Ta ce “Kai ma”.
Duk suka yi dariya ta daga hannu kiran akawo musu
abin sha.”Yasmin na ji dadi haduwa dake, kuma ba na fata haduwar mu ta zama ta karshe a rayuwar mu”
Ta na kallo cikin idanuwansa zuciyarta na habaka da
soyayyarsa, ita kanta ta yi mamaki da Raunar sa ta shiga ranta lokaci guda,
“Am.. Akwai wani sirri a zuciya ta, ban taba sanarwa
• da kowa ba, in za ka iya saurare na ka kuma rike min sirrina yau zan fade shi”
Ya gyara zama. Dai dai lokacin da aka ajiye musu
lemoka da dan abin tabawa.
Ya gyara murya ya ce “Kunnuwana a bude suke da suji, sannan zuciyata ba za ta gaza daukar nauyin sirrin ki ba,Yasmin ki gaya min”
Suka hada ido lokaci guda suka kawar da kawunan su
gami da murmushi “Ban iya so ba, dalilin da yasa idan mu kasamu sabani da dan uwana na kan kasa bacci, na kasa ci na
•kuma kasa sukuni kwata-kwata har sai mun shirya”
Ya yi murmushi gami da jin sakon ta “Haka
yakamata zumunci ya kasance daurarre ba yasasshe ba”Ta iinjina kai “Yana wahalar da zuciyata, domin baya jin magana, na sani akwai wata rayuwa bayan ta cikin gida, dole watarana zan samu wani na dora masa ragamar wannan soyayyar domin na zauna a inuwa daya, shekara da shekaru na gaza tsayarwa zuciyata waye zan rayu da shi ba mai damuwa kamar dan uwana ba, wadda ba zai dinga sani damuwa irin haka ba, Umar damuwa na wahalar da ni burina farin ciki”.
Ya gyara murya “Yasmin yardar farko tana ga
idanuwa, sannan amincewar juna ta na ga yanayi, yanayi shi ne abin da hankali ya amince da shi. Me ki ka fahimta dangane da yanayi na, sannan me yasa ki ka zabe ni a matsayin wadda zaki bawa wannan aikin”.
“Me yasa kai kake da wayo ne?’
Ya yi dariya “Saboda Abin da yake cikin raina shi ne
a naki, Yasmin tun ranar da na dora ido a kan ki na ji ina son ki, babban abin da ya dame ni rabuwar mu, ina jin a raina ba zamu Kara haduwa ba, na kasa bacci ne saboda tunanin haka, na bawa abokina labari na hadu da wata na, ji ina son ta, sai dai ta fi
Karfina na san ba za ta taba so na ba”
“Wani dan digon hawaye ya zubo mata zuciyarta ta
karya “Me yasa baka fahimci halin da na shiga ba, me yasa baka ga soyayyarka a kwayar idanuwa na ba”.
“Na ga ni, amma na kasa amincewa wata kamar ki zata so kama ta”
Ta goge kwallar idanuwanta “Za ka rike min sirrina,
za ka rayu da ni komai wuya komai dadi Umar?”
“Wadannan kalaman nawa ne ba naki ba domin ni ne
wuyar kece dadi, saboda ni ba kowa ba ne, kece kowa har na tafi tunani yadda zan maye miki gurbin halin rayuwar ki”
Ta girgiza kai “Umar ka na da abin da za.ka maye
min fiye da shi, babu abin da nake so nake buri face farin ciki, shi ne kadai burina a rayuwa ta shin ba zaka taba barina ba, za ka rayu da ni kamar yadda zaka rayu da kan ka”
Yasmin ina matukar son ki, so mai zafi fiye da yadda
kika ji ni a rayuwar ki, na amince na dauki alkawari idan har na ci amanar ki na yadda amanar Allah ta ci ni”Na baka duka rayuwata daga yau Umar”
Umar ya amshi ta yin da yake nema a cikin
rayuwarsa, wadda hakan shi ne asalin faruwar bakin ciki na rayuwa da kuma farin ciki.
Soyayya tsakanin Yasmin da Umar ta kai ga suna jin
ba zasu iya rayuwa in ba juna ba, soyayya ce mai matukar sukar zuciya da wannan ciwon na su bai tsaya a nan ba sai da ya kai yana taba rai da ruhinsu.
Babu ranar da Yasmin ba za ta gayyaci Umar zuwa
wani waje domin su huta ba su yi hira, har. ta kai ta kai dauke su a mota su nufi hanyar fita daga Abuja su samu wani waje mai kyau su danna cikin jeji su samu waje su share su saka kafet su zauna suna hira. A cikin irin ranukunne watarana
“Umar kana ina ne?”
“Ina gida Yasmin”
“To ga ni nan.”Ta sanar da shi ta yi saurin mikewa dan ta yi shirin fita ta na shiryawa mahaifiyarta ta shigo ta same ta a dakin ta.
“Yasmin Abbas na jiran ki a falo”.
Ranta ta ji ya baci to amma sai ta dauke damuwar domin ta san babu wadda zai tilastawa rayuwarta, don haka ta ce wa “Mom me zai yi min ni fa Mom kin kasa fahimta ta na tsane shi wallahi ko ganinsa bana son yi”.Ta harare ta, “Wai me yake damun ki, duk garin nan wa zaki samu fiye da Abas din mene ne matsalar ki da Abas”.Ta dubi Mom din ta cikin Karfin gwiwa “Bai yi min ba, wannan shi ne kawai ba na Kaunarsa wallahi na tsane shi’Hajiyasailuba ta dafe kai cikin takaici “Wai kina nufin yaron da kike waya da shi kike so ki ce shi ne wadda ya yi miki Yasmin, mai gyaran computer Yasmin wannan wane irin abin kunya zaki jawo mana Yasmin”.Tun lokacin da mahaifiyarta ta nufi sashin Yasmin don kiran Yasmin Abas ya biyo ta a baya ya rabe a bayan kofar, don haka yana jin duk wani abu da su ke tattaunawa.Mom komene ne shi ko waye shi ni ce zan rayu da shi zan zauna tare da shi don Allah Mom ki kyale ni na yi rayuwar da tafi wa zuciyata, kamar yadda kowa ke yi, Allah bai halicce ni da soyayyar abin duniya ba, saboda haka ba na kaunar na siyar da kai na da abin duniya baidame ni ko a ina ne ni zan rayu da shi shi na ke so”.
Da bacin rai ta fita daga cikin dakin ko da ta dawo ta
• same shi a falo a zaune ya yi tamkar bai ji komai ba. Ya yi murmushi ya dubi Haiiya ya ce bayan ya duba agogon* hannunsa. Ya tabbatar ba za ta fito ba.
“Mom me ke faruwa ne na gá kin fito cikin facin
rai”.Ta zauna ta hada tafukan hannayenta a fuska “Karka damu da na, duk yadda zan yi sai na yi domin na ga ka samu Yasmin, na san kana son ta sosai kuma na san ba za ta taba samun wadda ya fika ba”
Ya yi shiru can kuma sai ya ce “Na ji shiru ina bros?”
“Ya tafi makaranta” “Agaida min shi idan ya dawo a gaya masa zan zo da daddare”.
«Zan gaya masa Abas, amma abu mafi muhimmanci
ka kwantar da hankalinka”
Mota ya shiga ya bar cikin gidan sai da ya yi nisa
sannan ya dakata, adai-dai lokacin da ya tuna abin da mahaifiyarta ta ce masa cewar “Shiri take yi na san fita za ta yi amma bari na gaya mata kana iranta.”
Yasan dole za ta fito daga cikin gida yanzu don haka ya dakata. Babban abin da yakekokarin sani waye saurayin nan, a da a na tayi masa: Karya ba ta da saurayi amma yanzu ga shi a sadaka yasa ni, mai gyara computer. A yau dai sai dai ba zasu hadu da shi ba, amma zai kashe dukkan harkokin kamfani domin ya ga waye wannan sannan yasaka a kashe shi.
Lokacin da ya hango hancin motar ta ya leko ya
jinjina kai wato hakansa ya cimma ruwa, kamar yadda ya yi zargi ba hanyar office din ta ta nufa ba, saboda haka ya juya motar sa.
A lokacin mahaifin ta yana saman bene ya hango duk abin da ya wakana don haka ya dauki wayar ta ya kira.
“Ina zaki je ne kike sauri haka?”
Ta yi mamakin tambayar kuma saboda rashin gaya
masa da bata yi ba cewar za ta je gayar da iyayen Umar ne yasa tayi masa karya cewar “Zan je gidan kawata ne”
In dai dan kawar ta ne babu wani abun damuwa, inma ya bi ta zai ga tunanin da yake yi bai ba shi dai-dai ba ya gan shi lokacin da ya labe a bakin kofar Yasmin- yanzu kuma ya ji korafin da mahaifiyar ta take yi akan Umar da yar sa ta ke so dalili ke nan da ya hau can sama domin tunaninsa ya ba shi cewar zai bibiye ta ne ya ga waye saurayin kamar yadda ya ji tana da saurayi.Yasan halin mahaifinsa duk rashin imanin mahaifinsa yaron ya dora a kan na shi, matukar suna son abu to ko da waye zasu yi takara sai dai su hakura su janye. Akan kwangilar aiki sukan iya kashe rayuka domin su mallake ta.
“Ki kula ‘ya ta kin san yanzu Abbas yabar gidan nan”
Ta yi wa mahaifinta godiya ta ci gaba da tafiya ba ta ta shi tunanin wani abu ba sai da ta zo bakin titin da zasu hadu da Umar ta na hango shi a titi adai-dai lokacin tambayar da mahaifinta ya yi mata ta fado mata in ba ya ga wani abu ba ba zai ce ta kula da Abas ba, tabbas akwai wata a kasa. Da sauri ta dubi meror Abas ba mota daya yake hawa ba, amma ganin falleliyar motar dake biye da ita ta tabbatarwa kanta cewar Abas ne ke biye da ita.
Don haka ta na hango Umar amma ta wuce shi yana
tsaye yana dubanta, a tunaninsa ba ta gan shi ba ne ya kira wayarta ta yi saurin cewa ya katse akwai dalili. Shi kuma kokarin yake ya fahimci damuwar ta don ya magance mata ya dauka ta na cikin matsala ne.
Kokarin da take yi ta Sacewa Abas shi kuma bai
fahimci ta gano shi yana binta ba sai Kara wuta yake yana tsoron ka da ta guje masa.
Allah ya taimake ta ta samu wani shop sai ta tsaya ta yi parking ta shiga ta yi wasu siye siye da dama tana da Kudirin siyen abin da za ta jewa mahaifansa da shi.
Ta na fitowa ta dora ido akansa a lokacin bai lura da
ita ba yana can yana waya da mahaifinsa a game da rashin zuwansa da wuri ga shi abubuwa sun tsaya cak mahaifin fada- yake masa akan ya zo office yanzu komai yake ciki don yana nema yasa a soke wasù ayyuka da zasu yi.Juyowar da zai yi suka yi ido biyu ta shi ta na tsaye.Abas”Ta fada cikin mamaki. Ya ji faduwar gaba sosai amma sai ya matse “Me kike yi anan Besti”.Duk a lokacin da ya fada mata wannan sunan ta na jine tamkar ya watsa mata ruwan zafi a fuska don sai ta dauke fuskarta daga dubansa don tsabar takaici.Kai ya dace na yiwa wannan tambayar mai kake yi anan wajen na ga baka da wani abu da zai shigo da kai irin wadannan areas din?”
Ya fara kame kame “Ah no, Wata makaranta ce za a
gina…shi ne na zo”.Da kan ka kuma?”
Ta yi masa tambayar son ta kure shi.
“Na fahimta, bi na kake yi”
Hmmm