MAI TAFIYA CHAPTER 6
Ranar wanka ba a boye cibi
Kano, Nigeria
Hindatu ce ke zaune a gaban mudubi tana kwalliya, tayi da wani maneminta zasu hadu karfe hudu na yamma daidai. A wayarta ta saka wata wakar sa’adu bori da take so tana bi da baki6
Lale hadiza lale lale hadiza yar malummai ka ga hadiza ta birgeni
Ina cikin yawona ka ga hadiza ta birgeni
Yara suna kiranta amare manya suna kiranta amare
Zama da kishiya tilas ne ba don uwargida na so ba!
Kai! Duniya tana kaunar Saadou Bori Allah dai ya jikan sa. Anya idan ta tashi aure da Alhaji Awaisu ba za ta kira yaron saadou bori ya wake su ba? Irin arzikin Alhaji Awaisu ai sai da haka yanda za ta fantama a cikin kawayenta.7
Ita yanzu duk yanda za a yi bata iya auren wanda bai tara dukiya ba, wanda ba zai gina mata tamfatsetsen gida ba da motoci na alfarma suna harabar pakin. Ya bata ko da miliyan goma ne ta hado lefe na kece raini, Allah ta tuba ina tsiya tsiya ina miliyan goma a wajen Alhaji Awaisu! Ai wuce nan.8
A cikin akwatin ajiyarta ta banki ma jiya miliyan 2 ya sa mata duk da ta ji dan sa ya kira shi daga zaria inda yake makaranta kan cewa lokaci yayi na biyan kudi kuma yace baya da. A wayarsa uwargidansa ta dau nambarta ta kira tayi mata zagin uwa da uba. Har da cewa wai8
” Halin da kika sani ni da ‘ya’yana da sannu sai kin fada! Inshallahu sai kin yi kuka da idanunki!”5
Ji wani mugun fata! Yo ita ta aike shi? Ita ta sa Alhaji Awaisu yawon ta zubar har da za a kafa mata kahon zuka? Tun kan a haifeta yake yawon bariki amma kawai kawai dan an rainata sai a aza mata jakar tsaba? Bai zai yiwu ba fa.8
Don haka ta dau aniyar auren Alhaji Awaisu ko don ta nuna wa uwargidansa ita ba komai ba ce. Da sannu zata gane wa ta zaga da sannu zata koya mata hankali.
Da wannan tunanin ta kammala kwalliyarta. Wani jan leshi ta daura ta dau komai fari ta saka. Dama bata yafa mayafi don ba zata iya ba. Ta dau jakarta kenen wayarta tayi kara. Kallo daya ta yiwa wayar ta ja tsaki, safara ce kanwarta.2
Ta san ba zai wuce roke roke ba abunda ta tsana. Ko korafe korafe wanda ita ba zata iya saurare ba kar ta makara. Ita fa tunda ta dauke yaranta ba sosai take lekawa ba, ina za ta iya? Ka je ayi ta maka dogon wa’azi kamar kai ka yiwa shedan ungozoma.9
Sai ta ki dauka. Kara kiran da aka yi ne ta dauka a fusace tace
” Safara wai menene wannan irin kira haka kamar na dau kayan wani”
A zafafe ita ma safara din ta ce
” Mai da wukar, Hajiyarmu tun jiya take kawance emergency na asibitin Nassarawa. Idan kin yi raayi za ki iya zuwa” kit! Ta kashe wayar tana mamakin irin mugayen halayen da Hindatu ta koyo.
Sai taji gabanta ya fadi dam! Daga larurar idon nan Hajiyarsu bata cika ciwo ba. Sai taji jikinta yayi sanyi da ta tuna rabonta da ta leka gidan ma ta manta. Hidindimu sun mata yawa.2
Sai ta dau motarta kawai ta wuce asibitin. Ko da ta isa sauran kannenta ne akan hajiyar suka gaisheta sama sama ta amsa a banzace. Daga nan sai ta fara borin kunya2
” wani irin abu ne haka? Saboda tsabar rashin hankali hajiyar ta kwanta tun jiya a rasa wanda zai kira ni a waye ya fada mun sai yanzu? Sai ka ce wata bare”
Babu wanda ya tankata a cike suke da ita tam!Sai suka bar ta da halinta kawai dama su suka dage a kira ta, hajiyar cewa tayi a kale ta.
Ta kara da cewa
” Bani takardar magungunan da ba a siya ba na je na siyo”
Wannan maganar ce ta sa hajiyar ta dago kai a hankali ba don tana gani ba ta ce
STORY CONTINUES BELOW
” wanene zai siyo min magani?”
Suka ce
” Hindatu ce”
Sai a lokacin tayi kokarin zama ta kalli sashen da Hindatun ke tsaye kamar zinariya ta ce a cikin murya irinta rashin lafiya
” Hindatu! Ki taso tun kina karama yar marainiyar Allah, na ciyar da ke da halal, na shayar da ke da halal, na tufatar da ke da halal, da karfin kwanjina na ilmantar da ke da halal. Amma duk abin nan da nayi miki ba ki gode ba sai kika kalli gazawa ta akan ki na wani dan kankanin lokaci! A yau ke zaki nema min lafiya da haramun? Shin idan kika min haka kin min adalci? Ki rike kudinki Hindatu, watakila ni lokaci na ne yayi. Ina miki fatan shiriya, ina miki fatan ki gane kafin lokaci ya kure miki!”14
Wadanan maganganu na Hajiya Uwani sun yi mugun bakanta ran Hindu. A gaban kannenta da suka sa mata ido suke watsa jita jita akanta za a yarfa? Ai ita ce mai haramun din? Wai me yasa sau dayawa naka shi ke maka bakin ciki? Kana talauce baka huta ba kayi arziki baka huta ba.2
Amma ta san laifin safara ita ce ta zuga hajiyarsa da sannu zata koya mata hankali. Ta ce
” Hajiya wallahi ki daina sauraren maganganun batanci na mutane akaina. Suna bakin ciki da ni ne kawai. Na sha gaya miki babban aiki na samu daga nan kuma na hada jari nake biznes na tafiye tafiye zuwa kasashe ina saro kaya. Dalilin kenen da ban cika zama ba. Amma dai kiyi hakuri”
Maimakon hajiyar ta amsa sai kawai ta kwanta abunta ta juya mata baya. Ai ita ba yarinya ba ce yaushe za a zaunar da ita ake tsara ta. Da Hindu ta ga kamar da ma an kira ta ne a wulakantata sai ta fice fuu cike da fushi. Daga nan ne ta kira karamar kanwarsu ta bata dubu goma. Ta ce duk abunda ake ciki ta gaya mata. Yarinyar ta ce tana jin yau za a sallame su ma. Ba ta bi takan hakan ba ma tayi gaba.2
A mota ma tana ta sake sake. Za ta je wajen malam a kama mata Alhaji Awaisu da kyau. Aure za tayi ko dan yan hassada su dauke ido akanta. Ga shi nan kiri kiri ana so a raba ta da mahaifiyar ta. Kai mutane ba su yi ba.2
Ta bar asibitin, har ta zo gadar lado sai taji karan wayarta. Gabanta ya fadi sosai don tunanin ko daga asibiti ne za a ce hajiya ta cika. Sai ta ga sabanin hakan. ‘Yar Modu ne . Ta yi sauri ta dauka ya ce
” Hindu kina ina?”
Ta gaya masa. Ya ce
” Maza maza bamu da nisa karaso kan titin maiduguri road ki sha kallo. Kyaun karya ai hallara! Ahayye yau naga abunda ya isheni abun zama ya mutu ya bar zani! Za a yi yakin ojuku a karo na biyu. Mu dai ‘yan mu hada ne ba ‘yan mu raba ba! Duk wacce ta raba wannan fadan ni ‘yar modu na ce Allah ya tsine ma ta!”7
Ba tayi wata wata ba ta ce
“gani nan!”
Cikin minti biyu ta karasa inda ‘yar modu yake ya fado motarta ya na cewa
” mu tsaya cak anan, ki zuba ido kofar kemis din can ki sha kallo”2
Ta buga tsaki ta ce
” Ji wani sabon salon iskanci. Ni na zata ma wani abun ne. Zan tafi wani babban uzuri ka tsare ni”
Ya kama haba ya ce
” Ke Hindu! Anya kuwa ba irinku ba ne ake bude kofar tuba gajen hakurinku ya sa har a rufe ba ku tuba ba! Minti nawa ne idan ma karya nayi za ki tsire ni? Uwar gajen hakuri! Ke idan gajen hakuri abun yi ne uwak
i ta kawo ki duniya?! Ai da garin garaje ta barar da cikinki! Ahap!”1
Abu daya ne tal ya hana Hindu mayar masa da martani zagin tsintar waken da yake yi mata. Al mustapha ta ga ya fito daga wani babban wajen siyar da magani dauke da karamar leda, a gefensa Rukky ce hannayensu a sarkafe! Suka shige wata bakar mota mai bakeken gilasai suka shura gaba.2
STORY CONTINUES BELOW
Saboda tsabar mamaki sai Hindu ta ji kamar ruwa ya cinyeta. Ta juyo ta kalli ‘yar modu da ke mata kallon hadarin kaji ta ce
” Me nake gani haka? Yau ni Hindatu me zan gani! Yar modu ko ido na ne”
Ya ce
” Ina fa idon ki..abun da yake akwai shi kika gani! Rukky ce take wasa da bakin bindiga! Duk inda harsashi ya subuce kin ga ai dole kan wani zai fada! Ahayye ana rikici a legas billahillazi har an kashe mutum dubu!”5
Mamakin Rukky da Almustapha ya kasa barin Hindatu. Ashe Rukky maciya amana ce. Ta san ita ta kwace Almustapha amma ta zauna cikinsu ake jaje? Abunda ya fi batawa Hindatu rai kenen.
Don ranar a gabanta ta karbi wasu binne binne ta ce zata taya Luba da su. Ashe makirci ne!? Ashe basaja ne! Wasanta take gyarawa taka bata na luba. Lallai ta yarda karuwa bata da amana. Amma za su shayar da ita ruwan mamaki.6
Ta kalli yar modu da kyau ta ce
” Akwai matsala, Akwai babbar matsala!”
*********************************
A safiyar Ranar da Almustapha ya farka ne a matukar gajiya. Ya yini da tunane tunanen tunkarar Rukky ya ji wani abu a kanta. Sai kuma mutanen jam’iyyarsa suka kira sa kan akwai fa mitin yau da tsakar dare.
Ba shi da wani zabi illa ya tafi can. Maganganu ne dai kan yarda abubuwa zuka dau zafi. Mafi yawan manyan manyan an yi musu kashedi da taka tsan tsan kan harkokinsu saboda abokanan gaba fa idonsu na kai. Neman dalili daya suke mutum ya tabka wani kuskure ko abun Allah wadai su yiwa mutum caa mutane su guje shi. Daga nan abu ya zo ya baci a rasa kuri’un dubban mutane. Abunda ba a fata.
Daga wannan mitin bai kwanta ba sai bayan asuba. Ya tashi karfe 10 na safe a gajiye tilis. Shi ma ba wani abu ba ne ya tashe shi sai kiran waya daga mahaifiyarsa.
Hankalinta kwance ta ce
” kwana biyu shiru kai baka leko ba idan an zo inda kake ma ba samunka ake ba. Abubuwan siyasa sun matso kuma ba a ganinku.”
Anan ya gaisheta ya kawo mata dan uzurinsa. Ta karba ba tare da ta wani damu ba tayi masa maganar wasu kudade ya ce zai turo. Sai daga karshe har za suyi sallama ne ta ce da shi.
” Ka san mahaifinka kuwa an kawo shi yau kwana biyu daga Niamey jikinsa yayi tsanani ko maganar kirki baya iyawa? Da kyar dazu na sa masu aiki suka shiga suka dan goge masa jiki ko ya dan ji dadi. Amma fa bai iya daga komai”
Wani irin abu ne ya tasowa Almustapha tun daga sassan jikinsa zuwa zuciyarsa ya tokare. Mahaifiyarsa ce kawai zata iya masa haka ya kale. Ubansa yana kwance irin haka sai yanzu zata gaya masa? Har take masa wasu zantattukan kudi? Wani wata irin zuciya ce da ita.3
Bai ma iya amsata ba kawai katse wayar yayi ya tashi ya shirya ya fice daga gidan. Gidansu ya wuce kamar yanda ya saba ya tardata a falo tana kallo. An kawo mata abun karin safe tana karyawa.
Gaisheta yayi sama don kar ma ta tsare shi da wata hirar ya wuce sashen mahaifinsa. Abu daya ne ya sa ya tsaya cak! Wani irin wari ne yake busowa da ya rasa na menene. Ya tsaya yana ta dube dube a falon amma bai ga komai ba. Sa’annan falon ma ba kowa duk tarin abokanan Alhaji da ke zama a babban falo babu alamarsu. Bai ga wadanda ake ce suna kulawa da shi ba. Wai meke faruwa ne?
Karasawa dakin mahaifinsa da yayi da tura kofar shi ya sa ya ji wani amai ya taso masa. Wani hamami ke fitowa ba kuma daga kowa ba sai daga Iliyasou Tillaberi.2
Da sauri ya karasa cikin mamaki yana taba baban nasa sai a lokacin ya lura kamar bacci ne ya fara daukan sa, an canja masa kaya zuwa jallabiya sai dai dakin idan ban da doyi ba abunda yake.
STORY CONTINUES BELOW
A fusace ya fice ya tarar da Hajiya Hadiza ta dauki wani yankakken tufa ta kai bakinta. Idonsa ya rine yayi ja saboda bacin ran ganin halin ko in kular da aka bar mahaifinsa ya ce
” Mummy menene haka wai? Ashe haka jikin abbanmu ya tsananta shi ne ba a kira ni ba? Ga dakin duk wari ba a gyara ba amma ba shi abinci ya ci kuwa? Ina masu aikin ne wai..in dauke su aikin gida su tsaya suna min sakarci! To yau kowa zai bar aiki tunda ba gidan ubansa ba ne! “
Ya fara kwala musu kira cikin bala’i. Ta kalle shi a lalace ta ce
” Duka na ka zo kayi kenen? Tun yaushe ake tsaye akansa? Ko kuwa don ba shi da lafiya sai kowa ba zai yi uzurinsa ba. Ita khulsomou da jiyyarsa ta isheta ta zo ta watsar shi anan wa yace tayi ba daidai ba? Tun da ya zo shekaran jiya ake hidima da shi, amma fa wari daki bazai daina ba don abun daga jikinsa ne. Wa zai jura?”
Kawai sai ya rasa me zai ce mata. Mahaifinsa yana da tarin laifuffuka akansa amma ba zai taba barinsa a haka ba. Wucewa yayi ya koma dakin a fusace. Yana jin takunta a bayansa bai kula ba.
Shirgin dakin ya fara watsowa waje. A lokacin ga lura mahaifin nasa ya tashi. Kokari yake yayi magana amma bakinsa kamar ya karkace. Abunda ya sa ya rude kenen. Yana masifa yana bala’i.
” mutum marar lafiya kamar wannan, a bar shi a gida. Sai ka ce marar gata!”
Ya dunga sirfawa yan aikin nan balai suna kwashe kaya. Yana cewa duk yau zai kore su daga aiki. Mafi yawan fadan da mahifiyarsa yake amma kuma ba zai iya fitowa ga da ga ya fadi hakan ba.1
Ya kama laluben waya zai yi magana da mai kula masa da harkar shige da fice kasashen waje. So yake a gobe su bar kasar ya kai shi asibiti.2
Kwala kiran da uwar take masa ne ya katse shi. Kiri kiri ta kasa shigowa dakin wai wari ya isheta. Ya fito ta ce da shi
” Kai kar ka soma daukansa ka fita da shi. Acan ma haka khulsumou ta ce ya ki, shi ne ta kawo shi ta watsar anan. Wani malami aka kirawo ya ce kuma ciwonsa ba na asibiti ba ne. Sihiri ne ya dawo masa! An masa wanka ya fi sau bakwai. Amman wallahi ya ce ba zai daina wari ba!”1
Wani abu ne ya sa gabansa ya fadi dam! Jikinsa yai matukar sanyi. Ya ce
” To yanzu ya za a yi?”
Ta ce
” Na sa a yiwa wani malami magana ya fara kawo masa rubutu ya sha. Amma fa yace babu wani abu da zai yi tasiri sai ya nemi yafiyar wadanda ya zalunta. To ka ji yanda ake ciki”2
Jikin Almustapha ya kara sanyi. Babbar magana ce aka baro kuma bai san ta inda zai liqe ta ba. Kawai sai ya koma dakin mahaifin nasa. Duk warin da jikin uban ke yi ya karasa ya kama hannunsa. Zafi ya ji rau! Ya ce da shi
” sannu Abba! Zan fita na siyo maka magani. Allah ya kara lafiya”
Ya dago ya kalli Almustapha. Wani irin huci jikin sa ke yi kamar ana dana masa wuta. Ji yake kamar ana jan sa! So yake ya ce masa kada ya wahal da kan sa ya siyo magani amma ya gagara. So yake ya gaya masa irin tafasar da jikinsa ke masa da mafarkan da yake yi da Ahmadou a kullu yaumin! Ko dai ya fadawa Almustapha sirrinsa ko zai samu sassauci?3
Da Almustapha ya ga yayi bakam sai ya zata ko bacci yake so ya koma. Sai ya fita yana kiran wani abokinsa likita da ya rubuta masa wasu ‘yan pain reliever haka ya sai wa uban. Daga nan ya fice daga gidan.
Fitarsa ke da wuya Rukky ta kira shi da ya biya ya dauke ta a wajen wani atm akan maiduguri road kan cewar bata fito da mota ba. Da ya dauketa ne ya tuna akwai wani wajen siyar da magani akan titin. Suka shiga ya siyo suka wuce. Anan ne yar modu da hindatu suka gan su.
Ko daya bar gurin gida ya mayar da Rukky. Ta kalle shi cike da damuwa ta ce
” kamar dai wani abu na damunka ko?”
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ya nisa ya ce
” Wallahi mahaifina ne ba shi da lafiya”
Yanayin fuskarsa ya nuna tarin damuwa abinda ya sa mata damuwa kenen. Wannan ne karo da farko da ta fara jin yayi magana akan wani nasa. Sai ta ji kamar ta ce za ta bi shi su duba shi. Amma ta san hakan ba mai yiwuwa ba ne. Tayi masa fatan samun sauki ya amsa mata da cewar zai dawo komin dare akwai maganar da zasu tattauna.
Da fitarsa ya koma gida ya tarda shi ya kara farkawa da alama dai baccin ba wani samuwa yake a gareshi ba. Ya ballo magunguna da ruwa a kofi ya tallafe shi zai ba shi amma sai ya ki.
Illiyasou Tillaberi ya kurawa Almustapha ido yana ta kakarin magana. Shi ma Almustapha yayi tsai yana kallon bakinsa so yake ya gane me yake son cewa. Sai daga baya ya gane
” Ni…ni..ni…nik kashe Ahmadou!!”6
********************************
Luba ce tayi sakaka da baki tana kallon Hindu da ‘yar Modu da suke labarta mata wani labari mai kama da alamara. Bayan sun gama rantse rantsensu kawai sai ta fashe da dariya ta ce
“Wai yau April ne? Har an fara april fool? Kawai dan ku samu abun fada akaina za ku ce Rukky ce ta kwace Almustapha? Ita Rukky in banda ranar da na kai ta wajensa ma yaushe ta san shi? Nawa Rukkyn take yarinyar da ki maganar arziki bata cika ba? Haba Hindatu idan yar modu yayi hakan dan ya ci kudina har da ke? Kin manta yanda muke da Rukky har za ki ci amanarta haka? Mu fa aminan juna ne!”2
Har cikin zuciyar Luba da gaske take domin kuwa tana kaunar Rukky da Hi ndu don a shekarun nan su kadai zata gani ta kira yanuwa. Tare suke fadi tashinsu a bariki kuma suke rufawa junansu asiri. Yanzu a zo daga sama a ce wai Rukky maciya amana ce ta yarda ai da sake. Sai ta ji Hindu ta fara fice mata a rai a ganinta kamar tana so ta yiwa Rukky cin dunduniya ne don wata manufa tata. Kai duniya ba gaskiya!1
Yar modu ne ya kama baki cike da mamaki sa’annan ya aunowa Luba dakuwa ya ce
” Ka ji ‘yar tselan uwa! Ana makadi ya fada ruwa kina ganga ta jiqe! Kanwar uwaki take Rukkyn? Allah ya sa kashin awaki kuke, kuna dirowa kawa rabewa za kuyi! Wannan da a mutanen farko kika zo billahillazi ba kya karbi shahada ba! Daga ganinki an ga su Abu jahal sarakan taurin kai! To ko ki yarda ko kada ki yarda sukari ita ce ta miki kwacen saurayi. Ta kwace Al mustapha. Ra’ayul aini muka gan su. Yadda na gan su Allah sa na ga annabi!”2
Luba ce ta kara kallonsa a sakarce ta ce
” ka ga annabi ko ka ga walakiri? Kayi abinda za ka ga annabin ne?”5
Ya ce
” Au au ka ga mutanen quraishi! Masu dangantakar jini da annabi! Ai abun rabo ne! To bari na labarta miki ko baquraishiya ce ke, idan ba ki shuka abun arziki ba, ke ba ki tuba ba, to ke da ganin annabi haihata haihata. Alquran sai dai ki ga gyatuminki! Ehe! Na dai gaya miki”9
Hindu ce ta kwantar da tarzomar ta ce
” look guys wannan fa ba abun musu ba ne. Ke luba tunda baki yarda ba sai ki shirya ki je gidan Rukky da dare. Jikina ya bani za ki same shi a gidan. Sai ki shiga ki ganewa idonki. Ai kyaun karya hallara!”2
Maganar Hindu ta sanya jikin luba sanyi. Sai ya zamana ta fara raba daya biyu. Ko dai? Don ta ga yanda suka hakikance to amma idan ta tuno fuskar Rukky sai ta ga kamar ba zata aikata ba.
Anan dai aka bar zancen cewa da dare za ta je zuwan bazata. Luba ta cigaba da waswasi a ranta.
*********************************
Da daddare kamar yanda Al mustapha ya alkarwanta gidan Rukky ya wuce. Gabadaya ya kasa sukuni, maganganun mahaifinsa ne suke dawo masa. Ya san yayi zargin hakan amma gaskiya ya so a ce ba hakan ba ne.
STORY CONTINUES BELOW
Wai ina zasu da hakki ne? Sai ya ji komai na kamfanin ya fara fice masa a kai. Tun ba a je koina ba mutane sun fara gudun mahaifinsa saboda wari hatta momynsa ya ga halayyar data fara nunawa.1
To yanzu menene abun yi? An ce sai ya nemi gafara to a ina zai nemi gafarar? Neman yarinya ya zama balai to amma yana ga lokaci yayi da zai fara sanarwa a gidajen radio. To amma ba hoto! Ba fasaltawar kamanni. Ga abubuwan siyasa da me zai ji ne wai??
Maganar Rukky ce ta katse masa hankali ta ce
” Almustapha za ka iya taimakona ka kwatarmin ‘yancina?”2
Ya tsaya yana kallonta a tsanake so yake ya gane inda maganar ta dosa. Ya san ba mai son tambayoyi ba ce yana tambayarta zancen zai watse. Sai yayi kasaqe. Ta cigaba da cewa
” so nake kayi fito da fito da makiyana!Ga nunawa duniya kai masoyina ne! “
Abu daya ne ya fado masa a rai..Luba! Sai yake gani kamar ya gane inda zancen Rukkyn ya dosa. Don haka sai yayi murmushi ya ce
” Baki da damuwa. Zan nunawa duniya ni masoyinki ne!”
Ranta ta ji yayi fes! A take ya wurgo mata wata tambaya a karo na biyu
” Ya aka yi kika fada karuwanci?”
Tsira masa ido tayi tana masa kallon tar. Tun bayan momodou bata taba jin wani a zuciyarta kamar Al mustapha ba wai me ya sa? Ta cigaba da gayawa zuciyarta cewa karuwa fa so ba nata ba ne amma ta kasa hana kan ta! Sai ta ji kamar tana so ta gaya masa ko ita wacece.
” Bam! Bam! Bam!”
Karan bugun kofar da ya katse musu kallon juna kenen. Ya kalle ta a mamakince ya ce
” wani irin bugu ne haka? Ko maigadin dana aika ne?”
Bata ba shi amsa ba ya karasa bakin kofar ya bude.
Luba ce a tsaye sanye da wani wando tri kwata da riga marar hannu. Komai da ke jikinta baki ne kuma ya kama ta tsam! Da dare ne amma sai ta dauki wani bakin gilas ta kwama. Aka tsaya ana kallon kallo tsakaninta da Almustapha!2
Gilas din ta kwabe tana dubansa a tsanake idonta ya kada yayi jazir na alamar ta sha wani abu. Bata ce da shi kazil ba ta wuce ta karasa cikin falon inda Ruky ta ke a kishingide. Ta dago suka hada ido karaf! Gaban Rukky ya bada dam!3
To amma da yake ita ma ta goge a bariki maimakon ta nuna rudewa kawai sai ta koma ta kishingida tana raunar cingam kas kas. Sai dai ayi wacce za a yi! Almustapha ba ta ga mai raba ta da shi ba!2
Luba ta bi Rukky da kallo a tsanake cike da tsannanin mamakin da bata taba ji ba tunda uwarta ta kawo ta duniya! Ta sha cin amanar mutane amma ko da wasa ba a taba gwada cin amanarta irin haka ba sai yau! A yau din kuma wai Rukky! Yarinya karama da a gabanta ta shigo bariki! Lallai yau ake yin ta!
Luba ta fara tafa hannayenta alamar jinjina ta ce
” lallai na baku award na manyan maciya amana na wannan zamani! Ashe batun da ake gayamin gaskiya ne? Almustapha ni ka yada ka dau aminiyata Rukky? Rukky ni kika yiwa zamba cikin aminci kika kwace Almustapha. Ku ka hada kai ku ka zambace ni!”2
Ya daka mata tsawa ya ce4
” Who the hell do you think you are? Ai ni a rayuwata ke ba komai ba ce! Ni ina da zabi akan irin yarinyar da nake so kuma ke ba irinta ba ce! Ni Rukky ita raayina kuma ita na zaba. Dan haka get the hell out of this house!!”
Luba ji tayi kanta na juyawa saboda tsabar yadda maganganunsa suka tarwatsa mata zuciya. Ita Luba da ta cika mace gaba da baya ita ake yabantawa kan wata aba Rukky? Wata irin tsana ce ta mamaye ta.
Ta juya tana kallon Rukky wacce ke karkada kafa na nuna alamun ta ci gari. Ta yi murmushin takaici ranta na raya mata sun tafka kuskure ta ce
” Ba ku ji gabanku ya fadi ba! Ba ku ji shakku zama abokanan hamayyata ba! Rukky ba ki ji kamar kin shiga ukun ki ba? Da lokacin da kika fara son Almustapha kin gayawa zuciyarki ba a wasa abakin wuta. Domin idan aka fada mutuwa ake!!! Da sannu zan nuna muku wacece Lubabatu! Da sannu zan saku da na sani. Watarana idan kuka ga wani zai ci amanata da gudu zaku hana shi domin kuwa bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne!”1
“Get out!” Abunda ya ce da ita kenen yana nuna hanyar waje. Ita kuwa Rukky ta kasa cewa kanzil! Cikinta fargaba ne taf! Dan ta san waccece Luba.
Luban ce ta kalle shi a tsanake. Ta mayar da gilas din ta ta nuna shi da danyatsa
” Ashe kai wawa ne! Ina ganinka kamar mai wayo ashe sakarai ne!! Wa ke fuskantar kura gaba da gaba? Da sannu za ka manta cewa kai ne! Ke kuma…!1
Ai ba tai wata wata ba ta daga hannu ta shararawa Rukky wani mahaukacin mari ji kake taaaaas!2
Ai bata ajiye hannu ba Rukkyn ta hankadata kan wani teburin glass na gefe ji ka ke tartatsaaaaa!
Ya yanki Luba a hannu yana digar jini. Ta dauki bangare daya na gilashin ta wurgi Rukky da shi. Ya yanketa a kuncinta na dama ya daki bango ya tarwatse!
Ganin idan ya kalle su za su iya hallaka junansu kawai sai ya hankada Luba waje ya kulle kofa. Tayi buge bugenta da zage zage da mugayen alkaba’i ta wuce.
Ya dawo ya tarar da Rukky na sharar hawaye ya fara lallashinta da irin matakan da zai dauka akan lubar. Ta ce da shi
” Ba ka gane dalilin kuka na ba! Raba ni za tayi da kai! Luba ba zata iya jurar ganinka da wata ba”2
Nan ya gaya mata maganganun kwantar da hankali da cewar da safe zai sa yan sanda su mata gargadi, a yi musu tsakani. A haka aka kwana.
Ko da ya tashi da safe nan ma gajiyar ce turum a kan sa. Kan sa ya dau caji ga shi ana jiransa a ofis game da wani mitin mai muhimmanci da za suyi. A haka ya bar Rukky da alkawarin zai dawo.
Yana tsaye a ofis ne da misalin karfe biyun rana sun yi meeting sun fito. Ya sa sakatariyarsa ta hada masa shayi ta kawo masa. Rabonsa da cin abinci ya manta. Tunaninsa bai wuce ya gama da ofis ba ya garzaya ya ga jikin mahaifinsa ba.
A lokacin ne wani daga cikin yan siyasarsu ya kira shi kan cewa ya kamata su fita kamfen wata karamar hukuma. Domin kuwa an yi ittifaki cewar su na da magoya baya dayawa a yankin.
Sakatariyar ta sa ce ta leko da bayanin wai wata na son ganinsa. Ransa ya fara baci, ya san ba zai wuce luba ba. Wato haukarta har ta kai ta zo masa ofis ta ce za tayi masa tijara? Ta san ko shi wanene kuwa? Kamar dai ya kamata ya nuna mata madafan ikonsa! Ya cewa sakatariyar ya ce ta shigo zai ga iya gudun ruwanta.
Ya juya bayansa yana waya so yake suyi sallama. Daga nan ya ji da wannan yarinyar , karamar kilaki! Ya ji shigowarta amma bai juya ba suka yi sallama a waya. Ya juyo fuskarsa a daure tam! So yake yayi mata gargadi na karshe! Babu ita babu Rukkyn sa. To amma me?
Sai ya tsaya cak!!
Idanunsa ya fara gano masa wata halitta daban.
Doguwa ce sambal mai dauke da garun jiki. Tana sanye da wata bakar riga a jikinta da bata kara mata kyau ko rashin kyau ba. Fuskarta fayau ba alamun nuna kwalliya. Kitso ne irin na karin gashin doki a kanta siri siri ta daure.
Suka tsirawa juna ido yana tuno abubuwa da dama! CACA!!
Wani murmushi ta saki mai ma’anoni daban daban. Ta ce
” Hello Al Mustapha”
Ya hadiye wani abu makwat! A makgwaronsa. Sai ya ji gabansa na faduwa, kawai ya san ba alheri ba ne.
Ya ce
” Hello REBECCA…… “
Sai ta tako a hankali har zuwa inda yake. Kawai sai ta saka hannu ta rungume shi. Ta zo daidai saitin kunnensa ta ce
” Our….. baby ……..is home!!!”Ai sharri kare ne, mai shi yakan bi!8
( i think i’m about to take a break)32
Kano, Nigeria+
Shekaru kadan da suka wuce
Harabar La mirage cike take da manyan motoci na masu fada a ji, wadanda shedan ya buga musu ganga suke taka rawa. Ranar ta kama asabar yawan yawan ma’aikata da suke Abuja da kaduna sun shigo hutun karshen sati. Mafi yawansu kan rashe a wannan waje domin nishadi, suna taba dan shaye shaye da caca.
Wannan karin wani mawakin Hausa suka dauka mai suna “dan mudubi”. Sukan yi hakan idan sun so nishadi ko su dauko masu garaya suna wake su kan su na fasuwa.
A ranar dai waken dan mudubi bai wuce kan Almustapha ba. Almustapha bai fasa yi masa ruwan nera ba kamar bai san ciwonta ba!. Ran dan mudubi fes! Har yakan ce
Ka ga Mustapha gwani na gwanaye!
Yaro da kudi abokin tafiyar manya
Mai takalmin karfe kowa ka taka ya taku
M
usty nera ka je las vegas sun buga sun kyale!
Wanan abu kan fasa kan Almustapha, sai ya dunga jin kamar shi kadai ne ya gawurta duniyar! Aka dunga cika masa kofi da gulder yana sha yana barin nera!
Akwai wani da ake kira Hafeez kamala. Wani matashin yaro ne mai irin zubin Almustapha. Shi ma gwanin caca ne ba karya kuma wannan kirari na dan mudubi yana sosa masa rai. Yaushe Almustaphan ya shigo bariki har da zai nuna musu ya isa? Karamin yaro dan haure asalinsa ma ba dan najeriya ba! Ya za a zo garinsu a fi su da rawa sa’annan a bi su tsinannen duka?! Ina ba za ta yiwu ba!5
Almustapha ya cigaba da cika tambulansa da giya yana durka ma cikinsa, yau nishadi yake ji! Wani abu da bai cika yi ba, buguwa da giya. Na kusa kusa da shi mazigansa da suke kiran kansu masoyansa sa suna kara ingiza shi nuna masa duniya fa ba komai ba ce.
Ana cikin wannan shagalin ne da Hafeez kamala fa ya lura Almustapha ya yi tatul sai yayi challeging din sa da caca. Ba ai wata wata ba aka share fili ana shirin ganin wannan wasa tsakanin gwanaye biyu. Kowa yana da magoya bayansa ‘yan shaida. Ba a komai sai iface iface da kumburawa mutum kai.
Sai a lokacin Hafeez kamala yace
” idan ka cika kai gwani ne na gwanaye. Yaro ne kai abokin tafiyar manya. Ga dan mukullin mota ta. Sabuwa ce dal! Zuwan shekaran jiya. Benz ce da za ta kai kimanin naira miliyan ashirin. A yau na sata a tsakiyar fili idan a yau kai ka ci cacar nan na ba ka ita!”
Ya dauko mukulli ya aje bisa tebur
Waje ya dau ihu da sowa Almustapha yana murmushin takaici. Kamar shi har za ayi challenging irin haka? A la mirage babu gwani kamarsa! Zai nunawa Hafeez Kamala ya ci ubansa ya dama a caca!”
Ya ce
” Na ka wasa ne. Me aka yi aka yi motar miliyan 20? A gurinka take kudi. Sabon kamfaninmu da zamu bude da zai doke kowani kamfani na sayarda kayan masarufi a Arewacin Najeriya gabadaya shi zan aza bisa tebur! In ka isa kai gawurtacce ne sai ka nuna a daren yau!Idan ka ci ni ka dauka na baka halak!”12
Yawa yawan mutanen gurin sun ga wautar Almustapha to amma su fa ‘yan abi yarima a sha kida ne. Sun san giyar kudi ke rudarsa, Idan ba don haka ba wa zai yi wannan gangancin?
Hafeez kamala ya ce a fusace
” karya kake ba zaka iya ba! Idan za ka iya dauko takardun a aje bisa tebur idan ka haihu cikin uwarka”1
To wannan abu ya fusata shi har ya bazama dauko takardun da ke compartment na motarsa. A ranar ya karbo su daga inda ya bada a ajiya a banki, mahaifinsa zai saka hannu à wani waje. Sai akai rashin sa’a wannan muhawara ta ritsa da su.1
STORY CONTINUES BELOW
Ganin abunda Almustapha ke yi kamar ba cikin hankalinsa dan nuna izza da isa ya sa sadiq abokinsa rike shi. Yayi nufin hana shi don ya san al’amari na giya to amma sai Almustaphan ya ki. Wai hakan zai iya nuna gazawarsa.2
Ihu da sowa bai mutu ba a harabar la mirage kowa idonsa na kan abunda ake yi. Aka fara buga wasan karta tsakanin Almustapha da Hafeez kamala.
Wasu lokutan ba kullum ake kasa kaya a sayar ba, duk yanda mutum ya so sai yayi bandaro. To hakan ce ta faru domin kuwa babu wani tsimi babu dubara Hafeez Kamala ya cinye wannan caca!Bai yi wata wata ba ya wawashe takardun nan muhimmai ya bar Almustapha da mutanensa a zaune cikin madaukakin mamaki!3
Wannan al’amari ya girgiza la mirage har ta kai fada ya balle.
Almustapha yana cikin dimuwa da tashin hankali. A tarihin la mirage bai taba rasa caca ba. Bai taba zaton Hafeez zai ci ba, ko kusa tunanin shi bai ba shi hakan ba. Da ya san zai ci ko da wasa ba zai fidda takardun nan ba domin hakan wasa da rai ne!5
Da kyar abokinsa sadiq ya janye shi ya kai shi mota. Dole abokin ya tuka ya kai shi gida. Ya kale shi da cewar zai garzayo ofis gobe su tattauna mafita.
A ranar Almustapha bai rintsa ba. Abubuwa biyu ke damunsa a rai. Da farko wannan kamfanin da shi za suyi suna. Ya mahaifinsa zai ji idan ya ji wannan ta’asar da ya tafka?2
Na biyu a lokacin suka bude sabuwar jamiyyarsu, tayi fice tana tashe. Magana daya zata fito yanzu sun shiga uku da ‘yan adawa. A bi shi da yamadidi. Watakila har wadanda suke ganin mutuncin shi su daina.
Duk abunda yake yi a boye yake yi. Almustapha mai son a ga shi mai tsantsani ne, mai tsoron Allah. Da hakan ya kan janyo manyan manyan mutane su so shi. Su so muamala da shi.2
Wani irin hali gare shi na musa a fuska firauna a zuci. Za ka gan shi gaba akan sahu, shi ne taron kwamitin masallaci, gobe shi ne babba a taron musabaqa. Gobe bayarda da tallafi ga daliban makarantun islamiyya.2
Bai cika son a san shi ciki da bai ba, yawa yawan dalilan da suka sa ya rabu da matarsa khairiyya. Yanzu idan zance ya fito kan ya nuna irin wannan ganganci da wani ido zai kalli mutane? Ya san ko giyar wake Hafeez ya sha bai dawo da takardun nan. Bai isa ya yiwa hafeez cune a sace takardun nan ba domin kuwa shi ma gwaskan kan sa ne! Dan duniya ne da ya dade a bariki. Abu kadan Almustapha zai yi Hafeez ya juyo kan sa, ya kuma san ba zai ji ta dadi ba! Don haka menene mafita?2
Dole ya san yadda zai yi ya dawo da takardun nan a karamin lokaci? Dole ne!
Da wannan ya kwana a ran sa.
**********************************
“Almustapha ya kamata fa ka gane” cewar sadiq” lalashin Hafeez ko yi masa fito na fito ba zai sa ya dawo da takardun nan ba. Wannan abu an yi shi ne specifically don a ci mutuncin ka. Ban ma yarda da wasan nan ba akwai wani magudi a ciki. Shin ko kana tunanin hada shi da hukuma?”
Wani irin numfashi Almustapha ya saki. Ya sa hannu ya loosing necktie din sa da yake jin kamar ya shake shi. Komai ya dagule masa a kwana 2 kacal! Me ye haka?
Hukuma? To ya cewa hukuma me? Ai kamar ya daga hannu ya caka ma ka sa wuka kenen. Makiyansa su ji suyi masa dariya. Bayan shi a karan kan sa ya san a sha cin makudan kudade da kadarori a la mirage. Ba a taba cinye shi a caca ba sai a ranar.
Ai ko dan cikinka ka saka a caca a la mirage ka fadi to ya cinyu! Balle takardun kamfani. Dama ai caca ta gaji haka ko ka ci ko a cinye ka.
Abun da yake tunanin ba komai ba ne ya zo ya tsaya masa a makoshi. Ba irin lallamin da bai aika an yi ma hafeez ba to amma abu ya gagara. Ya masa alkawarin kudade masu dama a madadin takardun amma ya ki. To shi yanzu ya zai yi?1
STORY CONTINUES BELOW
Kwanaki sai matsowa suke da mahaifinsa zai shigo da Niamey domin za a kaddamar da kamfani. Da me zai ji wai.
Ya kalli sadiq a tsanake. Abokinsa ne tun lokacin da daura alkawari da bariki. Ko banza sadiq idon gari ne kuma idonsa ne a wajaje da dama. Abokin sirrinsa ne domin kuwa yana matukar taimaka masa a harkokin lullube fuskarsa. Ya ce
” Sadiq kai na ya daure. Allah kwanakin nan ko runtsawa bana yi. Ni kawai ka bani shawara menene kake ganin za a yi?”
Sadiq ya nisa shi ma a kwana biyun nan ba kanta. Can kamar mai tunani sannan ya dubi Almustapha ya ce
” Amma ka san an ce idan gabas ta ki sai a koma yamma. Ba ka gani kamar ya kamata mu aje komai a gefe mu hada shi da malamai. Malamai masu aiki irin na hatsabibanci. Aiki irin na tsubbu! Su rufe masa baki su rufe masa gani ya dawo da takardun nan ko ya ki ko ya so!”1
Kallin galala Almustapha ke yiwa Sadiq. A rayuwarsa iskancin sa ya iskancinsa amma bai taba shiga harka ta irin dube duben nan ba. Ma fi yawan lokuta ma bai yarda da su ba. Gani yake wani ne kawai yunwa ta ishe shi ya baza buzunsa yake yin damfara.
Ya ce
” Kai sadiq wadannan yan damfara ne kawai! Me za su iya mana banda su karbi kudaden mu su ware? Ka sake shawara”
Dariya sadiq yayi ya ce
” yallabai kenen. Ai idan baka san gari ba to ka nemi dan jagora! Da gaske malamai na damfara , to amma wannan kankat ne! Dalili kuwa lokacin da mahaifinmu ya rasu ka san ya bar mata da yara dayawa. To an ta yin hatsaniya wajen rabon gado.
Mahaifiyarmu da take mowarsa akwai takardun gidajensa da filaye dayawa a gurinta. Magada suka yi mata caa ta fito da su ita kuma bata ga dalilin hakan ba. Wallahi da ta ga sun sako ta gaba ba shiri ta dauke ni muka je wajen wannan malamin aka rufe bakinsu. Har jini sai da aka zubar!Ka san Allah? Yau shekara goma kenen da rasuwar wallahi har yau! Ba wanda ya kara daga maganar filayen nan!”2
Wani irin shock ne ya shigi Almustapha har ya kurawa sadiq ido. Karara ya gane gaskiyarsa yake fadi. Bai yi mamaki ba amma abun ya tsorata shi. Wani sashe na zuciyarsa na raya masa ya je wani na hana shi. Ya ce
” Sadiq anya hakan kuwa ba babban zunubi ba ne? Ga hakkin mutane da kuka danne ga kuma shirka?”
Sadiq ya dan jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi ya ce
” Lallai mutumina ba duniyar kake nema ba. Ai me neman duniya baya tone tone. Duk wadanan manyan mutanen da ka ke gani attajirai da manyan masu kudi a tunaninka haka sunka zauna? Wa billahillazi sai da tsaro! Ko ba ka nemi kayan yaki ba ai ka nemi na kariya.
Kuma waye ya gaya maka shirka ne? Ba fa boka ba ne. Ba a daji yake ba a gidansa yake a zaune.Kawai dai yana da ilimin Almatsutsai da taurari. Da su yake amfani ya taimaki mutane su biya bukatarsu. To..to idan banda abunka ma Allah ai gafurur rahimu ne. Idan ka gama al’amarunka na biyan bukata ba kawai sai ka roke shi gafara ba! Ka tuba, wallahi yafe maka zai yi.”2
Sai zuciyar Almustapha mai tsananin son biyan bukata ta ga ai hakan ne! Kuma ga shi shi bama hakkin wani zai danne ba hakkinsa ma zai kwato. Me ye a ciki? Shi ba jini zai zubar ba
Kuma inshallahu zai tuba.2
Da wannan suka shiga mota suka tafi wani yanki na kauyen Rano ba su tsaya ba sai a kofar soron malamin nan.
Tsoho ne amma ba tukuf ba. Ya shaida sadiq domin kuwa yana yawan ziyartarsa shi da mahaifiyarsa. Babu wani bata lokaci suka yi masa bayani. Ya yi ‘yan zane zanensa a kan kasa ya dago ya kalle su yace
” Za a yi aiki, ba kuma wani abu ne mai wahala ba. Da kan sa zai dauko takardun ya dawo da su, kuma ba zai kara tada zancen ba, ba zai taba bari a masa zancen ba kuma ba zai kara saurarar duk wanda ya masa zancen ba!”
STORY CONTINUES BELOW
Almustapha ya ji ran sa fes! Anya ba zai dawo wajen mutumin nan akan alamuransa na siyasa ba? So yake ya kafa kansa watakil shekaru kamar goma masu zuwa sai ka ga ya zama gwamna!2
Ya ci gaba da kallon tsohon yayin da tsohon ya cigaba da bayani kamar haka
” kafin hakan ta faru sai ka nemi tauraruwarka. Sai kayi mu’amala da tauraruwarka na kwana daya tal! Daga nan ba zaka kara waiwayenta ba. Yadda baka waiwayeta ba haka hafeez zai dawo maka da takardun nan ba zai waiwayeka ba. Ba a so ka kara haduwa da ita daga wannan rana, idan kuwa har hakan ta faru duk abinda ya biyo baya kayi kuka da kan ka!”
Sai da gaban Almustapha ya fadi. Sai ya ji kamar abun ya fara fice masa a kai. Kamar tsafi. Me ya kawo shi ne wai? Sai a ranar ya fara jin ya tsani caca da duk wani abu da ya dangance ta don ga shi bata kare shi da komai ba sai wahala.
To amma ya zai yi? Idan bai bi shawarar malamin nan ba wata shawara zai bi? Ko da wasa ba zai iya bar wa hafeez takardun nan ba inaa..da sake.
Y
ayi gyaran murya ya ce
” Ina fatan dai ba za a zubar da jini ba?”
Tsohon yayi jim sannan ya ce
” Ni dai ban ga zub da jini ba, kuma ta bangare na bazan saka zubar da jini ba. Sai dai kuma abunda ke boye a gaba wanda kai zaka iya fi na sani”
Wata magana yake masa kamar zaurance. Amma sai ya share. Ya ce
” to ita mecece tauraruwar tawa”
Tsoho ya ce
” Mace ce..kuma ta zo a Ahlul kitabi”!
AlMustapha ya ji gabansa yana wani irin lugude na tsoro amma ya kasa hana zuciyarsa abunda take so. Ya ce
” To a ina zan gan ta? Ya zan gane ta?”
Tsoho ya ce
” Ba a garin nan take ba..tana wani gari a kudancin kaduna. Zan fasalta maka inda zaka je. Tana siffofi kamar haka:
Bata da yawan hasken fata amma ba za a saka ta a bakake ba,doguwa tana da ingarman jiki, tana da idanuwa masu kama da na kyanwa. Tana yawan saka bakaken tufafi. Ahlul kitabi ce mabiya addinin kiristanci. Tana zaman kanta ne a wannan gari kuma shahararriya ce, tana zaune a wani sanannen gidan mata da ke garin. Idan ka cigaba da ziyartar wannan gidan matan zata wuce za ka ganta za kuma ka san ita ce. Zaka neme ta na kwana daya ba za kuma ka waiwayeta ba. Ba za ayi sati ba zaka zo ka bani labarin dawo da takardun nan.”2
Tsafi ne! Siddabaru ne! Shirka ce!
Abinda ke yawo a ran Almustapha kenen. Kawai sai ya ji ba zai iya ba ya tashi ya bar tsohon nan a gurin. Sadiq na kwala masa kira bai waiwayo ba. Kawai wani huci mai zafi yake fitarwa daga bakinsa.
” Bana so in zama haka, bana so in so duniya har haka!”
So yake ya ceci imaninsa amma kamar abun ya gagara. Wataran yakan yi tunanin halayensa ya ga ya kamata fa ya daina wani abun domin lokaci fa tafiya yake kuma mutuwa bata sauraren uzuri. Amma sai ya ji ya kasa.
Har ya koma gida yana tunanin mafita, ya san Sadiq yayi fushi da shi. To amma ya zai yi?
A ranar ya gane ashe ba shi da abokin shawara ko da kuwa uwarsa ce mahaifiya? Ashe shi kadai ne? Ina ma Momodou na nan ko zai yarda? Wata shawara zai iya ba shi? Yawan yawan mutanensa ya san suna tare da shi ne dan dukiya da daukakar da Allah ya ba shi. A yau ina masoyi na gaskiya?
Ran sa bai dagule ba sai da ya samu kira daga mahaifinsa a wannan dare da yasa shi yanke hukuncin da bai shirya ba. Ya gaya masa nan da kwanaki zai karaso shi da mutanensa. Ya cigaba da masa jawabin cewa sun samu investors da yawa da suke burin saka hannun jarinsu a wanan kamfani. Yana yiwa Almustapha albishir da cewar sun kusa kafa record bama a yankin su Niger da chadi da makusantan kasashe ba, har ma a Najeriya gabadaya.2
STORY CONTINUES BELOW
Yadda mahaifinsa ke magana da dandazon da ya san za a tara ya sa ya yanke hukuncin bin maganar malamin nan.
Ya daga waya ya kira sadiq, a bugu na uku ya dauka muryarsa ba walwala. Almustapha ya ce
” ka shirya gobe mu dau damarar tafiyar nan, zamu je neman tauraruwar nan”1
***********************************
Ko da suka je kaduna garin da tsohon nan yayi magana ba su wani sha wahalar gane gidan matan da ya ambata ba. Wani gida ne na masu zaman kan su daga garuruwa daban daban suka taru suke aikata abunda ran su ya so.
Babu kalar kabila ko addinin da babu a gidan. A gaban gidan wani wajen sayar da abinci ne mamallakin magajiyar gidan mai suna REBECCA.2
Rebecca ba ta da asalin da wani zai labarta. Yawa yawan mutane na hasashen wai ‘yar bendel ce. Wasu kuma sukan ce yaren tivi ce da ke can jahar benue. Kawai dai ganinta aka yi ta zo garin da makudan kudade ta bude wannan gida. Ba zata haura shekara 35 da biyar ba amma shahararta da hatsabibancinta ya wuce karamin tunani. Tana jin yare sama da guda bakwai.
Wata kawarta bayan sun yi baram baram ta ce wai Rebecca mijinta ta kashe ta gudo da kudin ta bude wannan gidan. Ko da zancen ya fito bai damu rebecca ba , haka take abun kunya na duniya ba su cika damunta ba. Ita dai kawai ta samu kudi tayi facaka ta more.
An yi rikicin duniya akan rufe gidan nan , hukuma tayi iya yin ta amma abu ya faskara. To mafi yawan manyan mutane da suke rike da mukamai suna da karuwai a gidan. Dalilin da yasa kenen hukuncin rufe gidan ya ki tasiri.
Tana da mutane iya mutane babu kuma kalar zunnubin da ba a aikatawa a gidan na ta. Don haka ba kananan kudade take caska ba. Ta kuma bude wani katin gidan abinci a gaban wajen inda ake zuwa siya daga wurare da dama.
Mace ce da bata cika son yin kwalliya ba. Mafi yawan kayanta bakake ne kuma tana dauke da cross a wuyanta. Ga wanda bai san ta ba babu abunda zai hana ya ce mai zafin rike addinin kiristanci ce. To amma inaa..ko coci kafarta bata taba takawa ba. Yanayin ra’ayinta ne kawai.
Almustapha da sadiq suka sauka a wani hotel da ba shi da nisa da wannan gidan matan. Ba su da aiki sai su share guri a kofar hotel din su zauna, su je zagayen gari su dawo.
A kwana na uku ne Almustapha ya gaji ya dubi Sadiq ya ce
” kai ni fa na gaji. An taba gane mutumin da ba a taba gani ba? Kwananmu uku a gari ba wani bayani? Anya mutumin nan ba damfararmu yake ba?”
Sadiq ya ce
” To idan banda abunka mutumin da yace sai aiki ya ci zamu biya saboda tsabar sanin aikinsa. Muyi hakurin yau mu gani. Kai yallabai kamar ba ka san ita biyan bukata sai an cije an dage ba”
Da jin haka sai Almustapha yayi shiru. Yana ta tunane tunanen yawan aikin da ya bari a kano. Ga kiran da mahaifinsa ke ruga masa na nemansa da gaggawa. Sadiq ne ba bada shawarar su shiga gidan abincin nan su ci ko sa rage lokaci.
Shigarsu yayi daidai da fitowar Rebecca, suka kusa yin karo ita da Almustapha. Kallo daya ya mata gabansa ya yanke ya fadi dan tsoro sai da ya ji jikinsa na karkarwa. Bata da wani banbanci da yanda dan tsohon nan ya fasalta masa. Danqari!
Har ya zauna ya kasa dauke idonsa akanta haka ita ma. Shi don tsananin mamaki ita kuma dan tsananin kyawunsa da take gani. Gaskiya ya mata a ganin farko ta san ya mata. Sai abunda ya turewa buzu nadi.
Duk abinda suka ci a ranar ta hana su biya kudin. Sai shisshigewa Almustapha take. Ta yi masa masauki a kawataccen dakinta na alfarma. Kowa fa manufarsa a rai. Ita ta so da kaunarsa shi kuma na biyan bukatarsa.
Asubar fari Almustapha ya sulale ya gudu daga dakin Rebecca ba wai don wani abu ba kawai gani yake ya tsani gari da duk abinda yake cikinsa. Tun da ya aikata abunda ya kawo shi, to me ya rage? Kawai sai yayi komawarsa kano ba tare da ya waiwayeta ba kamar yadda tsohon nan ya fada ba kuma tare da ya bar wani abu da zata iya tunawa da shi ba. Bai kawo komai zai biyo baya ba bai taba kawo wa ba.4
STORY CONTINUES BELOW
Tafiyar Almustapha wani abu ne da Rebecca ta daukake shi ba nan kusa ba. Tun da take a rayuwarta bata taba jin son wani kamar shi ba. Ya zai yi mata haka? Duk yanda take tunanin zata neme shi tayi cigiyarsa tayi amma ba ko labari. Tayi kuka kamar ranta zai fita. Ta nisantar da kan ta daga kowani maneminta saboda tsabar kewarsa.
Daga baya ta hakura. Amma me? Bai yi wata biyu da tafiya ba ta gane tana dauke ta juna biyu. Ba sai ta bincika ba ta san babu tantama na masoyinta ne. Har zata zubar wata zuciyarta ta ce mata ta bar shi kawai, me ya fi da ya wuce ta ajiye dan masoyinta ta dunga kallonsa kullum? Ba ta dai gama tantancewa ko ta bari ba sai da wani abu ya faru.1
Wata kawarta ce Reema ta shigo da wata mujalla ta ‘yan wasan polo da aka yi a kaduna na wannan shekarar. A ciki ne ta ga hoton Almustapha a kasan a rubuta.
” Shahararren matashin attajiri kuma dan siyasa nan da ake masa taken ” yaro abokin tafiyar manya” mai suna Almustapha a wajen kallon wasan polo da aka yi a wannan shekarar”
Ba tayi wata wata ba ta karbi mujal
lar ta rungume. Ashe ma sananne ne! Ah ai ita ke da jari. Babu abunda zai hana illa ta ajiye cikinta ta haifo abunta. Samo Almustapha ashe ma ba abu ne mai wuya ba! Ashe sunansa kenen! Wayyo masoyinta Almustapha.
Ai da cikinta bata da wata danuwa. Za ta ajiye ranar da zata tunkare shi kuma dole ya saurare ta! Dole ne ya zamo nata. Dole ya aureta. Domin kuwa tana dauke da gudan jininsa.
Ba za tayi garaje ba, a sannu zata bi don ta cimma buri.
Da ciki ya isa haihuwa ta haifo santaleln danta mai kama da ubansa sak! Abunda ya fi burge Rebecca kenen. Babu abinda ya bari na ubansa har idanun. Ba tayi wata wata ba ta laka masa suna AL MUSTAPHA. Ai kyaun da , ya gaji ubansa. Zata fara kirga lokaci da Almustapha zai hadu da gudan jininsa. Tana bibiyar labaransa tana bibiyar takunsa ba tare da ya sani ba.3
Lokacin da ta ga abubuwansa sun kankama, siyasa ta zo ya kara bunkasa. Yaronta na yawo koina kamanninsa da ubansa na fitowa baro baro. Ta shirya tsaf ta tunkari garin kano, domin lokaci yayi. Lokaci yayi da Almustapha zai zamo nata, ita daya. Dole ne ya aureta ko ta shiga kafafen yada labarai da na sada zumunta ta bata shi! Ta bata shi a daidai lokacin da baya bukatar tozarci!
Ta san komai nasa , bata kuma sha wahala ba ta bayyana a ofis din sa. Za ta sanar masa da wani albishir wani daddaden albishir na samuwar gudan jininsa Al mustapha.
***** *****
Ko bayan da Almustpha ya koma kano bayan rabuwarsu da Rebacca bai kara tuna ta ba. Me zai yi da ita shi da aka ce kar ya waiwayeta.
Wani abun da ya bashi tsananin mamaki shi ne ba ayi kwana uku da dawowarsa ba sai ga Hafeez kamala ya kawo masa takardun kamfanin nan har ofis.4
Ko bayan tafiyar Hafeez din sai ya kama kan sa yana dariya wata irin dariya ta mutanen da suka samu duniya, ta zo musu a tafin hannu.
Sai ya kama kan sa yana yiwa kan sa kirari da
” Sai ni Almustapha, mai takalmin karfe..kowa na taka..ya taku!!”
Abinda Almustapha bai sani ba shi ne
Duniya tana zuwa maka ne a yadda ka dauke ta
Ba zaka taba girbar abunda baka shuka ba5
Sannan, shi sharri kare ne
Mai shi yakan bi!
*********************************
A YAU
” our baby is home”
Kalaman Rebecca da suka bakunci kunnen Almustapha suka tarwatsa masa zuciyarsa kenen.
STORY CONTINUES BELOW
Bai yi wata wata ba ya wancakalar da ita daga jikinsa ya na auna mata mummunan kallo. Ya ce a fusace
” What the hell are you doing in my office? Kar ki zo ki min iskacinku karuwai anan. You better behave yourself ko yanzu na saka security su waje da ke!”
Kallon shi take yi kamar tababbe sa’annan ta fashe da dariya. Ta san za a yi haka, fiye da haka ma ta san za a yi. To amma me? Ta shirya. Irin shirin da bai zata ba.
Ta ce
” look young man. Ba zai yiwu akan karya na taho daga nesa na ce kana da yaro ba. Ka kwantar da hankalinka da sannu zaka gane bayani na.”
Ta fito da wayarta ta nuna masa hoton da ha mamaye fuskar wayar ta ce
” Ga shi nan..ka kalle shi da kyau ka ce you havent seen a part of you in his eyes! Yana nan na rada masa sunanka. Kyaun da ya gaji ubansa!”
Kawai sai ta fashe da dariya
Ya ga hoton, ya kuma gane abu daya. Yaron nan ko ba dan sa ba ne jininsa ne. Don har sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi yarrr. Me ye haka? Me yasa balai yake danno sa ne?
Ta ce
” ko baka yarda ba za mu iya zuwa ayi muku Dna test bani da damuwa akan hakan. Fata na dai ka yarda ka gane yaronka ne”
Wani abu ya hadiye mukut don tsananin bakin ciki. Ya aka yi yarinyar nan ta shammace shi haka? Da ya san zata iya masa haka babu abunda zai hana ya sa a batar da ita. Shi zata batawa wasa.? Wasa a daidai lokacin da yake daf da cimma burinsa.
“What do you want?”
Tambayar da yayi mata kenen kai tsaye
Ta ce
” Ka aureni. Idan baka amince ba a shirye nake da na yayata ka na bata maka suna. Jaridar da zata fito a watan gobe bai wuce wacce ke dauke da sunanka ba da cewar ka min fyade! Har yayi sanadin da na samu ciki! Yaron nan dan ka ne ba ko tantama. Yaya kake ganin abokanan hamayyarka zasu dauki zancen nan? Ya ya ka ke ganin mutanen da za su zabi jamiyyarku saboda kai za su ji? Wadanda suke ganin mutuncinka fa?
Kai bari na gaya maka sai na kai ka kotu akan fyade. Sai nayi dragging sunanka in the mud! Kafin a gane gaskiya sunanka ya ri ga ya baci. Yaron dai yana gurina idan kana so muyi magana ga number na nan. Tick…tock”2
Ta fice ta bar shi a tsaye yana share zufa cikin tsananin bacin rai.
Almustapha bai yi wata wata ba ya aikawa sadiq waya yana masa neman gaggawa. Haka ya zo ya zauna suka yi jugub jugub suna neman mafita. Sadiq ya ce
” yanzu haka sharrinsu ne fa na karuwai. Har yaushe a kwana daya zata ce wai an bar ta da ciki. Kayi watsi da zancenta kawai. Kuma ai zaka iya musuntawa. Tunda bata da wata kwakkwarar shaida”2
Almustapha ya daki tebur din sa ya ce
” Baka gane ba sadiq, wannan matar ta dade tana shirinta. Ta riga ta kwana da makaman yakinta. Wannan yaron zan yi DNA test, amman fa jikina yana bani nawa ne. Ka san kuwa duk inda yaro ya zamo nawa dole ni ne a kasa. Ya zan yi idan a daidai wannan lokacin duniya ta ji ina da dan shege??”1
Murmushi sadiq yayi yana mikewa tsaye ya ce
” Mutumina wannan fa ba abun damuwa ba ne. To mene a ciki idan ka aureta? Sai kayi auren a sirrance. Kwana nawa ne an yi zabe an kare. Tarzoma ta kwanta. Ka zake ta ta kama gabanta. Ka ga kayi mata lumbu lumbu kenen wutar kaikayi. Duk inda ka aureta ka saki wa zai kama wani zancen fyade? Wa sai damu da wani shege. Ina ganin hakan shi zai sa ka tsira da mutuncinka”.3
Shi ma tsaye ya mike shawarar bata masa ba. Ya aureta yace ya auri wa? Kilaki ma kilaki irin Rebecca?
Amma me? Sai ya ji kamar yana son ganin dan. Ya kalli idon yaron a hoto sai ya ga kamar ya kura ma sa ido.
Ya sunkuyar da kan sa. Sadiq ya ci gaba da nuna masa auren nan fa shi ne dubara. A haka suka rabu.
Wani abu da Almustapha bai sani ba shi ne makiyansa suna tare da shi. Wadanda ya yarda da su , su suke masa gadar zare su suke neman ganin bayansa.
Sadiq da Rebecca bakinsu daya! Ita yake yiwa aiki. Babu wani shiri na rebecca da ba ta qulla hade da sadiq ba. Shi ke kawo mata labarin Almustapha. Shi ya gaya mata daidai lokacin da ya kamata ta shigo cikin rayuwarsa ta tarwatsa ta!12
Ya gaya mata zai ziga shi ya masa gadar zare har sai ya aureta, kuma da sannu za ta gano musu abinda Almustapha ya mallaka a hankali tana sato musu.
Haka suka je aka yi test tabbas da nasa ne. Sadiq ne ya nemo malamai da shaidu kalilan aka daura wannan aure.
Daurin auren da ya jawo aka fara yiwa matafiyan dauki dai dai!Haske shi ne maganin duhu…amma yaushe hasken zai zo? Yaushe zai bayyana?11
Kano, Nigeria
Kwance yake akan wani katafaren gado da aka lullube da wani lallausan zanin gado. Ji yake kamar yana bacci kamar idonsa biyu. Irin baccin nan da ka kan yi idan damuwa ta yi maka yawa, gabanka na faduwa fat fat.
Kafin wani lokaci ya ji kamar yana kasa numfashi. Sai a lokacin ya lura ashe wuta ke cin dakin.
Wani abun ban al’ajabi uku ne ya sa shi cikin dimuwa.
Na farko baya ganin hasken hutar illa tsananin zafin da yake ji. Na biyu wani DUHU ne ya mamaye shi ba ya ko iya ganin tafin hannayensa. Na uku ya kasa tashi ya gudu daga wannan duhun da ke mamayarsa.
Wannan wani irin al’amari ne?
Kamar babu iska…
Kamar ba ya numfashi…
Ka
mar baya gani..
Sai gata ta bayyana a cikin duhun, siffarta ce kawai kuma don ita ma bata tare da haske. Ta mika hannu kamar zata taimake shi. Amma sai duhun ya mamaye da ita!
Shin yaushe haske zai bayyana? Abinda yake tambayar zuciyarsa kenen.
Almustapha ya tashi firgigit daga wannan mummunan mafarki ya jike da zufa sharkaf! Har yanzu ya kasa daina jin zafin nan, duhun nan ya matukar ba shi tsoro. Me ke faruwa wai?
Wacce ya gani a duhu tare da shi, ko a mafarki sai ya gane surarta RUKKY ce!To me ya kawo ta irin halin da yake ciki?
Watakila hakan na da dalili na yarda ya sa ta a rai a ‘yan kwanakin nan. Ya wayi gari yana matsananciyar kaunarta! Kaunar da bai taba zaton ana yiwa karuwa ba!3
Yarinyar ta shigar masa rai ta zauna daram dam. Har yakan ji son kamar wani abu ne da aka halicce shi da shi. Ya lura ita ma ta kamu da son sa da kuma tsananin kishinsa.
Dalilin kenen da ko da wasa bai bari zancen aurensa na sirri da Rebecca ya kai gurinta ba. Zata haukace ne kawai a idonta yake kallon kishinsa da take.
To wai a haka za su kare rayuwa? Wai yaushe zai ‘yanta kan shi daga irin wannan rayuwar ta rashin tabbas? Lokaci yayi da zai san abinda yake ciki, shekaru ja suke, kwanaki tafiya suke. Da ya tuna mutuwa sai tsikar jikinsa ta tashi yarr.4
Shin ba sharri mahaifinsa ya kulla ba har ya sa yanzu ya fada wannan rayuwar. Shi ba matacce ba shi ba rayayye ba? Kowa ya guje shi harta matansa. Idan ba don shi Almustapha ba yana ga da yanzu ya rube ya lalace sabida wari da rashin kula.2
Wani abu ke daure masa kai shi ne, a kullum ya je wajensa a cikin sarkakken harshensa ya kan ce da shi
” Al..mus…tapha…duhu! Duhu shi..mmamaye ni!”
Kamar baya gani amma idanuwansa a bude suke. Haske ya kaurace masa duniya ta juya masa baya. Shin ko shi ne duhun?1
Da sauri ya tashi ya dauro alwala ya fara jero sallolin nafilar da ya manta rabonsa da su. Ya san laifuffukansa dayawa, ga shi nan kullum sai tsunduma kan sa yake cikin sabuwar matsala.2
Ko da ya je ofis a ranar tunanin bai bar zuciyarsa ba. Al’amarin Rebecca ya daure masa kai. Ya tuna ranar da yayi ido biyu da dansa, sai da ya ji kwalla ta tarar masa. Kamar an tsaga kara.
Shin wannan bai zame masa izina ba? A ce duk zamansa da tsohuwar matarsa khairiyya bai taba samun da ba sai akan karuwa? Wai shin ana yiwa Allah wayo?7
Sai ya ji yana so ya kaunaci yaron amma idan ya tuna wai shi ya haifi shege sai gabadaya ransa ya dagule. Kiri kiri ta hana a taho da shi aka bar shi ahannun mai kula da shi acan kadunan wai ita takamar kar ya cutar da shi. Shi ma dai ya ga fa’idar barinsa don hakan ma ba karamin taimakawa zai yi ba wajen adana sirrinsa.4
STORY CONTINUES BELOW
Me zai faru idan mummynsa ta ji? Ita mai mutane mai kawaye na zarra? Ai ya gama jawo mata abun kunya cikin mutanenta. Hakan sai ya zame ma ta abun gori. Balle kuma jama’ar duniya!9
Baya son zancen nan ya bullo, dalilin kenen da yake lallaba Rebacca kafin tarzomar siyasa ta kwanta ya dauki mataki a kanta.2
A halin da ake ciki tana zaune ne a gidansa tayi kane kane. Ta kuma uzzura masa da cewar ko yaya ne sai ya kira aminansa makusanta ko da guda 5 ne an yi wata dinner ta nuna aurensu. Wai ta san halin musulmai sarai, idan ba shaidu aka ajiye ba yanzu wani abu ka iya faruwa a ce ita ba matarsa ba ce.
Zancen da ya kawo cece ku ce tsakaninsu. Daga karshe ya amince ba wai don komai ba sai dan a lallaba a wuce wurin. Ya matukar gajiya da matar amma da sannu zata gane ko shi wanene.
Wannan yarinyar Rukky dole ne su zauna su san abinda suke ciki.
Watakila ya kamata su shiryu su daina zaman haram3
Watakila ya ce tayi istibra’i ta koma gaban iyayenta
Watakila ma ya bata jari yana ga hakan kamar zai tserar da ita cigaba da irin wannan rayuwa
Watakila ya aureta!wa ya sani??1
Watakila shi ma ya tuba!
Da alama irin duhun da ke neman mamaye mahaifinsa ne ya doso shi. Ba zai yi karshe irin na mahaifinsa ba ya tabbatarwa kan sa.
Kafin wani mugun abu ya faru da rayuwarsa zai tuba. Bari tarzomar siyasa ta kwanta.7
Iya yanayin tunaninsa kenen, hangensa da hasashensa bai wuce na yana da cikakken lokaci ba.
Haka mutanen duniya suke kamar Almustapha!2
Sukan kididdigi rayuwarsu tamkar su suka tsara ta.1
Sukan hangi tuba a wani abun da ka zo musu da sauki, da ka zo musu a lokacin da suka so.1
Mai karatu shin ko ka san illar lokaci?5
Shin ko ka san adadin kwanakin da suka rage maka a duniya?
Shin ko ka tuba?3
*********************************
Yara ne guda biyu dukanninsu ba zasu wuce shekara 13 ba. Suna zaune ne a kan benci a wani filin kwallo da ake horar da yara. Dan farin mai suna fahad ya cigaba da daura takalminsa na ball idanuwansa taf da kwalla da kyar yake daura takalmin ma. Daga gani yana cikin tashin hankali.
Abokin nasa Abba ya dafa shi ya ce
” wai me ya sa kullum za ka tafi sai kayi ta kuka?”
Maimakon yaron ya ba shi amsa sai ma ya fashe da kuka. Abinda ya tayar da hankalin Abban shi ma kwalla ta taran masa yana lallashin abokin sa. Daga karshe fahad din ya samu ya ce
” Mamanmu ce fa ta tafi ta bar mu. Kullum idan muka koma gida bata nan. An dade sosai kullum bata nan.Ta ce wai babanmu ne ya kore ta”
Wani tausayi ne ya mamaye zuciyar Abba. Da ya tuna yanda yake kuka shi ma lokacin da mamansa za ta tafi sa’ilin da suke gidan Hajiya uwani. Kwata kwata baya so mamansa ta tafi, ya fi son lokacin da take zama da su shi da kanwarsa Asiya.
Sai ranar nan ta zo ta tafi da su. Suka je wani gida mai kyau. Sai ya koma ba sa kwana da yunwa, suna zuwa sabuwar makarantarsu kuma suna da kayan wasa kala kala. Sai yake ta murna shikenen zasu zauna da mamansu yanda suka saba. To amma sai dai me?
Sai yayi kwana da kwanki bai ga mamansu ba. Asali ma wataran tana cikin gidan da suke amma ba sa ganinta. Sai dai yana ta ganin wasu suna zuwa masu manyan motoci kuma mamansu tana ta musu dariya.
STORY CONTINUES BELOW
Ranar da ya ga wani da mamansa sun fita ya zata cewa babansa ne. To amma mamansu ta ce babansu ya mutu kuma idan an mutu ba za a dawo ba. To shi waye???
Yana son mamansa sosai. To amma akwai wani abu da yake ji game da mamansa da ba zai iya gayawa kowa ba.
Yakan ji a gidan kakarsa hajiya uwani tana cewa wai mamansa bata da kirki. Wai kudinta na haram ne. Su Anti safara sun ce wai mamansa yar iska ce. Yan unguwarsu suna kiran mamansa wani suna..ko me? Ya manta.
Sai ya ji ya fara jin kamar baya son mamansa. To me yasa yaje jin haka? Me yasa?
Da ya tuna yanda yake ji idan mamansa bata dawo gida ba sai yaji tausayin abokin sa fahad ya lullube shi. Sai ya ce da shi
” kayi hakuri. Ka dunga yin addua wataran zata dawo. Ni ma babana da mamanmu tace ya mutu ina masa addua”.
Fahad ya share hawayensa. Ya ce
” ka san me? mamana ta ce wai wata ce ta raba mu da babanmu. Ita ce ta sa babanmu ya kore ta. Wai sunanta karuwa!”
Sai da gaban Abban ya fadi. Shin ba wannan sunan ne ya ji ana gayawa mamansa ba? Amma ta ce wai karya ne ba sunanta ba ne. Amma daga ji ya san ba abu ne mai kyau ba. Sai yayi shiru yana tunani har fahad ya ce masa
” To kai me yasa ba ka san komawa gida, sai ka wuto nan bayan ba koyan kwallon ka ke yi ba?”
Abba yayi shiru sannan ya ce
” Kawai gidan baya mun dadi ne. Saboda kullum mamana bata nan”
Sai fahad din ya ce masa
” kai ka ma ji dadi ai ko bata n
an tana dawowa, in ta dawo zaka ganta”
Abba ya kalle shi a mamakince ya ce
” wa ya gaya maka? Wataran a wajen aikinsu take kwana ai! Iya ce ke kula da mu. Rabe ya kai mu makaranta”
Fahad din yayi shiru yana tunani sannan yace
” Au har kwana mamanku take a aiki? Ko likita ce? Mamansu abokina Ridwan ma likita ce tana kwana a asibiti”
Shiru Abba yayi. Bai san me zai ce ba. Shi dai ya san mamansa ba likita ba ce don bata allura. Amma..?
Sai kawai ya bawa fahad ansa da
” Ban sani ba wallahi”2
Sai suka mike gabadaya. Zasu zauna a teburan da ke gaban wajen. Anan ne idan aka zo daukanka za ka gani. Suna tafiya a hankali fahad ya ce
” Babanmu ne zai zo daukana yanzu ko zaka zo mu ajiyeka a gida? Amma fa tare suke zuwa da wannan mai suna karuwan data kori mamanmu. Babanmu yanzu baya son mu kamar da. Da nace matar babanmu ce sai mamanmu tace wai bata auri babanmu ba. Ka san me mamana ta ce? Wai wataran sai ta kashe wannan me suna karuwan! “2
Wani irin abu Abba ya ji marar dadi. Shi ma sai ya ji ya tsani matar yana kuma tausaya mamansu fahad. Sai kawai ya ce
” Ba komai Allah zai saka wa mamanku”
Suka zauna a bakin gate din gurin. A lokacin motar baban Fahad ta iso gurin. Ya ce
“Ga babana nan ma ya iso ka zo mu sauke ka”
Suka doshi motar. Zaune yake a motar da wata mace tsaleliya a gaba. Sun iso motar kenen, juyowar da za ta yi Hindu tayi ido biyu da Abba dan ta. A firgice ya ce
” Mama”!!!15
**********************************
” Ahap! Wa billahillazi Rukky tunda uwata tayi kuskuren satalo ni duniya ban taba ganin kifin rijiya kamar ki ba” cewar ‘yar modu ” yo mace har mace da ke ,son kowa bakinciki da haushin wanda bai samu ba, abun hassadar wanda kika subucewa amma namiji dan babarsa ya miki haka! Kwarankwatsa dubu sukari ko ni mace ‘yaruwarki lalacewa nake a kallonki ballantana namiji dan hau!sarkin zalama ba! Namiji kenen. Ga abu a hannunka kana hangen na wani! Manta alherin jiya ba , ai sai maza mutanen mu!”3
STORY CONTINUES BELOW
Rukky ce zauna akan kujera mai cin mutum uku. Ta kishingida da wata rigar bacci a jikinta , zuwan yar madu bai sa ta tashi ba ko ta canja daga yanda take. Hira ma suke yi ta aminan juna. Bata da wata masaniya cewar yar modu ne ya kaiwa luba labarinta. Ta dai san kawai yanzu kowa ya san Almustapha na ta ne. Ko ma ya ta same shi wannan ba damuwarta ba ne.
Kawai dai yanzu harkar gabanta take yi tunda dai su Luba da Hindu dai ko lamarinta ba sa shiga. Bai dame ta ba, ita dai idan aka barta da Almustaphan ta to komai daidai kenen.2
Jin ranta take fes bata da wata damuwa. Sai take jin kamar duniya ta ma ta kadan ta sha shagalinta. Dama haka duniya ke da dadi? Mutum ya yi abunda yake so a sanda yake so? Ya taka uban kowa! Ga ta ga masoyinta mai zai dame ta? A halin da take ciki ne yar modu ya kawo mata ziyara har gida suna yar hirarsu sai taji zancensa ya karkata wani waje.5
Ta zunkuda kafadarta kadan cikin nuna halin ko in kula ta ce
” Au yau kuma ware ranar ka yi ka zagi maza? To kuwa baka zo a daidai ba don ni nan na dauke su ‘yan goyo da zani”
Ya kalle ta galala sai ya kwashe da dariya yana tafa hannu ya ce
” Ahayye nanaye..yau na ga abunda ya isheni. Ana ga annabi kina rintse ido. Yaki ya taso ina ruwanmu da kura? Shi wanda kika goya da turmin zanin kwarankwatsa dubu ya hankada ki rijiya kafa dubu! Ahayye nanaye..Ana tsiya tsiya a bariki..to kinji!”11
Sai ta dan tashi ta zaune. Ta san zancen duniya yana bakin ‘yar modu kuma baya kawo zancen karya. To amma ya sa ta a tunani. Ta ce
” wai me ke faruwa ne? Sai wani lauya zance ka ke. Ka fito sak ka fadi kawai abinda ke ranka. Wani abu ne ya faru da Almustaphan?”
Ya ce
” Yaki dai bai kare ba a legas, rikici ake zuuuuqar! Mutane sai mutuwa suke”5
Wani tsaki ta ja ta ce
” yo ai ta kashewa mana! Indai ba uwata aka kashe ba ina ruwana”
Yayi sauri ya ce
” Ta kwarankwatsa dubu wannan karin uwar ta ki ma bata tsira ba!”5
Ta kalle shi a fusace ta ce
” Ka san me kake cewa kuwa? “
Ya ce
” Yo ba fa sallah nake ba ballantana ki ce nayi rafkanuwa. Jarida ce da ni mai tsada. Iya kudinki iya adadin inpomeshan din da zai marabci kunnuwanki”7
Hannu ta sa a wata jakarta nan kusa da ita ta zaro kudi yayi caraf ya amshe. Sannan ya gyara zama ya ce
” Masoyinki Almustapha autan maza, wanda kika goya da turmin zani kwananansa biyar cif da angoncewa. An ce wai ya auri wata arniyar saman dutse”3
Wani abu ne Rukky ta ji ya tafi da ita kamar guguwa. Ta ji gabanta ya fadi ras! Cikin wani irin tsananin gigita ta ke kallon ‘Yar modu ta ce
” karya ne! Karya ka ke! Almustapha ba zai taba min haka ba. Ka san irin son da ke tsakaninmu kuwa? To ko aure zai yi ni kadai zai iya aura!”6
Ya kalleta galala ya ce
” Au Allah? Au Allah hurul aini cikomakon matan duk duniya! To ko da yaqutu aka sassaka ki ya samfe ya auri wata ba ke ba. Yo da ma bariki ai ta gaji haka. Ka warce a warce maka. To in banda abinki Sukari ba a yin ‘yar warce warce ke kya same shi?”21
Bakaken maganganun yar modu ba su dame ta ba, labarin da aka gaya mata ya fi komai daga ma ta hankali. Ji tayi kamar zata haukace, bata taba tunanin tana da kishi ba sai yau. Almustpha ya auri wata ba ita ba? To ina zata saka kanta? Ai sai mutanen gari da makiyanta irinsu luba ma suyi mata dariya. Ji take kamar ta mutu don bakin ciki!
STORY CONTINUES BELOW
Kawai sai ta ji kuka ya zo ma ta, abun da ta dade bata yi ba. Ta kalli yar modu a gigice ta ce
” Almustapha nawa ne, nawa ne ni kadai! Duk wacce tace zata shiga hurumin nan ta sha mamaki! Wallahi yar modu bazan iya barwa kowa shi ba! Da sannu za su sha mamaki na!”
Ta yi sauri ta wawuri wayarta da alama kiransa za tayi ‘yar modu ya sa hannu ya warce. Ya ce
” ke wawiya. Idan za a kaiwa makiya farmaki a ba a sanar musu. Dirar mikiya ake yi a tarwatsa komai”6
Ta kalle shicikin rudu ta ce2
” To ni yanzu ya zan yi? Ka san yadda raina ke suya kuwa?”
Ya ce
” shirunki. Ai ni haka nake idan mutum ya mun 10 to bi zatil rasulullahi sai na masa ashirin. Na ji a wata majiya anjima kadan za suyi wani dan taron cin abinci. To kawai bayyana za ki yi kamar mahadi mai karshen zamani ki tarwatsa komai! Ita kuwa annamimiyar ki mata billen Allah tsine uwar mai karya! Kayan sarki ai ba na ‘yan gari ba ne. To kin ji!”25
Ta ce
” Ai kuwa ka kawo shawara. Shi ma munafikin da bai gaya min ba ya sha mamaki na. Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Na rantse da Allah zan iya yin komai akan gayen nan!”
” shirunki sukari..ai ba kiyi farin banza ba.” Ya sa hannu yana zaro wasu kwalaben syrup da tabar wiwi yana cewa
” Ki sha ki sha kiyi mankas! Sannan ki tunkari abokanan gabarki. Yadda in kika je sai ki zagi uwar kowa! Yo uwarki ce? Yo ko uwar mutum kika zaga yaushe hakan zai dame ki, yaushe ma kika san kin yi? Yo me aka yi da maza inji karya??2
Almustapha na zaune a kujerar wani wajen cin abinci mai suna peacock. Kusa da shi Rebecca ce sai wasu abokanansa guda 4. Iya wadanda ya ga zai iya kira kenen.
Komai na rayuwwarsa yanzu taka tsantsan yake yi da shi. Ran sa a jagule yake komai na duniya ba ya masa dadi yin sa yake akan dole. Rebecca nema take ta zame masa kashi a wuya kuma ya rasa yanda zai yi.
Zuciyarsa ta gaya masa ya jure yayi hakuri na dan lokaci daga baya ya dauki mat
aki.
Abincin da aka kawo a gurin ma bai iya ci ba, rabonsa da ya ci cikakken abinci ma ya manta. Tun kwana biyu da suka wuce ya ke ganin misdcalls na Rukky amma ya gagara dauka. Ya rasa me zai ce, ya san har yanzu ba ta ji ba. Baya so ta ji har ayi a gama, burinsa kenen.4
Ko da Rukky ta bayyana a gabansu kamar mahaukacin kare , kan ta kamar ba daya ba saboda kayan mayen da ta sha. Gaban Almustapha ya bada daam! Duk inda hankalinsa yake ya tashi!
Ta kalle shi ta ce
” Ba don kai na zo ba bakin munafiki saboda na san ba yin kan ka ba ne. Amma daga lokacin dana dauki mataki akan ta zaka dawo hayyacinka.
Ta juya ga rebecca da ke mata kallon mamaki ta ce
” Ke! Kida….huma..arniyar kan titi. Ki kama kan ki Almustapha nawa ne ni daya. Kin taba ganin anyi sarki biyu a masarauta daya! Da kika rabe shi ba ki tambayi waccece sukari ba? Dakalin majina ce ni a hau ni a zame na hau mutum na zauna daram! Fitarki daga rayuwar Almustapha tamkar fitarki ne daga cikin uwarki! Shin za ki taba komawa?”10
Sai fa yan guri suka zama yan kallo abinda ke kara tayar da hankalin Almustapha kenen. Abin sirri ya koma abin tsiya?
Wohoho ina wuta Rebecca ta jefa Rukky. Kallonta take kawai cikin tsananin mamaki. Karamar yarinya irin haka har ita zata tare ta ta gaya mata maganganun banza kamar haka!8
Rebecca ke kallon Rukky da mamaki ta ce
” And who the hell are you? Kin san kina wasa da wuta kuwa? Kin san wacece ni?”
STORY CONTINUES BELOW
Ke din banza! Arniyar ka..n du..tse! Yar gabar bakin teku! Ub..an ku.turu yayi kankani Alqur..an!
Almustpha da wadannan abokanan na sa ne sukai nufin shiga tsakani. Sai ‘yar modu da ke neman janye Rukky wai zata daki Rebecca.5
Rebecca ba tayi wata wata ba ta cakumi Rukky tayi katantanwa da ita ta wurga kan wasu tebura masu tangaraye suka fardi tar…tsa..tsa!1
Abun da ya daki zuciyar Almustapha ba da wasa ba.
Kafin ya ankara Rukky ta dauki wata fasasshiyar kwalba anan ta doshi Rebecca da ita tana cewa
” Ni ki ka wurgar?..to ..daga yau..uwarki ma in taga kayana bata taba ba ballantana ke! Yau sai Na Kashe ki! Zan kasheki! Sai naga uban da ya tsaya miki! Ta nufo ta da fasasshiyar kwalbar zata caka mata.1
Wani irin wawan juyi Almustapha yayi ya cakumi Rukky a wuya ya shaketa. Ya kura mata kwayar idonsa ciki tashin hankali yake cewa
” Kina da hankali kuwa! Kina da hankali! Kin san me kike yi kuwa!”
Wannan abun ne ya sa tayi sanyi lakwas. Ya cigaba da kallonta a idonta yana ganin wasu irin abubuwa da ya kasa tantancewa. Sai ya ji wani tausayinta ya mamaye shi, wani irin tausayi da bai taba jin shi akan kowa ba. Ko hakan na da nasaba da mafarkin da yayi?3
A idonta ya ga wani abu da take kokarin lullubewa.
Akwai wani abu, dole akwai
” Lahaula wala kuwwata ni jikar A’i!” Cewar yar modu ” yau an bani an lalace. Karamar magana ta zama babba. Ke Rukky zo mu bar gurin nan tun kafin ki jawo mana alakakai”1
Abokanan hudu su ne suka janye Rebecca. Almustapha da yar modu suka fita da Rukky.
Abinda ya konawa Rebecca rai kenen. Kiri kiri ya nuna Rukky yake so. Lallai da sake, za su sha mamakinta.
Manaja din restaurant din yace su tattara su fitar masa ko kuma yanzu ya kira ‘yan sanda.1
Ko da suka je mota Al Mustapha bankawa Rukky balai yake na irin halin da ta nuna a ciki. Sai daga baya kuma ya lallashe ta da ta je gida ta saurare shi.
Kuka kawai take, ji take kamar zuciyarta zata tarwatse. Komai na rayuwarta ya dunga dawo mata kamar a majigi. Yanda ta rasa kowa. Yanzu ma haka zata rasa Almustapha.
Ta dauka haduwarta da Almustpha zai sa ta tuba, zai sa ta fita daga rayuwar karuwanci amma sai ga shi hakan na nema ya subuce ma ta.( ta manta don Allah ake tuba)3
A hankali ya cigaba da kallonta tana kuka sai ya dafa kanta ya ce
” I’m sorry, i’m so sorry. Ya kamata ni da ke mu gane wannan rayuwar ba rayuwa ba ce. Ya kamata ki koma gida hakannan. Ya kamata mu san abun yi tun kafin lokaci ya kure mana.
Lokaci na da illa babba, yakan tarwatsa mafarkai ne. DUHUn da ke rayuwarmu ya kamata ya yaye. Kina ga kamar yaushe haske zai bayyana?
Sai ta kara fashewa da kuka. Ta koma gida? Ina ne gida?. Ta san ma yaudarar ta yake. Kamar irin yadda take yaudarar kanta. Da me za a yi da ita? Dattin kazantar zina? Ragowar maza barkatai!
A hankali ta ce da shi
” In..a …ne gida? zuciyata ita kadai ce gidan da zan iya kira nawa!”
Da haka suka rabu yana kallonta a mamakince.
Sai daga baya ya gane dama ba su rabu ba! Dama ya hana ta tafiya! Da wata kila sun samu daddadan labarin adarwa. Watakila da rayuwa tayi kyau.2
To amma antaba gujewa rubutacciyar Kaddara?6
*********************************
Ko da ta je gida ba ta kara komai ba in banda banke banken kayan mayenta. So take ta manta da komai ta manta da kowa. Sai ta amince cewar babu abinda zai mantar da ita fiye da shaye shaye.
STORY CONTINUES BELOW
Kowa baya son ta. Ita abun gudu ce. Ba za ta samu farin ciki ba.
Washegari ne ta ga an aiko mata da wani text kamar haka
” I am sorry” Almustapha
Sai ta duba da kyau sai taga kamar sabuwar lamba. Wato canja layinsa yayi kenen. Dama wadancan layukan ko ka kira ma bata shiga. Haka yake da canje canjen layuka kamar marar gaskiya. Ko da yake ai marar gaskiyar ne ta ayyana a ranta.2
Sai taji ranta ya ma ta sanyi ashe dai bai manta da ita ba. Dama ta san Almustapha masoyinta ne. Wannan arniyar ce take son raba su, ta ga ma kamar asiri ta masa. Da sannu zata dawo da abunta hannunta.
Sai ta kira sabuwar number ta sa gama ta ringing amma ba a dauka ba. Tana ajiye wayar ne wani sakon ya shigo
” Mu dunga communicating ta sakon text kawai saboda kar Rebecca ta zargi wani abu”
Wani uban tsaki ta doka ta wurgar da wayar. Cikin takaicinsa ta ce
” sakarai matsoracin namiji kawai. Akan mace duk ya bi ya susuce. An ba shi ya sha a ruwa” ta cigaba da harkokin shaye shayenta.
Sai ya zamana har dare tana amsar sakonnin Almustapha da ke nuna yadda yake kewarta. Sai ta daina amsa shi saboda haushinsa da ya cika mata rai. Kira ba zai iya amsawa ba saboda yana tsoron matarsa amma a boye ya cika ta da sakonni. Kai namiji! Sai a bar shi. Wasu ta ba shi amsa wasu ta share shi kawai.
Washe gari da safe ne maigadinta ya shigo mata da sakon wasu jajayen furanni ya ce an ce a bata.
Ta karba roses ne, tana mutuwar son su. A jiki akwai wata ‘yar takarda an rubuta
” with love, from Almustapha”
Nan da nan ta ji ranta yayi fes. Ashe dai da gaske yake. Ita har ga Allah ta dauka yaudara ce kawai irinta maza. Wata zuciyar ta raya mata ko dai ta je ofis din sa? Da ta tuna abun da ya faru jiya sai ta fasa.
Ta tura masa da sakon godiya shi kuma ya bata amsa da kada ta damu. Ya dora da cewar zata ji shi nan ba da dadewa ba.
Ko ma dai yaya ne ta ji dadi. Sai ta fara dokin ranar da za su dawo kamar da. Ko da yake ya fa ce su bar irin wannan rayuwar. Ita ma kwanakin nan ji takeyi komai ya fice a ranta. Tana ga kamar lokaci yayi da zata gayawa Almustapha wacece ita. In ya so daga nan sai ya kwato mata dukiyarta daga wajen iliyasou Tillaberi. Daga nan sai su yi aurensu. Shikenen ta huta da wannan rayuwar marar tabbas. Tunaninta kenen4
Da misalin karfe 7 na dare sai ta yanke hukuncin zuwa wani club watakila ma ta biya wa kawarta Reza su je tare. Tana ga kamar hakan zai dan sanyaya mata zuciyar.
< p>
Text ne ya shigo wayarta
” Mu hadu a gidana da karfe 8, akwai muhimmiyar maganar da za muyi”3
Kawai sai ta daka wani uban tsalle. Duk yadda take tunanin abun ma ashe bai kai nan ba. Ta san ma nunawa Rebecca zai yi ita ba tsaran ta ba ce. Ahap!
Sai ta rushe zuwanta club da biyawa kawarta Reza. Ta shiga ta gyara kwalliyarta yanda kallo daya zai mata ya gigice. Ta dauki yar jakarta da bata rabuwa da kayan shaye shaye tayi gaba zuciyarta fes!
Ta shiga motarta tana bin wata waka turanci ta michael jackson mai suna thriller wacce a ka sa a gidan radio din da take saurare.
Ko da ta isa gidan 8 ta gota da ‘yan mintuna. Kallo daya maigadin ya ma ta ya gane ta don ba bakuwarsa ba ce. Gida ne da ya zama gidan zuwanta. Kwanan nan ne ma bai cika ganinta ba.
Ta wuce ciki ta faka motarta. Kai tsaye kamar gidan ubanta ta shige ciki jin ta take a sama. Jin ta take daidai da kowa.
Falonsa na sama ta wuce ta cigaba da trying layinsa amma ba a dauka. Ta yi masa text da cewa ta iso. Ta samu guri ta zauna. Ko ina hakimar ta ke? Oho wannan ruwanta don ba gurinta ta zo ba.
STORY CONTINUES BELOW
Ta fi minti talatin a zaune ba Almustapha tana ta kiran layinsa ba ansa. Ba ko tsoro ta fada dakunansa da ba bakin zuwanta ba ne tana duba shi amma baya nan. Sai ta fada kicin anan ta tarar da kuku. Ya san ta sarai suka gaisa. Ta ce
” ina ogan ka ne wai? “
Ya ce
” oga ai bai dade da fita ba”
Sai abun ya bata mamaki to ko ya gaji da jiranta ne ya fita? To amma me yasa ba ya daukan wayarta?
Ta ce
” To madam fa?”
Ya ce
” Madam de inside, for her part”
Kawai tsaki ta buga ta fice.
Gidan nasa da ma wani tafkeken gida ne me sassa daban daban. Shi yasa ma ta shigo gaba gadi saboda ta san sai ta shigo ta fita ma basu hadu da Rebecca ba.
Da ta jira ta ga bai dawo ba, kawai cikin fushi ta fice. Tana ganin wannan ma ai wulakanci ne. Amma zai san da ita ya ke. Ko dai ya fasa son ta ne? Ita ta ma yi zaton ma zancen auren zai ma ta, daga nan ya ce ma ta ya rabu da Rebecca.
Kawai sai ta ji wata kwalla ta tarar ma ta a ido. Ta tsani rainin hankali.
Sai ta wuce motarta a fusace ta shiga ta fice daga gidan. Maigadin na ma ta Allah kiyaye ko kallonsa ba tayi ba ta fice a guje. Idonta har rufewa yake don bacin rai.
Sai ta kama kan ta tana kuka.
Ba shiri ta ciro wata tabar wiwi ta fara zuqa ko ta ji saukin yadda take ji.
Ta yi tafiya kamar ta minti 15 aka tsayar da ita a wani checkpoint da ba ta yi tsammani ba.1
Abinda ya sa tayi sauri ta kashe wiwin kenen sai dai kuma har yanzu qaurinta ya mamaye motar. Ta tsaya tana kokarin kama kan ta. Ba karamin aikinsu ba ne yanzu ta kare a cell.
Baqi dogon dan sandan ya leko ta tagarta qaurin wiwi ya dake shi ya ce
” wai wai madam kaurin menene haka? Park well park well”
Ta gangara bakin titi ta paka motar tana jan uban tsaki. Ya kalle ta tsaf ya gane ta sha wani abu ya ce
” madam ina drivers license? Ina takardun motarki?”
A lokacin daya abokin aikin na sa ya karaso. Kaurin da ya ji shi ma a motar ne ya sa ya ce
” ke zamu je station da ke wato ku ne bata gari ko? Kuna shaye shayenku kuna tuki. Sai kun je kun doke wani a zo a ce tsautsayi ne.”
Sai a lokacin ta dan dirice don bata da ko daya. Ya ce ta fito daga motar. Sai a lokacin suka ga shigar jikinta babu marabarta kadan da tsirara. Takaicin ta ya kara kama su. Dayan ya ce ma ta
” you be ashawo ko? Lallai yau kin gamu da gamonki. A cell za ki kwana!”
Bata kawo komai ba don ta san kudi su ne kare magana. Tayi sauri ta zaro ‘yan dubu dubu a jakar da nufin ta basu toshiyar hanci jakar ta fadi ragowar kwalaben syrup syrup da ke cikin jakar da sauran wiwi suka tarwatse a kasa.
Na farkon ne ya ce
” ka gani ko? Ka ga irinta ko? Shi yasa a ka samu wannan patrol din kwannan nan. Saboda yan iskan gari. Ashe ma yar maye ce. Ba drivers licence , ba takardun mota sai kwalaben shaye ahaye a motarki. Wallahi ko waye ubanki yau sai ki je bayan kanta!”
Dama a qule yake, kawai sai ya samu wacce zai saukewa ya dunga zuba bala’i.
Suka ce sai sun caje motar suka fara haska cikin motar ita kuma tayi firi firi da ido ta ji zancen cell. Sai yanzu take bakin cikin fitowarta a wannan dare.
STORY CONTINUES BELOW
” Madam bude boot! Bude boot!”3
Ya buga motar bam!
“Yanzu haka ma dealer ce ke, ‘ya’yan masu kudin nan menene ba za a gani a wajenku ba. Duk zamu iya da ku..yau yau din nan kya gayawa aya zakinta”
Ta saka hannunta na karkarwa ta bude ta wajen mazaunin direba. Na farkon ya haska da tocila.
Akwai tayar mota a ciki sai kuma wani himilin abu an nannade kamar kayan wanki
Na biyun ya ce
” menene wannan? ” a fusace. Jikinsa na raya masa makamai ne, dama kasar na cikin tarzoma, ire irensu ke safarar makamai suna basaja. A haka a haka ake janyo balai a kasa.
Bai jira amsarta ba ya zunguri abun da bakin bindiga ya rikito yana me yaye mayanin.
Abu daya ne tal ya faru ya sa suka ja baya a tsorace cikin wani karaji!
Bayyanar wata shirgegiyar gawa!2
” what the hell”!!
Ihun da yasa ta leko boot din motar a firgice ita ma ta leka.
Sai tayi ido biyu da abinda ya sa numfashinta yake neman daukewa.
Shirgegiyar gawar Rebecca ce a boot din motar jini na malala ta wuyanta kamar an yanka rago.16
Sai ta daskare a tsaya
Tunaninta ya tsaya cak
Ta nemi yawun bakinta ta rasa
Ta nemi numfashinta ta rasa
Ta gane abu daya. DUHUn rayuwarta ne ya danno. An mata gadar zare ta fada!2
Yanzu ta gane. Shiri ne!
Ba da Mustapha take magana ba, makiyanta ne!
Su ne suka yi mata gadar zare ta rufta da ita.
Bata tantance halin da take ciki ba sai da ta ji dansandan ya auna mata hancin bindiga ya na cewa
” You are under arrest”!!
” You are under arrest”!!
” For murder”!!
A kwayar idonta sai ta ga kamar momodou yana kuka!!2
**********************************
Sakarai bata da wayo1
Na gano abun mamaki ta audu mai roko, an yi haihuwa a garinsu, ana ta gayyar barka
Uwargida ta tashi, ta debi ruwa sai taje ta rangada wanka sai ta dauro leshi
Daya kuma sai taje ta dauro supa
Sai ta kusa da su ta je dauro joji
Kuma ga yal gwaggwaronsu ga murjani1
Kuma sannan ga agogo ga takalma
Sakarai bata da wayo
Oh..yaya ni na bi ku?
Yaya ina gyautan nan da kike cincin in sassabe shi in bi ku…1
Karan da wayarta ke yi ne ya katse ta daga rawar da take takawa ta wakar barmani coge. Nishadi take ji, Shi yasa ta ware wakar mutuniyar tata a sipikun dakinta tana cashewa.
Ta rage karan wakar ta dauki wayar cikin murmushi tana sauraren abinda na daya bangaren zai ce. Ya ce
” An gama”
Ta murmusa ta ce
” Haka ake so, ka bace bat kamar walkiya. Zan neme ka”
Ya ce
” Aiki yayi kyau, komai ya tafi kamar yadda ake so”
Cikin izza ta ce
” Da sauran kyaun aiki. Da sannu jaridar gobe za ta samar musu da labarin da zai tarwatsa tunaninsu!
Kwatankwacin yadda suka tarwatsa nawa!
Mosoyiyar tasa na cinnawa karnuka!
Gobe Almustapha zai gane dukiya da suna kayan aro ne da duniya ta ba shi, shin ko ya zai ji idan ta buqaci ya maido mata kayanta????