MAFARIN SO CHAPTER 6
Www.bankinhausanovels.com.ng
Baki buɗe tabi ƙofar da kallo, tun sanda ta sanshi bata taɓa ganin irin wannan ɓacin ran a tare dashi ba, tuni har zuciyarta ta fara tsorata dashi, ‘anya bazata koma lallaɓashi ɓa?’ tuni kuma wani gefe na zuciyarta ke mata gargaɗi, ‘kashedinki Rabi’ah, karki kuskura ki ƙara bashi wani fuskar dazai rainaki, kema ya kamata ki nema wani hanyar da zaki rama’.
Babbar cuta ya gama mata ita, tunda ya aurota ya kawota nesa da gidansu, kuma yake goranta mata hakan, kullum yake gallaza mata.
Daga wurin bata matsa ba, anan ta duƙe taci gaba da kukanta, tsananin baƙin ciki kasa motsawa tayi daga inda take, fitar da yayi ta rasa daɗi ta mata ko kuwa.
Ta daɗe a haka tana kuka, baƙin cikin ɗaga hannun da Ahmad ya farayi a kanta, yasan bazai iya haƙuri da ita ba ya barota da gidansu da danginta? Garinsu da kuma yayanta? Ga kuma Hayrah da Hayran da suke ɗebe mata kewa ko a gidansu.
Zuwa nan da tayi da tunaninta yasa ta miƙe da sauri, wayarta ta ɗauko tana addu’ar Allah yasa kiran ya shiga.
Numbersu Hayran ne, cikin sa’a kuwa ta shiga, ta daɗe tana ringing, sannan taji anyi rejecting, gabanta ya faɗi, da sauri ta ƙara kira taji busy, kaman ta ajiye wayan, anma dai tunda ta samesu bazata iya haƙura ba, ta sake kira, wannan karan tana shiga suka ɗauka.
“hello Auntie! Auntie!! Auntie!!!” sune keta hayaniyar kiranta, ta saukar da ajiyar zuciyah.
“Hayrah!”
“naam Auntie, kinga Hayran ya hanani nayi magana dake, waishi zai fara”
“to wayan ba’a hannunki take ba? Ni ki bani mu gaisa da Auntie Rabi’ah”
“Ku tsaya kuji, ku kwantar da hankalinku zan gaisa da kowa”
A tare sukace, “we are missing you Auntie”
“missing you more yaran Auntie, ya akai bakuyi barci ba?”
“Hayran ke ƙarasa Homework”
“kananan da rashin sonyin homework da wuri ko Hayran? Ina Momie?”
Hayran yace “na daina Auntie, yau ne kawai da mukaje unguwa”
Hayran tace “tayi barci”
“Daddy fa?” yana falo yana kallo, shiru tayi tana mamakim Aunty Deejah, ba tun yau ba daman tasan halinta nayin barci ta ƙyale mijinta.
“ku kaima daddy wayan in gaisheshi” ta faɗa gabanta na faɗuwa, da gudu suka tafi kai mishi, suna bata labarin Aunty deejah ta anshe musu waya shiyasa basu kirata ba, sai Daddynsu ne ya mayar musu kuma babu numberta a ciki, har sukaje wurinshi suna mata fira, ta ɗan samu nutsuwa firar da tayi dasu, harta manta damuwarta ta wani lokaci.
Suna zuwa falon sun iske shima ya kashe kallon ya tafi, ba don taso ba ta haƙura anma taso tayi waya da Yayanta.
Da suka koma ɗakinsu, cewa tayi su saka handsfree su aje wayan, don su tayata fira har suyi barci, hakan kuwa sukayi, ba ƙaramin daɗi taji ba sun rage mata kewa sosae.
Ɓangaren Ahmad kuwa, yana shiga ɗakinsa, kasa zama yayi ya ringa zarya a bedroom, ya rasa yanda zaiyi da yarinyarnan, rashin kunyarta ya fara mishi yawa, yana matuƙar jin tausayinta, duk yanda yaso ya lallaɓata saita ɓata mishi rai.
Meye kaishi? Ta yaya harya ɗaga hannu zai doketa? Rabi’ah amanarshi ce, koba komai shi kaɗai ta sani a garin, babu wanda zata faɗa ma damuwarta duk duniyarnan, yasan tana cikin tashin hankali, anma rashin kunyarta ya hana ta kwantar da hankalinta.
Tun a lokacin ya fara nadamar marin da yayi niyyar yi mata, tausayinta ke ƙara kamashi inya tuna yanda ta zare idanu a tsorace, anma ai duk laifinta ne.
Toilet ya shige ya buɗe ma kanshi shower, ruwan na ratsashi ji yake kaman zai rage mishi zafin da yakeji a kanshi.
Koda ya fito kasa kwanciya yayi, tunaninsa dai halin da take ciki, ya tabbatar mai damuwa irin tata, ba lallai ne ta samu barci a daren ba, ballantana ita daya sani da yawan kuka, miƙewa yayi cikin zafin nama da niyyar komawa ɗakin.
Harya murɗa ƙofan zai shiga, kuma sai yayi tunanin ai raini ne zai ƙara jawoma kanshi, saiya fasa kawai ya koma ɗakinshi.
Washe gari data farka, hakanan takejin kaman an yaye mata rabin damuwarta, hankalinta kwance ta fara aikin da tunda tazo gidan batayi ba, kuma ba tayi tunanin zatayi ba, gyare ɓangarenta tayi tsab duk da ba wani datti yayi ba, ta shiga kitchen donta samu abunda ta girka, tunda bata ga alaman yau zai kula da abunda zataci ba.
Kalo ya isheta, ta rasa me zatayi gashi tunda ta tashi bataji motsinsa ba, kaɗaici ya mata yawa, taso kiransu Hayran saita tuna sun tafi Tahfiz, haka ta haƙura tai zamanta shiru.
Zaman gidan ya fara isarta, gashi akwai abubuwan da takeson siya wanda batason ya sani, anma ya hanata fita, haka ta miƙe da shirin zagaye gidan, a falo taci karo da mukullin motanshi aikam wani daɗi ta ratsata koba komai zata samu hanyar fita.
Daman a shirye take, mayafi kawai ta ɗauka don gudun karya dawo ya sameta, lokacin wurin ƙarfe 12 ne na safe. Wata ƙawarta da tasan garin Yola tama waya, ta faɗa mata inda zata samu Shopping Mall.
Ahmad kuwa tunda ya tashi ya shirya, bai nema sanin halin da take ciki ba, ya duba mukullan daya shigo dasu bai samu ba, ya ɗauka wata motar kawai ya wuce gidansu gaishe da iyayensa,
Umminsa ce ta tsayar dashi akan maganar bikinsa da Khadija,
“gashi har baifi 1month ba kuma banga alamun kana wani shirye-shirye ba”
“to ae Ummi naga bikin akwai saura, gidan da zamu zauna Abba yaa saka an gyara, lefe duk sanda kukace sai a bada a siyo”
“tohm naji, ita kuma Khadijan kunyi magana da ita kaji ko akwai abubuwan da takeso?”
Sai lokacin ma ya tuna da tayi mishi waya tanason suyi magana,
“zan tambayeta insha Allah Ummi”
Kallonshi takeyi duk yaa wani canja, kaman wani dole akai mishi da auren khadija, bayan su suka fito fili suka nuna sunason junansu, ita dai daman tun dawowanshi daga kt take ta ganin canji a tare dashi.
Daga ɗakin mamanshi yama Khadija waya ta sameshi a harabar gidan, sannan ya fita cikin mota, ba ɓata lokaci sai gata da alama lokacin ta tashi daga barci.
Buɗa motan tayi ta shiga tana murmushi, sannan ta gaisheshi.
“kin tashi lafiya?”
“lafiya lau” duk suka yi shiru kuma, sannan yace.
“lafiya dai kike nemana?”
“shikenan ni bazan nemeka ba sai babu lafiya?”
“kaman fa cewa kikai kinason magana dani”
“hakane, naga a waya bamu samun lokacin magana, gashi biki nata matsowa ƙawayena sai tambayana anko suke”
Dafe kanshi yayi, “kece baki tunamun ba, kuma dai don wannan ai ko text sai kimun, nawane zasu isheki?”
“bara na shirya dai, inka dawo daga office sai muje na zaɓo”
“A’ah, kije da kawayen naki dai, idan na dawo akwai inda zanje, ko nawa zasu isheki zan miki transper account naki”
Murmushi ta sake mishi,
“nagode sosai mijinah, Allah ya saka da alkhairi”
Shima murmushin ya mayar mata ya ɗaga kai.
Yana tafiya kam ya mata transper na kuɗin, wanka kawai tayi ta shirya fita ko ƙawayen nata bata nema ba, misalin ƙarfe 12 ta fita saboda tanason kai ɗinki duk a ranar.
Napep ta ɗauka zuwa shopping mall ɗin da Rabi’ah ta tafi da motan Ahmad.Sannu a hankali take takunta cike da tsantsar murna, Amman kallo daya zaka mata kayi saurin gane yanayinta akwai damuwa a atattare da ita,
saboda jikinta a sanyaye yake ahankali take siyayyarta .
Tana zaɓawar kanta duk abinda taga ya mata kuma da zai dace da ita, ba wasu kayan azo a gani bane ta siya wanda zai dame ta.+
Cikin hanzari ta hango wata kyakkyawar budurwar itama tayo siyyaya ta nufi wanjen biyan kuɗi. Kafin ƙarasowar Rabiah har ta biya tayi gaba abinta.
tana tafe tana rausaya kamar wata sarauniya a haka ta ƙaraso itama taje ta biya nata kuɗin .
Daidai wajen da tayi parking ɗin motarta ta iske buduwar nan data Gani da dukkannin alamu tana cikin damuwa dan tsugunne take gaban kayanta da suka tarwatse a kasa tana tattarasu.
Ahankali Rabia ta ƙarasa har inda take haka kawai taji tana son taimakawa yarinyar dan haka bata tsaya wani ɓata lokaci ba, ta tsugunna ta soma tayata tattara kayan, khadija ta dago idanunta tana kallonta fuskarta dauke da murmushi tace,
“nagode fa yaruwa,
wlh kayan ne suka min yawa gashi ni kaɗai nazo”
Sai da suka gama tattara kayan waje ɗaya cikin mayan white lailon,
Sannan Khadija ta miƙe tace,
“dan Allah yaruwa ɗan taimakamin ki jiramin kayan in ɗan kira mai a daidaita sahu”
Kallon mamaki Rabi’ah tayi mata dan da ganin yanayinta kawai ya isa yasa ka gane ba daga gidan babu ta fito ba.
Amman dai saita share kawai tana nan tsaye har Khadija ta dawo tana murmushi ba tare da mai adaidaita ba .
tace, “nafa gode sosai”
itama murmushi Rabi’ah tayi haɗe da cewa karki damu.
tace, “baki samu bane?”
Khadija tace, “wlh gaba ɗaya ma banga alamunsu ba Amman nasan zuwa anjima zan samu”
Rabi’ah tayi murmushi tana ɗan cizan lip’s ɗinta kaɗan sannan tace,
“in bazaki damu ba muje na sauke ki kawai”
da farko khadija ta ɗanji tsoro Amman kuma daga baya taji zata iya shiga motarta dan lokacin daya taji Rabia ta kwanta mata a rai, dan haka tace,
“shikenan ba damuwa, nagode fa”
Key ɗin dake hannunta ta ɗan matsa sannan ta buɗe but ɗin Khadija ta zuba kayanta.
Sai lokacin Khadija ta shiga kallon motar da number motar kamar motar Yayanta Ahmad,
Amma kuma aranta tace ‘me zai kawo motar gun wata mace’.
A hankali tace kai ba ita bace, sunyi iri ɗayane dai.
Sannu a hankali take tuƙi tana tambayar Khadija hanyar da zata bi,
Khadija tayi murmushi ta nuna mata tace,
“Amman dai ke baƙuwace a garin ko?”
Rabiah tayi murmushi kadan tace,
“me kika gani?”
Khadija tace, ɗaya-ɗaya ne wanda bai san unguwar dana faɗa miki ba.
Rabi’ah tace,
“haka ne, ni ɗin baƙuwace aure ne ya kawonu nan Amman ni Ƴar katsina ce, ban jima da zuwa garin ba”
Khadija ta jinjina kai kawai.
Suna shigowa layin su khadija tace,
“yauwa kina wuce wancen bakin get ɗin sai namu”
Dai-dai bakin get ɗin ta ja ta tsaya, khadija ta fito ta kwashe kayan ta ajiye a gefe, ta dawo a hannun da Rabi’ah take tace,
“gaskiya yaruwa na gode kwarai da gaske kin min kirki sosai”
Rabia tace “karki damu”
khadija tace,
“baki faɗamin sunanki ba da address ɗin inda kike, don na kusan yin aure nan badaɗewa kuma dai zanzo gayyatarki”
Rabia tayi murmushi ta sanar da ita sunanta da unguwar da take, sukayi Sallama haɗe da exchange ɗin number juna.1
Sannan ta juya kan motarta a hankali take driving tana jin wani irin nishaɗi a ranta, tasa hannu ta ɗauko wayarta dake ƙara tun lokacin suna tare da Khadija sai yanzu hankalinta yaje kan wayar, tana dubawa taga misscall din Ahmad ne yafi goma taja tsaki tace,
“ɗan rainin hankali kawai”
Sannan taci gaba da tuƙinta harta ƙaraso gida, tana parking ɗin motar, ta fito da kayan shopping ɗinta da wayarta kira ya sake shigowa.
Tana yamutse fuska kamar yana kallontaTace,
“wai meye ne zaka dami mutane da kira?”
“ke dan Allah malama banason rainin hankali kina ina har yanzu da baki dawo gida ba?”
tace, “anƙi a dawo ɗin kuma ni karka dameni”
A haka harta shigo cikin falon gidan tana yatsuna fuskarta.
Kwance yake akan three seater yake waya da ita har ya hango shigowarta tana girgiza jiki tana yatsuna fuska yace ‘lallai ma yarinyar nan tayi masifar rainani’.
Dai-dai zata wuce ta gefensa dan ita bata gansa ba ko alamunsa kuma bata kawo a ranta zai dawo da wuri haka ba.
Ji tayi an fizgota, ta faɗo jikin mutun a firgice ta ɗago haɗe da ƙwalla ƙara, yasa hannunshi ya rufe mata baki sannan ya matse gam ajikinsa yana sauke numfashi .
Yace “fara faɗamun dai, waye ya dame ki da kira? sannan kuma wa yace ki ɗaukar min mota ki fita da ita?”
Tayi tsuru-tsuru tana zaro ido waje yace
“ba dake nake ba? Ko taki ce?” ta hau girgiza masa kai yace,
“ok to meyesa kika ɗauka?”
Tayi shiru na ɗan wani lokacin, ko tunanin me tayi? sai ji yayi Tace,
“dan Allah kayi haƙuri wlh Allah bazan sake ɗauka ba”
(Rabi’atu tacemun, “da alama takwaratah ta fara shiga hakalinta dai”, nace “muje zuwa mu gani dai”)
Yaci gaba, “Kuma dan wulaƙanci, kin wani shigo gida kina jijjigawa mutane jiki, kuma dan iskanci da wannan kayan kika fita?”
Ta turo masa ɗan ƙaramin bakinta sai kuma Tace,
“to ina ruwanka da kayan dana saka?”
Ya ware idanunshi sosai yana kallonta,
“ok haka ma zaki ce?”
Ta lumshe idanunta bata ce komai ba,
Ya kai bakinsa yana shinshina wuyanta zuwa kunnenta, cikin sanyin murya yace,
“ni kike cewa ina ruwana da kayanki?”
Ta hau girgiza masa kai yace “yarinya kifa kiyayeni, bazan iya ɗaukar rainin nan naki ba”
Ta soma mutsu-mutsun ƙwace jikinta daga nashi, ta tattara duk iya ƙarfinta ta fizge jikinta ta miƙe tsaye, tana kallonsa idanunta lumshe tace,
“wannan ai wani sabon salon iskanci ne, da can ba haka nikeyin shigata ba har ka amince ka aureni? shine yanzu zaka zowa mutane da wani sabon salo”
Duk tunaninta inda ta matsa bazai iya kamota, ta buɗe baki kenan taji ya kwaso ƙafafunta tayi luuuuuuuu sai kan faffadar kirjinsa.
Sai jin Rabi’ah kake tayi luf kwance ba bakin tsiwa yace,
“uhmmmm, ina jinki kiyi magana mana, ashe ke muguwar mara kunyar ƙaryace”
A hankali muryarta a sanyaye tace
“ni dan Allah meyasa kakemin irin haka ne? Nasan saboda ka taimakeni ka aureni, haka ake taimako? Kuma idan ka gaji da zama dani ne to..to..ni, ka sakeni mana na kama gabana”
Abinda Ahmad ya tsani ji kenan wannan banzar kalmar nata Wanda ke baƙanta ta masa rai,
Ya haɗe rai take kuma yanayin fuskarsa ta sauya dan haka bai sanda yasa hannu ya ɓalle bakinta ba haɗe da matse mata bakinta sosai har ta saki wata gigitaccen ƙara wanda haka yasa Ahmad sassauta mata yana kashe mata ido ɗaya haɗe da ɗage mata gira alamun tambaya.
Ta murguɗa masa baki sai kuma hawaye ya shigo zubo mata tare da ita ya miƙe tsaye yace,
“ok kuka ma zaki wa mutane?”
Tace, “to ni yanzu mena maka dan Allah?”
Tana ƙoƙarin raba jikinta dashi Amman babu dama yaƙi sakinta ya manneta da jikinsa tsam har suka shiga ɗakinta, shida kansa ya rasa meyasa ya kasa rabuwa da ita, shi dai yasan a zahirin gaskiya ba sonta yake ba tausayine kawai take bashi, kuma shi a halin yanzu bazai iya sakinta ba,
Ji yake muddin yayi haka tamkar ya wulaƙanta aure ne
.Mutsu-mutsun da take na ƙwace kanta daga jikinshi ganin sun shiga ɗakin ne ya dawo dashi daga dogon tunanin da yake,
Murya a sanyaye take mishi magana, duk wani masifarta ta tattara ta ajiye gefe ganin bazata tsinana mata komai ba,
“kasan dai hukuncin miji me zalintar matarshi, don Allah kayi haƙuri ka ƙyaleni”
“eyyeh! Look who is talking, ke bakisan hukuncin matar dake ma mijinta rashin kunya ba ko? Wacce take ƙin bin umarninshi, zaki gane yarinyarnan, karki daina faɗamun duk abunda yazo bakinki”
Da sauri ta rufe bakinta data tuna ɓallar daya mata ɗazu, tana ƙara marairaice fuska,
“tohm aini kasan ba sonka nake ba, kuma ba jin daɗin zama nake dakai ba” ɗayan hannunta ne dake cikin nashi ya matse gam, aikam nan take ta cika mishi kunne da ƙara, sakinta yayi ya jefar gefe ɗaya, ya koma falo ya barta nan.1
Yana zuwa inda yabar wayarshi, kira na dai dai katsewa, ya ɗauka ya duba, 5misscalls ne duk daga Khadija, yana niyyar ajiye wayan wani kiran ya sake shigowa, yana kallon wayar harta kusa katsewa sannan ya ɗauka don baison ta dameshi.
“Hey Ango! Halan baka kusa nake ta kira baka ɗauka ba”
“eeh wani abu?” yanayin da yayi maganar a harzuƙe har sai da gabanta ya faɗi, tasan ƙila wani ne ya ɓata mishi rai, saita haɗiye tata maganar.
“ba komai daman don in faɗa maka na dawo, idan ka shigo sai kaga kayan”
“idan kin saka bazan gani ba? Ki bayar akai miki ɗinki kawai”
“tohm shikenan”
Ba tare da tunanin tana da wata maganar ba kawai ya kashe wayar ya jefar, yana hura numfashi.
“Mata Matsala”
Tana samu ya fita, ta bishi da Allah ya isa, daƙyar ta miƙe duk jikinta ya mata tsami saboda matsar da tasha, ga buguwar da tayi, a fili tace,
“indai haka ake aure wallahi Amaren dake faɗin daɗin aure rashin hankali ke damunsu, hakanan ake cewa aure ɗan haƙuri ne, koda wanda nakeso ne bazan haƙurin ba, ballantana da wannan banzan”
Tana son fita ɗaukan siyayyarta, anma batason fita su haɗu tasan bazai mata da daɗi ba, hakanan ta haƙura ta shige toilet ta watso ruwa, sannan ta haɗo da alwala.
Riga da wando ta saka, masu shegen kyau duk da bada niyyar kwalliya ta sakasu ba, tayi kyau sosai, sai ta kasa fita falon jin bai fita ba har lokacin, tayi kwanciyarta anan tana latse-latsen waya saiga kiran Khadija ya shigo.
Da sauri ta ɗauka tana fara’a,
“Hello er uwatah” inji Khadija,
“Amarya Ya gajia?”
“babu wallahi, ya kika koma gida?”
“lafiyalau Alhmdlh, yanzu kuwa nake tunanin mantuwar da mukayi”
“wacce mantuwa kenan?”
“kin manta baki nunamun ankon ba, kuma dai ya kamata inyi tunda zanzo biki”
“haba dai er uwatah, ae tuni na ware miki naki, yanzu zan kai mana ɗinki ma”
“kai sis, ya za’ai na saka Amarya hidima?”
“me a ciki? Ai mun zama ɗaya fa”
“aikam ngde sosai”
“babu godia a tsakaninmu, kira nayi na miki sannu da hanya daman”
“tohm na gode…Awwhhh, shikenan na go…” sukai dariya gaba ɗaya.
Rabi’ah tace “sorry ngde da kira”
Khadija tace “sai kinyi godiyar dai kenan”
“tohm ae naji daɗin kiran naki ne sosai, kin ɗan rage min kewa na wani lokaci”
“haba! Ina mijin naki ne?”
“oho mishi”
Dariya tayi, “kai sis yana gida anma kike nan”
“tohm mezan mishi?”
“kinfini sani ai, wannan sai dai inzo ɗaukar darasi, kinga sai anjima kar in shiga lokacinshi”
Tun kafin Rabi’ah ta sake magana khadija ta kashe wayan tana dariya, itama dariyan tayi, kaman ta ƙara kiranta kuma saita fasa.
“ai har abada wancan ɗan iskan mugun bazai samu lokacinah ba”
Bayan ta gama waya da Khadija, su Hayran ta kira, suna fara fira ba daɗewa aka kira sallahn la’asar, tace,
“kunji ga kiran sallah can ku tashi muje muyi”
“tohm Auntie”
Hayran yace “Auntie baki faɗamun ‘whole numbers’ ɗin ba”
Rabi’ah tace “Hayrah me ‘Whole numbers’?”
“whole number’s are numbers that can be devided into two”
“Yauwah Auntie, nama tuna, sune 2, 4, 6, 8 10….”
“dakyau yaranah, anma ka daina manta karatu kaji ko, in kuma ba haka ba idan zan dawo ban dakai tsaraba”
“yi haƙuri Auntie, bazan ƙara ba”
“Yauwah yaron kirki, muje ayi sallah sannan muyi Sos ɗin”
Hayrah tace “Auntie, momie tace mana bazaki dawo ba kin tafi kenan”
Shiru ta ɗanyi sannan ta bata amsa “idan kinga mutum ya tafi bai dawo ba ai sai idan mutuwa yayi, wanda kowannenmu jiran lokacinta yake, kuma gashi dai kunajin muryatah shaidar inanan daram, kuma zanzo na ganku insha Allah”
“eeh Auntie”
“tohm muje muyi sallahn, zan kiraku video call” duk suka miƙe suna tsallan murna, da sauri ta katse wayan kafin su sake sako mata wani surutun.
Data gama sallahn, yunwa ta dameta, ta ringa leƙenshi ta labule, saida ta tabbatar yabar gidan sannan ta fito da earpiece a kunnanta ta ƙura ƙara tanajin waƙoƙin mawaƙiyar data fi so, (demi lovato) tanabin waƙar tana ɗan takawa, haka harta shiga kitchen, tana girki tana bin waƙa.
Tuwan semonvita tayi, da miyar wake, gaba ɗaya gidan ya game da ƙamshi, girkinta take cikin nishaɗi tanabin waƙa sai tiƙar rawa take a kitchen.
Tunda ya jiyo ƙamshin abinci a kitchen ya tabbatar da tana can, don haka kai tsaye ya wuce kitchen ya hangota tana girki tana rawa, yanda take bin waƙar sai yaji har tafi ta demi daɗi, ba ƙaramin kyau ta mishi ba, saiya tsinci kanshi da kasa ɗauke idonshi daga kallonta, ya harɗe hannu kawai ya tsura mata idanu sai burgeshi take bai sani ba🤣.
Sai da ta gama girkin ta zuba nata, sannan ta saka sauran a cooler duk da tasan bazata ƙara ci ba.
Juyawan da zatayi sukai ido huɗu da mutum, ta ajiye plate ɗin sannan ta kashe waƙan.
“ni bansan sanda maza suka fara shiga kitchen ba”
“tun ranar da kitchen ya koma ɗakin rawa”
Karo na farko da taji kunyarshi ta saukar mata, ashe dai ya daɗe a tsaye yana kallonta,
Duƙar da kanta tayi, tazo wucewa ta gefenshi.
“nasan dai ƙwaƙwace ta shigo dakai, kingin abincinah na a cooler sai kaci”
‘an faɗa miki zanci jawalgwalonki ne?’ abunda yayi niyyar faɗa kenan kafin idanunshi su sauka akan plate ɗin nata,
Duk cikin abinci yafison tuwo, gashi kuma miyan wake yanason duk abunda zaici a saka wake ciki, sannan kuma shima yunwar yakeji.
“a katsina haka ake bawa miji abinci?”
“inama laifi da nace ka ɗauka? Ni ai ba girki nazo yi maka ba”
Na hannunta ya ƙwace, da sauri ta sakar mishi don karya zubar mata, ko meya tuna sai kuma ya miƙa mata,
“ki kaimun falo ki ajiye”
“ka tafi dashi mana, ba can zakaje ba”
Kallon da yake mata ae da sauri tayi hanyar falo ba shiri, tana guna guni, sai da ta ajiye mishi sannan ta dawo ta zuba wani.
A falo ta wuce shi, a ranta tace ‘da alama yau bashi da wurin zuwa’
Ta wuce tana waƙar,
“in kaga mai gida, in kaga me gida a bakin murhu, sauran abincin bai isheshi ba… Hmmm Allah dai ya ƙara nisanta mu da mazajen dake zuwa ƙwalama kitchen”
“kikace me?”
“waƙata nake” dai-dai lokacin yakai lomar abinci a baki, ya lumshe ido don daɗi.
“lallai yarinyar nan, ashe kin iya abinci zakimun ƙarya, sai dai kiyi ke kaɗai ko”
(uhm Su Ahmad an fara haɗuwa da babban sirrin kama mai gida)
Ta wuceshi batace komai ba,
“magana nake maki”
“tohh naji mana”
‘mutum ya fito fili ya faɗi abinci yayi daɗi zai wani tsaya kwane-kwane’
“daga yau na sama miki aikinyi, indai zakiyi girki dolene kiyi dani, kota nan ɓangaren zakiyi anfani, ya zanyi? Hakanan zan daure inci”
Bata tsaya bashi amsa ba ta shige ɗaki ta barshi, don ganinta daɗin santine kawai ke damunshi.Tana shiga ɗaki ta zube kan bed haɗe da runtse idanunta, abubuwa da yawa na yawo a kwakwalwarta ciki har da zamanta gidan Ahmad yadda Ahmad ya aureta ba tare da sanin iyayensa ba gashi tace ya saketa yaƙi, ta rasa dalilin dayasa ya killaceta a gidansa alhalin kullum cewa yake bai sonta a hankali wani bangare na zuciyarta ke bata amsa, kema ai ba son nashi kike ba Amman dai kinsan dai ya taimaka miki lokacin da kike neman taimako, haka ta kwana da wannan tunanin.
Washe gari data farka tana duba wayanta da niyyar ganin lokaci, message ɗinshi taci karo dashi,
“ki tashi kiyi aikinki, ko saina tuna miki?”
tsaki taja sannan ta Miƙe taje wardrobe ta ciro wata doguwar riga ta ajiye kan bed sannan ta cire kayan jikinta, bathroom ta shige bawani jimawa tayi ba.
Ta fito ɗaure da towel iya cinyarta ga gashin goshinta duk sun kwanta luf tamkar wata, da gefen towel din take goge every part of her .
Direct wajen mirrow ta nufa tana rausaya tayi tsaye tana kallon jikinta a hankali ta ɗan buɗe towel ɗin tana kallon yadda jikinta ya canza a ɗan zamanta a gidan sosai take kallon Brest ɗinta ganin yadda suka kara yin wani irin kyau da cika kmr wata mai shayarwa, ta lumshe fararen idanunta, tasa hannu ta ɗauki lotion ta soma milke jikinta dashi wani iri wani iri takeji a sansar jikinta, dole yanayin jiki ya canza cikakkiyar mace mai ji da kuruciya taci abinci mai kyau gun kwana mai kyau kuma su kwana gida guda da namiji ai dole ko ba soyayya aji bukatuwa ta sauke numfashi duk a ƙasan ranta take faɗin taci gaba da lailaye jikinta da lotion tana lumshe idanunta uhmmmm ina ma auren soyayya da mijinta yasha…., idanu ta zaro waje haɗe da sake dake towel din dakyau tana binsa da wani irin kallo .+
Sam bataji motsin shigowarsa ba ballantana tasan da tsayuwar sa agun ta mirrow ta hangoshi jingine da jikin ƙofa hannuwansa duka rungume a saman kirjinsa, kallon kallo suka shiga yiwa juna yayinda ita tsoro ya gama bayyana a fuskarta da gangar jikinta gaba ɗaya a firgice take yadda yake binta da mayen kallo, shima kuma tsaye yake har yanzu yana binta da kallo wanda hakan yasa Rabi’ah tayi saurin jan towel ɗin sama Sosai dan bai Ida rufe mata dukiyar fulaninta ba.
Ta takure jikinta waje ɗaya haɗe da ɓata fuska ta watsa masa harara ta cikin mirrow din ta juyo a tsorace muryata a dashe tace,
“meye haka Kuma zaka wani shigowa mutane daki ba ko sallama?”
A hankali yake tako inda take tamkar wani kumurci duk step ɗaya yake daidai yake da bugun zuciyarta, itama da baya da baya take daga ƙafafunta har takai kan bed ta zauna jagwab ta soma lalubo doguwar rigarta data ajiye kafin hannunta yakai ga rigar har ya iso gareta a tsorace tace,
‘wannan wani irin salon iskanci ne? kabari nasa kaya mana” yayi ɗan murmushin gefen baki a hankali yace,
‘karki damu nima ba wani abu zan miki ba” yasa hannunsa ya ɗauko rigar zai sa mata tayi saurin fizge rigar daga hannunsa ta ɗunkuleta cikin jikinta ahankali, ya motsata sosai ya ware hannunta ya ƙwace riga yana kokarin saka mata da sauri tasa ƙarfin ta duka ta tureshi, Amman ko motsawa bai yi ba.
Binta yayi da kallo ganin yadda jikinta ya ɗauki kyarma a ransa yace,
“ga tsoro ga tsiwa, ya sake tunkarota gadan gadan tayi baya da sauri, sai ƙarshen bed hannunta ƙwaƙume da towel ɗin jikinta .
Shi abun nata ma dariya yaso bashi, Amman ya share kawai a hankali ya ƙarasa har inda take ya jawo ƙafafunta, ta dawo tsakiyar bed ɗin ya mata runfa da faffaɗan kirjinsa a firgice ta runtse idanunta gam, daidai kunnenta ya kai bakinsa yace,
“matsoraciya kawai, me kike tunanin zan miki?
uhmmmm bayan tun ɗazu da kika buɗe towel din na gama ganin komai a sadaka” ya lumshe idanunsa yana kallon saman ƙirjinta dake up and down,
“abinda na gani kuma bai sani jin komai ba illa Haushi, kuma wlh kika sake kiramun kalmar iskanci a gida zakiga yadda zanyi dake”
ya busa mata iskar bakinshi wuyanta zuwa saman ƙirjinta sannan ya tattarota gaba ɗaya jikinsa ya saka mata rigar.
A hankali take sakin numfashi zuciyarta na wani irin dokawa da sauri da sauri yace,
“oya ki buɗe idonki”, tayi shiru taƙi motsi ballantana ta kai ga buɗe idanunta. Gaba ɗaya a tsorace take da yanayin sa muryarsa a kausashe yace
“ki buɗe idanunki before I count 3”
ahankali taji yace, “1…2..3….” ai da sauri ta bude idanunta da suke ɗauke da rikici iri iri ta narke fuska kamar zatayi kuka ya saki dariyar mugunta yace,
“meyasa kika buɗe? da kin tsaya kinga yadda zanyi da namanki, mai taurin kan tsiya” ya ja tsaki ya Miƙe sannan yace,
“karna ƙara tuna miki da girkinfa, banda tea ko indomie, daman abinda ya shigo dani kenan, sai gashi nayi kallon film a kyauta”
tace, “Allah ya isa da abinda ka gani” ya ɗaga kafaɗarsa duka alamun I don’t care, har zai bar dakin sai ya dawo
yace, “dan Allah karki girka yarinya kiga yadda zanyi dake”
Ta murguɗa masa baki tace, “to baza’a yi ba koni baiwarka ce”
yace, “that’s ur problem” sannan ya fice, ai kuwa yasha Allah ya isa har babu iyaka zagi ko babu wanda Ahmad bai sha ba daga ƙarshe ta fashe da kukan shagwaba.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan kwana biyu Rabi’ah kwance take kan three seater a falon tana kallon zee wold, kiran Khadija ya shigo wayarta cikin sanyi ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta.
“Amarya, ya kike?”
Ɓangaren Khadija tace.
“lafiya wallahi, daman nace zuwa anjima zan shigo na kawo miki ɗinkin ankon naki”
Rabia tayi murmushi tace,
“kai ashe dai da gaske kike Allah na ɗauka da wasa ne fa”
Khadija tace, “haba dai wasa, ai kin wuce haka”
Rabi’ah ta sake yin murmushi tace,
“to Shikenan nagode sosai sai kinzo kenan”
sukayi sallama Rabia taji Khadija ta sake shiga ranta sosai tace ‘ko ba komai zata rike matsayin kawa’ tasa wayar a silent saboda taji kallon film ɗin cikin natsuwa, kallonta take hankali kwance.
Ahmad taga ya fito cikin sauri ya sake koma ciki riƙe da waya ta ɗan kalleshi kaɗan sannan ta maida hankali kan kallonta .
Ita ko Khadija data amso dinkinsu har zata wuce kai tsaye ta kaiwa Rabiah kayanta gida, da taga ai layinsu ɗaya da Ya Ahmad, tayi tunanin ta koma gida ta masa girki kafin taje tunda shi kaɗai ne a gida kuma tana son ganinsa da akwai maganar da zasuyi bayan ta shirya masa jallof ɗin shinkafa da taji haɗin kabeje, sannan ta ɗau hanyar zuwa gidan.
Da farko dai abinda ya soma bata mamaki shine address ɗin da Rabi’ah ta bata shine a jikin gidan Ahmad gaba ɗaya kanta ya ɗaure,
Amman sai ta kawar da komai a ranta ta soma kiran layin Ahmad yana dauka tace,
‘gata a ƙofar gidansa’ hankali a tashe ya sake fitowa falo karo na biyu wanda kiran Khadija na uku kenan ya rasa yadda zaiyi ya hanata sai faɗa yake mata meyasa da zata zo batasanar masa ba tace,
“kayi haƙuri nazo layin ne biyowane zanyi, gani ma a bakin get”
Ƙarasawa yayi inda Rabia take, hankali a tashe yake kallonta har bai san sanda ya kamo tafin hannuta cikin nasa ba yace,
“Rabia taso please ki shiga ɗaki, wata sister ɗinace zata zo gidan, already ma tana ƙofar gida”
Wani kallon rainin wayo ta watsa masa haɗe da fizge hannunta da ƙarfi, sannan ta gyara zama tana harararsa tace,
“anzo gurin, nufinka na ɓoye kenan saboda sister ɗinka zata zo?” tayi ƙwafa.
“abinda bazai yiwu bane wannan ka canza shawara ko Kuma ka sakeni gaba ɗaya kowa ya huta da wani ɓoye ɓoye”
Ya fuszar da iska mai ɗumi wanda har hucinsa ya daki fuskarta, Rabia ta ɗan runtse idanunta ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa a hankali ya sake matsota sosai yana ƙoƙarin sake kamo hannunta tayi baya kaɗan yace,
“haba Rabi’ah kar kimin haka dan Allah karki shiga tsakanina da mahaifiyata, please muddin taji nayi aure a boye dake baza ta min ta daɗi ba, dan haka ki taimaka dan Allah just for 15 minti ne bazan bari ta jima ba”,
tayi banza dashi sai ma sake gyara zama da tayi taci gaba da kallon film ɗinta, rarrashin duniya babu wanda bai yi mata ba Amman taƙi ko gezau.
Yaji haushin kansa ganin yadda yaketa binta yaja tsaki haɗe da cewa,
“kar Allah yasa kiyi Yar rainin hankali kawai dan kinga ana lallaɓaki”
Ta taɓe baki, “kanka akeji, wa yace a lallaɓani ɗin?”
‘Naji nidai koma me zakice ki koma ciki please, wai ke meyasa….?”
Kiran Khadija ne ya sake shigowa, da sauri haka yayi shahada ya Miƙe jiki a sanyaye yabar falon, yana fita ta kwashe da wani irin dariya da bata san ta iyata ba har da kama cikin tace,
“kai ashe karyar rashin mutunci kake yi” saida tayi dariyarta mai isarta sannan kuma ko me ta tuna ta ɗan tsagaita ta Miƙe ta shige ɗaki tabar wayarta anan gefen kujera ba tare data sani ba.
Tana tashi sai gashi sun shigo hankalin Ahmad a tashe da ganinshi anga marar gaskiya, Amma sai me yaga falon wayon ba alamun ta.
A hankali ya rinƙa sakin ajiyar zuciya yana godewa Allah, waje ya nunawa khadija, ta zauna tana ƙarewa ko ina kallo komai tsab kamar ba namiji ne a gidan ba, Amman da yake ta san yadda Ahmad keda tsabta sai bata damu ba.
Ta gabatar masa da abinci, yace ‘ya gode Amman sai zuwa anjima zai ci, dan yanzu bai jin yunwa,’ sun ɗan jima zaune suna hira kadan kadan, sannan yace mata,
‘yana son ya fita ne dan haka ta tashi ya maida ita gida tayi shiru haɗe murmushi tace,
“haba dai yaya daga zuwana har zaka koreni?”
Ya haɗe rai alamun bayason ta kawo masa raini, tayi shiru ta ɗau waya ta soma dialing number Rabi’ah,
Gashi dai tana shiga Amman ba’a ɗauka ba ta kira ya kai sau goma, shiru gashi Ahmad ya matsa mata da zancen tafiya, dan haka ta Miƙe tana kallonsa fuskarta ɗauke da zarginsa kala kala saboda yadda yarinƙayi tamkar mara gaskiya har sanda suka fito compound ɗin gidan abinda ya sake ɗaure mata kai ganin motar Ahmad wanda irinta ce exactly Rabiah ta kaita gida dashi tayi shiru ta zubawa motar ido tana nazarinta gabanta taji yana faduwa , matsowa yayi kusa da ita yace,
“ya kike tsaya kuma muje mana”
take tace, “Yaya kayi aure ne?”
Yayi saurin watsa mata harara sannan yace,
“auren lafiya?”
Khadija tace, “tabbas naga wata da irin motar nan sak kuma ita matar aure ce, kuma harta bani address ɗin ta kuma wallahi nidai kwatancen gidannan ne”
Gabansa ne yayi mummunan faɗuwa, yayi saurin cewa,
“A’a kin jiki da wata maganar banza, sai aka ce miki ni kaɗai aka yoma irin wannan motar? Akwai masu irinta da yawa, address kuma ba mamaki kuskure tayi wajen baki”
Tayi shiru can kuma ta girgiza kai,
“Shikenan bari na tafi, gashi ma ina ta kiran number nata taƙi ɗauka”
Ahmad yace, “ki shareta kawai ƙila ma irin marasa gaskiyar nan ce tunda gashi nan taki receiving call ɗinki”
Haka ta bishi ya kaita gida batare data yarda dashi ba
.Gudu ya ringa shararawa a bakin titin, tana so ta mishi magana anma babu fuska,
Bayan isarsu gida, ta ɗan tsaya bata fita ba bayan yayi parking, ya ɗan kalleta ta gefen ido.
“in baki da abun cewa ki fita mana”
Bataji daɗin maganar daya mata ba, hakanan ta daure tace,
“maganar da nakeson muyi koka mnta ne?”
“shine nace ina jinki ai”
“kaga i.v bakace komai ba”
“me zance kenan?”
“maganar shirye-shiryen dake jiki, wuraren da za’ayi da abunda za’a bama baƙi, kaga kayan da zamu sakama har yanzu bakamun maganar ba, gashi har nan da kwana biyune za’a fara”
“wai ɗinkunan bazasu ƙare ba? Ki zaɓa cikin waɗanda kikayi ki saka mana”
“wannan dabanne fa, wanda zamu saka”
“nawa zasu isheki sai kije ki zaɓo? Wuraren da za’ayi ɗin da komai dai ki faɗi yanda zasu isheki”+
Shiru tayi tana rigimniyar haɗiye damuwarta.
“ba kuɗine matsalatah ba, bansan meka ɗauka hidimarnan ba, a matsayin dana ɗaukeka Ya Ahmad koda ace ba bikinmu ake nida kai ba ai nasan zaka taimakamun da hidimarnan, daman haka ake auren komai Amarya zatayi? Komai sai dai Auntie ko Ummi sumin?”
Shiru sukayi, babu wanda ya ƙara cewa komai, sai kokawar maida hawayen dake son zubo mata take,
Tausayi ta bashi, yasan bai kyauta ma Khadija sosai,
“tohm shikenan sauran duk ki barsu a hannunah, maganar kayan sakawa kuma ki daure kije ki zaɓo ɗin, kinga kona rakaki ba wani iya zaɓe nayi ba, ko kuma Auntie tayi magana a kawo maki ki zaɓa”
“tohm shikenan, anjima sai inyima ƙawatah magana ta rakani”
“Yauwah nidai na sanki da fahimta, wacce ƙawar taki Hafsat ko Aisha?”
“A’ah sabuwar ƙawatah dai matar aurennan, da alama ita ta iya zaɓe don bakaga yanda komai da tasa yayi kyau ba”
Wurin magana har yana ƙwarewa,
“kina da hankali kuwa? Matar auren ce zata rakaki zaɓar kayan? Kema kinsan ai ko mijinta bazai barta ba”
“ya akai ka sani kaida ba mijin nata ba?”
“anma aini namiji ne, kinga ki shirya ɗin anjiman zanyi ƙoƙarin rage abubuwan da nake sai muje”
Murmushi tayi don daman so take ta gwadashi, kayan da zasu sakanma tuni Auntie ta saka an kawo mata su daga dubai, kawai don taga yanda zaiyi ne inta yi mishi maganar Rabi’ah.
Sallama sukayi sannan ya tafi, tabi motarshi da kallo alamar damuwa fal a ranta, Addu’ah take sosai tana roƙon Allah karya tabbatar da zarginta ya zama gaskia.1
Daga nan gida ya wuce, a falon ya iske Rabi’ah ta fito ɗaukar wayarta, ya faɗa saman kujera yana sauke ajiyar zuciyah,
Ta taɓe baki,
“duk wannan ɓoye-ɓoyen bazai maka ba, malam ka sakeni kawai shine mafita, ba’a saka mutum cikin gida ana ɓoyenshi ba kaman mugun abu”
Ya mata banza ko kallon inda take baiyi ba, idanunshi a rufe yana tunanin tashin hankulan dake gabanshi, babban tashin hankalinshi shine aurenshi da Rabi’ah karya fita gidansu a sani, kuma dai yasan shi bazai iya sakinta ba, ga kuwa aurenshi da Khadija, duk da farko da amincewarshi za’a musu auren, anma yanzu jinshi yake kaman wanda za’ama auren dole.
“dakai nake fa, donma ka sani, duk randa wani en gidanku suka ƙara zuwa gidannan baka sakeni ba, bafa zan ɓoye ba, nida kaina zan musu bayanin zaman da muke”
Da raunannun idanunshi ya ɗaga yana kallonta,
“idan kin tashi kice zaman haramci muke, ke ko kaɗan bakisan kiga mutum cikin damuwa ba ki sarara mishi?”
“nina saka maka damuwarne? Ina ruwana da damuwarka? Kai ka sani mana”
“kema zaki sani ne”
Yaɗan miƙe, ta ɗauka wurin ta zai kufa aikam tayi saurin guduwa, ya kalleta kawai ya shige ɓangarenshi.
Misscalls ɗin Khadija ta gani sinfi 20, ta zaro ido badai har tazo ba tayita kirana, sauri take tayi ta kirata, tana shiga duk ta matsu ta ɗauka.
Sallama tayi, ta amsa da sauri tace,
“yanzu nake ganin misscalls ɗinki, ban kusa wallahi, yanzu zaki taho ne?”
“A’ah nazo fa harna tafi”
“haba sis, ya zakimun haka? Harfa address ɗin na tura miki inanan ina jiranki”
Ta ɗanyi shiru sannan tace,
“Address ɗinnan gaskia naje ban gane gidan ba, kuma ga hidimdimu yanzu sunyi yawa ai da sai in dawo, anma dai ke zakizo ko tunda kinga gidan?”
“zuwa kai insha Allahu, ki turamun da evens ɗin”
“tohm shikenan er uwah godia nake”
Sukai sallama suka kashe wayan.
Satin biki…
Da safe tana zaune tana gyaran akaifarta (ƙumba) ya shigo cikin shirin fita,
“zan fita…..”
Kaman jira take ya fara magana ta katseshi,
“toh ina ruwana? Tunda kake fita ka taɓa faɗamun ko sai yau don kinibibi?”
Da sauri ya nuna kanshi da hannu,
“ni nake miki kinibibi?”
“eeh ɗin, toh meye na faɗamun? Kaita fitarka mana”
“ya miki kyau yarinyarnan, zaki bayani ne idan baki saurari abinda zan faɗa miki ba yanzu”
Shiru ta mishi tana taɓe baki,
“rannan na miki kashedi akan ɗaukarmun mota ki fita, na hanaki fita anma kika tsallake maganata sai da kika fita, tohm wallahi wannan ya zamo kashedina dake na ƙarshe karki sake taka ƙafarki waje”
“taɓ! Wallahi bai yiwuwa kaman kaa kawoni prison kacemun bazan fita ba? Saina fita ɗin”
“haka kikace? Nadai faɗa miki”
“idan na fita fa?”
Ya ƙuta sannan ya ɗaga kafaɗa,
“kardai kice ban faɗa miki ba, komai zai biyo baya”
“wallahi ni kuma saina fita”
lallai yarinyarnan tayi nisa.
Hannunta ya matso ya ɗagota tsaye, yana shirin kamo kunnuwanta ta fara mutsulniyar ƙwacewa,
Da yake da razor ne take yanke akaifar, kawai sai dai taji taa kaima hannunta yanka, nan da nan jini ya fara kwarara.
Duk ya ruɗe da sauri ya sake ta,
“subhanallahi, kinga har kin jima kanki ciwo ko, mema ya kaiki amfani da razor?”
Ya kamo hannunta, ta fizge duk da jinin dake zuba,
“tashi kisa hijabinki muje asibiti”
“babu inda zanje”
Ta riƙe hannunta yana mata raɗaɗin ciwo ga jinin dake zuba, duk ya rasa mema zaiyi mata.
Hankerchip ɗinshi ya fara tare mata jinin, ta cire ta wurga mishi, tana ƙudundune hannunta cikin jikinta, bai haƙura ba, donjin ciwon yake kaman a jikinshi, su duka jikinsu duk ya ɓaci da jini.
Ɗakinshi ya tafi, ya ɗauko first aid sannan ya dawo tananan inda ya barta, hardasu hawaye, tana ganinshi ta ƙara ɓoye hannun.
Fisgoshi yayi da ƙarfin tsiya, ta runtse ido kawai ta sakar mishi.
Jinin ya fara goge mata, a hankali yakeyi yanda bazataji zafi ba.
Sai da ya gama ya rufe mata ciwon sannan ya saketa,
Wani wankan ya sakeyi, ya canja kaya duk hankalinshi na wurinta, fasa fitar yayi don bazai iya fita ya barta da ciwon ba, duk masu nemanshi sai dai ya musu waya bazai samu fita ba.
Sanda ya koma kwance ya isketa tayi shiru kaman mai barci.Kanshin turarensa ne ya soma isar mata da saƙon shigowarsa tun kafin ya iso gareta, ta lumshe fararen idanunta har cikin ranta take jin masifar son kanshin turaren.
Har inda take kwance ya ƙaraso ya zauna yana ƙare mata kallo. Shi kansa ya rasa taƙamaiman dalilin da yasa ya kasa rabuwa da ita
alhalin yasan ba sonta yake ba, gashi kuma bayason ganinta cikin damuwa da tashin hankali .
Tana jinsa har sanda ya iso gareta bata motsa ba, ballanantana ta nuna tasan da zamansa, A hankali ya kamo hannunta mai ciwo idanunsa ya zubawa saitin ciwon yana kallo har ɗan kumburi wajen yasomayi, yaji zafi a ransa tamkar ya cire mata raɗaɗin ciwon datake ji zuwa kansa.
Ahankali yasoma busa mata iskar bakinshi akan ciwon wai duk dai yanason wajen yabar mata zafi. Tayi shiru batace komai ba, Amman haka kawai ta tsinci kanta da jin faɗuwar gaba, yaci gaba da busa mata iska bakinsa wanda har cikin gangar jikinta sanyi iskar ke tsumata, tayi ƙoƙarin zare hannunta daga gareshi Amman yaƙi sakar mata hannu.
Ta ɗago idanunta suka sauka akan fuskarsa, shima ita yake kallo ya mugun tsareta da idanunshi wanda cikin second daya suka nemi birkicewa Rabiah kwanya, kallon junansu suke yayin da kowannensu da abinda zuciyarsa ke saƙawa a game da ɗan uwansa, da sauri ta kauda fuskarta zuciyarta na wani irin dokawa da sauri da sauri, the same reaction ne ya samesu a lokaci guda domin shima yaji makamanci abinda taji koma fiye da hakan.+
Yasa hannuwansa duka ya tattarota gaba ɗaya jikinsa, a firgice ta ɗago tana kallon ƙwayar idanunshi ya kashe mata idanunsa ɗaya haɗe da sakar mata murmushi. yana sake kashe mata idansa daya.
Ta lumshe fararen idanunta na second biyu sannan ta sake buɗesu fes akan fuskarsa ta narke fuska cikin sayin muryata tace,
“kazo ne ka takura rayuwata ko?”
A hankali ya girgiza mata kansa alamun ba haka yake nufi ba. Tayi lamo a jikinsa tana shaƙar kamshin turarensa mafi soyuwa a zuciyarta mai matukar dadi da sanyaya rai.
Zuciyoyinsu ke bugawa at the same time yayinda kowannensu ya fahimci halin da ɗan’uwansa ke ciki, ya ɗan ƙara matseta a jikinsa yana busa mata hucin numfashinsa a fuskarta zuwa wuyanta.
Ya soma magana
“Ra…bia…..”,
yadda ya kira sunanta ɗin ne, yasa gaba ɗaya jikinta ya mutu murus.
Abinda take jin yana mata yawo a jikinta ya sake nunkuwa sosae ta kasa ƙwaƙƙwarar motsi ballantana takai ga iya amsa masa shima bai damu da hakan ba yacigaba,
“dan Allah meyasa ke… bakya jin magana ne kalli abinda kika jawowa kanki yanzu”
ya sake kallon inda razorblade din ya yanketa.
“please ki rinƙa kiyayewa Banason duk abinda zai taɓamun lafiyar jikinki kinji, nafison duk sanda zan maida ke wajen yayanki ya kasance kina cikin ƙoshin lafiyarki ta yadda shima zai ji dadin ganinki”
Taja tsaki dan jin haushin abinda yace, wato ma da gaske kenan bai sonta shiyasa bai son zama da ita, dan takaici ma batasan sanda hawaye yashiga bin fuskarta ba ya gigice ya sake matseta a jikinsa yana tambayarta abinda yasata kuka tayi shiru taƙi cewa komai.
A iya tunanin sa abinda yasan zataji dadin jine ya sanar mata tunda burinta kenan kullum ya saketa ta koma gidansu, Amman kuma sai gashi tana kuka ya rikice ganin yadda hawayen ke silalowa akan kyakkyawan fuskarta.
Ya lumshe idanunsa yana jin raɗaɗi mai zafi a zuciyarsa duk da ba wannan bane karo na farko daya taɓa ganin kukanta, yaji gaba ɗaya ya manta kansa da kuma gaban wacce yake.
Ya ruɗe har baisan sanda yasa harshensa yana lasar hawayen dake silalowa akan fuskarta ba, haɗe da rarrashinta tamkar dai yadda akewa ƙananun yara .
Cikin sanyi yace,
“ple..ase.. Rabiah stop crying, wlh hawayenki na touching ɗin heart ɗina, bansan maganata zata bata miki rai haka ba,
Kiyi hakuri nayi sanadin da har ta kaiki gayin kuka”
Cikin sanyin murya tace,
“nima bana ƙaunar zaman da kai, ka maidani gidanmu yanzu tunda baka sona”
Abinma dariya yaso bashi Amman ya share kawai dan yasan any single mistake zai iya sa tasake birkice masa dan haka yace,
“nima abinda nake so kenan zan maidake Amman fa sai kin saki ranki sosai sannan ki rinƙa jin maganata, idan ma kika kiyaye ɓacin Raina zan iya mai dake nan bada daɗewa ba tunda kinsan nida ke bazamu taɓa son junanmu ba ballanantana muci gaba da zama tare”
ta sake jan tsaki, tace,
“karmu taɓa son junan mana, dan Allah malam sakeni ni kazo ka wani ƙwaƙwume mutun ka hanashi shaƙar iska mai daɗi”
Yayi murmushin gefen baki dan gaba ɗaya ya gama ɗagota tsab, ba wai batason komawa gidansu bane, A’a ita kalmar rashin sonta da ba yayi ne yafi komai taɓota dinta.
Yace,
“dan ma kin samu na saki a jikina shine zaki kawowa mutane salo”
cike da tsiwa tace,
“na sakane da zaka zo kana damuna da wani zancenka can?”
Yayi shiru ya zuba mata rikitattun idanunshi masu sa Rabia taji yanayinta na canzawa, idanu ya zuba mata yana cigaba da ƙarewa ƙaramin bakinta kallo take yaji yana samun reaction da sauyi a jikinsa itama hakance takasance da ita.
STORY CONTINUES BELOW
Ahmad dake zaune shiru Amman duk ilahirin jikinsa babu inda baya rawa, gaba ɗaya sha’awarta ta soma karya masa garkuwar jiki .
Duƙo da kansa yayi saitin bakinta ya ɗan bata light kiss a lip’s ɗinta, a
tsorace ta zaro idanunta tana kallonsa da mamaki ɗauke a fuskarta, ya kauda fuskarsa tamkar bai san abinda tayiwa hakan ba .
Cikin mutuwar jiki ya kwantar da ita gefe sannan ya Miƙe ya soma tafiya domin barin ɗakin jikinta a mace ta ɗan Miƙe zaune ta jingina bayanta da jikin gadon ta zubawa bayansa ido har yabar dakin idanunta na kallon ƙofar da yabi ta runtse idanunta gam tana jin yadda zuciyarta ke beating dum…dum…dum, hannuta tasa duka ta dafe saitin zuciyarta dashi tana faman kokuwa da numfashinta. ta sulale ta koma ta kwanta ta runtse idanunta tace,
“wayyo Allahna meye haka kuma yake nufi?”
wani part na zuciyarta ke bata amsa,
“bakomai bane face zama waje ɗaya da kike yi da Ahmad”
Buɗe laɓɓanta tayi ta soma magana in a slow voice,
“kai ba haka bane akwai abinda ke
shirin faruwa dani wanda bansan ko manene ba,” tamkar zata zubda kwalla.
Ko a daren ranar sai da Ahmad ya sake shigowa gun Rabiah ya jaddada mata kar ta kuskura yaga ƙafarta a waje da sunan fita, ta mishi banza yakaraci maganar sa ya fice .
Washe gari tana zaune a falo kiran Khadija ya shigo fuskarta ɗauke da murmushi tasa hannu ta ɗauki wayar ta manna a kunnenta tace,
“amarya kenan, ya shirye shiryen biki?”
Ɓangaren Khadija ma murmushi tayi tace,
“Alhamdulillahi er uwah na jiki shiru yau ɗin, keda zaki shigo da wuri ki shiya anan”
Rabia ta ɗanyi shiru sannan tace,
“anjima kaɗan zaki ganni, anma ko nazo bazan daɗe ba”
khadija tace,
“ba komai nagode sosai da hakan ma” sukayi sallama.
Da misalin ƙarfe uku dai-dai na yammacin ranar Rabi’ah ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar da taji aikin stone work sai kyali take zubawa ta yafa ɗan ƙaramin mayafi wanda da kaɗan ya wuce kafaɗunta.
Ta dawo falo tana dube duben inda tasan Ahmad yake yawan ajiye makullin motocinsa taga wayam gaba ɗaya bama alamun ko ɗaya.
Taji haushi ya kamata kamar ta fasa ihu, taji fitar ta fice mata a rai Amman kuma sai wani tunani yazo mata ta ɗan ciza gefen lips ɗinta ranta a ɓace ta nufi ɗakin Ahmad ta soma duba wardrobe ɗinsa nan bata ga komai ba ta dan tsaya can kuma ta soma duba bedside nanma bata ga komai ba sai tarkacen takardu da file file ta juya fuuuuuu zata fice daga ɗakin, sai kuma ta dawo ta duba wata ƙaramar loka a hankali ta sauke ajiyar zuciya ganin ɗaurin kuɗi dumus da sauri tasa hannu zata zari dai-dai yadda take tunanin zasu isheta.
Sai kuma ta tuna ai ya kamata ta bawa Khadija gudanmuwa, kuma batasan inda zata samu atm ba, dan haka ta ɗauki ɗauri ɗaya ta bar ɗakin da sauri ta soma kiran Khadija a waya Bayan ta ɗauka tace ta turo mata da full address ɗin gidansu saboda bata san sunan unguwar ba da kanta ne zatayi driving ɗin zata gane.
Da fama wayarsu ko minti 2 ba’ayi ba taji shigowar message, shap shap ta sake gyara kanta sai da ta tabbatar komai na jikinta yayi tsab sannan ta bar gida tana fita ta tari drop har zuwa unguwarsu Khadija.
Daidai bakin get ɗin gidan ta nuna ma mai adaidaita, yaja ya tsaya ta Miƙa masa kudinsa sannan ta sauka tana sake gyara mayafin jikinta.
Ta kira number ɗin Khadija Bayan ta ɗauka ne tace mata gata a bakin get Khadija tace,
“ki shigo ciki mana, ganinan fitowa yanzu”
Cikin nutsuwa take takunta mai ɗaukar hankali harta shiga compound ɗin gidan.
Can saiga Khadija ta nufota fuskarta ɗauke da murmushi taja hannun Rabiah har cikin gidan kai tsaye ɗakinta tayi da ita yayin da rabia ke biye da ita, tana murmushi ta nunawa Rabiah wajen zama.
Ta zauna ba tare data ɗaga kai ta kalli mutanen ɗakin ba, Bayan sallamar da tayi, khadija ta ɗauko mata kayan anko dinta ta zube mata su a saman cinyarta sannan tasoma introducing ɗin rabia ga sauran kawayeta nan dai suka gaisa da juna, har wani na tsokanarta da yanda khadija ke basu lbrn ƙawarta Rabiah dai.
Khadija tace,
“baki duba ɗinkin kayan ba” ta ɗan yi murmushi tace
“ni da zan saka ma gaba ɗaya zan gani ai”
Khadija taji daɗin zuwan Rabiah sosai sai nan nan take da ita, itama kuma Rabia taji daɗin Sosai dan hargun ummin Ahmad Khadija ta kaita suka gaisa dai-dai zasu fito ne daga part ɗin Ummi suka haɗu da Ahmad shi kuma zai shiga ciki.
cak yaja ya tsaya jikinsa har tsuma yake saboda fargaba itama Rabiah tana ganinsa tasha jinin jikinta sai dai bata bari Ahmad ɗin ya gane yanayin data shiga ba har sanda suka ƙaraso inda yake tsaye Rabia ta koma gefen Ahmad tana sakin murmushin ƙarfin hali ya ɗan matsa daga kusa da ita, muryarta a sanyaye ta cewa khadija,
“kinga wanda yaso hanani zuwa Kamunnan, daƙyar na lallaɓashi ya kawoni”
Ahmad ya mata wani kallo haɗe da watsa mata wata uwar harara yace
“waye ya kawokin? tukunnama a ina kika sanni?”
Yana girgiza mata kai yana kallon Khadija
Muryasa a kausashe yace,
“ke ina kika samo wannan?” ya nuna Rabiah da yatsansa,
Fuskarta ɗauke da murmushi Khadija tace,
“kawatace dana baka labarinta itama anan uguwarku take aure” duk da bata ji daɗin yadda Ahmad yayiwa Rabia ba.
Ya taɓe baki sannan yace,
“itace ta baki wrong address kennan”
Tace “eh”
yace “Allah sarki, Sannu “
Kallon kallo Ahmad da Rabia suka shiga yiwa juna, shi yana tunanin Rabia nema take kawai ta tuna masa asiri in bancin haka ai sai da yace mata kar ta kuskura yaga ƙafarta a waje wato sai ta nuna masa bai isa da ita ba, yayi ƙwafa a ransa yafi sau dubu.
Tsaye take tana mamakin Ahmad da zantuttukansa Khadija ta gyara tsayuwarta tana kallonsu can kuma tace,
“Rabia ga yayana,” Tayi shiru yayinda take mamakin kasancewar Ahmad yaya ga Khadija, Bata gama dawowa daga duniyar tunanin ba ta sake jin Khadija tace
“Rabiah ga Yayana Kuma angona insha Allahu, shine wanda zan aura”
Take jikin Rabia ya ɗauki kyarma ta dinga kallon Ahmad da Khadija kamar wasu halittu na daban da bata taba ganinsu ba sai a yau ɗin nan .
ta ringa binshi da kallo tamkar zata zubda ƙwalla a ranta tace
“ashe aure zaiyi shine bai sanar da ita ba dan wulakancin”
Ganin irin kallon da Khadija ke binsu dashi yasa ta wayance tana sakin murmushi tace
“kai Amman fa kun dace da juna, Allah ya tabbatar da Alkhairi, na tayaki murna” ta ƙarasa maganar muryarta na rawa,
Khadija tayi tsaye sororo tana kallon ikon Allah, duk wani alamar da zata ƙarasa tabbatar mata da zarginta ta gama samu.
A kallon da takewa Ahmad ma ta hango tsantsar rashin gaskiyarsa a fili.
hanky taga ya ciro daga aljihun gaban rigarsa yasoma goge gumin dake tsattsafo masa a hankali ya juya gabansa na wani irin dokawa da sarsarfa yabar wajen.
Wata Abokiyar wasanshi da tazo wucewa na mishi tsiyar, bazai iya haƙura ba anjima kaɗan zaiga amarya sai wani binta yake, anma ko kallonta baiyi ba.
Rabi’ah ma ta kalli Khadija da yaƙen ƙarfin hali,
“kinga sis bara dai nazo na wuce”
Tace, “haba dai er uwah, daga zuwa dai?”
“eeh mana, kinga daman na faɗa miki bazan daɗe ba”
“hakane, anma dai ai kya tsaya a fara ko,”
“A’ah, ai akwai gobe insha Allah”
Khadija duk bataji daɗin yanayin da Rabi’ah ta shiga ba, hakanan dai sukai bankwana ta tafi.