Ya yi shiru domin ya rissina ta gama gano shi don haka ta daure fuska “Wai Abas wata irin gaba,ce kake so ta shiga tsakanin zaman lafiyar iyayen mu, wacce irin mummunan alaka ce kake so ka Kulla a tsakanin family biyu da suke tafiyar da rayuwarsu a inuwa daya. Abas ka fahimci zuciya, bata iya aminta da abin da bata gamsu da shi ba.
“Yasmin ki yi kokari ki cusa ni cikin ranki koda
• zuciyarki ba ta so, ni ne mafi alkairi a gare ki, domin ina son ki fiye da yadda nake son kowa a duniya hatta kaina”
Ta tsura masa ido da wani mugun kallo “Ni kuma
bana son ka, bana kuma son rayuwa da kai don haka ka rabu da ni na yi rayuwata”
Daga fadin hakan yasa ta nufi mota yana kiranta, da
yake fitattacen mutum ne a jaridu da gidajen talabijin kowa yasan
‘shi, yasa mutanen da suke wucewa a titi suke kallon su, wadanda. basu ma san shi ba motarsa kadai abar kallo ce. Don haka sai ya yi sauri ya shiga mota ya dora kai a kan sitiyari wani tukukin bakin ciki na tumurmusarsa.
Dole ya hakura ya rabu da ita a yau domin ta gaya
masa kalmar da take saka shi zubar da hawaye, tabbas sai ya mallaki yarinyar nan sai ya aure ta, kuma sai ya kashe duk wani wadda yake kokarin shiga tsakaninsu, ko yanzu ko nan gaba zai gane waye yaron da yake tsokane mata ido har ta ki saurarensa.
Lokacin da ta koma zuwa kan hanya tuni ta kira
Umar don su shiga ciki. Tun da ya shigo cikin motar yake tambayar lafiya.
“Kin kasa gaya min abin daya ha naki tsaya alhalin
kina kallona?”
A wani lokacin da suke tare da shi ya taba tambayarta
cewar “Shin Yasmin babu wani a ciki zuciyarki kuwa?”
“Akwai”Ta ba shi amsa tana murmushi «To waye?” tambaya lokacin da yake kallonta cikin fargaba. Ta dan kusance shi akan table din da suke ta na kallonsa da daradaran idanuwanta
“Umar Shi ne a cikin zuciyata, shi ne ya bude min ita, shi ne kuma wadda ya shiga, babu kuma wani da zai taba shiga cikinta domin na rufe “Kin san me yasa na yi miki wannan tambayar?’Sai ka fada
“Ba zan boye miki ba, sau tari in muna tare a kan kira
ki a wayasai ki kasa dauka a gabana, na yadda dake na aminta dake shi yasa bana kawo cewar wani ne yake kiran ki, ina uziri da cewar daga gida ne, amma wani lokacin in an kira daga gidan ki kan dauka har kice kina tare da ni, amma waccan layin shi me yasa bakya dauka in muna tare.”
Ta yi dariya “Ka yadda da ni?”
Ya jinjina kai “Na fi kowa yadda dake?’
“To babu kowa, kawai akwai lokacin da in muna tare
koma waye ya kira bana son dagawa”
Ta dawo daga tunanin abin da ya faru a tsakaninsu
kusan wata shida da suka wuce. Tabbas ta yi kuskure da tuntuni ta gaza gayawa Umar nacin da Abas yake yi mata, to me zai faru idan ta gaya masa. Ba sai ta gaya masa ba domin ba wani abin damuwa bane tunda ba son Abas take yi ba, komai me zai yi iya karsa yanzu muddin suka yi aure komai ya wuce.
Ta ce “Tunawa na yi ban siyewa su Yusra komai ba
yasa na Karasa wani shop a gaba don na siyo musu, na ce ba zan je da kai ba.
Ya juya bayansa ya ga hilimin kayan da ta siyo ga
kuma sunan shop din ya yi dariva
“To amma me yasa ki kayi haka?”
“Wannan dalilin yasa na ce ba zan tsaya ba, malam
nuna min hanya?”
Ya yi murmushi “Yau kuma Malam na koma. Ita ma
dariya ta yi. Ya ci gaba da nuna mata hanyar har suka zo gidan.Ba laifi ba za a ce da gidan su Umar basu da shi ba,duk wani rufin asiri da mai karamin karfi ya mallaka a matsayin rufin asiri suna da shi. Gida na su ne, abin hawan Babansu Mashin ne, tsohon kafinta ne kuma shahararre ga dansa ya taso da kwazo wajen aiki sun hada kai suna rufawa juna asiri da gidan haya su ke yi, daga baya suka saye shi. Saboda suna kaunar zama a unguwar an san su ana mutumta su ana girmama Malam Abubakar domin mutum ne mai dattako mai mutumci da kowa, hakanne yasa ya zama limammin masallacin unguwar saboda iliminsa.
Ta kalli gidan itan ma bata yi tsammani ba yadda
Umar yake durkusar da su sun fi yadda ta yi tsammani, gida ne mai dan matsakaicin kyau mai girma da farfajiya isasshiya. Ga tsari nakwatance.
A lokacin da za ta shiga cikin gidan tace ya tsaya. Ya
tsaya yana dubanta “Ka daina kallona?”
Ya dauke idanuwansa “Na daina”:
Ta rinse idanuwanta gami da daga hannuwanta sama
“Ya Allah Allah yasa na yiwa Surukaina su amshe ni hannu biyu biyu.
Dai dai lokacin da take haka Baba Aisha ta zo zubar
da shara tana kallon ta tana murmushi Umar yana duban Baba yana dariya. Ta na bude ido ta yi ido biyu da Baba a tsaye.
Wata irin kunya ta kamata kamar ta juya da gudu.
“Zo yake ‘ya ta ka da ki ji kunya ai addu’ a ki ka yi, kuma addu’ ar ki ta amsu, ba mu da wani haufi akan duk abin da ‘ya’ yan mu suka ga ni sukace suna so”
Ta riko hannunta Umar na gefe yana murmushin jin
dadi “Zo mu shiga, Ina Yusra zoda sauri bakuwar da muke jira ta iso”
Ita dai Yasmin kunya ta gama kashe mata jiki ta
rakube jiki tana hararar Umar.
Yusra da ta fito daga dakinta da sauri ta na oyoyo
oyoyo. Ta Kara so “Kai yaya wannan wane irin zabe ne, wannan ai ka wuce gona da iri”
“Au haka zaki ce kanwata, kin manta irin yadda ‘yan
mata suke rushing a kaina, ni ne na wucé gona da iri ko dai ita
“Ka ji yaya, yaushe matan suke rushin akan ka, bayan
kowa cewa take yi baka sakin fuska. Antina wai ya a ka yi kuka saba da shi, tsoron mata ne da shi”
Yasmin ta galla masa harara. Baba ta fita da sauri don
yin wani abu a nan ta samu ta na bawa Yusra amsa. “Dagäske kike yi kanwata?” “Wallahi Anti Kawaye na tsoronsa suke ji, cewa suke
yayana da mai fara’a da mara fara’a, ki gaya min ya aka yi kuka saba?”
Yasmin ta yi murmushi ta ce kin san ya a ka yi ne
hmmm min ya yi, ya dinga bina ko ina na je sai ya bi ni”
“Kai yayan?”
“Kan wata ba za ta taba yadda dake ba, ko Yusra kin
“- yadda”
Ta kalli Yasmin ta ce “Kai Yaya ko Sarki zai bi
yayanta na yadda da ita”
Suka kyalkyale da dariya “Yusra Mama ta kwalo kira
da Yusra ta fito waje ta fara lekawa dan ta hango mota a waje ko dai a mota ta zo, to yar waye wannan daga ni gidansu masu kudi ne, ko kayan da ta sanya sun nuna hakan.In saka ka aiki?”
Ta tambaye shi yana murmushi yana dubanta “Yau
gaba daya hidimarki zan yi, me zan yi miki?”
“Ba zan iya tashi daga nan ba duk ka gama bani
kunya da ka ga Baba ta fito ba sai ka tabo ni ba shi ne ka yi min shiru”.
“Na ji dadi da ta fito ta gan ki?’
“To amma ba dadi hakan, amma zan rama?”
“Zaki rame dai”.
“Ta mika masa mukkullin mota “Bawa kanwata ta
dauko kaya a motar wallahi ka ba ni kunya ba zan sake sosai ba Ya yi dariya “Kin canza shawara ke nan
“Da me?”Maimakon ni kin ce Yusra”,
Ta yi dariya “Ka fiya wayon tsiya wai kai kana shiga
cikin zuciyar mutum ne?”
Murmushi ya yi ya ce “Taki zuciyar tawa ce, ta wa taki ce bahaka bane”.
Ta yi dariya tana kallonsa shima murmushi yake yi,
amma da ya ga ta kura masa idó yasa ya ce “Mene ne?”Kun burge ni, Allah ka da ya hana ni shigowa cikin
wannan family duk abin da zai hana Allah ya kawar da shi” “Ameen Ameen Yasmin babu ma abin da zai haña ki shigowa cikin mu, iyayena suna son ki, kuma zasu ci gaba da son ki, ki daina dari-dari da ni”.
Ziyarar farko da Yasmin ta kai gidan su Umar wadda tun daga Wannan lokacin ta ke kokarin zuwa ko yana nan ko bayanan sau tari sai dai a yi masa waya ace Yasmin tana gidan.
Shakuwar sa ta kai ga kokarin zama miji da mata,
Umar ya’ mayar da hankalinsa gami da neman abin da zai yi iya bakin kokarinsa wajen auren Yasmin, tare da ita suke tsara komai. Da ayyukansa da kuma taimakon da iyayensa da dan uwansa ke masa ya tara kudi sama da dubu dari takwas abin da yake so ya yi mata laifen miliyan daya saboda darajarta ta wuce ya yi mata abin na karanci, cikin ikon Allah yana samun ayyuka sosai wani irin bude ya gindayowa rayuwarsa duk da cewar ya fi mayar da hankalinsa akan samun aiki da kungiyoyi ko manyan kamfani domin gwamnati duk in da zai nufa da takaddunsa basa su sake su ba shi aiki ba domin neman irin su ake ruwa a jallo, ya riga yasan da haka ko a lokacin da suke karatu sau tari ana cewar dan waye shi shin an tsaya masa ne akan samun aiki har yake fata lokacinsa akan zama Engeneer na softwear shi kuma ya tafi a cewar zai zama ne saboda yana samun aiki a hannu a hannu.
Kuma cikin ikon Allah yasamu babu laifi.
Bai taba tunanin mayar da hankalin kan samun aiki
ba kamar haduwarsa da Yasmin, yana ganin yar masu hali ce kuma ta na kaunarsa donhaka yake kokarin ganin ya gini rayuwarsa da fadi domin ya rage ta da abin da ta baro a gidansu. •
Yasamu aiki a yanzu sai dai maganar da ake yi masa
a kano ne, kuma albashinsa dubu dari da hamsin sannan kamfani ne mai tasowa, abin da yakegudu karyewar Kamfanin. Don haka ya kore aiki domin a cewarsa ya kan samu fiye da hakan a watan duniya a wajen aikace aikacen bankuna manyan kamfani matsalar kawai aikinsa wataran akan jima ba a samu ba, wataran kuma in aka samu sai aikin ya rincabe masa. Suna zaune a can bayan gari kamar yadda suka saba a karkashin bishiya motar ta na gefe sun shimfida katuwar darduma ga kayan alatu a gabansu suna amfani da shi a duk lokacin da suka bukata,
Hmmmm