MAFARIN SO CHAPTER 4

MAFARIN SO CHAPTER 4

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shiru-shiru ta jira bai tashi ba, miƙa ta farayi hannunta ya kusa taɓoshi da sauri ya wuntsila,

     “ke wai me kike nufi ne?”

    “oho maka! Kaji na tankaka ne?”

    Ta saka hannu kaman zata cire kayanta

    “kaa ganninan, ban saba kwanciya da kaya ba, Yauwah ina fatan dai bazaka damu ba don wani ya ɗaura maka ƙafa a barci, ehen da munshari ma, fatan bazai hanaka barci ba”

     “ke wai wacce irin magana kike? Nifa bazan sauka ba”

    “na ƙara cewa ka sauka ne? Kwanciyar dare ɗaya kam ae ba matsala bne”

    “in don kwanciyar dare ɗaya nima banda matsala donna kwana a tabarma, an bar miki gadon”

     Dariya sosai ta kama mishi, “ke meye abun dariya? Kin bani tausayi ne kawai yarnya”

    “eeh naji dai”

Ya koma saman tabarma ya kwanta, ya barta a gadon tana mishi dariya, har barci ya kwashesu.

    Har tayi barci wayarshi na a hannunta, sai dai tunda suka shiga wurin network ɗin wayar tashi ya ɗauke, hakanan ta haƙura ta kwanta tayi barci.

    Washe gari sanyin Asuba ne ya tasheta daƙyar saboda gajiya, ga kuma daɗewar da tayi bata kwanta ba, donma ta saba da tashi sallahn, saman tabarman da yake kwance ta duba babushi, a hankali ta sauka ta fita daga ɗakin, matar mai gidan ce ta gani tana ƙoƙarin hura wutar girki, ta ɗago ta kalleta,

    “barka da tashi”

       “Yauwah sannu da aiki” ta kawo buta gabanta

    “ga ruwan Alwala”

        “Na gode”

Ta amsa, tayi alwala har tayi sallah bataji ya shigo ba, gari ya fara wayewa shiru Rabi’ah bataji koda motsin Ahmad ba.

    Da taji shirun ya mata yawa, ta tashi ta fita matar gidan na wanke-wanke ta kama mata, da yake daman a gida tana taimakawa en aikinsu idan bata komai, suka gama zatayi shara shima ta amsa ta mata, Rabi’ah da bakinta bai shiru tanayi tana bata labarin bikin da sukaje da yanda sukai ta motarsu, saida suka gama sun zauna gari harya fara haske, gabanta sai fargaba yake to ina ya shiga ya barta?

    Ta kalli matar tace “waini wancan mutumin bai faɗa miki inda ya tafi ba?”

    “wanne mutumi? Mijina ne fa sarar itace ya shiga daji”

     “A’ah bashi ba, wannan saurayin da mukazo tare”

   “Awwh mijinki kenan, sanda ya tafi ina sallah gaskia”

   “na shiga uku, badai guduwa yayi ya barni a wurinnan ba”

    “guduwa kuma kaman yaya? Ba mijinki bane? Haba ya za’ae ya tafi ya barki?” sai tambayoyi take mata, ita kam Rabi’ah hankalinta a tashe, sai gashi sun hangoshi yana tafe, fararen kayannan nashi duk sun ɓaci da baƙi, fuskarta cike da masifa take kallonshi, anma ganin matarnan ya hanata magana.

      “harkin tashi kenan? Ina can wurin gyaran mota sai yanzu aka kammala, zamu wuce ko?”

   Sai sannan ta sauke ajiyar zuciyah, “bara in ɗauko mayafina”

    “zaku wuce da safennan? Kun tsaya dai ko kalaci kuyi ko, gashi mai gidan ma bai dawo ba” inji matar gidan.

     “haba ba wani abu, ae munga wuri insha Allah zamu dawo, ƙara mu isa gidan da wuri don nasan duk hankalinsu ya tashi”

    “tohm Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kaiku gida lafiya”

    “Ameen mun gde fa, Allah ya saka da Alkhairi”

    “Ameen”

  Suka kama hanya, har zuwa wurin da motarsu take, suka kama hanyar katsina, da yake cikin ƙaguwa take su isa gida ko hankalinta zai kwanta, sai tayi shiru ba taƙalen masifa, shima ya maida hankalinshi akan tuƙi.      +

   Yayanta da ko runtsawa baiyi ba a ranar, tsabar fargabar inda Rabi’ah ta shige, ya tasa ƙofa da wayarshi a gaba, ko nan da can bai zuwa don gani yake kamar yana tafiya za’azo nemanshi da maganar Rabi’ah ko kuma a mishi waya bai kusa, gidajen radio kam da duk kafafen yaɗa labarai, ga ofisoshin en sanda tun daga kano har katsina babu inda bai sa anyi sanarwa ba, gidan tunda safe harya fara cika da en uwansu ana jajantawa juna, shikam duk hankalinshi ba’a jikinshi yake ba.

    Ita dai Auntie deejah bakinta ya kasa shiru, sai maganganu take, ita da take zaune da Rabi’ah ita tasan halinta, ta fita sanda taga dama tayo kwanakinta sannan ta dawo, bata jin maganarta kullum yawo cikin gari, samari kala-kala take tarawa, su fita yawo sai dai saurayi ya ajeta, maganganu dai gasunan tanayi tana ƙara ƙirkirowa, wasu sun yarda wasu kam basu yarda Rabi’ah zatayi haka ba.Suna tafiya a hanya, Ahmad ya lura da Rabi’ah duk taa damu, fuskarta babu walwala,

“ke lafiyanki kuwa?”

“ina cikin tashin hankali, nasan Yayana dole ya damu da rashin komawa na gida jiya, anma bansan wacce irin tarba zaimun ba, bansan mezance mishi ba”

Sai daya nisa sannan yace “cikin abubuwan da suka faru jiya, akwai abunda bazaki iya faɗa ma yayanki bane?”

“A’ah”

“Yayanki ya yarda dake ba?”

“eeh”

“tohm ki faɗa mishi gaskiyar abunda ya faru, zai fahimceki”

“tohm anma don Allah zakamun abu ɗaya?”

Kallon Rabi’ah kawai yake, a ɗan lokacin daya santa, bai taɓa ganin wannan yanayin a tare da ita ba, lallai Yayanta nada muhimmanci a wurinta.

[11/6, 13:57] Rabiatu Sk Msh: “ki faɗi kawai”

“don Allah muje gidanmu a tare, ka ƙarama Yayana bayani”

“haba! Amanarki fa aka bani, ai dolene in kaiki har gida insha Allah”

Jinjina kai kawai tayi taci gaba da kallon titi, lokacin sun isa cikin garin katsina, tana mishi kwatance da sannu har ƙofar makeken gidansu.

Tunda aka buɗe gidan taga alamar da mutane gabanta ya fara faɗuwa, mai gadi na ganin itace ai ya danƙara a guje faɗama yayanta, ta fito daga motan tace Ahmad ya gyara parking ya shigo.

Kusan ƙofar shiga falon sukaci karo da Yayanta, Auntie deejah na biye dashi, kwantar da kanta tayi a kafaɗarshi ta fara kuka,

Shikam Yayan nata duk a ruɗe yake yama rasa mezaice mata, cikin tsawa Auntie deejah tace,

“Ya zaki wani fasawa mutane kuka bayan tashin hankalin da kika sakamu?”

Hannu ya saka ya dakatar da ita, “banson jin komai yanzu, share hawayenki Ƙanwatah, idan kinyi wanka kin shirya kya faɗamun abunda ya faru”

ajiyar zuciyah ta sauke, yayanta akwai sanyin hali da fahimta

“kamanya tayi wanka ta shirya? Duk hana idonka barcin da kayi badon kaji abunda ya tsaida ita bane?”

“badon inji abunda ya tsaida ita bane, don insan halin da take ciki”

Wani ƙanin babansu ne da yake cikin garin yace “bai yiwuwa, ƙara dai ta faɗa mana inda ta kwana”

Gabanta ya ƙara faɗuwa, anma da yake ta yarda da gaskiyarta, ta buɗe baki ta fara musu bayani.

“lokacin da mukayi waya na taho, to a hanyane motan ta lalace”

Cikin tashin hankali yayan nata yace “motah ta lalace miki cikin dare? Ya kikayi kenan? Ina motar taki?”

“ba’a motatah bane, bani kaɗai bace”

“keda wayene?”

“nida shine”

Ta nuna Ahmad da ke dai-dai shigowa, kowa ɗakin tsit yayi saboda wutan data ɗauke musu.

Sai Aunty deejah dake ta faman tafa hannu,

“Alhamdulillahi, yau dai gashi gaskiyata ta fita a gaban kowa”

Girgiza kai kawai yake cikin jimami, “da motanki kika fita a gidannan, anma bada motanki kika dawo ba, kuma ta lalace muku a hanya ke dashi, a tare kuka kwana kenan?”

“eeh Yayana, anma….”

Kafin ta ƙarasa ya kwasheta da wani wawan mari, da sauri ta saka hannu ta dafe, tana taɓo kunnanta da take tunanin ya faɗa ciki🤣.

Idanunshi jawur yake kallanta, ya tafi kaman zai faɗi da sauri ya riƙe kujera, juyawa yayi zai bar falon.

“don Allah Yaya kayi haƙuri ka saurareni”

“ba yanzu ba Rabi’ah, na saurari duk abunda nakeson ji daga gareki, kin riga da kin shafe duk wata yarda dake tsakaninmu”

Zaro idanu tayi tana kallonshi, “ƙwarai ma kuwa, kinci amanata, kin cuci kanki, Allah ya gani tun tasowarki nake ƙoƙarin kare miki mutuncinki, duk wani gata na duniya na nuna miki shi, na soki fiye da yaran dana haifa, na fifita soyayyarki fiye da yanda nake son kaina, da abunda zaki sakamun kenan?”

Kuka kawai take tana girgiza kai, ta rasa kalmomin da zatayi amfani dasu wurin kare kanta, ga Ahmad tsaye sai zufa yake ko kaɗan bai ɗauka Al’amarin zaiyi zafi haka ba.

“ji yanda kika tsayamun a wuri, Rabi’a wa kike tunani zai kalleki a wannan abun da kika aikata ya aureki? Wazai auri macen data kwana da wani namijin a waje?”

“ni zan auri Rabi’ah”

Gaba ɗaya kallo saiya koma kan Ahmad da baisan sanda ya furta hakan ba, kallonshi yayan nata yake da rinannun idanunshi ko ƙiftawa baiyi.

Ahmad yaɗan fara inda-inda, “ina nufin idan ka amince, zanso ka bani auren Rabi’ah”

Ba tare da wani shawara ba Yayan nata yace “ka shirya nan da sati ɗaya” ya miƙe yabar falon ko kallon Rabi’ah baiyi ba da zuciyarta ta kusa bugawa.

Alhamdulillahi

Kuci gaba da haƙuri damu dai masoya, karkuji shirun yayi yawa, shiyasa zamu ɗan dakata anan, insha Allah zakujimu a cigaban MAFARINSO, wanda muka canja ma suna zuwa MATAR AHMAD, ku kasance damu a ranar farko ta sabuwar shekara donjin cigaban wannan labari.

Akwai fa rikici da yawa a gaba.

Shin Rabi’ah zata amince da Auren Ahmad? Ahmad yanason Rabi’ah kuwa? Ya rayuwar aurensu zai kasance idan kuka tuna kullum cikin faɗa suke? Gaskia zata fito kuwa? Shin wanene Ahmad ma? Ina fatan dai baku manta da labarin Abdullahi ba…. Domin jin amsoshin tambayoyinnan saiku kasance damu a cikin littafin MATAR AHMADJitayi zuciyarta  ta tsaya cak ta daina aiki na wani lokaci tukun taci gaba da bugawa, ji take maganarsa ba kunnenta kadai ya tsaya ba har cikin  zuciyarta takejin komai sakamakon ɗacin kalmar da yayanta ya kusantata da ita, kuka ta saka mai cin rai meke shirin faru da ni cikin tashin hankali da firgici ta matso kusa da kanin mahaifinsu  so take ya karyata mata abunda taji yayanta ya furta yazama ba gaskiya bane.+

     Ƙanin mahaifinsu ya numfasa sannan  yace “Rabia sai dai kiyi hakuri  da hukuncin da yayanki ya yanke akanki hakan shi kadai ne mafita a gareki”    

    tace, “dan Allah Kawu kasa baki kar amin auren nan bazan iya juran halin da zan shiga ba”

    Yayi shiru  yakasa cewa komai, ta juya saitin da yayanta ke tsaye ta zuba masa Ido tana kallonsa yayin da hawaye idanunta suka cigaba da zuba  duk wani kuzari da karfin jiki babu shi atattare da ita baya ga tashin hankali,  ji take  kamar ba ita bace   hakika ta aikata laifi Mafi girma ga yayanta abin sonta   shikenan tata ta ƙare da sauri taje ta durkusa a gaban yayanta takamo kafafunsa gam tarike,

    “dan girman Allah yaya kayi hakuri kayafemin kada ka aura dani gawani, wani ma wanda baka sani ba, nasan nayi kuskure”

     Tana kuka tana bashi hakuri tasoma tunanin wannan mutumin dake tsaye a gabanta anya kuwa yayanta ne mai sonta da son farin cikinta, mai damuwa da damuwarta.

    Tun tasowarta Yayanta bai taɓa barin tayi maraici ba, anma sai yaune takejin mutuwar iyayenta sabuwa, lallai da iyayenta suna raye bazasu yanke hukuncinnan a kanta ba, saboda tayi yaƙinin cewa sunfi kowa yarda da yaransu, sai yanzu tasoma fahimtar bata isa tasa Yayanta zame mata tamkar iyayenta data rasa ba,

  Aunty deejah dake tsaye a gefe daya har yanzu bakinta baiyi shiru ba.

    “ai gara ai miki auren ma kowa ya huta nasha, ai daa da nake faɗa maka abunda take ƙin yarda kayi, sai ka maida maganata banza  gashinan har kwana awajen ta soma tana neman jamana abun kunya…” Ai bata kai kaga karasa maganar taba ,da hannushi ya dakatar da ita cikin zafin rai da kunar zuciya.

   Yace, “ya isa haka ban sonji komai daga gareki,  dame kike son naji”.

   ya dago idanunshi da suka gama rikiɗewa tsabar tashin hankali dayake ciki  har yanzu Rabi’ah adurƙushe take agabansa

    “dan Allah Yayana ka yarda dani ba abunda kake tunanin bane ya tsaidani” kuka take tana girgiza masa kai tarasa kalmomin dazatayi amfani dasu wurin Kare kanta,   

    Kamar zararra ta miƙe zumbur cikin zafin nama takamo hannun Ahmad dake tsaye har yanzu sai zufa yakeyi bai dauka al’amarin zai yi zafi haka ba,

     tace, “dan Allah Ahmad  kafaɗawa Yayana gaskiya babu wani abu daya shiga tsakinmu”. Tsaye Ahmad  yake yakasa ko motsi gaba ɗaya duniya ta cukuɗemasa waje ɗaya bai taba sanin haka tashin hankali irin wannan dayake ciki yake da ciwo ba, ya ɗauka Mafi sauki agareshi bai wuce ya aureta ba akan zargin da Yayanta yake musu ba, tunani yayi muddin ya tafi  yabarta cikin zargi nan zai Yi wuya tasamu mai auran ta  kuma zai kasance   shine sanadin bata mata suna da shiga tsakaninta da yayanta, aurenta shi kaɗai ne mafita agaresu,

    Girgizashi tayi “kayi shiru ka buɗe baki ka musu bayani mana ko baka magana ne”    Gaba ɗaya sai Kalo yakoma kan Ahmad  falon ya dauki shiru bakajin  komai sai sautin  shessheƙan kukunta .

Ƙanin mahaifinsu ne yasake magana yace, “kai yaro kana iya tafiya abunka inyaso daga baya katuro mana magabatanka”

    Ahmad yayi shiru ya kuma shiga wani  tashin hankali dan shi kansa yasoma danasanin dan bai san mai zai cewa mahaifiyarsa da danginsa ba, daƙyar ya iya buɗe baki cikin sanyin jiki yace

     “Iyayenah nesa suke, bikin abokina nazo, yanzu haka basu ƙasarnan sai nan da sati ɗayan zasu dawo”

   Yayan Rabi’ah ya tsaya kam yana  sake dubansa yana mai Kare masa kallon tsab, tabbas babu alaman ƙarya a tare dashi, hakanan yaji hankalinsa da Ahmad,

    Yace, “koma  ƴan inane tunda ka amince da aurenta, nizan bakata ita kuje can kuƙarata”, ai kuwa rabiatu ta saki hannun Ahmad  ta sake durƙushewa agaban Yayanta ta fashe da wani sabon kuka mai ban tausayi, tausayinta ne ya kama Yayanta Amman ba yadda ya iya aurar da ita  kadai ne kwanciyar hankalinsa, ya zare kafafunsa daga jikinta ya juya yabar falon cike da tausayin kanwarsa yasa hannu yana goge hawayen da suke kokarin zubo masa.

Dadi da farinciki ne ya taru ya mamaye zuciyar Aunty deejah murmushin ne  ya nemi kufce mata dan tsabar  murna, koba komai zata rabu da qaya ta huta babu boka ba Malam, cikin sanyin jiki shima Ahmad ya juya ya soma tafiya yanajin  tashin hankalinsa nasake nunkuwa, motarsa yashiga yabar gida kai tsaye masaukin sa ya nufa .1

Mikewa tayi itama cikin sanyi jiki ta nufi dakinta ta faɗa kan makeken gadonta Ta saki wani kuka mai ban tausayi. Wani irin tausayin kanta takejin yana shigarta, zuciyarta kebata shawara ba kuka yakamata ki tsaya yi ba  mafuta yaka mata kinemo.

     Da misalin karfe tara na dare tana kwance a dakinta taji kira yashigo wayarta wanda kusan tun 3hours da suka wuce take Jin wayarta na kara Amma rashin kuzari ya hanata dauka  hannu tasa tajawo wayar tamanna a kunne ba tare da duba screen ɗin ba, saukar sautin  muryarsa taji tayi shiru yayinda zuciyarta ke dukawa da sauri da sauri       

    “ke dai wallahi kin cika matsala gashinan nima kin gogamin”

    tashi tayi zaune tace, “ai kaine mugun ɗan matsala, tunda na haɗu dakai nake ganin tashin hankali a rayuwatah, gashi nan kashiga tsakanina da ɗan uwana”

    “dan Allah kimin shiru dan halinki ne yawo ko bakiji abinda matar yayanki tace ba zaki rainawa mutane hankali”  

   Kasa maida mishi tayi, sai shessheƙar kukan data fara,

    “kuka ma zakiyi  dan zan taimaka miki  sai ma nafasa auran”,

    “to kafasa mana sai me  ce maka akayi narasa masu sona ne”,  hawaye ne ke silalowa daga idanunta yana jiyo sautin kukanta ya  ja tsaki haɗe da kashe wayar gaba ɗaya ya cilli da ita yasa hannushi  yayi brushing din kansa dashi  kaiwa da kawo yashiga Yi yarasa meke masa dadi  shida yasan ba sonta yakeyi ba taimaka mata kawai zaiyi  .

   Kwance yake akan gado hannuwansa rungume da filo idanunshi ƙyam akan celling dakin sosai yayi zurfi cikin tunanin wayar sa dake ƙara ce tadawo da shi daga duniyar tunanin daya Lula  ɗauka yayi ya duba ganin sunan dake jikin screen din ne yasa shi ya Mike da sauri ya zubawa wayar Ido, kiran ya amsa sannan ya saita wayar a kunnenshi haɗe da yin sallama  bayan sun gaisa  cikin zafi Ake tambayar sa daga dayan ɓangaren . 

   “wai yaushe zaka dawo ne kaje kayi zamanka shiyasa ban so zuwanka katsina ba”

    Cikin kwantar da murya yace “kiyi hakuri ummi wani sati zan dawo tayi Jim sannan tace shikenan Allah ya nuna mana”

       “Ameen”A cikin sati dayan nan kallo daya zaka mata kasan tana cikin tashin hankali da firgici, ta fige, tayi baki, ta rame  bazaka taba tunanin wannan kyakkyawan yarinyar  bace  mai taƙama da ji da kai bace, ko abinci bata ci sai dan ruwa Lipton  shima sai kanwar mahaifiyarsu Aunty zee ta matsa, wanka ma dai tanayi ne dan baza ta iya zama da kazanta ba kasancewarta mai tsananin tsafta da kyankyami, banda kuka babu abunda tasa agaba yayin da shima Ahmad yasa ta gaba da  baƙaƙen kalmominsa masu sake tarwatsa mata zuciya.

      Tayi kuka kamar ranta zai fita tayi datasanin zuwanta Kano  kai amarya  da  yanzu tana zaune cikin farinciki da kwanciyar hankali da yayanta.+

     Dangi gaba ɗaya sun hallara sakamakon shirye shiryen da za’ayi  kamar dai yadda yayanta ya furta cikin satin dayan daya shirya aura da ita  ga Ahmad ɗin.

     An ɗaura auran Rabia da Ahmad tare da jagorancin wani ƙanin mahaifinsa batare da  sanin iyayensa ba, tsayawa Yi muku bayanin yadda daurin auran yakasance zan iya cika pages din nan  batare dana gama ba.

Duk wani tashin hankali da’ake labarinsa Ahmad yashiga fiyye da haka  kallo daya zaka masa kasan baya cikin natsuwarsa tsabar karfin hali ne kawai da mazantaka irin nashi, gefe ɗaya Kuma abokinsa Abba  wanda sanadinsa ne yazo katsina ke ƙoƙarin kwantar masa da hankali da bashi baki  akan yayi hakuri komai muƙaddari ne, haka Allah ya rubuto  ….

    Allah sarki rabia iya ƙoƙarin tayi wurin ganin tabawa yayanta hakuri akan afasa auren nan Amman hakan yaci tura  ta ɓangaren Ahmad ma bawani nasara tasamu ba saboda sanin mahimmanci kaifin magana ɗaya da yayi wa Yayanta akan zai aureta bancin haka shima yana Jin kamar ya saba alkwarin da yayi, wani lokacin takan bashi tausayi har ma ya tsaya rarrashinta wanin sa’in Kuma idanta dameshi da maganar buɗe mata wuta yakeyi haɗe da   gurza mata rashin mutunci, dan gani yake duk ita ta jefa su cikin wannan matsalar….

Washegari ɗaurin auren kwance take a gado yayin da sauran kawayenta ke gefe a zaune suna hira Aunty deejah ce ta shigo da sallama, su zahra  suka gaishe ta ta amsa musu a ya tsune

   tace, “ita wannan har yanzu tananan a kwance”   zahra tace,  “wlh Aunty taki sakin ranta na rasa meyasa Rabia takeyin haka”

    Aunty tace, “sai kitashi ai ga mijinki can yazo, kisa meshi a falon baki yanzu”   

   ko motsawa batayi ba daga inda take bare asa ran zata Miƙe, Aunty tace,  

  “ke bansan iskanci ki tashi kiwuce ko sai kin nuna nasa rashin tarbiyar taki, da kika sabawa mutane.

    Rabia cikin kuka tace” zanje anjima yanzu yayyafi akeyi, a bari ruwan ya tsaya”, 

   Wata ƙanwar mahaifiyarsu dake  tsaye shigowarta kenan

  tace “A’a tashi kawai kije ga lemarki can, ki kibi da ƙofar falo”

      A falon baki ta samesu shida Abokinsa Abba har Aunty zee tasa  ankawo musu abinciccika, tun shigowarta ya kafeta da Manyan idanunshi wanda ya rufe da bakin glass yana jijiga kafarsa daya baza kace ita yake kallo ba.

    Ƙafafuwanta ne suka shiga harɗewa tsabar rikicewa da tayi, sai da Zahra taɗan kamota har ta zauna  idanunshi na kanta jiyayi an take masa kafa yaɗan juyo suka haɗa Ido da Abba, Abba  yace, “kallon ya isa haka kai da za’a kai mawa gidanka” ya waske yana jan tsaki, 

    Zahra ta  zaunar da ita kusa dashi  cikin sanyin jiki  ta zauna ta rasa meke mata dadi  gaba ɗaya yau tazo mata da abubuwa dayawa  masu wuyar mantawa da rikitar da zuciyar dan Adam Abubuwa da yawa bata taɓa tsammanin faruwarsu akanta ba sai gashi tashi daya ta tsinci kanta ciki wai ita yau akama auran rashin galihu, auren ma da mutumin da tafi tsana a rayuwar ta , gaba ɗaya falon ya garwaye da  ƙamshin turarensa kawai ta tsinci  kanta da faduwar gaba.

Tsabar Haushi da takaici ne ya kamashi ganin ta shigo ko kallon Inda yake batayi ba bare  yasamu  matsayin agaishe shi yace,    

    “ke….” cikin kwasasshiyar murya yadda yakirata din yasa zuciyarta dokawa sannan ranta yayi  mugun baci    ta ɗan  juyo da niyar ta saci kallonsa aiko idanunsu suka haɗu waje daya Ido  cikin Ido suke kallon juna  sannan ya dauke kansa yace

   “ke…bada ke ake magana ba kinajin mutane kin wani tsareni da idanu” Ta dago suka sake haɗa Ido wannan karan harara taa zabga masa

    tace, “ni ba ‘ke’ bace, kamar bakasan sunan mutum ba zaka wani kirani da ke”. haɗe da murguɗa masa baki,

    yace, ‘ok ni kike murguɗawa baki zaki gane baki da wayo ne bari kishigo hannuna” cikin tsiwa tace

“in na shigo hannunka dan Allah kar kabarni da rayuwata ka kashe kowa ma  ya huta” ya  tsareta da kyawawan idanunshi..

    ya sake cewa “Ahmad bai yarda ki sake zuwa ko ina ba, koda kuwa compound ɗin gidannan ne”

    Ta kalleshi kamar zatayi kuka tace “harda makaranta?”

    yace “Eh har da karatun ai tsakanin yau da gobe ne kawai za’a kawo min ke”

   Ta soma kuka sosai ” kenan ba abun zanyi”. taji wani tsoronsa ya soma shiga jikinta, gaba ɗaya ya canza daga Ahmad ɗin data sani zuwa wani daban,

   Ganin kukan da takeyi yasa ya kira sunanta  tayi banza dashi,

    yace, “menene shirinki daga yau zuwa gobe da ba zai kammalu ba, dan ban San tafiyar ta wuce yau ko gobe?”

   Tayi shiru taƙi magana taci gaba da kukanta,

    “kuka ma zakiyima mutane, ok keep on crying, idan kukan shi zai sa na barki”

    tayi sauri tace “nidai dan Allah kabarni zuwa sati”

  Ya zuba mata idanunshi yana kallon tsukeken bakinta  ya bukaci sanin mezatayi har sati daya.   Aciki ta amsa tace,

    “bansani ba Kuma wlh karka sake tambayata abunda zanyi”

   Yadda tayi maganar ne  ta sashi dariya, yayi murmushi,

   Abba ne ya kira sunan Zahra “shirinku daga yau zuwa gobe bazai kammalu ba kuma dai kunji  maganar da Ango yayi, yanaso yaga amaryarshi zuwa gobe”

    tace, “ku daiyi haƙuri ko kwana uku ne abamu kunga  bamuyi wani shiri ba, kunga dai yadda auren yazo”

   “me zakuyi” Abba ya bukaci sani,  Ahmad yace, “A’a basu kwana uku in har bbu wulakancin a ciki lamarin ,in kuwa naga dashi to wlh  bazan lamunta ba”

   Zahra tayi saurin cewa babu wulakancin da za’ayi, suka tashi har Rabi’ah zatabi bayan Zahra ta tsinkayi  muryarsa, “kindai ji abunda nace kar naga ƙafarki awaje”

    Ta juyo tana watsa masa harara “in anki fa”   

    “Zakiyi bayanine yarinya”

    “dan Allah ni malam dakatamin karka takuramin katakurawa rayuwata aurena kayi ba siyana kayi ba, sai wani iko kake nunamun kaman baiwarka”,

   Yayi murmushi, “ina so kizama baiwa ta dolenki ki zama, ko yanzu in ankaiki gidana zaman bauta zakiyi”.

   wasu hawayen ne suka sake zuba mata tace “ta Allah ba taka ba mugu kawai, Allah zai sakamun”   

   Ta ƙara sauri ya Miƙe zai bita, Abba ya riƙoshi “haba Aboki ya kamata ka sassauta mata haka ka kyale yarinyar”

    yace, ai kai kurma ne bakaji abinda tace min  ba”

   “kaine ka soma tsokanarta, irin taku salon  soyayyarnan ta daɗe tana birgeni” ya Miƙe yana ya jan tsaki haɗe makawa Abba harara,

   “Kai kasani sarai banda lokacin yin soyayya balle har naso wannan abar, get up dan Allah ni malam tashi kar ka batamin lokaci”

Yola shine garinsu Ahmad,  gaskiya Ahmad mai yan’uwane sannan kusan su a kammale suke a unguwa ɗata wato estate.   Ko kaɗan baiyi gangancin yin unguwarsu da ita ba, tun farko daman shi ba maison zama unguwar bane, don haka can ya fita yayi gininshi wani unguwar daban, a can suka wuce dasu Rabi’ah.

   Tun daga harabar gidan suka saki baki suna kallon daular duniya duk da dare ne hakan bai hasu ganin tsabar kyaun wurin ba an zagaye gidan da wasu fitilu masu matukar kyaun gaske, Allah sarki rabiatu duk sai taji ta Raina kanta da kyawun gidan yayanta duk haduwarshi datake gani.

   uhmmmm cikin gidan kuwa ba a magana komai na cikin gidan abun kallo ne abinci mai rai da motsi aka kawo musu.

   Tana daga inda take  kwance can ƙarshen gado ta juya musu baya duk wani  tarin jindadin data hango acikin gidan, hakan bai sa taji tanason zama da Ahmad ba,

   Aunty zee tace “wai ni ke bazaki ci abincin bane?” tace “Eh” ba tare data juyo ba,

   “saboda me bazakici ba bayan duk wunin yau banga abunda kika sawa cikinki ba”

   Cikin muryar kuka tace “na koshi” ta zauna kusa da ita tana mai  ɗaura kan rabia a saman cinyarta tana Jin yadda kukanta kesata Jin wani iri, tace “zuwa yanzu ya kamata ace kinyi hakuri kindaina kukan nan haka, kuka ba maganin da zai miki” Gwaggo data ɗaga robar holandia tasha ta ajiye ta kankance idanuwa  tace, ‘kema biye mata zakiyi kar Allah yasa taci cikinta ko naki yarinyar sai taurin kan tsiya, kima godewa Allah day  yabaki wannan  gatan ya jihoki cikin daula fiye da wadda kika baro, ke dan Allah ma na sonki ai abunda kika aikata ko sadaka aka bada ke….da Kyar za’a samu mai amsarki ja’ira kawai”

   ta gaji da sauraron banzayen  baƙaƙen maganganun gwaggo, masu ƙona mata zuciya, miƙewa tayi cikin sanyin jiki tashige toile can taci gaba da kukanta har sai data tadaina Jin motsin su alamun sunyi bacci sannan tayi wanka  ta fito.

  

   Tana kwanciya wayarta ta fara ƙaran sauti mai dadi batare data duba screen ɗin wayar ba, ta dauka  shiru tayi, taƙiyin magana.

   Cikin sanyayyiyar muryar shi yace “kinyi  bacci ko har yanzu kukan murna kikeyi an kawo gidan Ahmad”

   “meye damuwarka da kukana”

   “Babu, karamar mara kunya”

    “to meyasa ma ka kirani?”

   ya ɗaga kafaɗansa kamar tana ganinsa,

    “kawai zan so ki kwanta ki daina tunanin nawa ne dan haka kiyi bacci ai kin rigada kin zamemun ƙarfen ƙafa ya zanyi dake?”

   yayi ƙasa da murya  “ni Ahmadd tawa ta same ni daga taimako an maƙalamin ke” ya ƙarasa ciki Sanyin murya,

   “gashi duk kin rusamin budget dina dan haka kibini ahankali”

   wani irin haushi ya mamayeta  ji tayi kamar tasa ihu.

   yace,  “yarinya naji kinyi shiru ko kin fara nadama ne?”

    ta sauke nannauyen ajiyer zuciya sannan ta numfashi tamkar mai Asma “idan wannan  dalilin yasa ka kirani kasani bbu wuri a zuciyata dazan sakaka  har na tsaya yin banzan tunani akanka”  

  Yayi ƙasa da murya  yace, “karya kikeyi yarinya dolenki kiyi tunanina, nadai kirane naji ya ciwon kan naki”

    tace “ai tunda ka kirani ya dawo”

    dariya tabashi  ya ɗanyi  murmushi ya kamo lip’s ɗinshi ya soma tsotsa  sai da yaji tana niyyar ajiye wayar sannan yace, “kigama duk iskanci ki zakizo hannuna ne”

   tayi shru  ba tare da tasake magana ba ta ajiye wayar tana taɓe baki.

Ajiyar zuciya ya sauke yana mai lumshe idanunshi sannan ya mike ya shiga bathroom……Washe gari sun daɗe basu farka ba, saboda gajiyan tafiya.

    Kaman yanda ta saba, toilet ta shiga tayi brush sannan tayo wanka, ɗaya daga cikin towel ɗin data gani ta ɗaura a jikinta, sannan ta yafa wani a haka ta fito.

    Gwaggo na zaune tana breakfast ɗin daya aiko musu dashi, ta kalleta yanda idanunta suka kumbura saboda kuka, ta taɓe baki.

      “indai kukane kyayishi kya gaji…” bata ƙarasa ba saboda ƙwarewan da tayi, duk da halin da Rabi’ah take ciki sai da dariya taso kubce mata.

     Mai kawai ta shafa, sannan ta fara neman kayanta ta canja, sai dai me? Ta manta batazo da kaya ba ko ɗaya, a zuwan ita bazata zauna ba, gashi kuma bazata iya

maida kayan data saka ba.+

   Aunty zee tace “keda bakizo da kaya ba, wanne zaki saka kenan?”

      “wallahi nima ban sani ba Auntie, ban ɗauka da gaske kawoni zakuyi ba”

     “in bamu kawoki ba a can zamuyita zama dake? Nina rasa irin wannan aure da ko lefe bai miki ba” Gwaggo ta katse musu maganar da suke.

     Kwantar da kanta tayi a cinyar Aunty Zee saboda kukan da yaso ƙwace mata,

      “ban sonshi Auntie, wallahi banson aurennan, don Allah ki taimakeni karku tafi ku barni a gidannan, please Auntie”……

     Hannu tasa tana bubbuga bayanta alaman rarrashi,

    “subhanallahi! Keda kanki kike roƙona da in raba aure? Kima daina wannan maganar, ke ba yarinya bace, da iliminki kinsan duk wani hukunce-hukunce akan aure, ki kwantar da hankalinki  ,kima mijinki biyayya”

   Ɗauke kanta tayi daga saman Auntie Zee, ta koma can gefe taci gaba da kukanta, tunda bata ga alaman zata samu mafita daga gareta ba.

“kukannan bazai miki maganin komai ba, ki tashi ki shirya kafin ya shigo, gidansu zamuje dake kaman yanda akeyi”

        “ni babu inda zanje”

   “haka zaki zauna da ɗaurin ƙirji kenan?”

     “inajin na manto kayana a gida”

     “A’ah da idona naga sanda Deejah ke sako miki su” Aunty zee, ta tashi dubawa, anma sun duba duk jikkunan kayan da sukazo dasu babu na Rabi’ah. Sai dai hijab ɗinta ta bata aro ta saka, don kayanta  bazasu mata ba.

A ɓangaren Ahmad kuwa, yana tashi yayi wanka da break fast, sashen mahaifiyarshi ya fara shiga ya gaisheta. Tana zaune cikin ƙayataccen falonta ta kishingiɗa a saman kujera.

    Tun daga yanayin data hangoshi tasan bai cikin walwala, gaisheta yayi cikin yanayin fara’ar da yake ƙaƙarowa, sannan ta mishi barka da zuwa cikin kulawa.

    Jin shiru baice mata komai ba, ta sake kallonshi, “Ya na ganka wani iri, meke damunka?”

     “ba komai Ummi, me kika gani?”

     “yanayinka gaba ɗaya ya canja mana, komai naka da alamun damuwa a tattare dakai”

      “gani kusa da Umminah mezai dameni? Kawai dai yanayin tafiyarne”

    Murmushi tayi saboda jin daɗin maganarshi da tayi, anma duk da haka bata gamsu da bayaninshi ba, Addu’ah kawai ta mishi a ranta, ‘Allah ya yaye mishi koma menene’..

Daga ɗakin Umminshi, saiya shiga ɗakin kishiyar mamanshi Hajia ladidi itace ta biyu ya daɗe yana jira kafin en aikinta su mishi iso, gaisawa kawai sukai ya fita zuwa ɗakin Aunty Zaliha itace ta Uku kuma Amarya.

     Sallama yayi a falon, babu kowa, yana niyyar neman wurin zama yaji an riƙoshi ta baya, juyawa yayi yana kallonta ta sakar mishi murmushi, (Khadijah ce, ɗiyar Yayar Auntynshi, kuma yarinyar da aka musu baiko da ita) sakin baki yayi yana kallonta, donshi tsakani da Allah har a zuciyarshi yama manta da ita.

    Jijjigashi tayi ya dawo Hayyacinsa, ta ƙara sakar mishi murmushi.

     “muje ko?” saukar da ajiyar zuciyah yayi, sannan yabi bayanta har zuwa dinning, taja mishi kujera ya Zauna, ta zuzzuba mishi girkin data mishi sai binta yake da kallo kawai.

    Murmushi ta ƙara mishi, “kaci please, tunda naji ka dawo, na tashi tunda safe na girka maka”

    Duk da baijin cin abincin, hakanan ya fara ci  duk da ya kasa ce mata komai, gashi taƙi nuna alaman shi mai laifine a fuskarta.

     Dankalin farko da yakai bakinshi daƙyar ya haɗiye, sai da ya haɗa da tea sannan.

   Ganin ya fara ci, ta nisa  sannan ta fara magana, “Meyasa baka kirani ba daka tafi? Kuma ni kona kiraka bazaka ɗaga ba, idan na samu ma ka ɗaga sai kacemun zaka kirani, laifin mena maka?”

     Baisan amsar dazai bata ba, don ya kauda maganar kawai yace mata ” Auntie ko bata tashi bane?”

    “bata farka ba, ka bani amsa please …..mena maka ne dana cancanci hakan daga gareka?”

     “bakimin komai ba, kinsan na faɗa miki biki naje, hidima ban samun lokacin dazan kiraki bane”

     “Yanzu lokacin da zamu wayane ma bazaka samu ba?”

    Miƙewa yayi cikin ƙosawa da maganar “bazaki gane bane”

      “Ya isa ace na gane hakanan Yaya Ahmad, baka damu dani bane kawai, anan hidimar aiki na hanaka nunamun kulawa, a can kuma hidimar biki ba” ta ƙarasa maganar cikin kuka….

    Hankalinshi ne kuma ya tashi, kukan mace na karyar mishi da zuciya, cikin rarrashi ya fara magana,

     “me na kuka kuma? Niɗinnan naki ne, duka yaushene zamu zauna a inuwa ɗaya? Kinga ta waya ma ya ƙare kullum ina tare dake”

   Maganarshi taɗanyi mata daɗi, taɗan tsagaita da kukan.

    “Yanzu akwai inda zanje, idan na dawo sai muyi magana ko?” tun kafin ta bashi amsa yayi hanyar fita, ba tare da ya jira abunda zatace ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *