MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 17 BY RABI’ATU ADAM SHITU

“Me babu wata fa a kasa, abokiyar aikina na ce, ni

ban ma yadda da ita ba, don Allah Mama ku daina”.

Ta bar abin da take yi “Wai kai me kake nufi, Oho na

gane, har yanzu yarinyar nan ba ta fita daga zuciyarka ba ko?”.

“Mama ki dinga fahimtar abu kafin ki bude baki ki yi

magana ya za a yi ace matar wani ba ta fita daga raina ba”

“Okay ai ga shi nan daga kama zancen ka gano da wa

na ke magana wadda a kalla ya ci ace ka manta da ita shekara uku”

Ya sunkuyar da kai “Mama dan Allah ku dan daga

min kafa akwai abin da nake kokarin gudanarwa idan na kammala ba sai kun yi kumfar baki ba”

“Koma dai nene ne a zuciyarka, ka tsaya ka yi

nazari akan Zulaihat, ko jiya mun jima muna magana a kanta da dan uwanka da kuma mahaifin ka”

– “Babu wani abu a tsakani na da ita Mama, haduwa ce ta aiki ba wani abu ba, ni ban san ta ba ban san halin ta ba ba kuma zan iya auren ta ba”

“Saboda waccen yarinyar ko?”

“Mama bari na je wajen Baba ba sai na ¡ira shi ba”.

Zai fita sai ga Yusra ta dawo daga makarantar

‘Islamiya, ta gaida shi za ta fara masa surutún nata ya ce “Bari zan dawo”

“Jiya wata zukekiya ta zo a mota, ba ka ga abubuwan

da ta ba ni ba”.

Ya jinjina kai “Zan dawo na ce miki”

Ta dubi mahaifiyar ta bayan ya fice “Me a kayi

masa?”

Yana shiga mota ya dauki lambar Zulaihat ya kira ba

ta daga ba, don haka ya hakura har sai sun hadu.

Wajen mahaifin sa ya je da maganar yadda za a

* Kawata wajen na su, sannan ya yi masa magana akan ya nemi Karin ma’aikata don a bunkasa harkar, mahaifinsa ya ce shi duk baya buqatar wannan maganar aure ce yanzu ya dace a yi. Har ma ya zo masa da maganar Zulaihat din. Nan ma da ya baro babu dadi don haka bayan ya idar da sallar isha’i gida ya nufa. Sai dai lokacin da ya shiga wani titi da bai da

hayaniyar motoci bai sa ni ba mota na biye da shi tun da ya bar kamfani sai a dai-dai lokacin wata mota ta zo ta sha gabansa. Ya fito da niyar yin magana wasu Karata uku suka shiga cikin motar sa, suka wani garjejen kato kuma ya zagayo ta bayansa, ya toshe masa fuskarsa da wani farin kyalle tun yana turjiya har ya daina.

Bai ta shi farkawa ba sai da kusan tara na dare sannan

ya bude idanunsa. A cikin wani gini ne wanda ba a karasa ba da alamu sama ne sosai don yana hango fitilo da dogayen gidaje daga can nesa. Ya mike zaune yana gyara wuyansa domin ya ji yana masa ciwo

Dariya ya ji a gefansa wasu karata ya ga ni su kusan

goma suna karta warin wiwi ya cika wajen.

“Kai wannan yanyan din ya farka”

Wata katuwar murya ya ji daga cikinsu wani kato ya

ta so ya yo gaba da katon cikinsa da bindiga karama a hannunsa.

Sannan wasu kattin suka biyo bayansa.

Umar ya mike tsaye yana kallon su “Malamai lafiya

me na yi muku?”

Wannan katon na gaba ya kece da mahaukaciyar.

dariya ya ce “Ka ga dan birni, mu bamu ka taba ba, maigidan mu ka taba, kuma ka san hükuncin taba ogan sama, aike zuwa lahira ne”

Umar ya ci gaba da kallon su yana tunani kai tsaye ya

gano in da suka nufa.

“A kan me gidan naku ku ka kawo ni nan, to yanzu

me ku ke nema a wajena?”

“Shegen kai, oga wannan fa yana ja”

Wani narkeken kato mai wando iya kaúri da singlet

ya yi furucin.

“Jan kunne ne yanzu amma nan gaba”

Ya daga bindigar dake hannunsa “Ba sai na gaya

maka ba, zan saka maka ita ne”

Ya dora masa bindiga akan goshinsa sannan ya kece

da dariya ya ce “In fasa maka kwanya ka huta da barazana

“Ni me na yi muku waye ogan ku”. “Ka san komai, abin da nake so da kai yadda na

ganka wayayye to ka tafi a haka, hadin kanka shi ne ka saita sahunka ka daina rawar kai a in da kake. Bakar magana daya mutuwa ce a gare ka.

“Jalaye ba shi mukullin motar sa, ka da na ji ka da na

ga ni’ Wanda aka kira da Jalaye ya cillawa Umar mukkulli

ya daki kirjinsa ya fadi kasa ya sunkuya ya dauka. Har zai tafi sai ya tsaya. Ya juyo ya dube su “Zan yi kokari na rage abin da kuka umarce ni da aikata wa ammma yana da kyau ku fahimci wane ne ni, haifaffen garin Abuja ne ni, na kuma koyi darasi daga mai gidan ku, ku gaya masa zan sauya salo”.

Wata dariya suka barke su dukan wani na cewa

shegen ya ga no. Sai da ya fice wani daga cikin su ya ce “Ba fa: abin dariya ba ne wannan, ku yi duba da furucinsa ba wai ya tsorata ba ne.

Ogan da ake kira da Ojile ya cije baki ya ce “Na

fahimci abin da ka fahimta, to amma bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne, sannan kuma ko da makaho ya ce a yi wasan jifa saboda yana takamar ya taka dutse, ka da ka manta mu ba dutse mu kataka ba, harba ka mutu muka mallaka, na fahimce shi sarai wasa wasan mutuwa yakeso a yi.”

Saboda tsananin jigata dagajiya da ya yi, ya so ya je

ofishin “*yansanda ya yi report amma sai ya kyale saboda ba shi da wata cikakkiyar hujja, dadin dadawa ba su yi masa wani abu ba.

**

Gidan Alhaji Hashim a lokacin da Abbas ya dawo kai

tsaye dakin Yasmin ya shiga, ya yi sa’a kuwa ta fito daga wanka tana shirin kwanciya bacci.

Tana tsaye ta gama shafa wa jikinta turare kwatsam ta

ji an turo Kofa, kamar wacce aka tsikara haka tayi, gefe guda ta yi ta na masa kallo lafiya

“Mene ne haka?”

Ta fada ta na zare masa ido. Murmushi ya yi, ya Kara

so in da take “Wannan kyakkyawar jikin mallaki na ne, amma saboda tsananin so da bege na hakura da shi don kawai na faranta ran ki, Yasmin har yaushe zaki dawo hankalin ki ki gane irin soyayyar da na ke yi miki, ki fahimta mana Yasmin”

Yana fada yana Karasowa in da take tsaye, ta masa da

ta ga hankalinsa ya gushe sai ta daka masa tsawa gami da ture shi gefe. Take’ ya dawo cikin hankalinsa ya jinjina kai “Yasmin wacce irin kiyayya kike nuna min shin ba ki yaba da son da nake yi miki ba ne?”

Ta daka masa tsawa “Ka fitar min daga cikin dakin

idan ka Kara taku daya zuwa in da nake zan bar gidan nan ba zan Kara shigowa ba”

Ya kidime lokaci guda “Ki yi hakuri na gaza kwantar

da hankalina ne, ki yi hakuri bari na tafi sai da safe”.

Ta na rakube jikin gado tana kallonsa har ya kai

bakin kofar sai ya waigo “An ce kin zo kamfani dazu, har kin shiga ofishin Umar shin kin je ki ba shi hakuri ne dangane da abin da ya hada ni da shiko wani aiki ya kai ki” Cikin tsawa ta ce “ka fita na ce, ina ruwan ka da mutanen da na damu da su, ka fice”

Ya zuke wata iska kansa ya yi wata iriyar sarawa

-hankalinsa ya tashi, babu yadda ya iya ya ja mata kofa.

Ya jima a kofar dakin nata sannan ya hakura ya nufi

sashinsa, yana cikin tafiyar mahaifiyarsa ta sha gabansa “Lafiyar ka kuwa dana?”

Wani irin kallo ya yi mata. Ba tare da ya ce ko kanzil

ba ya ci gaba da tafiya.

Geust dinsa ya nufa, da ma ya tanadi kayan kodimo

dinsa da kuma karuwai, take ya yi wa Zaid waya ya sanar da shi ya shigo ta baya yana nan ya yi masa babban tanadi

Ai kuwa bai bata lokaci ba ya faki idon iyayensa

bayan sun yi bacci ya gudo wajen sashin Abbas.

Washe gari saboda shaye shayen da Abbas ya yi ya

kwanta, ba shi ya tashi daga baccin da ya afka ba sai kusan karfe goma na safiya lokacin tuni Yasmin ta yi sammako ta shirya girki da kanta ta saka ‘yan aiki sun kai mata komai mota, saboda haka yana jin abin da ya wakana ya yi sauri ya shirya bai bari wasu direbobin sun tuka shi ba ya nufi company, domin a tunaninsa ta yi wa mahaifinta ne za ta kai masa A lokacin da Yasmin ta isa kamfani kai tsaye masu

aikin wajen ta nema suka daukar mata barket din dake cike da kayan ciye ciye wadda ta san Umar na bukatar su..Umar na cikin offishinsa ya kira lambar Zulaihat ya

ba ta umarni ta zo ta same shi yanzu.

Yana ajiye waya Yasmin na yi sallama. Ta ci ado na

• Kawa ta yi matukar kyau ta fito a asalin Yasmin din ta. Da mürmushi suka wadatar da zukatan junan sanan ta yi masa sallama ya amsa, da sauri ya zo ya tayata amsar kayan dake hannunta.

Tana kokarin shirya masa ya ce “A’a ai abin ya yi

yawa, bari a shirya da kaina, kallon sa kawai take yi tana zaune

• tana murmushi Zulaihat ta turo kofa. Yadda ta same su suna zaune cikin nishadi da walwala kowanne farin ciki ne a cikin ransa. Take sai tunanin Zulaihat ya dawo dai-dai lokacin da Yasmin ta ga Umar a lokacin da ya bar wajen lokacin da suke hayaniya da Abbas, tabbas ta ji ta ambaci sunansa.

“Shigo mana Zulaihat kin tsaye bakin kofa?”

Umar ya sanar mata. Ta yi sallama suka gaisa da

Yasmin ranta babu dadi ta fahimci akwai Yasmin ce a zuciyar Umar, a dalilin sun rabu ne ya bar gida ya dawo kano tsawon shekaru uku, to yanzu ya dawo sun Kara haduwa, to abin da yake daure mata kai mene ne hadinsa da ita a matsayin ta na matar aure.

Ya zama dole ta zama macen gaske wajen mallakar

Abin da take so, wannan sarari da take bawa Umar har ta kai ga ya fahimce ta ba zai yiwu ba ragon salo ne sannan kauyanci ne a yanzu

“Dear ka na kira na kana bukatar wani abu ne?”

Wata harara Yasmin ta zabga mata, suka yi ido biyu

da Zulaihat, sai ta dube shi ta ga a halin da yake ciki. Fuskarsa babu yabo ba fallasa, “Na je gida jiya, Mama ta sanar da ni kin je”

“Eh na yi suprise din ka ne, shi yasa ban nemi da ka

San zan je ba”

“Waye ya nuna miki hanya?”

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *