MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 2 BY RABI’ATU ADAM SHITU

MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 2 BY RABI’ATU ADAM SHITU

 

 

Ita kam babu abin dake cinta a rai har ta manta a gaban wa take ta gabza masa rashin mutumci idan ta ji yana cewa da ita dear wannan kalmar yasa ta mike ta fice ta koma bangarenta.

Ai kuwa Abbas na barin gidan Mominta ta bi bayanta “Wai me yasa kike yi wa yaron nan haka, don ya nuna yana kaunar ki, Abbas da kowa ‘yake mararinsa ace kin zauna yana mugun son ke kina wofintar da shi”Mommy bana son Abbas, wallahi bana kaunarsa, ku daina Kokarin kakaba min shi domin kamar kuna so ku rusa rayuwata ne”.

Da ta ga abin da gaske ne sai ta fara da lallashi ta dafa kafadarta “Haba ‘yata, mene ne Abbas ya rasa, kyau, dukiya Mahaifin Abbas shine mai gidan mahaifin ki, alfarmarsa mu ke ci

“ya ta idan har kika ce bakya kaunar Abbas…

“Sai mu tsiyace, sai mu rasa alfarmar da muke samu daga mahaifinsa”

Ta fada a kufule ta bar jikin Mommy din nata ta yi taku biyu zuwa window

“Mommy Da kyawu da dukiya ba su ne abin nema a wajena ba na zabin abin da na ke so, ba zan zabi Abbas a matsayin so ba, bana kaunarsa, na tsane shi, ki ga ne mana, ni shi yasa kodayaushe na fi son Daddy shi ba zai taba matsa maka akan abin da baka so ba”

“Ya ishe ki ya ishe ki”. Mom  ta jinjina kai ta kufulu iya kufula. Ta fice daga cikin daki da sauri

Yasmin ta zauna a bakin window tana kallon sararin tsakar gidan, maganganun Momy na Kara bata mata rai.Bana sonsa kuma da na aure shi gwanda na mutu” Ta fada a sarari,

Zaid da ya biyo bayan Abbas har motar. Sun yi shiru na dan lokaci Abbas ya ce “An yi kuwa Zaid ka na min bincike yadda yakamata, ya za a yi ace babu wani wadda Yasmin take so, dole ka Kara kokari ka yi bincike sosai ka gano min, saboda ba zai yiwu taqini ba alhalin babu wanda yake hore mata kunne”Yaya kullum ina sanar da kai gaskiya ban tada boye maka ba, ni ban taba ganin yaya tana zance da wani ba, ko a waya take magana da kawayenta kawai take waya su ma din sai ta jima, bata neme su ba.Abba ya jiniina kai “Ni ma a nawa bangaren kullum na saka a saka min ido a kanta waye suke tare amma babu wani labari, to me yasa bata so na ne, Zaid ban hadu ba ne?”

Zaid ya yi murmushi ya ce “Karshen haduwa yaya, ina jin ko auren ne bata so”.

“Ba haka bane Zaid, amma ka ci gaba da saka ido, zan gano koma mene ne, kuma Yasmin tawa ce ni kadai babu wadda ya isa ya raba ni da ita.”

“In sha Allah yaya”Abbas ya zaro wani abu a cikin leda ya mika masa, “Ka bi a hankali ka da ka bari su ga ni. Zaid ya soke a cikin aljihun rigarsa, har zai fita daga cikin motar ya ce “Ga wannan, ka ji dadin ka

Ya wullo masa rafa dubu dubu, «Zan neme ka in na samo mana ababen hutawa ka ji dadinka Kanina”.

Zaid ya jinjina kudi “Ina godiya big yaya sai na ji kiranka”

Abbas ya ta shi mota ya fita daga cikin gidan ransa a matukar bace “Ban ga abin da zai hana ni auren yarinyar nan ba, koda kuwa wanene a kasar nan yake sonta na fi karfin wani ya kasa ni wajen diya mace, duk alfarmarsa bai kai ni ba, duk dukiyarsa bai kai ni ba takama da jiji da kai da izza, idan iskanci ne kowane dan iska a bayana yake, tabbas idan wani ne yakeshige mata, tabbas zan hallaka shi na binne sirrin a cikin kasa.

GIDAN SU UMAR

Umar bai isa gida ba, sai da ya sayi wasu muhimman abubuwa da zai kai gidansu. A lokacin karfe takwas ya rufe shagonsa, sai da ya tabbatar ya hada gyara sannan ya táho da su gida don idan ya ta shi da safe ya mika musu. Ba sai ya biya shagonsa ba.

• Kamar kullum duk bayan isha na duniya zaka samesu a cikin gidansu suna zaune suna hira, ya riko wa kowa ta sha salalar dan abin da ya rike na deposit din gyaran da ya amsa.

Khalil ya fara hango shi a lokacin Yusra ta na wajen tana kwashe kayan da ta yi shanya, “To fa da alamu dan uwa yau yana cike da nishadi ya kasa rufe bakin. Su duka suka dubi in da Khalil din yake kallo Yusra dake daf da shi ta suri kayan dake hannunsa. “Yayana me ka siyo min?”

Da fara’a ya dube ta amma ya kagu ya bawa yayansa Amsa, da kuma yiwa iyayensa sannu da gida.Ya za a yi baki ya rufi bayan na siyowa Yaya abin da yafi so”

Ledar kayan da aka siyo tana hannun Yusra°ta hana kowa sai duddubawa take yi. Mama ta hau ta da fada. “Wañnan yarinyar wane sako ta aike ka da shi ne da take ta faman lalube?”

Baba ya ce “Yusra ba zaki gyara halin ki ba ko?”

Yana murmushi ya ce “Ku kyale ta, iyaka nata rabon za ta dauka ba za ta dauki rabon kowa ba, Baba sannu da dawowa”. Ya jinjina kai “An ce ka je da safe dafatan komai lafiya?”Komai lafiya Baba. Mama dafatan an yi tuwo mai

dan karen dadi”Ta na murmushi ta ce “Zolaya kake yi ke nan aikuwa tuwon na yi

Saboda sun san shi da rashin son tuwon tsiya duk da cewar baya nunawa, amma sun fahimci hakane saboda duk ranar da a ka yi tun lokacin kuruciyarsa da in har za a yi tuwo a gidan to zai kwana da yunwa ba tare an fahimci hakan ba.”

Ya dubi Yayansa yana murmushi “Wai da gaske”

Khalil ya yi murmushi “Mama zolayar ka take yi, tun da na gaya mata aiki. ka tafi ta ce to bari ta yi maka mutuniyar taka, shinkafa da wake ne”

Ya fadada fara’arsa “Ka dai yi sallah ko?”

Baba ya katse shi, “Na yi sallah Baba, na samu jam’i a hanya kawai na sauka na bi su, don na san kan na zo gida takwas ta wuce

“Ya yi kyau, Allah ya yi muku albarka”,

“Amen Baba”Yusra na ta faman kicin kicin da leda Bashir ya fito daga falo ya ce “Yaya na kai maka ruwan wankan ka “Good boy, da girman ki ba ki san abin da zaki yi ba,

Kanin ki daga jin sallama ta ya mike zuwa yi min abin da yasan « shi zan yi” Ta yi dumu dumu da sweet din da ta ciro wacce ta

san ma ita ce ta ta, tun kan a ba ta. kowa yasan abin da aka siyo masa a gidan.

“Jeka ka dauki tsarabar ka, ka ji kani na”

Daga nan ya shiga sashinshi don watsa ruwa ya kuma fito a yi zaman hira Akwai Tsire wanda kusan na dubú uku ya siyo wannan na kowa da kowa ne, sai kuma tsarabar kowa ta daban. Don haka ba a fito da tsiren ba sai an dauko abincin dare. Yana watsa ruwa yana jin wani nishadi a cikin ransa yana tunano abubuwa da suka faru a yau, kai tsaye kwakwalwarsa ta tuna masa da katafaren gidan da ya shiga, dakin karatu ne kawai. Ya jinjina abin a ransa. Yaran hutu suna more rayuwa Allah ya ba shi dama yana so ya faranta ran ‘yan uwansa, yadda suke kokarin daga rayuwarsa yana so ya biya su da dukkan karfinsa. Ya fito daga wanka yana mamakin yadda Yasmin ke Zuwa cikin ransa a dan kankani lokaci, yarinyar bata da girman kan kai da jiji da kai kamar yadda yake tsammani “ga ya’ yan masu kudi. Yanayin da take ba shi hakuri yake tunawa, dagaske har cikin ranta take hakan.

Ya saka kaya mara sa nauyi domin zuwa cin abinci da iyayensa yasan shi kadai suke jira.

Ya dawo cikinsu, yayansa yana danna waya a

hannunsa ya lallaba yana lekawa, ashe game yake yi mai miciji, iyayen suna kallonsa shi yayan na sa Khalil da yake kishingide bai ma sani ba sai da ya ji hirarsu ta tsaya ya dago kai sai caraf ya ga dan uwansa Umar a kansa yana kallon wayarsa.Kai yaya, maimakon na ga abin da nake tsammani sai na ganka kana game, wai yaushe za ka fara zuwa hira ne’Umar ya dafa kafadarsa ya zauna kusa da shi. Khalil

ya jinjiria kai ya ce “Kai nan jira kake ka zo ka kama ni ina hira da wata yar, neber Ya fada cike da korari. Murmushi Umar ya yi ya ce,

“Dadina da kai cika baki ranar da wata za ta kama maka zuciya ka daina zaman hirar daren nan damu, ta na nan zuwa yaya”.

•Za ta jima bata zo ba, ka shiga ka shanya, mu muna so mú ci abinci ka bar mu a nan zauna ni mu ci ka da ka ‘ishe ni”.Ya dubi mahaifiyarsa ya gyada kai “Mama kuna ji fa, sai yaushe za ku rabu da katon gwauron nan ne?”

Mahaifinsu murmushi kawai yake yi domin a kodayaushe idan suna zaune ana raha irin haka wani farin ciki ne . yake mamaye shi, tabbas Allah ya ba shi iko ya*cika burinsa na zamar da yayansa tamkar abokanansa, jansu a jiki, da kuma koyar da su dukkanin abin da yake so, tsakanin su ba za ka ce yaya da

“kani ba ne idan suna zolayar juna, haka ma kanwarsa yadda suke ji da ita suke kula da ita suke kishinta, ko yanzu ya koma ga mahaliccinsa yasan cewar ya bar bayan da zasu amfanar da iyalinsa.

•Umar shi ne mutum na farko da yake da zuciya irin tashi, domin Umar na iya toshe kunnuwansa ga dukkan wani abu na rashin jin dadin da yayannasa yake masa a lokacin yarinta, har

-Allah ya kawo girmansu suka daina samun sabani. ta bangaren Khalil. Babban abin da yake tsoro a yanzu bai wucewa guda daya ba, Yusra, Yusra ita ce ya daya mace a gidan, bai sa ni ba ko gata ne ya yi mata yawa ko kuma son rai ne irin na “ya’yan zamani.

Yusra na da son rai da son zuciya da duban abin da bata da shi ta so ta mallake shi,

Ta na saka yayyanta a gaba a duk lokacin da taga’ wasu kawayen nata da abu ta ce ita ma sai an yi mata, basa gajiyawa da hidimarta ita kuma ta kasa dannewa ta sauya dabi’unta. Sukan hana shi yi mata fada akoyaushe suna cewa ‘ya mace ce ita, dole a yi mata abin da take so domin in ba su yi mata shi ne babbar matsalar, basa bukatar watarana ta zo ba tare da suna da abin da zasu yi mata ba. Haka suka wanzu suna dariya suna cin abinci. Har” tara ta raba Umar ya fita don siyo musu ruwan sanyi, da kuma kaiwa abokinsa Jabiru ziyara don yau sun rabu tun safe ya kira shi ya sanar da shi kuma yana so su hadu don haka ya fita domin su hadu. Ya zaro wayarsa ya duba, ko za ta kira wayarsa bai ga

kiranta ba. Ya ja wani dogon tsaki. Me na dauki kaina da waccen kyakkyawar yarinyar za ta kira ni a yau, shi da Kara haduwa da ita sai dai idan computer ta samu matsala ko kuma shi ke nan daga yau ba zamu sake haduwa ba. Yusra ya fadi sunan’ yana murmushi. Wata kila mu hadu wata kila kuma shi ke nan mun rabu ke nan

*********

*Yusra tare da iyayen ta a bisa dinning din cin abinci su hudu ne sai masu yi musu hidimar aikace aikace a gidan wadda kokarinsu su hada table din cin abinci.Yasmim ina lura dake akan abin dake tsakanin ki da Abbas, ki san me kike yi bana son kina wofintar da shi a gaban mutane?.

Ta dago ta dubi mahaifiyarta ta daina cin abinci ta nade hannuwanta a kirji. Mahaifinta ya dubi Mahaifiyarta Sailuba cikin alamun bai ji dadin hakan da ta yi ba. Sannan ya mayar da kansa ga yarsa Yasmin.Wani abu ya faru ne?’

Ta kada kai “Ban sani ba Dady”.

Hajiya Sailuba ta harareta “Alhaji kana daurewa

yaran nan gindi bai dace ace ta na nuna kiyayyarta akan mutumin da su ne rayuwar mu ba, bai kamata abin da take yi wa Abbas ba”

“Me ta yi masa, shine amsar da kawai zaki fada min”Ta nade hannu Duk yadda yake nuna soyayyarta ba To ba ta son shi, ko akwai wani abu da ya zama dole, ta sa shi ya so ta ne?, kuma daga yau ka da na Kara jin kin furta cewar su ne gatan da muke ciki, nema na ke a tare da su,

• yadda nake tallafawa kasuwancinsu da kuma yadda suke samun riba ta bangare na basu biya ni kaso tamanin cikin dari ba, saboda haka arzikin kowa yana cin na wani, sannan na sha gaya miki, ba zan bawa ya ta auren wadda bata so ba, ba yarinya ba ce, idan da auren kauye a ka yiwa Yasmin yanzu tana da yayan da suke zuwa makaranta shekarunta sama da ashirin, ki sarara ki ga wadda za ta kawo mana a matsayin zata aura.

Hmmmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *