhtar ne ɗan gidan Alhaji Umar , shine tun watannin baya yake tare ni yana cewa wai yana so na , shine yau ya tare ni a gidan su har ya riƙe min hannu wai na taimake shi yana so na ,

Nan take fushi mai tsanani ya bayyana a fuskar malama maryam , ta shiga yin faɗa meyasa tun ranar farko lubna bata sanar mata ba ? Ita kuma ta faɗawa baban su lubnar ya sami mahaifin yaron anyi musu tsakani ba ,

Faɗa take yiwa lubna tamkar zata doke ta , a karshe ta gargaɗe kan ko kusa ta da shi bata yadda ta sake tsayawa ba kuma zata faɗawa baban su ya sanar da mahaifin yaron su ja kunnen ɗan su , ya fitar harkar ƴar su ,

STORY CONTINUES BELOW

Sororo ! Yakaka tayi cikin jin mamakin malama maryam menene abun tashin hankali haka ?

Da son kwantar mata da hankali tace ,

Anty ai hannun ta fa kawai ya riƙe , kuma fa cewa yayi ta taimaka masa ,

wani irin kallo malama maryam tayi mata ,

Yakaka ,

Namiji baligi ya kama hannun mace baliga haramun ne a musulunci , muddin ba muharamman juna suke ba domin tafarki ne na samar da ZINA a tsakanin mace da namiji ,

Zina kuma haramun ce a musulunci, kuma tana daga cikin manyan laifuka wanda ake kira Kaba’ir.

Allah ya fada cikin Qur’ani

و لا تقرب الزنى

Wato kada a kusanci zina.

Hikimar fadin hakan shine ba aikata zina kadai ba, aikata abunda zai janyo zinar irinsu rungumar juna , taɓe-taɓen juna da shafe-shafen jikin juna tsakanin namiji da mace dukkansu Allah yayi hani domin hanya ce ta kusanta kai ga zina ,

cikin sanyin murya yakaka tace

Anty menene ZINA ??

Zina ita ce Saduwa a tsakanin namiji da mace ,( ina nufin mace da namiji su kasance cikin abun rufuwa ɗaya jikin su na cikin na juna , azzakarin namiji yana cikin farjin mace ) ba tare da hukuncin aure ya shiga tsakanin su ba , duk mace da namijin da suka yi tarayya irin haka ba tare da an ɗaura musu aure kamar yadda addinin musulunci ya koyar ba to babu shakka sun aikata zina ,

kamar yadda na faɗa miki ita zina tana cikin manyan laifukan da Allah yayi hani da su sannan kuma ya tanadi hukunci ga duk waɗanda suka aikata ta ,

Hukuncin Zina a shari’ance , ita zina ba’a tabbatar wa da mutum ita dole sai da hujjoji, hujjoji guda biyu ne ko dai mutum ya yarda da kanshi ya aikata , ko kuma mutane huɗu su ganshi turmi da taɓarya a wannan hali ne ake tabbatar da zina,

Amma ko mutune uku ne suka ce sun ganshi turmi da taɓarya sai ɗaya yace shi dai ya gansu a tube suna shafe shafe to baza a karbi shaidun su ba, za’ai musu bulalar ƙazafi tamanin tamanin ,

Amma idan shaidu sun kammala ko mutum ya amsa da bakin sa yayi zina Hukuncin sa a shari’ance shine bulala ɗari ga waɗanda basu taba aure ba. Kamar Yadda Allah ya faɗa”

الزانية والزانى فاجلدا كل واحد منهما مأة جلدة، ولا تأخذكم بهما رأفة فى دين الله إن كنتم تؤمنون بالله واليوم الآخر.

Wato mazinaci da mazinaciya ayi wa kowanne su bulala ɗari, kada tausayi ya kama masu dukan idan har sun kasance masu imani da Allah da ranar lahira.

Sai wanda yayi aure akwai hadisin da yace duk mai aure ko wanda ya taɓa aure idan ya taɓa zina za’a jefe shi, amma sai idan shine da kanshi yazo yace yayi zina yana so a jefe shi, amma idan bai yadda a jefe shi ba ba za’ayi mishi dole ba za’a barshi ne.

Wani irin tsoro da tashin hankali me tsanani ne ya dirar mata , cikin wata irin muryar da ke bayyana tsantsar firgicin da ruhin ta ke ciki , tace1

Anty ko da mutum taimako yayi ,

Malama maryam cikin tsanaki tace ban fahimce ki ba yakaka wanne irin taimako ne yake zuwa ta hanyar aikata zina ??

Anty ina nufin ko shi namijin cewa yayi mace ta taimaka masa , sai ita ma ta taimaka masa , suka yi , shikenan tayi zina ??

STORY CONTINUES BELOW

Su dukan su sun aikata zina , saboda babu biyayya ko temakekeniya tsakanin bayin Allah wajen saɓa masa , su dukkanin su basu da hujjar kare kan su , suyi gaggawar tuba ga ubangiji domin zina babbar musiba ce ,

Sannan kuma yakaka ai duk namijin da zai cewa mace ta taimaka masa ta bashi kan ta suyi zina , ai wannan babban maƙiyi ne a gare ta , bata da maƙiyi sama da shi , mugu ne kuma macuci domin na farko zai ɓata tsakanin ta da ubangiji , yasa ta aikata abunda Allah zai yi fushi da ita , da zai hana ta samun ganin Alkhairi da dacewa cikin rayuwar ta duniya da lahira har sai idan ta tuba ,

Na biyu duk ranar da mutane suka san me suke aikatawa, mutanen kirki zasu guje ta , za’a dunga mata kallon fasiƙa, mazinaciya ƴar iska , karuwa .

Na uku idan ta hanyar zina da suka aikata ta samu ciki ta haihu , abun da ta haifa idan ya girma shi ma da kan sa zai tsane ta , ƙimar ta zata zube a idanun abunda ta haifa , saboda ta zamto sanadin da mutane zasu dunga ƙyamatar sa da ganin sa wani mutum da aka samar da shi ta haramtatciyar hanya ,

Bayan haka illolin zina suna da yawa , daga ciki akwai ɗaukar munanan cututtuka da zasu iya kai me su ga mutuwa ,

A ƙarshe namijin da duk zai yi zina da mace abu ne me wuya ya aure ta , ko da ya aure ta kuma bazai taɓa ganin ƙimar ta da mutuncin ta ba , sannan ƙanƙanin kuskure zai iya haifar da zargi a tsakanin su da zai lalata musu aure ,

Kuma duk macen da tayi zina kafin tayi aure bata da wata martaba a idanun duk wani namijin da zai zo ya aure daga baya saboda ta rasa ƙima da mutuncin ta na ƴa mace tunda tayi zina .

Ki gujewa abunda duk zai kai ki ga aikata ZINA yakaka cikin ta akwai tarin masifu kin ji ko ??

Bata amsa ba illa miƙewar da tayi bata tsaya ba ta taka da gudun gaske tana barin gidan ba ta ko tsaya ta sanya takalman ta ba bare ta saurari ƙiran da malama maryam take mata ,

gudu take bata ko dub Inda take jefa ƙafar ta ,

Da ƙarfi ta tura ƙofar ɗakin tana shiga ta zuɓe a tsakiyar ɗakin tana sakin wani irin kuka marar sauti da yake tuƙowa daga ƙasan ruhin ta ,

Cikin wata irin murya ta fisgo kalmar ,

ALLAH NA TUBA , NA TUBA ALLAH , BAZAN SAKE BA ,ALLAH NA TUBA KA YAFE MIN ,

Kuka take tana maimaita kalmomin nan jikin ta har tsuma yake ,

Ashe haka ne girman laifin da ta aikata batare da ta sani ba ? Ashe ita ɗin me tarin zunubi ce ? Ashe baza ta samu wani alkhairi ba arayuwar ta tunda tayi zina ,

Ta jima a zaune a wajen tana kuka har duhun dare ya shigo , zuciyar ta ta tsorata iyaka , neman yadda zata yi Allah ya yafe mata take yi , sai dai bata san yadda zata yi Allah ya karbi tuban ta ba , ji take kamar zata mutu ,

Tashi ta sake yi tana gama hanya saboda kukan da ta ɗauki lokaci tana yi yasa kan ta sarawa tare da fara jin jiri ,

tana gama hanya ta fito , bata ko dubi ɗakin samy baɓy da kiɗa ke tasowa ta cikin sa alamun da ke nuna ta dawo gidan ba , ta sake fita ,

hanyar gidan malama maryam ta sake ɗauka ,

tana so ta san yadda zata yi Allah ya yafe mata , tana so ta san yadda zata yi ta gyara kuskuren ta ,

STORY CONTINUES BELOW

a falo ta tarar da malama maryam tare da iyalan ta suna cin abincin su na dare ,

Babu sallama ta rakaɓe daga bakin ƙofar gami da sakin kuka me ciwo ,

hankali tashe malama maryam ta tsame hannun ta daga abincin da suke ci ta miƙe , ta zo ta kama yakaka ,

Tambayar ta take lafiya ?meye ya same ta ? Ko wani abu ya samu antyn ta ? Daman yanzu take so idan ta gama cin abinci lubna ta raka ta gidan nasu ta duba ta domin ɗazu ta fita bata cikin nutsuwar ta yanzu kuma ta dawo tana kuka , shin menene yake damun ta ??

Cikin muryar ta da kuka ya fara disarwa , tace nayi ZINA malama maryam , ki taimake ni ki faɗa min yadda zan yi Allah ya yafe min , ban sani ba malama maryam wallahi ban sani ba ,

Ta shi , ta shi mu shiga ɗaki ki nutsu ki min bayani yadda zan fahimce ki ,

Ta kama hannun ta zuwa ɗaki ta zaunar ta bakin gado , ina sauraran ki me kike son faɗa min yakaka ?

Tiryan tiryan , yakaka ta fara bada labarin tun daga farkon haɗuwar ta da yarima har yanayin yadda abubuwa suka kasance har zuwa yadda alaƙar ta da samy baby da yadda ta yaudare ta ta zo da ita garin abuja ta baro ɗanyar jaririyar ta tare da makauniyar ƙanwar ta, bata idasa ba malama maryam ta katse ta ,

Kin yi kuskure yakaka , kin yi kuskure , kin yi kuskure ,! Kaicho

wani irin tausayi chakuɗe da bacin rai take ji cikin ran ta , tamkar wata makusanciya a gareta ce ta aikata abubuwan da yakaka ta aikata ,

tun farkon fara koyar da yarinyar ta fahimcin tana da raunin sani sosai da sosai game da addini , kusan ma bata san kome ba , shiyasa ta ɗaura aniyar ganin ta kawo sauyi ta fidda ta daga duhun jahilci , cikin rashin sanin ta ashe jahilci tare da rashin wayon yarinyar har ya kai haka ( Bata san menene zina ba ) ? Ta yadda aka yi amfani da jihilcin aka cutar da ita cuta mai tsanani irin haka ?

Kukan da yakaka take ya tsansnta ganin shirun malama falmata ya ɗau lokaci tare da bayyanuwar matsanancin tashin hankali bisa fuskar ta ,

ALLAH zai yafe miki yakaka , muddin kika nemi yafiyar sa tare da niyyar baza ki sake komawa ga aikata saɓo irin wannan ba , ALLAH me yawan gafara ne ga bayin sa ,

Duk da cewa akwai bayanai daga malamai game da mutumin da ya aikata saɓon Allah alhalin bai san cewa sabon nan me girma bane da zai iya kai me shi ga shiga wuta ,ko kuwa bai ma san saɓo bane baki ɗaya, akwai hukunce hukunce , hukunci na farko shine , Shi JAHILCI ba’a uzuri da shi, sai dai cikin wannan hukuncin akwai bayanai da suke nuna akan karbi uzurin JAHILI , idan ya kasance gurin da ka tashi babu addini , babu malamai masu koyarwa ,ko kuwa an hana ka damar fita neman ilmin kuma ba’a koyar da kai ba a gida , to za’a iya yi maka uzuri da wannan , amma idan gurin da kake akwai addini akwai malumma , sai kaƙi fita ka nemi ilmi kasan hukunce hukuncen addini kayi zaman ka cikin jahilci to wannan baka da uzuri a addini , jahilcin ka ba uzuri bane ,

to amma idan ka rasa damar samun ilmi ne , akwai hadisin manzon Allah sallalahu alaihi wa sallam da yake cewa :

Allah ya ƙetarar da Al’umma ta abu uku , ma’ana ya yi musu afuwa akan abu uku , na farko shine mutum yayi abu cikin rashin sani , na biyu mutumin da ya aikata wani kuskure akan mantuwa , sai na uku wanda aka tilasta ma sa aikata saɓo, !

To idan aka yi duba ga wannan hadisin za’a yiwa mutumin da duk ya aikata wani saɓo cikin rashin sani , uziri a sassauta masa , sannan shi kuma yayi tuba zuwa ga Allah , tsarkakaken tuba ,

Manzon Allah yana cewa : duk wanda yayi tuba na gaskiya to zai kasance kamar bai taɓa aikata wannan Zunubin ba , amma wanda yake tuba alhali yana komawa ga aikata zunubin sa to tamkar yana yiwa Allah izgili ne .

kiyi Tuba na gaskiya yakaka tare da niyyar baza ki sake kusanta kan ki ga aikata ZINA ba a rayuwar ki , Allah zai yafe miki ya wanke ki a idanun Al’umma domin Laifin shi kika yiwa ,

Sannan , ki tashi ki nemi ilmi ki kuma yi aiki da shi idan dama ta samu gare ki kome ƙanƙantar sa ki koyar da ilmin da yake gare ki domin sauran Al’umma su amfana ,

shiriya ta zo miki hasken ilmi ya zo miki ki sa hannu biyu ki karɓe su ƙwarai akwai falala tare da samun dacewa a cikin su , ki manta da rayuwar baya ki himmantu wajen neman gafarar ubangiji akan saɓon da kika wanzu kina aikatawa , da fatan kin fahimce ni ??

bata amsa ba illa hannu da ta kai ta rungume malama maryam , idanun ta na zubar ƙwallar da ita kaɗai ta san dalilin sauƙar su a daidai wannan lokacin

Godiya ta dunga jerowa malama maryam har lokacin da ta sanya ƙafar ta tana barin gidan lokacin dare ya fara shiga karfe goma saura ,

kan titi babu kowa garin ya sake ɗaukar sanyi , a hankali take tafe iska yana ɗaga hijabin ta , tayi zurfi cikin tunani , daki-daki take tuno kome da ya dunga faruwa a rayuwar su ita da ƙanwar ta ,

tana so ta zargi iyayen su akan killace su a gida da suka yi suka hana su neman ilmi , sai dai so irin na tsakanin ɗa da iyayen sa ya mata dabaibaiyi yaƙi bata dama , ji take suna da wata hujjar su , babu shakka akwai dalili ,1

tunanin falmata da baby mama yayi mata dirar mikiya , wata irin kunyar falmata ta ji tana nuƙurƙusar ta , yaya zata Ji ranar da duk ta san irin kuskuren da tayi har ta samar da baby mama ta gudu ta bar mata ita ? Wataƙila daga ranar zata fara tsanar ta ,

tsoro take ji tsoron girma ya zowa baby mama ta samu sani akan irin ta hanyar da aka samar da ita , ? Me zata cewa waɗannan bayin Allah biyu ??

Lalle wajibi ne a gare ta ta nemi ilmin addini ko domin ta samun ƙarfin guiwar da zata iya fuskantar su tare da tarin hujjoji da bayanan da addinin ya tanadar domin ta gamsar da su ta kuma wanke kan ta a idanun su su san cewa ta aikata kome ne cikin DUHUN JAHILCI ,!1

Ko zasu fahimce ta ? Ko falmata zata yadda ta cigaba da riƙe ta a matsayin ƴar uwa masoyiya ? Ko baby mama zata yadda da ita a matsayin uwa ?? Yaushe wannan ranar zata zo ? Zata zo nan kurkusa , ko sai bayan shuɗewar tsawon wani lokaci ? Abun da ta riga ta sani muddin su na raye wannan ranar zata zo ,

YARIMAN MARAƊI ,

Zuciyar ta ta auno mata da sunan sa da kome da ya wakana cikin rayuwar ta a wannan gaɓar shine sanadi ,

bata gan shi ko kusa tare da duhun jahilci makamancin nata ba , kome da shi yayi mata yayi ne cikin ilmin sa ,da sanin sa ya aikata Zina da ita ,

zuciyar ta take ji tana wani irin buɗawa da sabon yanayin da yake shigar ta akan sa da sabon matsayin da ya kamata ta ajiye shi tun farko a ran ta ,

Tunowa ta fara yi filla filla da farkon haɗuwar su har zuwa ranar ƙarshe da ya kore ta daga motar sa a tsakiyar titi tana kuka , yayi tafiyar sa ya bar ta har yau bai sake waiwaiyar ta ba ,

tabbas shi macuci ne azzalumi agare ta bai chanchanta da samun soyayyar ta ba ko kaɗan ,1

bai taɓa son ta ba , kawai amfani yayi da jahilcin ta ya ribaci gangar jikin ta ya yasar da ita tare da cikin da yayi mata , wani irin yanayi mai ƙarfi da kaifi ta ji yana keta zuciyar ta a game da shi , hannun ta ta kai ta tattaro bakin hijabin ta ta riƙe tare da cije gefen leɓen ta na ƙasa da ya zo daidai da zubowar hawayen ta da yake nuni da mummunan ƘULLACIN da tayi masa …. !!!!!!Ba ƙaramin kaɗuwa Youssouf ya yi ba lokacin da Maimartaba yake shaida masa zancen auren sa da Siyama , da har an riga an miƙa dukiyar auren ta ga mahaifin ta dake niamey , za’a yi ɗaurin auren sa da ƴan matan duk biyu a rana guda kamar yadda ya buƙata ,2

Ya jima a zaune gaban Maimartaba yana jin yadda zuciyar sa take cunkushewa da tarin takaici ,

Ba tun yau ba ya gama lura da take-taken yarinyar , shi yasa sam baya sakar mata fuska ashe bai sani ba har tayi girman da zata iya yin tsaurin ido irin haka a matsayin ta na mace ta doshi iyayen sa da buƙatar son a haɗa su aure ? Babu shakka zata ɗanɗani kuɗar ta a hannun sa , sai tayi danasanin wannan mummunan shisshigi da tayi ta kutso kan ta cikin rayuwar sa da take a hargitse a halin yanzu ,

Ganin shirun sa ya tsawaita ba tare da ya amsa da amincewar auren ba , ya sa me maimartaba yin gyaran murya

  Da fatan ba zaka bijirewa oumarnin mu ba ? Bisa ga wannan haɗi da munka yi na amre tsakanin ka da ƴar ouwar ka , saboda ba muyi haka ba face sai da munka hango tarin alkhaire tare da dacewa sannan munka so ƙulla igiyar amre a tsakankanin ku , wannan ɗiya ɗiyar ƴar uwa ta ce , kai ma kuma ƴar ouwa take gare ka , ina yi maka oumarni ka karɓi amren nan da hannu biyu da ikon Allah gaba kai zaka yi farin ciki .

Kalmar ‘Umarni, ta daƙile dukkanin wani yunƙuri da zai iya yi , domin shi ɗin me yawan biyayya ne ga iyayen sa , haɗi da sanin da yayi a yanzu shi me tarin laifuka ne , wanda yake neman wata kafa ko yaya ne da zai iya faranta ran iyayen sa ta dalilin ta, ko domin su iya masa uzuri a duk ranar da laifukan sa suka bayyana a gare su , su duba irin faranta mu su da yayi su sassauta masa hukunci ,

Cikin harhaɗa kalmomin da suke suɓcewa daga harshen sa saboda kaifin su da yake iya ji ya furta ,

Na Amince , Allah shi ƙara girma da ɗaukaka .

Da murmushi bisa fuskar sa yace

Madallah da kai , Allah shi maka Albarka , Ya Albarkaci zuri’ar ka , Allah shi yi katanga tsakanin ka da miƙiya , kana iya tafiya ka fara shiri doumin nan da sati biyu da ranar tayi dai-dai da gomma ga watan gobe ake ɗaurin amre .

Godiya yayi ya miƙe yana barin shigifar sarki , kai tsaye gidan da zai tarar da Tafeeda ya nufa ,

Cikin sa’a ya same shi dawowar sa kenan daga aiki da sanyin la’asar ,

Babu walwala a fuskar sa ya samu wajen zama bisa kujerun shan iska ,

  Ɗan ouwa ka kuwa san me ke shirin farouwa gare ni ?

Maida ganin sa yayi kan sa , bayan ya miƙa masa sassanyan lemun da ya tsiyayo masa a kofin gilashi ,

Sanar da ni ɗan ouwa

Wai amren mataye biyu a rana gouda , kuma amre tare da yarinyar nan siyama da ko ƙamnar duban ta bana yi , shin baka yi tounanin akwai wani dalili da ya sa maimartaba haɗa min amren mataye biyu a rana gouda ba ?1

    Ɗan guntun murmushi tafeeda yayi

Banda abun ka Yarima shin amren mataye biyu a rana gouda ba gata bane ?

   Ita siyama ai duk inda ake neman macen amre ta zarta ,

  Maimartaba bashi da sani kan kome wataƙila hasashe ne yayi irin nasu na manya ya sanya shi yi maka gatan amra maka mataye biyu a rana gouda ,

Juyar da kan sa gefe yayi yana jin yadda ran sa ke sake ɓaci , kan batun auren , ga kuma ya lura Tafeeda ba shi da niyyar taya shi jimami , shi ina zai kai mata har uku a shekarun nan nasa ??

   

Kurɓar lemun sa tafeeda yake yi yana satar kallon youssouf da yayi tagumi hannu biyu ya nisa cikin tunani ,

   So yake ya masa tambaya game da al’amuran sa na ƙasar nigeria , ɗiyar sa da take can , ƙaƙa ya ƙarƙare da barin ta a chan ? Hannun wa ya baro ta ? Sai dai rashin son tuno masa da ita ya sanya shi haɗiye tambayoyin sa , ga zaton sa Biyamuradi yayi amfani da shawarwarin sa , ya baro duk wasu kuskuren da ya aikata a inda ya aikata su !1

STORY CONTINUES BELOW

Farin cikin da Siyama ta tsinci kan ta cikin sa bai misaltuwa , domin duk wani da ke mu’amala ta kusa ko ta nesa da ita zai iya shaida farin cikin tare da walwalar da ke tare da ita , da ɗai bata taɓa farin ciki me yawan haka ba cikin rayuwar ta ,

   Ƙulluwar aure a tsakanin ta da Youssouf wani abu ne da tayi shekaru tana mafarkin sa a bacci ko a farke , bata taɓa zaton zata samu damar mallaƙar sa a matsayin miji a sauƙaƙe haka ba , a kuma daidai lokacin da take zaton ya sulluɓe mata zai zama malakin wata ba ita ba , duk tunanin ta na bata sai wani nisan shekaru wataƙila idan da rabo suyi aure , ga haɓakar farin cikin ta ashe tabbatuwar mafarkin ta zuwa gaske yana kurkusa , ashe tare zasu mallake shi ita da wacce take tunanin ta fita sa’a , ashe sa’ar na gare ne su biyu ,?

Bata ji ko ɗar ba akan sanin da tayi auren su auren haɗin iyaye ne , tare da sanin da take da shi akan irin tsanar da shi yake gwada mata , ta ji ta gani ta amince ta kuma shirya yin zaman aure da shi da gasken gaske , cikin kowanne irin hali , tana jin son da ita take masa zai ishe su rayuwa ita da shi ,

   Soyayyar sa ga gimbiya maimouna bata razana ta , illa kishi da ke nuƙurƙusa ran ta , dan haka ta sha alwashin ko da ƙaƙa , sai sun raba soyayyar youssouf biyu ita da maimouna kamar yadda zasu mallake shi a matsayin miji su biyu a lokaci guda , idan ya so ita na ta kason soyayyar idan ya so ya zubda a rariya , bata da damuwa son da take yi masa ya ishe su , .

Shiri take ka’in da na’in ubbo tana taya ta haiƙan , gefe guda hajiya umma na bada ta ta gudummawar a matsayin siyama na ɗiya a gare ta , ɗiyar da ta goya tayi rainon ta tun tana tsumman goyo ,

Lokacin da gnala take sanar da gimbiya maimuna dangantakar dake tsakanin youssouf da siyama har ma da zantukan da ta ji siyama na tattaunawa da  ubbo , bata wani ɗau batun da muhimmanci ba , saboda wasu dalilai nata da take ganin ko da ace zai aure su su biyun ita bata jin hakan zai dame ta , burin ta ɗaya tal , shine ta samu nasarar aiwatar da ƙudurin da zai sa ta aure shi .1

Dan haka ko da yake kame-kamen sanar da ita batun auren sa da siyamar yana bin ta da kalaman rarrashi , kwantar da murya tayi ta dunga zuba masa sassanyan rikicin da ya sake ɗaga darajar ta a idanun sa tare da sake dilmiyar da shi cikin ƙaunar ta ,

     Ya dunga jin yayi sa’ar samun nutsattsiyar mace kuma me haƙuri, wacce mace ce a zamanin yanzu da za’a yiwa kishiya gab da lokacin auren ta , a kuma haɗa su aure rana guda , ba’a yi danbarwa da ita ba ? Ƙwarai ƙwarai maimouna ta ƙara ƙima a idanun sa ,2

Samun haɗin kan ta farad ɗaya ya lafa guguwar ƙin auren a cikin ran sa , sai ya samu nutsuwar fuskantar shirye-shiryen auren tare da cigaba da zarya wajen sabon gurin aikin sa da aka tura shi Dosso , inda zai zama shugaban soji na baki ɗayan yankin na jahar Dosso ,

Tafkeken gida aka mallaka masa tare da motocin hawa biyu , ƙari da tarin hadimai sojoji tun daga kan masu gadi , direba , har zuwa kan me girki .

Tsakanin jahar Maraɗi da jahar Dosso babu tazara me yawa , dan haka lokacin da yake da samun tabbacin wajen zama a dosso , sai yayi niyyar bayan bikin su , zai dawo da gimbiya maimouna nan gidan sa na dosso , kusa da shi , ita kuwa siyama ta cigaba da zama can a maraɗi , tunda ita ta zaɓi auren cikin gida sai ta samu matabbata a cikin gidan , !

Sai dai yana sanar da hajiya umma niyyar sa , a take ya ga sauyin fuskar ta ,

     Abu guda ta ce da shi .

Kome tsanani kayi ƙoƙarin kwatanta adalci tsakankanin matayen da Allah ya baka amanar riƙon amren su , kar ka kuskura ka karkata ga ɗaya daga cikin su , saboda gujewa fushin Allah da azabar sa ka kiyaye , siyama da maimouna duk su biyun matan amren ka ne .

*****

Tun farkon satin aka fara gudanar da shagulgula da wasannin daga bangaren masarautar maraɗi har da ta Agades wanda suke da tarin wasannani da al’adun gargajiya fiye da na maraɗi , haɗi da shiri sosai da suka yi na bikin kasantuwar kowa ya san gimbiya maimouna ɗiyar gata ce ta sosai ,

STORY CONTINUES BELOW

Har zuwa yau da take ranar sakun lalle ga amare , gobe juma’a za’a ɗaura auren

Kamar yadda al’adar masarautar maraɗi take , duk lokacin da za’a yi sakun lalle ba’a yi a cikin masarauta ,

can tsibirin maraɗi ake tafiya da amayar ,”wani ƙaramin gari ne da yake ƙarƙashin jahar maraɗi da ake ƙiran sa tsibiri bashi da nisa sosai da ainahin cikin garin maraɗi ,

Gidan sarkin tsibirin nan ake sakun lallen a cikin gidan akwai wata mace da ake ƙira ,inna , wacce sunan sarautar ta ce ,inna ɗin ,” ita take sakun lalle ga amaren da duk za’a shigar ko za’a fitar daga masarautar maraɗi,

Karfe ɗaya na rana gimbiya maimouna tare da ƙanwar mahaifiyar ta da ƙanwar mahaifin ta da matar maimartaba sarkin agades ta biyu tare da wasu daga cikin matan ƴan uwa na ƙurƙusa tare da rakiyar amintattun hadiman ta mata biyu da bayu maza uku  sai kuma ƙaramar jakaɗiyar agades,  jirgin su ya iso tashar jirgin sama na maraɗi daga agades ,inda nan take motocin da suke jiran su domin kai su tsibiri suka ɗauke su kai tsaye zuwa tsibirin maradi ,

Tarɓa me cike da girmamawa aka yi musu , inda suka tarar da gidan cike da manyan mata masu sarauta na kurkusa da fada cikin su har da manyan yayun biyamuradi ,”Ammi da Dada da Asma’u da ake ƙira ma’u ƴar wajen hajiya mama ta farko . ,” da kuma ƙaramar jakadiya .

Tsakanin su bai cika awanni biyu ba siyama ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙannen maimartaba sarkin maraɗi su biyu tare da hajiya mama da ubbo sai kuma ƙannen baban ta su biyu ,

Ta ko’ina buɗa da ƙirari ne yake tashi saboda makaɗa da maroƙa da suka cika faɗar sarkin tsibiri duk da cewa an dakatar da su daga shiga cikin gidan inda aka fara shirin sakun lallen amaren

   

  Shimfiɗa ce aka yi da manyan jajayen dardumai , a tsakiyar babban ɗakin , inda aka ajiye babban tum-tum na zama a tsakiyar shimfiɗar ,

Inna tayi umarni da a shigo da siyama za’a sanya ta a lalle ,

Ko kafin bangaren gimbiya maimouna su ce kome , hajiya mama ta yunƙuro ,

  Wacce siyama kouwa ? Ai ita maimouna ita ce matar farko dan haka ita za’a fara sanyawa ga lalle ko kouwa ?

  Hakka zance yake ranki ya dade uwagijiya ta ,

  cewar ƙaramar jakadiyar Maraɗi

Aiyuriyuriyyyy ayuririyyyyyy ayyuririyyyy !!

Wata zazzaƙar guɗa ta fito daga hancin jakaɗiyar agades , saboda jin babban matsayin da uwargiyar su ta samu ,

  Taka a sannou-sannou ƴar sarki jikar sarki , matar yarima ɗan sarki surikar sarki , gaban ki salama bayan ki lafiya  farar macce fitila gida , tauraruowar ki me ƙarfi ce wacce hasken ta ya tarwatsa ya zagaya nahiya tun dagga birnin agades har yankin maraɗi , wouce gabba kin yiwa sauran mata zarra , kin yi gado ba haye kika yi ba mahaifiyar ki ai ita shugaba ta matayen agades ,

 

  A hankali ta sanya kan ta cikin ɗakin tana jin yadda ginshiri irin na sarauta yake sanya ta ƙasaita da jin faɗi.

Bayan shigar ta guda daga bangaren mahaifin ta tare da guda daga bangaren mahaifiyar ta suka rufa mata baya , ubbo ta yunƙura zata shiga hajiya mama ta dakatar da ita tare da yiwa ma’u umarni da ta bisu kamar yadda al’adar take mutum ɗaya daga bangaren dangin miji ke shiga ɗakin sakun lallen .

Bayan zaman gimbiya maimouna inna ta janye hular alkƴabbar dake bisa kan ta , baƙin gashin ta da ya sha gyara ya bayyana , inna ta sanya wata ƴar kyakkyawar kibiyar kitso ta raba gashin biyu hagu da dama ,

STORY CONTINUES BELOW

Matar da take waziriyar inna ta miƙo mata wani ƙoƙo cike fal da madara sanuwa/nono , ta karkata ƙoƙon a sannu sannu ta fara zuba madarar a daidai tsakiyar tsagun ,

A hankali kakkauran nonon ya fara kwaranya , bisa tsagun kafin ya saki layi ya tarwatse a gaba ɗayan cikin gashin maimakon ya bi kan hanyar da aka masa ƙaɗai ,

Nan take inna da waziriyar ta suka haɗa ido suna masu gƴaɗa kai a hankali , yayin da fuskar ma’u ta sauya tana bayyana ɓacin rai a sarari , har aka gama zuba nono nan haka yayi faca-faca akan fuska da jikin kayan gimbiya maimouna ,

A fusace ma’u ta juya ta fita daga ɗakin gefen mahaifiyar ta ta je ta tsugunna ta mata raɗa , nan take fuskar hajiya mama ya bayyana wani sirrantatcen murmushi , kafin tayi gyran murya tayi wa jakadiya alama da ido ,

Nan take jeka ta karkace kai ta rangaɗa ƙaƙƙarfar guɗa da ta sanya , mutanen agades samun kwanciyar hankali musamman innonin gimbiya maimouna da duk suka sha jinin jikin su , kan shirun da suka ji daga ɗakin ko dai ƴar ta su tayi kuskure ne cikin rayuwar ta ?

Amma jin buɗa daga bakin jekadiyar maraɗi ya sa hankalun su ya kwanta yayin da tasu jakadiyar ma ta karkace kai ta dunga sakin zaƙaƙan buɗoɗi ,

  Bayu mata biyu suka jawo wata ɗirkekiyar tunkiya fara sol suka ɗanka ta ga hannun matar sarkin agades ,

   Tunkiyar gimbiya maimouna ce ta sakun lalle , nan take bayun agades suka kama igiyar tunkiyar suka riƙe gam .

Ma’u ta koma ɗakin ƙarƙashin umarnin hajiya mama ta sanya farin kyalen ta share fuskar gimbiya maimouna gami da jan hular alkyabbar ta ta rufa mata akan ta ,

Suka fito daga ɗakin ,

Bayan an sauya shinfiɗa da wajen zama aka yi umarni a shiga da siyama ,

Ƙanwar mahaifin ta ɗaya tare da hajiya mama sai kuma ubbo su ne suka shiga da ita ta zauna akan tum-tum

Inna ta tsaga gashin ta , ta karbi ƙoƙon madarar ta shiga tsiyayo mata shi daga tsakiyar kan ta sannu sannu ya shiga bin layin yana gangarawa har zuwa kan siririn karan hancin ta yana ɗiga a gaban rigar ta , har nono ya ƙare bai karkace hanya ba ,

Wata ƙarƙarfa guɗa ce ta taso daga hancin inna da tayi amsa kuwwa har fada da nan take makaɗa suka ƙara ƙarfin kiɗan su da ƙirari ,

Daga waje ma bayun masarautar maraɗi suka dunga sakin buɗa ba ƙaƙƙautawa ,

Zuciyar hajiya mama tayi bakikkirin lokacin da ubbo ta sunkuya ta ɗau farin kƴallen tana gogewa siyamar madarar fuskar ta idanun su suka gauraye cikin na juna sassanyar ƙaunar da take tsakanin su tayi tasiri idanun siyama suka ciko da ƙwallar murnar ganin wannan ranar me cike da ɗinbin tarihi a wajen ta , a hankali ubbo ta kai hannun ta duk biyu ta rungumo siyamar zuwa jikin ta , a hankali ta raɗa mata a kunne4

   Madallah da ke ƙauna ta ɗiyar kirki , me daraja ,Madallah da ke mace tagari abar alfaharin iyayen ta da mijin auren ta !

Ko kusa ran hajiya mama bai yi daɗi ba da cikar budurci da alamu suka bayyana ga siyamar kamar yadda al’adar daman take nuni ne da macen da take cikakkiyar budurwa ita ce wacce nonon ke bin dai-dai tsagun layin ba tare da ya karkace ba , ta so ƙwarai ace an samu matsala irin wacce aka samu ga gimbiya maimouna ,1

domin tayi amfani da damar wajen hana yiwuwar auren siyama da youssouf wanda ta ji zancen sama ta ka babu zaton ta babu tsammani , kuma a zahiri bata ƙaunar duk wani abu na alkhairi ya raɓi youssouf ,

STORY CONTINUES BELOW

Sannan irin tashin hankalin da mommoudu ya shiga da jin zancen haɗin amre tsakanin youssouf da siyama , alhalin shi zuciyar sa ta rayu tsawon lokaci ɗauke da dakon soyayyar siyamar , meyasa kome na cigaba da samun nasarar rayuwa yana ga youssouf ba shi ba ? Meyasa maimartaba ya tattara duk wasu gata da kulawa ya bada ga youssouf alhalin ga shi , shine kuma ƙarami ?

*******

Biki aka yi na bajinta da gata , irin wanda ba’a taɓa yin makamamcin sa ba a tsakanin jahohin biyu , aka yi biki aka gama lafiya lau amare sun ka tare a gidajen su da suke cikin da’ira guda sai dai kowaccen su tana sashin ta yayin da sashin biyamuradi yake tsakiyar nasu , gini ne guda uku a tsaye ,

Daren ranar lahaɗi da aka yi wuni aka watse shine daren da farkon sa yake zaƙi ga youssouf kafin zuwan tsakiyar sa da kome ya rikiɗe ya kuma sauya ya birkice ya hautsine masa , ya sanya shi shiga ruɗani , nadama bakin ciki tare da tarin tsoro ,

Maimouna ita ce macen da ya ɗau aniyar kwada mata ƙauna da soyayya irin wacce yake da burin nunawa ga matar auren sa , hakan kuma ya fara gwada mata a tun farkon daren da yake jin tamkar ya haɗiye ta dan so ko kuwa ya buɗe cikin ƙirjin sa ya cusa ta , sai juyi da ita yake yi yana lallaɓa ta daki-daki tamkar ƙwai , kafin kome ya kankama , zuwa lokacin da zai fahimci bara gurbin ƙwan da ya ɗaukowa kan sa ya kuma ta’alaka soyayyar sa akan ta , har ma ya sallama mata duk wani so gami da yadda da ya mallaka ,

Ashe yayi kuskure ne , shin ashe ta riga ta so wanin sa kafin shi ? Har ma ta mallaka masa abu mafi daraja agare ta wato gangar jikin ta ? Ashe ita ɗin ta ha’ince shi ne ? Shin ko dai shine ya ha’inci kan sa ? Shin ko dai ayar Ubangiji ce ke tabbata akan sa ? Idan kayi zina da matar wani ? Idan kayi zina da ƴar wani ?  Idan kayi zina da ƙanwar wani ?? Uwar wani ??3

Tunanin hakan ya tsorata shi tsoro me tsanani , da ya hana tasirin fushin sa bayyana har ya nuna shi ga gimbiya maimouna da ta cigaba da yi masa lamɓo da nuna masa salo salo na gogaggun mata har da ƴan ƙananun koke koken ta , ita ciwo take ji ,1

Sai yayi wani zugum kamar soko ya sanya mata ido , ah to shi zata yi wa bariki ?? Ai ya san me ake nufi da budurci , ” amma tunaninikan da suke bijiro masa da shuɗaɗɗen laifin sa suke barazana ga nutsuwar sa saboda zuwan dodo-dodo da suke masa suna sake maimaita kan su tare da bada fassara akan halin da ya riski matar sa a ciki ,1

Hannun sa ya kai da ƙarfi ya jawo ta ya jefa kan ta kan ƙirjin sa yana jin yadda iskancin kukan da take yana sake dagula masa lissafi ,

Ɗan Allah ki min shiru

  Yace da ita , a tsawace

Da yake daman kukan gulma ne sai tayi luf kafin gajiyar biki tare da gajiyar farkon daren su danne ta bacci me matuƙar ƙarfi da daɗi ya silalo ya chafke ta ,1

A hankali ya zame ta daga jikin sa ya miƙe daga kan gadon , rigar baccin sa ya ɗauka ya saka , ya fara taku yana barin ɗakin ,

Yayi zurfi a cikin tunanin abun da ka iya je ya dawo cikin rayuwar sa , mama ita take ta kai kawo cikin ran sa , rayuwar ɗiyar sa yake hangowa , yana jin wani irin al’amari me girma wanda yake tafe da tsoro akan ta , yana son tsare ta , so yake ya boye ta kar laifin da ya aikata ya shafe ta , tsoro yake kar tarihi ya maimaita kan sa ,2

Bakin cikin da yake shaƙa kaɗai a wannan daren yayi masa yawa ma , me yafi ka san cewa matar ka tayi tarayya da wani ta hanyar zina sanya bakin ciki da ruɗani a cikin rai ??

Wani irin kishi me tsanani yake ji , wani irin yanayi yake ji akan ta , ji yake ƙimar ta na zubewa tana zagwanyewa daga ran sa tamkar narkakkiyar roba a cikin wuta , ji yake tamkar yana ƙyamar ta ,

STORY CONTINUES BELOW

,” yaya maimounatu zata min haka,”??

    Yake tambayar kan sa , yana sake maimaitawa ,

  Meyasa ? Meyasa ? Wai meyasa ?

Bai san cewa ya fito har harabar gidan ba sai da ya ji ƙaƙƙarfar iskar dake wajen tana ɗaga rigar sa da bai ɗaure maɗaurin ba , a hankali ya kai hannu ya ja igiyar yana ɗaurewa ,

Tun da ya fito idanun ta suka sauƙa a kan sa saboda daman ta gagara bacci ban da juyi babu abunda take , ita mace ce me zafin kishin abunda take so , dan haka sanin cewa da tayi yau ɗin biyamurdi zai kasance da gimbiya maimouna ya ta’azzara soyuwar ran ta , ya sa bacci gagara ɗaukar ta duk kuwa da iya satar sa ,

   Dan haka ta fito ta barandar ɗakin ta dake sama tana iya hango gaba ɗayan harabar gidan ta kurkusa daga inda take , duk kuwa da sanin da tayi dare ya raba ƙarfe 1:30am , to amma zafin kishi haɗi da bagen so ai rufe idanun me su suke yi .

  Me ya fito da shi a wannan daren ??

   Ta tambayi kan ta

Ta san shi farin sani kamar yadda duk wani motsi nasa yake kusa da zuciyar ta , take kuma iya fassara kowanne motsi nasa

Kada dai inda ya saba fita ya tafi a dai-dai wannan lokacin ya nufa ?? Wani irin tashin hankali ta ji ya taso mata ,

   Zato take ya daina ? Tunda tun bayan dawowar sa daga nigeria bata ji alamun fitar sa ba , bata kuma gan shi ya fita ba ,13

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga ya ɗaga kan sa sama tare da waiwayowa sashin da take ,

   Da sauri ta tsugunna tana ɓuya a bayan ginin gaban barandar ,

Cigaba yayi da kallon sashin nata lokacin da zuciyar sa ke kitsa masa wataƙila ita ma wannan ɗin da aka liƙa masa , ta riga ta gama sayar da nata mutuncin a waje ,

ya dangana kome da ya faru a matsayin hakkin baiwar Allah yakaka da ya ɗauka , ya jagorance ta suka aikata mummunan laifi , shi daman Alhaki ai kuikuyo ne .!1

*****

Asubar fari ya hau shiri , garin baki ɗaya yayi masa wari , so yake ya tafi , yana son zuwa ya ga mama yasan ganin fuskar ta ne kaɗai zai iya sassauta masa zafin da ran sa ke yi ,

Daga sashin sa kai tsaye cikin gida ya tasamma sashin hajiya umma ba tare da ya dubi sashin kowaccen su ba tsakanin sashin gimbiya maimouna da tun barin sa da yayi cikin dare da sashin siyama wacce bai ko kai da sanin launin kayan da suke cibge a ciki ba ,

Yana ratsa sararik gidan yana amsa gaisuwar bayu da hadiman da suke kai kawo suna gyaran gidan da sanyin safiyar .

A falo na ciki ya tadda hajiya umma tana Azkar , gefen ta ɗan ƙaramin tire ne da aka jera gorar ruwa da ƴan kofunan gilashi ,

Tana ganin sa farin ciki ya bayyana kan sa bisa fuskar ta , cikar haiba da mutuntukar da ta hango tare da shi ya sa ya yi mata ƙwarjini a yau , tabbas aure cikamakin addini ne , cikin sa akwai martaba tare da girma me yawa ,

Gaishe ta yayi sai dai saɓanin da da yake shigewa kusa da jikin ta , yau ɗin tanƙwashe kafafun sa yayi a gaba kaɗan da ita ya sunkuyar da kan sa ,

Kallon tsanaki tayi masa ba sai ya faɗa mata ba ta san yana tare da damuwa me girma wanda a jiya kafin rabuwar su da yamma babu wannan damuwar a tare da shi , dan haka take hasashen ko menene damuwar sa tana da alaƙa da iyalan sa , ita kuma bata da burin zama ɗaya daga cikin iyayen da suke bincikar rayuwar gidan auren ƴaƴan su dan haka sai ta yi kamar bata ga damuwar ta sa ba , ta matsa zuciyar ta da ke son sanin meye ya same shi ?

STORY CONTINUES BELOW

Yaya kwanan ɗiya na su dukkanin su da fatan kun tashi lafiya ? Basu da buƙatar wani abu ?

Duk kowa lafiya umma na basu buƙatar kome ,

  Umma zan tafi bakin aiki doumin an ƙira ni daga niamey bisa ga wani aiki na gouggawa da ya taso ,

Aiki ? Ba an baka houtu ba na tsawon sati gouda ?

Umma aikin mu na kare rayuka da dukiyoyin al’umma ne koyaushe ana iya ƙiran mu kuma a kowanne yanayi da lokaci , !

Shiru tayi tana nazarin sa , kafin ta jefo masa tambayar da ta sanya shi ɗago kai

Tare da siyama zaku tafi kou ?

Shiru yayi kafin ya tattaro ƙarfin halin da ya yi masa saura

     Niamey zan tafi ba dosso ba Umma , idan na dawo daga niamey zamu tafi dosso tare.

bata jaa ba tayi masa addu’o’i kamar yadda ta saba tare da ƴan nasihohi , ƙarshe ta sake tunasar da shi girman nawin da ke kan sa a yanzu , !

****

Tunda ya hau kujerar zaman sa a jirgin da zai ɗaga da shi zuwa niamey ya zurfafa cikin tunani daki-daki ,

Da hantsi ya samu isa ƙofar gidan , kan layin shiru , da yake unguwar babu yawan mutane , ya cire ƙuɗin me taxi ya biya shi , ƙarasawa yayi jikin ƙofar gidan ya ƙwanƙwasa

Hajja wacce take tsakiyar sharar ƴar harabar gidan ta saurara da kyau ta tabbatar cewa gidan nasu ake bugu , ta ajiye tsintsiyar ta ƙaraso jikin ƙofar ta tambaya wanene ??

Hajja ni ne ,

    Ta shaida muryar sa dan haka ta zare sakatar ƙofar ya samu shigowa gidan , sai fara’a take masa tana lale marhabin da shi ,

   Shiga ciki Babban soja bari na ƙarasa ture ɗan wajen nan zan zo mu gaisa , sannu ka sha doguwar tafiye ince kwana kayi a hanya ?

Murmushi yayi ba tare da ya amsa mata ba ya sanya kai cikin gidan ,

Ƙiiii

   Ƙarar turo ƙofar sa ta sanya ta ɗago kan ta ta dubi sashin da ta ji motsi ,

   Hajja sannu da aiki !

Tace cikin ƴar muryar ta ,

Bai amsa ba saboda baki ɗaya hankalin sa da idanun sa na ga fuskar mama wacce take jingine da jikin falmata akan cinyar ta  , su duk biyun suna fuskantar ,

Taku ya fara yi yana jin yadda shauƙin son ta ke ɗibar shi , da sassarfa ya ƙarasa gaban su ya tsugunna gami da kai hannun sa ya kama ƴan kafafun ta da suke sanye da ƴar safa ya sunkuyo da fuskar sa ya sumbata yana me rufe idanun sa da jin yadda ƙaunar ta ke sake ratsa shi tare da wata nutsuwa ta musamman , me yake ƙauna irin ta tsakanin ɗa da iyaye ƙarfi tare da tsafta ??.

Lokacin da ya ɗago kan sa falmata ta kawo hannunwan ta duk biyu ta ɗora akan fuskar sa , a hankali tayi yawo da hannuwan ta tana shafar fuskar sa da idanun sa ke rufe ,

Tamkar wuta ta jaa ta ta janye hannuwan ta da sauri , tana ɗauke mama ta ɗora kan kafaɗar ta ,

  Da farko tayi zaton hajja ce ta shigo, sanin cewa daga ita sai hajja a gidan .

Wa-waye ne ? Tace tana ƙoƙarin miƙewa ,

  

   Koma ki zauna Fatima ni ne ,

Ya kai hannu yana ƙoƙarin karɓar mama ,

Ta gane muryar sa dan haka ta sakar masa mama a hankali , tana dai-daita numfashin ta da firgici ya sa shi hargitsewa ,

Yana karɓar ta yayi mazauni akan ɗaya daga cikin kujerun wajen ba tare da ya janye idanun sa daga kan ta ba ya shiga sumbatar kumatu zuwa goshin ta ,

STORY CONTINUES BELOW

Bai ko ji gaisuwar da falmata wacce ta zauna daga ƙasa a gefe take yi masa ba ,

    ita ma shiru tayi ganin bai amsa ba

Shigowar hajja ya sanya shi rungume mama a jikin sa suna gaisawa shi da hajja ,

     Soja garin nan na ku kuwa ya karɓe ka , ka ga yadda kayi fes da kai kana ƙyallin fuska sai ka ce sabon ango ? Ah lalle miyar umma da zaƙi ta sa kayi shar da kai duk wannan hautsinewar sojin sun kau , ke Fatima kin kuwa gaishe da maigidan naki ??

Na gaishe shi hajja ,

To ban ga kin kawo masa ruwa ba , ?

Zata miƙe ya dakatar da ita ƙyale ta hajja ita da take da larura baza ta iya aike ba !

Ƴar dariya hajja tayi

Zata iya Babban soja ai matar ta ka ba dama akwai lura da kaifin ƙwaƙwalwa saurin gane waje ne da ita , ka ga dai ba mu rufa wata guda ba a gidan nan amma ta haddace kusan muhallin kome da kome da yake cikin gidan nan ,

ita da kan ta take zuwa ta ɗau ruwa a firiza ko ta je kitchen ta haɗa madarar mama , kullum addu’a nake mata Allah shi kawo mata waraka .

Ɗan murmushi yayi yana duban falmata wacce ta koma ta zauna ta juyar da kan ta gefe ,

Kalaman hajja sun tuno masa da abunda ya so mantawa , watau kai falmata asibiti tare da samar mata gurbin karatu ,1

Ya zama dole yayi duk wani abunda zai iya yi gurin kyautata rayuwar falmata ko domin ya samu girman laifin sa ya ragu a wajen Allah .

Hajja ku shirya zamou tafi babban hospitalisé a duba lafiyar idanun fatima yanzu. !

   To to yanzu kuwa , falmata tashi ki shirya bari nima na ɗan kintsa , !

Niamey national hospitalisé nan suka je , inda basu wani ɗau dogon lokaci ba suka ga ƙwararren  ophthalmologist , bayan haske-hasken da tarin tambayoyin da yayi mata akan idanun nata , a ɗakin gwaje-gwaje .

Suka dawo ofishin sa inda youssouf ke jiran su , bayani ya soma yi masa daki-daki

A sakamakon binciken da nayi a zahiri ban hango wata cuta ba a idanun nata sai dai raunin ƙwayar idanun nata watau ainahin jijiyoyin idanun suna da rauni , a tambayoyin da nayi mata nayi ƙoƙarin sanin tayaya ta fara samun rashin gani ko da shi aka haife ta ?  amma sai ta shaida min bata da masaniya akan mafarin samuwar rashin gsnin ta ,

A takaice cikin binciken da muka gudanar da kuma sakamakon amsoshin da ta bayar yayin yi mata gwaji da akwai yiyuwar dawowar wani kaso daga cikin ganin ta idan har za’a samu ƙwararrun kayayyakin aikin da zasu taimaka wajen dawo da ganin nata ,

Sai dai a halin yanzu bamu da waɗannan kayayyakin a nan gida niger da sauran ƙasashe masu tasowa , sai a manyan ƙasashen duniya da suka yi fice wajen samun ingantattun asibitoci masu isasssun kayayyakin aiki tare da ƙwararrun likitoci ,1

Dan haka a yanzu abunda zamu iya yi mata kaɗai shine zamu bata magungunan da zasu iya taimakawa wajen bada kariya ga idanun nata daga kamuwa da wasu cututtukan da zasu iya kassara sauran ƙarfin jijiyar idanun da kuma hana idanun yin ciwo ƙaiƙayi da zubar ruwa ,

   Da fatan kun fahimce ni ?

Mun fahimta Doctor mun goude zamu dawou gare ka idan buƙatar neman taimakou game da asibitin da ya kamata a kai ta a wata ƙasar ya tasou mun goude ƙwarai Madallah .

Washegarin ranar Biyamuradi bai zauna ba , ya shiga binciken makarantar makafi me kyau da yake son ya kai falmata ta fara karatu kafin lokacin da zai sake yunƙuri me ƙarfi akan lafiyar idanun nata a karo na biyu .

Association Nationale Pour la promotion des aveuglés , nan ne inda ya ji gamsuwar sa akan ya kai falmata nan ta fara ɗaukar darasi , wacce jibiya ce ta koyar da makafi tare da basu tallafi me tushe daga ƙasar amurka , da ta tanadi ƙwararrun malaman makafi ,

Cikin sati guda yayi mata rajista da duk wasu abubuwan da ya kamata , ya samar mata da direba bayan ya sa an kawo masa ɗaya daga cikin motocin sa da suke maradi ya danƙa makullin ga hajja wacce take cike da farin cikin wannan cigaba da falmata zata samu a rayuwa .

Ranar da zai bar garin zuwa bakin aikin sa jahar dosso , ya yi musu sayayyar kayan abinci da abubuwan da zasu iya buƙata tare da ƴar ƙaramar waya me sauƙin amfani ya ba wa hajja bayan ya zuba mata lambobin sa a wayar ya adana ta su a ta shi wayar ,

Suna zaune a falo yana musu sallama akan yau zai koma bakin aikin sa , sai kuma zuwan ƙarshen wani watan zai komo

Godiya me tarin yawa hajja ta yi masa ,

    Ya amsa tare da waiwayawa sashin falmata da take ta faman lila mama akan ɗan lilon ta wanda baban ta ya sayo mata su tarkacen kayan wasan yara iri-iri har da wanda ya fi ƙarfin shekarun ta , tun daga kan lilon yara , kekunan koyon zama har zuwa ƴar mota ta yara da ƙananun kayan wasanni irin na ƴaƴan gata na sosai  , bayan suturun da ya daɗa jibgo mata.

   Fatima baki da wata matsala kou ?

Shiru tayi tana ɗan lila mama a hankali ,

  Falmata hala kin samu kurunta ? Kina jin Babban soja na magana kin yi shiru ? Uhum yau ni naga abunda ya shallake tunani na ,4

     Babu kome kawai ina son unmh

    Uhum ina jin ki me kike so ??

A kaini makaranta

  Ai na sanya ki makaranta fatima sati me kamawa zaki fara zouwa ,!

Na islamiya ? Ina so a cigaba da koya min karatun addini ma ,!

Toh babu damouwa idan Allah ya yarda zan bincika a samu me koyar da ke na Islama ma ,

Akwai wata damouwa bayan wannan ?

Daman ka gaya musu zan dunga zuwa da mama makarantar ko ?

Babu inda zaki dunga goyon ta kina tafiya da ita anan waje na zaki dunga barin ta idan ya so kafin ki dawo na sauya ta , ko kuwa na gudu da ita,  kina nufin baza ki maida hankali kan karatun naki bane ? Zaki dunga ɗaukar ta kina zuwa da ita makaranta ki ɓige da raino memakon karatu ni ke meyasa ana nuna miki hanya kina daɗa bauɗewa ne ??2

Ɓata rai tayi ta ɗauke kai

Murmushi youssouf yayi , shi dai rigimar hajja da falmata na ba shi dariya 1

Duba fatima ki bar mama a wajen hajja har ki tai école ki dawo Kin ji kou ?  Ba’a tafiya da yara école.

Shiru tayi idanun ta na kawo ƙwalla ita dai bata ƙaunar abunda zai raba ta da mama ko na ƴan mintoci ne bare fa makaranta da awanni zata yi a can , kai anya zata iya , ?

To hajja mu dunga zuwa tare da ke mana makarantar ? Sai ki dunga riƙe min mama nayi karatun na fito ?

Ke raba ni da wannan gudun birin , gotai gotai da ni zani makarantar ? Yaushe rabon duniya da ayyaraye ?  Babu inda za ni ke kaɗai zaki tafi makarantar ki ki dawo ki same ni ina nan , ilmin ai shine Babban gatan ki falmata kin ji ko ?

Naji hajja

Yauwa mutuniyar ai shiyasa nake son ki akwai ki da saurin fahimta ,1

Sallama suka yi da youssouf yana sake yiwa hajja godiya me tarin yawa tare da ɗanka mata ƴan kuɗaɗe wanda da kyar hajjan ta yadda ta karɓa sai da yayi ta roƙon ta da Allah  .

Daga nan Dosso yayiwa tsinke bai jin marmarin zuwa maraɗi duk da cewa fiye da kaso talatin na ɓacin ran sa game da sha’anin sa da gimbiya maimouna ya kau , domin har sun yi waya ma cikin kwanaki biyun .

  

Assalamu Alaikum kowa da kowa !

Da fatan kuna lafiya ?

Ina neman afuwar ku bisa jinkirin zuwan wannan shafin , hakan ya faru ne sakamakon tafiya da ni zuwa gida , ban samu zama ba ziyarar dangi da sauran Al’amuran yau da kullum .4

Da fatan zaku cigaba da haƙuri da tsaikon da ake samu cikin ajizanci irin na ɗan Adam ?

NagodeBayan Shekaru Biyar

Lokaci baya jira sai dai a jira shi , ba’a masa shamaƙi a yayin wucewar sa , Lokaci gudu ne da shi fiye da saurin bugun zuciyar ɗan adam ,+

Lokaci yayi juyi ya juya ya zo da sauyi ta mabanbantan fuskoki a rayuwar mutane a cikin tsawon shakaru biyar .

Yakaka tana ɗaya daga cikin mutanen da suka samu sauyi ta fuska me kyau tare da tarin nasarori daki-daki cikin rayuwar ta , wanda a yau ta kawo matakin kammala makarantar ta secondry wacce ta rayu tsawon shekaru biyar tana faɗi tashin neman ilmi a cikin ta , da jajircewar ta tare da nuna ƙwazo ya sa aka ɗaga ta aka mata tsallaken aji na shekara guda daga jss3 zuwa ss2.

Da hakan ya kawo kammaluwar karatun nata cikin shekaru biyar kachal .

Ta fito da sakamako mafi kyau da ya sanyata farin ciki ita da duk wasu makusantan ta musamma malama maryam da lubna waɗanda da jajircewar su cikin taimakon yakaka a harkar ilmin ta har ta kawo wannan matsayin .

Samy baby ma wacce ta tashi daga matsayin samy baby ta koma ,Hajiya samira ,” ita ma ta taya yakaka farin cikin kammala karatun ta wanda duk wasu kuɗaɗen hidindimun karatun daga farkon sa har ƙarshen sa ya fito ne daga aljihun Alhaji Gali da har kawo yau suke liƙe a naniƙe da juna , bata da wata maraba da matar sa , kai har ma ta zarta matar sa ta aure iko da shi tare da samun kuɗaɗen hannun sa , Alhalin kuwa har yau da suke samun wajen shekaru takwas tare sun gaza yin aure .”illar bariki kenan ,!3

Karo na uku yakaka ta ajiye ƴar madaidaiciyar taɓaryar hannun ta da take dakan fura da ita , ta murza tafin hannun ta da suka yi ruwan hoda hoda saboda dakan da basu saba yin irin sa ba ,

Ta ɗago fuskar ta tana yamutsa ta ,

Ummi wallahi nagaji da dakan nan ɗan Allah ummi a min sassauci ki yadda na tafi ko’ina ne cikin garin nan na nemo furar nan nayi sadakar nan da ita , Allah bazan iya yin fura da hannu na ba ,

Malama maryam wacce take zaune daga gefe akan kujerar tsakar gida tana karatun littafin Al’mauduat Al’kubra , ta ɗan janye littafin daga fuskar ta

Fuskar ta babu alamun wasa ta ce ,

Sai fa kin daka furar nan yakaka kiyi sadaka da abunda kika sha wahala wajen samun sa yafi ɗaukaka darajar sadakar ki a wajen ubangiji , tsawon shekaru biyar kina faɗi tashin neman ilmin nan , a yanzu kin samu kin kai wata gaɓa me kauri ashe baza ki iya dakan fura kaɗai kiyi sadaka domin nuna godiya ga ubangijin ki ba ??

Jikin yakaka a sanyaye ta amsa

Zan iya ummi ,

To maza kiyi sauri ki gama dan shabiyu ta kusa , kar har a sauƙo daga juma’ah baki gama ba kin ga kamata yayi a ce ki rabar da ita ga mabaratan da suke bakin masallacin juma’ar unguwar nan kin ji ko ?

To ummi tace tana saɓar taɓaryar ta fara daka ,

Lubna wacce take zaune a gefe kusa da ita kan ƴar darduma tana yankar ƙumba , ta ɗago kan ta fuskar ta da murmushi ta sanya hannu cikin faffaɗan kwanon silver da aka ajiye guntun dafaffiyar furar da ba’a kai ga daka ta ba , ta gutsuro wata ƙatuwa ta sake jefawa cikin turmin da yakaka ke daka ,

Yauwa ƴar ummi yi maza ki daka, na ɗebo madara na fara damu ni ce ta farkon sanya Albarka a result ɗin nan kin sani ko ?

Ummi kina ganin ta fa ? Tana ƙara min wata bayan na kusa gama dakan

Lubna maza ajiye nails clipper nan ki karɓi dakan nan ki taya ta ,

Ta furta hakan tana gyara zama gilashin idanun tana cigaba da karatun ta .

Ummiii , dan Allah ni lokacin da nayi nawa dakan futar gama makarantar ta taya ni Haba ummi dan Allah,

Wallahi na taya ki kin manta ranar ….

STORY CONTINUES BELOW

Yanzu aikin samun ladan kuke yiwa haka ?

To shikenan duk ku bari ni zan zo na ƙarba nayi tunda da alamu ku lada yayi muku yawan da ya sa har kuka fara gudun sa ,

Da sauri lubna ta zaburo tana ƙoƙarin karɓe taɓaryar hannun yakaka ita kuma yakakar ta riƙe gam ta hana ta ,

Dan Allah ki bar ni na taya ki kin ji sahiba ta.

Tare da marairaice murya

Naƙi ɗin , nima zan daka kaya na duk na mulmula na ɗau abuna a kai naje na rabar , kin ji sahiba ta .

Wayar lubna da ta ɗau kiɗa ita ta raba musu gardama

Cikin sauri lubna ta ɗau wayar ta ta yi hanyar falo tana satar kallon ummi wacce bata nuna alamun ta san duk abunda suke a wajen ,

Yakaka ta bi bayan ta da kallo tana murmushi

Ta kai gaf da shiga falon ta ɗaga murya tana cewa ,

A gaishe min da yayan namu da kyau da kyau kin ji sahiba ta ?

Da gudu lubna ta ƙarasa shigewa falon tana dariyar jin kunyar ummi .

Ƙarfe biyu dai-dai da idar da sallar juma’a yakaka da lubna sun kammala ɗaura fura guda uku uku a cikin farar leda tare da kindirmo me ɗan dama shima a ƙulle a leda daban , suka haɗa su suka zuba a ƴar bakar leda daban daban , ba laifi dayawa ,

Yakaka ta jaa hijabinta saka lokacin da ta gama saka socks ɗin ta a kafa ta zura hijabin tana kallon lubna wacce take ƙoƙarin ɗaura niƙaf ɗin ta ,

Sahiba dan Allah muyi sauri kar mabuƙata su watse ,

Taku biyu tayi ta ɗauko niƙab ɗin ta ruwan madara , mahaɗin hijabin ta ta fara ƙoƙarin ɗaurawa a fuskar ta ,

Da sauri lubna ta riƙe niƙaf ɗin ,

Haba sahiba ta ? Ina mun yi cewa kin daina saka niƙab ɗin nan haka sai bayan kin yi aure ??

Hararar ta tayi

Shiyasa na ga ai kema yanzu da za ki fita babu naƙib ɗin a fuskar ki , ni dan Allah sakar min mahaɗin kwalliya ta , cikamakon martaba ta ,na sanya abuna ,1

Amma ai ni kin san dai an riga an sanya rana , babu sauran wani ɗa namiji da zai sake cewa yana so na na kula shi ,

Ok to maza yi min gorin aure sahiba ,

Ta furta hakan muryar ta babu alamun wasa .

A hankali ta sakar mata niƙab ɗin , Allah ya baki haƙuri sahiba ba manufata ba kenan . Mu tafi .

Yakaka wacce bata furta zancen da wata manufa ta daban ba daga cikin ran ta sai domin ta samu lubna ta sakar mata niƙab ɗin ta da take neman ƙarfi da yaji ta hana ta sawa a cewar ta shi yake hana samari kula yakakar tunda ba ganin fuskar ta suke ba , duk sai ta ji ta ba daɗi da ta ga kamar zancen ta ya sa aminiyar ta a damuwa .

Tafe suke akan hanyar su ta dawowa daga rabar da furar suna tafe suna hirar su hankali kwance irin ta shaƙiƙan ƙawayen da halin su da ra’ayoyin su suka zo ɗaya suke kuma ƙaunar juna domin Allah ,

Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon ,

Su biyun suka haɗa ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar ,

Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za’a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa ,

Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,

Suleiman meye hakan kake kuma ?

Yace yana kai kallon sa gare shi ,

STORY CONTINUES BELOW

Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,

Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar ,

Da sauri suleiman ya fice daga motar ,

A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya ,

Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba ,

Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da ƙwarjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taƙi amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar sa

Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,

Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su .

Dan Allah kayi hakuri,

tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu

Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama ,

Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra’ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari .

Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani .

Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya ƙafa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa’ar haɗuwa da ƙawar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta ,

na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta ,

Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi ,

A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba ,

To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha’awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba ,1

Wuce su suka yi a hankali ,

Lokacin da suleiman ke bashi amsa

Hamza kenan kai dai na rasa wanne irin tabo mace tayi maka a duniya kake musu irin wannan kuɗin goro , duk kuwa da yadda safiyya take tarairayar ka tare da lelen ka kamar wani jariri sabon haihuwa , bana jin ta taɓa saɓa maka a rayuwar zaman auren ku .2

Ya ƙarasa zancen tare da dariyar shaƙiyanci .

Murmushin takaici doctor hamza yayi ,

Baza ka taɓa ganewa ba suleiman !2

Ya maida ganin ga madubin motar sa , yana hango ta ta jikin madubin ƙwarai tafiyar ta ta ɗau hankalin sa , mace ɗaya ya taɓa gani da salon takun nan , wacce bai ko son giftawar tunanin ta cikin ran sa sai fa yau da ya sake ganin wata wacce fuskar ta take a rufe Bai kai ga ganin kamannin ta ba .

STORY CONTINUES BELOW

Yakaka ashe daman irin zaman da kike da ni kenan ??

Cewar lubna idanun ta na bayyana ɓacin rai ,

A kaikaice yakaka ta dube ta , kin ga sahiba bana ciki da rigima , daga kawai mutum …

Hmm

Lubna ta katse ta ,

Wallahi sahiba abu ɗaya zan faɗa miki a matsayin ki na wacce na ɗauka ƴar uwa ,

Kar ki yadda kiyi wasa da damar da ta zo miki , idan har wannan mutumin da gaske yake ki bashi dama ku fahimci juna , aka yi bincike bashi da wani aibu wallahi ki bada dama kuyi auren ku shekarun mu sun fara tafiya ishirin da biyu mun rufa ta da uku muke hari ,wallahi wasa ba namu bane dama kuma sau ɗaya take zuwa a rayuwa ,

Shiru yakaka tayi

Kalmar ,”Dama,” na maimaituwa a cikin kan ta , ita har tana da wata dama da ta rage mata kuwa ? Ai damar guda ɗaya da take da ita ta riga ta zo ta wuce tun a shekarun baya , ” damar da mahaluki ɗaya ya bata wanda ta tabbatar baza ta taɓa samun makamancin sa ba, bata yi amfani da damar ba a maimakon haka ma sai tayi masa mummunan sakamo da har yau idan ta tuno shi kunya tare da nadama basa ƙasa a guiwa wajen danne ta ,3

ina ma ina ma ina ma ?? Da ace dama zata dawo mata ? Da ace zai sake ba ta dama ko da gutsire daga irin damar da ya bata a baya ? Wataƙila da ta gyara kuskuren ta ta wata fuskar ,

, abunda ta sani shi ɗin ya riga ya mata nisa ita ta zama wata shuɗaɗɗɗan lamari da ya taɓa giftawa cikin rayuwar sa ,

Bata da wani shauƙi ko tunani mai armashi akan wani ɗa namiji har yau ta gaza sake son wani ɗa namiji , ” zata iya cewa ta ƙi maza ,” ƙi irin na wanda kunama ta taɓa harbin sa babu shakka idan ya ga gizo-gizo kakkaɓe shi yake , dangantakar nesa nesa ce ke tsakanin ta da maza ,

shiyasa har yau ta gaza samun saurayi ɗaya tak , ita ce bata saurarar su bata bada fuska , take boye kan ta tare da killace surar ta daidai da fuskar ta a rufe take , ta zaɓi hakan , ta kuma fi son tayi tsarayuwar ta a haka ba tare da wani ɗa namiji ya sake ratsa rayuwar ta , burin ta ɗaya ne shine tayi ilmi kuma tana godiya ga Allah tana godewa malama maryam tare da addu’ar Allah saka da alkhairi ga baki ɗayan zuri’ar ta ,

Ko da ko kusa bata sahun malumma amma kai tsaye a yau ta wuce a ƙira ta da jahila , ta nemi ilmi tana kan nema kuma zata cigaba da nema har…..

Har suka kawo gida bata cewa lubna ƙala ba ,

Sai da suka shigo gidan ta ruga da ɗan gudun ta ta rungume malama maryam wacce take tsaye daga ƙofar kitchen tana amsa sallamar su .

Ni bazan yi aure ba har sai nayi ilmi na zama kamar ummi malama ta , sai ki san yadda zaki yi da mutumin da kika ba wa phone number .

Murmushi ummi tayi ,

Anya kuwa yakaka ? Aure ai shine cikar darajar ɗiya mace

Lubna wacce take zama akan kujera ta shiga bada labari tiryan tiryan tana yi tana hararar yakaka wacce take yanka musu cabbage da zasu ci abincin rana da shi .1

Sosai malama maryam ta yiwa yakaka faɗa daga ƙarshe ta ƙarƙare da yi mata nasiha tare da faɗa mata fa’idojin aure da girman matsayin sa a addini .

Jikin yakaka yayi sanyi har idanun ta na tara ƙwalla , ta gaza cin abinci na kirki .

A ƙarshe ta jaa kunnen ta akan daga yau kar ta ƙara ƙin saurarar duk wani namijin da yake da kamala da ya nuna yana son ta , ta ƙoƙarta ta saurare shi na ɗan wani lokaci ta fahimci wanene shi , daga nan idan ta yarda da halayen sa na ƙwarai ta bashi dama ita ma tayi aure , ko kusa kar ta kawo aƙidar ƙin aure kusa da ran ta saboda wani shuɗaɗɗan dalili nata , .

A ladabce ta amsa mata da zata yi yadda ta faɗa mata .

Bata wani jima ba saboda yadda walwalar ta tayi ƙaura ta musu sallama tana barin gidan ƙarƙashin rakiyar lubna wacce duk ta damu da rashin walwalar ƙawar ta ta , sai faman jan ta da hirar raha take ,

STORY CONTINUES BELOW

Har ƙofar gida ta rako ta ,

Zata tura ƙofar gidan ta shige lubna ta riƙo hannun ta , ta waiwayo tana kallon ta da sakakkiyar fuska .

Sahiba idan baƙya son sa idan ya ƙira insha Allah zan faɗa masa dan Allah ki bar damuwa .

Murmushi yakaka tayi ,

Ni dai ban ce miki ba , kawai ….shiru tayi ,

Baza ki gane ba sahiba .

Zan gane dan Allah ki faɗa min meye ne ? Duk banji daɗi ba da naga ranki a jagule

Ni bana son kowanne ɗa namiji ilmi me zurfi nake da burin yi saboda ina da mummunan rauni a zuciyata wanda jahilci ne ya assasa min ina so na samu ilmin da zai warkar min da ciwon da na ji akan jahilci ,

A hankali lubna ta gyaɗa kai tana sakin hannun ta ,

na fahimta,

ta furta hakan ba domin ta fahimce ta da gasken ba , abunda ta daɗe da sani cewa yakaka tana da wani binannen ƙuduri wanda take dakon sa boye cikin ran ta da ita bata riga ta san wanne irin kuɗiri ne ba .

Daga cikin niƙab ta sake yin murmushi ,

Sahiba sai gobe zan zo ki bani labarin yadda kuka yi da ,”direba,”

Ta ƙarasa zancen da dariya cikin muryar ta , ko kafin lubna ta bata amsa wacce ta yamutsa fuska tare da ƙanƙance ido

Ta shige gidan da ɗan gudun ta tana jin lokacin da lubna ke cewa daɗin abun ma direban jirgin sama ne .

Da sallama ta shiga falon duk da cewa tayi ne ba domin tana sanya ran za’a amsa mata ba sai dan sanin muhimmancin sallama a musulunci da ta riga tayi .

Kamar yadda ta zata kuwa daga samira har hamshaƙiyar ƙawar ta da take haƙimce akan kujerar falon babu wanda ya amsa sallamar ta , hirar su suke cigaba da yi da take cike da shewa da dararraki irin na yaran matan da suke juya duniya a tafin hannun su .

Rage tsawo tayi ta ɗan durƙusa ,

Anty samy sannu da hutawa ,

Ke ke yaks wanne irin iskanci ne wannan ?? So nawa zan faɗa miki bana son kina shigo min gida da wannan maya-mayan yadikan da kike yawo da su a jiki , musamman ma na fuskar nan taki kamar wata korarriya daga makka ? To na faɗa miki yau ce rana ta ƙarshe .

A hankali yakaka ta kai hannu ta kunce niƙab ɗin fuskar ta , lokacin da sofi take kai ganin ta kan ta ,

Kiyi hakuri anty na cire .

To ya dai fi miki , yo Allah na tuba na sanya wannan mayanin a fuskata ai ya shaƙe min numfashi ya sheƙa da ni barzahu ban shirya ba ,1

Kallon kallo suka yi a tsakanin su , kafin sofi ta janye idanun ta tana yatsina fuskar da ya zama halittar ta ,

Kirjin yakaka yayi dakan lugude , tsawon shekaru biyar bai isa a ce ta manta fuskar sofi ba matar da ganin farko haɗuwar su ta fari ta ɗau karan tsana ta aza musu ita da ƙanwar ta falmata , dan haka cikin hanzari ta miƙe tare da haɗiye kalaman gaisuwar da tayi niyyar miƙa mata , ta juya tana nufar ɗakin ta .

Friend wannan wacece ? Aina kika samo ƴar ƙwara ? Ko dai ko dai …. Ta ƙarasa zancen tana sakin wata shashashar dariya .

Ɗan murmushi samy baby tayi cikin ran ta bata mamakin rashin gane yakaka da sofi ta yi , ko ita da kan ta bata gajiya da kallon yakaka , wata irin fata ce da ita wacce bayan haske tana ɗauke da wani irin taushi tare da ƙyalli a idanu , ya haɗu da gyara tare da jimaka me kyau da take samu daga ita samy baby , haɗi da girma tare da cikar macen da take kan ganiyar ƙuruciyar ta , sai ta zama tamkar farin wata idan ta gifta dole ta ɗau hankali , ɗan tsararren jikin ta da yake a murmure kowanne irin kaya ta sanya masa kyau yake .

Ai ba domin tirjiya da yakakar take gwada mata ba da tuni maƙudan kuɗaɗe sun fara shigo mata ta hanyar yaks , amma wani ɗan lokaci kaɗan take jira wanda zata kammala aiwatar da nufin ta , ta kuma fara kwasar adashen da ta dunga zubawa a dalilin ta ,

STORY CONTINUES BELOW

Friend wannan wata haja ce da nayi tsintuwar ta a gari ,

Kalaman samy baby suka zo daidai da zaman yakaka a bakin ɗan gadon ta , daga inda take tana iya jin muryoyin su ,

Daɗi ta ji da samy baby bata jaa dogon bayani ta sanar da sofi ko ita ɗin wacece ba .

Taɓ kina nufin wanna ƙatotuwar budurwar kika bawa mafaka a gidan ki ? Ah lalle ,

ta ƙuta

Kawai dai dan ke ma ba miji ke gare ki ba , idan ba haka ba ina ke ina kawo annoba muhallin ki ?

Ai ni tsakanina da ire-iren waɗannan matan masu kama da barbarar yanyawa ko gaisuwar kan titi babu ,

Ai ko sama da ƙasa zasu haɗu bazan bar ido irin na yarinyar nan ya gauraya da na doctor na ba ,

Wai Allah har bugun numfashi na ya fara sassarfa bala’i .3

Dariya samy baby ta kwashe da shi , daɗi na da ke freind akwai bala’in kishi ,

Sha kurumin ki sanya ranki a sassanyar inuwa tunda har kika mallaki doctor hamza a matsayin miji ke da kan ki kin san naki ne ke kaɗai mutuniyar ,

Wata sakaryar dariya sofi ta sake tare da ba wa samy hannun suka tafa .

Ni yanzu kin ƙi ki faɗa min sirrin friend wai tsakani da Allah wacce duniyar kika samu haka a Boston da har kika ajiye waɗannan manyan kayan haka ? Kin gan ki kuwa sofi cikin shekaru huɗu jal kin sauya ta jiki ,

ai wallahi wanda duk ya san ki a da da kike bulugari bazai gane ki ba a yanzu da kika koma wata katafila, ke ni anya kuwa doctor yana iya yin nisa da ke wannan irin abebaɗan more rayuwa da kika haɗa a jiki ahayye duniya gidan daɗi ɗan Allah ƙawata bani sirrin !

Kalaman samy baby na kusa da ƙarshe ya sa fara’ar fuskar sofi raguwa ,

Cikin jimami tace ,

Ai lamarin doctor ajiye shi gefe guda friend , kullum jiya iya yau ke wataran ma jiya ta fi yau ɗin domin ko yanzu kafin su kawo ni nan su ajiye baki ga yadda ya nemi min cin fuska a gaban abokin sa ba , akan sutura , wai kayan da na sa sun matse ni , bazan hau masa mota a haka ba sai dai na tafi na hau taxi shi babu abunda ya dame shi , ya dunga balbalin bala’i da daman ƙiris yake jira tun kafin mu baro US yake kumburi shi ɗaya uwa fulawar da yis yayi mata yawa, ina dai lallaɓa sa ne ,

Wallahi tsawon shekaru uku da muka yi a US da zan lissafa miki irin baƙin cikin bawan Allah nan da na ƙunsa sai kin ji tausayi na , gangar jikin sa kaɗai na mallaka , ruhin sa na wani waje wanda nake zaton ya min nisa duk kuwa ƙoƙarina akan kome nasa , ke dai kin san yadda daman aka yi auren nan namu , to duk da haka ban zauna ba malamai da bokayen yi nake na ƙarƙare miki ƙanƙat ɗin tsafi dai har india na je akan a min yadda zan yi na samu mazauni na dindin a gurin sa na amshi sararin zuciyar sa,3

Zuwa na karnataka india ne ma fa da aka min wani mugumugun aiki aka min filla filla da tunanin sa na samu yake kula ni har muke iya haɗa shimfiɗa ,

A hakan ban zauna ba kullum ni ce a gyara saƙo da lungu na jikina tare da matso kyau , rana ɗaya na lura kamar

Yana son mace me manyan kaya , saboda bin wata mata da kallo da na ga yana ta yi a gidan cin abinci a boston , na dubi matar na ga idan banda himilin cinya da ɗuwawu bata fi ni kome ba , tun daga ranar na shiga faɗi ta shi ganin yadda zan yi nima na ajiye manyan kayan nan ,

magungunan ɗago ɗuwaiwai da ƙara faɗin cinya babu irin wanda ban afa ba , amma da yake jikin nan nawa marke ne , shiru maƙatau bulunbuƙui , jiya iya yau , na kasa haƙuri na faɗa miki tare da jagorar wata ƴar * ƙawa da nayi a boston balarabiya ce ƴar duniya ta ƙarshen ƙarshe , ita ta kai ni aka min aiki me ƙanƙat ,2

aka tatso tare da ɗago tudun bayan nan da kike gani , azaba babu irin wacce ban sha ba a lokacin aikin nan da bayan gama yin sa ,

amma na shanye , kuma babu shakka ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu , domin wasu cin kashin da yake min da yawan fushin sun ragu , duk da dai da farko ya tada ɓallin sai na faɗa masa me naje nayi jikina ya koma haka ya dunga bincikata , da yake lokacin aikin nan na karnataka na kan zafin sa , zancen bai yi nisa ba ya manta ya kuma haɗu da shima yana son manyan kayan ai hajiyata shiru kike ji malam ya haɗiyi shirwa !

STORY CONTINUES BELOW

Sai dai ki ga idan na gifta yana zaune yana haka da ido ,”ta wani yi ƙasa-ƙasa da ido tana kwatance , ” yana bin abebaɗan da kallo , ni kuwa sai na sake jujjuya masa su da kyau yadda zan sake kamo sa , a raina ina “faɗin kai da abubuwan ka ai daman sakin jiki kayi ka ƙure musu kallo meye na wahalar satan kallo kamar ba naka ba ” ah to abun duniya menene ?? Sarkin fawa da kyautar ƙaho !

Wata ƙatuwar dariya me ɗauke da haniniya samy baby ta kwasa sofi tana taya , suka chafke4

Shegiya tawan baki da kyau ! Watau shi tsuntsu me wayo ta wuya ake danƙar sa ,

Charaf kuwa

Ah to ai na faɗa miki friend babu abunda bazan yi ba babu kuma inda bazan shiga ba akan soyayyar doctor buri na ɗaya , shine ya kasance nawa ni ɗaya har abada ..

Kin kuwa kamo hanyar , ko ma nace kin isa ga matakin .!

Wata dariyar suka sake saki kamar sabbin mahauk….

Yakaka wacce dararrakin su ya mugun takurawa , saboda rabo da tayi da jin hayaniya sosai ya haka da kuma kalmomin su da basu mata daɗin saurare ta sanya ƴan yatsun ta biyu ta toshe kunnuwan ta ,

hakan bai mata ba sai ta ɗauko ƴar ƙaramar wayar ta wacce samy baby ce ta saya mata tana da memory a ciki wanda yake ɗauke da ƙira’o’in Alqur’ani izifi sittin tare da wa’azizzikan manyan malamai ta jawo ear plugs ta maƙala a kunnuwan ta , ta sanya ƙira’ar AlQur’ani ta fara saurara bayan ta jingina da jikin gadon nata .

Niamey

A

ɗakin zaman marasa lafiya na musamman dake cikin national hospitalisé , mata biyu ne bisa kan ɗan gadon marasa lafiya , babbar ta jinginu da jikin sa ƙarfen gadon yayin da ƴar ƙaramar take kwance a jikin ta kan ta na bisa ƙirjin babbar dukkanin su biyu idanun su a rufe suke ,

Ɗan motsawa ƙaramar tayi tana yamutsa ƴar fuskar ta da take fayau !

Kafin ƴan daƙiƙai babbar ta buɗe nata idanun tare da tallafo ƙaramar ta miƙe zaune da ita sosai daga kishingiɗar da tayi ,

Sannu Mama , ya kike ji yanzu jiki ya daina ciwo ?

Duban fuskar maman ta tayi da raunanan idanun ta , ta kai ƴan hannuwan ta duk biyu ta ɗaura bisa fuskar mamar ta shafa tun daga goshin ta zuwa haɓar ta ,kafin cikin ƴar muryar ta me zaƙi irin ta yara masu wayo tace

Na ji sauƙi maama kin ji ko ?

Da ɗan raunannan murmushi a fusksr falmata ita ma ta sanya hannu ta shafi fuskar mama yadda tayi mata ,

Naji daɗi mama na ta ji sauƙi ,Allah ya ƙara miki rangwame tare da sassauci , me zaki ci kafin ki sha magungunam ki ? ,

Mayar da kan ta tayi ta kwantar bisa ƙirjin mamar ta ,

Maama bana cin kome , !

Idanun falmata suka kawo ruwa tana jin wani irin ciwo daga ƙasan ran ta , ƙaƙƙarfan tausayin mama kamar kullum yana sake cin ran ta , da ace tana da dama da tayi musanyan jinin jikin ta da na mama wanda ke gauraye da ƙwayoyin ciwon da a kullum yake barazana ga rayuwar ta tare da sanya ta a tsananin ciwo , to sai dai bata da dama ciwon mama muƙaddari ne daga Allah tun lokacin samuwar halittar ta .

Bai tare da cikakkiyar nutsuwa ya turo ƙofar bakin sa ɗauke da sallama , jin muryar sa ya sanya mama ɗagowa daga jikin falmata , ta waigo shi da buɗaɗɗun haƙoran ta ,

Papa !

Da sassarfa ya ƙaraso , ciɗak ya ɗaga ta tare da rungume ta tsama cikin jikin sa yana shafar lallausar sumar ƙan ta da take a tsefa an tufke mata ita a ƙeya .

A hankali yayi baya yana zama kan kujera ɗakin ya tare da ajiye ta kan ƙafafun sa ya riƙo fuskar ta da hannayen sa biyu idanun sa na bayyana tsantsar damuwa da soyayya yace mata .

désolé ma chérie comment tu te sens maintenant ? ( sannu my dear ? Me kike ji yanzu?

Je me sens mieux maintenant papa! ( naji sauƙi yanzu papa )

Ta furta hakan tana me shigar da kan ta zuwa ƙirjin sa ta kwantar da alamun rashin ƙarfi a tare da ita ,

Runtse idanun sa yayi da ƙarfi yana jin yanayin da ya gan ta a ciki na narkar da ruhin sa ,

A hankali ya ɗago kan sa yana duban sashin falmata daidai lokacin da ta kai ƴan yatsun ta tana ɗauke hawayen da ya biyo kan kumatun ta ,

Tausayin ta me ƙarfi ya taso masa ,

Fatimah ,

Ya ƙira sunan ta a ƙasan maƙoshi

Sashin da take jin tashin muryar sa ta waiga ba tare da ta amsa ba .

Meyyasa ba’a sanar da ni tashin ciwon mama ba ? Sai doctor ta ne daga nan ya ƙira ni yake sanar min ?

Muryata ƙasa-ƙasa ta ce

Hajja ce ta hana a faɗa ma tace duk shekaranjiya ka tafi daga niamey , !

Miƙewa yayi tare da ƴar sa a kafaɗa bai ce kome ba , sai da ya kai bakin ƙofa yace mata

Bari mu tai ga likitan ta !

Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin .

Kichiɓus suka yi da hajja wacce take kan hanyar dawowa ɗakin bayan ta ɗan zaga ta motsa ƙafafun ta.

Riƙe baki tayi nuna alamun mamaki !

O Ni , yanzu ashe Babban soja sai da ka taho ? Kai da shekaranjiya jiyan nan ka tafi bakin aiki ? Banda abunka ai mun riga mun saba mun kuma fahimci kan ciwon mama tana fara nuna alamun rashin lafiya da hanzari muke zowa da ita asibiti , ai da kayi zaman ka bakin aiki .

Gaishe ta yayi a ladabce

ta amsa da sakakkiyar fuska .

Babu kome hajja ai lafiyar mama ta sa’a wuce aiki muhimmanci bari mu je ga likitan ta .

Bayan dogon bayanin da kamar maimaici ne gare shi akan cutar ƴar ta sa wacce take ɗauke da ciwon Amosanin jini , ” da a turance ake ƙiran sa da Sickle Cell Anemia,

Ya ɗora da yi masa bayani akan binciken da shi youssouf ya sanya likitan ya yi masa akan wannne asibiti ne mafi kyaun kayan aiki tare da ƙwararrun likitoci da zai iya kai ƴar sa ayi mata aikin da ake sanya ran idan har anyi sa da dacewa masu cuta irin na ta kan iya warkewa baki ɗaya .

Fitaccen asibitin nan a duniya da yake ɗauke da ƙwararrun likitoci dake ƙasar amurka ,”Mayo Clinic ,” shine asibitin da likitan ya tabbatar da ƙwarewar su akan aikin dashen ɓargo ga marassa lafiyan da ya shafi manyan cutukan cikin jini .

Miƙawa likitan hannu yayi suka yi musabaha lokacin da yake miƙewa akan ƙafafun sa domin barin ofishin .

Likitan ya kai duban sa ga mama wacce tayi luf a jikin baban ta tana wasa da adon gaban rigar sa na soji .

Madame Safiyya Baskore sommes-nous bien maintenant? pas plus d’injection non?

dariya tayi kafin ta amsawa likitan dai-dai lokacin da suke ƙarasa barin ofishin ita da baban ta .

oui je me sens mieux maintenant plus d’injections .

Dariya likitan yayi yana ɗaga mata hannu alamun ! bye bye !

A hankali ta motsa laɓɓan ta tana kwantar da kan ta kan kafaɗun baban ta

au revoir ! ( Bye ) ..1

Assalamu Alaikum kowa da kowa !

Surprise ?? 😂

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *