MAIRO CHAPTER 2

MAIRO

CHAPTER 2


fisgota momi tayi ta jefar k’asan carpet “lallai Maryam baki da hankali daga ganin mutun baki san inda ya fito ba ki wani rumgumeshi dubi yadda kika bata masa riga”
momi ta kalli yarima “dan Allah Yarima kayi hakuri hankaline bata da”
cikin kuka Mairo tace “nida hankalina niba mahaukaciya bace”
hannu momi ta ɗaga zata ɗaketa Yarima ya rik’e “no momi plz”
hannu yasa ya ɗago Mairo yana bata hakuri,

kuka Mairo tace yanzu ta fara daman mai nema a duhu balle an yada duk yadda yaso tayi shiru k’iyawa tayi.
fuskarta ya kama da hannayensa biu ya rik’e iya karfinsa ta kasa juya fuskarta shi kawai take kallo.
“yi shiru kinji in kina son na baki apple da abu mai daɗi”
kai ta ɗaga “to na daina”
“good girl”
handkerchief ya ciro ya share mata hawaye ya cire mata majina,

juyawa tayi tana hararar momi k’asak’asa ta gefe Yarima yayi murmushi ya rika hannunta ya “muje ki raka ni”
lakkame masa hannun tayi “ba kace zaka bani abun daɗi ba”
baice mata komai ba ya kalli momi yana murmushi yace “ni ban wuce momi in Qasin yazo ki gaishe shi”
fuska a sake momi ta amsa mishi “to zan faɗa miki mun gode a gaida gida”
kuɗi ya ciro masu ɗan dama ya aje mata sannan ya fice rike da hannun Mairo.

motarsa ya nufa harya buɗe rike yake da hannunta yana zaunawa ya kama ɗayan hannum ya rike “faɗa min miye dan gantakarki da gidan nan?”
turo masa baki tayi “to ni nasan mi kake nufi ne”
shiru yayi yana tunanin yadda zai mata ta gane “faɗa min momi mamar suwa ce?”
kai ta ɗaga sama “maman yaya da Siraj da Usman da Nura su kenan”
“good ke kuma ina mamanki?”
“mu bamuda mama sai dai Gwaggo tana can gida”
“yauwa to faɗa min ya akayi kika zo nan gidan?”
“da sukaje can suka zo dani nan gidan”
“to faɗa min Qasin yace miki wani abu da ya gamu tare?”
“a a baice komai ba”
banɗir ɗin 500 ya ciro ya dora mata saman hannu yana faɗin “karki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake kinji”
da karfi tace “to bazan faɗa ba” tana wani kallon kuɗi tana dariya.
har kasa ta duka tana masa godiya,
kunnenta ya kamo yana faɗin “duk kika faɗawa wani saina ɓata dake kuma bazan sake miki komai ba”
ɗagowa tayi tana kallonsa “wlh ba zan faɗa ba ko za a kasheni”
murmushi yayi “yauwa jeki kar moni taga kin daɗe”
tashi tayi da gudu ta nufi cikin gida.

saida yaga shigewarta sannan yayi ma motarsa key.
kaura suka tashi yi da Qasin daya kunno kai cikin gidan shi kuma yana k’ok’arin fita da sauri Qasin ya bashi hanya dan yasan shi ba jaye mishi zaiyi ba, saida ya fita sannan Qasin ya karaso parking space a ransa yana mamakin abunda ya kawo Yarima yanzu,

da sallama ya shigo parlour momi ta amsa masa Mairo ta nufeshi da gudu tana nuna masa kuɗin “yaya ka gani Yarima ya bani duka kuma ni kadai”
kuɗin ya karɓa ya duba yana kokarin zaunawa yace “momi miya kawoshi yanzu kuma”
“jiyara ta kawoshi kuma yace a gaishe ka”
“a gaishe ni? yanzu fa kasa bari yayi na shigo saida na kauce masa”
momi tace “to ai kasan halin kayan ka”
Mairo ta riko hannunsa “yaya kuma harda mumi yaba kuɗi masu yawa”
lakatar mata hanci yayi “ke wai ba ance miki momi ake cewa ba ki daina cewa mumi”
turo baki tayi tana kallon momi “to kuma yaya momi tace mun banida hankali”
kamin Qasin yayi magana momi tace “ai ba kida hankaline Maryam”
kara ɓata fuska Mairo tayi “kaji ko?”
Qasin yayi dariya yace “haba momi Maryam fa nada hankalinta komai na hankali take dan Allah ki daina ce mata mahaukaci”
“Allah ni bana mata ɗaukar masu hankali kaga abunda tayiwa Yarima yanzu?”
“mi ta masa?”
“bata fa sanshi ba daga ganinshi ta tazo a guje ta rumgumeshi ga hannayenta ba kyau har cup ɗin hannunshi ya faɗi”
Qasin ya kalleta “amman ya dakeki ko?”
momi tace “bai mata komai ba dama zan daketa hanani yayi inajin yan k’aurai ne bisan kai harda fa kuɗi ya bata”
murmushi Qasin yayi ya shafa kan Mairo.
yace “ya santa ne shiyasa”
“ina ya santa?”
nan ya bata labari kamar yadda Mairo ta faɗa masa da kuma haduwar da sukayi Dubai Mall,
Momi tace “shiyasa kika rumgumeshi ni ai nayi mamaki yadda naga ya sakar mata fuska harda share mata hawaye”
uhum kawai Qasin yace yana kallon siraj dake saukowa downstairs.

Story continues below

“Maryam faɗa min mi Yarima yake ce miki daya rike miki hannu?”
wani irin ɓata fuska tati ta ɗago tana kallonshi “ni baice min komai ba kawai yace yace yace yana siyomin kayan daɗi kuma kuma yana in yana gaida momi”
taɓe baki yayi “aikin banza”
momi tace “kaga halin nan naks Siraj sam bana sonsa ai kodan girmanka da yayi yaci ake ka gaisheshi amman kaki”
“wlh momi matukar bai sauke wannan girman kan dake tare dashi ba to baza mu taɓa haɗa hanya ba”
cikinsa momi tayi da faɗa “bana fason shashanci Siraj bai girmeka miye abun girman kai a ciki mutun ya tako kafarsa har nan cikin parlour nan ka kasa yi masa magana kaifa da kanka ka buɗe masa kofa ina ruwanka da girman kansa”
murmushi yayi ya nufi kofa “Siraj”
kiran Qasin ne ya juyo dashi “na’am yaya”
“nasan bai fika da komai ba amman ka rika masa magana tunda momi bata so”
kai ɗaga masa ya fice.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*17*

tsaki momi taja “da gaskiya Yarima da yace Siraj bashi tarbiya”
kallonta Qasin yayi “shi yace haka?”
“eh”
“shi Yarima har ya iya buɗe baki yace Siraj bashi da tarbiya”
momi tace “ai da gaskiyarsa ace murun ya shigo ka kasa masa mana dama fa na tambayeshi cemun yayi baisan ko wanene ba jifa”
“haba momi duk abunda Siraj ai baici ace gaban idonki ya furta bashi da tarbiya ba shi har ya isa yayi miki wannan maganar gaban idonki duk fa wadda ya aibanta maka abu kaiya aibanta babu wadda zai buɗe baki kaf duniyar nan yace yayan gidan nan basu da tarbiya”
cikin faɗa yake magana cike da jin zafin maganar.

momi tace “miye na wani tada jijiyar wuya akan wannan maganar”
tashi yayi tsaye yana faɗin “hmm iskancin Yarima yayi yawa sai yayi nadamar furta wannan kalamin”
tashi ita momi tayi tsaye “Qasin bance kayi rigima da shiba wannan maganar kuma ta wuce karka kuskura ka masa wani akan wannan maganar kaji na faɗa maka”
tana kawai nan ta nufi upstairs.

Mairo tayi war da ido ta rufe baki “tho momi tayi fushi kuma kaine”
murmushi yayi ya shafa kanta ya fice.

saida momi taji ficewarsa sannan ta fito tun kamin ta karasa saukowa Mairo tace “momi yaya yasa kinyi fushi ko?”
momi ta karasa saukowa tana faɗin “a a ni banyi fushi ba”
“to mi yasa kika masa faɗa kuma kika shige ɗaki saida ya fice kika fito?”
basarda maganar momi tayi “muje cikin mu karasa girki kar babanku ya dawo bamu kare ba”
da sauri ts nufi kicin momi ta rufa mata baya,

*_washe gari….._*
tara saura Qasin ya shigo part ɗin momi zaune ya tararda ita tana kallon aljazeera news saida yaɗan kalleta sannan ya zaina kusa da ita yana gaisheta,
juyowa tayi ta kalleshi fuskarsata ba yabo ba fallasa bayan ta amsa tace “ga abun breakfast ɗinka can inka kare zamuyi magana”
faduwa gabansa ya ɗanyi jin harsun karya basu jirashi ba,
su jiki a sanyaye ya kalli momi yace “ke har kun karya ne?”
“eh yau tea kawai nayi su Usman da Nura sunci nasu sun tafi makaranta”
“ke fa momi?”
“ni tun part ɗin babanku na karya nida Siraj maryam ce kawai bata tashi bachi ba”
bai sake cewa komai ba ya tashi ya nufi dining.

ruwan tea kawai ya zuɓo ya dawo kusa da momi ya zauna “momi wace magana ce?”
shiru momi tayi na ɗan wani lokacin kamin ta kalleshi tace “akan maganar matarka ne”
faduwa gabansa ya ɗanyi “momi wani abun ne?”
“a a ba wani sabon abu bane kawai dai na gaji da dafa maka abinci kana ci,
matarka na kwance tana yadda taga dama da aurenka ace kullum sai kazo nan kaci abinci kaci na rana kaci na dare banda na safe  tu na maka wannan lokacin da baka da aure yanzu kan bazan maka gaka ba”
Qasin jim ya ɗanyi sannan ya kalli momi yace “momi bata saba bane kota girka ba wani daɗi yake ba”
“to ta rika girka maka haka nan ko ruwa ne ta rika dafa maka kana sha daga yau dai bazan sake aje maka abinci ba kodai kayiwa kanka abun kunya kaci na kasuwa ko kuma ka cilasta mata ta girka maka”

Story continues below

“to momi a bamu maryam saita ri..-”
hannu momi ta ɗaga mishi “dan Allah karka soma na baka maryam ita da bata san zafin gikinta ba ko? kai da ka iya kare mata in anyi magana ka iya kareta ita yar masu kuɗi yar boko bata iya komai ba sai hutu ko to nadai faɗa maka kuma bazan bada maryam ba in yar aiki zaka ɗauko ya rage naka”
kansa na kasa har momi takai aya,
ko kaɗan bai jidaɗin maganar ba.
       “shikenan momi zan san abun yi shine kawai matsalar?”

kai ta ɗaga mishi tana kallon Mairo dake saukowa sanye da kayan bachi.
murmushi ya sakar mata “maryam kin tashi?”
“eh momi ina kwana yaya ina kwana”
“lafiya kalau kin tashi lafiya?”
kusa da momi ta zauna tana “kalau momi yau ba ayi kari ba?”
“anyi kinga naki can kan dining”
zata tashi Qasin yace “momi nafa nema wa Maryam makaranta”
sai lokacin momi ta ɗan sakar masa fuska “amman kuwa daka kyauta gaskiya a ina?”
“nan tudun wada Alex international school makarantar nada kyau kuma suna karatu sosai”
wani daɗi Mairo taji ta riko hannunshi “yaya da gaske?”
“da gaske mana ina miki karyane?”
“a a kuma zanje?”
“eh yau zamuje su tantanceki in aka shirya komai saiki fara zuwa”
tashi tayi ta shiga rawa tana taɓi da hannu momi tayi dariya “yau fa abun nema ya samu sai a dage ayi karatu in yaso sai a samu wadda zai rika miki lesin kina ɗan karawa”
Qasin ya tashi yana faɗin “nima haka nake sonyi yadda zatayi ssurin fahimta da kuma islamiya sai a nema mata ta na kusa kidai shirya mata kamin 11 sai muje ayi komai”
“to saika fito”
Mairo ta kalleshi “yanzu zamuje?”
“a a saikin karya kinci abinci”
“to bari nayi sauri”
da gudu ta nufi dining shi kuma ya fice yana murmushi,

”’   *    *    *   ”’
tunda suka fita sai basu dawo ba sai dare Qasin na rike da hannunta suka shigo parlour.
Siraj ne ya taresu yana zolayar Mairo “eyye yar kauye an sata makaranta eyye aiko za a ga kauyanci kai”
murguda masa baki tayi “eh naji koma minene naji mai k’aton kai”
momi tayi dariya “a a maryam kan yar birni ce ko?”
nan Mairo ta nufeta “eh momi kuma karantar nada kyau kuma gidan sama ce har sun bani kayan makarata kuma momi wlh suna ta turanci harda yan yara”
Siraj yace “ke kan harki kare bazaki gani komai ba sai shinkafa”
ɓats fuska tayi “momi kin jishi ko?”
momi ta shafi fuskarta “ke kyaleshi xuwazuwa kema zaki iya ai da tambaya akan zama malami”
dariya tayi ta kwanta jikin momi tana rufe ido,

momi tana kallon Qasin tace “an kare komai ko?”
“eh anyi komai sunce monday zata iya fara zuwa ga uniform nan sun bata na biya kuɗin scul bos zata rika zuwa 7:30am tana ɗaukar ta in kuma suka tashi zata kawo ta”
“to Allah ya taimaka abbanku ma ya jidaɗi sosai”
murmushi yayi ya tashi “bari naga abbah naje na kwanta”
kai momi ta ɗaga mishi Mairo ta ɗago tana kallonsa “baza kaci abinci ba?”
kallon momi yayi dake kallonsa,
can ya ɗauke kai yace “bana jin yunwa”
ya sun kuyarda kai ya fice.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*18*

wasawasa Mairo ta fara karatu a’na mata lesin a gida na makaranta ma Qasin ya sakata.
in kuma lokacin islamiya yayi momi ta tura bata samun zama inba weekend ba da dare ma Siraj ne yake tisa mata ko Usman,

*_2:30pm…_*
schools bus ta sauke Mairo.
da gudu ta shigo parlour tana faɗin “momi yau”
bata karasa magabar tayi shiru ganin Yarima zaune saman kujera.

ware mata hannaye yayi yana murmushi kaɗan kaɗan ta karaso tana kallon upstairs.
saida ya mata kiss a goshi sannan ya rumgumeta,

da sauri ta ɗago tana masa magana kamar mai raɗa “ina momi?”
schoolbag ɗinta ya shiga cirewa “bata nan nima ban tararda ita ba”
“tana ɗaki ko tana kicin”
kai girgiza mata “bata nan ta fita”
“a a bari dai na duba”
kicin ta nufa ta fara duba bata ga kowa ba nan ta nufi ɗakin momi nan ma bata nan haka ta fito ta nufoshi hannu a baki ta ɓata fuska,
hannu ya mika mata yana murmushi “zo nan bana faɗa miki bata nan ba”
ba musu tazo kusa dashi ta zauna hannu yasa ya cire mata takalmin makaranta da safa ya kara janta kimusa dashi ya riko mata fuska,
“pretty gal wani sirrin zanyi dake”
shiru tayi sannan tace “na minene?”
“bazaki faɗawa kowa ba?”
“wlh Allah ni bazan faɗa ba kofa wannan da kace karna faɗa har yanzu ban faɗawa kowa ba”
hannunsa yasa yana taɓa lips ɗinta “da gaske kodai kin faɗa?”
“wlh ban faɗa ba”
“yauwa haka nake so wannan ma karki faɗawa kowa kuma karki bari kowa ya gani kinji zan baki abun daɗi da kuɗi kinji”
“tho amman ka xaka kawo min kayan daɗi da gaske harda ice cream da madara kuma kaje dani yawo”
hannunsa yasa yana shafa gefen fuskarta “zan miki duk abunda kike so matukar zaki mun abunda na saki”
da sauri tace  “zanyi minene?”
“zan fada miki zaki daiyi ko?”
war tayi da ido “eh da gudu ma”
murmushi yayi ya shiga mata chakulkuli tana dariya saida tayi mai isarta ya jata jikinshi ya rumgumeta yana shafa bayanta,

Story continues below

“Maryam….”
kamar daga sama taji muryar Qasin da sauri ta ɗago tana ganinshi jikinta ya shiga rawa Yarima kuna bai fasa shafa bayanta da yake ba koma ɗagowa baiyi ya kalli Qasin ba saima haɗe fuska da yayi yana wani tsusar baki da yake na salon iskancin.

tsawa Qasin ya katsa mata “mi kike nan?”
tashi tayi tsaye cikin rawar murya tace “momi bata nan”
“bashi na tambayeki ba?”
razana tayi sosai tayi bayabaya tana son yin kuka zatayi magana Yarima ya tari numfashinta ba tare daya kalli gurin da Qasin yake ba “ba komai take ba miye matsalarka?”

kara haɗe fuska Qasin yayi yace “I thought da ita nake Magana”
tashi Yarima yayi tsaye yasa hannayensa Aljihu ya nufi Qasin cikin wata tafiya ta isa da tak’ama,

saida ya isa daf da fuskar Qasin ya sakar masa wani shu’umin murmushi yace “don’t put words into my mouth. I have got plenty to say”
wani kallo ya watsa masa tun daga samansa har kasa ya ɗauke kai ya fice.

wani kallo Qasin ya bishi dashi cike da jin haushi can ya juyo ya watsama Mairo wata muguwar harara,
aiko jikinta ya kara shiga rawa kamar mai jin sanyi.

cikin tsawa Qasin yace “baki san wanene Yarima ba ko miya tsayarda ke gurinshi?”

kasa masa magana tayi babu abunda zuciyarta take nuna mata saita shige cikin ɗaki ta kulle karya ɗaketa duk da bai taɓa dukanta ba amman haka zuciyarta take nunama ganin yadda yake harararta,

hankalinta bai kara tashi ba saida taga ya nufo gurinda take,
sakar masa ido tayi saida ya kisa kawowa kusa da ita ta watsa da gudu,
cikin zafin nama ya kaɗe mata k’afa ta faɗi.

gashinta ya riko ƴya tada ita tsaye “ina zaki ba tambayarki nake ba?”
fashewa tayi da kuka tana rokonsa “dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan kara ba wayyo Gwaggo momi”
saida ta kira momi ya tuna da ita da sauri yaja hannunta suka nufi kofa.
tana masa ihu ya buge mata baki yana mata alamar tayi shiru ba shiri ta rufe baki tana son mayarda kukan,

part ɗinsa ya nufa da ita wani emptyroom ya nufa da ita.
saida suka shiga sannan ya sake mata hannu ya kulle ɗakin ya zare bel ɗinsa ya buɗe mata ido “mi ya kaiki kwanta masa a jiki?”
baya tayi tana kuka ta kasa mace masa komai,
matsowa yayi yana faɗin “duk na sake ganin kin rumgumeshi saina miki shegen duka na rufeki cikin ɗakin nan babu wadda ya isa ya ceceki”

sai a lokacin ta soma magana “dan Allah yaya kayi hakuri bazan sake ba wayyo momi”
bel ɗin ya ɗaga sama kamar zai buga mata wani irin ihu ta saki tayi cikinshi ta rumgume mishi kafafu tana kuka,

“lafiya Qasin miya faru?”
mansura ce take masa tambayar tana jijjigar kofa.
nan Mairo ta koma kiranta “anty mansura zoki ceceni”
ɗagota “aya rufe min baki”
da sauri tasa hannu ta toshe baki tana ɗaga masa kai.
juyawa yayi ya buɗe kofar ya dawo parlour bel ɗin dake hannunshi mansura ta rika kallo kamin ta kunno kai cikin ɗakin tana duɓe duɓe,

bata ga komai ba sai Mairo take tsaye rufe da baki tana shawaye.
rikota mansura tayi suka fito gurin Qasin ta nufo tun kamin ta karaso ta jefa masa tambaya “mi kayi mata Qasin?”
ba tare daya kalleta ba yace “mi kike tunanin zanyi mata?”
“ka bani amsa ta kawai Qasin ya zaka saka ta cikin ɗaki harda zare bel zaka ɗaketa mi tayi maka?”
wani dogon tsaki yaja ya tashi fuska a haɗe ya fisgi hannun Mairo suka fice.

tunda suka fito Mairo take masa magiyar karya daketa,
yana shigowa parlour ya jefarda ita saman kujera yana kiran momi.
jin shiru yasa ya nufi upstairs. bai jima ba ya fito ya nufi kicin nan ma bai jima ba ya fito ya nufi gurin Mairo dake kuka,

da sauri ta tashi zaune tana share hawaye sai wani numfashi take kamar zai ɗauke,
“ina momi?”
“ta fita koda na dawo ban ganta ba Yarima kawai na isko”
cikin rawar muryar kuka take masa maganar,

Story continues below

ido ya tsura mata tayi kasa da kanta hawayen na zuba.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*19*

ajiyar zuciya ya sauke ya ciro handkerchief ya kama fuskarta yana share mata hawayen “yi hakuri kinji bazan sake ba daina kuka”
kai ta ɗaga masa tana wani wahalallen numfashi,
kwantarda ita yayi saman kujera “wanta kiyi bachi?”
harta kwanta sai kuma ta ɗago ta kalleshi “yaya karka faɗawa momi kaji?”
kai ya ɗaga mata ya tashi ya fice.

takura kanta tayi saman kujera ta matse guri ɗaya kamar wadda aka cilasta tana matsar kwallah har bachi ya ɗauke ta,

”’   *   *   *   ”’

*_2 hours letter…_*
can cikin bachi taji muryar momi da Siraj,
    da sauri ta tashi tana soshe2.
Momi na kallonta taja wani dogon tsaki “haba Maryam ace mutum kana girma kana cin k’asa kamar ki ace inkin dawo makaranta ba kisan ki cire uniform ba saidai ki samu guri ki kwanta dubi kiga har lokacin islamiya ya wuce kuma baki san ki saka uniform kije ba”

ɓata fuska tayi “to momi ba fita kikayi ba kika barni”
nan momi kasa ce mata komai tayi dan takaici in banda tsakin data sakeyi ta nufi kicin,

momi na shigewa Siraj yaja mata kunne “ba wani daman baki son makaranta yar kauye”
fashe masa tayi kuka ta tashi tana aika masa mugayen duduna tana son huce haushinta akansa.

tsawa momi ta katsa mata “wuce ki cire uniform ɗin nan kiyi wanka kila ma ko abinci baki ciba?”
kai ta ɗaga
Momi tace “Allah ya shiryaki maryam wuce kije kiyi wanka duk kika sake yin abunda kikayi yau saina miki shegen duka”
kamar ta fasa kuka ta nufi stairs Siraj na zolayarta,

ta kusan minti 30 toilet ɗin tana wasa ruwa saida taji motsin momi a bedroom sannan ta fara wanka,
koda ta fito momi na zaune saman kujera tana duba wasu matirial da atanfofi.
     kallonta kawai Mairo tayi ta nufi waduraf ta ɗauko wata atamfa red colour riga da saket tasa ko mai bata shafa ba ta janyo k’aton hijab ɗin momi tasa ta shimfiɗa carpet ta soma sallah,

momi na kalle da ita saida ta rama azahar sannan tayi la’asar.
bayan ta sallame ta cire hijab ɗin ta jefar saman bed ta nufi kusa da momi ta zauna,

    “momi kayan waye?”
kyaleta momi tayi saida ta kare danne2 wayar da take sannan ta kalleta “na siyarwane”
shafa kayan ta shigayi “wlh momi suna da kyau suma siyarwa zakiyi?”
momi bata amsa ba ta kama hannunta ta kira sunanta a natse “Maryam”
dariya tayi “na’am momi”
“magana zamuyi ki bani hankalinki kinji banason kisa wasa ki daina dariya kinji?”

wani haɗe fuska tayi saida tasa momi murmushi sai kace wani cartoon ta wani tada kafaɗu “thom ina jinki?”
a natse  momi ta soma mata magana yadda zata fahimta “maryam ki daina abunda kikeyi kinji ba kyau kinga kara girma kike ba ragewa ba ya kamata ki rika sanin ciyon kanki ki daina abunda kike”

“tho ni kuma momi mi nayi?”
ajiyar zuciya momi ta sauke “yanzu fa saida kika rama azahar sannan kikayi la’asar kina ganin kin kyauta?”
kai ta girgiza alamar a a momi tace “tho kingani wadda fa yake haɗa salloli azaba ake masa ba kyau ki daina kinji?”
nan ta ɗaga kai “kuma kinga in kika dawo makaranta maryam basai nace ki cire uniform ba ki rika cirewa duk abunda kika san aikin kine ki rikayi basai nace kiyi ba kinji? ki zama yarinyar kirki”
wata dariya ta rikayi tana kallon momi tana tsutsar leɓenta na kasa,
can dai ta kawarda fuska tace “tho momi na gane koma minene kike nufi”
shafata momi tayi “yauwa yata haka nake so kuma ki dage ki rika karatu ba wasa banda faɗa ko jan magana kinji?”
nan ma kan ta ɗaga ta tashi tsaye “nidai bari naje naci abincin yunwa nake ji”
bata ko tsaya jiran abunda momi za taceba ta fice.

Story continues below

tana saukowa downstairs Qasin na shigowa.
suna haɗa ido ta juya da sauri zata koma hannu yakai ya rikota “ya haka ina zaki?”
upstairs ta rika nunawa “ɗaki zan kwanta ne”
murmushi yayi yaja ta suka nufi kujera bayan ya zauna ya zaunarda ita “baki san ba kyau bachin maraice ba?”
“eh ni ban saniba”
“tho ba kyau ki daina karki sake bachi da maraice”
“tho na daina bazan sake ba”
idonta a kasa take amsa masa dan tsoron kallonsa take.
lura da hakan yasa ya sakar mata hannu yace “tsorona kike ko maryam?”
shiru tayi tana wasa da hannayenta fuskarta ya riko “faɗa min mana tsorona kike ne?”
ɓata fuska tayi ta soma magana “nidai bana son duka in mutun yana dukana tsoronsa nake sosai”

murmushi yayi “tho na daina bazan sake ba ai ban dakekiba”
“eh amman ai kaso ka dakeni dan dai anty mansura tazo ne ka kyaleni”
tana maganar tana wani langwashe langwashen kai da turo baki,

dariya yayi tace “ai ba mansura ce ta ceceki ba daman ba dukanki zanyi ba”
harara ta watsa mishi “kai wlh karya ne tho miyasa ka ɗaga dankon zaka buga min?”
“minene sanki?”
rufe ido tayi tace “wannan wadda kaso ka dakeni dashi”
“bel?”
kai ta ɗaga tana kara matse ido dariya yayi yace “ki yarda maryam bazan iya dukanki ba kawai dai horaki nayi”
kwanta masa tayi saman jiki tana dariya,

“wlh karya ne dukana kaso kayi”
kunnenta riko ya rika murɗawa “ni nake karya?”
dariya ta rikayi tana faɗin “na daina ba kaiba”
haka ya rika wasa da ita soma masa kuka sannan ya saketa ta nufi kicin shi kuma ya fice.

washe gari tunda safe Mairo ta shirya kanta duk abunda momi ta saba mata ita tayiwa kanta,
sosai momi ta jidaɗi da schoolbus ɗinsu tazo har bakin gate momi ta rakata ta buɗe mata motar ta shiga.
hannu ta rika ɗagoma momi har suka fice,

*_2:30pm…_*
ta shigo gidan da sallama ta shiga parlour momi ta amsa mata da fa’ah “wa’alaikissalam yar mama an dawo?”
kai ta ɗaga mata tana cire takalmin makaranta,

daga gurin da take zaune ta jefasu gurin da aka tana da dan ajeye takalmin tana faɗin “momi yau Yarima ya kai mana ziyara a makaranta”
Usman dake zaune kisa da momi yace “da gaske?”
“eh wlh harda chocolate ya raba mana”
momi tace “gurinki yaje ko makaranta gaba ɗaya”
“a a makaranta dai kofa jiya yaje kuma yazo gidan na-”
shiru tayi ta kasa karasawa sai rabon ido take. momi tace “jiya ya zo nan? bayan fitana ko?”
wata dariya tayi “ke momi na tuna mafarkine nayi ba gaske bane”
tashi tayi da sauri ta nufi upstairs “bari naje nayi sallah nayi shirin islamiya”
  tanayi tana waigo momi harta shige.
momi kan daɗine ya isheta tana gani ta fara samun kan Mairo.

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*
 
    *_KHADEEJA CANDY_*

*20*

washe gari ma Mairo ita ta shirya ma kanta komai bayan ta saka safa ta riko schoolbag ɗinta ta nufo downstairs.

da dariya ta sarasa saukowa ta rumgume Qasin dake zaune saman kujera rike da laptop,
aje laptop ɗin yayi yana murmushi ya zaunar da ita saman kafafunsa “maryam har kin shirya?”
ɗagowa tayi tana murmushi “eh kuma ni na shirya kaina”
saukar da ita yayi jin motar makarantarsu ya karɓi jikar hannunta yasa mata,
da sauri momi ta fito kicin rike da kular abincinta tana faɗin “oya karɓi ga abincin ki naji motar ku”
da gudu ta karɓa ta nufi gurin da takalminta suke ta saka harta fice sai kuma ta dawo ta tsaya bakin kofa “momi ba zaki bani komai ba?”
“mi zan baki?”
shiru tayi tana bugun kofar parlour.
hannu Qasin yasa aljihu yana cirowa ya mika mata ɗari biyar,
wata dariya ta saki jikina na rawa ta karɓa tana masa godiya “na gode yaya” kai ya ɗaga mata ta fice da gudu.

ɓata fuska momi tayi tace “Qasin bana so karka sake ka ɗauki kuɗi har ɗari 500 ka bata”
hannu ya ɗaga “shi kenan na daina amman naga kamar bada yawa bane”
cikin faɗa momi tace “tho na dai faɗa maka bana so duk kyautar da ita karta wuce 100 zuwa k’asa”
tana kaiwa nan ta nufi kicin,
da sauri Qasin yace “owk momi yi hakuri ai ya wuce zo kiga wani abu?”
yi tayi kamar bata jishi ba shige kicin ɗin saida ta kare abunda take sannan ta fito.
har lokacin yana zaune ƴyana danne2 sa,
kujerar dake kusa dashi ta zauna “gani ya akayi?”
ɗagowa yayi ya kalleta “momi ɗan ruwan tea ma bazan samu ba?”
taɓe baki momi tayi “au daman jiran kake na ɗauko maka breakfast? inma shine dalilin zamanka nan tho tashi ka koma part ɗinka dan kasan munyi ba’ada dakai tun farko”
dariya yayi “a’a momi bashine ba abu zan nuna miki”
laptop ɗin ya ɗauko ya ɗora saman jikinta “kinga wani design ɗin wata kwangila da za’ah ba kanfaninmu”
duba momi ta shigayi tana faɗin “amman kan abun da girma sosai mi za a gina haka?”
“wani kanfani suke so a gina musu na sarrafa motoci _JAMES GLOBAL AUTOMOBILES_ sunan kanfanin shine na farko da zai kafa branch a Nigeria”
momi tace “aiko dasun kyauta muma mu ɗan samu cigaba kuma matasan mu su samu aiki”
“sosai ma momi kinga in aka ginashi mutun kusan ɗari biyar zasuyi aiki karkashin su kinga ai an ɗan rage kuma kanfanin sun iya motoci ana son motocinsu sosai sune zakiga J.G.A mutunin ɗan amerika ne”
momi tace “amman naji daɗi to kai zaka gina musu gurin ne?”
“tho haka ake tunani amman dai ba ni kaɗai bane mu uku aka kaimusu zasu zaɓa ne saisu bada kwangilar ga wadda suka yarda da aikinsa amman dai mutane da yawa ni suke cewa saboda kanfanin fitaccen kanfanine kuma muna aiki babu kissa ciki”
murmushi momi tayi “tho ai haka ake so Allah ya taimaka yasa ka samu”
“amin momi dan gaskiya zamu samu kuɗi masu yawa”
“to Allah ya yarda ya taimaka”
“amin”

Story continues below

tashi yayi rike da laptop ɗin yana kallon “bari naje can na karya”
kai momi ta ɗaga mishi “da yafi”
murmushi yayi ya fice.

*_7pm…_*
Mairo na zaune parlour kasan carpet ita da Siraj yana duba littafanta na makaranta sai zolayarta yake tana masa kuka yana sa ta karanta gurinda bata iyaba yayi mata dariya ita kuma ta buga masa fillo. suna haka sukaji an taɓa kofa duk juyawa sukayi suna kallon kofar,

cike da takama Yarima ya shigo ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke,
wani irin haɗe fuska Siraj yayi kamar bai taɓa dariya ba,
wannan karon Mairo batayi unkurin tarboshi ba ido kawai ta sakar masa tana dariya.
da murmushi ya karaso kusa da ita tashi Siraj yayi tsaye da niyar tafiya tunowa da magagganun momi yasa ya kalli yarima yace “sannu da zuwa”

banza ya masa yana tsutsar lips ɗinsa.
juyawa Siraj yayi cike da bachin rai ya fice,
            hannu Mairo ya riko yana murmushi ya nufi kujera suka zauna tare.
     
kallonsa tayi tace “ba kaji Siraj yana mska magana ba?”
lakatar mata hanci yayi “na jishi bana jin amsa masa ne”
murmushi tayi gyaɗa masa kai,
wasa ya shigayi da hannayensa yana faɗin
“pretty gal ya maranta?”

“lafiya kalau”

“ina momi?”

“tana ɗaki na kirata?”

hannu yasa yana taɓa lips ɗinta “a a karki kirata”
saida ya ɗaga kansa ya kalli upstairs sannan ya kalleta yace “gurinki nazo kinsan munyi dake zan saki abu ko?”
kai ta ɗaga “eh kuma kace zaka bani kuɗi kuna kace zak-”
rufe mata baki yayi da sauri jin motse saukowar mutun downstairs,
saida yayi mata alama da tayi shiru sannan ya juya da murnushi yana kallon momi.
“Yarima yanzu ake tafe?”
“eh momi ya wunin gidan?”
taka kokarin zaunawa tace “lafiya kalau maryam baki ɗauko masa abun sha ba?”

war tayi da ido tace “lahh mantawa nayi bari na ɗauko”
tana sauka ya riko hannunta ya tashi tsaye “a a momi barshi kawai yanzu zan wuce”
“da wuri haka?”
“eh kinga an kira sallar isha kuma daman biyowa kawai nayi naga Maryam”
da ɗan mamaki momi tace “owk tho a gaida gida”
hannu yasa aljihu ya ciro dubu 20 ya aje mata “ayi hakuri da wannan momi”
murmushi momi tayi “Yarima kenan Allah dai ya amfana”
baice komai ba yaja hannun Maryam suka fice,

motarsa ya buɗe mata ta shiga bayan ya rufe ya zagayo shima ya shiga.
“ina zamu?”
tambayar data fara jefa masa kenan tana kallonshi,

baice mata komai ba yasa hannu baya ya ɗauko laptop ya ɗora mata saman jiki “kinga wannan abun?”
“eh”
“kin taɓa ganinta?”
“eh sunanta kwanfuta”
mirmushin jindaɗi yayi “good wa kika taɓa gani da irinta?”
“malamin makarantarmu da yaya”
“tho kinsan mi nake ao dake?”
kai ta girgiza “a a”
“ta yaya nake son ki ɗauko min”

da sauri tayi waje da ido ta rufe baki “kaikai nidai babu ruwana baya so fa ina taɓa mishi kaya”
“ke mayarwa zanyi kawai inason na arane na ɗanyi wani abu sai na baki ki mayar”
lake kafaɗa tayi “a a gaskiya saidai nace ya aro maka”
haɗe mata fuska yayi “a a karki kuskura kice masa haka bazai bayar ba kuma inma yaji dukanki zaiyi kuma nima na ɓata dake”

hannu yasa ya ɗauko wata leda dake bayan ya mika mata “kinga kayan daɗi nan na siyo miki kuma gobe zan karo miki wasu kullum zan rika siyo miki kuma na baki kuɗi amman fa sai in kin aikata abunda nace”

shiru tayi tana tunani kamar ta fasa kuka ta kalleshi tace “amman inna ɗauko cewa zaiyi mi zanyi da ita”
“no ai bazaki bari ya gani ba a boye zaki ɗauko karki yarda kowa ya gani koda kuda ne”
“tho inna ɗauko ina zan ɓoye?”
shiru yayi yana kallonta kamin yace

“ke bakisan gurin da zaki ɓoye ba?”

“eh duk gurinda zan ɓoye gani za ayi”

“tho ki kaɗa rijiya”
“kai rijiya?”

“eh koki jefar wani gurin innazo sai ki faɗamin na ɗauko”

“ba zai lalace ba?”

“ba zaiyi komai ba kinji”
kai ta ɗaga mishi sosai yaji daɗi ya shafa kanta “good pretty gal”
“amman mi zakayi da ita”
idonsa ya shiga susa kamar wadda abu ya faɗawa “am zan ɗan ɗauki wani abune a ciki na cofa sai na baki ki mayar kinga bazai gane ba ko?”
da mirmushi ya karasa maganar itama tayi masa murmishin karfin hali,
kuɗi ya ciro masu yawa ya mika mata “gashi ki siye duk abunda kike so amman kinsan bazaki faɗawa kowa munyi wannan maganar dake ba ko”
“eh bazan faɗa ba”
“good kuma tsakanin gobe sa jibi nake son ki ɗauko min ita”
kai ta ɗaga mishi,

daga nan ya mika hannu ya buɗe mata motar shima ya buɗe suka fito tare.
Qasin na tsaye bakin kofa yana kallonsu yana rumgume da hannayensa fuskarsa a haɗe,
faɗuwa gaban Mairo yayi da sauri ta juya ta riko hannun Yarima ta soma kuka “nidai bazan iya zuwa ba ga yaya can yana kallona”
mirmushi yayi yaja hannunta suka nufi kofar parlour.

har suka isa Yarima bai kalli gefen da Qasin yake ba,
ita kadaice ke masa kallon tsoro jikinta har wani ɓari yake, da kansa ya buɗe mata kofar data shiga yayi mata byebye yana murmushi hannu itama ta ɗago mishi sannan ya rufe kofar,

yana juyowa Qasin yace “ka bani kunya ka kuma zubar da girmaka momi bata taɓa yiwa yayanta gurɓatacciyar tarbiya ba kuma bana tunanin za’a samu matsala a maryam dan haka ta banbanta da sauran matan da kake gani.
maryam karamar yarinya ce in zakayi sama kayi kasa ba za ah aura maka itaba balle baka daman lalata mata rayuwa dan haka banga abunda zai haɗaku ba”
yana kaiwa nan ya juya ya shigewarsa parlour.

kasa tafiya Yarima yayi sosai maganganun suka ɓata masa rai sai wani busar da iskar baki yake,
_ɗan iskane ni Qasin na karshe har yanzu baka gama sanina ba zan nuna masa true color na_
a zuci yake wannan zancen yana wani kashe ido.

Mairo na zaune kusa da momi tana nuna mata kuɗin,
Qasin na shigowa ta tashi tsaye da sauri tana masa kallon tsoro gabanta sai faɗuwa yake ganin yadda ya haɗe fuska,

yana karasowa kusa da ita ya fisgota ya jefar kasan carpet ya cire bel ɗinsa ya watsa mata,
wani ihu mairo ta saki ta durkushe guri ɗaya,
da sauri momi ta tashi ta rik’e “lafiya Qasin miya faru?”
kallon momi yayi rai a bace yace “bata jin magana ne momi so nake nayi mata dukan da in taga Yarima ko kallonsa ba zata sake yiba”
bel ɗin momi ta karɓe “miya faru wani abu tayiwa Yarima?”
“ba wani abu tayi masa ba shi daine yake son yayi mata illah”
kallon mamaki momi tayi masa “wani abun yayi mata ne?”

“momi kinfi kowa sanin halin Yarima ba mutunin kirki bane taya zaki rika barinshi yana keɓanta da maryam?”
sai a lsokacin moni ta gane inda ya dosa kallon maryam “Ke Tashi Kije ɗaki”
tashi maryam tayi ta gudu ta nufi stairs tana kuka.

saida ta shige sannan momi ta kalli Qasin tace “mi yasa kake da zafin zuciya haka ne Qasin?”
“ba zafin zuciya bane momi ina tsoron abunda zaije ya dawo ne kinfi kowa sanin halin Yarima saboda mi zaki barta ta keɓanta dashi ba ɗan’uwanta bane ba wani nata bane hasalima bashida wata alaka da ita ta dalilin mi zai rika bata kuɗi haka masu yawa kuma ki zuba ido kina kallo keda kanki kika ce bakison ina bata kuɗi mai yawa saboda karta lalace to akanmi zaki barta da Yarima?”

cikin faɗa yake maganar har jijiyar wuyansa na tashi,
kai momi ta girgiza tace “bana tunanin haka Qasin nasan waye Yarima”
wani murmushin jin haishi Qasin yayi ya fice,

a hankali momi ta kai zaune saman kujera tana nazarin kalamansa.
sai a lokacin wani tunanin ya soma bijiro mata,
ta kusan awa biu a haka sannan ta tashi ta shiga ɗaki.

*_washe gari…_*
Qasin na zaune garden ya wani aiki a computer yaji an dafashi,
a hankali ya ɗago suka haɗa ido da mairo da gefen fuskarsa ya kunbure,
murmishi ta ɗan sakar masa tace “yaya”
shima murmushin yayi mata yaja mata kujera ta zauna a kusa dashi “maryam kin tashi?”
“eh tun ɗazu”
“eh kaima kaci?”
kai ya ɗaga mata yana yana taɓa gurin daya kunɓurar mata “dukan da nayi miki jiya ne?”
taɓa gurin tayi “eh shine yaya karkayi fushi dani”
laptop ɗinsa ya matsar gefe ya kara matso da kujera kusa da ita “ba zanyi fushi dake ba maryam dukan jiya ma rai nane ya bace kiyi hakuri kinji?”

hawaye ne suka zuɓo mata “yaya ni banma ce ya bani kuɗi ba shine ya bani kuma bance ya sani mutarshi ba shine ya sani”
cikin kuka ta karasa maganar,

tausayinta Qasin yaji duk sai yaji ba daɗi hannunsa yasa yana share mata hawayen “ya isa daina kukan haka kinji bazan sake dukanki ba”
ɗagowa tayi ta kalleshi “kayi alk’awari?”
“eh nayi”
saida taja majina tace “malamin mu yace ba kyau saɓa alk’awari”

dariya yayi yace “maryam kwan wayo na yarda amman sai in kin min alkawari nima kin yarda”
“eh minene?”
ido ya tsura mata yayi shiru yana mata murmushi,

ganin haka yasa tace “yaya lafiya?”
ajiyar zuciya ya sauke yace “kalau kesan mi nake so dake?”
“a a saika faɗa”
“so nake karki sake kula Yarima duk abunda ya baki karki sake karɓa”
shiru tayi “koda kuɗi ne yaya”
“eh koma minene”
kai ta ɗaga mishi “tho bazan sake ba”
murmushi yayi ya rumgumeta yana faɗin “yauwa maryam ɗina”

“yaya mi yasa baka shiri da Yarima?”
daidai kunnensa tayi masa tambayar.
ɗagota yayi yana murmushi ya tashi ya rufe laptop ɗin ya mika mata “jeki ki kaimun ɗaki”
tashi tayi tsaye jikinta na rawa ta karɓi laptop ɗin tana kallonsa,
juyawa yayi ya nufi part ɗin momi ya barta nan tsaye.

Story continues below

laptop ɗin ta tsurawa ido tana shafawa maganganun Yarima suka rika mata yawo akai tunawa zuciyarta ta shiga mata zance biu akai akai takan kai duba gurin rijiyar dake gefen gurin sai faman haɗeye yawu take,
dukan da Qasin yayi matane ya faɗo mata rai nan da nan sai tsoro ya shigeta,
da sauri ta juya ta nufi part ɗinshi.

”’ ***************** ”’
*_6:15pm…_*
Qasin ya shigo part ɗin momi da sallama yana murmushi,
Nura da Usman suka amsa masa Maryam kuma ta tashi da gudu ta tarɓoshi “oyoyo yaya”
shafa kanta yayi “maryam oyoyo bita kikeyi?”
sakinshi tayi tana faɗin “eh kuma yaya iya”
zaunawa yayi yana sauke gajiya “yayi kyau haka nake so ina momi?”
“tana ɗaki bari na kirata”
da gudu ta nufi ɗakin tana kwalawa momi kira,

tare suka fito tana rike da hannun Mairo da murmushi ta zauna tana kallon Qasin “injin anyi nasara?”
dariya yayi yace “anyi momi saidai fa akwai yar matsala”
nan da nan yanayin fuskar momi ya chanja “wace irin matsala kuma?”
“wai sunce zasu min interview gobe bance wadda suka min yau”
“daman abun harda interview akeyi sai kace ɗaukar aiki”
ajiyar zuciya ya sauke “nima abunda yaban mamaki kenan momi kuma kinsan wani abu?”
“a a minene?”
“Yarima ne zai min interview ɗin kuma wai sai nazo da laptop ɗina sunga irin aikin da nayi”

lumshe ido momi tayi “oh ni har ka faɗarmun da gaba wannan tho ai ba wani abun ɗaga hankali bane sai kaje da ita ka nuna musu kuma duk abunda suka tambayeka ka basu amsa”
“momi bakiji mi nace ba Yarima fa zai mun”
“tho minene a ciki ai baka kirsa cikin aikinka ko kaɗan bana fargaba akan aikin da za’ayi maka”
“momi tsoron nake kar Yarima yayimin wani abun kinsan halinsa”
“karka taɓa saka wannan a ranka ka yarda da kanka Qasin karka bari damar nan ta wuce ka kaifa kmda kanka ka faɗa min kuɗine masu yawa”
kai ya ɗaga mata yana kallon maryam,

Usman yace “yaya ya akayi Yarima ya zama shine zaiyi maka interview ɗin”
Qasin yace “nima ban saniba amman dai kasan yana hulda da motocin kasashen waje kuma kasan tunda Illustrator ne inajin shiyasa”
“Allah dai ya baka nasara yaya”
duk suka amsa da ‘amin’
sun ɗan jima suna fira saida aka kira sallar magriba sannan kowannensu ya tashi momi da maryam kuma suka nufi ɗaki dan sallah.

*_Monday @10:30am…_*
cikin nasara akayiwa Qasin interview duk yadda Yarima yaso ya samu matsala Allah bai yarda ba duk abubuwan da suka bukata saida ya nuna masu Yarima yayi mamaki sosai ganin laptop ɗin,
bayan fitarsa akayiwa mutun 3 duk basuji sun gamsu dasu ba kamar yadda sukaji da Qasin sun daɗe suna ttaunawa kamin su yanke hukunci sosai Yarima yaso a bawa wani ba Qasin ba amman suka ki yarda dan sun lura da gwarewarsa nesa ba kusa ba,

*_2 hours letter…_*
suka aika aka kira Qasin daya shigo suka sake yi masa wasu tambayoyi,
ya amsa musu fiye da yadda suke tunani nan suka kara jindaɗi Yarima suka bawa files ɗin cike da jin haushi ya mika masa,
Qasin na murmushi ya karɓa yayi sign fuskarsa a sake ya mikawaƳYarima files ɗin yana murmushi yace “thank you”
murmushi Yarima wadda bai kai zuci ba “ur welcome Men”
hannu suka rika mikawa Qasin sunna masa congrats,

”’**********************”’
cike da jindaɗi Qasin ya shigo gida kai tsaye part ɗin momi ya nufa tun daga sallamarsa ta gane haka bata masa magana ba saida ya zauna “an daiyi nasara ko?”
dariya yayi ya mika mata jakar dake hannunshi “anyi momi sun bani”
ba karamin daɗi momi taji ba saida ta gama duba laptop ɗin sannan tayi ma Allah godiya “Alhamdulillah Allah mun gode maka haka nake so Alhamdulillah Yarima yaje?”
“eh tare dashi akayi komai shima ya bani files ɗin nasa hannu”

“masha Allah Allah ya tayaka riko”
“amin momi kinga fa ko breakfast banyi ba”
maganar yake yana wani sosa kai,
taɓe baki momi tayi tace “zakaci albakacin wannan ranar zan baka na yau”
murmushi yayi “aiko momi da kin kyauta”
tashi yayi ya nufi dining yana faɗin “yau momi gidan sit ba kowa”
“to ai kasan yau monday wazai zauna nima anjima kaɗan fita zanyi”
“tho bari na daukeki dan nima fitar zanyi”
taahi momi tayi ta nufi upstairs,
“bari na shirya wani abin kamin ka kare”
“owk momi”

Story continues below

kujera yaja ya zauna ya hau cin abincin har wani sauri yake yana lumshe ido raban da yaci abinci mai daɗi haka har ya manta kullum cikin siyen takeaway yake gashi abinci inba na momi ba baya jindaɗinshi,

kusan plate biu yaci yasha zoɓon da momi ta haɗa ya tashi yana hamdallah,
part ɗinsa ya nufa bai daɗe ba ya fito ya sake nufo part ɗin momi bayan ya ɗan watsa ruwa ya chanja kaya, zaune ya tararda ita tana jiranshi,
“momi har kin shirya?”
“eh so nake nayi saurin dawowa kar maryam ta dawo gidan ba kowa”
agogon hannunsa ya duba “gashi ko sun kisa dan 12 ta kusa”
tashi momi tayi ya ɗaukar mata jekar dake gabanta suka fice.

*_2:34pm…_*
Mairo ta shigo gida kamar ta fasa kuka ta nufo parlour dan tun gate maigadi ya faɗa mata momi bata nan,
jefa tayi da jakarta tsakiyar parlour ta nufi upstairs,
tana shiga ta cire uniform ɗinta ta ɗauki tawul ta ɗaura ta shiga bathroom wanka tayi tare da alwala sannan ta fito sai wani tureturen baki take tana matsar kwallah,
wadurof ta nufa tana buɗewa taji an kira amsawa tayi duk da bata san mai kiran ba ta rufe wadurof ɗin da sauri ta nufi kofa.

candynovels.wordpress.com

© *Khadeeja Candy*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*22*

da sauri ta sauko stairs tana rabon ido dan bata ga kowa ba har ta nufi kofa taji an rikota,
juyowa tayi da sauri suka haɗa ido da Yarima sosai ta razana ganin fuskarsa a haɗe gashi batayi tsamaninsa,
kokuwa ta shigayi dàshi tana son kwace kanta jikinta har wani rawa yake.
iya karfinsa yayi wurgi da ita saman kujera cikin jar fuska yace “mi yasa kika karya alkawarin?”
tashi tayi zaune tana kuka tace “yi hakuri dan Allah karka dakeni”
risinawa ya shafa gefen fuskarta “baki son na dake ki miyasa kika ki aikata abunda na saki? mi yasa maryam?”
shiru tayi tana kallonsa hawaye na mata zuba.
hannu yasa yana share mata wayarsa tayi ringing,
saida ta kusan katsewa sannan ya ɗauka banji mi akace masa ba saidai naji nace “Gret mun faɗi sai dai mu tari gaba… owk sai na ganka”
yana aje wayar ya tashi tsaye yana tafiya bayabaya fuskarsa ɗauki ke da murmushi saida ya kai kofa sannan ya juya ya fice,

ajiyar zuciya ta sauke ta kawanta saman kujera dafe da zuciya.
ta kusan minti 20 a haka sannan ta tashi ta nufi ɗaki,
cikin kankanen lokacin tayi shirin islamiya ta ɗauki littafanta ta nufo downstairs.

cike da tsoro ta sauko sai leke2 take har ta samu ta fita parlour,
har ta isa harabar gidan bata daina jin tsoro tana kisan isa gate motarsu momi ta kunno kai,
Qasin nayin parking mairo ta nufi momi ta rumgumeta idonta cike da hawaye.
murmushi momi tayi ta rumgumeta “maryam kin dawo?”
kamar tayi kuka tace “eh momi ki daina fita kina barina”
“tho na daina maryam jeki islamiyar karkiyi latti”
kin ɗagowa tayi saida taji an ja mata kunne sannan ta juyo da fuskar ta kalli Qasin,
murmushi ya sakar mata ya buɗe mata mota “shiga na kaiki”
ba musu ta shiga bayan ya rufe ya shiga mazaunin direba yayi ribas suka juya momi kuma ta nufi cikin gida.

tukin yake yana kallonta ita kuma kanta na kasa sai murza yatsunta take tana haɗiyar yawu,
A’hankali ya rage gudun da yake ganin haka yasa ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido yace “mi yake damunki maryam?”
shiru ta ɗanyi sannan tace “babu komai”
Qasin yace “kinsan ba kyau karya ko?”
kai ta ɗaga mishi
“tho faɗa min miya ke damunki?”
“nace maka babu komai”
“Yarima yazo?”
batace masa komai ba har yayi parking daidai gate ɗin makarantar saida ta buɗe motar zata fita sannan tace “eh yazo”
da sauri ta rufo motar ta nufi cikin makarantar,

saida ya daina hangota sannan yayima motar key da sakesake ya iso gida yana tuna yadda mairo ta rumgume momi,
har ya nufi part ɗinshi wani tunanin ya dawo dashi gurin maigadi ya soma masa tambayoyi bayan sun gaisa “Sadiqu bayan fitarmu waya shigo?”
“babu wadda ya shigo inba Yarima ba”
“ya jima nan?”
“a’a bai jimaba ya fita”
kai Qasin ya ɗaga mishi “owk na goɗe”
ya juyo ya nufi part ɗin momi,
da sallama ya shigo saidai bai samu mai amsa masa ba dan babu kowa parlour.
guri ya samu ya zauna yana sauke ajiyar zuciya sai kallon parlour yake ta ko ina kamar wani bako,
ya daɗe haka sannan ya tashi ya nufi part ɗinshi.

Story continues below

*_washe gari…_*
*7am* Qasin ya shigo part ɗin momi,
momi na kicin tana aiki taji shigowar mutum hakan yasa ta nufo parlour,
Qasin na ganinta yace “an tashi lafiya momi?”
“lafiya kalau”
“masha Allah maryam tqa tashi?”
da ɗan mamaki momi tace “eh tana ciki shirin makaranta take yi lafiya dai”
murmushi yayi ya nufi stairs “lafiya kalau momi abu zan bata”

a hankali ya tura kofar ya shiga tana zaune tana saka safa tana ganinshi ta saki murmushi “yaya ina kwana?”
“lafiya kalau maryam kin tashi lafiya?”
“lafiya kalau”
zaunawa yayi kusa da ita yana faɗin “shirin makaranta kikeyi?”
“eh”
“yayi kyau”
kafarta ɗaya rika yana saka mata safar “maryam jiya da Yarima yazo mi yayi miki?”
ɓata fuska tayi “nidai ba nace maka bai min komai ba bai min komai ba”
“tho miya yace miki?”
“nidai baice komai ba kawai yace gurin momi yazo kuma bata nan harda kuɗi ya bani amman ban karɓa ba sai yayi tafiyarsa”
tana maganar tana wani ɓalɓal da ido karya gano karya take.
daɗi Qasin yaji sosai da kanshi ya saka mata jikar makarantar yana murmushi yace “yauwa maryam daɗina dake jin magana kin kyauta da baki karɓi kuɗin nan ba”
rufe ido tayi ta fashe da dariya da gudu tabar ɗakin,

”’***********************”’
tafiya yake yana shewa (fito) hannayennsa na lakkame a bayansa.
duk gurin da yabi sai sun gaisheshi jiki na rawa amman ko kulasu ba yayi bare ya amsa gaisuwar sai wani rangashi yake har ya iso maidaidaicin parlour,

guri ya samu ya zauna bayan ya gaisheta ya ɗora kafa ɗaya saman ɗaya yana wani lumshe ido,
tsakin da yaji tayi ne ya sashi ɗago kai ya kalleta yana kalkatar dariya “haushi nake baki ko hajiya?”
taɓe baki tayi “Yusuf na gaji da maka magana na gaji da saka maka ido haba Yusuf sai kace wani yaro karami kullum ayita faɗar abu ɗaya ana maimai tawa”

rufe baki yayi kamar wani mai jin hamma “sorry hajiya komai ya kusa zuwa karshe na samu wadda nake so jira kawai nake ta karasa girma”
kallon rashin fahimta Haiyar tayi mishi “ban gane ba?”
murmushi yayi “na samu wadda nake so saidai karamace amman idona na kanta data girma zan ɗauke abunta”
maganar yake yana wani ɗaga hannu sama yana taɓe baki kamar wadda yasha wani abu,
kai Hajiya ta girgiza “Yusuf lafiyarka kuwa ban sanka da wannan halin ba”
dariya yayi yace “nayi miki kama da yan shaye2 ko kinfi kowa sanin bana shaye2”
“tho mi yasaka cikin wannan halin?”
“tsabar bakin ciki ne kawai”
“bakinciki kamar ya?”
kafaɗunsa ya ɗaga ya tashi tsaye yana faɗin “barshi kawai hajiya kona faɗa miki bashi da rana”
cikin rashin jindaɗi tace “Allah ya sauwake”
dariya yayi yace “amin bari naje ciki”
kofa ya nufa yana saida ya kusa fita sai kuma ya juyo ya kalleta yace “wlh hajiya bana shaye2 kuma ba wani abun na shaba karki saka wannan a ranki kinji dai na rantse wannan abun da nake tsabar bakincikine da kuma yunwa”
a jiyar zuciya ta sauke iya Tabbacci tana dashi akan Yarima baya shaye2 ko babu komai yakan yi mata irin haka wani lokacin saidai ba kamar na yau ba.
a kasale ta kalleshi tace “na yarda dakai Yusuf baka taɓa aikata irin wannan amman mi yasa ka bakinciki haka?”
yana rike da kofa yace “wani abin na sawa gaba kuma ban cima masara ba shiya ɓata min rai har na kasa cin abinci tun jiya amman karki damu yanzu zan koma daidai dan na hari gaba”
“Allah ya yaye maka ko minene Yusuf na yarda da kai”
murmushi ya sakar mata “good mother”
saida ta masa murmushin sannan ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*23*

yanzu hankalin mairo a kwance yake dan ta daina ganin Yarima ba tada wata matsala inba ta jarabawar da suke ba dan momi bata barinta ta zauna data dawo gida kullum ciki karatu take banda wadda ake mata a makaranta da kuma wanda Siraj yake tisa mata Qasin ma wani lokacin yakan mata,

”’*********”’
yau Mairo da far’ah ta tashi ita ta da shi kowa na gidan tare suka shiga kicin da momi aikin komai tare sukayi,
bayan sun kare ta shiga jerawa a dining tana wakewake momi na zuba mata abinci a kula tace “maryam yau far’ah me kike haka?”
fashewa tayi da dariya “oh momi kin manta yau muke kare jarabawa shikenan sai hutu”
momi ta rufe kular tana faɗin “o na ganoki shiyasa kika tashi tun safe haka tho Allah yasa a kara muku wata har 8”
da fuskar zolaya momibta karasa maganar
mairo ta marairaice fuskar “Allahumma a’a Allah karka amsa momi wlh bana son haka”
dariya momi tayi tace “tho na daina amman dai kinsan ta ɗaya zaki ɗauko mana ko?”
dariya tayi ta rufe ido “momi dan kinga ban iya ba ko?”
“a a kin iya maryam Allah dai ya bada sa ah”
“amin momi kin san kince in an mana hutu zaki kaini gurin Gwaggo ko?”
“eh anyi haka tho bari a muku hutun”
rumgume momi tayi cike da jindaɗi kamin ta sake ta ta ɗauki kular makarantar ta fice dan tuni motar makarantar ta iso,

Story continues below

*_2:37pm…_*
ta shigo gida uniform ɗinta duk ya bace da k’asa tafarta ma babu kyau gani,
tafiya ta rikayi laɓalaɓa har ta isa kofar parlour ta shiga leke.
cikin rashin sa’ah ta hango momi zaune ita da Siraj da sauri ta koma baya,
can kuma ta sake lekowa momi kamar wadda aka tsikara ta waigo suka haɗa ido.
“lafiya maryam kike laɓe?”
kara laɓewa tayi ta yadda fuskarta kawai ake gani tace “momi uniform ɗina duk yara sun lalashi”
“kamar ya? shigo mana”
“kasa suka samin kuma nidai banma yi qasan kasa ba sune suka samin”
“tho shigo”
“bazaki dakeni ba?”
“eh shigo”
daker ta shigo parlour tana wani kakkaɓen2 muna furci.

ɓata fuska Siraj yayi “yanzu maryam da girmanki zakiyi wasan kasa haka?”
harara ta watsa masa “ina ruwanka nida momi nake magana bada yara kananuba”
dariya Siraj yayi momi kuma tayi murmushi hakan yasa ts ɗan saki jiki ta matso kusa da momi “momi ni yarane suka ɓata uniform ɗin harda kular suka fasa marfin kawai suka barmin”
sai a lokacin momi ta lura da murfin kular dake hannunta,
Siraj yace “karya kike kedai kika fasa da kanki ai nasan halinki”
kamin mairo tayi magana momi ta tari numfashinsa “tho ai babu komai sai a siya mata wata aini tunda tana karatu komai zan iya yimata”
gwalu tayiwa Suraj tana daddalomai ido “yaee an bashi red card”
shikan inbanda dariya babu abunda yake ganin abun nata ba mai karewa bane yasa momi ta riko tace “kyaleshi haka jeki wanka kiyi sallah sai muci abinci”
saida ta kara masa gwalon sannan ta nufi stairs.

da dare mairo na zaune parlour ita da Qasin suna game Siraj ya shigo,
aiko daman neman tsokana yake haka yasha mur yace “ke tashi muje kiyi karatu”
juyowa tayi ta kalleshi tayi mai fari da ido “kai dan Allah ja can yaro ba sauran karatu mun kare jarabawa hune kawai zayi mana yaro”
dariyace ta suɓucewa Siraj Qasin ya kalleta yace “Siraj ɗin ne yaro?”
“eh yaro ne man baka ga ka girme shiba”
“tho ai shekara kaɗan na bashi”
“eh duk da haka dai yaro ne”
maganar take tana wani war da ido tana jujjuya baki,
fashewa Qasin yayi da dariya Siraj ma da dariyar ya nufi dining.

game ɗin Qasin ya kashe ya rika hannunta “tashi muje muci abinci”
ɓata fuska tayi ta taɓe baki “yaya bamu gama game ɗin ba fa kuma momi bata zoba barre muci abincin”
hancinta ya lakkata “momi yau ba nan zata ci abinci ba kisan abbah yana nan g(me kuma gobe zamuyi tunda ba makaranta tashi muje”
tashi tayi yana rike da hannunta suka nufo dining saida yaja mata kujera ta zauna sannan shima ya zauna ya soma zuba mata abincin”
Siraj dai kallonsu kawai yakeyana cin abincinsa yana murmushi saida suka fara cin abincin sannan yace “yaya kasan momi tace ka daina ci mata abinci fa”
harara Qasin ya watsa mishi “tho momi ka gani nan ne”
rufe baki mairo tayi tana dariya “lahh yaya Allah sai na faɗa mata”
dariya Siraj yayi Qasin ya haɗe fuska
“kaga bana son iskancin nan fa Siraj ina ruwanka”
Siraj yace “gaskiya ce ai ace mutum da matarsa amman kullum sai yazo gurin momi yaci abinci”
banza Qasin yayi mishi ya cigaba da cin abincinshi,
Mairo kan dariya kawai take tana kallon Qasin.

can ta dafe ciki ta koma kuka kamar ba ita ba “na bani cikina ciyo yake”
duk suka kalleta Qasin yace “ciki kodan kinyi dariya ne?”
“a a tun safe yake min ciyo kuma sosai”
Siraj yace “kinsha magani?”
“a-“
waje tayo da ido tunowa da bata son magani da sauri tace “eh na sha momi ta bani magani mai shegen ɗaci”
wani ya mutse fuska tayi kamar da gaske
Qasin yace “tho ci abincin sai kije ki kwanta”
kuka tasa masa
“ni bazan iya ciba Allah ciyo yake sosai”
“owk jeki ki kwanta”
tashi tayi da sauri tana yiwa Siraj ɗageɗage,
har ta kama hanya sai kuma ta dawo ta nunashi da yatsa ta maida baki gefe tace “kai kuma yaro kayi sauri ka cinyeshi duka”
juyawa tayi ta cigaba da tafiyarta tana wani rausaya kamar wata tsohuwar karuwa,
Siraj kai ya girgiza yana dariya,
murmushi Qasin yayi ya bita da kallon har shige.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*24*

*_washe gari…_*
9 da yan mintuna mairo ta nufo downstairs sanye da kayan bachi fuskarta babu annuri,
duk ɗagowa sukayi suna kallonta harta zauna momi nakai wainar kwai tace “maryam lafiyarki kuwa?”
kara ɓata fuska tayi “momi cikina ne yake ciyo sosai tun jiya”
Siraj ne ya gwaleta “dan Allah can ji kanta”
“kai yaro wlh ka kyaleni”
dariya yayi “Allah momi in bata daina cemun yaro ba dukan gwarai zanyi mata”
momi na mika mata cup ɗin tea tace “karma ka soma ka daketa bakai ka fara wasa da itaba”
gwalo mairo tayi mishi “ance yaro yaro yaro yaro yaro yaroooooo”
Usman yace “ba cikinki ke ciyo ba kenan?”
nan ta rike cikin ta langwashe “momi ni ko tea nan bazan iya shaba ciyo yake sosai”
momi tace “wani abun kika cine?”
“a a ni banci komai ba”
Qasin na kurɓa tea yace “bakince kinsha magani ba ko karya kike?”
soshe2 ta shigayi yana son kawarda maganar “uhm momi kinsan kince yaya bazai kara ci miki abinci ba ko jiya yaci kuma yau yana ci”
kallonshi momi tayi “tho yana iya da abunda yafi k’arfin wuta inji kishiyar k’onanna”
dariya yayi yace “Allah momi abinci inba naki ba bana jindaɗinshi”
momi zatayi magana Siraj yace “nidai duk ba wannan ba dan Allah momi karki barta taje ki hanata”

Story continues below

mairo da Qasin suka kalli momi mairo ce ta riga tambaya “minene momi wa za a hana?”
da fork Siraj ya nuna ta “ke mana ke za a hana”
“ina zataje?”
Qasin ya tambaya,
momi badan taso ba ta soma masa bayani “jiya ne bayan fitarka Yarima yazo wai yana son maryam ta rakashi wani taro da za ayi na buɗe wata kungiya ta taimakon yara”
ɓata fuska Qasin yayi ya taɓe baki “tho saboda mie sai ita zata rakashi miye haɗin ta ta kungiyar?”
Siraj ne ya karɓa mishi “wai shine zai kaddamar da abun kuma yana son yaje da yarinya da zatayi jawabi a maimakonsa jifa”
momi tace “tsarin ne yazo da haka dan haka aka tsara komai har ma abunda maryam zata faɗa a rubuce yake”
tsaki Qasin yaja “aikin banza maryam ce kawai yarinya ai yana da kanne mata da maza yaje dasu mana babu inda zata je”
momi tace “yafa riga ya bada abunda zata karanta har kayan da zata saka ya kawo”
tashi Qasin yayi tsaya yana faɗin “tho a mayar masa da kayansa momi dan Allah karki barta taje”
momi bata ce mishi komai ba sai maryam take kallo data ɓata fuska kamar ta fasa kuka,

tana ganin ya fice tace “momi nidai zanje inason nayi jawabi”
Usman da Nura dai kallonta kawai suke basu ce komai ba
kai momi ta ɗaga mata “ai zaki je inma kike kare zan baki takarɗar kiyita bita kamin assabar kin iya”
daɗi sosai mairo taji za a rika Microphone ayi jawabi.
baki sake Siraj yace “momi kina nufin barinta zakiyi taje duk magangganun nan da akayi”
shima banza momi tayi dashi mairo nata watsa masa harara harya kare cin abincin ya fice.

”’***”’
koda 12 tayi mairo na zaune ɗaki tana karanta takardar da taji motsi ta ɓoye dan kar Siraj ko Qasin ya shigo ya gani,
haik’an ta ɗauki abun ta rika tarewa a ɗaki duk abunda da bata gane ba ta tambayi momi,
islamiya ce kawai take tasa ta aje idan ta dawo ta cigaba,

a waya Yarima yake kiran momi tabawa mairo yana jin yadda take karantawa dan yasan zuwa gidan ba zai masa daɗiba kuma daman momi tayi dashi akan komai zasuyi ayi a waya karya zo gidan inba weekend ba ranar da zasu tafi,

kullum Qasin da Siraj cikin nanatawa momi suke akan karta barta taje. a fili momi nuna musu take bazata barta ba dan karsu dameta,
mairo har zumuɗi take taga assabar ɗin tayi duk wani ciyo da take ji daina faɗawa momi tayi dan karta hana ta zuwa,
cikin kwana biu mairo ta haddace abunda yake fefar kasancewar ba wani jawabi ne mai yawa ba,

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*25*

*_Saturday morning…_*
_8:24am_ Qasin ya shigo part ɗin momi cikin kananan kaya,
parlour ya tararda su suna karyawa.
momi na ganinshi gabanta ya faɗi a haka ta ɗaure ta amsa gaisuwar da yayi mata “lafiya kalau ya naganka cikin shiri haka?”
yan duba agogon hannunsa yace “wlh meeting ne wai zamuyi da wasu kuma basu faɗa min ba sai jiya da maraice gashi anjima zasu wuce balle nayi cancle ɗinshi”
wani daɗine ya jiyarci zuciyar mairo da momi mairo kasa jurewa tayi saida tayi dariya,
cup ɗin tea momi ta aje mishi “xauna ka karya mana”
ɗaukar tea yayi a tsaye yana sha “bani da time ɗin tsayawa ina Siraj ne?”
“yaje birnin kebbi”
fuskar mamaki yayi birnin kabbi gurin mie?”
“nima ban saniba baba hajara ce ta aiko tana nemansa tun da 7 ya tafi”
iskar bakinsa ya busar “owk maryam tashi ki chanja kaya ki rakani”
da sauri momi ta kalleshi “gurin meeting ɗin zata rakaka?”
“eh momi ban yarda da barinta cikin gidan nan ba”
faɗa momi ta taso masa dashi “tho bazata ba in baka yarda da magana naba sai kayi abunda zakayi nifa na haifeka Qasin ba ni ka haifa ba”
kasa yayi da kansa yana sauke ajiyar zuciya,
duk sai yaji ba daɗi ganin yadda ranta ya bace haka ya juya jiki ba kwari ya fice.

*_9:41am…_*
motar Yarima tayi parking,
ya kusan minti uku ciki motar sannan ya fito ya nufi parlour.
da sallama ya shigo mairo ta amsa masa tana murmushi,

Story continues below

tsaye yayi yana kare mata kallo ganin yadda tayi masa mugun kyau doguwar rigace jikinta golden colour sai ɗan karamin bakin hijab da momi ta saka mata da da jan janbaki sosai tayi kyau,
a hankali ya karaso kusa da ita ya risina ya kai hannu ya taɓa gefen fuskarta yana haɗiye yawu,
murmushi ta sakar masa “ina kwana”
bai amsa mata ba
ya mayar mata da murmushin yana mata wani kallo,

jin an taɓa kofa ya sashi tashi ta sauri ya matsa baya yana kallon momi data nufo downstairs.
“Yarima ka iso?”
“eh momi naga har kin shiryata”
“eh kasan kace mun 9:30 zaka zo”
agogon hannunsa ya kalla “bari muje momi kar muyi african time”
“owk tho Allah ya kiyaye”
hannunta ya rika suka fice tana yiwa momi byebye.

murmushi momi ta bita dashi har ta fice ko kaɗan momi bata son tafiyarta dan dai babu yadda zatayine tunda tana ganin inta hana mairo zuwa bata kyautawa Yarima ba,

”’*************”’
Qasin ne tsaye tsakiyar ɗaki yana kai da kawo kana ganin yanayin fuskarsa kasan ransa a bache yake.

momi ma zaune take saman kujera dafe da kai lokaci lokaci takan kai dubanta gurin agogon dake parlour.
wannan karon *9:21pm* ya nuna hankalinta ne ya kara tashi,
da sauri ta janyo wayar dake hannunta tana kiran number Yarima duk sakamoko ɗaya ake bata kamar ɗazun wayar a kashe,
juyowa Qasin yayi ya kalleta “kinga ni ko momi saida nace miki karki barta taje kika ki yarda da magana na gashi yanxu abunda ake yiwa gudu”
numfashinsa momi ta tara “babu abunda zai samesu insha Allah kawai dai bana son sukai 10 ne”
magana take kamar abun bai dameta ba saɓanin cikin ranta dake cike da tashin hankali,
kai Qasin ya girgiza “hmm ace tun safe mutun ya fita har yanzu babu labarinsa”

da karfi Mairo ta turo kofar parlour ta shigo idonta zurun zurun.
duk juyowa sukayi suna kallonta babu wadda ya iya taɓuka komai harta karaso kusa dasu,
lumshe ido Qasin yayi yana sauke ajiyar zuciya.

da fata momi tayi tana kallon bayanta “ina Yarima?”
“yana can basan inda yake ba sawa yayi a kawoni”
magana take muryarta na rawa kana gani kasan tsoro take ji sai waiga bayanta take,

juyowa Qasin yayi da ita “maryam mi yasa kuka daɗe?”
shiru tayi tana haɗiyar yawu “ba ba babu komai”
tsawa Qasin ya katsa mata yana girgiza ta “faɗamin min gaskiya tun safe ku fita sai yanzu ki dawo kice mun babu komai faɗa min miya faru?”
matsawa tayi ta rike momi tana kuka “yace duk na faɗa sai ya kasheni”
sanyi jikin Qasin yayi momi kuma tsigar jikinta ta tashi,
a hankali momi ta rika zata zaunarda ita kin zama mairo tayi ta ɗan ɗaga rigarta cike da tsoro tace “momi kayana duk ya ɓata dubi jini na min zuba”
da sauri Qasin da Momi suka kalli jinin dake bin k’afarta.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*26*

waje Qasin yayi da ido cikin rawar murya yace “maryam..-“
da sauri ta kalleshi itama idon nata a tsaye.
zai rikata momi tayi saurin rika hannunta “muje ciki”
janta momi tayi suka nufi stairs jikinta babu karfin,
Qasin ma haka yake kallonsu jiki ba kwari har suka shige sannan ya faɗin zaune yana kallon gurin da jinin ya zuba,

sai kusan 10 da wani abu ya tashi ya nufi part ɗinshi tafiya yake kafafunsa na masa nauyi zuciyarsa sai bugawa take da karfi,
baiyi sallama ba ya shigo parlour.
har ya zauna bai lura da mansura dake zaune saman kujera ba
dafe kanshi yayi ya kulle idonsa gam yana cizon baki,
jin an dafashi yasashi ɗago kai ya kalleta.
tashi hankalinta yayi yanayin yadda taga idonsa yayi ja tasan ba lafiya ba,
tana shafa gefen fuskarsa tace “Qasin lafiya na ganka haka?”
janye mata hannun yayi “babu komai jeki kwanta”
“kamar ya naje na kwanta bayan kai hankalinka ba-“
cikin tsawa ya tari numfashinta “nace miki kije ki kwanta babu komai”
tashi tayi tana masa wani kallo kamin ta juya ta nufi ɗaki,

Story continues below

dafe kai yayi ya sake rumtse idon abunda ya faru ɗazu ne ya rika dawo masa,
jin yayi bashi da natsuwa yaji wani irin abu ya tsaya masa a zuciya da sauri ya tashi ya nufi firij yana buɗewa ya ɗauki gorar ruwa ya kafa a baki,
kaɗan yasha ya ɗire ta saman firij ɗin yana maida numfashin,
ya daɗe tsaye a gurin sannan ya juya ya nufi kofa.

part ɗin momi ya sake nufowa yadda yabar parlour haka ya tarardashi kai tsaye upstairs ya nufa,

tun kamin ya karasa hawa yayi tsaye jin shinshikar kukan momi wani abu yaji ya tsikareshi tun daga ɗan yatsan kafarsa har tsakiyar kansa karfen stairs ɗin ya rike da karfi ya matse hannunsa ciki yana dantsar hakora,

jin bazai iya jure tsayinba yasashi zaunawa a gurin,
lumashe ido yayi saida yaji abunda ke zuciyarsa ya ɗan kwanta sannan ya tashi ya nufi ɗakin momi,

a hankali yakai hannu ya tura kofar ɗakin.
tsaye yayi yana kallon mairo dake saman gado kwance tana bachi kamar gawa.
ɓachin ransa dake ransa ya karu saurin ɗauke idonsa yayi ya mayar gurin momi dake zaune kusa da ita hana sharar kwallah,
cikin dakisasshiyar murya yace “momi kuka kikeyi?”
ba tare data kalleshi ba ta girgiza masa kai alamar a’a,
kai ya ɗaga “itama naji kukanta ɗazu”
sai a lokacin momi tayi gyaran murya tace “eh ina tambayar tane ko yayi mata wanin abun ne shine nace zan daketa inbata faɗa ba shine take yiwa kuka”

saida ya ɗanyi jimmm sannan yace “mi tace momi?”
ita shirun ta ɗanyi kamin ta bashi amsa “ina jin menstruation ne Qasin dan banga wata alama data nuna yayi mata wani abun ba kuma ita bata faɗa ba”
sai a lokacin ta kalleshi

murmushi yayi “yes momi menstruation ne saida safe”
bai tsaya jiran mi zata ce ba yayi baya baya yaja mata kofa daman can bai karasa shiga cikin ɗakin ba,

cikin wani yanayi ya nufo downstairs yana tafe hawaye na masa zuba har sauko.
saman kujera ya zauna saida yaji hawayen sun tsaya masa sannan ya tashi a kasale ya nufi part ɗinshi,

*_washe gari…_*
Mairo na zaune saman gado tana wasa da kafafunta Qasin ya turo kofa ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi,
tana ɗago kai suka haɗa ido murmushin da ta gani a fuskarsa ya hanata jin tsoronsa tun kamin ya karaso tace “yaya ina kwana?”
saida ya risina kisa da ita sannan ya amsa mata murya kasakasa “lafiya kalau kin tashi lafiya?”
“lafiya kalau”
“ina momi?”
“tana kicin”
hannayenta ya riko “faɗa min maryam mi Yarima yayi miki?”
“ni bai min komai ba yaya”
shiru yayi ya soke kai

can ya ɗago kai ya kalleta “jinin dake miki zuba har yanzu yanayi ko ya daina?”
“a’a ya daina koda na tashi da safe bai min zuba ba”
da sauri ya lumshe ido bugun zuciyarsa ya karu.

“ba abunda kake zargi bane Qasin jikina bai bani haka ba kuma na bincike ta banga haka ba”
momi ce take maganar lokacin da ta karaso kusa dashi.
sakin hannunayen nata yayi suka tashi tsaye tare shida Mairo,

wani irin faɗuwa gabansa yayi lokacin da ya juyo suka haɗa ido da mansura dake tsaye bakin kofa rike da kofar ɗakin.
cikin rashin ta karasa shigowa tana faɗin “miya faru da maryam?”
da sauri momi ta tari numfashinta “babu abunda ya faru da ita gimuwa ne tayi da kuma ciyon kai”
karasowa tayi kusa da mairo “gimuwa a ina?”
nan mairo ta soma mata bayana “a a jiya ne da-“
tassssss Qasin ya wanke mata fuska da mari saida ta faɗi tun bata kai ko ina a zancen ba,
da sauri mansura ta kalleshi “Qasin mi-“
marin itama ya watsa mata saida tayi baya ta dafe kunci.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

_dedicated this page to maama Hajiya Zainab Kano kakar yan biu 🙈 LOL_

Story continues below

*27*

da sauri momi ta riko Qasin da fuskarsa ke ɗauke da bachin rai tace “mi yake damunka Qasin mi suka maka?”
kallon kawai ya rikayi ba tare daya amsa mata ba,
sun minti 10 haka ɗakin tsit sai shehsekar kukan Mairo ke tashi.
mansura ce tayi karfin halin sake yin magana “momi mi yake damunsa ne tun jiya na kasa gane kansa?”
nan momi ta saki Qasin ta matsa kisa da mansura “abunda ya kawo ki kenan? daman nasan baki taɓa leko part ɗina ba sai a wata bukatar kanki ta taso”
kasa tayi da kanta har alokacin tana dafe da kuncinta hawaye na mata zuba,
“indai har abunda ya kawo ki kenan tho ki juya ki barmin ɗakinki ai mijinki ne kinfini sanin hanyoyin da zakibi ki fahimcin abunda yake damunsa”
kamar *HAWAINIYA* ta soma tafiya kanta a kasa har ta fice,

juyawa momi tayi ta nufi mairo ta tashe’ta tana share mata hawaye cikin sanyayyeyar murya momi ta soma magana da Qasin ba tare data kalleshi ba “bana son kowa yasan da maganar nan Qasin koda Siraj ne”
nan ma baice komai ba ya kaɗa kai ya fice,

mairo sai taga ya fice sannan ta kalli momi cikin muryar kuka tace “momi minayi masa?”
“baki masa komai ba maryam”
“amman momi ya mareni haka da zafi”
murmushi momi tayi “baya son idan manya na magana yara su saka baki”
shiru mairo tayi tana shafa gurin,
momi ta kwanto ta ita jikinta “maryam”
cikiciki ta amsa “na’am”
“duk wadda ya tambayeki mi akayi miki kice komai karki kuskura kice Yarima yace in kika faɗa sai ya kasheki ko kice ranar jini yayi miki zuba kinji?”
“tho momi”
“koda fa can ne kauye karki faɗawa kowa kinji?”
“tho bazan faɗa ba”
“yauwa Maryam ɗina yar albarka tashi muje muyi breakfast”
“tho”
da sauri ta tashi momi ta rika hannunta suka fice,

parlour suka tararda Qasin zaune saman tree-setter rike da cup din tea.
da kallo ya bisu yana kurɓa tea a hankali har suka zauna sannan ya tashi ya nufi kofa,
“yaya yau ba dakai za ah karya ba?”
Siraj ne yake masa maganar yana kokarin saka T-shirt ɗin dake hannunsa ya nufi dining.
kai kawai ya ɗaga masa ya fice,

haɗe gira yayi ya kalli momi “lafiyarsa kuwa?”
momi tace “lafiyarsa kalau saidai ko in wani gurin aka taɓoshi”
kafaɗunsa ya ɗaga alamar bai damu ba yaja kujera ya zauna yana tsokanar mairo,
“miya kunbura miki fuska haka yar kauye?”
turo baki tayi ta kalli momi “momi kingan shi ko?”
kai momi ta girgiza “oh Siraj dan Allah ka rabu da ita bana son fitinar nan dan Allah”
murmushi yayi ya noce kansa ya soma cin abincin.
lokaci lokacin ya kan ɗago dasun haɗa iɗo da mairo yayi mata gwalo ita kuma ta murguɗa masa baki,
daga ita har momi ba suyi wani cin abincin kirkiba suka tashi daman ita Siraj ya tsangwameta

*_2:55pm…_*
Qasin ya shigo part ɗin momi saida ya karewa kujerun parlour kallo sannan ya kalli momi dake tsaye dining yace “Yarima yazo?”
kallon mamaki momi tayi masa “Yarima? mi zaya maka?”
jijiyar kansa ce ta tashi jin yayi kamar ya ɓalɓalowa momi masifa amman ba dama dan mahaifiya ce. dole tasa ya tausasa harshensa “magana nake son miyi dashi momi na ɗauka ta shigo ne”
“tho bai zoba kuma in har akan maryam ne karka kuskura masa magana kaji na faɗa maka”
kallon rashin fahimta yayi mata “momi karfa ayi masa magana kikace”
kallonshi tayi ido cikin ido “eh nima mahaifiyarta ce ina tunanin ko ni kaɗai nayi magana dashi ya isa”
wani murmushin ban haushi Qasin yayi ya juya ya fice,

Gardem ya nufa yana tafe yana tunanin hali irin na momi,
wakewaken Mairo ne suka ɗago da hankalinsa yakai gareta
tana zaune karkarshin bushiyar mangoro rike da gwallon gwaiba tana ci,

sai a lokacin ya soma jin tausayinta nn d nn idansa suka cika da kwallah wata irin tsanar Yarima yaji ta taso masa a ɗayan ɓangaren kuma yana son ganin laifin momi,
ya daɗe yana kallonta zuciyarsa sai wani tunani take kawo masa saida ya fisgi kansa sannan ya samu karasa kusa da ita,

da sauri ta tashi tsaye ta jefarda gwaibar tana masa kallon tsoro.
risinowa yayi ya ɗan sakar mata murmushi “maryam…”
da sauri ta amsa “na’am yaya”
hannu yakai ya shafa gefen fuskarta kamin ya jata jikinshi ya rumgume,
_’ya lalata miki rayuwa Maryam ya cutar dani yayi miki taɓon ds zakiyi bakinciki nan gaba amman zan nuna masa kuskurensa sai yayi nadamar abunda ya aikata’_
a zuciyarsa yake wannan maganar yana cige da lips.

Story continues below

kalamanta ne suka dawo dashi daga tunanin da yake,
“wlh yaya kaci arziki yanzu na daina fitsara na shiryu da baka isa ka mareni na kyale kaba”
hannu yasa ya ciro handkerchief ya share hawaye da suka zubo masa ya ɗago yana murmushi yace “da gaske?”
“Allah wlh kai hmm”
gefen fuskarta ya lakata “ashe ke matsifaffiya’ce ko?”
dariya tayi ta rufe ido “a’a ni mai lafiya ce”
dariyar yayi shima “mai lafiya ai sunan wani ne”
wannan karon rumfumeshi tayi tana dariyar
“yaya zaka bimu kauye?”
“yaushe zaku je?”
“da anyi hutu ranar juma ah za ayi mana hutu”
saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yace “zanje Allah ya kaimu”
rawa ta rika masa “yauwa yaya na gode ina sonka sosai”
murmushi kawai ya shafa bayanta,
can ta ɗago “bari naje nayi shirin islamiya kar momi tayi faɗa”
kai ya ɗaga mata ta masa byebye ta nufi cikin gida da sauri.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*28*

Mairo na zaune parlour gaban tv tana buga game Siraj ya shigo,
da far ah ya karaso kusa da ita yana ya zauna,
kallonshi tayi taja tsaki ta matsa nesa dashi tana harararsa.
hannu ya kai ya kashe game ɗin ya ja mata hanci,
tashi tayi tsaye ta ɗauki fillon kujera ta rika buga mishi iyakar karfinta.

rikota yayi ya fisge fillon yayi ya jefar ya shiga kokuwar zaunar da ita,
daker ta zauna koshi dan ya rike mata hannayene haka ta rika kokuwar kuncewa ganin bazata iya bane yasa dole ta hakura ta zauna kurum,

bakinsa ya ɗora daidai kunneta yace
“plz maryam magana nake son muyi dake ta fahimta ba faɗa”
banza tayi masa ta kara turo baki ta ɗauke fuska.
murmushi yayi “haba my sis plz”
“tho ka faɗa mana ai kunne ne yake ji kuma ka sakeni”
sakinta yayi ta zauna daidai tana fuskartarsa “maryam kinga yau aka muku hutu kuma momi tace kauye zata kaiki dan Allah in kukaje karki yarda a baro ki kice ke bazaki zauna ba”
wani kallo tayi masa ta ɗaga baki sama “saboda mie?”
“kinga can ba daɗi kuma ba abinci mai kyau irin wannan ba gurin bachi mai kyau ba daɗi kinsan ai kauye ba daɗine dashi ba”
“nikan inaso a haks zan zauna har hutun mu ya kare inason naga gwaggo da tsoho da kawayena da kowa da kowa”
“oh maryam bazaki gane ba yanxu fa in kikaje can bazaki sake ganinmu ba sai anyi hutu”
tashi tayi tsaye “eh naji nidai ka kyaleni”
kallo ya bita dashi har ta haye stairs tana masa gunguni.

*_6:30pm…_*
momi na zaune ita da Usman,Nura da Mairo Qasin ya shigo da sallama,
da gudu mairo ta rumgumeshi tana murna momi bata kulashi ba Nura da Usman ne suka rika kallonsa har ya zauna,
gefensa Mairo ta zauna tana rike da hannunsa “yaya mi yasa ka daina zuwa nan gurin momi?”
shiru yayi yana kallon fuskar momi data ki ta kalleshi,
nan mairo ta sake jefa masa wata tambayar “kuma yaya ka daina cin abinci nn?”
sai a lokacin ya kalleta yana murmushi yace “aiki ne ya mun yawa bani da time ɗin kaina shiyasa kika daina ganina”
kai ta girgirza tana dariya,

juyawa yayi ya kalli momi “momi an wuni lafiya?”
amsa mishi tayi still bata kalleshi ba “lafiya kalau Qasin ya aiki?”
“Alhamdulillah”

bai sake cewa komai ba in banda wasa da yake da yatsun mairo momi ma ko kallonsa batayi ba barre ta sake ce masa wani abu,
suna haka aka kira sallar magariba haka ya sashi tashi yana kallon momi “bari naje nayi sallah an kira magariba”
sai a lokacin ta kalleshi “ka shirya ranar assabar zamuje kauye”
kai ya ɗaga “owk momi har da mansura”
“a a daga ni sai kai sai maryam zamuje”
“owk Allah ya kaimu”
“amin”
kallon su Usman yayi “ku ba zakuyi sallar bane?”
tashi sukayi ko wane na sosa kai suka nufi kofa, nn ya juyo gurin mairo “kema je kiyi sallah”
“tho”
da sauri ta tashi ta nufi stairs saida ta shige sannan ya maso kusa da momi ya risina hakan yasa momi ta kalleahi cikin sanyayyiyar murya yace “momi fushi kike dani ko?”
“mi zai sa nayi fushi dakai Qasin mi kayi min?”
shiru yayi yana kallonta kamar mai tunanon abunda zaice,
tashi momi tayi “nikan bari na shiga ciki nayi sallah”
bata tsaya jiran mi zai ceba ta nufi stairs saida yaga shigewarta sannan ya tashi ya fice.

Story continues below

*_washe gari…_*
tun 7am Qasin ya shigo part ɗin momi ya tare a parlour murna gurin mairo ba a magana haka ya sake jikinshi kamar ba shiba momi dai sai kallonshi take.
tare sukayi breakfast sai kusan 10am ya koma part ɗinsa bai daɗe ba ya fito cikin shiri ya yabar gidan.

da dare ma nan ya ci abinci ya rika jan momi da fira tun tana shareshi har ta gaji ta sake jiki, saida dare ya raba sannan yayi mata sallama ya nufi part ɗinshi,

haka Qasin ya rikayi duk wani bachin rai dake ransa dannesa yayi ya barshi a ranshi saidai duk lokacin daya kalli mairo sai yaji ba daɗi,

da sallama ya shigo kaya nuki nuki a hannunsa banci wa yanda Siraj da Usman suka riko,
gaban momi suka ɗire kayan nn da nn mairo ta shiga budewa “momi kayan waye?”
ɗan kwalin dake kanta Siraj ya cire yaja mata gashi saida tayi uhu,
da sauri Qasin ya kalleshi “kai mi yasa kake son mata keta haka ne?”
mairo ta watsa masa harara “mugune shi mai katon kai ai gobe ba zaka gannin ba”
murmushi yayi ya kalli momi yace “dan Allah momi karki baro ta”
shafa kanta momi tayi “a a can zan barota sai taga gari sannan a dawo da ita”
gwalo tayi masa tana masa rawar kai,
dariya Qasin yayi yace “gobe mirna gurin Gwaggo ba a magana”
momi tace “lallaikan an kwana biu ba a ga mairo ba”
rufe baki Siraj yayi “momi mairo kike ce fa”
“eh ai haka suke ce mata can kauye”
aiko nan ya hau kiran suna nata yana fashewa da dariya tun bata kulaba har ta soma tsarguwa ta tsuke baki “tho sai miye dan kace Mairo ai sunane haka ake kirana”
gwalo yayi mata “ai ba mairo yake ba mero yar kauye”
fashewa duk sukayi da dariya haka yasa ta haɗe fuska kamar ta fasa ta turo baki,
nn Qasin ya sake fashewa da wata dariyar yace “Siraj shi yasa ta raina ka ka cika mata shinshigi da yawa”
“ba shinshigi bane Allah mero ne sunan”
da fata momi tayi “ke kyalesu tashi kije ki kwanta kinsan gobe sammako zamuyi”
tasgi tayi kamar ta fasa kuka ta nufi daki.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*29*

*_washe gari…_*
koda 8am tayi mairo tayi shirin tafiya kasa yin breakfast tayi saboda murna ruwan tea kawai tasha ta tare saman kujera tana kallon su momi dake karyawa,

can taja tsaki ta kalli agogon dake hannunta “mts momi duk kun ɓata min lokaci har 9tayi”
juyowa Siraj yayi ya kalleta “eyye yar kauye an waye yanzu kin iya agogo ko mero?”
kawarda fuska tayi ta masa banza momi ta tashi tana faɗin “bari naje na shirya muje na kaiki gurin Gwaggo ki huta da matsalar Siraj”
kallonta Siraj yayi “momi dan Allah karki baro mana Maryam wlh miss ɗinta zamuyi”
kallonta kawai Qasin yayi ya kara kurɓa tea dake gabansa ya tashi ya fice,

mairo ta kalli momi “nidai kije ki shirya momi kar ki daɗe”
Usman yayi dariya yace “yau Maryam har gudun mu akayi ne dan zakije kauye”
Siraj kamar mai tsira ya hau tsokanarta “kaji fa wai kauye babu ma daɗin faɗin”
taɓe baki mairo tayi ta kalli momi “momi kije dan Allah ki shirya muje”
stairs momi ta nufa tana faɗin “tho yar gidan Gwaggo”
itama tashi tayi tana rufawa momi baya tana hararar Siraj,

*✧*

sha ɗaya da yan mintuna suka kama hanya,
mairo na front-seat Qasin na driving momi kuma a gidan baya surutu kan mairo shi tasawa gaba inta ɗauko wannan ya ɗauko wannan momi dai saurarenta kawai take inta kai gana dariya ba ta tamata saɓanin Qasin da fuskarsa take haɗe hankalinsa ma a wani gurin yake,

hannu Mairo takai ta taɓoshi da sauri ya kalleta “ya maryam mi kikace ne?”
murmushi tayi masa “bance komai ba naga dai kayi shirune baka magana kuma ka ɓata fuska”
sakin fuskar yayi “ina tunanin wani business nawa ne”
“tho ka ka daina haɗe fuska”
murmushi yayi yace “na daina Auntie”
dariya tayi ta kwanta tana kallon t-t,
motocin dake wucewa ta rika lisafawa har bachi ya ɗauketa.

Story continues below

”’*************”’
tsayawar da motar tayi da karfine yasa ta farka a figice tana rabon ido,
rana ne zagaye dasu sai tsalle suke suna ambatar mairo.
da sauri ta fita motar tana uhu suka shiga rumgumar juna ita dasu suna tsalle² ta gina wasu matan aure suka rika lekenta,

tuni momi da Qasin suka kunna kai cikin gidan,
ita kan saida suka gama ɓata mata kaya da kasa sannan ta shiga cikin gidan. da gudun ta karasa ta rumgume Gwaggo dake zaune saman tabarma tare dasu momi, idon Gwaggo cike da hawaye ta soma ture mairo “ni ɗagani ai guduwa kikayi kika barni”
kara rumgume tayi “Gwaggo ni ba guduwa nayi ba ai daman nace miki zan dawo kuma ba gashi na dawo ba ni babu inda zanje”
momi tayi murmushi tace “haba aiko duk kika kori mairo baki mata adalci ba dan kullum zancenki take ita dai Gwaggo ta dai”
Qasin yace “Gwaggo yar matsifa ke kullum matsifarki karuwa take ba raguwa ba”
nn Gwggo ta dawo kansa “eh ai daman kaine ka hure mata kunne tunda kazo taki ta samu matsuwa sai ta biku”
dariya yayi “tho Gwaggo ba gata yanxu mun dawo da ita ba da nan fa da can duk ɗaya ne tunda duk abu ɗaya ne”
momi ta karɓa masa “duɓe ta ki gani na gyare miki ita ta zama yar zamani”
gaban Gwaggo mairo ta dawo tana jujjuyawa kamin ta fashe da dariya ta faɗa jikinta ta rumgumeta,

*_two hours letter…_*
“kingani ko Gwaggo mairo ta sami lafiya ai daman nasan cikin biu sai anyi ɗaya kodai a maidota dan mugun halinta ko kuma ta chanja hali”
Halilu ne ke maganar yana kai lomomin shinkafs da wake bakinsa,
taɓe bag Gwaggo tayi “ai daman ba wani mugun haline da ita ba kaine dai ka bi ka matsa mata”
halilu yayi dariya yace “Allah Gwaggo in zaki faɗi gaskiya kema kinsan mairo ta chanja jifa har take bari yaran na su taɓa ta inda ne ai basu isaba ballan tana ma ta dawo daga birni”
“gaskiya kan ya gashi yanzu har girma maryam tayi kuma tayi hankali”
maganar momi take tana kallon fuskar Gwaggo,

Gwaggo ta taɓe baki “ai dole tun Allah kaɗai yasan hawalar da kuke gwada mata ai duk abunda zai sa mairo ta zama haka ba karamin abu bane”
Halilu ya tashi yana faɗin “Gwaggo ai ba zasu dai yi mata abunda kike nufi ba”
momi tace “ai muna zuwa duk wani abu da tasan bana Gwarai bane zubarwa tayi kuma muka saka ta a makaranta”
juyowa Halilu yayi da far’ah “harda makaranta kuka saka ta momi gaske dai ta kara chanja wa tayi kyau yanzu”
dariya momi tayi “kaji Halilu shi boko har sawa yake mutun yayi kyau?”
“Allah kuwa momi kinga ai yanzu ta natsu kuma ta waye ba kamar daba daman burina kenan naga mairo a makaranta kuma cikin rayuwar jindaɗi”
harara Gwaggo ta watsa masa “kuma can da kake dukanta?”
“yau ai saboda bata jin maganane shiyasa kuma kinga dan ta dainane ake mata haka”
“hmm tho chanjawa tayi ne ai babu irin dukan da bata a hannunka ba”
dariya yayi ya aje kwanon dake hannunsa “ai ba zaki gane ba Gwaggo ni dai bari naje Qasin na jirana mu zaga gari”
momi ta kalleshi “kar kuyi nisa halilu yanzu zamu je gidan tsoho mu koma gida dan ba daɗewa zamuyi ba”
“tho momi bari na faɗa masa”
hannunsa ya ɗauraye bayan yasha ruwa ya kurkure baki ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*30*

momi ta kalli Gwaggo tace “wai halilu ya daina karantun da yaje ne”
“wane karatu?”
“ba nasan da yana zuwa can sokoto gurin karatu ba”
Gwaggo ta taɓe baki “karatu kan ai yasha kashi tunda babu kuɗin karasawa”
“ayyah haba nijan kasan yana karatu a da digiri yake ne ko mie?”
“karki tambayeni ni sanin nayi yadda abun yake ne can dai su suka sani”
dariya momi tayi tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta,

abincin dake gaban momi Gwaggo ta kalla tace “kema bazaki ci abincin ba ko Qasin ma yace ba zai ciba ku yan birni baza kuci na kauye ba”
“a a aini kinfi kowa sanin ba haka nake ba tun kamin mu baro gida saida muka ci abinci kuma ni bama abincin ne a gaba na ba”
“ko a siyo miki wani abun ne kici?”
“a’a ai inason shinkafa da wake ni wata magana nake son muyi dake Gwaggo”
kara juyowa Gwaggo tayi tana fuskarta “wace magana ce hauwa?”
“cewa nayi wai mi zai hana ayi haɗin gida”
“haɗin gida kamar ya kiɓfito kiyi magana tunda ba kunyata kike jiba kuma ba bakuwarki nake ba”
dariya momi tayi ta matso kusa da Gwaggo “ina nufi auren gida a haɗa Maryam da Qasin”
faɗaɗa fuskar Gwaggo tayi da far’ah “masha Allahu hauwa kin kawo magana daman abunda aketa magana kena a gari wai mun bayarda mairo can birni dan kwaɗayi mamakon muyi mata aure ai kara lalacewa zatayi magagganu kalakala babu daɗin ji
shekaran jiya fa tsoho yake cewa shidai cewa zaiyi a maido da mairo ya huta har nace nidai ba zanyi magana ba indai ba garin kukazo”
dariya momi ta girgiza kai “ai koda man munce fushine kikeyi”
“ai babu yadda halilu bai yiba kan yaje ya ganota na hana amman gaskiya naji daɗin maganar nan kin kawo shawara tho amman kunyi magana da Alhaji?”
“da haɗin bakinsa nake wannan maganar saida muka tattauna komai dashi kuma ya aminci shi da kanshi yace in nazo nayi miki magana ke kuma kiyiwa tsoho magana kinga duk yadda kukayi in muka dawo sai muji”
“tho insha Allah haka za’ayi abu mai sauki”
sosai momi ta jidaɗi dan batayi zaton zata samu goyon bayan Gwaggo ba,
abincin taja ta fara ci suna fira da Gwaggo, daf da zata kare Qasin ya shigo tare halilu.
zaunawa yayi kusa da ita yana kallon agogon hannunasa yace “momi tashi muje gurin tsoho so nake muje gida da wuri mansura tace nayi baki”
banza momi ta masa saida ta gama cin abincin sannan ta tashi suka nufi gidan tsoho,

”’ * * * ”’
sai bayan la’asar suka dawo gidan Gwaggo har lokacin mairo bata dawo gida ba,
sosai momi taso ta ganin mairo kamin su wuce.
amman ba dama dan halilu yayi nemanta har ya gaji baiga inda ta shiga ba, haka yasa dole momi tayiwa Gwaggo sallama. godiya Gwaggo tayi ta musu ita da halilu suna ɗsgs musu hannu har suka daina hango su,
sannan suka koma cikin gida.
kuɗi halilu ya ciro aljigunsa ya mikawa Gwaggo “ga naki kason”
da far’ah ta karɓa “yayi ɗan albarka abun ya samu”
yana dariya yace “Qasin ne ya bani ɗazun da muka fita”
zaunawa Gwaggo tayi tana faɗin “ai yaron nan yana da albarka wlh shiyasa ni na jidaɗi sosai da haɗin auren na da za’ayi shida mairo”
faɗuwa gaban halilu yayi nn da nn yanayin fuskarsa ya chanja tsigar jikinshi ta tashi a kasali ya kalli Gwaggo yace “aure za a haɗa mairo da Qasin?”
“eh abunda muka tattins da hauwa kenan kuma alhaji ne ya aikota yace a faɗawa tsoho kuma ni wlh nafi kowa farinciki wannan abun da za ayi ksgs ms mun huta da tsegumin mutane-“
da karfi halilu ya haɗeye yawu duk sai yaji maganar ta cika masa kunne, ya juya jiki ba gwari ya nufi kofa, kallo Gwaggo ts bishi dashi baki sake har ya fice,
tsaki taja ta taɓe baki “ai daman kai bason mairo kake ba kafison ka rika gwada mata azaba kamar haihuwarta”

”’***************”’
cikin dare su momi suka shiga sokoto _Rahama Restaurant_ momi tasa Qasin ya biya sukayo takeaway sannan suka iso gida,
Qasin nayin parking ya nufi part ɗinsa, momi ma a gajiye ta nufi nata part ɗin,

*_washe gari…_*
sai kusan 10 momi ta kare haɗa breakfast saboda gajiyan tafiyar jiya gashi kuma mairo maitaimaka mata bata nan,
Nura ne ya taimaka mata gurin jera abincin a dining, Usman yayi dariya “ayyoh Allah momi har nayi miss ɗin mairo”
momi na shirin zaunawa tace “ai nice nayi miss ɗinta yanzu haka ita nake tunani aikin nan duk sai naga yayi min wata kala”
Qasin yayi murmushi “ai momi ko ita sai tayi miss ɗinki balle ma can da nan ai ba ɗaya ba”
Siraj ya kalli momi “Allah momi da ba dan wani abu ba dasai nace Allah ya kara ai saida nace karki barota kika ki ɗaukar shawara ta”
“ai dole na barota wata nawa bata ga gida ba sai yanzu bamabfa shi kaɗai ya kaini ba”
Siraj yace “tho miya kaiki momi?”
tana buɗe marfin filas tace “auren maryam naje nemawa Qasin…”
kamar daga ssma sukaji maganar da sauri Qasin ya tashi tsaye yana kallonta
Usman da Nura ma duk ita suke kallo Siraj baisan lokacin daya saki tea cup ɗin dake hannunshi ba.

“aure fa kika ce momi?”
Siraj ne yake maganar yana mata wani kallon rashin fahimta,
murmushi momi tayi “aure mana miye abun tada hankali a ciki?”
Qasin da tun ɗaxu ya kasa fahimtar ta yace “kamar ya momi nifa naji kin anbata?”
ɗago kai momi tayi ta kalleshi “eh kai na nemawa inason ka auri Maryam ne”
a hankali ya zauna yana kallonta “saboda mi momi nifa ban fahimta ba?”
“bari mu gama cin abinci sai muyi magana”
juyawa tayi gurin Siraj “zauna mana Siraj”
zaunawa yayi yana kallon wainar kwan dake gabansa momi ta sake haɗa masa wani tea ta mika masa,

Qasin kasa cin komai yayi shidai moni kawai yake kallo zuciyarsa cike da tambayoyi,
Siraj ma cin abinci kawai ba dan yana jidaɗinsa ba
wayarsa nayin ringing kamar mai jira yayi sauri tashi tsaye ya ciro ta a jihu ya kara a kunne ya fice,

momi saida ta kare cin abincin tsaf sannan ta tashi ta nufi stairs ko minti uku ba tayi ba Qasin ya rufa mata baya,
gefen gado ya samu ya zauna yana kallon momi dake tsaye gaban madubi yace “momi kefa nake saurare nama kasa fahimtar abun kike nufi?”
zaman kujerar mirrow momi ta zauna “kasan me nake nufi Qasin auren maryam nake so kayi”
“saboda mie momi?”
“saboda inason ka kara aure”
“ban gane na kara aure ba mansura fa momi?”
“mansura ba mata bace Qasin so nake ka auri matar da zaka san kayi aure kasan waye kai”
kai ya girgiza “momi ni ban shirya kara aure yanzu ba haba momi ni bazan iya zama da mata sama da ɗaya ba”
leme baki momi tayi
“soboda mi baka san macce hudu Allah ya halitta maka aure ba?”
“na sani momi amman gaskiya ni ban shirya kara aure yanzu ba”
momi tace “ban fahimceka ba Qasin baza iya ba kamar ya?”
shiru yayi ya maida dubansa wani gurin fuskarsa ɗauke da damuwa,
ido momi ta tsura masa tana jiran amsar da zai bata.
ganin bashida niyar magana yasa tace “ina saurarenka faɗamin dalilinka?”
juyowa yayi ya kalleta “momi da wane ido zan kalli mansura bama zata fahimta ba momi inma gwadanine kike dan Allah ki daina”
“mansura…” momi ta faɗa “itace ta faɗo maka a rai ko baka kada wata matsala sai ita. kar dai ranta ya bache kana gudun bachin ranta amman ita bata gudun naka”
kallon mamaki yayi mata “momi muna zaine lafiya da ita fa ba muda wata matsala”

a hankaɗe momi ta kalleshi “na faɗa maka mansura ba mace bace Qasin har yaushe zaka san waye kai ne tunda mansura tazo gidan nan bata taɓa girka maka na safe da rana da dare kaci ba saidai ka siye takeaway koka zo nan kaci, wata hidima ta dangi bata taɓa tashi ta wanke kafarta taje ba bata taba shiga familinmu ba wani daga familinmu bai taɓa zuwa gurinta tayi masa kyakyawar tarba ba bata taɓa tako kafarta tazo nan part ɗina da sunan tazo gaidani ba matarka bata son haihuwa duk wannan bai taɓa damunka ba bai taɓa bata maka rai ba?”
da karfi momi take masa faɗan saida ya rumtse ido,
“mi yasa son mansura ya rufe maka ido haka Qasin? miyasa baka ganin laifinta baka son bachin ranta wanyannan abubuwan dana lissafa nasan suna damunka amman ka ɓoye saboda kar ranta ya bachi thobin kai ka jure ni bazan iya jurewa ba umarnine nake baka ba neman shawara ba kuma mun riga mu yanke shawara da babanka maryam zaka aura”
kallonta yayi da raunanniyar fuska “momi naji amman fisabilillahi a rasa wadda za a ce na aura sai maryam”
“kamar ya sai maryam
maryam ba mutum bace?”
kamar ya fasa kuka yace “momi kankanuwar yarinya ai kowa ma yaji dariya zai mun”
“kwarai za’a maka dariya kan tunda ka auro dodo ko aljana kamar maryam kake cewa kankanuwar yarinya shekara goma sha?”
tashi yayi tsaye yana kallonta yace “momi am more than 30 now taya kike ganin zan auri yarinyar da bata kai shekara ashirin ba?”
“tho abun kunya kayi ko saɓawa addini kayi Annabi (S.A.W) ya auri nana Aysha tana da shekara 6 aka kaita gidansa tana yar shekara 9 auren duk kuma abunda Annabi ya aikata Sunna ce ba akanka aka fara ba barre a kare kanka dan haka ni maryam nake son ka aura”

lumshe ido yayi ya buɗe “amman momi kona sureta hankalina ba zai taɓa kwanciya da ita ba ba zan taɓa samun natsuwa ba”
momi tace “saboda mi Qasin baka son tane?”
ya daɗe kansa a kasa kamin ya bata amsa “inason ta momi ina sonta sosai amman-“
shiru yayi ya kasa karasawa,

Story continues below

tashi momi tayi tana murmushi tace “ka zamo min ɗa Qasin bana son ka bani kunya mun riga mun kate magana da babanka kuma na sanar a kauye amincewarsu kawai muke jira mansura zaɓinka ce Qasin kasan ko kaɗan bana son aurenta amman na hakura saboda ka samu farinciki dan na fahimci kana sonta sosai tho nima inson ka farantamin ka auri maryam”
baice mata komai ba ya sauke ajiyar zuciya ya fice.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*32*

*_K’auye…_*
taliya ɗaya ɗaya Mairo take ɗauka tana kaiwa baki tana kallon Halilu Da Shima Taliyar Yake Ci Tana Dariya,
“wai lafiyarki mairo mikike dariya haka?”
Gwaggo ta tambaya cikin dariyar Mairo tace “Halilu ne yake bani dariya”
ɗagowa yayi ya kalleta “dariyar mie nake baki mairo?”
nan ta ɓata fuska “ni dan Allah ku daina cemun mairo nan a birni fa maryam ake cewa yafi daɗi”
Gwaggo tayo dariya “lallai mairo yanzu fa an waye ko ɗan zuwan nan da kikayi tho ai nan k’auye duk mai suna maryam mairo ake ce masa”
“ni dai gaskiya ku daina cemun mairo haka fa jiya su hawwa damary suka rika cemun mairo duk naji haushi”
Gwaggo tace “lallai xuwa birni yayi miki daɗi mairo an fara chanjawa ga kiba ga fari ni har maganarki naji ta fara chanjawa”
“ai dole Gwaggo kullum fa da nama muke karya wa da rana ma muci da dare ma haka ga kwai ga madara ga komai na daɗi ai dole nayi kiba”
wani guntun tsaki Halilu yaja “Gwaggo sai kace marar ido yanxu dan Allah ina kibar da mairo tayi nan daman can ai tanada ɗan jikinta saida kice tayi fari da ɗan girma koshi ba sosai ba”
leme baki Gwaggo tayi “ai kai daman ba son kake a ambaci abun alkharin taba”
murmushi yayi ya ɗauke kai
Mairo ta watsa masa harara tace “aiko Halilu duk wadda ya gannin sai yace nayi kyau nayi fari nayi kiba”
Gwaggo tace “ke fita harkarsa ai shi haka yake baya kaunar a ambaceki da alkhari saidai abunds zaisa ya rika dukanki yana shuri kamar an aiko shi”
mairo tace “aiko Gwaggo kinga ɗana je can ba duka ba komai”
ta karasa maganar tana yiwa Halilu gwalo,
hartatarar ta yayi “dan Allah gafara can ai bazaki koma ba”
“ai wlh sai na koma da hutun mu ya kare zan koma birni na barka nan dan yaro”
kwafa yayi “gani kike kamar wasa nake ko tho bari ki gani bazaki koma ba kowa yayi miki tsaye”
ganin da gaske yake yasa Gwaggo ta kallonshi tace “kamar ya bazata koma ba?”
“babu komai kawai dai bazata koma ba”
“koma warta aiko yanzu ma take dan mai dalilice za’ayi sai in abunda ake son k’ullawa bai yiyu ba kuma bama fatar haka”
ɓata fuska Halilu yayi “tho karma ku soma Gwaggo wannan haɗin da kuke son yi ba zaifa haɗu ba”
Gwaggo ta leme baki “sannu baba ba zai yiyu ba tunda kai ka haifeta wai miyasa baka son mairo ne Halilu? mita tare maka?”
“Gwaggo ba wai bana son cigaban mairo bane ko kaɗan babu wannan a zuciyata hasalima nafi kowa son cigabanta amman Gwaggo ina son ki duba wannan lamarin da kuke son haɗawa kwata² bashi da wata ma’ana”
rike baki Gwaggo tayi “bashi da ma’ana kamar ya nifa ban gane inda ka dosa ba?”
matsowa yayi kusa da ita ya sassauta murya “dan Allah Gwaggo karki yarda da abun nan dasu momi suke son hadawa wata kila ma wata cutace zasuyi ya za ace kamar mairo Qasin ya aure ta haba Gwaggo ki duba fa”
Gwaggo tace “ban fa gane maka ba Halilu ka fito fili kamun bayani yadda zan fahimta mana mi kake nufi ne?”
“Gwaggo taya za ace kamar Qasin yace yana son mairo? mairo tashin yaushe ce kuma yar kauye yaushe mairo tayi wayewar da har zaice yana sonta shifa digirine dashi kuma mai kuɗi ɗan birni.
kuma fa har yana da mata haba Gwaggo ki duba fa”
“tho in banda abunka Halilu minene aciki Qasin ɗan’uwanta ne ka kuma san inda wani abun cutane babu yadda za ayi babansa da mamarsa su amince har suzo tambayar in an basu kuma fa muma abunda muke nemane ya samu tunda kafi kowa sanin abunda uan garinnan suke cewa anki ayiwa mairo aure an kaita birin minene² kananan maganganu anyi kara anyi ice tho yanxu dan an bashi aurenta ai ba wani abun bane tunda ko ba shiba dole ne ai ne ayi mata aure”
“th tunda har haka ne ai kinga kara ma a aura mata wani ɗin ko ɗan gujewa masu cewa dan kwaɗayi aka kaita birni kinga yanxu ai sai su kara cewa wani abun in aka haɗa auren”
Gwaggo tace “babu fa abunda zai sa mu fasa haɗa auren nan duk kuma uban da bai zagemu ba bai haihuba dan an zagemu zagin lake mana zaiyine maganar banza”
da tsaki Gwaggo ta karasa maganar cike da bachin rai.
Mairo ta aje kwanon abincin ta matsa kusa dasu tana musu kallon rashin fahimta tace “mi kuke yiwa faɗa Gwaggo?”
tashi halilu yayi tsaye fuskarsa babu yabo ba fallasa yace “aure za’ayi miki mairo Qasin za’a aura miki”
da sauri ta nuna kanta tana kallon Gwaggo “ni?”
“eh ke aure za ayi miki mairo ai kinsan kin kai munzalin aure ai”
kamar ta fasa kuka tace “ni wlh Gwaggo bana son aure ni yar k’ank’anuwa dani za’ayi mun aure ga yan mata nan a birni manya dasu ba ayi musu aure ba sai ni”
hannunta Gwaggo ta riko ta zaunar da ita kusa da ita “mairo nan kauye ne ba birni ba kuma kinga mutane sai gulma suke suna faɗin anki yi miki aure”
“tho ni ina ruwana dasu nidai ma bana son hutun na fasa a mayarda ni gurin momi”
halilu yace “momi itace ta kawo wannan shawarar tace a aura miki Qasin”
shiru mairo tayi tana tunani, Gwaggo tace “karki ji komai mairo alkharine ake nema miki ba sharri ba kinga ma sai kiyi ta zamanki can birni kina yin yadda kike so, ko bakyaso?”
kai ta ɗaga “ina so Gwaggo amman nidai ina jin tsoro”
idonta cike da hawaye ta ke maganar.
nan Gwaggo ta shiga tallaɓata tana kwantar mata da hankali
ido halilu ya tsura mata kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fice.

Story continues below

”’*****”’
“dan Allah Momi ku nemawa Nura admission a A.B.U Zaria nidai ganibnake kamar can yafi”
Usaman ne ke maganar yana kallon Momi dake zaune saman tree-setter tana cin abinci,
Momi saida tasha ruwa sannan tace “ni bana ra’ayin A B U nan nafi son State University nan da aka buɗa ance ana karatu sosai kuma kaga nan garin ne hankalina yafi kwanciya iddan yayana suna kusa dani”
dariya yayi yace “momi ni da nake ɗan fodio fa?”
“eh tho ai duka ɗaya ne tun cikin sokoto take nidai bana son ayi nesa ne kawai irin gari haka ko wata kasa”
“amman momi ai kinga yaya ba nan yayi karatu ba shi har kasar ma ya bari”
kafin momi ta bashi amsa aka turo kofar parlour,
juyowa sukayi suna kallon Yarima daya shigo cikin wata bugaggiyar shadda sky blue.
ba tare da yayi sallama ba ya nufo gurinda suke zauna hannayensa sanye cikin aljihu yana tsosar baki kamar mai shan sweet.

*©Khadeeja Candy*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*33*

Saida ya kusa kawowa kusa dasu sannan yayi sallama Momi ta amsa mishi da Usman,
kujerar dake kusa da Momi ya zauna yana yiwa Usman wani kallon raini ciki² Usman ya gaisheshi, ba tare daya amsa ba ya kalli Momi yace “sannu Momi an wuni lafiya?”
da far’ah Momi ta amsa masa “lafiya kalau Yarima kana nan?”
“no shekaran jiya na dawo dan naje Uk ne tun ranar da muka fita da Maryam”
“Allah sarki tho ya gida ya da kowa²?”
shiru ya ɗanyi kamin ya bata “Lafiya kalau kowa yake”
juyarda fuskarsa yayi gurin tv, Momi ta cigaba da cin abincinta Usman ya tashi ya fice,
daf da zata cinye ya juyo ya kalleta “Momi ina Maryam?”
“Maryam ta tafi Kauye kasan anyi hutu ta tafi ganin gida”
shiru yayi ya ɗan ɓata fuska “yau kwananta 6 tun ranar asabar taje sai kuma hutu ya kare”
gefen fuskarsa ya shafa “oh Momi nako yi mata tsaba na ɗauka tana nan”
“da yake baka cikin garin shiyasa baka sani ba”
tashi yayi tsaye yana murzar zabban hannunsa “ni zan wuce kuma Hajiya tace na faɗa miki tana son ganinki”
Momi ta kalleshi “lafiya dai ko?” wani murmushi yayi “yo ni momi ya za ayi na sani sai dai kinje zakiji”
“tho shikenan sai gobe zanzo insha Allahu ka gaisheta”
kai kawai ya ɗaga mata ya fice yana kallon upstairs,

*_7:12pm…_*
“Assalamu Alaikum”
a hankali momi ta ɗago kai ta kalleshi tare da amsawa ciki² “Amin wa’alaikassalam”
suku² ya nufi kujera ya zauna kansa a kasa yace “Momi an wuni lafiya?” momi fuska babu tabo ba fallasa tace “lafiya kalau ya iyali?”
saida ya haɗeye yawu sannan ya amsa mata “lafiya kalau Momi”
gyaran murya momi tayi tace “Qasin in baka aikin komai inason ka kaini gidansu Hajiya yanzu ta aiko tana nemana ɗazu naso na ɓari har gobe kuma dai hankalina bai kwantaba nafi son yanje naji koma minene”
“wace Hajiyar Momi?”
kallon mamaki momi tayi masa “Auntie Hasana mana”
“Yarima yazo nan ne?”
“eh shine ya faɗa min ai”
tashi yayi tsaye yana faɗin “bari na kiran Siraj sai ya kaiki akwai inda nake son zuwa”
haɗe fuska momi tayi cikin tsawa tace “babu wani gurin da zakaje Qasin kawai ka fito fili yace baka son zuwa gidan iya isa ba sai kayi min nuku² ba”
lumshe ido yayi ya dafa kai “oh Momi baki fahimceni ba-“
hannun Momi ta ɗaga mishi tana tari numfashinshi “na fahimceka Qasin na san abunda kake nufi amman karka amta wannan Yarima ɗan’uwanka ne kuma inason ka sani bazan taɓa yardar maka ba ka ɗauki kiyayyah ka ɗora masa babu wani dalili nayin haka koba ɗan uwanka bane ai ba abun kwaraine bane ballantana ɗan uwa mi yasa baka da tunanine in kaje gidansu Yarima faɗuwa kayi shi da yake tako kafarsa har nan gurina fa,
ya fika sanin muhimmancin yan’uwan taka Qasin ya fika iya siyasa dan ko kiyayyah ce Yarima bai taɓa fitowa fili ya nuna maka ba ballantana ni har a zuciyata nasan Yarima baya kiyayyah dakai”
komawa yayi ya zauna ya kama hannayen Momi ya rike cikin sanyayyiyar murya ya shiga mata magana “bana kishin Yarima ko kaɗan Momi bana kishinsa kawai dai halayensa ne banaso kuma momi bazan taɓa yarda na faɗa a gadar zaren da yake kullamin ba momi kinfi kowa sannin waye Yarima kinsan duk inda ya ganni ko yaga wani dags cikin familinmu sai ya musguna masa kodai ya faɗa masa gana mara daɗi ko kuma yayi masa wani abun na bachin rai ni kuma na tsani haka momi saboda babu abunda Yarima zai nuna min
sannan momi kin hana na rama momi kince Yarima ɗan’uwana ne nasani shiyasa ma nake ɗaga masa kafa amman momi kinsan Maryam ma yar’uwata ce ko kuma duk abunda ya sameta ya sameni bazan taɓa mantawa ba”
lumshe ido momi tayi ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana _…ba zaka taɓa ganewa ba Qasin…_
can ta buɗe idon ta kalleshi tace “naji zaka iya tafiya”
“momi ki shirya na kaiki mana”
“a’a sai goben kafin ka fita”
“momi kar kimun rashin fahimta bana nuf-“
numfashinsa ta tara tare da tashi tsaye “a a Qasin na fahimtace ka karka damu gobe zaka kaini”
bata tsaya jiran mi zai ce mata ba ta nufi stairs,
Momi na shiga ta tararda wayarta saman madubi tana ringing da sauri ta karasa ta ɗauka Hajiya ta gani a screen kamin ta ɗanna picking ta kara a kunne,
_”Amin wa’alaikissalam Hajiya ya gida?”_
banji mi akace mata ba na daiji tace _”eh ina gida lafiya dai?”_
_”tho sakin iso”_
sauke wayar tayi gabanta na ɗan faɗuwa tana mamakin abunda yasa Hajiya take son ganinta haka.

Story continues below

*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*34*

*_9:35pm…_*
Hajiya ta iso gidan tun kamin ta fito mota momi ta fito ta tareta cike da far’ah, rumgume juna sukayi kowane na dariya suka shigo parlour,
momi bata barta ta zauna ba suka nufi bedroom drinks kala² momi ta jere mata da kayan ciye² bayan ta zauna suka ɗauko firar yaushe gamo,
can momi ta kalli Hajiya tace “nifa Hajiya ina mamakin zuwan nan naki haka kawai”
murmushi Hajiya tayi “ba zuwan haka kawai bane maman Nura ɗazu ai nayiwa Yusuf sako ya faɗa min kince sai gobe zaki zo shiyasa ni kuma na kasa hakura har goben nace bari nazo yau”
“nima ai na tashi zuwa ɗazun bayan magriba sai kuma nace bari dai na bari har goben lafiya dai ko?”
Hajiya ta dafa momi “lafiya kalau ɗanki ne yaga wata yarinya yace yana so”
farincikine ya bayayyana a fuskar momi duk da faɗuwar da gaban ta yake “masha Allahu ba dai Yarima ba?”
“shifa ai nima farinciki kasa ɓuyiwa yayi a gareni kuma yace nazo na tambaya masa shine fa nace tho ya kira min daya faɗa min kince sai gobe ni kuma na kasa hakuri”
momi tace “ai dole abunda aka ta jira shekara da shekaru nima ai na jidaɗi sosai”
Hajiya tace “yace yarinyar tana nan gidan ke kike rikonta yace mun sunanta maryam”
wani irin gaɗuwa gaban momi ya karayi shiru momi ta ɗanyi kamin ta haɗe yawu tace “maryam Hajiya?”
yanayn yadda tayi maganar yasa Hajiya ta kalleta “eh ita koda matsala ne?”
“a’a ba wata matsala kawai dai naga yarinyar karama ce dan bazata wuce 13 ba”
murmushi Hajiya tayi “kar wannan ya dameki ys faɗa min daman karamar yarinyace har yake cemin kiyonta yake sai ta girma tukuna tho shekaran jiya nida Mai Martaba muka sashi gaba muna masa faɗa mishine fa yake faɗa min shi babu yarinyar da yakeso inba ita ba sai kinga yadda mahaifinshi yayi murna”
momi jiki ba kwari tayi murmushi tace “ai dole kan abunda kowa yske mafarki nimaai nayi farinciki”
Hajiya tace “ina kika sani nima daɗin nake ji kamar me shine babbah yanzu kingaya kamata ace yanzu yayo aure kanensa na biu fa yanzu za ayiwa aure shi yasa ma ai abun ya damu mai martaba yasa yayi masa haka dan cewa yayi im bashi wadda yake so tho shi zai mema masa duk wadda yaga dama shine fa sai ya faɗa mana ita kaɗai kawai yake so dafa duk akayi magana sai yace shi bai samu wadda yake so ba kinga sai yanxu Allah yayi”
ajiyar zuciya Momi tace “kinsan komai yana da lokaci wata kila sai yanzu Allah ya kaddaro za ayi saida fs hajiya wani hanzari ba gudu ba”
kallonta Hajiya tayi “ina jinki minene?”
“its maryam ɗin yar kauye ce kuma ba tsyi wani karatu ba dan zuwannan ma da nayi da ita Qasin ya sata makaranta”
“kar wannan ya dameki duk ba matsala bace tho da dai har yace yana so ai duka ɗsys muke gurin Allah babu wadda yafi wani”
lumshe ido momi tayi ta buɗe ta kallii hajiya tace “shikenan zanje kauye sai nayi masa magana dan yarinyar ma tana can hutun na da akayi sai na kaita ganin gida”
“wai yar insce?”
“wlh kanwar su Qasin ce yar kanne mahaifinsu da mukaje kauye sai muka zo da ita……”
“tho yanzu dai kije kauyen ki nema masa”
cikin karfin hali momi tace “insha Allah haka za ayi”
hajiya tace “ki faɗawa mai gidanki dan ni cikin satin nan nake son aje inma ta kama har dani duk sai muje koda da Mai Martaba ne”
“a a ni ma ai ns isa na nema masa ba sai kunjeba inma dolene kuje ai sai na faɗa muku amman sai in babansu ya dawo dan yayi tafiya”
murmushin jindaɗi Hajiya tayi “ai ba matsala bace Allah ya dawo dashi lafiya ana nan anata harkokin business ɗin ko? ba hutu”
“eh ai shi koyaushe baya samum zama gida neman kuɗi kawai aka sawa gaba ba a nan ba a can zamansa gida kaɗsƙan ne kuma a koma”
“tho mai sa akan ai daman bai gaji zamaba musamman in akwai iyali”

haka momi tayi ta smsa mata firarda suke kamar marar lafiya sai kusan 11 da wani abu ta bar gidan,
daren momi kasa bachi tayi tana tunsnin yadda zata billowa lamarin, har a ranta Qasin take son maryam ta aura sai kuma yanzu dabo biu ziciyarta take mata akan maganar da hajiya tazo da ita dan Hajiya ba tada wani farinciki sai na yarima taya zata yarda Qasin ya aureta ga yarima in kuma ta yarda Yarima ya aureta rigima ce ba yar kaɗan,
kai ta dake ta zauna gefen gado _…oh ni mi yasa ban faɗawa hajiya anyiwa maryam miji ba…_ sai yanzu take jin haushin,
_…amman kuma in har taji Qasin ne ai zata iya cewa ya barwa Yarima kuma gashi har na rig na faɗa a kauye Qasin yana sonta yanzu kums si sai su ga ɓayi musu magana biu…_ busarda iskar bakinta tayi ta lumshe ido.

Story continues below

*_© Khadeeja Candy_*
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*35*

*_washe gari…_*
_10:47am_ Qasin ya shigo part ďin momi zauna ya tararda ita a dining area,
a kujerar daya saba zama ya zauna yana kallonta “momi ina kwana?”
a hankali ta kalleshi kana ganin fuskarsa kasam tana ďauke da damuwa “lafiya kalau ka tashi?”
“eh momi ke kaďai kike karyawa?”
“a a duk sun karya sun tafi makaranta ne kai ka daina karyawa nan ko?”
ďauke fuska yayi ya ďauko wani zancen “momi ya maganar tafiyar so nake na kaiki sannan na wuce dan yau zan wuni busy”
tea momi ta k’urɓa tace “ai tazo tun jiya”
kallon mamaki yayi mata “nan gidan laifiya dai ko?”
“lafiya kalau wata magana mukayi”
“tame momi?”
“sirrice”
“kamarbya momi nasan duk abunda zai sa Hajiya tazo gidanna ba karami bane dan Allah ki faɗa min minene kodai wani abun aka cene?”
momi bata ce masa komai ba ta tsura masa har tsargu ya tashi dan kanshi ya nufi kofa da tunane²
“Qasin…” murya kasa² momi ta kirashi da sairi ya juyo ya dawo “gani momi”
“ka faɗawa matar maganar aurenka?”
kasa yayi da kansa ya daɗe kamin ya bata amsa “a a momi ina tsoron abunda zai biyo baya ne kinsan ba fahimta zatayi ba”
ajiyar zuciya momi ta saike tace “yayi kyau zaka iya tafiya”
kallonta yayi kamar yace wani abu sai kuma ya juya ya fice,
dafe kai momi tayi tana nemawa kanta mafita sa kusan minti 30 haka sannan ta tashi ta nufi stairs,

”’ * * * ”’
kusan isha’i Siraj ya shigo part ďin momi ganin ba kowa parlour yasa kai tsaye ya wuce ďakinta, zaune ya tararda ita ta rafka uban tagumi tana kallon windo,
“lafiya momi?”
a sanyaye ta kalleshi da murmushin karfin hali “lafiya kalau Siraj ka shigo”
yana k’ok’arin zaunawa kusa da ita yace “momi gaskiya ba lafiya ba dan tunda safe naga damuwa a fuskarki akwai abunda yake damunki momi”
batace komai ba ta sauke ajiyar zuciya ganin haka yasa yace “barin kashi a ciki baya maganin yunwa momi babu kuma wadda ya dace ki fafawsa sirrinki irina hankalina bazai taɓa kwanciya ba momi matukar naki bai kwanta ba dan Allah ki faɗamin abunda ƴake damunki”
kallonshi tayi “kona faɗa maka Siraj ba magani zaka mun ba”
“naji nidai dan Allah ki faɗamin momi indai ba so kike nima na shiga damuwa ba”
momi ba dan taso ba ta fayyace masa komai,
Siraj ya daďe yana jinjina al’amarin kamin ya kalleta yace “yanzu momi mi kike gani shine fita?”
“nima ban saniba Siraj ita nake ta nema na kuma kasa samu”
Siraj yace “tho momi ga wata shawara…”
kallonshi momi tayi “ina jinka”
“momi mi zai hana kik’i yarda Qasin ko Yarima ya aureta”
“saboda mi?”
juyo yayi yadda zata fuskanceshi da kyau yace “kinga yanzu in kika bari Qasin ya aureta Yarima zai yita ganin laifinki shida mahaifiyarshi kuma otama zata taga kin mata cin fuska kinki bari Yarima ya aure kika bawa Qasin ya yaje ɗanki kimsan Hajiya bata tada wani Farinciki sai na Yarima tunda shi kaɗai ta haifa zata iya ɓatawala da kowa akansa kinga in kika mata haka ba zata taɓa mantawa dake ba kuma kinga zata ga baki tashi aurawa Qasin ita ba har saida Yarima ya ganeta yace yana so tunda baki riga kin faɗa mata kin nema masa ita ba kuma itama ba ganewa zata yiba sannan kinga shima yaya sai naga kamar bayason maryam sosai kuma kinga yana kaunar matarsa ko auren maryam yayi za suyita samun matsala,
in kuma kika yarda Yarima ya aureta nan ma baki tsira ba dan kinsan yaya bazai taɓa yarda ba kuma nima bazan yarda ki aura masa ita ba dan zai iya musguna mata kodam ganin daga falinmu take kuma kodan muji haushi zai iya yi mata hakan koda yana sonta dan kinsan halin Yarima ishesshen kanshine ko yanzu baki san dalilin da yasa yace sai ita kaɗai yake so ba tunda akwai yan mata da yawa a garinnna kuma suna sonsa dan babu wadda zaice yana so ta kishi kodan dukiyarsa balle ga mulki ga kyau amman ya nace shi sai maryam bakisan abunda yake shiryawa ba kuma kinga duk ya cuceta mudai ba kyalewa zamuyiba kauye kuma dake za suyi kuka dan haka ni abunda nake ganin mafita shine kawai ki bari can kauye ayi mata aurenta duk wadda suka ga damar haɗa shi da ita sai su aura mata”
gyara zama momi tayi tana nazarin kalamansa,
“ka kawo shawara Siraj amman kuma har yanzu da saura in har haka ta faru ita hajiya mi zan ce mata suma kauye dana riga nace Qasin na sonta ya zance musu har yanzu da sauran rina a kaba”
murmushi yayi “no momi kawai ki samu baba ku tattauna sai a warwar zancen auren Qasin ni da kaina zan kaiki kauye in yaso sai kice musu daman bakiyi shawara da Qasin ba kuma yanzu yaji bai amintaba kuma matarsa yar matsiface dan haka kina tsoron abunda zaije ya dawo dan haka a bar zancen aure kawai duk wadda suka dama su aura mata ita kuma hajiya in kika dawo saiki faɗa mata an riga anyiwa maryam miji alkawarine tun tana karama dan haka iyaye sunce bazasu tada ba koda tace ki kaita kauyen karki yarda kikaita dan zata iya zuwa ta rokesu ta nuna musu kuɗin koma shi Yarima da kanshi dan a yarda a aura mishi kuma kinga ko aura mishi ita akayi wahala zata sha dan kinga karamar yarinya ce sannan ba wani tsayawa zai kikayi yana bata hakkinta ba kuma zai iya ganinta tankar kaunarsa koma yarsa da ta masa abu ya daketa koma karki faɗa masu har sai an ɗaura aure, kawai momi wannan shine abunda nafa ya dace kiyi”
murmushin jindaďi momi tayi ta shafa kansa “ka kawo shawara Siraj haka zanyi Allah yayi maka Albarka”
shima murmushin yayi yace “amin momi shikenan damuwa ta wuce ko?”
kai momi ta ɗaga masa ya tashi tsaye yana faɗin “tho muje kici abinci dan nasan bakici abincin dare ba”
“jeka gani na zuwa”
“owk”
juyawa yayi ya fice cike da farinciki.

Story continues below

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*36*

A waya Momi ta kira Abbah sukayi magana dan kasa hak’uri tayi ganin ta samu mafita sosai yaso ta bari har ya dawo suje tare amman tak’i dan yadda Hajiya ta matsa mata kullum cikin kiran wayarta take,
ranar alhamis tun da safe Siraj ya fitarda motar da zasu shiga suna karyawa suka kama hanya,

*_K’auye…_*
ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke tace “wannan magana ai kamar anyi sara akan gaɓa ne”
Momi tayi mata kallon rashin fahimta “mi kike nufi wani abun ne?”
Gwaggo tace “akan maganar nan ne wai Halilu yanzu ya fito wai sonta yake bai tashi magana ba saida yaga anyi wannan maganar kiji mun rainin hankali”
Momi ta rik’e baki “yanzu Halilun ne yace haka?”
Gwaggo tace “ai kuma baki san wani abun haushi ba wlh tsoho yayi tsaye shi sai Halilu zai aurawa”
“amman tsoho yaji da Qasin ne ake son haɗa auren?”
“wlh yaji kinsan matsalar da aka samu? ya rigani zuwa yayi magana dan ni a yadda na yanke sai an ɗan kwana biu kusan zata koma sannan nsyi maganar kinga koma minene amsar in kukaje sai kuji aiko yana jin haka sai kawai yaje ya faɗawa tsoho wai shi sonta yake ni kuma da naji haka sai naje nima nace ga abunda kike ce aiko tsoho k’in yarda yayi ya dinga ganin laifi yace nice nake son juyarda abun haka ai da kunso shi zaku samu kuyiwa magana ba niba wai shi daman yana son ya haɗasu amman yana tsoho amman yanzu tunda har haka ta faru shikena ta kwana gidan sauki shi Halilu zai bawa babu yadda banyi ba amman yayi tsaye shi lallai sai Halilu balle nasan ya kwashi k’arya da gaskiya ya faɗa masa”
Momi tace “tho injin ita Maryam ɗin tana sonshi?”
“uhmmm aifa kinji inda matsalar take nan itakan tayi tsaye wlh bata sonshi yanxu haka in kikayi mata maganar kuka zatayi”
“dank’ari aiko akwai matsala tho ba’a faɗawa tsoho bata soba?”
“hmm ai sai kiyi abunda tsoho yake nema ai shine ya tsaya kai da fata wai ko bata so sai anyi shi daman ya yanke shawarar aurarda ita dan ya gaji da tsegunmi mutane”
Momi tace “amman kuma Gwaggo ai naga kamar shi Halilun bashi da wata matsala”
“aiko shine da matsa nifa na rik’ashi tun yana k’arami yanzu haka ganin da kike masa baya noma tho ɗsn k’auye in baiyi noma ba mi zaiyi sannan babu sana’ah babu aikin fari babu ma bak’i in kinmai magana yace shi karatu zai bazai iya rayuwar k’auye ba kuma karatun nan bai wani yi zurfi ba balle ace aiki kuma ance aikin nan fa ko a can birni wahala yake tho ina wani abun k’aurai tunda babu abun ci da mata”
Momi ta jinjina kai zatayi magana taji an rumgumeta da karfi,
dariya tayi jin Mairo ce tace “tun ɗazu mukazo ban ganki kiba kina can gurin yawo ko?”
dariya Mairo tayi ta k’ara rumgume Momi “a’a Momi tunda kukazo naga Siraj yaje dani yawo sai yanzu muka dawo Momi nayi mesage ɗinki”
“missed ake cewa yar boko”
Gwaggo tayi dariya tace “haka muke da ita abu kaɗan sai turanci ita yar boko”
Momi ta juyo da ita ta zauna daidai “ina kukaje yawo wato kings shigowa amman da kiks gs Siraj sai kiks shareni ko?”
“a’a Momi yawo fa mukaje da mota ko’ina sai kallonmu ake”
ta karasa maganar tana wani marmarɗen ido,
Gwaggo tace “kin samu abunda kikeso ko kiyiwa mutane kuri tho ina kika baroshi ko ya sake fitane?”
“a’a waya yake yi yanzu zai shigo”
kallon Momi tayi “Momi kinci abinci?”
da murmushi Momi tace “a’a Gwaggo ki bata bamu ba amarya”
nan da nan Mairo ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka “Momi bana so ki daina”
Momi ta dafata “ai dole kiso kedai tashi ki ɗauko mana abincin”
matsawa tayi gefen ta takure kanta ta haɗe rai, Siraj na shigowa ta rushe da kuka.
da sauri ya karaso kusa da ita “lafiya mi akayi mata”
Momi tace “wai dan nace mata amarya shine take kuka”
“kamar ya auren za’ayi mata ne?”
“eh Halilu za’a aura mata wai ita kuma bata sonshi”
murmushi yayi ya shiga tallaɓata yana bata hak’uri, daker ya samu tayi shiru ta tashi ta nufi ɗaki,
gurinsu Momi ya nufo yana faɗin “wai yanxu daga yin magana har anjuyarda abun zuwa ga Halilu?”
kamin ya zauna Momi tace “a’a daman rigimar da aketayi kenan wai shi sonta yake………………..”
nan Momi ta labarta masa komai,
Sosai Siraj yayi mamaki ya kalli Gwaggo yace “mi yasa bakison auren Gwaggo? Halilu bashida hallin k’waraine hala?”
Gwaggo tace “a’ wlh yana dashi nina rik’ashi tun yana k’arami gaskiya bashi da wani mugun hali”
Siraj yace “tho mi yasa bakison ya auri Maryam ni aganina ba wani abu bane kinga shima ai ɗan’uwane kuma duk duniya bana ganin akwai wadda ya dace ya aureta sama da shi kefa kika reneshi Gwaggo ya tashi a hannunki yanzu dan yace yana son Maryam in kikak’i baki ganin xai iya shiga damuwa? ni aganina koda ahi baiyi magana ba kema ya kamata ki haɗasu ballantana har yayi gaskiya Gwaggo in kikak’i goya masa baya baki masa adalciba kuma kin nuna masa ke bake kka hafeshi ba”
shiru Gwaggo tayi tana nazarin maganar.
“amman fa Sirajo ita Mairo bata sonshi fa”
“karma ki kawo wannan Gwaggo Maryam k’aramar yarinyace bata san soba ko a birni ksmar Maryam za’a iya aura mata wadda akaga dama balle k’auye kune kuke k’ara sa tana cewa bata sonshi kawai kibar ma wannan zancen inta girma gidansa a babu zance k’i”
dariya Gwaggo tayi “kuma fa haka ne Sirajo da maganar ka Allah dai ya zaɓa mana abunda yafi zama alkhari”
duk sukace ‘amin’
Siraj yace “amman dai Gwaggo ba zaku raba ta da karantunta ba ko?”
Gwaggo ta leme baki “karatu kan ai yasha kashi tunda in an mata aure ai tarewa zatayi kaga ko babu zancen karatu”
“amman gaskiya Gwaggo ku barta tayi makarantar ta koda anyi auren ne inta k’are sai ta cigaba da zamanta na aure”
ido Gwaggo ta nuna masa “kaga nawa ni yanzu kuma fa ako auren akayi nan zatayi ta zama dan bashida gurin ajeta sai yayi gina”
shiru Siraj yayi ya nuce kai bai sake magana ba,
can Momi tace “wai ins wadda taje ɗauko mana abinci?”
Gwaggo tace “aifa sai kiyi bafa zata ɗauko ba da nan fushine take dake”
Momi tayi dariya “in banda abinki Maryam daga faɗar gaskiya sai cibi ya zama k’ari”
Gwaggo ta tashi ta nufi ɗaki tana faɗin “bari na ɗauko miki indai wannan ce saiki shekara”
tashi Siraj yayi “ni bari naje bakin kasuwa kamin ki k’are cin abinci”
“kai ba zaka ciba?”
“kai Momi kinsan ni kan bazan iya cin abincin nan ba bari dai naje can ko zan samu abunda zanci”
kai Momi ta ɗaga mishi ya saka hannayensa aljihu ya fice.

Story continues below

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*37*

kai tsaye Siraj bakin kasuwa ya nufa daman ɗazu da suka wuce ya hango gurinda Halilu yake zaune,
Halilu na hangoshi ya ɓata fuska aransa yana _babu wani magiya da zaka mun na barma ku ita wlh boko dai nima nayi dan haka baka fini wayeba_,
Siraj ya k’arasowa kusa dashi yayi masa sallama tare da mik’a masa hannu, ciki² ya karɓa ya juyarda fuska,
murmushi Siraj yayi ya zauna saman teburin da yake zaune yana faɗin “kai kaɗai kake zaune?”
“eh ina hutawane”
Siraj ya kalleshi “Halilu ka saki jikinka dani bana nufin cutarda kai ko cilas taka yin abunda baka tashi ba ni shawara nazo na baka kuma inason kayi nazari ka ɗauki shawarar karka kalleni a matsayen ɗan’uwan Qasin inason ka kalleni a matsayin ɗan’uwanka”
juyowa Halilu yayi ya kalleshi “wace shawarace?”
dafashi Siraj yayi yace “naji ance ka fito kana son Maryam ita kuma bata sonka kuma kaga yayana ma yana sonta banci shi kuma akwai wadda yake sonta can birni sannan naji ance baka kada sana’ah ba kama da gurin ajeta tho kuma yanzu naji tana zance sai ta bimu birni tho abunda nake so da kai shine kayi sauri ka matsa a ɗaura muku aure koda baka da gurin ajeta ɗin dan in kayi sake tho rasata zakayi kaga in ka aureta koda tace sai taje birrin kana iya kyaleta taje tayi karatunta amman fa da aurenka kaga kamin ta k’are kai kuma ka samu aiki kayi gidan ajeta ni zan iya taimaka maka ka cigaba da karatunka amman karka yarda wani sati yayi ba’a ɗaura maka aure da ita ba”
ido Halilu ya tsurawa Siraj yana son tantance abunda yake faɗa,
_ta yaya zai yi masa wannan shawarar bayan shi ɗan’uwan Qasin ne miyasa yake son shi ya aureta sama da Qasin can wata zuciyar tace amman kuma fa gaskiya ya faɗa min tunda banida gurin ajeta balle abun ciyarda ita kuma nasan yanzu Mairo bazata yarda ta zauna k’auyen nan ba tunda nama ji ta fara zancen sai ta bisu kuma gashi har yace zai taimaka min na k’arasa karatuna inhar da gaske yake kuma fa inna aureta na huta koda taje can birrin wani ya ganta yana so na dai riga na aureta……_
dafashi da Siraj yayi yasashi dawowa daga duniyar tunanin daya tafi,
Siraj yace “ka yarda da shawarata Halilu shine kawai mafita a gareka”
ajiyar zuciyar Halilu ya sauke yace “maganganunka abun dubawa ne Siraj saidai na kasa ganewa taya zaka goya mun baya na auri Mairo bayan yayanka ma yana sonta?”
murmushi Siraj yayi yace “shiyasa tun farko nace karka ɗaukeni a’matsayen ɗan’uwan Siraj ka ɗaukeni a’matsayin ɗan’uwanka Halilu bana nufi cuta a gareka nayi haka ne saboda shi Qasin yana da mata sannan kuma zuwan da Maryam tayi birni ne ya ganta yace yana so saɓanin kai da tun tana k’arama kake sonta ko ɗazu na faɗawa Gwaggo babu wadda ya dace da Maryam irinka,
Halilu nifa bance dole ka ɗauki shawarta ba kawai in tayi maka shikenan in kuma batayi maka ba duk ɗaya ne”
ya karasa maganar tare da tashi tsaye. Hannu halilu ya mik’a masa “na gode sosai Siraj zanyi tunani a kai”
“nima na gode da bani lokacinka da kayi Allah ya shige mana gaba”
nan sukayi sallama Siraj ya nufo gida,

”’ * * * ”’
bakin k’ofa ya tararda Mairo zaune rik’e da ɗan karenta tana zane a k’asa,
da murmushi ya fito motar ya nufota, saida ya kusa kawowa kusa da ita sannan ta ɗago ta kalleshi ta wani turo baki wai ita gamai fushi,
sai da ya zauna kusa da ita sannan yace “fushin mi kike Maryam?”
“wai Momi ce tace bazata je dani birni ba”
“tho ai hutunku bai k’areba kuma kinga aure za’ayi miki babu ma zancen komawa birni gaba ɗaya rayuwarki ta dawo nan kenan”
da sauri ta kalleshi “ni wlh ba zan zauna ba kuma ni bana son aure wlh bana son halilu”
da kuka ta k’arasa maganar,
saida Siraj ya duba yaga babu mai kallonsu sannan yace “in baki shawara?”
kai ta ɗaga mishi
yace “karki yarda a aura miki Halilu kinga ɗan k’auyene kuma duk wani abun daɗi da kikasan kinaci da kin aureshi kin daina cinsa kenan kuma kings babu ke babu karatu babu zuwa birni nan zakiyi ta zama kina daka da zuwa daji kina ɗebo kara shikenan kinyi bankwana da jindaɗi muma ba zaki sake ganinmu ba har Momi”
k’ara fashewa tayi da kuka da sauri ya rufe mata baki yana kallon k’ofa “shinnnnn kar sujiki kina son na baki wata shawara?”
nan ma kan ta ɗaga yace “koda an ɗaura miki aure da Halilu karki yarda ki zauna kice ke gurin mu kikeso kiyi ta musu kuka kice kesai an barki kinyi karatu in kikayi haka nasan za’a iya barinki ki bimu amman inba haka ba shikenan ba zaki k’ara jindaɗi ba kinji”
cikin muryar kuka tace “tho Gwaggo zanyiwa ko tsoho?”
“dukansu har Halilu kice indai yana sonki yabarki kije kiyi ta musu kuka kina murje² in kikaga sunk’i yarda sai kice ke sai kin kashe kanki….”
maganar yake yana wani kalle² kamar wani munafiki,
ita ko sai kai take ɗaga mishi, hannunta ya rik’o “Maryam kimin alk’awari komai akayi bazaki faɗa ni nace kiyi haka ba”
“nayi wlh bazan faɗa ba”
murmushi yayi “yauwa ai inma kika faɗa ɓatawa zanyi dake dan haka karki faɗawa kowa kinji share hawayenki”
hannu tasa tana share hawaye yana tayata saida ya goge mata fuska sannan ya rika hannunta suka shiga cikin gidan,

Story continues below

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*38*

biye² Momi tayi dan duk inda wasu ɗangi suke na kusa saida takai Siraj,
da shine bai san dangi sosai ba sai kusan magariba suka dawo gidan Gwaggo danyi mata sallama, tana zaune tana tuki tuwo suka shigo Mairo na genta,
“Assalamu alaikum” Momi ce tayi sallamar Gwaggo ta amsa mata “amin wa’alaikumussalam ku wayannan sai yanzu?”
momi tace “tho ya muka iya Siraj ne ai ya tsayarda mu yanzu kan ai sai kama hanya”
“a’a zaku tsaya kuci abinci kan”
Siraj yace “a’a Gwaggo k’ara mu wuce kawai bason tuk’in nan na dare nake ba koma can ai munci abinci”
tashi Gwaggo tayi tana faɗin “kai ai da yayanka daman bason cin abincina kuke ba Allah dai ya kiyaye hanya”
dariya yayi ya ciro kuɗi aljihunshi ya mik’a mata “ga daishi a siye goro”
karɓa tayi tana godiya nan ya sake sa hannu ya ciro dubi kusan 5 ya mikawa Mairo, k’in karɓa tayi idonta suka ciko da kwallah “a’a nidai zan biku bama son nan”
hannun Momi ta rike ta fashe da kuka,
lallasarta Momi ta shigayi “haba Maryam ki bari har hutunku ya k’are sannan kinji kinga ko yanzu tsoho saida yayi ta mana masifa akanki kinga in mukaje dake faɗa zaiyi”
“nidai kije dani haka inaso Momi dan Allah karki bari”
risinawa Momi tayi ta dafata “tho ya isa daina kukan haka kinji ki tambaye Halilu in ya yarda sai na aiko a ɗaukeki amman fa sai inya yarda da zarar ya yarda kisa a bugamin waya kawai zam aiko mota aje dake?”
lak’e kafaɗa tayi “a’a nidai kije dani yanzu dan Allah Momi”
kuka ta ringa rusawa tana k’asa tana sama duk sai Momi taji ba daɗi babu irin lallaɓar da basuyi mata ba amman ta k’iyin shiru,
har bakin k’ofa ta biyosu tana jan gyalen Momi, nan Siraj ya shiga lallaɓata shida Gwaggo ganin abun nata na gaskene, k’in daina kukan tayi nan idanuwan Momi suka koma kwallah. daker ta samu tayi musu sallama suka kama hanya,

”’*****”’
cikin dare suka iso gida bayan Siraj yayi parking Momi ta fito rai ba daďi ta nufi part ďinta
palour ta tararda Qasin zaune yana kallon k’ofar data shigo, gyara zamansa yayi yana faďin “sannu da zuwa Momi”
wani irin haushinshi Momi taji ciki² ta amsa mishi “yauwa sannu”
saman kujera ta zauna tana sauke gajiya, Qasin ya kalleta yace “Momi yau ina kukaje haka tun safe naga kun fita kuma sai yanzu ka kuka dawo lafiya dai ko?”
“lafiya kalau k’auye mukaje”
Siraj ne ya bashi amsa yana k’ok’arin zaunawa kusa,
Qasin yadda yaji gabanshi ya faɗi yaji bazai iya k’ara tambayasu wani abu ba tashi yayi yasa hannayensa aljihu yace “sleep tight Momi saida safe” bai tsaya jiran amsarta ba ya nufi k’ofa,
saida ya fice Siraj ya kalli Momi yace “gaskiya Momi Maryam taban tausayi sosai banji daďin da muka barota ba”
wani guntun numfashi Momi taja tace “tho ya muka iya tunda haka suka zaɓa mata kuma kasan indai ba Halilu ya aminceba ba zasu bari muzo da ita ba”
“eh ai naga haka amman ya kamata a masa magana ya barta ta dawo nan kamin ya kammala shirye² kinga ta ɗan k’ara samu illimi”
“tho ai sai yaga dama tunda yanzu shi zai aureta”
taɓe baki yayi ya tashi yana faɗin “saida safe Momi”
“Allah ya tashemu lafiya nima ai bari na shiga ciki nayi sallah”
har zai fice Momi tace “amm.. Siraj gobe ma ka shirya muje gurin hajiya na mayar mata da amsa”
murmushi yayi yace “In’sha Allah” ya juya ya fice,

”’*** *** ***”’
*_3:47pm…_*
wani uban ta gumi Hajiya ta rafka wadda ya rufe mata fuska da kuma hanci,
cikin yanayin damuwa Momi tace “Hajiya babu yadda zanyi ne na buga na buga sukace ina su sam bazasu chanja zaɓin ds sukayi mata ba babu yadda banyi ba amman suka k’i aminta wai tun tana k’arama mahaifinta yayi wannan alk’awarin na haɗasu aure dan haka su bazasu tada ba”
saida Hajiya ta sauke ajiyar a’zuciya sannan ta kalli Momi tace “kin kuwa faɗa musu wanene yake sonta?”
“hmm Hajiya babu abunda ban faɗa musu ba inma baki yarda ba sai ki kira Siraj kiji komai dan tare mukaje ke in takaice miki labari magagganu babu daɗin ji nima ai kamar kar naje sai kin gani”
kai Hajiya ta girgiza “ni yanzu bansan yadda zan cewa Yarima ba ba fahimta zaiyi ba kuma yanzu yana iya cewa inba ita ba saidai ya fasa aure”
Momi tace “ni wlh dama zaki ɗauki shawarata a nema masa wata tunda yan’matan ne gasu nan kuma kyawawa”
Hajiya tace “ai inda matsalar take yace yana so ɗin”
dafata Momi tayi “ki yarda dani Hajiya In’sha Allah wannan sai yace yana so dan babu abunda akeso ga ‛ya mace wadda Allah bai bata ba babu wadda zai ganta yace baya sonta ‘yar k’awata ce kawai ki bari mu haɗa shi da ita muga kuma abunda Allah zaiyi”
shiru Hajiya tayi kamin tace “tho yanxu mi kike ganin zance sa game da wannan yarinyar ta k’auye?”
“karki faɗa masa anyi mata miji dan inyaji haushin haka zai iya rufe mishi ido yak’i son wannan kawai ki bari inna kirata yaje ya ganta kinga in yace yana so sannan ki faɗa masa Maryam anyi mata miji kinga babu wani shan wahala nasan zai amince da wannan”
sosai Hajiya ta jidaɗin shawara daman mafita take ta nema,
da fira Momi ta jata sai kusan biyar ta baro gidan,

Story continues below

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*39*

*_K’AUYE…_*
tun tafiyar Momi Mairo bata kara walwalah ba duk tabi ta takura kanta kullum cikin kuka take tana kiran Momi duk tabi ta rame dan bata cin abinci ga ɗan banzan ciyon kai da take fama dashi wadda ya sakar mata zazzaɓi sanaɗin kukan da take, Gwaggo babu irin rarrashin da batayi mata ba har ta gaji ta zura mata ido,
yau ma kamar kullum tana zaune saman ta barma tana rusa kukanta data saba Halilu ya shigo,
tana ganinshi ta juyarda fuska ta k’ara fashewa da kuka,
saman tabarmar ya zauna yana bata hakuri. maimako tayi shiru sai abun ya k’aru Gwaggo ta tabe baki tace “aifa sai kayi ai duk kasan matsalar yarinyar nan ka barta taje birni kak’i ka dai riga kasan halin Mairo tun ba yau ba ba daina kukan nan zatayi ba dubi yadda duk tabi ta rame dan Allah ko abincin kirki bata ci amman baka tausayinta shiyasa mani nake tsoron auren nan naku wlh kar kaje can kayi ta gallaza mata daman ka saba”
Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kanshi,
_ba nida wata mafita sai wannan inhar na barta taje birni tho na rasata kenan dole ne na ɗauki shawarar Siraj dan itace kawai mafita agareni_
kallon Gwaggo yayi dake ta masa masifa yace “shikenan zan barta taje birnin amman sai in an ďaura mana aure ta tafi da aurena inma karatun zatayi taje tayi in yaso daga baya sai ta tare”
kafin Gwaggo tayi magana Mairo tace “da gaske halilu?”
kai ya ɗaga mata yana murmushin da baikai zuci ba “da gaske Mairo tunda naga kina son zuwa birnin”
k’ara matsowa tayi kusa dashi “yanzu ka yarda gobe naje?”
“a a sai an ɗaura aure”
“tho a ɗaura mana ni na ƴyarda a ɗaura sai naje”
bakinta Gwaggo ta buge ta kalli Halalu tace “indai har da gaske kake tho kaje ka sanarda tsoho duk abunda yace shikenan”
kai ya ɗaga “In’sha Allah haka za’ayi anjima zan sameshi mu tattauna”
da sauri Mairo ta rumgimeshi tana masa godiya,
fisgeta Gwaggo tayi ta jefar tana mata faɗa wai bata da kunya, Halilu kan daɗi yaji dan gani yake yanzu Mairo na sonshi tunda ta daina kukan aurenshi sai na a barta taje birni,

”’*** *** *** *** ***”’
cikin satin nan aka saka ranar ɗaurin auren, murna gurin Mairo ba’ah magana ko yar kunyar nan da yan matan k’auye suke yi ita batayi ba,
duk wadda yagani sai yayi zaton son Halilu take itakan bata ma kulaba murnar zuwa birni take, a’waya aka sanarwa da su Momi dama duk wasu dangi da suke nesa,
duk wannan abun da ake Qasin bai saniba dan ya daina zuwa part ďin Momi indai ba wani abun zaiyi ba Momi kuma ta fita sabgasar,
ana gobe ɗaurin aure Abbah ya dawo dan Momi ta faɗa masa ranar laraba za’a ɗaura,
*_2:45pm…_*
Momi na shirye² kaima Abbah abinci Qasin ya shigo rike da wata leda a hannu,
saman kujera ya dire kayan yana faɗin “gashi inji Abbah yace na kawo miki”
ba tare data kalleshi ba tace “shaddodin ne?”
“eh sune”
“ok barsu harna tashi amm ka shirya gobe zamuje ɗauri aure k’auye”
haka yaji maganar kamar wadda aka jefowa abu daga sama da k’arfi ya haɗeye yawu ya kalleta yace “auren wa Momi waza’ayima aure?”
tsayawa Momi tayi ta kalleshi “Maryam za a ɗaurawa aure amman bada kai ba da ɗan’uwanta Halilu”
a hankali ya kai zaune saman kujera “Momi ban gane abunda kike nufi ba?”
kusa dashi Momi ta dawo ta zauna tace “Qasin na fahimci baka son Maryam kuma kana tsoron matarka dan haka nake ganin inna aura maka ita na cilas maka na kuma shiga tsakaninka da matarka shiyasa nace musu ka yanje zancen nemanta su kuma sukace koda kai ko ba da kai ba su daman aire zasuyi mata dan haka suka zaɓa mata Halilu a matsayen miji gobe ne ɗaurin aurensu na sani ko ba yau ba wata rana kai da kanka zaka nemi k’ara auren”
kai ya girgiza baki na rawa yace “wlh Momi ina sonta Momi na shirya bin umarninki kodan na faranta miki miyasa kika yi haka ba tare da kinyi shawara dani ba haba Momi”
“aikin gama ya riga ya gama Qasin sannan banida tabbacin kana sonta ko a’a bazan iya kai Maryam gurinda nasan zata cutu ba inason ka shirya gobe ka halarci ɗaurin aurenta”
kasa ce mata kamai yayi ya tashi idonsa cike da hawaye jiki ba gwari ya fice.
da dare Qasin kasa bachi yayi haka yasa ya dawo parlour,
_tunani fal a ransa jin yake bai kyautawa Momi ba da kuma zuciyarsa dan harga Allah yana son Mairo saidai natsuwace bayaji a tare da ita haka yasa sai kuma yaji daďin yadda Momi tayi dan yana ganin hakan kamar mafitane a gareshi tunda yanzu tayi aure ai dole ya daina sonta_ juyawa yayi daga kwancen da yake, ya lumshe ido.

Story continues below

*_WASHE GARI…_*
tun 6 na safe Qasin yabar gidan, kuma ya kama duk wayoyinsa ya kashe,
haka su Momi da Abbah suka Kama hanya ba dashi ba Siraj dai inbanda dariya babu abunda yake yana faɗin wai Qasin kishi yake.

*_©Khadeeja Candy_*

candynovels.wordpress.com
[11/5, 9:43 AM] Khadeeja Candy 🍧: *♡… MAIRO …♡*

*BY*

*_KHADEEJA CANDY_*

*40*

*_K’ARFE 2:30PM…_*
aka ɗaura auren Mairo da Halilu babu laifi anyi taro saidai wasu yan’uwa na nesa basu samu halarta ba ango kan baki har kunne sai murna yake,
gudumuwa kan ya samu sosai musamman gurin Abbah.
ɓangaren Mairo ma farincikin ba baya ba dan ita zuwanta birni ne kawai a gabanta, da su Momi zasu dawo lak’ewa tayi sai ta biyosu daker aka samu aka lallaɓata bayan an aje ranar da Momi zata aiko a’je da ita.

”’*** *** *** ***”’
“miya hana ka zuwa ɗaurin auren nan Qasin?”
zaune yake saman kujera kansa a k’asa Momi kuma na tsaye kansa tana masa magana, a hankali ya ɗago kai ya kalleta yace “wani meeting ne mukayi da wasu chenis shiyasa na fita da wuri”
taɓe baki Momi tayi tace “tho Allah ya kyauta daman zancen karatun Nura ne inason ka nema masa admission a state University tun kamin lokaci ya k’ure”
“abun yana raina Momi nayi magana ai kuma In’sha Allah gobe zanje makarantar ma”
“Allah ya kaimu”
“Amin”
haka ya tashi ransa a jagule ya fice,

*_4 DAYS LETTER…_*
ruwan sama ake kamada bakin k’waya harda k’ank’anra,
Qasin na zaune parlour sanye da k’ananan, laptop na gabansa yana yan danne² sai cup ɗin drink dake gefen laptop ɗin. a hankali yaji ana shafashi ɗagowa yayi suka sakarwa juna murmushi “daman ba bachi kike ba?”
“a a idanuna huɗu baka jin sanyi dear kake zaune parlour?”
murmishi ya sake sakar mata “tho ya na iya so nake na k’are aikin nan kamin gobe dan-“
ihun daji yasashi kasa k’arasa maganar ya tashi da sauri ya nufi windo,
yana ɗaga labulen gabansa yayi wani dakan uku² ganin Mairo na gudu cikin ruwa tana son kama lema. kasa tantance abunda yake gani yayi mamaki ya rik’ayi yana tunanin abunɗa zai kawo Mairo gidan cikin wannan lokacin haka ya rik’a k’acce² wai ko idonsa ne suke masa gizo,
gani haka yasa Mansura ta karasa kusa dashi tana kallon windom tana ganin Mairo ta ɓata fuska ta taɓe baki “mts miye abun kallo gurin wannan mahaukaciyar ai daman ni nasan sonta kake”
juyowa yayi yana kallonta fuskarsa ɗauke da mamaki kwata² baya jin abunda take faɗi dan hankalinsa na can wani guri har ta k’are surutanta ta shige ko ɗaya kunnensa bai ɗauka ba,

*****
“gaskiya ni har yanzu sanyi nake ji sosai”
Mairo ce take maganar tana sanye da atamfa red colour da hijab tana saukowa downstairs,
Siraj dake zaune saman kujera ya kalleta yace “ai dole duk fa ruwan nan da akayi saman kaki suka k’are”
“tho ba lema naje kawowa ba sai suka jik’ani” “tho dan kinje kama lema sai akace ki tsaya cikin ruwa kiyi wanka?”
dariya tayi ta zauna saman kujera tana k’ank’anme jiki “kai kuma Siraj ba murna nake nazo birni ba saida fa nayi ta kuka sannan aka barni nazo”
rigar sanyin dake jikinsa ya cire ya mik’a mata yana faďin “ai naga duk kin rame k’arɓi wannan rigar ki saka”
saida ta k’arɓa sannan tace “kaifa?”
tashi yayi ya nufi stairs “bari na ɗauko wata”
kai ta ɗaga mishi ta shiga saka rigar,
takan mata yawa sosai saida kuma ta fitar mata da kyaunta sosai tana jan zip taji an buga k’ofa, da sauri ta nufi kofar tana buɗewa ta sako idanu “lahh Yarima”
“na’am pretty gal”
da murmushi ya amsa ya kai hannu ya shafa gefen fuskarta, sannan ya shigo.
hannunta ya rika suka nufi kujera Siraj na tsaye yana kallonsu da murmushi har suka zauna, sannan yace “ke Maryam tashi daga nan yanzu ba kamar da bane”
da sauri ta koma a ɗayar kujerar Yarima ya ɗago yana masa wani wulakantaccen kallo, can kuma ya ɗauke kai yana kallon Momi dake saukowa dwnstairs,
saida ta zauna sannan suka soma gaisawa “Yarima yau kaine a gidan namu da maraice haka?”
saida ya daɗe kamin ya bata amsa
“eh an faɗa min Maryam tazo ne”
mamaki ne fal a fuskar Momi “waya faɗa maka?”
“mutum…”
a takaice ya bata amsa yana kallon zoben hannunsa,
murmushi Momi tayi zatayi magana Siraj yace “Momi ya kamata yasan halin da Maryam take ciki yanzu Level ďinta ya chanja ba”
kallon Momi Yarima yayi alamar bai fahimci abunda Siraj ke faďi ba,
cike da tsoro Momi tace “Yarima…Marya…m fa yanzu ..matar..aurece.. satin da ya wuce aka ɗaura mata aure”
wani kyakkyawan murmushi ya saki wadda ya kara fitar da kyauwunsa yace “kidding me it’s funny Momi”
Siraj yace “ba wasa ake maka ba yanzu Maryam igiya uku ce a kanta in kuma kana shakku kaje ka tambayi Hajiya ko kuma ita Maryam ɗin gata nan”
kallon Maryam yayi dake kallonshi tana dariya da rufe fuska, ya sake kallon Momi kai Momi da gyaɗa mishi tace “wlh an ɗaura mata aure Yarima kaji kuma na rantse”
tashi yayi tsaye ya wani yarfarda hannu “ohhh Momi inma gwadani ne kike tho ki daina bazai taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa bari kiji na faɗa miki tunda hajiya ta haifeni ban taɓa neman abu na rasaba wht ever I luff is my nd my only inason ki rubuta ki aje Maryam tawa ce no mttr wht dan haka in so kike ki gwadani k’ara ma ki daina in kuma so kike ki aura mata wani tho ki janye wannan tunanin…”
yana kaiwa nan ya karkaɗe rigarsa ya fice,
lumshe ido Siraj yayi yana _k’arya kake Maryan tawa ce duk wannan plan ɗin nawa ne tunda har yayana baya sonta tho mine mijina ba kaina she s my_ a zuciyar yake wannan zancen yana wani lafiyayyen murmushi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *