“Besti ka san me ye?”
Ya girgiza kai “Sai kin fada”.
Ta dan yi tsaki yanayinta yasauya “Yamma ta yi ga
shi dole yanzu zamu koma gida, baka jin wani abu”
Ya yi dariya “Yasmin ki watsar da damuwar nan, na
sha gaya miki fatana ace in fito a gidan ku domin na zo na dauke ki na kai ki muhallina mu yi rayuwar din-din-din”
Ta yi shiru ta na wani tunani “Na yi magana da Dady,
tun last week shi ya dakatar da ni cewar zai min magana idan ya gama shirye shiryensa.
Ya yi shiru har ya kasa magana da kanta ta fahimci yasa damuwa a ransa. “Umar ya ka yi shiru?”
- Ya dube ta ido cikin ido "Soyayyar ki da yawa a cikin raina Yasmin, ina tsoron ranar da zan rasa ki, ba ni da wata fargaba da ya wuce na rasa. Na 'san cewar na yi zire na so macen da dama ba zan taba samunta ta ruwan sanyi ba, amma kullum tunani na shi ne ta ina yakin nawa zai fara, daga gare ki, ko daga
‘ya’yan manyan da dole sun san cewar ke lebel din suce, ko kuma da iyayen ki”.
“Umar ka daina mana, me yasa kake haka ni ta ka ce
bazan taba yadda ka rasa ni ba, domin rasa ni tamkar rusa wayuwar mafi Kululuwar jin dadi na ce, ko ina zan je zan wulakanta kaina alfarma ta za ta guje takama da yangata ba zasu yi wani tasiri ba, ka daina zurfafa fata irin wannan ni takace kai nawa ne, babu abin da zai raba mu”Allah yanuna mana lokaci mafi mahimmanci a rayuwarmu tare dake, ni dai fatana ko DUK DUNIYA ZASU KI NI KADA KE KI BARNI, KO DA A CIKIN ZUCIYARKI NE KOMAI NISAN DA MU KAYI WA JUNA Ka daina karya min zuciya kana so na koma gida cikin matsananciyar damuwa please Umar ka daina
Har hawaye ni ya fara zubowa daga cikin idanuwanta.
Daga nan hirar ta daina musu dadi karshe suka ta shi
don komawa cikin gari
Kowa ya tafi duniyar tunani. Akwai abin da
mahaifinta yake boye mata kamar yadda take zato yana cikin matsananciyar damuwa mai tada hankali dalilin da yasa ke nan yaqi bayar da damar zuwan iyayen Umar, duk da ta takura dolenta ta kyale shi saboda mahaifinta na dabanne a cikin rayuwarta tana matukar son sa da kaunarsa domin shi farin cikin sa shi ne ya gansu suna farin ciki. Bai da son kansa bai kuma da son rayuwar takurawa iyali shi mai kyautatawa ne mai kuma fahimtar mutum da saurare.[expander_maker id=”1″ ]Read more hidden text[/expander_maker]
Ta dawo cikin gida ta so ta shiga cikin studio din ta
dan taba wasu ayyukan da ba ta yi ba, to amma ganin motar Daddy yasa ta shiga cikin gidan ko za a yi sa’a ya gaya mata saka ranar da su Umar zasu zo neman auren ta. Daf da bangaren dinning ta ga Mansura na kwashe kayan abinci alhalin ba a ci komai ba. Ta dubi kayan ta dubi Mansura “Ke da zan ga kuna shirya abinci yana ga kuna kwashewa ba dai har su Mommy sun ci sun tafi Bedroom ba?”
‘Mansura ta girgiza kai “Ba su ci komai ba, Daddy tun
da ya dawo ya haye can farfajiyarsa ta sama ya ce a kyale shi yana bukatar shan iska ne?”
“Me ya faru, Ina Momm, Ina Zaid”.
“Zaid bai dawo ba, Mommy kuman..”
Ba ta karasa fada ba ta nufi can saman gidan in da
far farjiya take. Yasmin ta Karasa hawa saman ta na tura kofa ta ji ta a rufe. Waya ta zaro ta kira lambar Daddy, bai amsa ba sai kawai bude kofar ta ji an yi. Suka yi ido biyu “Daddy lafiya?”
Ya jinjina kai gami da hadiyar wani madaci mai
tukuki, shigo ‘ya ta”.
Jikinta a sanyaye ta Karasa shiga cikin kujerun da
suke kewaye a wajen ya yi mata umarnin zama ta zauna tana dubansá da yadda yanayinsa yasauya.
“Daddy mai ya faru?”
“Kwantar da hankalin ki ‘ya ta, wata”yar damuwa ce
amma ta kusa shigewa in sha Allahu”
“Daddy za ka iya gaya min?”
“Me zai hana ‘ya ta, amma ki nutsu magana ce ta
kamfani, wala’ allah ki fahimce ni wala’ alla ki kasa, Yasmin wani abu ya faru a kamfani wadda na kasa sanin ta ina ya faru, Amma Allah na ga ni kuma yana ji”. “Daddy na kagu na ji me ya faru mene ne dan Allah
ka gaya min?”
“Kwantar da hankalin ki ya ta, babu wani abu da zai
faru sai da yaddar Allah, wani signing ne na yi shi, akan wasu takaddu wajen amsar wata kwangila ba bisa ka’ida ba, sannan a cikin badakalar akwai abubuwa marasa kyau da suka faru, ga wasu ma’ aikata to tunda na san ba hannuna a ciki insha Allahu zan fita kar ki damu”[expander_maker id=”1″ ]Read more hidden text[/expander_maker]
“To Daddy mai hakan ke nufi?”
– Ya kamo hannunta “Ki kwantar da hankalin ki, Ina
yaron da kuke soyayya da shi Umar?”
“Yana nan lafiya daddy yanzu mu karabu?”
“Insha Allahu gobe idan komai ya kammalu zan ba ki
dama ki sanar da su su zo a wannan satin da zai kama”.Daddy hankali na ya gaza kwanciya akan maganar da kake gaya min ban fahimci komai ba, wacce irin matsala ce?’
Ya yi shiru kafin ya ce “Yasmin ina fuskantar kamu
da EFCC da kuma hukumar ‘yansanda akan kashe mutane biyu saboda kokarin amsar wata kwangila
Ta zaro idanuwa. tana mai kurma ihu “Me”.
Ya rirrike hannayenta, “Komai zai wuce ki kwantar da hankalinki Yasmin”.
Cikin kuka take fadin “Dad ta ya ya za a yi hankalina
ya kwanta alhalin kana cikin irin wannan matsananciyar damuwar da ban taba ganin ka a cikinta ba
Ya yi shiru yana jinjina al’amarin daga bisani ya
dago ya dube la “Ta muje kasa, mu ci abinci koma ya wuce Ba ta iya zama a dinning din ba dakinta ta shiga ta dauki waya ta kira Umar don su yi hira ya dauke mata damuwar da ta ke ciki a cikin hirar ne take sanar da shi cewar Akwai labari mai dadi cikin gobe ko jibi ka gama shirin komai Besti na.
A can kuma Mahaifiyarta Sailuba ce suke tsaka da
musayar magana da mahaifinta Alhaji Sunusi kan yadda zai shawo kanta a game da rabuwa da yaron ta auri Abas.In ba za ka gaya mata ba ni ka bar ni da ita na gaya mata” Ya jefe ta, da harara, “Muddin kika kuskura ki kayi wani zance da ita akan abin da ya faru abin da zai biyo baya ba mai dadi ba ne, don haka in kin, shirya tarbarsa bismillah”
Ta yi shiru ta harde hannaye “To Jiran me kake yi da
ba za ka gaya mata ba, babu wata hanya da zamu kubuta da ta wuce wannan, mene ne abin jan tsawon lokaci”Shi ma rataye hannayensa ya yi a kirji yana tsaye yana sintiri akan faffadan dakin kwanansu.
“Ni na san wannan abin dagangan aka shirye shi, an
shirya shi domin kawai su’ samu Yasmin daga shi har uban nasu da hannunsu a cikin lamarin ni kuwa zain yi duk iya yi na na dawowa ya ta farin cikinta duk daren dadewa”.A dai-dai lokacin ta fito daga na ta sashin zuwa kiching ta hango Zainab ta na kokarin shiga kiching “Ki hada min shayi mai zafi, sanan ki sako min Shawarma daya ina caki”[expander_maker id=”1” ]Read more hidden text[/expander_maker]
Zainab ta duka cikin girmamawa “An gama ranki ya
dade”Ta juya ta shiga kiching din Yasmin ta juya dan nufar na ta sashin ba ta san lokacin da tunanin mahaifinta ya fado mata ba. ta juya da nufin tunkarar dakin nasa ta juyo. maganganu tsakanin Dad da Mom a lokacin da Mom din ke cewa “Bamu da yadda zamu yi Alhaji, yaron nan ba wani aibu ne da shi ba….
“Ni zaki gayawa Abas, tare muke da shi a kamfani
dare da rana, kin san kuwa irin mummunar dabi’ arsa, bari ki ji in gaya miki na gwammace na tafi a tsare ni a kurkuku ko nan ne zan Karasa rayuwa a can matukar rayuwar ‘ya ta za ta yi sanyi… ba zan bari ta yi rayuwa da Abas ba tun da ba son sa take ba, da zarar na gana da iyayen Umar zan yi sallama a kama ni”
“Me? Ta fada da Karfi gami da bude kofar ta shigo
cikin tashin hankali “Daddy Daddy me yake faruwa?”
Ya tsaya cikin tunanin abubuwan da suka faru.
Yana zaune a office dinsa Abas ya shigo tare da
damuwa akan fuskarsa ya ajiye masa wasu takaddun Signing din gini mai tsawon hawa bakwai wadda gwabnatin tarayya ta bayar da aikin ga Ma’aikatar JIS wadda daga bisa ni ya jagoranci Kamfaninsuna HASHIM BUILIDIN. Domin amsar aikin kamar yadda Alhaji Hashim ya umarce shi cewar sun gama magana cewar kamfanin sun amince zasu bayar da aikin ga nasu kamfanin.
Ya duba file din abin da ya ba shi mamaki babu
tambarin kamfaninsu a jiki, sannan ga singing dinsa nan na amsar aikin daga wancan kamfanin Na JS.
Da sauri ya dago kai ya dubi Abas “Me yake
faruwa?”
“Kana tambaya ta abin da yake faruwa alhalin kai ne
ka aikata shin ba kai ne ka yi singning contaract din ba
Ya bubbude papers din “Tabbas ni na yi amma abin
da ya ban mamaki ban ga tambarin kamfanin mu ba, me yake faruwa[expander_maker id=”1″ ]Read more hidden text[/expander_maker]
Abas ya jinjina kai “Mu ma abin da ya ba mu
mamakike nan, an samu aiki daga Gwabnati mai ya kai aiki JIS ta ya a ka yi aka kawo aikin su ya zama na mu, ka san badakalar dake ciki?”
Alhaji Sunusi ya mike tsaye a firgice
“Me yakefaruwa ka gaya min?”
“Ka yi singning din contract da ake bukatar bincike
akan sa”ne?”
“Bincike kamar yaya Abas, me kake shirin gaya min
“Kamfanin JIS sun yi amfani da karfi wajen amsar
contract din wadda aciki sun kashe rayuka, dalilin da yasa suka ba ka aikin ke nan saboda su dorawa kamfanin mu laifi?”
Cikin Bacin rai Alhaji Sunisi ya mike “To mene ne a
ciki muna da hujjar kare kan mu, ai ba mu gwabnati ta bawa ba su ta bawa. «To za ka iya kawo shaidar kamfanin da ya amsa daga wancan kamfanin, ko kuma za ka iya ja da Kamfanin Jis akan wannan tirkatirka”.
“Ji nan Abas ban yi komai ba sai da sahalewar
mahaifin ka, wannan takaddar da ba shaidar kamfanin BIN HASHIM ban san ya a ka yi hakan ta faru ba”.
Dariya Abas ya yi ya ce “Wannan shi ne matsalar da
ka afka babu ta yadda za a yi mu jona matsalar kamfanin mu da kai komai zai faru kai zai shafa”
Hmmm