MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 1 BY RABI’ATU ADAM SHITU

MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 1 BY RABI’ATU ADAM SHITU

 

 

Tafiya yake a kasa cikin gajiya da damuwa fal a ransa, ya Ragu ya kai ga inda ya nufa don ya samu ya huce gajiyar da ya-.. kwaso. Yana tafiya yana kallon mutane»: al’umma musamman wadandake bakin fama don neman abin da zasu kai bakinsu, daga nesa ya hango dan uwansa Khalil yana fama da gudama wajen dukan kosa, yanayi yana yarfar da gumi ya Kara so wajen cikin murmushi ya dafa bayan yayan nashi Sannu da kokari yayana, kai kadai ne.

Yayan nasa shi ma ya dago kai cikin kulawa yana masa murmushi ya danki hannunsa suka gaisa kana ya dafa kafadarsa yana kallonsa daga ina haka? Ya dan yi ajiyar zuciya, Yayana kai dai bari kawai a kasa na Kara so, ban da kosisi ina kofar gida Yusra ta bukaci two hundred a wajena dan kada Mama ta fahimci ba ni da kudi yasa na bata, dama na ajiye ne na je amso wani aiki, ya Ina Baba?”Baba ya je siyayyar kayan aiki a kasuwa”.

Ya dube shi “Kana mene ya ya? Yakamata Baba ya daina hawa mashin din nan yana shiga gari, kai ya dace ka je”

Khalil ya juya kai kai ma kasan ba laifi na bane Umar, Baba ba ya son zai yi abu a katse masa hanzari, tunda bai ba ni ba, na san kawai yana so ya je ya hadu da mutanensa da suka saba na kasuwa, ko ma watakila zai amso bashi”

Umar ya sosa saman idonsa “Allah ya yi mana magani, ya kawo mana sauki, Ina Bashir?” Ya fada yana dubansa”.

“Na aike shi samo mana ruwan sanyi yau ana rana”.

Umar ya amshi gudamar yana dariya “Yaya da me zan tayaka ne?”

Khalil ya yi murmushi ya amshi gudamar yana laluba aljihunsa, “Wannan ba aikin ka ba ne, ka bari sai muna bukatar disgner na kujeru sai mu kawo maka ka fitar mana a computer mai kake da bukata yanzu?”

“Duk abin da ka ba ni yaya?”

Khalil ya zaro naira dari biyar aljihunsa, ya mika masa “Za ta ishe ka?”

“Har ma na yi maka sautu”.

Suka kwashe da dariya. Dai-dai nan Bashir ya nufo wajen da da fara’arsa ya iso wajen “Yaya”

“Bash, Zan tafi ba mu hadu, yau ba makararita ka labe anan?”

Ya amshi ruwa daya ya fasa yana sha kamar yadda yayan nasa ya yi,

“Da Baba muka taho tun bakwai na safiya?”

Ya jinjina masa “Yaya Jarumin Kanina, bari na je me zan taho maka da shi.?”

-“Yaya komai ka kawo min na gode”

Ya yi masa murmushi gami da dafa kafadarsa.

“Zan maka

zabi na dai-dai da abin da kake so. Yaya ka isar min da sako gaisuwa wajen Baba, ka ce na samu wani aiki zan je na amso na Zo na tattaba, ya yi min addu’ a sai na dawo.

Ya bar wajen ‘yan uwan nasa da fara’arsa suka hada baki Allah ya ba da sã’a”

WAJEN GYARAN KAI

Ta na zaune a cikin wajen gyaran kai, an gama hada mata komai tana kwance a bisa wata doguwar kujera ta kwanta tana duban wayarta. Sanyin AC na Kara ratsa ta. Ta yi wuf ta mike-kamar wacce ta tuna da wani abin “Zan iya tafiya yanzu dai ko Mery na gaji ina son in je gida”

Mery ta yi murmushi ta ce «Zaki iya tafiya in kina sauri, dan kadan zai kara bushewa”

..In dai ba matsala Mery zan wuce gida ina da abubuwan yi da yawa ga shi ina son kai gyaran System dina, ban san ya zan yi ba idan yamma ta yi ba a hada min ba”Ba matsal. You can go”

Ta na magana ta na hada kayanta. Ta cunkuso kudi a jaka bata san adadinsu ba ta mika wa Merry “Thankyou Mery Mery ta durkusa har kasa tana godiya Yasmin ta fita daga cikin Saloon ta bude motarta tana kokarin yiwa motar key amma shiru motar taqi amsa, ta yi ta kara gwadawa tsaki ta ja. Kafin ta fito Mery ta fahimci abin dake wakana ta fito da sauri.

“Madam Lafiya?”Ban sani ba Mery amshi mukullin motar nan bakanike zai zo ya dauka, ina sauri ba zan iya jira ba.”Ta fito daga cikin motar tanä neman Tasi kowacce tasi ta zo wucewa da mutum a ciki, tana tsaye wata ta zo giftawa ta saka mata hannu kawai ko da mutum ko ba mutum a taimaka mata.Umar na cikin tasi din ya zuba ido yana hango ta direban bai yi niyar tsayawa ba, amma sai Umar ya ce “Wannan da alama a Kagauce take, ka tsaya idan hanya daya zamu yi sai ku wuce da ita tun da na kusa sauka ni”.

Direban ya fara rage gudu don tsayawa. Ba Karamin dadi ta ji ba da ya tsaya ta ce “Nan APO please”.Ya juya ya kalli Umar dake baya. Ita ma Umar din ta kalla Umar ya jinjina kai ba tare da yayi magana ba,Ta bude ta fado ta fahimci alfarmar Umar ce tasa ta shiga motar don haka ta Kara juya wa don yi masa godiya “Na gode”

Ya yi murmushi “Kina sauri na ga alama?”

“Wallahi kamar ka sani, na makara ina son Zuwa

gida, akwai ayyukan da zan yi da dama, ga shi zan Kara fitowa shi yasa ni nake ta sauri, hudu nayi komai zai zama matsala”

Ya jinjina kai “Kin yi sa’a mun yi hanya daya, duk da ni zan tsaya ne a zo a shiga da ni, sai ya wuce dake?”Ta jinjina kai “Nagode maka, Allah ya biyaka, amma me yasa ba za a shiga da kai ba, zan iya wucewa da kai?”

A’a ka da ki damu mun yi haka ne da wadanda suka neme ni, suna can suna jiran karasowa ta”.

Ta yi murmushi ta na kallonsa da ya kalle ta sai ta dauke idanuwanta, a ranta ta na cewa Very handson guy.

“Don dai ka ce haka, amma zamu shiga lafiya lau tare”.No, ba matsala fa, nima system din yara ce zan amsa na je na saita musu wasu abubuwa na dawo musu da ita, amsa zan yi kawai na juyo”.

Ta rike baki gami da fadada fara’arta. “Na gode Allah”.Kana gyaran system ne?”

Ya dan saci kallon ta “Eh ni Softwere Engencer ne, amma ina karambanin ina taba ciki, saboda yau da kullum”Allah na gode maka, Wallahi wannan dalilin yasa nake sauri, ina da system ta dauke gaba daya, ga shi da abubuwa muhimmai a ciki ka taimake ni mu je ka duba min ita mana.”

Ya yi ajiyar zuciya “Wane company ne?”

“Appelle”Me kike tunanin ya haifar da matsalar?”

“Wallahi ni dai kawai ta ki kunnuwa”

“Bana jin babbar matsala ce, bari mu je na ga ni, idan kuma sai na taho da ita kafin zuwa gobe ba matsala Wane gida ne za ka je?”

“Gidan Tsohon Gwabna kano ne Balarabe Alkali”.

Ta fadada murmushinta “Ka yi musu waya kawai ga kanan har ciki bayan gidan mu gidan yake?”

Ya kira wayarsu kamar yadda suke ta musayar waya “Ku jira ni a gida zan zo na samu shigowa area din an shigo da ni zan duba wani abu a wajen daga nan sai na zo na amsa”

Suka a jiye wayar cikin amince ta kalle shi tana murmushi Ba matsala ko?”

“Eh ya ce bai ma fito ba hakan shi ma ya yi masa dadi”. Ko ina aka shiga da an ganta ake ba su hanya su wuce har cikin gidansu. A bakin Kofar suka tsaya. Ya dubi get din gidan kansa abin kallo ne, ya yi kokarin bawa Mai mota kudi ta hana shi ta sallame shi biya mai tsoka sannan ta danna wani madanni aka bude get din. Ta yi wa maigadin sannu sannan ta gaya wa wani dake kusa da shi. “Ka shiga da shi Study room dina please Gidan yakebi da kallo yana bin wanda zai raka shi har Zuwa Study

Yana zaune a ciki wata zankadediyar budurwa ta shigo da faranti a hannunta da kuma wata jaka a rataye a bayanta, ta a jiye masa farinti da yake dauke da ruwa da kuma fruits sannan ta ajiye jakar a gefe.Ta ce ka yi hakuri tana fitowa yanzu?”

Ta fita tana rangaji, Umar ya jinjina kai wasuna jin dadi a rayuwarsu, Allah yasa basa wasa da ibadarsu. Kamar ya bude jakar don a tunaninsa computer na ciki, sái

ya gimtse bai fara ta6a komai ba daga abin da aka kawo masa ba.

Lokacin da ta shigo bai gane ta ba, don dama ba wani cikakken kallo ya yi mata ba, sannan ga rana ta taba ta, a wannan

karon ya dauka farar balarabiya ce, ne, domin ta yi wani haske ta sauya kaya wata doguwar riga ta sanya har tana jan kasa, ga shi

tana da adon wasu jajayen dowatsu. Da kyakkyawan murmushi akan fuskarta.Ka yi hakuri nabata maka lokaci”

Ta kai dubanta ga jakar “Ayya baka fito da computer ba, kuma baka ci komai bai haba kada ka yi min haka mana”Ya yi murmushi ganin ta damu da yawa ganin yadda ya bar

farintin yadda aka kawo shi ya dauki ruwan roba “Ki yi hakuri bani da damuwa da wani abu ne shi yasa, amma bari na ci kada kice ko tsoro nake ji

Ta yi murmushi “Tsoro. Ban kawo haka ba, saboda na san ka saba ziyartar inda baka sani ba a garin nan Ya jinjina kai “Kin fadi gaskiya”

Ya dauko jakar ya bude zip din ya jawo laptop din ya bi tada kallo, ya jinjina kai domin Karshen Apple ce sau biyu ya taba aiki da irin ta. Ya zaro ya danna wajen kunnawar bata kawo ba.

“Kaga ni haka nan”.Ka da ki damu ba wata babbar matsala ba ce in sha Allahu

watakila switch din ne Allah yasa dai ka da ta kai sai an tafi da ita”.Ya zaro wata karamar sukundireba ya fara kwancewa, yana

cewa “In sha Allahu, yadda ta rintse ido tana son ganin abin da zai biyo baya yasa shi yi mata tambaya “Shin kina da aiki mai

muhimmanci a ciki? Wallahi kamar ka sa ni, ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba

a yau”In ma da matsala zan iya cire miki Hard disc din ki saka a wata computer ki yi amfani da ita, sai dai ban san a in da kike serving ba”.

“Kai dai ka da ka karaya Allah yasa ta yi”

Ya kwance ta tsaf ya fara duba guri bayan ya bushe ya dan tattaba yana mayarwa ya danna sai ta kawo wani tsalle tayi tana murna. Ya fara hada mata “Nagode da sosai”

Bayan ya hada ya mika mata “To bari na je ka da su ga ji da Ta yi saurin dakatar da shi “Ka dan jira please”Ya dube ta, “Zasu damu in suka ji shiru, musamman akwai … mai yi musu aiki saboda irin wannan rashin cika alkawarin’ suka

neme ni, ka da tun farko su sare da ni”.:

•sallamarka”Kana da gaskiya, amma ka dan jira za a kawo maka Ka da ki damu aikin ki ba shi da bukatar sai an yi sallama, na gode da karramawa”A’ah ya za ka ce haka”.

Ya juyo yana dubanta “In nã saka farin ciki a zuciyar mutum kadai yana wadatar da ni fiye da wani abu da za a ba ni, na faranta ranki domin na yi miki abin da kike so, ina so ki bar kokarin sallamata domin farin cikin da na saka miki yafi sallamar tawa”Ya yi hanyar waje ta biyo bayansa “Amma ka tsare ni da abin da ba zan iya ketarewa ba, to nagode kwarai da gaske, sai ka ba ni number saboda gaba ko” Nan take yasanar da ita

ta rubuta, sai kuma ya duba aljihunsa ya ce “Kin gama ga kati na nan zai fi zama safe. Ya mika mata ta amsa tana godiya. Ya yi mata sai an jima ya juya yana tafiya. Ta jima tana kallonsa.

Bai jima da fita ba don ko Studi room din ba ta bari ba tana kokarin tattara wasu litattafanta ta ji an turo kofa.Dan uwanta ne Zaidu, da suke kira da Zaid ya shigo cikin Studi room din.

“Kina nan ashe yaya?”

Ta dago ido ta na kallonsa “Zaid ya dai?”

“Yaya Abbas ya zo yana jiran ki, yana falo tare da

Mommy”AbbasS a dai-dai warinan lokacin me yake nufi da yana nemana me zan yi masa. .

“Yaya!, me yasa kike yiwa Abbas haka kin san kuwa irin abin da ya zo da shi gidan nan saboda kawai Birthday din ki da za a yi à ranar Asabar, please yaya ki daina nuna masa’ haka mana, ko ba komai dan uwan mu shi”

* Ta dafe kai “Zaid wai me ke damunka ne, ba abin da ya hada mu da shi, da ya wuce zumuncin iyaye, kuma in dan uwana ne ma sai ya dinga shiga sabga ta, dole ne sai yasa na so shi, zuciyata taqi ta amshe shi Zaid ka fahimta bana son ko jin sunansa, ku fahimtar da shi ya fahimta mana”.Yaya ki yi hakuri mu je dan Allah ka da ki fara fusata ya ga yanayinki a rikici please yaya”.

• “Zaid! Ta daka masa tsawa. Ya yi alamun jin rashin jin dadi haka ya sosa ranta domin bata son abin da zai taba ran dan uwanta Zaid. Ta daidaita kanta “Shi ke nan je ka zan zo”

Ya yi mata murmushi ga mi da juyawa cikin farin ciki.

Tana shigowa cikin falon suka yi ido biyu da shi yana zaune yana murmushi “My Dear ina kika makale ne, zo ki zauna kusa da ni”

Da kyar ta saita jin haushinta mahaifiyar ta ta dube ta gami da galla mata harara. Ta karasa in da yake dan nesa da shi ta zauna, yana dubanta yana murmushi “Me ya same ki na ga kamar kina da damuwa”Ba ni da wata damuwa Yaya Abba me ke tafe da kai”.Maimakon ya ji haushi sai ya yi murmushi domin idan da sabo ya saba jin murdaddun kalamai daga gare ta. Ya nuna mata da hannu. “Lissafi bai kwace min ba, na ga saura kwana uku ki yi Birthday din ki, shi yasa na zo miki da duk abin da zaki bukata, sannan hall din da zaki yi taron shi ma yana karkashin kulawa ta..

“Na gaya maka Yaya ABBAS ka daina batar da kudin ka a kaina, ka barni na yi manage da abin da nake da shi, ka daina dafawa rakumi shayi, bana bukata” Ya dan jinjina maganganunta mahaifiyarta yadda ka san ta jawo ta ta kifa mata mari. Aiki ne a kaina na farantawa Dear di ta rai, in ma zuma zan dafawa rakumi ashirye nake. Idan da akwai wani abu da ka ji tana bukata Zaid”

Ya juna masa yatsunsa a hannu alamar ya kira shi ya sanar da shi.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *